Hausa Novels

Siyasa ; Dalilin Yasa Adam A Zango Ya Bar APC Ya Koma PDP

ME YASA ZANGO YA BAR APC?

Fitaccen Jarumin Finafinan Hausa Adam A. Zango, ya bayyana ficewar sa daga Jam’iyyar APC inda ya koma Jam’iyyar adawa wato PDP.

Jarumin, ya yi kira ga masoyan sa tare da sauran magoya bayan sa da su zabi Alhaji Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasar Nijeriya a zabe mai zuwa. Kafin komawar sa jam’iyyar PDP, Zango yana daya daga cikin mawakan da ke nuna goyon bayan su tare da yada manufofin gwamnatin Buhari.

Yau kusan kwanaki 4 kenan, wasu daga cikin mawaka da jaruman Finafinan Hausa magoya bayan jam’iyyar APC, suke zargin wani Fitaccen Mawakin Siyasa da yi masu sama da fadi da zunzurutun kudi wanda akalla ake tunanin za su kai naira miliyan 25.

Masu zargin na cewa an ba shi kudin a madadin su baki daya a ranar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zo Birnin Kano, amma sai ya rika daukar dubu dari dari, yana ba su. 

A ganin su ya zalunce su. Sai dai har yanzu Kafar watsa labarai ta ‘Kannywoodexclusive’ ba ta tabbatar da sahihancin zargin na su ba. Shin Zango ne kawai ya fice ko akwai sauran wadanda za su bishi a cikin mawaka da kuma jaruman Finafinan Hausa?

Akwai sauran bayanai ku biyo mu..

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button