Hausa Novels

Da dumi-duminsa : Kayi gaggawar sakin Dasuki da El-Zakzaky – Sheikh Gumi ya gargadi Buhari

Shahararren malamin nan na addinin Musulunci, 
Sheikh Ahmad Gumi yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta saki tsohon mai ba kasa shawara a harkar tsaro a mulkin Goodluck Jonathan, 
Kanal Sambo Dasuki daga gidan yari. Malamin Musuluncin ya kuma yi kira ga a saki Shugaban kungiyar yan uwa Musulmai na Shi’a, 
Sheikh Ibrahim Zakzaky. Sheikh Gumi wanda yayi rokon a yayin rufe Tafsirinsa na wannaN shekarar a masallacin Sultan Bello a ranar Lahadi yace gwamnati na bukatar bin umurnin kotu domin sakin mutanen biyu daga inda suke a tsare. 
Gumi ya kuma cewa babu wani fa’ida a ci gaba da tsare su tunda dai kotu tayi umurni kan a sake su. Yace ya kamata gwamnatin tarayya ta yi zaman sulhu tare da Sheikh Zakzaky maimakon tsare shi. 
“Anan Najeriya, zan so gwamnati tayi duba ga lamarin Kanal Sambo Dasuki sannan ta sake shi ba tare da bata lokaci ba. Sannan su kuma saki Shugaban Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky.
“Ba wai suna rike da shi (Zakzaky) saboda ya kasance dan Shi’a ko wani abu bane. Su sake shi sannan su tattauna dashi. Ya kamata gwamnati ta san cewa ba daidai bane rashin bin umurnin kotu. 
“Ya zama dole gwamnati ta zamo abun koyi ta hanyar sakinsu musamman Kanal Sambo Dasuki,” inji shi.
 SOURCES ; https://hausa.legit.ng/1241387-kayi-gaggawar-sakin-dasuki-da-el-zakzaky—sheikh-gumi-ya-gargadi-buhari.html

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button