Labarai

Wata Sabuwa:- Azumi shida (6) Bayan Ramadam Bidi’a Ne – Dr Ahmad Gumi

Shahararren Malamin addinin Islama dake garin Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya bayyana cewa azumin guda shida da Musulmai ke yi bayan kammala azumin watan Ramadana, a cikin watan Shawwal bai inganta ba, kuma bidi’a ne.
Gumi ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo daya watsa a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni, inda yace a fahimtar babban Malamin addinin Musulunci, Imamu Malik, Azumin Sittu Shawwal bai inganta ba, sahabbai, tabi’ai, duk basu yi ba

Shiga nan 👇👇👇 Domin kallon Videon.

Sheikh Ahmad Gumi ya karanto ruwayar wani magabaci da ake kira Yahaya wanda yace “Naji Malik yana maganan yin azumin sittatin na bayan an bude baki, yace bai taba ganin ma’abota ilimi da fikihu sun yi azumin ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button