Fatawa

Yadda Ake Sujjadar Karatun Al-qur’ani Da Hukuncin Wanda Yawuce Baiyiba ?!

*YANDA AKE SUJJADAR KARATUN AL-QUR’ANI DA HUKINCIN WANDA YA WUCE BAI YI BA ?*

*Tambaya*

Assalamu warahmatullah inaimaka fatan alkhairi sakon gaisuwa tamusamnan zuwa gamalam Tambayata itace yaya matsayin Wanda yake karatun Al Quran saiyazo wajen sujjada saiyawuce baiba yinhakan laifine kuma inza ayi sharadinta saida alwala kuma Sai ankalli gabas bissalam

*Amsa*

Wa’alaykumussalam
Jamhurun malamai daga cikin su akwai ma’abota mazhabobi uku wato malikiyya da shafi’iyya da hanabila duk sun tafi akan sujadar tilawa sunna ce ba wajibi ba, wanda yayi yana da lada wanda baiyi ba babu komai akan sa..
Duk da mazhaba ta hanafiyya sun tafi akan wajabci, amma zancen farko yafi inganci..

Jamhurun malamai daga cikin su akwai ma’abota mazhabobi hudu duk sun tafi akan cewa alwala sharadi ne na sujadar tilawa..
Imam kurdubi yana cewa: babu sabani cewa sujadar tilawa tana bukatar duk abinda salla ke bukata na tsalki, alwala, niyya, kallon gabas… Aduba tafsirin kurdubi 9/438

Amma wasu malaman sunce alwala ba sharadi bane na sujadar tilawa daga cikin wadannan malaman akwai shehul islam ibn taymiyya..sunyi riko da abinda imamul bukhari ya ambata cewa Abdullahi dan umar ya kasance yakanyi sujada ba tare da alwala ba… Aduba fatawal kubra 5/340
An tambayi malaman lajna sunce ana sujadar ko ba alwala aduba: fatawa lajna 7/263.
Kama ma sheikh bin bazz ya bada fatawa a cikin fatawar sa..
Da sheikh Ibn Usaimeen.
Imam Shaukani a cikin littafin sa Nailul Audaar 5/347 yana cewa : babu wani dalili a cikin duk hadisan mazon Allah da ke nuna akan cewa lallai sai me sujada ya kasance cikin tsalki/alwala..

Hakazalika fuakan tar gabas ba wajibi bane a sujadar tilawa..

Amma Sheikh Ibn Usaimeen yayi wata magana mai kyau a cikin littafin sa  fatawa warrasa’il mujalladi na 14 babin sallar tadauwu’i..yana cewa: “Abinda ya bayyana a gareni shine cewa mutum dai yayi kokari inso samu ne kada yayi sujada face yana cikin tsalki/alwala kuma ya fuskanci bagas domin hakan shi yafi dacewa wajen girmama Allah, kuma manzon Allah da kansan yana cewa yana matukar son kada ya Ambani Allah face yana cikin tsalki… “

Don haka in anyi alwalar kuma aka kalli gabas haka akafi so, in kuma babu damar haka toh ayi duk yadda ya saukaka..

Dan karin bayani a duba littafin (Taisirur rahmani fi Ahkamis sujudi tilawatil Qur’an na babban malami Assaam Abdu rabbihi)

Wallahu A’alam

*MALLAM NURUDDEEN MUHAMMAD (MUJAHEED)*

27/06/2019

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button