Fatawa

Shin Ko Za’a iya Saka Mutum Musulmi A Akwatin Gawa?!!

*MUSULMI ZAI IYA SIYAR DA AKWATIN GAWA ?*

*Tambaya*

Assalamu alaikum warahsmatullahi wabarakatuhu Mallam ya halarta Musulmi ya sai da akwatin gawa (coffin)? Allah ya saka da akhairi amin

*Amsa*

Wa’alaykumussalam
Malamai duk sunyi ittifaqi akan cewa rufe mutum cikin akwati (coffin) makaruhi ne.. Domin babu haka cikin sunnar manzon Allah da aikin magabata na kwarai, Saifa idan lalura ce karbabbiya a shari’a tasa sai an rufe mutun cikin akwatin.
Kamar yadda malaman lajna suka ce 2/312.

Don haka sayar da akwatin gawa irin wanda christoci suke rufe mutane da shi makaruhi ne, domin taimakawa ne wajen aikata makaruhi, bugu da kari yin haka ba aikin musulunci bane, aikin yahudawa ne kuma an umarce mu damu saba musu…

Wallahu A’alam.

*MALAM NURUDDEEN MUHAMMAD (MUJAHEED)*

28/6/2019

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button