Labarai
Nicki minaj tafasayin chasu a kasar Saudiyya
Shahararriyar mawakiyar nan ‘yar Amurka, Nicki Minaj, ta fasa yin wasan da za ta yi a makon gobe a kasar Saudiyya.
.
A makon jiya ne aka bayyanata a matsayin wadda za ta yi wasa a dandalin wani taron raye-raye na shekara-shekara a birnin Jeddah, abin da ya jawo suka a ciki da wajen kasar.
.
Ta ce goyon bayan da take nuna wa mata da kungiyoyin kare ‘yancin ‘yan luwadi da madigo a matsayin dalilan da za su hana zuwa kasar.
.
Yayin da wasu suke adawa da ziyarar da za ta kai kasar saboda yadda kasar ta yi kaurin suna wajen take hakkin dan Adam.
.
An shirya mawakiyar hip pop din ta Amurka za ta gabatar da wasan ne a bikin Jeddah World Festival ranar 18 ga watan Yuli da muke ciki.
#BBCHausa #BBCNewsHausa