Budurwa ta mutu garin kashe kwarkwara/keya
Wannan budurwar wadda ke yi wa kasa hidima a Najeriya (NYSC) ta mutu sakamakon amfani da maganin kwari na Sniper don kashe kwarkwatar da ke kanta.ðŸ˜
.
Hukumar NYSC reshen jihar ta tabbatar wa da BBC cewa Ayomikun Ademorayo ta mutu ne a ranar Lahadi.
.
Rahotanni sun ce ta sanya sniper din din a kanta ne don kashe kwarkwatar amma jim kadan bayan hakan sai ta fita hayyacinta.
.
Daga nan ne aka garzaya da ita asibiti inda ta mutu a can.
.
Hukumar NYSC ta ce ta sanar da dangin marigayiyar batun mutuwar budurwar.
.
Kawayenta da suke hidiimar kasa tare a jihar Osun sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da take kokarin kwance kitson da ta yi domin yin sabo don shirin bikin zagayowar ranar haihuwarta.
.
Sun ce sun yi kokarin ceton ranta, amma hakarsu ba ta cimma ruwa.
.
Marigayiya Ademorayo dai marainiya ce da ta rasa dukka iyayenta kuma tana da kanne da take kula da su da daukar dawainiyarsu.
.
Ta kammala karatun digirinta a Jami’ar Tai Solarin da ke Ijebu-Ode a jihar Ogun.
.
Maganin kwari na Sniper yana da matukar karfi sosai, kuma a baya-bayan nan ana samun rahotanni na karuwar yadda matasa ke amfani da shi wajen kashe kansu.
#BBCNewsHausa #BBCHausa