Labarai

Me Ya Kai Fatima Musa Yunkurin Kisan Mijinta A Kano?

Me Ya Kai Fatima Musa Yunkurin Kisan Mijinta A Kano? …kowa zai iya samun kansa a wannan mujarrabi… Daga Aliyu Usman Adam

A kwanakin baya wani abu da ya faru a Kano wanda Fatima Musa ta yi yunkurin kashe mijinta mai suna Sa’id Hussaini ta hanyar caka masa wuka a ciki wanda a yanzu haka yana kwance a asibiti.

Faruwar abun ke da wuya, sai ga ‘yan uwan Fatima Musa suna kokarin kare ‘yar uwansu da cewa ta yi yunkurin kare kanta ne saboda dukan da mijin nata yake mata. Har wasu a Social Media suke kokarin ba ta kariya da cewa an zalunceta, saboda yanke hukuncin abun da ba ka sani ba.

An yi hira da Sa’idu Haruna bayan ya fara samun saukin jinyan da yake yi, inda ya bayyana musabbabin matsalolin da kuma yadda ya kama matar tasa da hulda da wasu mazaje a waje har ya fada wa iyayenta kuma suna da masaniya a kan haka.

A gaskiya a wannan  lamarin akwai matsaloli ta kowani bangare wanda a nan ba muhallin a rika bai wa wani bangare laifi ba ne domin kuwa dukkan wannan lamari zai iya zama mujarrabi daga Allah kuma babu wanda ya fi karfin Allah ya jarrabe shi.

Bai inganta ta rika fadin duk abun da ka ga dama ba idan ka ga wani a cikin halaka ka roka masa Allah ya fitar da shi ta hanyar nema masa shiriya ba wai kawai ka rika fadin son ranka ba. Dukkanmu masu laifi ne sai wanda Allah ya shiryar. Kamata ya yi mu roki Allah shiriya ba wai mu rika zage-zage ba.

A sharhin da na karanta tun bayan faruwar wannan lamari wasu suna bai wa mijin laifi da cewa yana zaluntarta, wasu kuma na cewa ai ya san ba ta sonsa ya aureta, wasu kuma na bai wa yarinyar laifi ne da cewa tana bin maza. Wani ma ya alakanta faruwar wadannan abubuwa na samun sabani a tsakanin ma’aurata da wani magana da Sarkin Kano ya yi na cewa duk macen da mijinta ya bugeta ta rama.

A yanzu mu nemawa Fatima Musa shiriyar Allah da mu kanmu domin kuwa kowa na iya samun kansa a cikin wannan mujarrabi. Mu kuma sanya Sa’id Hussaini a cikin addu’a Allah ya ba shi lafiya. 🤷‍♂🤷‍♂🤷‍♂🤦‍♂🤦‍♂🤦‍♂ 🤷‍♂🤷‍♂🤦‍♂🤦‍♂🤦‍♂🤷‍♂🤔🤭🤐. More kallo kyauta a www.nishadi.tv

#nishaditv #drbabuhassada #arewa #matasa #hausa #hausabride #hausafulani #hausawedding #hausawedding #arewabride #arewapeople #arewafashion #arewawedding

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button