Labarai

Mutum 5 da Arzikinsu yafi kasafin kudin Nigeria

Wani rahoton da kungiyar agaji ta Oxform ta fitar ya bayyana irin mummunar tazarar da ke tsakanin masu kudi da talakawa a yankin Afirka ta Yamma.
.

Rahoton ya ce masu kudin yankin guda 10 sun fi kasashe 16 na yankin arziki. .

Oxform ta ce kasashen Afirka ta Yammar na asarar akalla dala biliyan 9.6 a kowacce shekara ta hanyar dage haraji ga kamfanonin kasashen duniya.
.

Irin wadannan kudaden, in ji rahoton, za a iya amfani da su wajen gina asibitocin zamani guda 100 a kowace shekara a yankin.
.

Najeriya ce ta fi kowacce kasa arzikin man fetur a Afirka, amma ‘yan kasar da dama na fama da zazzafan talauci, wanda ake alakantawa da cin hanci da rashawa da rashin adalcin shugabanni.
.
Masu arzikin Najeriya

Rahoton Oxform ya ce mutum biyar masu arzikin Najeriya da arzikin nasu ya kai dala biliyan 29.9, ya yi wa kasafin kudin kasar na shekarar 2017 shal wanda ya kama naira tiriliyan 7.29, kwatankwacin dala biliyan 23.97.
.

Jaridar Forbes ta wallafa sunayen mutum biyar ‘yan Najeriyar da suka fi arziki a kasar kamar haka:

Aliko Dangote

Mike Adenuga

Abdul Samad Rabiu

Folorunsho Alakija

Femi Otedola

#BBCNews #BBCHausa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button