Labarai

Kotun Kaduna Zatayi Zama Domin Duba Yuyuwar Barin Zakzaky Fita Kasar Waje Neman Lafiya!!

Gobe Kotun Kaduna Za Ta Yy Zama Domin Duba Yiyuwar Barin Zakzaky Fita Kasar Waje Neman Lafiya
Daga Bilya Hamza Dass

Babbar kotun Jihar Kaduna ta bayyana gobe Alhamis (18 ga watan 7 2019), domin zaman kan duba yiyuwar barin Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa su fita waje domin neman lafiya. A zamammakin karshe da akayi ne shugaban Lauyoyi masu kare Shaikh Ibraheem Zakzaky ya karanto wata takarda a gaban kotu wanda ke bayyana neman bada dama daga kotun ga Sheikh Zakzaky da matarsa su fita kasar waje domin neman magani kasantuwar yanayin jikin nasu.

Shaikh Zakzaky dai ya kasance yana fama da rashin lafiya mai tsanani na matsalar gefen jiki. Bugu da kari, har yanzun nan a kwai kwanson arsasai a jikinsa da dama shi da mai dakinsa wadanda har yanzun nan ba a cire su ba kaman yanda Likitoci suka bayyana a bincikenan da sukayi kwanakin baya. Zaman da Kotun za ta yi a wannan makon mai zuwa, ranar Alhamis 18 ga watan Julin nan, na yiyuwar barin Shaikh Zakzaky ya fita waje, harwayau ya kunshi sakamakon shawarwarin da Likitoci suka fitar bayan sun duba shi a watan Aprilu. Kwararrun Likitocin sun bayyana hatsari dake a kwai na ci gaba da tsare Malamin ba tare da anyi gaggawar fitar da shi waje ba domin ya nemi magani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button