Hausa Novels

Sojan Nigeria ya maayar da Naira Miliyan 15M daya tsinta

Rundunar sojan saman Najeriya ta ce wani jami’inta ya mayar da makudan kudi naira miliyan 15 kwatankwacin (Yuro 37,000; $41,500; £33,300),da ya tsinta

Bashir Umar na cikin Tawagar Kar-ta-Kawana ta Mayakan Sama ta rundunar wadda aka aike zuwa filin jirgin sama na Kano da ke arewacin Najeriya domin tsaro.

A wata sanarwa da ta fitar rundunar sojin saman ta ce Bashir na tare da wani abokin aikinsa ne suna sintiri yayin da ya tsinci damin kudin.

Sai dai maimakon ya danne kudin, rundunar ta ce sai jami’in ya duba jikin takardar da kudin ke nade a ciki inda ya ga lambar wayar mai kayan, ya kuma kira shi.
.
A yanzu dai rundunar ta ce za ta saka wa jami’in don a kara wa sauran jami’ai kwarin gwiwa kan kamata gaskiya. Sai dai ba a yi bayanin irin sakamakon da za a yi masa ba.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da jami’ai masu kamanta gaskiya suke mayar da abin da suka tsinta a filayen jiragen saman Najeriya ba.

A watan Agustan bara ma, hukumomi a filin jirgin saman Legas sun karrama masu gadin wajen biyu, wadanda suka mayar da makudan kudi da abubuwa masu tsada da suka tsinta.

Haka ma a watan Satumba, an jinjinawa wani mai share-share kan mayar da wasu kayayyaki masu tsada na wani fasinja da ya yi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button