Labarai

Labaran duniya : boris Johnson ne sabon fitaiministan Birtaniya A Yanzu!

Jam’iyyar Conservative ta Burtaniya ta zabi Boris Johnson a matsayin sabon shugaban jam’iyyar Conservative inda zai zama sabon Firaiministan kasar.
.

Mista Boris ya yi nasara a kan abokin takararsa, Jeremy Hunt bayan samun kuri’u 92,153 fiye da 46,656 da Jeremy Hunt din ya samu.
.

A ranar Laraba ne dai Boris Johnson zai karbi ragamar shugabanci daga hannun Theresa May.
.

A jawabin da ya gabatar bayan an bayyana shi da wanda ya yi nasara, Mr Johnson ya yaba wa Theresa May inda ya ce ” Abin alfahari ne yin aikin da na yi a gwamnatinta”. #BBCHausa #BBCNewsHausa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button