Fatawa

Hukuncin Yin Azumin Arfa A Ranar Asabar – Sheikh Aminu Ibrahim daurawa

HADISI YAZO YANA HANI GA YIN AZUMIN RANAR ASABAR, IDAN BA AZUMIN FARILLA BA.
HADISI YAZO YACE KADA AYI AZUMI RANAR JUMAA KAWAI, SAI IDAN ZAA HADA DA ALHAMIS KO ASABAR,

MALAMAI SUNCE BABU LAIFI AYI AZUMI RANAR ARFA, KA RANAR ASHURA DA TASUA DA KWANAKIN HASKE WATO RANAR 13, 14, 15, IDAN YA FADO RANAR ASABAR,

DOMIN BA DOMIN ASABAR AKAYI AZUMIN BA, KUMA HAKAN BAI SABAWA HANI GA YIN AZUMIN RANAR ASABAR BA.

WANDA YAYI AZUMIN ARFA RANAR ASABAR BA DOMIN ASABAR YAYI BA. YAYI DOMIN ARFA,

AMMA SHAIK MUHAMMAD NASIRUDDEEN ALBANI YACE BA ZAAYI BA IDAN YA DACE DA RANAR ASABAR, AMMA WANNAN MAZAHABAR CE DA RAAYINSA DA FAHIMTAR SA.

WANDA YA GAMSU DA FAHIMTAR SA KADA YAYI, WANDA KUMA YA GAMSU DA FAHIMTAR SAURAN MALAMAI DA HUJJOJINSU.
SAI YAYI BABU MATSALA FAHIMTA FUSKA CE,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button