Labarai

Duk Wani Mataimakin Shugaban Kasa Da Akayi A Nigeria Lalatattu ne Amma Banda Atiku Inji Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa babu mataimakin shugaban kasar Najeriya da aka taba yi wanda ya samu dama yayi aiki irin na shugaban kasa kamar Atiku Abubakar.

Obasanjon ya bayyana hakane a wajan wani taron kasuwanci da ya gudana a jihar Legas, Yau, Laraba,

Ya kara da cewa a lokuta da dama Atiku ya jagorancin zaman majalisar koli lokacin da suka yi mulki tare. Ya yiwa shugaba Buhari da ya shafe kwanaki 104 a kasar Ingila shagube.

Inda yace amma abinda zai sa wasu zasu ga kamar be sakarwa Atiku mara yayi aiki sosai ba shine saboda shi be taba yin tafiyar da ta daukeshi kwanaki 104 baya kasarnan ba.

Yace Atiku ya samu horaswa daga gurinshi sosai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button