Matsalolin da Cutar Sanyi Take Haifarwa Maza da Mata
MATSALAR DA WANNAN CUTA TAKE HAIFARWA GA MATA DA MAZA
1. Matsalar rashin haihuwa ta hanyar kassara kwayoyin da ke Samar da ciki, sai kaga mace ta qi haihuwa.
2. Tana haddasa wani ciwon ido me suna (Opthalmia Neonatorum) ga jarirai, Wanda mace me ciki kan iya gogawa yaro ta hanyar fitowarsa ta farji, tunda dama nace cutar tana zama a mafitsara da sauransu.
3. Tana sa zubar chiki/6ari.
4. Raunin qarfin mazaquta da zubar farin ruwa.
Tabbas ciwon sanyi na mata da maza babbar matsala CE ga rayuwar dan-adam, har ma takan yi barazana ta fuskar auratayya. sannan ita wannan cutar takan kamata wasu daga cikin sassan jikin mutum. Nah sha jin wasu masu tallen maganin gargajiya;
suna ta yada qarya da qarerayi cewa: wai ciwon sanyi, sanyine na qorama, ko na ruwa, ko na damshi. Wai shi ke haddasa wannan ciwo na sanyi (INFECTION),
Wanda kuma ba haka bane, qarya suke yi, suna fadan hakan ne kawai domin kasuwancinsu ya yi armashi ga jahilai wadanda basu sani ba, domin kai daga jin irin wannan talla kai ka San babu bincike a cikin tsarin.
Suna yada jita-jita ne kawai labarin qanzon kurege, kuma Allah zai iya kamasu da laifin yada qarya a kan abinda basu yi bincike a kai ba.
Ita dai wannan cuta ta sanyi (Wato Infection) akwai hanyoyin da ake daukarta kamar haka.