Gyaran Jiki

Micece Cutar PID da Kuma Yadda ake Maganinta

MECECE CUTAR P.I.D KUMA YA TAKE

Wato P.I.D wata nau’in cuta ce dake kama mahifar mata kadai, sakamakon yaduwar kwayoyin cutar bacteria na saduwa wato S.T.I (sexual transmitted infection), a hausa kwayoyin cuta da ake dauka ta hanyar saduwa, ita wannan cuta tana faruwa ne sakamakon faruwar cutar sanyi ta ghonoria, (wato cutar da ake dauka ta saduwa ba ta sanyi na yanayin gari ko na ruwan sama ba). Ko kuma cutar chlymidia, ko candidiasis, da sauransu, Wadanda sukan rayu ne a waje me danshi kmr mahaifa da farjin mace.

Related Articles

to idan su wadannan cutar misali ta ghonoria mace na dauke da ita sannan ba’ayi maganinta ba, to takan yadu ta bar farjin mace sai ta gangara mahifa, sai ta illata madaukan mahaifa ko (pollofian tube) ko kuma ta illata ita kanta mahaifar ko kuma ta illata su kwayoyin haihuwar mace(ovarries).

To sakamakon tashi da tayi daga farji zuwa mahifa to tabar nau’in kwayoyin cutar saduwa ta koma P.I.D. Daga nan se mace ta fara jin wadannan alamun\

 

1. zafi yayin fitsari ko kuma yin fitsari dan kadan.

2. Zazzabi

3. Zafi yayin saduwa(sex)

 

4. yawan yin al’ada cikin wata takan iya yi sau 2-3

5. fitar farin ruwa marar dadi me wari.

6. Ciwon mara

7. Idan yayi karfi yana hifar da ciwon baya me tsanani

 

Sannan idan suka jima ajikin mace sukan haifar da 6arin ciki,(misschariage)rashin haihuwa (infertility) da sauransu. Sbd haka wadan nan sune alamomin cutar ta p.I.d sannan wasu matan ma bazasu ji wadannan alamun ba musamman idan cutar chlamydia ta haifar da shi P.I.D din.

Babban hanyar kariya shine

 

1.Da zarar anga kuraje ko anji kaikayi ko fitr farin ruwa a farji a garzya anemi magana Dan ciwo babba Ba karami

2. Mata su dena saka pant me lema sbd su kwayoyin cutar irin su candida albicans su suna alaka da damshi ne se su shigi mace su kawo mtslr

 

3.A rinka sanin yanayin da za a sadu da namiji ba saduwa da maza barkatai ba masu neman mata.

4. A kiyaye yin madigo (lesbin) sbd ana saka cutar ta dan yatsa wajen fingering da sukeyi

5. A rinka tsaftace inda ake fitsari ko da garin gishiri ko isol ko da ruwa kamun ai fitsari

6.Sannan a dena saka dan yatsa a farji ba tare da an tabbatar da tsaftar yatsan ba dan shima yakan saka cutar D.S.S. in yatsan ba a wanke yake ba Dan wlh ayanxu bbu abinda yapi damun Mata

Kamar wannan ciwo dolene ya sa iyayena mata ku tashi ku nemi magani a inda ya dace a kuma gun Wanda ya dace, Domin ku kare kanku Daga wannan ciwo. P.I.D.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button