Minene Ciwon Sanyi (Infection)
CIKAKKEN BAYANI A KAN CIWON SANYI NA MATA DA MAZA (INFECTION) DA KUMA HANYAR MAGANCE CUTAR GABADAYA DUK TSANANINTA DA YARDAR ALLAH!
Fita ta daya
A yi hakuri a bi rubutun nan a hankali a karanta shi a nutse domin an gama duk wani bayanin ciwon sanyi Rankatakaf a cikin wannan Rubutu Har bayanin yadda ake hada maganin gabadaya an yi bayani tun daga Fita ta har zuwa fita ta a hade a gu daya cikin wannan Rubutun kawai dai akwai bukatar me karatu ya ankare cewa in ya zo karshen rubutu zai ga an rubuta read more da kalar shudi wato Blue a 6arin dama,
hakan na nufin ka dangwala yatsa a kai zaka ga ka kara budo Sauran bayanai, haka zaka yi ta yi a kowanne karshen bayani da ka ga read more har sai kaga ka zo karshen karatu amma baka ga read more ba toh shine yake gwada maka cewa: Rubutun ya kare Kenan.
MENENE CIWON SANYI (INFECTION)
Amsa:
Ita cutar ciwon sanyi wata kwayar cuta CE ta bacteria ke haddasata, wacce turawa suke kiranta da suna (Neisseria Ghonorea), sannan ita wannan cuta tana rayuwa ne a waje me damshi a jikin dan-adam mace ko namiji. Ba wai don an kirata da ciwon sanyi hakan yana nufin sanyi na yanayin duniya ke kawota ba! Ah a an kirata da ciwon sanyine sbd ita cutar gun jiqa/damshi take zama a jikin DAN-ADAM. Misalin inda cutar take zama:
1. Farji=farjin mace wani kogo ne da baya rabuwa da jiqa/damshi, shiyasa da zarar cutar ta shiga ciki sai tayi wahalar fita ko warkewa.
2. Mahaifa/mafi tsara=duka wadannan wurare basa rabuwa da damshi.