Hausa Novels

Kishi ko Hauka Hausa Novel

🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
KISHI KO JAHILCI

Story & written
By

Related Articles

Ummu Ameer💃

Short story

Page1⃣

Mata ne cike d falon ana daga kayan lefen d aka kawo, sai faman shewa d guda ake tare d yabon kayan d aka kawo, domin kuwa kaya ne n gani a fada, naira tayi kuka anan, duk wani abinda ke ciki ba na banza tun daga kan sutura zuwa sarkoki mayukane abindai sai wanda y gani, yan uwa d abokan arziki n fadin Amarya tayi goshi, Ana t sanya Alkhairi d fatan Allah y nuna mana ranar biki, can bangaren kuwa amarya ce cikin daki tare d kawayenta sai xolayarta suke daya daga cikinsu mai suna hafsa tace matar mutum kabarinsa, Aysha ba irin wulakancin d bakima Abbas ba y jure kamar karamin yaro lallai y cika jarumin maza gashi nan ynx y kamaki a hannu ta kare maganar ta sigar zolaya t dan bugi Amaryar acinya, ita dai kawai murmushi tai, a zuciyarta kuwa Allah Allah take bakin d suka zo karbar lefen su tafi take domin t ganewa idonta kayan d kawayenta suke t zuguguta wa ankawo mata.
Ita kam uwar amarya sai wani cika take tana batsewa tare d wurgawa kayan muguwar harara ita a dole kayan basuyi mata adalilin rashin sanya sisinan gwal, kasancewarsu yan bidiri wayo ‘yan maiduguri, Anty salma ce ta matso kusa d ita tai mata rada a kunne tace mata don Allah Anty kiyi hakuri ki saki fuskarki a gaban jama’a ne fah, kar ki ba da mu plx.. Kuma m ai bawan Allah nan yai kokari daga baya ai sai ai mishi magana. Sai alokacin t dan sakin murmushin d bai zuci ba, inda aka shiga tattare kayan ana maida su cikin akwatinan, har mutane suka fara watsewa cike d yabon kayan, y rage daga anty salma sai d kakar Amaryar wato uwar Amaryar d kannen amaryar a wurin, kawayen Amarya kam uwa jira suke su watse suka fito aka sakw baje kayan suma suna t santin lefen tare s Amaryar itama sai washe baki take tana duba kayan, inda kakar tace “OH ni hauwa yaran zamani ynx d ke ake duba kayan naki Rukayyah”
Goggo nikam kin sa min ido da yawa zamaninku da bamu ai ba daya bane, ko kishiru kike ne da kaya ta kare maganar d yi mata gwalo tare da mikewa ta ruga Daki a guje tana dariya, goggo tace ja’ira da kin tsaya sai na koya miki hankali.

Nan dai aka tattara kaya aka maida su cikin akwatunansu, mommy kuwa tashi tayi tabi Rukayyah Daki, ta sameta suna waya da Abbas, Rukayyah kuwa ganin yanayinsa mom din nata yasa ta saurin katse wayar tace masa ‘sorry I will call you back”
Ta cire wayar daga kunenta, ta tattara nutsuwarta Ga mom wacce ke ta jifanta d harara, tace momy Lfy kuwa,? Bansani ba ta bata amsa a gajarce, ina so ki gaggauta kiran Abbas kice ina son ganinshi!
Mommy me y faru ne don Allah?
in yazo kyaji a wajensa, Tunda na fuskanci kina neman xubar d darajarki a wajensa Tun kan ki shiga ciki gidansa, komai yayi a wjenki daidai ne kin Dora wa kanki son mai mata, sai Kace kin rasa masoya ne, ta juya ta fuce daga dakin.

Rukayya kam doguwar ajiyar xuciya ta sauke tare da fadin, mommy ban san ran da zata canja ba, bawan Allah nan kullum cikin mata biyayya yake kamar ita ta haifeshi amma bata gani?

Daukan wayar tayi tai dialing no shi, “hello”
Baby mommy tace tana son ganinka plx…
Ok insha Allah zanxo bayan magriba, ok sai kazo bye! Ta katse wayar.

 

Ku biyoni don jin yadda zata kasance…..

By ummu Ameer💃

🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀KISHI KO HAUKA

Story & written

By
Ummu Ameer

Short story:

Afuwan ‘KISHI ko HAUKA’ ne nai mistake a page 1

 

 

Page 2⃣

 

Rukayyah zaune gabab dressing mirtow tana make-up, ta gama kwalliyar tana Yana mayafin abayar da ta saka ta dauki turare ta feshe jikinta da shi,tayi kyau ba laifi simple make-up tayi dake ita Bata cika son kwalliyar fuska ba in ta shafa powder ta dan saka lip glow a lebenta shikenan ta saka flat shoe, wayar ta ce Tai ringing sunan da ta gani a fuskar wayar ne yasa saka ta sakin murmushi, ‘babynta’ ta daga wayar tare da fadin gani Nan fitowa” baby”!

 

Dakin momy ta wuce direct domin sanar Mata da cewa Abbas ya iso, sallama tayi tare d tura kofar, Nan ta sameta tare da wata kawarta Anty batula, rukayyah ta gaishe ta sannan tace Mata “momy Abbas din ya zo!
Ok! Kije ki shigo da shi falo ganinan zuwa..
Ok, ta Bata amsa tarr da fita zuwa wajen bakon nata,

 

A hanyarta ta fita ne ta hadu da kaninta wato junior tace junior “zo ka raka ni, a guje ya karaso yace Anty uncle Abbas ne yaxo tace “ae”
Nan ya hau murna domin yasan duk sanda zaizo sai ya kawo Masa tsarabar kayan kwalama su chocolate, ice cream, f dai sauransu.

Tun dosowarsu wurin kamshin turarnsa y mamaye farfajiyar da kamshi.
Sallama Tai masa tare da sannu da zuwa, ya amsa cikin farin ciki tare da riko hannu junior,
Uncle Ina wuni!
Lfy lau junior ya su momy?
Lfy!
Ya bashi amsa yace to ga tsarabar ka Nan,
Ya amsa tare da fadin
Thank you!

To maxa ka shiga cikin gida, ganinan shigowa,
Ya ruga a guje.

Allah yasa Masa son yara, Abbas don ko a gidansa in ya dawo haka yara zasu xo suna ta amsa tsarabar sweet ko capri-sonne.

Ya tatttara nutsuwarsa ga gimbiyar tasa, my luv! Ina fatan dai lfy ko when momy, ta bashi amsa da cewa lfy lau, tace dai tana son ganinka ne,
Ok!
Tace Kaya fa sunyi Allah y Sanya Alkhairi ya Kara budi,
Ameen-Ameen,
In Akwai abinda Bai yi ba sai ki fada acanxo Miki,
A’a wlh komai yayi Allah y saka d Alkhairi,

Yaji dadin yabon kayan da tayi domin yasanta da yaba kyauta gata d kawaici
Kazo mu shiga momy tana jira, Tai masa jagora izuwa falon, yana biya d ita.

Can dakin kuwa momy da Anty batulu, sai xuga momy take akan irin rashin mutumci d zataiwa Abbas,akan rashin cika Alkawarin saka sisin gwal a cikin lefen, har tana ce mata wlh indai bazai saka ba kice sai dai yaxo y kwashe lefensa domin ko bashi ne kadai namiji a duniya ba ehe,
Momy tace hmmm! Bar ni da shi zai gane kurensa tare d daukar mayafinta tana Shirin fita zuwa wajensa,

 

A zaune ta sameshi a kasan carpet, ta Sami daya daga cikin kujerun ta zauna Tai kicin-kicin da ita,
Momy Ina wuni!
Lfy !
Ta amsa Masa a gajarce!
Dama na Kira ka ne akan lefen da aka kawo, Raina yayi matukar baci da rashin ganin sisin din gwal da na fada was rukayyah ta Gaya maka tsarin mune duk sanda za’a kawo lefe y Zama dole a saka shi ciki, Amma ka tashi k kawo lefe ba tare d ka cika Al’adar muba, ba lallai ba dole in kaga Abin yai ma tsauri to ka iya kwasar kayanka domin ko ba Kai kadai namiji ba,

Subhanallahi!
Momy kiyi hakuri ya furta hakan cikin ladabi, wlh Bata gaya min ba,ai da an saka aka saka sarka ma balle sisi, kiyi hakauri insha Allahu xa’a kawo gone insha Allah!

A zuciyar ta ko ta cika taf da mamakin wanna diyar Tata kwata-kwata ta yi nisa a son wanna mutumin da ke da Mata, ko me ta gani oho!

Doguwar ajiyar zuciya ta ta tare da ce Masa ka iya tafiya,
To godiya nake momy a tashi lfy.
Ya tashi,ya fita
Ita ko bin bayansa Tai cike da tsana, ita dai Bata kaunar Abbas tun da yazo neman auren diyarta don kawai Yana da mata, acewarta ita Bata da kishiya sai diyarta zata je ta tarar da kishiya, don aurenma ba’a son ranta ta yarda ba fin karfinta ne kawai akai.

Ta tashi ta Mike don komawa daki wajen kawarta.

Tana shiga ta sameta a kishingide ya kukai sis?
Dake haka suke Kiran juna.
Ke dai Bari wlh yarinyar Nan fa in banyi da gaske ba wlh sai ta tixartani a idon jama’a,
Ashe wai Bata gaya masa.
Ah lallai sai kin you da gaske Alan rukayyah domin na fahimci tana da shegen taurin Kai,

Amma yace gobe za’a kawo.
Yafi Masa ai indai Yana son aurar diyarmu!
Cewar Anty batulu,

Anty batula Aminyar momyn su rukayyah ce, bazawara ce, tayi aure ya Kai sau hudu ta kasa Zama gdn Miji, kasancewarta mace Mai son Abin duniya gata da munafurci ga hassada Bata son ta ga wani ya fita ki kadan, ga yawo Bata iya Zama waje daya, kusan kullum tana gidan momyn, Tai ta kitsa Mata mugayen halayya.

Rukayyah ki tun da ta fito wajen Abbas taga yanayinsa ya canza, axiciyar ta tace, na bani, ni rukayyah ki me tace Masa oho!
Ta karasa wajensa a sanyaye tace har ka fiyo?
Na fito!
Amma Ina fushi dake
Me nayi Kuma ta tambayeshi cikin sanyin jiki.
Momy ta Baki sako ki gayan kafin akawo Kaya Amma Baki fada min ba.
Why?
Shiru Tai na Dan secondAm bashi amsa da Kai hakuri na manta ne shiyasa.

Kinga ran momy y baci, Amma nace za’akawo gobe.

Zan wuce ni ynx in kin shiga ciki ki Kara Bata hakuri, kinji my luv!
Gyada Masa Kai tayi ,
Ya bude motar zai shiga ya tsaya Yana dan kallonta yaga kamar fushi take, me y faru ne luv! Naga kin canxa, bashi amsa Tai cikin shagwaba ba Kaine xaka tafi daga zuwa ba,
Sorry my luv! Wlh akwai uxurin danake da shi ne shiyasa ai goben zan dawo tunda yau Kinga zuwan momy ne ko ta gyada Masa Kai
Tace bye!
Sai da safe baby, Allah y tsare
Ameen!
Ki kularmin da kanki
Insha Allah suka rabu cikin kewar juna tana daga Masa hannu.har ya fuce daga gidan.

Ta juya domin komawa cikin gida Amma a xuciyarta ranta ya baci akan abinfa momy tayi, kuma tasan wanna munfukar matar ke zugata, ta shige dakin su, tana shiga ta Sami kanenta biyu Aisha da zainab, suna hira,
Anty rukayyah lfy Naga ki haka kuwa cewar Aisha dake sunfi kusanci da ita Kuma ko wane matsala tare suke sharing sun shaku da juna sosai,
Tace momy ce fa tasa na Kira Baby, akan zancen sisin gwal da ta fada na Gaya Masa Ana sawa alefe, shine da Bata gani ba tasa aka kirawo shi, Kuma Ina sane naki Gaya Masa ai tunda shi ba Al’adar mu daya da shi ba.
Aisha tace da kin sani kema kin fada tunda kin San hakin momy, Kuma don dai Bata son auren kune,Amma kiyi hakuri kiyi ya addu’a Kuma kiyifatan rabuwa d ita lfy,
Nan dai sukai ta hirarsu ta yan uwa.

 

 

Ki biyo ni domin sanin wacece Rukayyah
Da Kuma Abbas?

By
Ummu Ameer💃

🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
KISHI KO HAUKA

story & written

By

Ummu Ameer💃

 

Page 3⃣

 

Wacece Rukayyah?

Rukayyah diya ce ga Alh usman, Alh Usman mutum ne Mai karamci da sanin mutumcin mutane yana da hakuri gashi da tausayi.

Matarsa daya wato Haj. Binta wadda suke Kira da momy, wacce Tai karatun degree dinga a ABU Zaria inda ta karanci mass “communication” mace Kuma duk anan gdn Alhaji Usman Tai karatun, kasncewarsa mutum ne Mai son karatun ya Bata damar yin kartunta agdnsa har ta kammala a lokacin suna d yara uku, ta farko Rukayyah, sai Aisha, sai zainab sai junior shine karaminsu, mai sunan Baban momyn ne wato mallam Abubakar.

Momy mace ce mai fadin rai gata da hangen rayuwar wasu ita kullum gdn wane sunyi kaxa grn wance sun you kaxa, a kullum Raina rauuwat da take ciki takeyi, Alhalin ba abinda ta rasa, a gidanta.

Wannan yasa ta burin tana gama karatu aiki zata Fara yi.

Alh. Usman ko Yana aikin banki ne, Kuma Yana da rufin asiri, ba abinda suka nema suka rasa, mutum ne Mai kyautatawa iyalansa ko da ace shi zai takura ne,

Yana hakuri sosai da halin momyn, ko kadan Bata raga Masa a matsayinsa na mijinta.
Sai dai shi Kuma ya Sha alwashin bazai barta tayi aiki ba.

Ya saka yaransa a makarantu masu kyau da teada domin shi indai akan karatun yayansa sai dai inda karfinsa ya Kare.

Rukayyah ta gama kartunta na sakandire,ynx haka tana level 200 a buk.
Sai Aisha inda take s.s 3
Sai zainab tana j.s 3
Sai junior dake primary 1

Momy Yar Asalin garin maiduguri ce haifaffiyar maiduguri, lokacin da Alh.Usman yaje service din shi ne suka hadu har Allah yasa ya aure ta , Shima lokacin auren nata ba karamin wulakanci ya Sha ba gurin danginta don wai su Basu cika son aurawa bahaushe ya’yansu ba haka dai sukai ta bujiro Masa d Al’afinsu, ya jure duk wani bidi’oinsu har akai bikin nasu, ba don sun so ba, kasancewar ita da ta dage akan lallai shi takeso. Kuma baburawa ne daman.

Gashi in ta Fara bala’i kamar da rashin mutunci Abin ba dadi. Ki ya’yan nata tsoronta suke kamar me, rukayyah ce ma da Bata cika shakkar ta ba irin cin fuskar da take wa mahaifinta in ta tashi yi ko gaban wa aye Bata shakkah.
Hakan tasa rukayyah ranta ke matukar baci da halayar mahaifiyarta.

Kuma Bata fiye shakkarta ba kamar sauran yaran, ita sai dai suna da way halayyah guda:
In ransu y baci dikkansu kamar ba su ba misali ko fada y hada su da wani ko makamancin haka, Amma a zahiri suna d fuskar Kamala da hakuri a fuska Kuma ba laifi suna da tarbiyyah dai dai gwargwado.

Rukayyah sun kwashe akallah kusa da shekaru uku suna soyayyah da Abbas, tun tana ajin karshe a secondary, suka hadu, ta dalilin wata kawarta ‘sadiya’

Watarana taje gdn su sadiya da yamma shine, shi Kuma ya raka friend din shi wajen yayar sadiyar, tun daga lokacin y kyallah ido akanta yace wa yayar Yana kamu.

Tun daga ranar sadiya ke ta kokarin kafa gwmnatin Abbas Amma kememe yarda da soyayyarsa, ba irin wulakancin da Bai Sha ba Amma fir Taki shi saboda Bata son zuwa gdn kishiya.
Sbd tana da wani saurayi dake karatu a B.u.k, Shi Kuma a wajen yayansa yake d Zama kasancewar su iyayensu sun rasu, sunan jamilu, Yana level 300 a lokacin haka dai Kuma yaro ne karami, Bai yI 25 ba a lokacin, haka dai soyayyah ta shiga tsakaninsu Mai karfi don ko duk ranar da basuyi waya ba sai ka ganta kamar wata mara lfy, har tayi candy Kuma ta Sami kyakkyawan result inda ta Sami admissions itama anan b.u.k.

Inda ita Kuma alokacin ta dage kan lallai sai ta Fara aiki domin har a wake biyu ta Sami offer, shiko Daddy yace Sam Bai San zance ba, sai dai ta zaba aiki ko aurenta Nan ko ta zabi aiki, take ya Bata takardar ta saki daya, dama kawai hakuri yake da ita hattah Yan uwansa Basu d damar zuwa gdn sbd babu fuska ko kallon arziki basu samu a gidan Dan uwansu, suna ji suna gani gidan Dan uwansu y gagaresu, Dama suna zaune a k.d a unguwar tudun wada, Amma Asalin iyayensa Yan garin Kano ne a unguwa g/Kaya, mahaifinsa y rasu sai mahaifiyarsa mace Mai mutumci da karrama mutane, domin ita ce ma Mai tausasa zuciyar Dan nata akan halayen matar sa itama Bai fi sau uku ta taba zuwa gaishe da mahaifiyarsa ba, sai dai yaran da suke zuwa in sun samu hutu domin suna Jin dadin Zama da kakarta tasu. Ko da taji labarin sakin da yai Mata Bata ji dadi ba ko kadan ranta ya baci.

 

Bayan rabuwarsu ne tace ita Kam bazata bar yaranta ba anan domin kuwa ita baxata bar yayanta ba, ai ko Nan akai ta tafka muhawara har da su zuwa kotu daga karshe dai ya hakura ya bar Mata da sharadin Yana aure zai karbi yayansa.

 

Haka ta tarkata yaranta taje ta Sami gida Mai kyau ta Kama haya da sharadin ubansu ne zai dinga biya, domin Bata dauke Masa komai ba, Alan yaran duk Abinda ya tashi shi ne yake yi shiko Yana yi ne kawai don yaransa, mutum ne Mai matukar kaunar yayansa.

Bayan shekara biyu da rabuwarsu ne mahaifinsa y auri wata diyar mutumci da karamci gidan dattijai masu dattako, sunan Nasiba, Amma itama bazawara ce, tana da yaro daya Ahmed, Bai wuce 4yrs ba, mahaifinsa ne y rasu, Kuma y amince zai rike shi kamar shine mahaifinshi.

 

Itako momy tuni ta Fara aikinta a gidan t.v, dake nan k.d. Anan ta hadu da wani Alh. Yace zai aureta ganin kudin da ya ke da shi ne yasa ta amincewa Nan da Nan akai bikin, suka tare a wani gidan tare da yaran Shima gdn haya ne Amma Yana da kyau sama da kasa ne, part dinsu daban na yaran daban, Amma yaran duk Basu so ba, sunfi son gdn mahaifinsu , duk da suna zuwa hutu, Kuma matar tana kaunar su don duk Abinda suka ga dama suke Yi ba kwana ba hantara, suna Jin dadin Zama da ita sosai.

 

By
Ummu Ameer💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
KISHI KO HAUKA

 

Story & written

By

 

Ummu Ameer

 

 

 

Page 4⃣

 

 

A lokacin ne Kuma daddy ya cewa Rukayyah in da gaske jamilu yake y fito, don baison doguwar soyayya.

Ta shaidawa jamilu sakon mahaifinta, shi Kuma y shaidawa yayansa Nan yace Bai San zance ba, nawa yake da zai dauko aure ynz ko karatunsa Bai karasa ba, Nan hankalinshi y tashi saboda Yana kaunar Rukayyah, suna so juna, tun daga lokacin ya Fara janyewa daga gareta, itako duk hankalinta y tashi ta Fara tunanin dama soyayyar yaudara yake Mata, itama duk ta fita hayyacinta ta shiga matsananciyar damuwa.

A lokacin dama tana gidan dady, mahaifin nata y kirata yake tambayarta damuwarta, Tai shiru Bata bashi amsa ba, nasan baxai wuce akan jamilu bane, yace kiyi hakuri ki kyaleshi haka Allah yaso, ki maida hankalinki kan karatun ki kinji, Allah y musanya Miki da mafi Alkhairi a gareki,
Tace to daddy ngd!
Yace yawwa doughter
Allah ya yi Miki Albarka,
Ameen

Tashi tayi ta shiga dakinsu, da suke sauka in sun xo hutu.

Ita ma Antyn su wato matar babnsu Nasiba, lallashinta Tai tayi, har take ce mata ki dauki dangana Allah yayi bashi bane mijinki,
Kuma ba kina da wani dake sonki ba, wai Abbas kwananki Zainab take bani lbrinshi, har da wulakancin da kike Masa Kuma Kinga shi daga jin lbrinshi na fahimci auren ne ya kawo shi gurinki da xaki daure ki bashi dama ki gwada irin soyayyarsa ki gani ko kuwa?

Tace Anty fa Yana da aure da yara, gaskiya ni shiyasa ma tun farko naki Amincewa da shi Kuma har ynx ma Yana min waya, kawai dai naki bashi dama ne.

To ki daure ki bashi, tunda har ynx Yana tare da ke,Kuma da be damu dake ba da tuni ya kyale ki, Yana sonki,kinji Yar gidan daddy, Kuma insha Allahu Alkhairi ne a gareki.

Gyda Mata Kai tayi, tare d nuna Jin dadin nasihar ta, tana matukar Jin dadin Zama da Matar babanta, sbd mace ce Mai saukin Kai kuma ta daukesu kamar it’s ta haifesu, Rukayyah tana matukar Alfari da ita, domin tana samun kulawar da ko momy Bata Mata.
Ko shawara ne da ita take wani lokacin ko basa tare ta waya zata buga don neman shawara.

Ita momy barta da son ya’yan a Baki Amma Bata cika jansu ajiki ba, harkokin ta sun fi shige Mata gaba, dake tana business, bayan aikin da take har tattaki tana zuwa lagos, Abuja domin gudanar da kasuwancin, ita dai neman kudi ta ko ina😄

Shiko mijin da wani ba babba bane ta maishe shi mijin tace abinda taso shi take yi, sai yadda tayi da shi, wannan yasa duk lokacin da taso tafiya zata tafi tayi sati daya ki biyu, kasancewar akwai wata dattijuwa a gidan dake kula d yaran ita ke musu girki da sauran ayyuka.

Mijin kuwa aurensa biyu suna rabuwa da matan akan rashin haihuwar da bayayi, ita dama momy tun akan junior tace ta gama haihuwa hudu sun isheta.

 

A hankali rukayyah ta Fara saurarar Abbas, har ya zamo soyayyah da shakuwa ta shiga tsakaninsu Mai karfi, har tana ji sai ynx ne ma take soyayya saboda Abbas irin mazan Nan ne da suka iya soyayya, in suna waya har Bata so dena, ita kanta tana mamakin irin soyayyar da take Masa.

 

 

Itako momy tunda ta fuskanci wa take so, hankalinta ya tashi, tace Sam Bata Isa ba ta rasa Wanda zata so sai Mai mata, mazan sun Kare ne .

Tun wuri ki gaggauta fita a rayuwarsa don muddin Ina Raye bazaki auri Mai Mata ba, kina yarinyarki Zaki je ki Fara was kanki bakin ciki.

Itako yarinya ta kafe akan lallai ta ga miji, shi take so Tai aura duk da itama da ta dauko tsarin uwarta, Amma daga baya ta gane shi yafi dacewa da ita Kuma matarsa Bata dameta kowa zaman mijin sa zaiyi.

Tunda ya Mata Alkawarin cewa kowa da gidansa bazai hada su ba.

Rigima sosai akai akan batun auren inda Daddy yace shi Wanda diyarsa ta kawo tana so shi zai bata, indai ya Yaba da shi.

Momy ko tace Abinda bazai yiwu bane muddin Ina Raye
Aiko yace mu zuba Dani da ke tunda ‘yar Taki ce ke kadai.

Daga karshe ma sai gidan mahaifinta ta koma.

Anan ne ma yasa ta Kira Abbas Yana son ganinshi , ta sanar Masa da sakon daddy.

Bayan magriba suka zo shi da Abokinsa Mai suna Nasir.

Daddy yai musu tarbar mutunci suka gaisa, yace Yana son Jin takaitaccen tarihinsa,
Nan ya fada Masa shi maraya ne iyayensa duk sun mutu a hannun yayansa ya taso inda ya Gaya Masa yayi a ynx haka shi Dr. Ne Amma doctor ne na bangaran yara wato” peadiatric”
Kuma Yana da Mata da yara guda 3,
Yana zaune a unguwar hotoro GRA.

Daddy ya Yana da nutsuwarsa da girmama mutane, Nan ya amince Masa da ya bashi rukayyah. Allah yayi Miku Albarka.
Ameen! Cewar Abbas.

Abbas yaji dadin ganawa da mahaifin rukayyah, sukai ta yabon shi shi da Nasir, har Yana ce Masa
Kayi dace da sueuki nagari.

Nan suka tafi cike da farin ciki.

Momy kuwa da taji labari kamar zatai HAUKA,
Da kyar akai ta lallashinta ta akan ta amince ba’a jayayyah da Abinda Allah yayi.

Ta Amince akan zata kafa Masa dokoki akan yarta, kafin aauren.

Ta saka aka kirawo shi akan cewa bazai hada ta da kishiya ba Kuma xata dole zaibi Al’adar su ta Yan maiduguri duk Abinda ake na Al’ada sai yayi, Kuma ita zata nemo irin gidan da za’a saka yarta a ciki.

Bai Musa Mata ba duk da a zuciyarsa kawai daurewa yake Yana karfin halin bin ta Amma tuni ya gama surewa da halayyar surikarsa, don dai Yana kaunar Rukayyah ne, Amma a zuciyar sa kan Sanya Masa shakku akan abinda zai iya biyo baya duk da ya yasan ita rukayyah Bata da wani Hali na kyama.

 

 

Wannan kenan

 

Ki biyo ni don sanin waye Abbas?

 

By

Ummu Ameer
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
KISHI KO HAUKA
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

 

Story & writing

By

Ummu Ameer💃

 

 

 

Page5⃣

 

 

Abbas dan danbatta ne dake a jihar kano, haifaffen can ne, mahaifinsa Mallam muktar da mahaifiyarsa haj. Binta, duk yan danbattan.

 

Sai dai tin Abbas yana d shekaru 5 a duniya mahaifinsa y bar duniya ya rasu, ya bar haj binta da yara 5 maza 2 mata 3.

 

Da sadiya itace baba, sai karima, sai Fatima, Sune matan, maxan kuma Abbas shine babba sai mustapha, autan kenan.

Mallam mUktar kafin ya rasu bashi d wata sana’a saita kiwon shanu, yana fita da shanunsa kiwo. Suna d Dan rufin asiri daidai gwargwado, matan bai saka su a makarantar boko ba sunyi dai na addini dai dai gwargwado.

Amma yaci burin yaransa maxa zasuyi karatu boko. Abbas yana pri.1 Allah yaima Mallam muktar rasuwa, inda matan kowacce tana dakin mijinta.

Haka haj. Binta ta tsaya tsayin daka ta jajirce da tarbiyar yaran nata da kuma burin cikawa Mallam burinsa na yin karatu.

A alokacin da y gama karatun sakandire alokacin ne ya koma gdn cousin dinsa Wanda yake a matsayin yayanasa da Mallam d babansa uwa daya uba daya, shi yayi karatu boko mai zurfi, yana da matarsa Amina d yaransu hudu, habibu da bashir d sadiq, sai karamarsu Asma’u, a unguwar hotoro.

Tin rasuwar Dan uwansa yaso y karbi Abbas d mustapha a wajen innar, amma fur taki tace abin Sai yai mata yawa gashi ba Mallam kuma n yara haka ya hakura Ya bar Mata su, amma yana zuwa lokaci zuwa lokaci yana musu Alkhairi.

A wani zuwa d yayi alokacin jarrabawarsu t fito y samu kyakkyawan sakamako, shine ya nemi Alfarmar inna ta barshi y tafi da shi domin ya samo mai admssion hakan kuwa akayi tare suka tafi da shi.

Nan da nan ya samu admission a A b u zaria, Inda yake karanta medical doctor, Ya maida hankali sosai kan karatunsa ko yaushe cikin karatu gashi kuma da hazaka yai fice a makarantar “Dan boko” Wasu friends dinshi Ke kiransa sbd son karatunsa.

A can bangaren inna ko dama tana gama d hawan jini kuma in ya tasar mata kamar bazata yi ba, wani tasar Mata da yayi wajen wata guda tayi asibiti har tasa mustapha ya kira Mata Abbas a waya tai ta yi masa wasiyyah da ya kula d dan uwansa ko bayan ranta domin tana jin ciwonta ba na tashi bane, hankalinshi ya tashi sosai domin yana jin innarsa a ransa domin mace ce mai hakuri da juriya da kaunar yaranta ta su ajikinta ita dai burinta tagansu cikin farinciki ko yaushe.

Kafin ya iso inna tace ga garinku’ hankalinsa ya matukar tashi da rasuwar mahaifiyarsu, nan sukai ta kukan rashin inna aka rasa mai lallashin juna shi da mustapha.

Haka aka dauki gawarta zuwa gida aka kaita makwancinta na gaskiya, bayan share zaman makoki na bakwai Yayan nasu yace mustapha y shirya su tafi, babbar yayarsu wato sadiya taso a barshi a gurinta amma yace tai hakuri zai dinga kawo su lokaci xuwa lokaci.

 

*************************
Bayan tafiyarsu ne shi kuma Abbas y koma school, amma duk ya canza bashi da abinyi said kika abokan shi suyi ta lallshinsa suce addu’a kawai zaka dinga yi mata mai makon kuka.

A kwana a tashi har ya dangana ya fawwala ma ubangiji, amma yana Mata addu’a sosai.

Haka rayuwa ta dinga tafiya, idan anyi hutu y koma gdn yaya sule, suna zaune cikin walwala a gidan domin Ha Amina mace ce mai kirki da mutunta mutane ta dauke su kamar ita ta haifesu ba abinda suka nema suka rasa.

A kwana a tashi har Allah yasa y kamala karatunsa, ba tare d bata lokaci ba kasancewar kwarewarsa a fanninsa yasa y samu aeki a hospital din da yai practical.
Akth. Aminu kano taaching hospital kano, a fannin yara”. peaditric”.

Shikuma mustapha a alokacin y shiga buk Bayero university kano yana karanta geography.

Ku dai biyoni don jin labarin
KISHI KO HAUKA….

 

 

 

 

By

Ummu Ameer💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
KISHI KO HAUKA
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

 

Story &written

By

Ummu Ameer💃

 

Kuyi hakuri kunjini shiru kwana biyu.. Uxuri ne yai yawa.

 

 

Page6⃣

 

Akwai wata rana Abbas yana hanyar sa ta zuwa wurin aeki, a titin maiduguri road Wasu yammata zasu tsallako Titi shi kuma yana y danno motarsa ji kake ‘kiiiiiiiiiiiii” y sautin taka burki sakamakon wadannan yammatan da suka tsallako, jira suka su ji motar ta bugesu, sun makale juna sun rufe ido har ya fito daga motar y karaso inda suke basu sani ba su dai sun Riga da sun saddakar.

 

Qamshin turarensa ne ya doki hancinsu tare d min motsin mutum sukai hanzarin bude idonsu, a lokaci daya, shi dariya ma suka bashi, ganin yadda suka kankame juna cike da tsoro, amma azahiri a fusace ya fito daga motar domin sun saka shi a fargaba don baiyi tunanin motar bazata taba su ba, Allah ne kawai ya kiyaye.

Kallonsu yayi tare da cewa ba kwa gani ne kuka tsallako, kuna ganin mota ta taho?

Daya daga cikinsu wadda kana ganinta tafi dayar razana tace don Allah kayi hakuri wlhy bamu kula ba shiyasa.. Itama dayar ta bashi hakuri. Shi kam tuni hankalinsa yana man wadda ta fara masa magana tun da ta fara magana ya ji sautin maganar tata ta shige shi a take yaji wani yarrrrrr, saboda zazzakar muryar ta, dubansu yayi yace ba komai amma don Allah ku dinga kula in zaku tsallaka titi kunji.

Toh mungode suka fada a lokaci guda tare da rike hannun juna, har sun fara tafiya yace makaranta zaku je ko, suka eh!

Yace to in ba damuwa ku shigo na sauke ku.
Lokaci guda suka kalli junasu da alamun tambaya,

A’a mungode xamu samu Dan sahu ynx, ba yadda bai yi ba kememe suka ki shiga ba don komai ba Sai nasihar mafinsu kan hana su shiga motar Wanda basu sani ba.

Haka ya hakura yace wadda ya kurama ido wadda ta fara bashi hakurin ta bashi no. Ta fiir taki Sai kawartata ce ta bashi, yace kunki yadda na sauke ku a school ko? Kunga hanyace tunda naga f. G. C zaku da idan nai dropping naku Sai nawuce office.

Tace ba komai wlhy mungode ynx xamu samu abin hawa, haka ya hakura sun rabu akan zai kira no.

 

Maryam da zainab kawayene, a unguwar tarauni gidansu wajen kasuwar tarauni dake a jihar kano, gidansu kusa da kusa ne, kawayene kuma aminan juna school dinsu daya, wato f. G. C kano dake unguwa uku, nan suke zuwa suna final year a halin yanzu suna xana waec ne.

Akwai shakuwa mai karfi a tsakani domin kullum in basa gidan su zainab to suna gdn su maryam.

Basu kai 18 ba a shekaru, maryam doguwa ce ba can ba tsaka tsakiya tana da dan haske amma ba sosai ba, yana da kyawu dai-dai don Sai ka yi Maya kallon tsanaki zaka fahimci irin kyawun nata, tana da hanci tare d Dan karamin Baki kamar an dasa mata, Sai fararen idanuwata sexy eyes in ka kalli idanuwan Sai kayi tsamanin barci take saboda yalwar gashin idon da take dashi wato “eye lashes ga zazzakar muryar in tana magana kamar me rera waka..
Iyayenta duk yan Asalin garin kano ne kuma mahaifnta da mahaifiyarta auren xumunta ne cousin’s ne.

Alh kabiru ma’aikacine a WRECA, manager gidan ruwa ne, mutumin arxiki ne shima yana zaune da kowa lfy kuma y iya mu’amula da jama’a.

Ummi shine sunan da suke kiran mahaiyarsu suna da yara 5, hudu maza namiji 1.

Sun bawa yaransu Tarbiyyah sosai don yaran kam a unguwar har kwatance ake da su a unguwar wurin tarbiyyah, da girmama na gaba, suna zuwa islamiyyah don ko waccensu kafin suyi candy suke sauke qur”ani mai girma.

Aisha ce babba, wadda suke kira da hanan sbd sunan kakarsu t wajen uba taci sai Amina itama Amira ake kiranta, sai maryam itace ta uku said hafsa sai autan ummi khaleel.
Suma yaran sun taso da matukar kaunar yan’uwansu domin in suka ga daya cikin damuwa duk sai hankalinsu y tashi.

Alh kabiru yana da rufin asiri gwargwado mutum ne mai xuciyar yi akwai wadatar zuci.
Ya aurar da yara biyu aunty hanan da aunty Amira, sai maryam da take daf da kammalawa secondary sai hafsa tana junior section, said auta dake primary 3.
Alh kabiru mutum ne mai ra”ayin karatun boko domin yaransa ma sai sun kammala karatun jami’a yake aurar da su.

Maryam kuwa a halin ynx masoya sun mata caaaa da xarar ta fita to ba’arasa maau kyasawa amma ko kadan bats bash fuska, duk da shi a tsarin mahaifinta bai basu damar saurarar samari ba saboda karatun da Ke gabansu.
Duk da dai dokar tana neman faduwa a kan maryam saboda yawan Samarin dake sintiri akanta, tana da farin jini ne sosai, ganin maneman auren nata kowanne da gaske yake kuma direct wajen iyayenta sun neman ixini shi kuma ya basu hakuri akan cewa karatu zatayi, har ya fara jin kunyar fada musu hakan.

A haka ne har suka hadu da Dr.Abbas, a wajen tsallaka titi, kuma tunda yai tozali da ita yaji ya kamu da kaunarta, kuma bai taba soyayya da wata mace ba.

Tunda ya je office yaje office ba abinda yake said daman tunanin maryam, Wanda sai ynx ma yake tuna bai tambayi sunan ta ba, dukNo da dai ya amshi no.
Nan take yai dialing no. Yaji “switch off”
Nan ya tuna fa Ashe school fa suka tafi shi yasa wayar akashe…

 

By

Ummu Ameer💃
: 🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

*story*& *written*

*by*

*ummu Ameer*💃

 

 

Page7⃣

 

Bayan su maryam sun dawo gida daga school ne, tana zaune tana cin abinci, wayarta ta hau ringing.

Bakuwar number ta gani had xatai picking sai ta fasa, saboda ba kasafai take amsa no da bata sani ba, haka wayar tai ta ruri har ta gaji daga karshe ma tasa ta a silent.

Amma a xuciyarta tana zargin wannan mutumin da ya kusa kadesu wajen tsallaka titi, da ya fado Mata a rai sai ta dinga jin faduwar gaba.

Amma itama haka ta wuni tana tunaninsa tare da kwadayin son Kara ganinsa kuma cikin ikon Allah shine kadai a cikin masu sonta take jin wannan yanayin akansa.
Har barci yai awon gaba da ita.

*************************
Bangaren Abbas kuwa yinin wannan rana ya kasa samun nutsuwa so yake ya sake jin zazzakar muryarta tare da sake ganin kakkyawar fuskarta, haka ya wuni duk ya canza Hatta da friends dinshi sai da suka tambaye shi KO lafiya take yace ba komai.

Haka ya hakura ya koma gida cike da rashin samunta a waya, gashi yai rashin sa’ar tambayar kawarta nomber ta.

 

Washegari zainab ce a gidansu maryam, tai sallama ta hadu da ummi a kitchen tana hada breakfast ta tsuguna ta gaisheta, ‘
ummi Ina wuni’
Lfy lau zainab
Ya ummantaki take
Lfy lau wlh tace ma a gaisheki. Ina amsawa cewar ummi, ki shiga tana ciki mutuniyar taki tana shiryawa.
To ummi!

Tana shiga ta same ta adaki a gefen gado tana kokarin Sanya safa akafarta, oh! Maryam kullum nazo sai na jiraki kinsan yau paper safe muke da shi kuma kinsan halin invigilator’s din nan basu da kirki in suka ga anzo late suyi ta embarrassing din mutane.
Maryam dai said dariyar masifar zainab take, tace to haj. Fada yi hakuri Ai na gama breakfast dinma idan ma dawo naci, ta dauki Jakarta sannan ta day wayarta daomin ta kasha, sai ta massage ya shigo kamar haka

“Assalamu Assalamu, Da fatan min tashi cikin koshin lafiya? Na kira ki jiya kin ki ki picking, I think KO don Baki san number bane, to Abbas ne Wanda kuka hadu da shi a hanyar ku ta zuwa school, don Allah kiyi kokarin amsa kira na idan na kira, Domin isar miki da wani muhimmin sako.
Ngd daga
Daga Dr. Abbas Danbatta”

Nuna ma zainab wayar tayi ta karanta, karbar wayar tayi ta kashe tace muje ma karasa maganar a hanya mun yi late, fitowa sukai daga dakin suka yi wa ummi sallama tace bazaku tsaya ku karya ba, maryam tace said mum dawo ummi wlhy mum makara, tace to Ai shikenan Allah ya bada sa’a sai kun dawo!
Suka amsa Amen!
Said min dawo.

Haka suka tafi a hanya ne maryam ta gaya Mata kiran da Abbas yai mata bata daga ba, tace gara na ja masa Aji! Maxa said da aji,
Zainab tace in aka ja da yawa ai ya tsinke. Don na fahimci wannan bawan Allah ya samu waje a zuciyarki, murmushi Tayi tace ba haka bane kawai dai Ina jin faduwar gaba a duk sanda ya fado min a rai, zainab tace sonshi kike yi,
Maryam tace daga faduwar baba sai so?
Alamun su ne AI, cewar
Zainab, tace amma don Allah in ya kiraki ki dauka jan ran yayi yawa.
Haka sukayi ta hirarsu har suka isa school din.

 

***********************
Bayan sun dawo zainab bata tafi gida ba sai da ta tabbatar da maryam ta amsa kiran Abbas, Domin suna kunna wayar kamar jira yake a kunna kiransa ya shigo.

A kunyace take wayar kasancewar wannan ne karo na farko da ta fara yin waya da saurayi, anan yagaya Maya abinda me ransa kuma shi da gasket yake ya kuma nemi izinin zuwa ya fara ganawa da iyayenta, ta amince masa, sun Dan taba hira daga karshe yace ta bawa zainab, suka gaisa tare da yi mata godiya don yasan da taimakonta a yiwuwar al’amarin.
Sunyi sallama Akan gobe zai gana da iyayenta.

 

Washe gari Abbasa ya gana da iyayenta tare da neman izinin zuwa wajen maryam. Ton fah! Abinda Abban maryam ya furta a zuciya kenan domin wannan ba shine Karo ma farko ba, amsar da yake bawa sauran *ba yanxu ba* amma tun shigowar bawan Allah nan yai man kwarjini, kuma shi kanshi ya fara kunyar su Akan hakan, yai doguwar ajiyar zuciya, yace mallam Abbas ko?
Ae haka ne.
To ba komai na baka izinin zuwa in had da gaske kake kuma azahirin gaskiya ire-irenku sunzo min da irin wannan batu amma amsa daya nake basu karatu xata yi yanxu ba aureba, har na fara jin nauyin gaya musu hakan, kasancewar duk yan’uwanta sai da suka kammala karatun jami’a nake aurar da su.
Amma inKa amince zaka barta tayi karatu to ba Matsala.
Abbas yace Abba ba Matsala indai wannan ne damuwar ka, domin nima Ina da ra’ayin karatun.
Yaji dadin kalamansa soaai yai masa addu’a tare da fatan cika Alkawari. Sukai sallama ya tafi.

Abbah ya yaba da nutsuwar Abbas Sosai gashi da kwarjini da kamala.
Ya zayyana ma ummi duk Abinda ya faru tsakaninshi da Abbas itama taji dadi sosai Domin bata son wannan ra’ayin yarinya sai ta gama karatu ai aure.
Nan ummi take tambayarshi to kaji ra’ayin yarinya ne?
Yace to ai ita ta bashi izinin zuwa.
Murmushi tayi tace ai zance ya kare.

Itako daman tana nan alabe tana Jin hirar su ummi, tana ta fargabar kar Abbanta ya hana shi xuwa kamar yadda ya saba, jin hirar iyayen nata ya sanya ta farinciki,
Had kanwarta hafsa tana tambayarta anty maryam wai me ya faru ne naga kina ta farinciki?

Ba komai hafsa Ina murnar gama paper mu na karshe ne,
Hafsa tace to Allah ya bada sa’a.
Ameen! Inji maryam

Tin daga nan soyayya ta kullu mai karfi tsakaninsu magana har ta kai ga magabata sun shiga maganar anyi “baiko” sosai suke junansu.

 

An Sanya ranar aure, ranar aure wata uku masu zuwa shiko Abbas ji yake kamar sun yi masa yawa, yana matukar jinta a ransa gashi da tsananin kishi, in suna tare KO tari tayi kada kaso kaga tashin hankali a wajensa.

 

*by*

*ummu Ameer*💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

*story&written*

*By*

*Ummu Ameer*💃

 

Page8⃣

 

***shirye shiyen biki ake tayi, domin saura sati biyu kenan, ango saboda doki tun ya rage 1month, biki ya aiko ma amarya invitation, shi ji yake kamar ya janyo ranar.

An kawo lefe akwatuna 2 set pink&blue, an zuba kaya na gani na fada aciki komai yayi sai fatan Alkhairi ga ma’auratan.
Maryam kuwa ta shiga busy, domin kullum gyaran Jiki na amare take zuwa gidan wata hajjagana dake da zama a unguwar zoo road tayi fice wajen gyaran amare.
Aikuwa amarya tasha gyara Jiki sai kyalli take, yadda Kasan fatar jarirai, ango kam duk ya Kara susucewa akan amaryar tashi.

*************************
Yau saura satin daya a daura aure duk sun gama rabon invitation cards da taimakon ango amarya ta kaima duk friends dinta invitation domin cewa yayi bai yarda garin raba I. V ba amaryarsa ta kode ba sannan a gane masa mata, duk gidan da ya kaita sai ya jira ta fito sannan su tafi wani wajen kuma, amma duk fitar da Suke da zainab suke fita, tare suke gudanar da shirye-shiryen bikin.

“””Bangaren amarya kuwa tuni an mata jere a gidanta dake hotoro amma da taxara tsakaninshi da gidan yayan shi, shi ya gina gidanshi gidan ya tsaru ba laifi amma falo ne babba, sai kitchen a falon da kuma 3 bed room sai kuma farfajiya wadda in ka shigo gate din gidan zaka gani wacce zata dauki motoci biyu. Ba wani girma ne da shi sosai ba amma ya tsaru abin sai Wanda ya gani, wajen dining din tafi daukar hankali wani decoration da akayi da wani labule mai duwatsuna ga wata cupboard a gefe an jere plates da cups, duk wani glass cups da tea cups har da roses guda hudu daya biyu a sama biyu a kasa har da wani colour Daga cikin cupboard din dake bayarwa a ciki daga sama da blue da pink da kuma red, daga kasan dining din kuma an sa carpet purple n white har kujerun suma purple ne hatta da fentin falon ma haka yake, gida yayi kaya sunyi masha Allah.

A yaune dandazon jama’a aka shaida daurin Auren “mukthar usman Danbatta da kuma maryam kabir Muhammad”
Kada kaso kaga ango Baki yaki rufuwa friends dinshi na tsokanarshi, har cikin gidan suna shiga akai musu pictures da iyayenta amarya da amaryar tare da kawayenta, tayi kyau ba kadan ba, domin kwalliyar da akai mata tayi mata kyau sosai domin kwalliyar ta canxa mata kama kamar ba ita ba, gashi da ta gifta wani daddadan qamshi Ke tashi irin na turara jiki dinnan.

Bai bar gidan ba sai da ya samu ganinta yana shaida mata wai Dama su tafi yanzu tunda an daura aure daga baya azo ganin amarya? Ko babynah ya wani maze a dole shi da gaske yake, aikuwa wata dariyace ce ta kufce mata, har saida wushiryarta ta fito, tace haba husby! Ka fiye gajen hakuri duka awa nawa ya rage mu kasance tare a gidanmu, husby, din da ta kirashi ne ya Kara narkar da shi domin ji yayi kamar itane ta hallici kalmar saboda dadin sunan, dubansa ya kai ga hannunta da yasha jan lalle da kuma Baki zanen yayi matukar kyau yace muga hannun, ta boyeshi cikin mayafin data yafa, kwatsam sai ga zainab tace ohhhhh nan kula taho kuke soyewa hakane daman in asking yaxo gaban goshi tafi zafi dama, ango duk kunya ta kamashi yana soda keya yace to baby sai na kira ki take care! Ya fada mata tare da kanne mata Ido daya…
Ya tafi wajen friends dinshi dake jiranshi a waje, suma haka suka yi ta masa tsiya, daga nan suka wuce reception.

Ana ta gudanar da shagalin bikin cikin farinciki da kwanciyar hankali, Amarya tasha kayan gyara abin ba magana sai turarrata akeyi da turarukan qamshiiii.

 

Da misalin karfe5pm na yamma motocin daukar amare ta iso, ciki har da ango, wai shi da Kansa zai dauki amaryarsa, tunda daga kan kai kudin aure har kai lefe shi yake kawo su, sai ya jira a waje😄

An shirya amarya cikin wani tsadadden leshi dark blue, ya masifar yi mata kyau dinkin ma ya dace da jikinta taui kyau sosai, an turareta da da kayan qamshi, yan uwan iyayenta da iyayenta sun mata nasiha da kuma hakuri da rayuwar aure domin shi aure hakuri ne gabadayansa, sun mata nasiha mai ratsa jiki ta shigeta sosai sai kula take, an kaita wajen mahaifinta shima yayi mata nasiha daga karshen yace nasan ki da biyayya ba abinda kika taba yi mana ina fatan ki dore ahaka, ya kare da Sanya mata Albarka a rayuwar aurensu nan ma kukan taita yi da kyar aka dauketa a wajen, ummi ma daki ta boye tana ta kuka har kannenta na tsokanarta wai batai wa sauran ba.

Kanwar Abba ce ta hana Abbas daukar maryam tace ita zata kaita a motarta su debi kawayen amarya, haka ya hakura ba don ya so ba.

Saida aka sata Tayi addu’a kafin tashiga tare da shiga da kafar dama,tsarin gidan ya burge su sosai kuma sun lura da canja tsarin jeren da akayi, kuma wannan din yafi tsaruwa, an kai amarya har dakinta suna manne da zainab sai faman Kukan rabuwa da juna suke, da kyat aka lallashesu, sannna aka kara yima amaryar make-up kasncewar duk ta bata da kuka, aka Kara fesheta da turaruka, yayyenta ma sun mata fada sosai da kuma wayar da ita akan zaman aure.

Duk an watse daga amarya sai kawayenta yan siyan Baki, ba dadewa sai ga angwaye sin rako ango da ya matsa musu su taho tun daxu suna ta mai tsiya Akan rawar kan da yake akan amaryarsa,

Ba tare da bacin lokaci ba an siya Baki Alan 50,000 abokan ango suka debi kawayen amaryar domin maidasu gida.

Ango kam sai da ya tabbatar da ya kulle ko Ina na gidan sannan ya shiga wajen amaryarsa, tura kofar yayi tare da sallama…….

 

Ku biyoni domin
*yanzu aka fara*

 

By
*Ummu Ameer*💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍

*story&written*

By

*ummu Ameer*💃

 

*JUMU’AT KAREEM 2 OL MUSULEEM*

*Allah ya bamu Albarkar wannan rana Ameen*

*Ina jin dadin comment dinku Allah ya bar zumunci*🤝

 

 

Page9⃣

 

Sallama yayi bai jira amsawarta ba ya nufeta cikin sauri ganin kukan da takeyi dago fuskarta yayi fuskarta duk ta jike da hawaye,
Yace” baby why are u crying?
Ba kyason ganina?
Girgiza masa kai tayi, yace to “why”
Ni gida zanje.. Ta fada cike da shagwaba, sai alokacin ya gano kukan rabuwa da gida takeyi, lallashinta ya hau yi yace ai zasu dinga zuwa akai-akai, ba wai ta rabu da gidan bane.
Nan ta saki fuska tana murmushi, yace yawwa baby ko kefah, fita yayi daga dakin kitchen ya nufa ya dauko fresh milk tare da kazar da ya siyo ya dauko plate ya Dora tare da cups guda biyu ya nufi dakin ya ajiye kan carpet din dake tsakiyar dakin ya umarce ta da tayi alwala suyi sallah, tashi tayi duk jiki a sanyaye ta nufi toilet din dake dakin ta yo alwala, bayan ta fito shima ya shiga.
Bayan ya fito suka gabatar da sallar, ya danyi mata tambayoyi game da addini kuma ta bashi amsa yaji dadi sosai da ya sameta mai ilimin addini, yai musu addu”ar samun zaman lafiya tare da zuri’a na gari, bayan kammala sallar ne ya janyo musu tray din naman da milk, ya zuba bashi a cup, itama ya zuba mata da kanshi ya dauka zai bata ta kauda kai wai ta Koshi, nan ko yunwa ce Ke kwakularata, amma ta kafe bazata ci ba said da kyar da ta ga ranshi ya baci sannan ta fara kurbar milk din shi ya dinga bata saida ya tabbatar da ta koshi sannan shima yaci nashi, ya gashi ya kwashe kayan ya maida su kitchen.

Yana fita ta shiga toilet, Tayi wanka ta shafe jikinta mayuka masu laushi da turaruka masu tayar da hankali, ta dauko rigar baccin da ta saka amma duk ita ji take kamar ta cire kamar rashin kunya ne hakan, daga karshen dai hijab ta dauko ta sanya bisa rigar barcin.
Shima Abbas din Dakinsa ya shiga domin yin wankan bayan ya fito ya sanya turare mai dadin qamshi tare da sanya singlet da boxer said ya dora jallabiya akai sai yai fes da shi, Abbas dogo ne amma yana da dan kauri tare da faffadan kirji yana da yana da Dan haske ba sosai ba yana da kyau dai dai misali ga sajen dake zagaye a fuskarsa gwanin sha’awa, yana da kwarjini da cikar kamala, yammata da yawa suna kawo tayin soyayyrsu amma duk ba wacce tai mai sai maryamunsa.

Y kashe fitulun dakin tare da janyo kofar ya kashe komai na falon ya wuce dakin amarsuuu. Yana shiga ya sameta a zaune a gefen gadon har ta fara gyangyadawa, hura mata iska yayi a fuska firgigit ta tsorata, yace wannan zumbulelen hijabin fa baby ba kyajin zafi yai saurin daga kai duk ta tsorata da shi, ango kuwa tuni ya gama rikirkicewa tare da zumudin wannan dare, tashi yayi ya kashe wutar dakin ya nufi gadon tare da janyo ta ta fado jikinsa….

dole dae nima fitowa nayi, domin iya abinda xan iya gani kenan.

 

 

“”””””Fadin farincikin Abbas bai misaltuwa a wannan dare sai faman addu’a yake mata tare da Sanya mata albarka, wani irin Sonta ne ke kara ratsashi yaji dadin samunta yadda ya kamata tare da samun nutsuwa.

Da asuba ya tashi ya shiga wanka, a toilet din dakin bayan ya fiyo ya taimaka mata wajen hada mata ruwan zafi ta gasa jikinta, ba karamar wuya ta sha ba, domin kuwa har tsoronsa take tare da wata matsananciyar kunyarsa ko hada ido bata yadda suyi, sai da ta gama gasa jikinta ta tabbatar da duk wata gajiya ta sake ta sannan ta fito tai gabatar da sallah sannan ta shirya cikin wani material doguwar riga ta Dan yi silent make -up ta yafa Dan karamin mayafi akanta ba karamin kyau tayi ba.

Shima Dakinsa yaje ya shirya cikin kananan kaya sun masa kyau ya feshe jikinsa da turare sai qamshi yake tashi, kasancewar sa ma’abocin turare. Ya shirya tsaf ya nufi wajenta tana Dakii a zaune ta kasa fitowa,
Shiga yayi ya sameta a zaune gefen gado ta kimtsa dakin tsaf, tsugunawa tai ta gaisheshi Ina kwana kanta a kasa ruko hannunta ta yayi suka sake gaisawa lfy lau my lovely wiffy!
Yai ta mata godiyar rike mutumcinta da ta kawo gidan aurenta. Ruko hannunta yayi suka fita falon kan dining ya ajiyeta ya shiga zai hada tea kenan sai suka ji knocking yaje ya bude daya daga cikin yaran gidan yaya ne aka aiko shi da break fast, ya amsa yai godiya, farfesun kayanciki ne da irish&egg da yaji source da akayi da kayan lambu sai kunun gydar da sha madara, daman shi ma’abocin kunun gyada ne, zuwa yayi ya kawo plates da cups ya zuba musu yace da kanshi zai bata tace da kanta zataci bata wani sake ba ta dan tsafura amma tasha kunun sosai.

Bayan sun kammala break fast ne ya ja ta ya Nuna mata ko Ina na gidan, suka dawo falon suka zauna ya kai musu tashar m.BC 4, ya jawo kusa da shi kamar wani zai kwace masa ita, aiko tuni bacci yayi gaba da ita fuskarta ya kurama ido yana kallon kyakkyawan idanuwanta da gashin ido ya rufe shi ba karamin kyau tai masa ba da baccin, gyara mata kwanciyar yayi har da dauko abin rufe ya rufeta.

 

***** **** *****
Sun gudanar da amarcinsu cikin so da kaunar juna ji yake kamar kar ya koma aiki hutun yayi kadan ya zauna yai ta kula da amaryarsa.

 

*muje zuwa*

*ummu Ameer ce*👌
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

*story&written*

*by*

*Ummu Ameer*💃

 

 

*page*🔟

 

“””””Wata uku kenan da aurensu maryam ta Kara haske da tare da cikowa, kana ganonta kasan amarci ya karbeta kowa sai yabon ango yake akan ya iya kiwo.

Sosai Abbas yake ji da maryam ko office ya je cikin kiranta yake lokaci zuwa lokaci, Itama kuma tana kokarin kyautata masa duk wani abinda tasan zatai ta burgeshi tana kokarin yi, Ko ta fannin girki ne duk abinda tasan yana so to sai ta kware basirarta wajen yi mai yadda yake so.
Ta fannin kwalliyah ko ba’a magana domin gwana ce kuma ta hadu da miji mai son kwalliyar, ko yaya tai make-up sai ya yaba har da tukwici, haka ma ko girkin ne in dai tayi sai ya yaba, yana Alfahari da ita wajen girki wannan ne yasa bai shakkar kawo friends dinshi cikin gidan, in dai suka zo to haka zasuyi ta yabon girkin nata, har da kyauta. Shikuma kai ya fasu an yabi Abin Alfaharinsa, haka ta fannin tsafta ma ba daga baya ba wnn kuma kamar gado ne domin ko ummi mace ce mai tsaftar gaske, duk sanda ka shiga gidanta ko Ina tasss yake so wannan training dinta shi yasa yaranta basu da matsalar kazanta a gidan aurensu.
Babu yadda za’ayi ka shiga gidan maryam baka ji qamshi na tashi ba ita ko yaushe cikin qamshi gidanta yake ko girki ta ke to qamshin girkin daban na turaran gidan daban, wannan ne yasa ta sace masa zuciya gabadaya ya gama sakankancewa da ita ya mallaka mata kansa baba daya, ko bako ne yaje gidan sai ya fito yana yabon soyayyarsu suna burge mutane.

Duk inda Zata shi ne yake kaita da kansa kuma ya jira in yana da uxuri ko saidai ta hakura da fitar. Har danbatta ya kaita wajen ‘yan uwaansa sunji dadin ganinsu sosai, amma anty sadiya babbar yayarsa bata wani sakar mata fuska ba, ganin irin rawar kan dake yi akanta, gani take kamar ta asirceshi ne, sauran yanuwansa kuwa sun nuna Mata kauna sosai ta saki jiki da su har ta nemi a bata yar diyar yayarshi ta biyun tai hutu a wajenta, haka kuwa akayi tare suka taho da ita amma shi baiso hakan ba.

 

Ranar wata asabar ne lokacin yana gida hutun wkend maryam ta tashi da wani matsanancin ciwon ciki tunda safe take ji kadan-kadan yana lura da ita duk yanayinta ya canza ba walwala a tare da ita duuk yabi ya rude yana tambayarta meke damunta tace bata Jin dadin jikinta ne duk ga kasala, yace tun yaushe tace tun last 2days amma dai yau har da ciwon ciki tunda nai breakfast yake ta min ciwo.. Ta kare maganar cike da shagwaba kamar xatai kuka, yace amma babyna shine Baki fada min ba kina barmin jikinki yana ta wahala Har tsawon kwana 2 karki sake kinji koya kika ji wani changes a jikinki just tel me, okay! Gyada masa kai tayi, maza dauko hijab muje hospital shi kuma yace bari naje na dauko key.

Bai zarce da ita ko Ina ba sai asibitin STANDARD hospital dake nan tarauni bai kaita asibitin da yake ba saboda yasan delaying dinsu, kuma shi standard din nan gidan yayanshi suke zuwa indai bukatar asibitin ya taso.

Banyan sunje suka samu wata Dr. Hauwa daman sunsan juna tana aiki a AKTH in ta tashi daga nan da gama sai ta wuuce can standard din ranar wkend kuma tun safe take zuwa.

Bayan sun gaisa ne yake ce mata ya kawo madam ne tana fama da ciwon ciki, nan tai mata tambayoyi na masu ciki, sannan akai p.T test, an tabbatar da cewa tana da cikin wata uku, ajikinta farinciki wajen Abbas bai misaltuwa, Dr. Hauwa tai masa murna sannan ta batashawarwarin da ya kamata tayi don kula da lafiyarta da na babyn, itama kam murna da tsoro ne suka hadu mata a zuciya domin tunda ta taso take tsoron haihuwa sosai a rayuwarta gani take kamar bazata iya ba in tazo haihuwa mutuwa zatai, ganin Wasu da suke haihuwa ace ai garin haihuwa wance ta rasu, shine take ganin kamar itama hakane… Lol.. Kuruciya

Tun daga hospital din kada kaso kaga yadda ya tattara duk wata kulawa akanta, da suka zo fitowa a hospital din ma rungumo ta yayi a jikinsa sai kace irin wadda ta galabaita dinnan ya wani shawabata itako Dama abin ne ya samu tai luf a jikinsa ya bude Mata motor ya zaunar da ita, ya zagaya ya shiga suka nufi gida, Wasu had kallon su suka tsaya yi a asibitin saboda sun burgesu wasu kuma na taya ta murnar samun miji mai kulawa irin wannan.

A motarma ma duk hankalinsa yana Kanta gabadaya, yana tambayar ta ko cikin ya daina tace eh! A Hanya ya tsaya ya siyo mata pizza Da burgar saboda yasan tana sonsu sosai kusan duk sanda zai dawo gida saiya siyo mata.

Tun daga ranar ya Kara dora soyayyarsa AKan maryam Da unborn baby dinshi, ya hana yin wani aikin Da zai wahalar Da ita ko abinci cewa yayi ta bark zai dinga taho musu Da takeaway in zai dawo tunda a gidan ya samo musu wata dattijuwa baba larai tana yin aikace aikacen gidan, har avincin ma tanayi amma yace shi Sam bazai ci avincin mai aiki ba saidai nata gudun kar Ya takura mata yasa yace zai dinga taho Da shi, ita kuma tace a’a ai yin girkinsa ba zai gagareta ba.

 

*muje zuwa*

By

*Ummu Ameer*💃

More comment more typing…
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

*godiya mai yawa gareki yar’uwata ta kaina kinfi kowa son book dinnan Allah ya bar zumunci*

*Story&written*

*by*

*Ummu Ameer*

 

*page* 1⃣1⃣

 

Haka maryam tai ta fama da laulayin ciki sai dai abin ma yazo mata da sauki tunda bata amai da zubda miyau, abin da yafi damunta ma ciwon ciki kuma Ba waikullum ba sai dai rashin Jin dadin bakinta da bata yi da kasala da tayi dan aiki kadan sai ta gaji, Abinci ma komai dadinshi da ta fara sai ta kasa ci hakan yasa ta danyi rama sai haske da ta Kara yi tare da kyawu.

Abbas kam Indai yana gida bai barinta tayi komai ya dauki son duniya Ya dorama ma unborn baby dinshi haka zaka ga yana tayin magana da shi kai kace amsa masa yake yi, Kullum addu’ar shi Allah ya sauke ta lafiya tare da dokin ganin ranar da zai zama daddy.

A lokacin da cikin yai 4month ne ta fara zuwa awo zuwanta na farko akai mata scaning domin ganin lafiyar cikin, kuma ba wani Matsala komai normal tare da yin gwaje-gwajen da tabbatar da lafiyar ita kanta mai cikin, kuma Alhamdulillah shima normal sai magunguna na Karin jini da calcium aka bata.

Shima tunda cikin ya kai 4month haka yake siyo mata kankana kullum sai tasha domin shan kankana ga mai ciki yana wanke baby kaga jikinshi fresh da haske in ka haifi baby, maltina ma carton-carton yake siyo mata kafin wani ya kare ya siyo wani shima yana Kara jini ko da haihuwa aka xo yi to bazata samu matsala jini ba, sai dai in ya zo da matsala na bleeding.

Ranar wata Sunday ta sa masa rigima kan lallai sai ya kaita gida, shi kuma in ba zuwa hospital ba bai fiye son tana fita ba, haka ta sa shi a gaba tana masa kuka, a dole ya amince yace ta shirya su je, nan taita murna ta tashi da sauri had tana shirin faduwa yai saurin tallafo ta yace yace Kinga ni ko zaki wahal min da baby, shi yasa ban fiye son kina yin wasu abubuwan ba.

Tace wato kai ta babyn ka ma kake yi ba ni ba ko shikenan ai, ta kare maganar da shagwaba kamar wata yarinya, murmushi yayi ya lakuce mata hanci yayi yace tun yanzu har kin fara KISHI da babyna. Murguda masa Baki tayi tana masa dariya ta shige tai saurin rufe kofar, yace zaki fito ne yarinya.

A hanya suka tsaya a wani super market sukai danyi ma su ummi siyayya daman ka’ida ne duk sanda zasuje sai ya tafi da wani Abu basu zuwa haka, yana kyautatawa wa yan’uwanta, tare suka shiga yace ta zabi abinda ya dace.
Da isarsu yace karki dade just 30min, zanje gidan yaya indawo sai mu gaisa ki gaishe su sai da ya bude mata motor en har da riketa wai karta fadi sai da ya tabbatar da ta shiga sannan ya tafi tare da manna mata kiss a kumatu.

Tana shiga gida sai murna bare ummi da tai missing dinta kullum da ita take kwana take tashi a ranta, duk da kusan kullum sai sunyi waya, kowa yai farinciki da ganinta gashi sunga ta Kara kyau sosai sun yaba sosai da ganinta, sai alokacin ummi ta lura da juna biyun dake jikinta, ko hafsa da taje tai mata kwana biyu da bata da lfy duk basu gane ba, nan itama ummi tayi ta nan-nan da ita, Abba shima yayi farincikin ganin yar tasa yai ta shi musu Albarka, ko Abincinta ma ummi daban tai mata, tace ita tuwo takeso miyar kuka ummi tace sai dai tai mata miyar ugwu sai yafi amfani a tare da ita, haka kuwa tai mata lafiyayyen tuwo da miyar ugwu kuma tas ta cinye tana ta santi.

Sai bayan la’sar ya zo daukarta ya shiga suka gaisa da ummi sukai tai mai godiyar kula da diyarsu shima ya ji dadi sosai da add’ar su, ganinsu yake kamar iyayenshi yana matukar ganin girmansu yana Alfahari da samun surukai masu dattako kamarsu.

A hanyar su ta komawa yace su je BABY DREAM CENTER, su fara siyan kayan baby tace kai husby tun yanzu bamu sani ba fa ki me samu haifa yace ai unisex samu saya, haka suka shiga duk abinda ya mash sha’awa sai yace a dauka.

Bayan sun dawo ne daman ta taho masa da tuwon ummi yaci ya koshi shima yai ta santi yana cewa Ashe ummi ce ta koya mata girki masu dadi yai ta shima ummi Albarka.

Tashi tai tace bari naje na Dan watsa ruwa a jikina yace to bari na zo na cuda ki, tace a’a barshi na gode saboda tasan abinda zai biyo baya, itako yanazu kwata kwata abin ma ya fita akanta kawai dai tana daurewa ne tana kokarin bashi hakkinsaBy gudun jefa shi cikin wani hali.

Tana kokarin jure bukatarsa amma bata so tun sanda ta fara laulayin cikin, shima kuma yana tausaya mata duk da kasncewarsa mabukaci sosai.

“””””Haka suka kasance cikin so da kaunar juna tare da kulawa ta musamman ga cikin dake jikinta, yanxu kam cikinta ya kai 9month, ga cikin da girma sosai kamar na twins, ko bacvin kiraki bata samu ga motsin cikin kamar zai fasa mata cikin sau tari motsin ke hana ta bacci, shima barcin kaurace masa yake, zuwa yanxu sun gama hada komai haihuwa suke jira, hafsa ma tana gidan ko da wani abin ya taso in baya nan.

Ranar litinin da daddare misalin 11 daya na dare ta fara jin ciwo tun tana daurewa har ta kasa yace kawai ta tashi su tafi asibiti tace ya bari dae ciwon yafi haka duk ya wani rude ya kASA zaune ya tsaye, haka tai ta fama sai misalin 3 na daren suka tafi asibitin Mallam Aminu kano, direct akai shiga da ita labour room, yana kokarin binsu suka bana shi ya tausayi mata matuka.

Shiru haihuwa har asuba, ba labari hankalin shi yai matukar tashi ya sanar ma da su ummu da gidan yaya aikuwa ba bata lokaci sai gasu sun iso har da Abbah.

 

Munai miki fatan Allah raba lfy maryam.

*by*

*ummu Ameer*💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

 

*page* 1⃣2⃣

 

“””””Hankalin ummi ya matukar tashi ganin irin tsawon awannin da diyarta ta dauka duk da tasan daman haihuwan fari wasu kanyi doguwar nakuda, amma duk da haka ta tsorata ganin duk yaranta itace ta haihu a shekarunta, ganin cewa sauran da sai sun gama mallakar hankalinsu, gani take kamar tai kankanta, addu’a kawai take tayi ba kakkkautawa akan Allah Ya sa ta haihu lfy, shima Abban yana zaune yai jugum shima sai addu’a yake Mata a zuciya, *lallai maryam yar gata ce ga ummi ga Abba, ga husby.. Lol..*

Shi kam Abbas ya kasa ma zama da yaga an fito zai nufesu da sauri yana tambayar *ta haihu*?
Suce da saura, sai da Abba yai masa magana ya samu nutsuwa ya zauna Addu’a zai mata, ta sauka lafiya, yaya ma
da matanshi sun tausaya mata.

 

Sai da misalin karfe 9:am
Aka zo musu da Albishir din ta sauka, ta haifi *baby boy* Wata nurse ce tazo da Abishir din kada kuso ku ga farin ciki a wajen family din nan, Abbas ko daga hannu sama yayi yana ta fadin Alhamdulillah yana ta godewa ubangiji, hat da tukwici yaima nurse din, yana kokarin binsu suka ce ya dakata in an gyara babyn za’a miko masa abinsa sai tsiya suke masa na dokin shi.

Abba ma sai murna sai kace shine jikansu na farko, ummi kuwa an bata damar shiga don ta kintsa ta, tana shiga ta ganta da gani ba karamar wuya ta sha ba, ta nufe ta cikin Sauri tare da daukan babyn, tana tai Mata sannu, tace wannan babanshi ne sak, Rungumeshi tai tana masa addu’a.

Banyan an kintsa babyn aka kawo ma mahaifinshi rungumeshi yayi a jikinshi yana jlin wani irin son yaron aranshi bakinshi yaki rufuwa, yai masa huduba da sanyama yaron sunan mahaifinshi wato, *muktar*, ya kaiwa sauran yan’uwa suna masa murna kowa cewa yake kamarsu daya, abokanan aikinshi ma duk sunzo sunga baby sai pictures suke ta yi tare da babyn, suna cewa like father lyk son amma ya fika haske, jajir yake babyn kamar bature.

Banyan wasu awanni aka sallamesu ummi ta nemi da abata maryam domin tai wankan jegon a gida, fafur yaki yadda a tafi da ita, Abba yace a kyaleta a gidan mijnta a samu wadda zata je ta kula da su da jaririn.

Haka kuwa akayi suka wuce gida aka ce za’a kawo inna, kakar maryam wadda ta haifi ummi, duk da daman hafsa na gidan.

Bayan sun dawo tai wankanta tsaf da ita kamar ba ita ta haihu ba ta ciko tai bul-bul da ita, shiko yana zaune yana rike da babyn a hannunshi a gefen gadon, yace baby nah ba abinda zance da ke sai godiya kin Haifa min santalelen yaro zanso duk shekara ki dinga haifomin irinsu… Jifanshi tai da harara tace lallai kam tunda ba wuya ko???? Yace ba gashinan ya wuce ba. Bai bar dakin ba har sai da inna ta iso sannan ya fita.

*******************
Maijego ta samo kyakkyawar kulawa a wajen inna ta mata wankan jego yadda ya kamata, hatta dinkin da akai mata ya fara warkewa duk da cewa cin abinci ingantaccen shine jegon ba wai wankan ruwan zafi ba, shima anayi amma saffa-saffa.

Ranar suna ‘yan’uwa da abokan Arxiki sun halarta gida ya cika makil da abokanan arziki angon karnin ma a ranar bai fita ba wai da shi za’ai taron yan’uwasa na tayi masa tsiya yace naji dae.

An gudanar da shagalin suna lafiya maijego tasha kyau kamar amarya ansha make-up, sai canja kaya take na gani na fada, shiko duk inda ta gifta idonshi na kanta, sai hotuna suke tayi tare da shi ya wani rungumota ita kuma tana dauke da babyn, abin sha’awa.

Aunty sadiya kuwa sai wullah harara take ko picture ba ai da ita ba, in an kirata tace tana xuwa, sai taki xuwa.

Anyi taro an watse duk yawancin dangin nasa can gidan yaya zasu kwana, sai da aka gyara gidan tsaf kamar ba ai taro ba an turare gidan da qamshin turaren wuta.

Bayan ta yi wanka an ma babyn Wanda suke kira da mufid, ta daukeshi zuwa dakin abbas kasancewa da sauran mutane a dakin, kuma shi ka’ida ne da daddare yaron a hannunsa yake sai zai kwanta zai mayar da shi wajen mahaifiyarsa, a zaune ta sameshi Akan wata kujera da ke cikin dakin ta mika masa Shi ta nemi waje ta zauna, a kan gado, karbarshi yayi yana sorry my boy an wahal min da kai ko? Kasha hannun mutane. Tace ai an masa wanka yanxu zai ji dadi, ido ya kafeta da Shi yace baby Kinga wani kyau da Kika Kara yi kuwa? Dama in an haihu haka ake Kara yin kyau, taso wa yayi ya xauna kusa da ita yana wani mata wani irin kallotare rungumota jikinsa yana fadin wai yai missing dinta sosai ya kosa, tureshi tayi ta nufi kofa tana masa gwalo tace duka yau fa satinmu daya amma had ka fara korafi, tasowa yayi aiko tai maxa ta fita ta rufe kofar tana masa dariya, sai ga inna tace auuu dama can kika tafi Ina ta nemanki yaran zamani ba kunya.. Tace inna yaron na kai masa fah..

Tace muke maza kici abinci ace maijego ta kai had wannan lokaci bata ci abinci ba, tace inna ai yau ne kawai aka kai haka fah.. Ta fada da shagwaba, ita shagwabar ma ta zame mata jiki, ko Ina yinta take.

 

Watansu daya mufid yai kiba sosai kamar Dan wata uku gwanin sha’awa, ga yaron da farinjini ko asibiti suka je ai ta son yaron, Abbas kuwa tuni an bude shafin wani amarcin tun kan ai arba’in gyara kuwa tun bayan suna take seatbath da bagaruwa da ganyen magarya da tafito wanka kuma ta shiga tai turaran kanumfari, ba tai wasa ba wajen gyara kanta kullum cikin yin juice din fruit ko ta sha kankana da madara ta yanka, shiyasa sanda ta koma wajen oga ta Kara sukurkuta shi sosai.

Banyan arba’in suka ziyarci gidajen yan’uwa da wajensu ummi tunda suka je yana bayan ummi said dai in yana Jin yinwa a bashi ta maida shi bayan.

Sabuwar rayuwa suka bude mai cike da so da kaunar juna in Abbas yana gida shike rainon mufid had goya shi yake a baya in yana kuka, sai ya dauki lokaci mai tsayi yana masa wasa, kusan rabin rainonsa dadyn shine yake, har tsarki saka pamoers, da sauransu ya iya.

Itama maryam tana Alfahari da miji kamar Abbas gani take itace mace mafi sa’a a duniya da tai dacen mijin, ta gama sadaukar da soyayyarta gareshi tana jin sa sosai a ranta, ta ko Ina yana basu kulawa ita da babynsu. Inna ko tun kan ayi arba’in ta tafi tace tunda maijego ta warke ai shikenan😄
Sun hada Mata sha Tara
ta arziki sannan suka kaita har gida.

 

*muke zuwa*

*by*

*Ummi Ameer*💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

*kuyi hakuri da jina Kwana 2 da bakuyi ba, uxuri ne yai yawa, ngd da kulawa*❤

 

*page* 1⃣3⃣

 

 

 

“”””sun kasance cikin so da kaunar juna, inda mufid sai girma yake har ya fara rarrafe yaron tubarkallah fine boy da shi.

 

Shekararsa daya daddynshi ya shirya mashi birthday aka Tara yan’uwa da abokan arziki domin taya shi murnar cika shekara 1, yasha gift sosai a wajen friends din iyayenshi, an sha hotuna abin sha’awa, har da Abbansa akai birthday din duk rabin pictures din yana rike da shi a hannunsa.

A wannan lokaci ne kuma ya samo mata admission a kano poly, diploma a Business administration, duk da cewa yaso ta samu tai degree dinta a b.u. k, tunda result dinta yai kyau sosai, Allah baisa ta samu ba. Tayi murna kwarai anyi mata fatan Alkhairi tare da samuun nasara, Abba ma yayi farinciki sosai.

 

************************

Har sun fara lectures, inda suke fita tare sai ya kai mufid wajen ummi sannan ya kaita sch. Ita kam ta dage sosai wajen karatunta ta maida hankali sosai, tare da taimakon Abbas, ware lokaci yayi yana fahimtar da ita inda take da matsalar fahimta da goyon baya. Ai kuwa bata samu matsala ba tana samun point din da ya kamata.

 

A lokacin da take shekarar karshe wato N. D2 kuma ta samu wani cikin bayan yaye mufid din da tayi, tana shan wuyar cikin sosai ga karatu, a daddafe ta samu ta kammala karatun, a lokacin cikin yakai watan haihuwa.

Bayan kammala karatun ba dadewa ta haifi diya mace son kowa, farincikin sa bai misaltuwa, yarinya tasha gata ta fannin sittturu da dai duk wani Abu da jaririya yar gata ke mallaka, komai dinta na daban ne, an sanya mata sunan mahaifiyarshi wato, Fatima bintu suna kiranta da elham.

Ranar suna an sha shagalin suna cikin kwanciyar hankali, mufid kuwa ya koma wajen dad dinshi tare suke kwana shine ke masa duk sauran dawainiya, wannan Karon ma inna ce ta kula da su da babyn, saida sukai 1month ta tafi, kasancewar ynx hatta da wanka baby maryam ta iya.

Bayan arba’in Elham ta Kara girma sai dai ba ta kai kibar mufid ba shi yayi kiba sosai don kuwa tana wahala wajen goyashi, ko a hannu yake yana gajiyar da ita, to ita kuma bata da jikisosai saffa-saffah.

Ba abinda ya canza soyayyarsu suna cikin kwanciyar hankali, tana kokarin gyara jikinta bata wasa da kanta, ko ta fannin gyaran gidanta da kwalliyah ma sai abinda ya karu domin cewa tai ita ko haihuwa goma tai bazata daina wa mijinta kwalliyah ba, akasarin matan yanzu kuwa Ana haihuwa daya sai kaga duk sun sukurkuce ba gyara jiki bare make-up a tunaninsu ai komai ya kare tunda ba wani sauran soyayyah.

Duk da cewa suma mazan duk irin kulawa da soyayyah da tattalin miji da suke samu wajen matansu bai hana su Kara aure in suka tashi yi.

Kamar yadda ta faru ga wadannan ma’aurata, maryam ta fuskanci wasu canjin halaye ga husbynta wasu lokutan baya dawowa gida da wuri in ta tambayeshi yace aiki ne yai masa yawa, amma bai canza mata ba ta fannin kulawa da nuna soyayyah, yana sonsu ita da yaranta.

A lokacin ne ya hadu da rukayyah har zance yai nisa, ta kai ga magana aure duk da da farko an fuskanci yan kabulabale daga wajen ita yarinyar da kuma mahaifiyarta kamar yadda na fada a baya.

Lokacin shekarar Elham biyu taji zancen aurenshi taji labarin aurenshi, hankalinta ya tashi sosai tai kuka, shikuwa ya kasa tunkaratta da batun gani yake bazai iya gaya mata ba abin yai masa nauyi sosai, itama wajen matan yaya taji maganar kuma sai da tai ta lallashinta kan cewa ta kwantar da hankalinta mijinta na sonta, ba wai don ya daina Sonta ne zai Kara aure ba, haka dai taita lallashinta.

Itakam duk tunani ya cika mata zuciya ta rasa dalilin da yasa zai Kara aure ta tsayatsaf tai nazari ko Zata gano wani abinda ta gaza masa da zaisa shi Karin aure, amma ta kasa gaza ganowa. Kuma har ila Yau bai fada mata ba, saidai ya fuskanci ta sauya masa ba kamar da ba, duk ta rame, kana ganinta kasan tana cikin damuwa, shima ya fara shan jikinsa ya fara zargin ko ta ji labari, wannan ne kesa shi zulumin gaya mata yana tsoron abinda xai biyo baya.

Aunty sadiya ko da taji labari murna tai tayi wai ai yanzu zai samu yancin kansa wai yarinya tabi ta asirce shi bai ganin kowa sai ita yar karama da ita sai kissa da kinibibi, su kuwa Duran yan uwansa basu ji dadi ba suna ta fadin yarinya mai hankalin da sanin girman mutane, kawai ya jajubo wa kansa kuma Sunji labarin gidan da yarinyar basu da dattako ga tsirfa iri-iri.

 

 

Ranar wata juma’a da daddare suna zaune gabadaya a falo tare da yaran yana tai musu wasa suna hawa bayanshi yana musu doki, amma ita ba walwala a tare da ita, shiko yana kallonta Jefi jefi. Tasowa yai ya zauna kusa da ita, yace my luv meyake damunki ne na fahimci kina cikin damuwa ki fada min meyake faruwa ne yana shirin riko hannunta ta fuxge, yace to ynx na gano ni nai laifin ko? Shiru tai masa ta tashi ta shige dakinta ta fada kan gado tana kuka, biyo bayanta yai a zuciyarsa kam yace tabbas taji labari, shiga dakin yayi tare da fargaba mai tarin yawa a xuciyarsa…

 

*muje zuwa*

*by*

*Ummu Ameer*💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

*Story&written*

By

 

*ummu Ameer*💃

 

 

 

*page* 1⃣4⃣

 

 

Tura kofar dakin yayi tare da fargabar mai tarin yawa, a kwance ya sameta ta kifa kanta da pillow, sautin kukanta na tashi kadan kadan, zama yayi kusa da ita tare da dagota ya jinginata ajikinsa tana ta kokarin kwacewa shiko ya matse ta gam ajikinsa, yace babynah wai meye ke faruwa ne kin canza min completely kinsa kanki cikin damuwa ‘why’? Dallara masa harara tayi tace ba ka san meke faruwa ba ko?
To tashi ka fita wlh banason ganinka ta fada da ihu, niii yau kike kora adakinki baby?
Tureshi tayi da karfin da bata san tana da shi ba, tare da fadin Abinda yafi hakama zanyima, ta tashi ta mike tsaye tare da juya masa baya, laifin me nai haka, ka tambayi wadda kake shirin kawowa gidanka,
Tashi yayi ya fuskanceta yace ki zauna muyi magana plx, kamo hannunta yayi Zaunar da ita ma shima ya zauna, zuciyarsa yana godewa Allah da yasa abin ya tsaya iya haka, domin kuwa yana jin labarin wasu matan fa insunji za ai musu kishiya suke tada hankalinsu tare da HAUKA iri-iri.

Dubanta yayi yace Ina son ki nutsu ki fahimci Abinda Zan gaya miki, a zahirin gaskiya aure nake nema ba don na gaji dake ba ko kuma don na daina sonki, ko kuma don na kuntata miki, hasali ma wlh har yanzu bansamu macen da nake so kamarki ba, ba abinda kika gaza min kawai dai aure kaddara in Allah yayi ba makawa sai anyi, wlhy bani da ra’ayin mata biyu a tsarina, kawai lokaci daya naji abin a raina, kuma insha Allahu zan kare miki mutunciki babu wani mahalukin da ya isa ya taka ki in kyaleshi, Kina da matsayi na musamman a zuciyata kece zuciyata, bani niyyar wulakantaki balle har wata taga fuskan da Zata samu ta raina min Uwar ‘ya’yanah, hakika nasan duk macen da mijinta xai Kara aure tana shiga wani hali, wasu ma har su so kauce hanya, suna jin ciwon abin sosai a arai, Ina mai Baki hakuri ki gafarta min, ki ci gaba da kaunar mijinki tare da faranta min kuma muyi Addu’a samun xaman lafiya gabaki daya, Allah ya sa Alkhairi ne, Allah ya kawar mama da sharrin dake ciki.
Ya kare maganar da goge mata hawayen da ke fuskanta, ya dubeta tare da tambayatta Ina fatan Kin fahimceni kuma kin hakura komai ya wuce, taji dadin kalamansa amma zuciyarta ta kasa yadda da cewa Anya kuwa bashi da wani dalilin yin auren ko ba zai iya fada bane, wata zuciyar kuma tace ai kinfi kowa sanin halin mijiki shi bai boye mata Komai ko wani abin tai da bai ji dadi ba yana fada mata bai barinsa a zuciyarsa ita kuma sai ta gyara, sauke doguwar ajiyar zuciya tayi tare da fadin na fahimceka mijinah Allah ya tabbatar da Alkhairi ya kuma hada kanmu gabadaya, wata kyakkyawar hug yai mata tare da fadin I know u my wiffy, nasan bazan samu wata doguwar matsala daga gareki ba nasan kina da hakuri da juriya tare da hankalin yan shekaru 40 wannan ne yasa kullum kike Kara shiga zuciyata ngd uwar ‘ya’yana Allah ya Kara mana so da kaunar juna tare zaman lafiya mai dorewa har Abada, I luv u tare da manna mata kiss, dubansa tayi tare da gasgakata zancensa tace husby nah Ina maka fatan cika Alkawarin da ka dauka zan taya ka da addu’a domin zama adalin miji, Allah ya sanya Alkhairi. Yace Ameen! Bai bar dakinba saida suka sha soyayyah.

Sun manta da yara a falo, sukuwa yaran sunyi wasa har sun gaji anan bacci yai awon gaba da su, yace very sorry my kids naje Ina lallashin momynku, daukar mufid yayi yaje ya kwantar da shi a dakinsa ita kuma ta dauki Elham.

 

 

****** ****** ******
Koda su ummu suka ji labari abin ya dan taba mata zuciyah amma daga bisani ta fawwala wa ubangiji tare da yi musu addu’ar samun zaman lafia yasa kuma Alkhairi ne,

Akwai wata rana da maryam taje gida ummi duk taga ta dan rame ta yi duhu tai ta yi mata nasiha kan ta kwantar da hankalinta ba komai sai Alkhairi shima Abba yai mata nasiha tare da yi musu fatan Alkhairi amma a zahiri yaji tausayin diyarsa, duk cikin ”ya’yan ita Allah ya kaddarawa za a mata kishiya, Addu’a yayi musu.

Zainab ma da taji labari ta taya kawarta kishi, itama tai aure tana da yarinya guda 1, har gida tazo tai ta lallashinta duk da ma ta fuskanci tana da saukin KISHI, don ta fahimci ma bata wani damu sosai ba, tace kawata wlhy Ina tsoron kishiya duk ran da Abdul yace zai min bansan wane irin hali zan shiga ba wlhy domin ko amakota ne naji anyi wa wata kishiya karkiso kiga yadda nake taya su kishi, to bare a Kaina kuma, gaskiya kawata kin burgeni samun kamarki da wuya, tace ai dole in rungumi kaddarata, kinsan Dama shi aure ko wanne da irin matsalar ni dae fatana Allah ya hada ni da ta gari shikuma Allah ya bashi ikon rikemu da amana, wata shewa zainab ta saki tare da tafa hannaye tana fadin yayi kawata Allah ya sausaauta min kishi na kamar naki. Ameen maryam tace. Haka suka yi ta hirarsu har Abbas ya dawo suka gaisa tace ai tafiya zatai ya bata transport ta bata sukai sallama ta tafi, itama tawuce wajen mijinta domin tarbarsa.

Shiko ko yaushe cikin sanya Mata Albarka yake, da godiya ga Allah da ya bashi mace kamar maryam a matsayin Uwar ya’yansa.

Duk wani shirin auren da akeyi bai boye mata komai ba inda shaida mata sauran satin biyu ynx, har gidan da ya Kama haya sai da ya gaya mata kuma ya shaida mata yana sa ran zasu samu fahimtar juna domin itama bata da hayaniya kamar ita kusan halinsu daya, tace Allah yasa.

Ita ma an kawo mata kayan fadar kishiya duk wani Abu da ya sawa Rukayya itama ya sanya mata shi sannan ya canza mata furnitures, ya bata kudi ta sayi duk abinda take bukata.

Itako ba abinda tai da wannan kudi sai gyara domin cewa tayi sai ya kasa tantancewa, hafsa ta sa ta rakata taje ta kwaso English wears na neman tsokan dama ita gwana ce wajen sanya su ko don sunayi mata kyau ne oho! Don ita ka’ida ne kazo gidanta cikin kananun kaya take Da yamma ko dare, Suna mata kyau sosai shima yana son ganinta dasu sbd suna gigitashi, shima da kanshi in ya ga wadanda suka dace d ita yakan sayo mata, Ita duk abinda tasa ma yana mata kyau ta iya daukar dressing.

 

 

 

*ku biyoni domin cigaban labarin*

 

*by*

*ummu Ameer* 💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

 

*Story&written*

*by*

*ummu Ameer* 💃

 

*page* 1⃣5⃣

 

*cigaban labarin*

“”””””Saura 2weeks biki inda ake ta shirye2 anje an gano gidan amarya, sai da mommy tasa ya samo gida wajen 4 tana cewa bai yi ba sai a na katshen ne yarinyar tace ita yayi mata haka, hakanan ta hakura amma ba don ta so ba Uwar.

Ba karamin gyara yayiwa gidanba domin komai kusan sabo aka canja, gidan kuma yayi kyau sosai da ya sha gyara, gashi da girmansa, babban falo da 3bed room sai kitchen Babba a falon. A zoo road gidan yake.

 

Amarya kuwa sai gyaran jiki ake mata kusan 1month Ana yi, itama mommy hakanan ta saduda ta hau gyaran diyarta tare da sihirinsu da suke ma ‘ya’yansu in sun kusa shiga gidan miji domin kamashi ahannu.

Bangaren maryam kuwa tunda taji labarin mahaifiyar yarinyar ta shiga damuwa domin tana jin labarinsu in suka Auri miji fa to kishiyar ta shiga uku, domin mijin ma shakkarsu suke bare wata kiahiya, inko su aka fara aura to bai isa ya kara wata ba, ko da yayi ma to Zata yi gaba don azaba, duk da ba Dina aka taru aka zama daya ba, don kafin tai aure akwai neigbour dinsu yar maiduguri mijinta zai Kara aure, sbd bakin kishi ta kwance masa burkin mota, sai gawarsa,

Kukanta ta kai wajen mahallicin ta akan ya kawar da duk wani sharrin da ke ciki, ko bacci bata samu sbd nafilfilun da take yi da daddaren gashi ko yaushe cikin Azkar take.

 

Tuni an rarraba invitations har da na dinner, da farko Abbas din bai amince ba sai da Uwar ta ce ai ya zama dole ya shirya dinner, ba makawa, haka nan ya hakura ya amince ba don yaso ba, yana mamakin wannan karfin hali nata, tuni auren ya fara sure masa yana shakkar abinda zai biyo bayan auren ya na tantama akan ko zai iya jure halayen surukarsa, har fara ganin laifin kansa akan Karin auren da yake shirin yi, ba wani Abu da zaiyi sai ta Nuna bai mata ba, ya fara surewa da lamarin, domin tun kafin maganar tayi nisa ma yaso janyewa, ita kuma yarinyar ta shiga damuwa taita bashi hakuri akan halin mahaifiyarta, tana matukar kaunarsa, domin kuwa bazata iya hakura da shi ba gani take in ta rasa Abbas kamar ba zata samu kamarshi ba tana matukar kaunarsa, ko kiranta in baiyi ba sai ta shiga matsanancyar damuwa. So, halin da zai jefa ta in suka rabu ne kawai yake dubawa, kuma ko ba komai shima yana sonta. Shiyasa kullum yake Alfahari da iyayen maryam samun sirukai masu dattako kamarsu da wuya.

 

**** ***** *****
Itama maryam bai barta abaya ba, an gyara mata gidanta an yi Mata fenti da sauran gyare-gyare, ranakun biki nata matsowa, sai dai ba rawar kai Abbas kamar na maryam, har friends dinshi ke tsokanarsa wai baiyi Adalchi ba, shiko yace ai duk wani Abu na farko an fi Nuna doki da zumudi.

Gidan Amarya tuni sun fara gudanar da shagulgulansu tun ranar laraba, inda suka bukaci zuwansa amma fir yace yana da uxuri, hakan kuwa ba karamin bata ran amarya yayi ba, ganin irin bacin ran da ya nuna ne yace bayan magriba zai xo, sai a lokacin ta Dan ji dadi a ranta, ko ba komai yaxo yaga kwalliyar da ta sha…

Wata laffaya ta sanya lemon green ta sanya kananun kaya aciki, sai wata tafkekiyar sarka da ta sanya awuyanta ga wata ta sanyae a gaban goshi tayi kyau sai kunshin da ta sha a kafafuwa da hannaye, sai awawaraye duk an kusa cika hannayen da su sai wani takalmi mai tsinin gaske da ta sanya tare da wata karamar purse kamar ball, ta rike a hannunta, suna ta gudanar da Al’adarsu.

Abbas ko sai da ya koma gida YaI wanka Yai sallar magriba, ya shaidawa maryam zaije gidansu Rukayyah akwai program din da sukeyi Yau, sun bukaci zuwana tun daxu bansamu dama ba, shine zanje yanxu ba jimawa xanyi ba, kinji baby, rau-rau tayi da idanuwa a xuciyarta tace yanzu har ya fara zama nata kenan, nan da nan kishi ya turnuketa, sai dai bata bari ya gane ba, ta danne ta ce shikenan husbynah Allah ya tsare hanya, sai ka dawo, yace Yau ba rakiyar kenan binshi tai har bakin motor ita ta bude masa kofar ya shiga ya ruko hannunta Yai kissing dinshi, sannan yace na gode my lovely wife, samun kamarki da wuya Ina Kara godewa ubangiji da ya mallakamin ke, ita ko kawai murmushin yake take yi da bai kai zuci ba domin ta fara kasa danne kishinta ayanxu, tace masa a dawo lfy, sannan ta juya domin komawa cikin gida, tana shiga ta fada kan kujera tana kuka tace daga wannan satin mun zama mu biyu kenan a wajen mutumin da nake kauna fiye da komai Anya kuwa zuciyata zata ita jure ganin Abbas da wata matar, Anya kuwa zan iya! Sai alokacin ne tace dama tana da irin wannan kishin, ta dade a wajen tana ta tunanin abubuwan barkatai, daga bisani ta tashi taje tayi alwala domin gabatar da nafilfilin da addu’o’i ko ta samu saukin halin da take ciki.

 

 

*Allah sarki maryam sai munxo dannar kirji.. **😜

 

 

*by*

*ummu Ameer*💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

*naji sakonku masu cewa bai kamata aima maryam kishiya ba, Ina so ku gane wani Abu readers da kuma writers din tunda nake karatun novel ban taba ganin inda akayi ma tauraruwa littafi kishiya ba sai dai ace ai tursasa masa akai ko makamancin haka, amma ba ason ranshi ba, ni kuma abinda nake rubatawa a littafina kusan abinda yake faruwa ne a zahiri, domin Kuwa mazan yanzu kusan duk irin so da kauna da kulawa da haduwarki wajen gyaran jiki ko shan magunguna duk wannan bai hana su yo miki kishiya kusan ma sun maida abin kamar gasa, a zahiri akwai wadanda basu da ra’ayin mata biyu, wasu mazan kuma kawai ra’ayine suna son suga sun mallaki fiye da mace daya, amma a Hausa novel kullum wannan tauraruwa ita ce farko itace karshe Wanda a zahiri ba shine abinda yake faruwa a cikin Al’umar ba, ni dai fatana mu writers mu dinga kokarin isar da sakonin abinda zai amfanemu Baki daya ta hanyar kawo gyararraki a zamantakewar ma’aurata da masu shirin shiga gidan miji kuma shi wannan Karin aure ba wai yana nufin ya miji ya daina kaunarki bane, duk da cewa akwai mazan da suke da matsala da matayensu ta rashin tsafta ko rashin iya kula da miji ko rashin iya girki ko rashin bawa miji hakkinsa ko rashin gamsar da miji wadannan ma suna taka muhimmiyar rawa wajen jan ra’ayin miji ya kawo miki abokiyar zama, Ina fatan kun fahimceni, ngd*
*Allah ya bar zumunci*🤝

 

 

*story&written*

*By*

*ummu Ameer*💃

 

 

*page* 1⃣6⃣

 

 

“””” Abbas yana hanyar
zuwa gidansu Amaryarsa, amma sai jin wani muguwar faduwar gaba yake, sai “innalillahi wa inna ilaihirraji’un”yake ta ambato har wata zuciyar na ayyana mishi kawai ya koma gida, wata zuciyar kuma na bashi kwarin gwiwar zuwa har zai biya ya dauki abokinshi Yusuf su tafi tare kuma ya fasa gudun kar in-law din tashi tai wani abin maganar da ta saba, yana tuki yana ta sake-saken aranshi har ya iso gidan, tun daga waje yake jiyo qamshin turaran wuta kasancewar Yau ranar turarence, kusan kowa yana dauke da kaskon turare a hannunshi dauke da garwashi aciki, an zuba turaren a ciki ko wane da qamshinsa sai rawa suke suna waka da yarensu, hakan ne yasa daga waje ake jiyo qamshin turaren, can gefe kuma ga wani katon kasko a gefe shi wannan kuma da zarar ango ya bayyana a wurin ake zuba turaren da wata laya a cika, to dazarar anyi hakan tun daga lokacin zai dinga yi mata wani irin so tare da shakkarta.

Kiranta yayi a waya ya shaida mata ya iso, nan da nan ta Kara gyara make-up, ta fito domin shigo da shi ciki, dama a harabar gidan suke ta shagalinsu. Tafiya take kamar tana tauayin kasa ga takalmin data sanya mai tsinin ba iya tafiya tai dashi sosai ba, shiyasa take tafiya a hankali, shiko yana jingine jikin motar ya harde hannayensa,sanye yake da wata dakakkiyar shadda blue tai masa kyau sosai da hularsa itama blue sai faman qamshi yake zubawa, sai murmushi yake mata, itama haka,tuni ta Kara jin wani irin sonshi na Kara shigarta a zuciya tana zuciyarta fal da farincikin ta kusa zama mallakinsa, matarsa kuma Uwar ‘yayansa inshaAllah, tana isowa tai saurin jingina da motar tana maida numfashi, yace lfy dai? Wlhy baby takalmin nan ya wahal dani tsiininshi yayi yawa, yace to meyasa kika sanya shi ko so kike ki wahal min da kanki, tace banma yi tafiya da shi ba tunda na sanya Ina zaune kan kujera, bayan sun Dan taba hira tace baby mu shiga ciki hannunshi ta rike suka shiga tun dosowarsu aka kunna wannan turaran na musamman da aka tanada domin shi, sai faman guda suke suna kowacce da kasko ahannu suna binsu suna waka, bayan sun Dan zauna ba dadewa aka fara pictures ko wanne tana makale da shi ta rike shi kamar za’a kwace mata, anan ma saida uwar tace akwai wani dan akwati da angwaye duke zuba kudi yana daga cikin Al’darsu sai da ya zuba kusan 70k Allah ya so ya taho kudi, amma ita yarinyar bata son abinda mahaifiyarta keyi, har wajen karfe goma yana wurin amma duk an watse, sai friends dinta a gurin, shima yace zai wuce gida tace haba baby tun yanzu baka zo fa da wuriba, yace ai dai nazo ko, na fita ko ba sabulu, tace to muje na raka ka mota, tare suka jwra har zuwa gurin motar tashi, ya shiga ya zauna ita kuma tana rike da murfin kofar tace amma baby gaskiya banso zaka tafi yanzu ba, ban gaji da hira da kai ba yace Saura Kwana nawa ya rage duka ki tare a gidana kiyi hakuri kinji luv! Tace to shikenan baby Allah ya Nuna mama wannan rana yace Amiin! Tace amma baby mai yasa baka zo da friends dinka ba, yace suna da uxuri ne shiyasa.
Tace okay!
A gaida gida ka kula min da kanka plx!
Yace insha Allah!
Kunyi kyau Amaryata
Nan aka hau juya idanuwa tare d fadin tanx angonah!
Kunna motar yayi zai tafi itako sai faman daga masa hannu take tana masa bye! har sai da motar ta bace, sannan ta juya Zata koma ciki.

Zuciyar ta fal da kishi aranta wai yanzu Ma haka sauri yake ya koma wajen matarsa shiyasa ya damu ya koma, mtsss tsaki tayi aranta tace Ina tunanin Randa zan budi ido in gansu tare da ita zuciyata fashewa zatai don kishi, Ina ma ace ni ya fara aura da bai isa yayi tunanin wata ba, ni mai ya kaini in ba don son da nake masa ba ma, Ina zan auri mai mata, amma ba komai tunda gidana daban zan samu saukin kishin..

*Anya kuwa*?

 

 

Shikuwa a hanya motarsa ta samu matsala tayar motar tai faci gashi duk masu gyaran sun tashi sbd dare ya fara yi, yana tsaye a wajen yana tunanin abinyi, can ya dialing no musa da yake masa gyaran mota, ya shaida masa motaraa tayi faci ya taho masa da spare ya bar tashi gida, nan da nan ko ya garzayo ya taho duk da cewa yana gida alokacin.

Sai kusan 11;20pm aka kammala yace musan ya shiga ya rage masa hanya, azuciyarsa ko baiji dadin delaying din da ya samu ba, don yasan maryam zatayi tunanin ko yana can tare da amarya duk da yasan tana da saurin fahimta, amma shi bai son bacin ranta ko kadan, bashi ya iso gidaba sai to-12.

 

Maryam kuwa ranta ba karamin baci yayi ba ta Hama kufuluwa tace tun yanzu har an fara haka daga cewa ynx zan dawo had yanzu shiru, gashi ta kira wayar tana ta ringing bai dauka ba, shiko ya aje ta a motar sanda ake canja tayar, kuma ko da ya shiga bai duba ba, itako batai tunanin komai ba sai suna tare soyayya ta debeshi ya kasa picking call dinta abinda ya Kara kular da ita kenan,, tayi kukanta har ta gaji bata san ma lokacin da bacci Yai gaba da ita ba.

 

 

 

*muje zuwa*

 

 

*by*

*ummu Ameer* 💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

 

*story&written*

*By*

 

*ummu Ameer* 💃

 

 

*GODIYA MAI YAWA DA COMMWNT DINKU, ALLAH BAR ZUMUNCI* 🤝

 

 

 

 

*page* 1⃣7⃣

 

 

 

“”Bayan isowarsa gida yayi ta knocking ba’a bude ba, motar ya koma ya dauko spare key din ya bude gidan ya shiga, ganinta yayi a kwance kan 3seater, tana bacci, da alamu baccin bai dade da kwasheta ba, murmushi yayi a zuciyarsa yace Allah sarki wiffy, nasan da bacin raina kika kwanta, lekawa yayi daki inda yaran suke suna bacci, gyara musu kwanciya yayi, yai musu Addu’a, ya sumbace su a goshi yace gudnyt my lovely kids.

Fitowa yayi falon ya tarar bata da niyyar tashi, key din motar sa ya dan sa mata a kunne yana mata susa da shi, firgigit ta farka tana subhanallahi, ka bani tsoro wlh, sai ya yanxu ka dawo daga wajen amaryartaka, ai nazaci can zaka kwana ta karashe maganar da wullah masa harara, ta mike xata shige daki ya janyota ta xauna a cinyarsa, yace wlh baby Motana ne ya samu matsala wajen 2hrs na bata akanta, ba wai da gan-gan nai ba, ayimin afuwa, tace Amma nai ta kiranka kaki picking, why?
na bar wayar ne a mota.
Shikenan! Ta bashi amsa.

Muje kan dining kaci Abinci ba musu ya bita tai saving nashi, yace lallai in tana so yaci sai ta bashi, hakanan ta ringa bashi, yana ci yana santi, har ya koshi, tace ya Amaryar?
Yace tana gaisheki, sun dan taba hira daga bisani suka je suka kwanta.

 

*washe gari*

Ranar Alhamis kenan itace ta Kama Ranar kamu, ‘yan danbatta ma sun taho bikin a Ranar, gidan yaya suka sauka, sai daga baya ne sauran ‘yan’uwan suka leko gidan maryam din ta karbesu hannu biyu, kuma ta burgesu ganin ba wani damuwa da ta sanya aranta, akasin wasu matan da in Ana bikin mijinsu ko kallon arziki ba suyi yan’uwan mijin suna ganin kamar su suka Sanya shi. Hirarsu sukai tayi har wajen la’asr, Amma anty sadiya tana can gidan yaya bata karaso gidanba.

Angon ne yayi waya da misalin karfe 5:pm, yace zai zo ya kaisu gidan amaryar kamu, jimawa kadan sai gashi ya fara dauko aunty sadiya da matar yaya, sai yayar mahaifinsu da sauran yan’uwansa.

 

Suna isa ya sauke su ya nuna musu gidan ya wuce daman mota 2 sukai, da ta yaya sai kuma tashi yace zaije ya dawo, suna shiga gidan sun tarar da gidan makil da jama’a sai shagali suke, suka bayyanah kansu cewa dangin ango ne sunzo kamu, ba wani tarbar arziki da sukai musu sai wani kallon wulakanci suke musu, kowa sai binsu yake da kalloh, suna ta yin yarensu, aka kawo musu wata jallof fara fat da kuma zobo an kullah a leda don wulakanci, sannan suka ce suyi hakuri tuni an yi kamu, itako aunty sadiya an sa rai za’aje aci kaji, ba karamin haushi ta ji ba, haka suka dauko jiki suka fito jiki a sanyaye, sauran yan’uwansa na fargabar abinda Abbas ya debowa kansa, don ita uwar amaryar ma ko kula su bata yi ba, sai wani kallon kyama take musu, tana mai jin haushin ‘yarta da ta kwaso musu tarkace, dogon tsaki tsaki ta ja tayi shigewarta daki, sai aunty salma kanwar momynce ma ta sauraresu.

Suna fita suka ganshi ya dawo suka shiga mota suka wuce a hanya ne daya daga cikin yayunsa tace nikam Abbas me ya kaika kwasowa kanka irin wadannan mutane da basu san mutumcin dan Adam ba, wata acikinsu ta Kara da fadin ai ka ci gaba da kula da matarka Domin samun kamar maryam da wuya, daga ganinta Kasan ta fito gidan tarbiyya kayi dace da matar kwarai ka riketa amana ga hakuri yarinyar arxiki, yace gaskiya kam maryam ta dabance tana da hakuri, itako aunty sadiya ta6e Baki tayi ba magana.

Yace anty wani abun sukai mukune, suka a’a Amma dai gidan ba karamci a cikinsa.

Hira sukayi tayi har suka ISO cewa sukai ya wuce da su gidan yaya karsu takura musu, ga yara karsu isheku da kiriniya.

 

******* ****** ********
Bangaren gidansu amarya kuwa Mommy ce a daki ita da aunty batula, mommyn na gaya mata wai ita wlh Addu’a take Allah ya kawo sanadin da auren nan zai ruguje na tsani auren banso ko kadan, duk cikin yarana ba mai taurin kai irin Rukayyah da taji maganata da ba a kai ga haka ba, aunty batulu tace ai sai dai ki hakuri yar’uwa, abinda zamuyi ynx shine mu gina diyarmu, shine kawai
Kwafa mommy tayi,
Aunty batulu tace taso muje cikin jama’a kar azo Ana neman uwar amarya. Fitowa sukai da kaya iri daya suka sanya ita da kawar ta, suka cigaba da gudanar da shagalinsu na kamu, ita amaryar ma bata san cewa dangin Abbas sunzo ba, kuma tasan halin mommy da kyar in bata yi musu halin nata ba. Yau kuma amaryar sanye take da wani tsadadden lace, pink Riga da zani tayi karamar buba mai dogon hannu ta dora zanin akai sai blue head ta aka jera masa stones da takalmi blue sai irin maficin da amare ke rikewa, an mata make-up, tayi kyau ba laifi.
Dama tun safe sukai waya yace bazai samu xuwa ba, sai dai Ranar dinner.

 

 

Yau juma’a itace Ranar dinner tuni dama Abbas ya bada odar komai da komai a inda za’ai dinner din, na mutum 150.

Ba yadda baiyi ba akan maryam ta shirya suje Amma kememe taki tace ba inda zani.

Karfe 7:30pm tuni an fara kwasar kawayen amarya da sauran yan ‘uwa xuwa wajen, amaryama ango take jira ya iso su tafi, tayi kwalliyah cikin wata doguwar riga orange color head dinma haka, rigar tana jan kasa.

Ango kuwa yana can shima ya shirya cikin wani tsadadden boyel fari, sunyi masa kyau ya feshe jikinsa da turare mai qamshiii, maryam tace kayi kyau angon Rukayyah, yace ita Kadai, tace a yanxu ba, ai mu namu ya wuce, yace a wajenki ba, Kiran amarya ne yai ta shiigowa tun yana dauka har ya daina waii Ana ta jiransa, maryam tace muje na raka ka mota ka tafi, yau ma har mota ta rakashi sai dai yau da abokanasa guda biyu a motar suna ta yabawa madam din tashi ta burgesu da rashin nuna kishinta, sauran abokanan nashi kuma duk sun wuce daukan kawayen amarya xuwa wajen dinner.

Suna isa ya kira ya iso, aka taho da amarya aka bude mata bayan mota ta shiga kusa da angonta, sai Yusuf dake jan motar sai Ahmad dake kusa da shi,

Wajen dinner ya cika a haka ma an hana wasu shiga sbd in baka da gate pass, ba zaka shiga ba, uwar amarya da kawayenta ma duk an hallara sunyi ankon lace blue ita da kanennta da batulu itama aunty nusaiba matar babansu taje, Ana ta gudanar da programs din da suka shirya, an yi hotuna amarya da ango sunsha pic, ko wanne sai ta kwanto jikinsa, sun dauka, sunyi da uwar amarya da kawayenta, bayan ciye-ciye da akayi an taka rawa inda amarya da ango suka fito, amarya ta zake sai rawa take tana rike da hannun ango, shiko ba wata rawa da yayi shi kunya ce ma ta kamashi ga surukarsa itama ta zake da kawaye sai rawa suke Ana musu liki, fita yayi daga filin rawar yaje ya zauna yana mamakin surukarsa, wayewa ko zamani?

 

Sai kusan 12pm aka tashi ya maida amarya gida shima ya wuce yayi ma friends din shi godiya da ban gajiya, dama bai gayyaci yan’uwansa ba ko daya.

 

 

Ranar asabar AKa daura auren Dr. Abbas mukthar danbatta. Da Rukayyah usman. A masallaci. Akan sadaki naira 50k.

Kuma aranar ne za’a kai amarya gidan mijinta, itama maryam a Ranar har da shirya walima ta gayyaci kawayenta da yan’uwanta. Kada mai karatu kaso kaga yadda ta hadu cikin wani tsadadden code lace red, tayi kyau ba kadanba don ko amaryar sai haka kasancewar ta iya dressing ko yaya ta sa kaya yana amsar jikinta, anci ansha a wajen walima inda mai lecture da aka dauko tai tayi musu nasiha mai ratsa jiki, tare da shawarwari akayi ta Mata godiya.

 

Su Aunty Aisha ma wato yayun maryam sun yi Mata nasiha da shawarwari da kuma addu’oi da zata dinga yi, kuma suna ta yabon kanwar tasu ta burgesu bata dorawa kanta bakin Kishi ba.

Gidan Amarya kuwa sai a lokacin ne ake mata jere itama ba laifi an mata kaya gwargwado, duk da wasu abubuwan shi aka dorawa yi.

Tuni motocin daukar amarya sun ISO gidansu amaryar Ana ta divan mutane.

*mu hadu gobe insha Allah*

 

 

*By*

*ummu Ameer* 💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

 

 

*story&written*

*By*

 

*ummu Ameer* 💃

 

 

 

*page* 1⃣8⃣

 

 

 

“””An kai Amarya gidan Angonta, cikin wata laffaya green color ta Sanya ta sanya Riga da wando a ciki, ta sha kwalliyah sai da aka turara kayan da turaren kaya, gidan cike yake da mutanensu basu da niyyar tafiya. Itako Amarya ta kosa angon nata ya bayyanah.

 

Can wajen maryam kuwa itama shigar Riga da skirt tayi na atamfa yellow mai ratsin green, kayan sun Mata kyau ba kadan ba, itama tana tare da kawayenta da sauran yan’uwanta sai makota, sun tsaya domin su karbi amarya, a tunaninsu za’ai fara kaita gidan uwargida kamar yadda aka saba, ko da Abbas din yaima ‘yan’uwanta magana akan su fara kaita wajen abokiyar zamanta, cewa sukai ai ba itace ta auro musu diyarsu ba inda zasuje, in ita amaryar ta ga dama taje daga baya, ko kadan Abbas baiji dadin haukan ba yana mamakin rashin halin dattako irin na wadannan bayin Allah, shiko ba inda ya tsaya sai gidansa wajen uwar yaransa, Dama Already ya sanar mata a waya amaryar ba Zata samu xuwa ba, sai daga baya, tace ba damuwa ai kasan kowa da irin tsarinsu, itama ta sanar da wadanda ke jiran tarbar amaryar kowa ya Kama gabansa, zainab ko taso ta tsaya ta ga amaryar, haka nan ta tafi sai da ta Kara lallashin maryam da ban Baki, domin ta fuskanci ta fara shiga wani yanayi.
Duk an watse a gidan daga ita sai hafsa sai ‘yar yayarsa khadija kusan sa’ar hafsance jininsu ya hadu shiyasa suka kulla abota da juna, sune suka tsaya Domin taya maryam din kwana.

Sun gyara mata ko Ina sun turareshi ko gidan Amaryar sai haka.

Shikuwa Abbas da wani wanda zai dinga yi masa gadi ya taho kasancewar ynx ba ko yaushe zai na kwana agidanba, yana isa ya nuna masa masukinsa, ya kuma bashi amanar kular masa da gida, yana shiga gidan bai tadda ita a dakinba, sai su hafsa a zaune suna kallon Arewa24, gaisheshi sukayi, ya amsa yace bakuyi bacci ba, sukace eh!

Tunda bai gantaba anan ba yasan tana daki, direct ya shiga ko da ya shiga a zaune ya sameta tana latsa wayar hannunta Amma kana ganin yanayinta kasan tana cikin wani hali, sallama yayi mata tace sannu da xuwa, yace yawwa my wiffy, zama yayI sun Dan taba hira yana mai kwantar mata da hankali, itako tuni idanuwanta sun cika da hawaye tana tunanin yadda Zata fara wata sabuwar rayuwar, mijin da yake mallakinta ita kadai a yanxu ya zama mijin mata2.
Ganin dare yanayi ne ya kasa tafiya, tace husby ka tashi ka tafi dare yana yi, shiko dama ya kasa fadi ne, tashi yayi yaje inda yaran suke bacci yai musu Addu’a ya fito yaje dakinsa ya dauki wasu daga cikin kayansa da dan abubuwan da zai bukata ya zuba a wata trolley, ya kashe wutar dakin ya janyo kofar shima ajikinsa duk sai yaji wani iri! Duk jikinsa yai sanyi itako dama tana zaune inda ya barta tuni ta fara kuka, shima baisan sanda kwallah ta fara zubar masa ba a Sauri ya karasa inda take yana lallashinta, rungumeta yayi yana lallashi kamar yarinya, yace kiyi hakuri baby Nima ba yadda zanyi ne, am very sorry!
Ki gafartamin halin da na sanya ki ciki, nasan kin yi iya kokarinki wajen kiga kin danne damuwarki Domin ki faranta min, nayi miki Alkawarin ba abinda zai canja daga gareni, kiyi min Addu’a Allah ya bani ikon adalci tsakaninku, matsayinki na nan daram a xuciyata, sai ma karuwa yake sbd kyawaqan halayenki, rufe masa Baki tayi tace ya isa haka tashi ka tafi karka shiga hakkinta, tare suka fito ta rakashi bakin kofa sukai sallama, ya hugging dinta tare da manna Mata kiss, sannan ya tafi sai da ya ya tabbatar fa lafiyar komai na gidan ya kulle ya tafi…,.

 

 

Can gidan Amarya kuwa amarya ranta ya gama baci da rashin isowar ango har yanzu, tasan kuma yana can wajen matarsa tsaki tayi tace illar auren mai matar kenan.

 

 

 

 

 

 

Bai je da kowa ba shi kadai ya tafi wurin amaryarsa gudun kar ayi wani abin magana, aikuwa da isarsa gidan ya tarrada sauran ‘yanuwanta a gidan wai taya Amarya kwana🤔 yana shigowa suka bishi da guda sa’annan wasu kawayenta 2 suka Hans shi shiga wai sai ya banda kudin sayan baki, hakanan ya fito dash ya basu baima kirga ba, yana shiga ya sameta ta rufe fuska da laffayar da ta sanya, sallama yayi, ta amsa masa, yaita magana tai shiru ita adole fushi take yaje yai zamansa wajen matarsa, yace, ko maganar ma sai na saya amarsu, tace kaida ka tafi can ka manta amaryar taka, yace ayimin afuwa!
Tace anyi tare da bude fuskarta.
Yace bark na watsa ruwa ko na samu saukin gajiya,
Tace gaskiya kam, bayan ya fito ya sanya jallabiya saukai sallah suka ci naman da ya taho dashi, daga bisani ya je rufe gidan. Ba abinda ya shiga tsakaninsu sbd bakin dake gidan, amma bacvinau sukai manne da juna.

 

 

Bangaren maryam kuwa bacci gagararta yayij a wannan dare sai faman juyi take sai kusan 3na dare bacci barawo yai awon gaba da ita.

 

 

 

Washe gari da safe ya shirya tsaf zai je kai mufid school, tace baby wai Ina kake shirin zuwa da safennan, yace zan kai mufid school ne, adawo lfy tace, tayi tayi komawarta daki cike da jin haushi, tana shiga kuwa tace aiko bazai yiwu ba, ya bari in yana can ya dinga kaishi amma hakan ba mai yiwuwa bane.

 

Bayan fitarsa ne yan’uwanta ke tambayar Ina zashi haka ta fada musu inda zashi, zugata suka hau yi wai sai ta yi da gaske wannan matar ta gama dashi in bahaka ba ya za ai yana nan ace lallai sai je ya kai taro makaranta, ita me takeyi uwar da bazata kai shi ba, haka dai sukayi ta zugata, daga nan kuma wasu daga cikinsu suka hau hada breakfast.

 

Yana isa gidan ya tarradda an gyara gidan tsaf ko Ina fes sai qamshi ke tashi, ko gidan Amaryar ma ba sharar da akayi balle kunna turare, itama maryam din tayi kwalliyarta, daman ita ka’idane da asuba take wankanta tayo alwalarta, bata taba bari ya fita ba tare da kwalliyarta ba, mufid yana ganinshi ya tafi aguje ya rungumeshi yana Tambayarshi daddy Ina kaje banganka ba tun jiya yace, ai gani yanzu, dauki bag dinka mu tafi sch.
Hannu ya mikawa maryam suka gaisa yace Ina fatan ba wani matsala, babu tace masa, lakuce mata hanci yace really? Daga masa kai tayi yace ok zan kaishi sch. Anjima zan dawo tace Allah ya kaim

By

Ummu Ammer💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

 

*story&written*

*By*

*ummu Ameer* 💃

 

*page* 1⃣9⃣

 

 

Bayan duk bakin dake gidan sun Tafi, daga Amarya sai angonta, Amarcinsu suke ci hankali kwance, Amma ko kusa maryam tayi mata zarra, inda kuma duk wani abinda suka shirya a kansa yake tasiri a hankali akansa, don ma mutum ne da baya sake da addu’oi, ga addini, kuma tsayayyen namiji ne, amma duk da haka a ynx wani irin so yaji yana Kara yi mata idonshi ya rufe akanta, tunda ta fara girki rufe ido kawai yake yi yana ci, gudun kada ranta ya baci, ga rashin tsafta, sbd mugun son jiki ne da ita, ita dai barta in ta gyara kanta shikenan, hatta da bed room dinsu wata ran haka take yini sai ya mata magana sannan ta gyara, an saba da rashin aikin tun agida, abubuwa yai ta gani kala-kala kawai daurewa yake yi, a daddafe yai sati guda kamar yadda aka saba, amma kullum sai ya je wajensu maryam ya duba lfyrsu da ta yaransa, safe da dare, haka kai mufid sch. Kullum ba fashi, Randa zai bar wajen Amaryar kuwa naga kirsa da kisisina dauke hankalinsa tai tayi da salo na kissa da yaudara wai ita bazata iya Kwana ba tare da shi ba, da kyar ta samu ta sake shi da sharadin sai ya dauko mata kanwarta da kuma junior, haka kuwa akayi sai da yaje ya dauko mata su, bashi ya bar gidan ba, sai kusan karfe 9 na dare.

 

Itako maryam Ana can Ana ta shirin tarbar miji tun yamma, amma shiru abin ya sosa mata rai, kuma taki kiran wayarsa, bashi ya iso gidan ba sai kusan 10 na dare yara kuwa tuni sunyi bacci har sun gaji da jiran daddynsu, taci kukanta ta koshi, har ta fidda rai zaixo, sai ga horn din shi, dama duk sanda ya dawo sai yayi horn su kuwa yaran suna jin horn din shi zasu tafi a guje suna daddy oyoyo! Wata ran ma har da ita ake zuwa tarbarsa, tana jin horn dinsa tai sauri ta gyara fuskarta da powder ta Kara fesa turare, fitowa tai ta zauna a falon tana jiran shigowarsa, sallama yayi ta amsa tare da yi masa sannu da zuwa, fuskarta ba yabo ba fallasa amma bata wani sakar masa fuska ba, sai Abin hannunsa da ta amsa, yace baby, yau ba kiyi hakuri wani uxuri ne ya rikeni, shiyasa nai dare, shiru tai masa ba amsa, gajiya yai da surutun, ba amsa, yace Ina yarana? tace sunyi bacci, ayyah banso sukai bacci ba naso idonsu biyu mu sha hirarmu, ita kuwa juya kai tayi ta tabe Bakii azuciyarta tace Baka so ganinsu bane, Dakinsa ya wuce ta bishi, ruwan wanka ta zuba masa tare da madarar turaren da ta saba sanya masa a ruwan wankan ta ajiye masa towel, tuburewa yayi wai adole ita zatai masa, itako kememe taki, daga karshe ma fita tayi adakin, hakanan ya shiga Yai abinsa ya fito ya shirya, cikin singlet da boxer, yaje ya sameta tana zuba masa abinci a plate, aiko ya zage ya kwashi gara yaushe rabonshi da cin abinci mai dadi haka, itama tai mamakin irin avincin da ya ci ta zaci ma bazai ci ba ko ya kwashi na Amarya, yana ci suna hira. Yana ta yabon girkin.

 

Washe gari tun sassafe Rukayyah ke ta kira wai ai ya kamata gari na wayewa ya kira ya ji lfy ta tashi, amma gashi har ynx baizo ba, hakuri ya bata yace zai kai yaro makaranta ne ynx anjima zai xo, azuciyarsa yace wannan yarinyar ta fiye mita wlh.

 

Bayan yai wanka yai breakfaast, yace Maya zaije gidan Amarya daga nan zai wuce office.

Yana isa gidan ya taradda ba shara agidan balle kunna turare, ita kanta ko wanka ba tai ba sleeping dress ce ajikinta ko breakfast batai wa kanta ba. duk da cewa mutum ne mai tsafta ko tsinke baison ganin adakI, bayan sun gaisa ne, sannan ta hau shirin yin wanka, shiko yana mamkinta, maryam tai mata xarrah ko kadan ma basu hada hanya ba, ko 30min baiyiba yai Mata sallama ya wuce office.

 

Haka rayuwa taita tafiya Abbas yana kokarin yin adalchi a tsakaninsu, kowacce yana kokarin bata hakkinta, sai dai wani irin shakka da tsoronta yake ji, duk abinda ta gaya masa ya zauna daram. Amma hakan bai hanashi yin adalchi ba, yana kokarin ganin ya sauke nauyin dake kansa.

 

Bayan wata guda da auren matsaloli sukai ta kunnowa daga wajen Rukayya wai ranar girkinta gidan matarsa yake zuwa yaci abinci inta girka nata baici, haka zata saka shi gaba taita kuka, sannan in ya tafi can ranar girkinta sai ya ga dama yake dawowa, ita inde ya fita ya dade a waje to ba abinda take zargi, sai gidan uwargidansa ya tsaya Wanda a zahiri wasu lokutan uxuri ne yake masa yawa, ita fa ko yaushe cikin korafi take, Wanda baisamun haka wajen maryam bata taba kai masa wani korafi akan Amaryarsa ba, bata dorawa kanta wahala ba, duk da cewa taga salo irin -iri da wasu sabbin dabi’u daga gareshi. Wanda tasan dama hakan zata faru, duk inda miji yai aure to ko Amaryar buxuxuce dole sai Kinga rawar kai wajen mijin saboda anyi sabuwa dole ayi doki, amma in akayi hakuri na Dan lokaci ne, kamar ace mutum yayi sabuwar Riga ne zaki ga kullum cikin son sanya ta yake amma daga baya sai kiga an koma ma tsohuwar sbd ingancinta har tafi sabuwar, so, dole ne sai an daure, an kau da kai, sai ya kasance in yazo sallama wajenta da dare Allah-Allah yake ya koma kar ranta ya baci, kana ganin yanayinsa kasan ba’a hayyacinsa yake yi ba, koda maryam ta fuskanci hakan addu’a ta shiga yi masa akan Allah ya yaye masa halin da yake ciki.

 

 

By

Ummu Ameer💃
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

 

*story&written*

*By*

*ummu Ameer* 💃🏻

 

*page* 2⃣0⃣

 

Akwai watarana ranar girkin Rukayya Abbas yaje sallama da daddare waken maryam, dama duk wacce bata da girki gidanta yake fara sauka in ya tashi daga aiki, a ranar maryam tayi baki, ne kuma daga danbatta suke, yan’uwan Abbas ne, hakane yasa shi daukan lokaci, suna gaisawa da bakin, amma duk da haka hankalinshi duk baya wajen yana ta tunanin abinda zai tarar a wajen Rukayyah, sai wajen 9;30, ya tafi yai musu sallama, amma zuciyarsa cike da zulumin abinda zai Tarar daga wajen Rukayya.

 

Ita kuwa tana can ta gama kuluwa, har da kiran mommy ta fada mata wai kullum haka yake yi sai ya tafi gidan matarsa yai zamansa inta yi masa magana, yace wai yaransa, aiko uwar ba abinda ya fito a bakinta sai to in ya dawo kar ki sake ki barshi ya shiga gidan ki rufe gidan ki ki kwanciyarki, ni kuma gobe insha Allahu zanxo zan ci masa mutunci, haka dae tai ta kitsa mata tsiya, daga karshe tace koma meya miki ai ke kika siya da kinji maganata da haka bata faru ba.

Yana isowa yai ta knocking taki budewa wai ka koma inda ka fito, shi mamakinta ma yake sbd kwata-kwata bai tsammanin tana da irin wadannan halaye ba, tun lokacin da ta tare a gidansa ya fuskanci duk ba halayen da ya Santa da su bane ta canja ba Rukayyan da ya sani bace kenan boyemin halinta tayi kenan ko kuwa haka take? Ya tambayi kansa, a daaa, har yana tunanin kusan halinsu guda da maryam dinsa na rashin son rigima da biyayya, kawaichi da hankali, kunya, nutsuwa, mutunta na gaba da ita, sai yanzu ya fahimci maryam ce kawai mai wadannan kyawawan halaye, lalle yayi zaben tumun dare.

Yana nan tsaye kusan 30min a wurin har yayi zuciya zai koma, ko tunanin me tayi kuma sai ta bude, wai wallahi kaci Albarcin son da nake maka in ba haka ba.. Kwafa tayi tare da komawa cikin gidan, shi kuwa ko saurararta baiyi ba, amma zuciyarsa fal da shakkarta, har mamakin kansa yake yi.

 

Shigewarsa yayi daki wanka ya shiga, itako ko bata ko kalli inda yake ba, dama halinta ne indai suka samu sabani to fa a ranar kuntata masa takeyi ta ko Ina, Wanda ko bai saba da wadannan halaye ba daga wajen matarsa ko da bata mata rai yai to hakan baisa ta ki yi masa abinda ya dace, bata tauye shi ki kadan, hakane yasa aduk lokacin da irin haka ta faru shi da Amaryarsa to kwana yake yana shi wa maryam Albarka, tuni ya fara ganin laifin shi ko kuma rashin godiyar Allah da matarsa Mai kokarin kyautata masa ko yaushe amma bai hakura ba sai da ya kawo mai shirin ruguza masa rayuwa.

Hannu ya daga sama yana mai rokon Allah ya bashi ikon cinye wannan jarrabawa da ka yi min.

Dole ya bita ya sameta yana lallashi, da kyar ta hakura ta saurare shi, amma tace ka tsimayi zuwan mommy gobe, gara taxo ta taka maka burki, don nan gaba bamu san me zaka yi ba kuma

Tana ambaton mommy yaji wata mummunan faduwar gaba, baisan dalili ba duk sanda suka hadu da ita wani irin shakkarta yake yi, dama ita fuska ba rahma a tare da ita, don kafin kaga murmuahinta za’a dade, to gara ma in suna tare da kwayenta, bare ma anty batulu.
Allah ya kaimu yace.

Sai a lokacin ne taji Dan tausayinsa, tason in suka hadu da mommy bata masa da dadi ko kadan, shiyasa ma sanda tana gida bata son haduwarsu da mommy, ita kuma gani take kamar uwargidan ta Riga ta gama da shi gara tun wuri aima tufkan hanci, gashi kullum jin wani irin sonsa takeyi yana shigarta, shiyasa bata so ko kadan ya dinga nesa da ita, in aka ce zata fita girki kuwa ranar kamar zatai hauka don kishi.

 

*washe gari*

Washe gari tunda safe kafin Abbas ya fita office mommy ta dira a gidan, banyan an kawo Mata break fast taci, sa’annan Abbas yazo ya gaisheta, ta amsa a Takaice, ta fara mgana dama ba wani abune ya kawoni ba Akan complain din da take kawo min ya isheni haka, tace kana zuwa gidan uwar gidanka kai zamanka har kaci Abinci acan to wlh bazai yiwu ba, Baka isa ka maida min diya bora ba, in anyi magana kace yara, to in ma yara 100 ne da kai ba abinda ya shafeni, ni tawa na sani dole ne abinda zakai acan ayi anan kana jina, shi dai kawai daga kai yake yi, kanshi akasa.

Sbd haka ya zamo farko ya zama karshe kar in kuma jin wani complain daga gareka, yadda kake kaunar yaranka, haka nima nake ji da tawa, ta fada tare da tashi ta dauki Jakarta ta fice, yace a sauka lfy!
Yar ta bita tana mata a gaida gida, tare da bata wani kulli a Leda tai Mata a rada a kunne. Ta wuce.

Bayan ta dawo ciki ne taje tana masa wata munafukar kissah wai baby kayi hakuri da mommy, haka take, shiko ko tanka Mata baiyi ba ya ce na wuce office, tai masa Allah tsare.

A cikin mota kuwa ba Abinda yake masa yawo akai sai maganganun surukarsa suka ta maimaita kansu a kunnensa, har ga Allah ranshi ya matukar baci, ji yake bata da wani sauran daraja ynx atare dashi, ya fara gajiya da halayesu completely.

Itako sai faman murna take da sakon da mommy ta kawo mata gani take da zarar tayi amfani da wanan magani kashin maryam ya bushe, wani mugun murmushi tayi, tare da fadin yarinya zaki gane kurenki, sai kin koma inda kika fito ne, Abbas da ni kadai yafi dacewa….

 

 

*ummu Ameer* 💃🏻
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

 

*story&written*

By

*ummu Ameer* 💃🏻

 

 

*page* 2⃣1⃣

 

 

“”””” sai dai kuma Rukayya ta manta da cewa Abbas ba a gidanta yake ba, said daga baya ta tuna hakan, ko da Abbas ya dawo gidan rukayya ya wuce kamar yadda ya saba, yana shiga yadda ya bar gidan da safe haka ya sameshi ynx bacci ma ya tarad tana yi ko qamshin turare babu, kuma ga turarukan nan da ita burjik amma kiwa ta hana ta kunnawa, yana takaicin wannan hali nata, ita bata san hanyar mallakar miji ba sai yadda zata kwace shi karfi da yaji, ba wani matakai da take bi, amma ko kadan shakkarta ya hana ya mata magana, don a zahiri bai son ya mata abinda zai bata mata rai. Amma shima yana mamakin yadda ba ya iya mata magana akan abubuwan da bai kamata ba.

Tashinta yayi daga baccin da take yi ta mike ta shiga toilet ta wanke fuska, sa’annan tazo yai masa sannu da zuwa, suka taba hira sama-sama yace zai tafi, nan ta shiga jan hankalinsa wai don ya dauki lokaci bai tafi ba, itama ta hada masa bom wajen maryam, mace akwai makirci, sai da yai wajen 2 hours sannan ya tafi, ita anfi xama qalau ranar da ba girkinta ba, sbd tafi samun damar yin makircinta a lokacin.

 

Bayan ya isa gidane tun a waje yake jiyo qamshi na tashi, har wata nutsuwa ya samu, tare da sauke ajiyar zuciya yana mai Alfari da ita, dabance a cikin sauran mata, yana shiga ya sameta zaune a falo tana kallo tana jin shigowarsa tai Saurin zuwa tarbarsa tana masa sannu da zuwa, yace yawwa uwargida sarautar mata, murmushi tayi ko kadan ba bacin rai a fuskarta na jimawan da yayi bai dawo ba, kuma bata tambayeshi dalili ba, daukar elham yayi yana Mata wasa shiko mufid yayi bacci, yace rago bai jirana in dawo yai baccinshi, tace wlh tun daxu yake ta jiranka da sunanka a Baki yai bacci, Allah sarki my boy! Zuwa inda yake baccin yayi yana shafa masa kai yai kissing dinshi.

Itako karbar jakar hannunsa tayi da ledojin
Ta ajiyesu, tace ga ruwan wanka can na hada maka, yace tnx my lovely wife, Allah ya miki Albarka duniya da lahira!
Ameen tace

Sanann ta bishi domin taimaka masa, bayan ya shirya da taimakonta, yai sallah isha’i sannan suka fito domin cin abinci, rike yake da elham a hannu ya zauna Kan dining dorata yayi a cinya yana bata abincin, tace husby karfa ka bata da yawa taci daxu sosai, yace ai ba abinda zai mata tunda tana ci sai abata, tace oh elham Baki gajiya da cin abinci ko, yarinya kuwa har da daga kai Alamar eh!, suka kyalkayale da dariya, haka suka gama xin abinci, cikin farincikin da annashuwa daka gansu kaga masoyan da suka yi nisa da kaunar juna.

Shi kanshi baya samun nutsuwa da kwanciyar hankali sai ranar da yake gidan maryam, tana iya kokarinta wajen kyautata masa, kuma ba wai bata kishin bane, tana yi amma na nutsuwa, domin nuna zazzafan kishi akan namiji ba shine solution ba, asali ma shi yake kawo zubewar kima da daraja, ko da ace wani abin yayi a cikin lumana sai ki gaya masa kuskurensa, kuma wlh zai gyara, kuma hakan zai jawo miki wani matsayi na musamman a zuciyarsa, maryam tuni ta gano tana jan ra’ayinsa ne, ya bata lokaci a wajenta, in ya dawo tai tunanin ko soyayyarta ta hana shi dawowa da wuri, shiyasa ko kadan bata taba nuna masa bacin rai ba, da dai fa itace, tai tunanin kowa ma haka yake.

 

Bayan Rukayya ta karbi girki ne, tai ta fama da rashin lfy, bata iya komai ko da suka je hosp. An tabbatar tana da juna2, na wata 2,farinciki a wajenta bai misaltuwa zata samu zuri’a da Wanda take kauna Faye da komai, shima ba laifi yayi farin ciki domin mutum ne mai kaunar yara, tun daga lokacin fa sabuwar kazanta tai sallama bata yin komai kullum wai ba lfy, hakane yasa aka samo mata wata dattijuwa tana zuwa tayi mata aikace2 sai ta tafi, to da taimakon yar aikin ne ma gidan yake samun tsafta, kuma wani lokacin kannenta na gidan bazata saka su suyi ba.

Shi kuwa Abbas zuwa ynx ya fara gajiya da sintiri tsakanin gida biyu, ya fara tunanin hade matansa waje daya, duk da yasan ba karamin Abu ya debowa kansa ba ta bangaren ruky da mom dinta, yana sane da tsarinsu na rashin son kasancewa da kishiya gida daya, domin sai da sharadin aka amince da aurensu, shi kuwa ganki yake rashin kasancewarsa da yaransa waje daya, yana rage shakuwa tsakaninsa da yaransa, wani lokacin sai sun yi bacci, zai dawo hakane yasa yake ganin gara ya hada su waje guda, domin hakane zai sama masa nutsuwa, shima ya huta da sintiri..

 

*tofa masu karatu kuna ganin kuwa hakan me yiwuwa ce a wajen rukayya da mommy*

Ki biyoni don jin yadda zata kasance…..

 

*ummu Ameer ce* 👌🏻
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

 

 

*Story&written*

*By*

*ummu Ameer* 💃🏻

 

 

*page* 2⃣2⃣

 

 

A kwana a tashi cikin Rukayyah sai girma yake lalaci kuwa sai abinda yai gaba, gashi sun koma sch. Abubuwa sun Kara kacame mata, rashin hakuri da bakin kishinta kuwa, sai abinda ya karu, domin kuwa kusan yajinta uku ynx, wani sabon salo ta tsiro da shi ko kuwa uwar ce ta kirsa mata, oho! Don ynx suna yin Abu da Abbas bai taka Kara ya karya ba sai tayi tafiyarta.

Ranar da ta fara yi kuwa watarana ce tace tana so ya kaita taga maryam, kuma dama gulmace zata kaita take taga wadda yake rawar kafa akanta, bai musa mata ba yace ta shirya su je, ta shirya cikin nadin laffaya blue ta sanya flat shoe sai yar powder da ta shafa, ita bata cika son yin make-up ba. Dama ranar girkin Rukayyan ne.

Shi kuma tuni ya buga mata cewa Amarya zata zo su gaisa, tace Allah ya kawoku lfy!

Ta hada mata lemon kwakwa, da Abarba snacks kuwa Dama bata rabo da yinsu ko da yaushe kaje gidan. Ta sanya wata Doguwar riga mai igiya ta ciki, ta daura mayafi akanta kalar rigar tai kyau.

Jin karar motar sa yasa yara suka nufi gun daddynsu, a guje suna masa sannu da zuwa, itama yace wa rukyn anty sannu da zuwa, tace yawwa ba tare da sakin fuska ba, daman ya taba zuwa da shi gdn har yake tambayar dad dinshi wnn wacece yace ita ma momyn kace, sau tari ma in zai kaishi sch. Itama in a ranar tana da lecture, yana biyawa ya dauko ta sai ya fara sauke mufid daga nan sai ya wuce ya sauketa a makarantar.

Suna isowa ya dauki elham tare da mika mata chocolate din da ya siyo musu sai mufid kuwa tuni ya shiga gida yana Kara fadawa momynshi ga dad da dayar mom dinsu, tace to sannunsu da zuwa.

Tun daga kofar gidan ta fara sanin ko wacece maryam domin ko Ina ta kallah tsaf da shi ga wani qamshi mai dadin ji, bata Kara raina kanta ba, sai da ta shiga falon, a zuciyarta tace ngd wa Allah da ba itace ta fara zuwa gidana ba, ai sai ta raina ni, sai a lokacin itama ta fara ganin laifinta na kiwa, ita ba yara ba, ga mai yaran ma amma gidanta yafi nawa kyan gani, zazzakar muryar da ta ji tana cewa zauna mana sis rukayya ita ta dawo da ita hayyacinta, ai nan da nan ta Kara kaduwa da ganin haduwa a wajen maryam, sai faman kallonta take, ba ko kyafta ido, ita ko mijinta ta tsugunna tai masa sannu da zuwa, bayan yan seconds, ta dan samu nutsuwa, ne suka gaisa maryam fuska a sake, bata wani nuna mata komai ba, amma a zuciyarta dannewa tayi ganin husbyn ta da wata matar sbd wnn shine karo na farko da suka da ta gansu tare, ita kuwa mutuniyar tuni fuskarta ta canja ita da bata iya danne Abu, bayan gaisuwar ne ya hada su yai musu nasiha, inda yace maryam ga Rukayyah, ke kuma rukayya ga maryam Ina fatan zaku bani hadin kai wajen gudanar da adalchi tsakaninku, ki hade kanki tamkar yan’uwan juna, Ina muku fatan Alkhairi gaba daya,
Maryam tace insha Allahu, Allah ya bamu ikon kyautata maka, yace Ameen, ita kuwa ruky tunda ya fara magana ko uffan bata ce ba, domin tuni ta gama raina kanta, ga kishin wai Abbas ya zauna kusa da maryam kamar itace da girki zai wullah masa harara take amma bata bari sun gani ba, yace rukayya baki magana ba, tace bani da abinda zance.

Maryam ta cika mata table, da kayan makulashe, tace bissimillah, ruwan kawai ta sha a kayan da aka kawo mata, duk inda maryam tayi dai binta fa kallo take tana mai jin haushinta, sbd maryam duk inda mace take ta kai, mai diri fa kyan siffah ga kyau ga nutsuwa, itako Rukayyah irin siraran matan nan ne da siffar jikinsu take mai kama da muciya, sun tafi 1 ba gaba ba baya, itama bakace amma ba can ba, tana da nata kyawun amma bata Kama kafar maryam ba.

Ba yadda ba ai da ita ba taki cin komai, shikuwa gogan tuni ya bude ciki sai faman kwasa yake hankali kwance.

Ruky kuwa tuni ta gama kuluwa da shi, yau ga zahiri ta gani daman tasan nan yake cin Abincinsa, shiyasa in takawo masa sai yaci kadan yace ya koshi, ba shiri ta mike, tashi mu tafi, tace masa, shiko yana ganin yanayinsa yasan akwai gwarama, nan da nan ya cika fal da tsoron abinda zai biyo baya, ya tashi ya shiga dakinsa ya kira maryam domin tambayatta ko da wani abin tace ba komai yai Mata godiyar tarbar mutumcin da tayi mata, tace ba komai ai kafi karfin haka a gurina, ya bata hot kiss a kumatu, sukai sallama y fita, ruky kuwa tuni tayi gaba, tunda taga sun shiga daki, yaran nasa kuwa ko irin jansu ajiki dinnan bata yi ba, suna fitowa suka ga ba ita, cikin sauri ya bita, ita kuwa tsayawa tai tana kallon ikon Allah!
Tace ko sallama bata tsaya munyi ba, ni da ya kamata nai kishin mijin ita takeyi, karfin hali! Don tuni ta gane ba abinda ke yawo da ita sai kishi, bata iya danne kishinta.

A mota ya sameta sai faman kuka takeyi, yace lfy ba sallama sai ki taho haka akeyi?
Dago fuskarta tayi cikin bacin rai tace bansani ba, maci amana kawai, dama ka kawoni ne don ka nuna mata ni ba kowa bace a wajenka, nayi nadamar aurenka, kasan kana matarka, mai yasa ka Kara yin aure, eyehh? Tambayarka nake?

Shiko tuni idanuwansa sun yi jajir da bacin rai, da mamaki ya kalleta, yace ni kike gayawa haka, an gaya maka kayi duk abinda zakai, tuni zuciyar sa ta fara ayyanah masa abubuwa da dama akanta, ace kanwar kanwarsa ta dinga gaya masa irin wadannan kalaman, ko daga murya maryam bata taba yi masa ba, bare irin wnn rashin kunyar, shiru yayi ya kasa ma magana don bacin rai, motar yaiwa key, ya figeta da wani mahaukacin gudu, tace mallam kada ka sake ka maida ni gdnka, don wlh bazan kwana a gidanka ba. Bai saurareta ba ya ci gaba da gudu kamar zai tashi sama, suna isa ta buga tsaki ta juya zata koma titi, bai hana ta ba, yana kalloh ta hau napep, shi kuwa cikin gidan ya shiga yana isa ya zauna Kan 2seathet, domin jin kansa na wani sarawa yakeyi, sai fadin inna lillahi wa’inna raji’un kawai yakeyi, tare da tunanin abubuwa barkatai game da wnn baiwar Allah yana tunanin lallai boye masa halinta tayi domin ya fahimci ta fara zama mahaifiyarta.

Yaso komawa wajen maryam, amma gudun kar tai zargin wani Abu yasa y hakura, yai kwanciyarsa.

Washe gari da sassafe ya fita, ya je daukan mufid Kana ganinshi kasan akwai damuwa a tartare da shi, amma gudun kar tayi masa katsalandan yasa taii shiru da bakinta
Kuma yace ta hada masa breakfast ya tafi da shi, nan ma kamar tai masa magana, tai shiru ba musu, ta hada masa, ta san dai tabbas da matsala, ganin bai gaya mata ba, itama tai gum da bakinta…

Yana fita wayar momy ta shigo wai tana son ganinshi ynx2 yace yana da patients in ya sallamesu zai zo… Bata jira wata mgn ba ta katse wayar…

Ta saka diyarta a gaba, sai faman masifa take mata, da farko cewa tai duk abinda yai miki ke kika jawo da kika nace sai kin aureshi, daga baya kuma sai tausayin yartata ya kamata ta hau tambayar kina amfani da wadannan abubuwan da na baki, tace eh!
Tace taurin kai ne da shi kenan zanyi maganinshi, zaizo ya sameni dani yake zancen…

Nan kuwa bata san mutum ne da baya sake da kare kanshi da addu’oi ba, ga matarsa da take hana kanta bacci wajen kai kukanta gurin ubangiji.

Duk da dai akwai wadanda suke tasiri akansa,

Bayan ya tashi daga office direct gidan ya nufa amma wnn karon zuciyar sa a dake take domin ya fara daina jin shakkarsu a shirya yake da koma me zai faru ya faru…

 

 

*ummu Ameer ce*👌🏻
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀

 

 

*story&written*

 

*By*

*ummu Ameer* 💃🏻

 

 

*page* 2⃣3⃣

 

 

Yana isa gidan ya aika ace musu ya iso, akace ya shiga, a falon ya tarar da su mommy, da anty batulu, sai Rukayyah zaune a kasan carpet, tayi wani firki2 da ita.

Sallama yayi anty batulu ta amsa masa, mommy kuwa tana hakince akan kujera sai jifansa da harara takeyi, bayan ya gaishesu ne, sa’annan anty batulu ta fara yi masa mgn akan abinda ya faru tsakaninsu da Rukayyah, haduwa sukai da mommy sukai masa cin fuska, har suka ce in ya ga bazai iya ba, ya bata takardarta, ai bashi kadai ne autan maza ba, ruky ko naji an fadi haka, tace mommy bafa shi yace na taho ba, nice na taho da kaina, shutup! In nasake jin bakinki sai ranki, ya baci shashasha kawai, Ana nema miki yanci kina shirmen banza.

Shi dai tunda suka fara shirmensu baice uffan ba, baisan me yasa ko da yai shirin maida musu martani bai iyawa, bai saba ba, ko kadan baijin zai iya jayayya da ita ko akasin haka, tunda shi daga gidan tarbiya ya fito sun san mutumcin mutane.

Abinda kawai yace shine ayi hakuri, bazata sake faruwa bah, itako tuni ta shiga daki ta dauko mayafinta, don tuni ta fara tsoron kar mommy ta guntule mata auren nata, don a gaskiya tana
matukar kaunar mijinta.

Mummy kuwa tsayawa tayi tana mamakin diyarta, zatai magana anty batulu tace kyaleta, Allah kiyaye hanya.

Sallama yai musu suka tafi….

Mummy kuwa kallon batulu tayi cike da mamakin diyarta tace Ina tunanin cire hannuna a lamarin yarinyar nan, kina ganin abinda takeyi? Sai kace wacce ya asirce, Ana kokarin nema Maya yancin tana hauka!

Batulu tace kyaleta ai namijin ne, namiji dan kunama, namiji takalmin kaya! Namiji buhun kaya! Ki zurata mata ido zaki sake jinsu ne, mazan ynx ma ka tsaya da kafafuwanka akansu ma ya ka kare bare ita da take wulakanta kanta akansa…

 

 

A mota kuwa tunda suka fara tafiya ba Wanda ya tanka, da ta ga shirun yai yawa, shine tai ta damunsa da surutu, shikuwa ko tanka mata bai yi ba, har suka isa gidan.

Ko da suka isa gida kuwa, ganin bil hakki fushi yake da ita yasa ya zo ta bashi hakuri, sannan ya saurareta.

 

 

Amma da aka kwana 2 sai da ta Kara tafiya har sau 2 amma gdn kanwar mommy ta tafi sai da tai wajen 2wks bai je ba, sai da Antyn ta kira shi, dake ita tana da hankali, ta binciki abinda ya hada su kuma ta gano laifin rukayyah ne, tai mata fada sosai, sannan ta bashi hakuri. Suka tafi….

 

 

Bayan abubuwa sunyi sauki ne, domin ya fahimci ta dan canja halin nata, a lokacin cikinta na wata bakwai, ya bujoro mata da batun yana son hada su gida daya da maryam saboda wasu dalilai, abinda yasa bai mata magana ba tun baya, lokacin da sauran kima fa shakkarta a zuciyarsa zuwa ynx kuwa babu, dama a zamantakewar aure “yaji” yana taka muhimmiyyar rawa gurin zubda kima a wajen miji, matakine na farko da yake taka muhimmiyyar rawa wajen rusa kanki, saboda su kansu mazan sun san matsayinki a wajensu, na tona zamantakewar rayuwar aurensu a wajen iyaye, ki bata su, ki shirya su kuma iyaye suna nan da tsanarsa a ransu tunda tun farko kin bata shi a wajensu…
Ga kuma karfin addu’ar da yake yi shi da matarsa, shiyasa ya zamto yanzu ba wani sauran shakka ko makamancin haka a ranshi game da ita, shi yasa ita kanta ynx wani shakkarsa take bata iya yi masa abinda take masa da…

Aikuwa tana jin ya ambaci hada gida batasan sanda ta mike cike da tashin hankali ba, tana fadin Abbas kasan abinda kake fada kuwa? Yace kwarai ma kuwa

Gaskiyane lallai na yadda namiji ba dan goyo bane, ynx na fahimci abinda mommy ke son fahimtar dani akanka..

Ina Alkawarin da kai min tun kafin na amince da soyayyarka Abbas, ynx irin sakayyar da zakai min kenan?

Ko daya yace ba nufi na kenan ba, kawai zuwa ynx ne naga bazan iya jurewa ba, na farko Ina da gidana na kaina kuma wadatacce, nan kuwa haya nake yi aciki gashi tsarin unguwar baimin ba, sannan Ina so na hada Kan yarana da matana waje daya…

Dakata mallam ni ba abinda na tambayeka kenan ba, kasan duk da wadannan me yasa kai min Alkawarin bazaka hadani da kishiya ba, kuma ka yi wa mahaifiyata Alkawarin hakan itama, to wlh tafiya gidanmu zanyi bazan zauna da kishiya ba, sbd matarka ta gama shanyeka sai abinda tace da kai za’ayi, shine ynx ma ta bujuro maka da wannan to wlh bazai yiwu ba ynx nan zanje na gaya ma momy..

Shi dai bai tanka mata ba, yasan dama za ai haka, kuma ko ta tafi yasan ma zata dawo ne…

Shiga daki tayi ta dauko akwati ta bi gidan da kallo, tace masa maci amana kawai ta yi gaba…

Shikuwa a zuciyarsa yace illar yar mace kenan.. Batuna kuma ba fashi….

 

 

 

*ummu Ameer ce* 👌🏻
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

 

 

 

*Godiya main tarin Yawa masoyan wannan book din Allah ya bar zumunci*

 

*Story&written*

By

 

*ummu Ameer* 💃

 

*page* 2⃣4⃣

Bayan tafiyar ruky, ya debi duk kayansa sai gidan uwargida, dama ko sallama baijje ba sun tsaya hayaniya da uwar kishi…

 

Ko da ya isa gida bayan ya saba yin abubuwan da yake yi kafin ya tafi, maryam ta ga bashi da niyyar tafiya, tace Abban mufid dare fa yana yi naga baka da shirin tafiya…

Shiru yayi na dan wani Lokaci Sannan yace ba tafiya xan yi ba anan xan kwana…

Sbd me? Ta tambayeshi yace matar gidan ce bata
nan..

Tunda taji haka tasan akwai matsala a tsakaninsu, bata sake tambayar shi ba, yace ta je ta hada masa ruwan wanka, ba musu ta tashi tayi kamar yadda ta Saba…

Bayan yai wankan ya kintsa ta kawo masa tea kamar yadda ya saba sha kafin ya kwanta..

Bayan ya gama ya samu nutsuwa ne, ya gaya mata abinda ke faruwa tsakaninshi da rukayya..

Itama kuwa ba karamin tashin hankali ta shiga ba, da jin zai hada su wuri daya,…

Abinda yasa ita bai fara gaya mata a tunaninsa baza a samu matsala daga gareta ba, kasancewar yasan bata da matsala, Kuma duk abinda Yazo mata da shi tana karbar shi hannu 2 koda ba tason abin a ranta..

Aikuwa tana jin haka tace haba Abban mufid kayi hakuri dae ka barta a can ko don kwanciyar hankalinka, acan dinma ya aka kare balle Kuma nan plxxx ka canja tunani gaskiya domin kuwa nima hankalina yafi kwanciya tunda tun kafin kai auren ka tsara haka..

Yace akwai dalilina na yin haka bana jin dadin yadda bana kasancewa da yarana ko yaushe.. Wani lokacin bana samun ganinsu sunyi bacci, gashi Ina son hada Kan yarana da matana waje daya domin samun nutsuwa, amma ni kenan cikin sintiri tsakanin gida 2, ba zai yiwu ba!

 

Shiru tayi a ranta tace ai da kafin auren bakai tunanin haka ba sai ynx..

Kuma tasan halinsa sarai in ya dage akan Abu to fa ba mai canza shi..

Itama nan ta barshi a wajen ta nufi daki, tana tunanin wnn gagarumin lamari da ya dauko, tace lallai idan har haka ta kasance to sai ynx ne zata san tana da kishiya..

Tunda wani lokacin ma mantawa take tana da kishiyar domin bata sa ta a ranta ba, ita dae ko yaushe cikin yin abinda tasan zai farantawa mijinta rai take, bata dameta ba ko kusa..

 

 

***********************
Itako rukayya ko da ta isa gida ta kwashe duk abinda ya faru ta gaya mata.. Aiko mummy najin haka tace wlh zamanki da shi ya kare gobe xan aika masa ya aiko miki takardar ki, bama taba hada inuwa daya da kishiya wlh, mayaudari kawai.. Yasan ba zai iyaba ya debowa kansa, ruky kuwa sai kuka take tace Allah ya isa.. Tsakani na da Abbas ya cuceni yaci amana ta, Allah sai ya saka min..

Mommy tace wnn kuma duk abinda yai miki ke kika jawa kanki ba, abinda nai ta hango miki kenan kika rufe idonki akansa, ai ga halacci nan yana ta binki dashi…

 

Washe gari da safe ta kira shi a Waya tace suna jiran takarda in ba haka ba kuwa ya jirayi sammaci a kotu..

A zuciyarsa ko yace ai ba sai ta kai ga kotu ba, cikin ruwan sanyi zaku samu..

Itako tuni ta katse wayar ta, sai faman bala’i take ita kadai kamar tababbiya..

Rukayyan ma duk ta tashi hankalinta ya gagara samun nutsuwa, sbd tana son mijinta amma bata jin zata iya zama da kishiya.. Kishiyarma wadda ta gama mallake mata masoyi, ta hana shi ganin kowacce da gashi sai ita! Ina bazai yiwu ba da ta kasance bora gara ta hakura da shi har abada.. Wata zuciyar kuma ke zugata idan na barshi ai dadi zata ji na barmata shi..

Idan ko haka ne sai na bi duk wata hanya da zai canja ra’ayin hadani da munafukar matarsa..

Ta kasa samun nutsuwa itace buge bugen Waya wa yan’uwansa wai yaci amanarta ya yaudareta ya karya mata Alkawarin da ya dauka tun kafin aurensu, har yaya ta kira yace tayi hakuri zai samu Abbas din komai zai daidaita insha …

Sai a lokacin ta ji sanyi a ranta sbd tasan Abbas yana jin maganar yaya baya ketare maganarsa..

Bayan sun gama magana da Rukayya ya bugawa Abbas in ya tashi daga office ya biyo yana son ganinsa, yace toh.

Itama maryam tana cikin fargaba, don kwata kwata ta kasa samun nutsuwa tunda ya bujuro da wannan lamarin, amma dake tana da Saurin fahimta yai ta lallashi da ban baki yace insha Allahu ba abinda zai jiyo baya sai Alkhairi.. Ta kwantar da hankalinta ba abinda zai canja haka nan ta hakura ta mika lamuranta ga ubangiji, don tasan ko bata hakura ba ma ba canja ra’ayinsa zaiyi ba in ya kafe akan Abu daya bai canjawa..

Yaje ya sami yaya sun tattauna akan batun inda Abbas din ya gaya masa Alfanun hadawar da zaiyi, ba yadda yaya bai yi ba amma ya kafe akan ayi hakuri a kyalleshi shi yasan inda ke masa yoyo!

Hakanan yaya ya hakura ya kyaleshi yace toh Allah ya sa haka shine Alkhairi a gareku baki daya yace Ameen!

Har gidansu Rukayyan yaya suka je shida amininsa, amma mommy ta rufe ido tace ta gama magana in bazai fasa hadasu guri daya ba, to ya sakar mata yarinya..

Da yaga bata da shirin saurararsu sukai tahowarsu cike da mamakin wannan suruka ta Abbas, ko me ya kaishi kwasowa kansa irin wadannan mutane!

Inda Abbas din Yace gara kawai ya sawwake mata tunda haka suke so… Yaya ya hana shi yace ka zamo mai juriya a rayuwa jarrabawa ce Allah yake maka kayi kokari ka cinyeta..

Haka dai ake ta fafatawa shi ya tsaya tsayin daka magana ba fashi ba Abinda zai canja… Suma su mommy sun kafe diyarsu bazata zauna da kishiya ba.. Sai dai ya saketa..

Magana har taje gun mahaifinta ransa ya baci da abinda suke ita da mahaifiyarta, yai ta yi mata fada akan lallai ta gaggauta komawa gidan mijinta kafin ranta ya baci, mahaifiyarta ko ta hana tace ai ba shi zai zauna miki da shiba, ya kyaleta itama tana da iko akan yarta..

Har Abbas ya bugawa yaita bashi hakuri akan abubuwan da suke faruwa yace ba komai daddy kar ka damu komai zai daidaita..

Yana matukar respecting dinsa sbd mutum ne mai dattako Albasa ce bata yin halin ruwa ba..

Haka ya hakura ya zuba musu ido tunda ya fahimci ta biye wa mahaifiyarta, shima Abbas din kyalesu yayi..

Itako mummy tuni ta sanya an kwashe kayan rukayyan daga gidan shima yaje ya kwaso ragowar tarkacensa ya kulle gdn ya basu mukullan gdn.

 

 

Tofa masu karatu zamuga waye zai yi wining tsakanin Abbas da su mommy…

 

*ummu Ameer ce* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

 

*story&written*

 

By

 

*ummu Ameer* 💃

 

 

 

*page* 2⃣5⃣

 

 

“”””Dukansu sun kafe akan magana daya kowa ya tsaya Akan maganarsa, da mahaifin rukayyah yaga Basu da niyyar bin umarninsa ya zame hannunshi daga ciki, sai daga baya ne kuma ya sami Abbas din akan cewa indai akan gida ne, to yaje ya sami gida mai kyau su zasu dauki nauyin biyan kudin haya, Abbas yace masa kayi hakuri daddy nima ba gagarata sukai ba kawai dai Ina son hada Kan iyalina ne waje daya.. Da dai daddy yaga ya kafe ya hakura ya kyaleshi, daman kuma kafin ya fara yi ma Abbas din magana sai da ya fara yima ruky, tace daddy dama matsalar kenan in dai ya janye ra’ayinsa xan koma amma ni bazan zauna da matarsa ba, saboda ta Riga ta asirce shi abinda tace shi yake yi.. Yace ya isa haka nan ki dinga yiwa mijinki kyakkyawan zato.. Kar ki debo halin mahaifyarki.. Toh tace masa sukai sallama..

 

Ko da rukayya taji labarin yadda sukai da daddy ranta ya matukar baci ba kadan ba, tace sai ynx na fahimci bawan Allah nan ba kaunata yake ba, neman hanya yake da ita, lallai kuwa Abbas ya cuceta gashi ya barta da ciki, Waya ta masa tai masa tas ba irin rashin mutuncin da batai masa, kuma tace in ya isa dan halak ya gaggauta aiko da takarda… Ranshi ya baci da kalamanta, ya harzuka sosai don har ya fara ayyanah sakin tuno da nasihar yayansa da kuma darajar mahaifinta take ci, in ba haka ba da tuni ya yarda kwallon mangoro ya huta da kuda..

 

 

Daga karshe suka hakura suka kyaleshi shima haka, sai da cikin ya kai 9month ne suka turo masa list din kayan haihuwa, cikin gadara suka rufe ido ba tausayi sukai masa list na mugunta tun daga Kan kayan baby har na fitar sunan mejogo, ko da ya gani yasan suna sane suka shirya wnn muguntar, shiko cewa yayi Abinda naga zan iya shi zanyi…

Ya sayi duk Abinda ake bukata daga Kan baby zuwa ita mejogo kuma ba laifi ya yi bajinta, domin shi duk abinda zai siya tsadadde ne, komai hassada sai an yaba, amma dake sharri suke binsa da shi sai cewa sukai ai kaya Basu yi ba, yace yayi abinda zai iya.. Aiko mummy ta kira ba ko kunya har da su zagi wai matsiyaci in ba kaddara ba, ai diyarta tafi karfinshi… Shiko katse kiran yayi don bazai iya jurewa ba, idonshi ya kada yayi ja don bacin rai.

 

Har tana cewa in ba kaddara ba, Ina Ke Ina hada zuriya da wnn dan kauyen.. Shiyasa tun farko naso ki zubar da cikin kika ki yadda.. Ai gashi nan ya barki da wahala..

 

Bayan sati biyu ta haifi yarta mace tasha wuya sosai don har an fara tunanin yi mata c.s Allah ya sa ta haihu da kanta, tace wa mommyn kar a gaya ma Abbas don ta Riga ta cire shi a rayuwarta bai cancanci zama uban yarinyata ba,

Mommy tace uban wa zai dauki nauyin biyan kudin asibitin ai kwandala ba zan kashe akan yarinyarsa ba, domin asibitin da ta kaita haihuwar ba karamin tsada ne dashi ba, tana sane ta shirya muguntar..

 

A take ta kira wayarsa ta shaida masa ta haifi diya mace, kuma ya gaggauta zuwa Ana nemanshi a hosp. Ta gaya masa asibitin da suke.

Yayi murna kwarai da jin haihuwar sbd yana da son yara, amma da ya tuna halinsu sai farincikin sa ya ragu.

Ya sanarwa da maryam itama tai masa murna da fatan Allah ya raya.. Tace elham anyi kanwa ko.

Tashi yayi ya kintsa ya shirya domin zuwa asibitin amma duk ranshi ba dadi sbd yasan sai ya fuskanci bacin rai daga wajensu, haka nan ya tafi jiki ba kwari.. Ya dan tsaya yai masu siyayyar abinda yasan zasu bukata.

Yana isa asibitin ya hadu da kanwarta tai masa jagora izuwa dakin da suke a lokacin mommyn bata nan, ta fita waje.. Ya sameta kwance babyn kuma na kusa da ita.. Ya karasa ya dauketa yana ta murmushi, yai mata huduba da sanya mata suna khadijat, itako ko kallon shi batai ba, yana tai mata sannu da jiki amma ko tanka masa batai ba, ita adole fushi take da shi..

Bayan wasu mintuna mummy ta dawo tare da shaida masa yaje ya biya bill za’a sallamesu ynx, yace toh, fita yayi yaje aka bashi bill an caje shi kudi mai yawa ba yadda ya iya haka nan ya biya, yace su zo ya sauke su a gida. Suka fara harhada kaya suka tafi..

Bayan isarsu ma haka ta Kara cajar shi kudi wai ko da bukatar wani Abu ya taso a zuciyar shi ko yace ko baki fada ba zan bayar.. Yai musu sallama ya wuce, ya gaya musu sunan yarinyar…

 

Bayan kwana uku yace wa maryam ta shirya ya kaisu suga baby…shiru tai na seconds sai can ta amsa da toh! Ji tayi tana fargabar zuwa sbd tasan rashin kirkinsu ba abinda baza su iya ba.. Kuma ma tunda da Abbas din zasu ai da sauki, ta tashi ta shirya cikin wata super red fa mayafinta red tai matching colour, tayi kyau sosai don bazakace ma ta haihu ba, yar caras da ita, suka tafi a hanya suka tsaya tace zata sai kayan barka, ya mika mata kudi ta shiga ta debo kayan babies masu kyau wajen 5colours har da du takalmi masu kyau 2pear ta hado da atamafa guda daya..

Suna isa gidan a falon suka sauka sai bayan kusan 30 mins sannan mommyn ta fito ta tsaya daga bayan kujera suka gaisa fuska ba rahma, sai faman wurga musu harara takeyi.. Ta koma ciki tace tana zuwa saida aka kuma wata 30mins sanna n rukayyah ta fito rike da jaririyar ta zauna suka gaisa da maryam din amma fuskarta a hade ba walwala, sai Abbas dinne ya gaisheta ta amsa a dakile ya amshi yarinyar ya mikawa maryam ta amsa da fara’a tana cewa tubarkallah kuwa da girmanta Allah ya raya. Abbas ya karba ya mikawa Abbas yace ga kanwarka nan, yaro ko sai washe baki yake yaga sabuwar baby..
Mummy tana fitowa taga jarirya a hannun mufid tai Saurin karbarta tana cewa wnn wane irin wauta ne zaku dauki new born ku bawa karamin yaro don ba ke kika sha wahalar haifota ba tai tsaki ta shige ciki rike da babyn.

Abin ya sosa masa rai yace ta tashi su tafi suka mika kayan da ta kawo sukai sallama, suka tafi cike da bacin rai..

A hanya yaita bawa maryam hakuri tace karka damu ba komai ai duk Wanda yai nagari kansa.. Itama tai ta kwantar masa d hankali kar ya sa damuwar su a ransa jarabawa ce.

 

Ya fadawa yan uwansa na danbatta yace ba sai sunzo ba, sbd akwai yar matsala amma anty babba ta kafe wai akan me matarka ta haihu kace basai anzo ba, duk yadda yaso fahimtar da ita amma taki wai gasunan zuwa Ana gobe suna, haka nan ya kyaleta tace ai ba gayya zamuyi ba mu uku zamuzo, yace sai kunzo.

 

Ranar suna tun safe yaya babba aka taho gidan Abbas dake a gidan yaya ta kwana ita da dayar yayar Abbas sai kanwar mahaifinsu, yace ai ba ynx suke sunan ba sai yamma.

Maryam ma tai kwalliyarta kuma tai musu lafiyayyen girki ta kawo musu sai godiya suke mata amma banda yaya babba sai faman habaici take mata wai takori Amaryar sbd bakin KISHI ta kalailaye miji…
Suna ta hana ta amma taki ji..

Sai maryam din sukai ta bawa hakuri tace ba komai amma har ga Allah ta gaji da wnn munanan halaye da take mata kuma bata taba fadawa Abbas ba, ita dai tasan tana iya kokarinta wajen kyautata mata.

Karfe 5 na gamma Abbas yace su fito su tafi tace ita uwargidan taka bazata bane ko kishi ya hana ta zuwa.. Yace ai munje tuntuni.
Tabe baki tayi suka tafi tai musu Allah kiyaye!

 

 

 

*ummu Ameer ce* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

*Godiya Mai tarin yawa masoyana Ina jin dadin karfin gwiwar da kuke bani,Nima Allah ya bani ikon faranta muku*
Luv u ol😘

*Story&written*

 

*By*

 

*Ummu Ameer* 💃

 

 

 

*Page* 2⃣6⃣

 

 

“””Suna hanyar zuwa gidan suna Abbas ke tuka motar da Yaya babba sai anty ..da Kuma kanwar babansu goggo turai sai matar Yaya.

Yaya babba ce ke tambayarsa wai me ya hada ku da amaryar taka ne ko kuwa makircin matarka ya koreta..

Yace ba ruwan Maryam ..duk Abinda ya faru su suka so..tai saurin katse shi da ai Bata da laifi a wajenka sbd ta gama da kai ..shanyayye kawai ..

Matar yaya tace Anty Baki San abinda ya hadasu ba fa, ba ruwan Maryam ta kwashe duk Abinda ya faru ta Gaya Mata..Aiko Yaya babba tace to me zai sa ka hada ta da wannan makirar matar taka ai da gaskiyarta ..ba zai yiwu ba kaje ka dawo da matarka gidanta ita kadai ..kaje ta kitsa maka shiyasa ka kafe sai ka hada su to bazai yiwu ba.

Yace Anty ai na Riga na gama magana Kuma ba gudu ba ja da baya,in taga zata dawo su zauna fyn in Kuma sunga haka suka zaba shikenan…

Iyyeh! Yaya babba tace ah lallai malamin Maryam ya iya aiki sai ta je ta Kara masa kwarin gwiwa,dama ai bazata barka ka zauna da wata mace ba, sai ita shafaffiya da Mai…

Haka dai taita sumbatunta ita kadai ba Wanda ya kula ta har suka isa gidan su Rukayyah,yai parking a kofar gidan yace su shiga shi zaije ya dawo in sun gama zai zo ya daukesu …

 

Suka shiga cikin gidan sun tarar da mutane cike da gidan, aka kira musu mejego ta taho da baby a hannunta, ba laifi ta amshesu sama-sama,ba yabo ba fallasa, an kawo musu abinci da Bai zai ishi mutum 2 ba balle su hudu,mommy kuwa ko kallon inda suke batai ba.

Kowa sai wani kallon wulakanci suke musu suna ganin ya wulakanta musu yar’uwa ya yaudareta,har habaici suka zo har gaban su suna yi wai ke ruky ma in Banda Abinki ma me ya kaiki hada jini da wadannan kazaman da basu da wani kyakkyawan asali,ai kinfi karfin mai mota sai Mai jirgi,Baki dace da Matar kanana ba, sai govenors ko yaran sarakuna ,Amma kin tashi kin kwaso Mana yuyuyu..

Cikin fushi ta dakatar da su da fadin haba Anty fanna me haka, ynx kin kyauta kenan abinda kukai…

Shashasha shi yasa yake gara ki kamar tayar Keke har wani kareshi zakiyi mutumin da ya gama tozarta ki a idon duniya ..ba wai kareshi nake ba Amma ai abinda kuke be dace ba ko…

Tashi sukai suka bar wurin har da tsartar da yawu wai wari suke..

Su matar Yaya kuwa tuni ransu ya gama baci da wnn can fuskar cikin bacin rai suka tashi zasu tafi ..taita Basu hakuri akan abinda yan’uwan mommy sukai, ko abinda aka kawo musu ma Basu ci ba dama waina ce kwaya 3 sinasir 1 da wata miya da Bata fi ludayi daya ba,sai nama 2 acikin miyar,Amma don jaraba Yaya babba nema take ta sa hannu taci naman don rashin zuciya,sai da goggo turai ta daka mata tsawa tace meye haka ne!

Sannan ta hakura ta ajiya ba don ya so ba,shine rukayyan tace ko ajuye muku ku tafi dashi Sika ce Alhamdulillah min gode sai da Maryam ta tai Mana Mai rai da lfy Mika fito..tana ji an ambaci sunan makiyarta ta daure fuska har da jifansu da harara ba tare da sun gani ba.

Tai musu Allah ya kiyaye..har sun tafi sai Yaya babba ta Kira Rukayyah tace zasu magana suka Dan kebe inda ba mutane tace Mata dama hakuri zan Baki kiyi hakuri ki dawo gidan mijinki,duk da nasan ba laifinsa bane laifin wnn munafukar matarsa ne,Amma kanina Yana matukar kaunarki baya cikin nutsuwa tun daga lokacin da kika barshi kullum bashi da magana sai ta amaryarsa,shiyasa Naga ya dace in sanar dake matsayinki a wajensa wlh mijinki Yana matukar kaunarki, ba yin kansa bane…🤔 Oh su Yaya babba girma ya fadi da karya…. itako an tabo Mata inda yake Mata kaikayi Nan ta washe Baki a zuciyarta tana cewa ai nasan Abbas Yana masifar Sona matarsa ce ta shiga tsakaninmu Amma tuda hakane Suma yan’uwansa sun gane zata gane kurenta sai na kwace mijinah…Yaya babba ce ta katse Mata tunaninta da cewa to Bari mu tafi Amma ki kula kinji kiyi tunani ki dawo gidan mijinki.

Tace ngd Anty Allah ya saka da Alkhairi Kuma naji dadin bayaninki zan yi tunani, har da ciro kudi 3k ta Bata tace asai goro ..ta karba cike da farincik Abin nema ya samu..sukai sallama ta tafi..su matar Yaya kuwa tuni sun gama kuluwa da ita har sun gaji da jiranta ..tana isowa suka Yi kanta kowa sai cewa yake abinda tayi Bai dace ba ita Bata kishin dan’uwanta akan wulakancin da sukai musu…

Tace yo ma Zama manyan banza Abu ya faru bazamu sulhunta su ba…goggo tace ai Basu dauko hanyar sulhun ba,ki dai canja wnn halin naki gaskiya na rashin kishin Kai ..haka dai suka sakata gaba kowa sai fadin Albarkacin bakinsa yake..tace naji za’a kiyaye!

Amma karku Gaya Masa wulakancin da sukai Mana Kar ya Kara kullatarsu ko kuwa…

Anty Fatima tace ai gara a Gaya Masa ya San matsayinsa a wajensu ai Allah ya Kara masa Yana zaune lfy ya kwasowa kansa jaraba..Ina amfanin hada zuriya da wadannan marasa mutuncin.. ni ai garama kawai ya sawwake Mata ya huta, goggo tace a gaskiya dai kananan mutane ne Basu da kirki ..Yaya babba Kuma tace hakanan zai hakuri ya dawo da ita zasu Dena ..Anty fati tace ni Yaya wlh bansan me yasa kike rufe idonki akan mutanen Nan ba ai dan’uwanki Zaki tausayawa ..tace yo ai yafi kowa sanin halinsu Kuma ya aura a haka Allah ya daidaita kawai..ita dai bakinciki. Maryam ta zauna ita kadai ne yasa ta ke son ya dawo da rukayyah ta dauki tsana ta dorawa Yar mutane ba gaira ba dalili kawai don ta zamo Mai biyayyah da sanin hakkin aure,shiyasa take gani kamar ta asirce shine …

Koda Abbas ya iso suka tafi yace ba dai matsala ko ..har Anty Fatima xatai magana Yaya babba ta tabo ta wai kar ta fada ..Shima ya gane akwai wani Abin Amma da ya ga suna boyewa Bai takura musu ba ya kyalesu …

A gidan Yaya suka sauka,suka ce gobe zasu zo suyi sallama zasu wuce danbatta ..yai musu godiya da sai da safe..

Washe gari sukai wa su Maryam sallama ta musu Alkhairi kamar yadda ta Saba suka tafi…

Amma Yaya babba ta ja kunensa duk yadda za ai yaje ya dawo da matarsa …ya bita da toh..

Bangaren Rukayyah kuwa ynx ta Fara saukowa akan fushin da take da shi..don kusan kullum sai ta Kira shi a waya..wani lokacin tace tana bukatar Abu kaza Kuma zai je ya Kai Mata sbd yasan hakkinsa ne yayi..a haka Kuma aka bude sabuwar soyayyah don Shima ynx kusan kullum Yana hanyar zuwa ganin babynshi..

Amma da ta tabo shi akan batun ya janye batun hadasu gida daya sai yace Nan fa daya …

Da dai ta ga ba shi da Shirin canzawa sai ta Fara tunanin sauke ra’ayinta tunda dai tana son mijinta Kuma ga Yar da ke tsakaninsu ..tana ganin gara ta hakura ta je tabi umarnin mijinta,Kuma ya Mata Alkawarin insha Allah u ba wata matsala da izinin Allah yace kece baki fahimci Maryam ba Amma mace ce Mai saukin Kai da fahimta a tunanina in kin kwantar da hankalinki ba abinda zai faru…

Tace sai ta sanar da mommy tukun taji shawararta akai..yace ba damuwa Allah ya sa muji Alhakiri….

 

Aiko suna gama magana da Abbas ta shaida ma mommy akan ta hakura ta kyaleta ta koma gidan mijinta ..insha Allahu yace ba wata matsala da zai biyo baya…

Mummy sakin baki tayi tana kallon diyarta da mugun mamaki…tace Do u know what ur saying ? Kina HAUKA ne Zaki zo min da wnn batun ..ok kinje ya gama siyeki da dadin bakinsa na yaudara shine kika so Nan Nima Zaki min ? To baku Isa ba wlh Ina so ki Kara shaida masa cewa indai Bai canja kudirinsa ba, Nima ba abinda zai canja nawa ..mu xuba ni da shi shege ka fasa..

Ruky kuwa najin batun mommy ta fashe da kuka ta shige daki da gudu ta rufe kofar ta fada gado tana kuka…sbd tasan halin mahaifiyarta in ta kafe akan Abu daya ..tace ynx shikenan Ina ji Ina gani xata rabani da masoyina sbd ynz ne ma taji tana Masa wani irin so Mara misaltuwa..

Ina ba zai yiwu ki kashemin aure ba mummy sai na san duk yadda nayi na koma gidan mijinah..wayarta ta dauka Tai dialing no. Daddy ta shaida masa cewa Abbas ya Bata hakuri Kuma ya Mata Alkawarin ba za’a samu matsala ba …ta Amince xata koma Amma mummy ta hanani…yace ki kwantar da hankalinki tunda ynx kin gane gaskiya to kamar kin koma gidan Abbas ne,ki kyaleni da mummyn Taki zan dauki mataki akanta tunda ba ita kadai ke da iko da ke ba..zamuje duk inda zamu akan haka..sukai sallama Tai masa godiya.

Farin ciki fal zuciyarta kwata kwata ynx ba abinda take so face ta bude ido ta ganta a gidan mijinta ..daukar Khadija tayi ta rungumeta tana cewa kwanan nan kema Zaki fara jin dumin jikin daddynki Zaki samu kulawa irin ta ‘ya da uba kinji my angel!

Ynx 3 month da haihuwarta

🤣🤣🤣

*Su ruky anga uwar bari waya Gaya mata borno gabas take …*

 

 

Muje zuwa …

*Ummu Ameer ce* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story&written*

 

 

*By*

 

*Ummu Ameer* 💃

 

*Page* 2⃣7⃣

 

 

Daddy kuwa Kiran mommy yayi yace ta fidda hannunta akan batun diyarsa tunda tunda Bata dorata akan hanyar da ta dace,in ba haka ba kuwa duk abinda ya biyo baya ita ta jawo….ita kuwa tace ai wlh banga abinda zai sa in bari rukayyah ta zauna da kishiya gida daya ba…ta Riga ta gama Zama da shi muddin bai janye ra’ayinsa ba…wancan karon ka ci galaba akaina Ina ji Ina gani ka bawa Mai Mata yarinyata na kyaleka ..kayi nassara ruguza min tsarina na hakura wnn karon kuwa baka Isa ba wlh …ba zan taba amincewa da kudurinku ba..gara ma tun wuri ka canja shawara..ita Kuma zata gamu da ni ne…ta katse wayar…

Daddy kuwa sororo ya tsaya Yana kallon wayar da mamakin wnn mugun Hali nata,wato ba abinda ta canxa a hallayyarta sai ma abinda ya karu …mu zuba ni da ke!

 

 

Bayan sun gama wayar da mommy ya Kira rukyn yace ta kwantar da hankalinta komai zai daidaita …tace ngd daddy Allah ya saka da Alkhairi..Kuma yai Mata nasiha akan ta daina biye wa mahaifiyarta…tace toh insha Allahu zan kiyaye!

 

 

Shi kuwa Abbas tunda ya fahimci ynx ruky ta Amince zata dawo …har ya Fara gyara a gidan …a yadda ya tsara gidan kuwa wnn falon da kitchen da bedroom dinta duk na Maryam sai dakinsa guda daya,saura 1 bedroom, shi aka barwa Maryam sai ya shigo da wani dan fili akai Mata falonta da kitchen …sai Kuma dakin ..tsarin da yayi ba lallai ma said sun hadu ba,sai sun so hakan don kofar shiga falon nata ma ta baya akai mata,toilet kuwa each room contain.

 

Ya zage sai gyara yake inda kuwa mummy ba ta canza ba,akan batunta duk tabi ta tsangwameta a gidan ta daina kulawa da ita har sai ta janye batun komawa gidan mijinta in ba haka kuwa zata cire hannunta a rayuwarta gabadaya…

Itako ta dage komawa ba fashi hakan ne yasa aka Fara zaman doya da manja da mommy d ruky…

Tabi duk gidan wadanda tasan tana Jin maganarsu akan ta hakura ta kyaleta ta koma gidan mijinta …Amma ta ki sauraran kowa ta rufe idonta ta kafe akan magana daya … daddy ma ba irin barazanar da Bai yi Mata ba Amma ta kafe …

Rukayyah kuwa ta shiga tashin hankali Mara misaltuwa,duk ta rame ta Kara Baki ta lalace,ita kuwa Khadija sai faman girmanta take tayi mulmul ba ruwanta…hatta da ita ma mommy ta rage kulawar da take Mata,duk da dinbin kaunar da take ma yarinyar..kawai dai tana yin hakan ne don rukayyah taji haushi ta canja ra:ayinta…Amma ta fahimci ko gezau, ta fahimci idon ta ya rufe,Bata Jin maganar kowa…

 

Abbas kuwa tuni ya gama gyara,Kuma ba laifi tsarin da akai mata yayi kyau itama,sai dai wajen Maryam Nan ne gidan.

Duk Abinda mummy ke yi da tsanar da take nuna masa,duk kwashewa take tana fadawa Abbas, *don HAUKA* ko soyyaya ce ko meye ita ta sani, duk da cewa Shima ya sani..

 

Lokacin da ya gama gyaran ma har daukarta yayi ya kaita ta gani,ya Yana Amma ta nuna inda take bukatar gyara … Ba yadda baiyi ta shiga ta gaishe da Maryam taki,sai Khadija dake hannunsa ya shiga da ita wajen yan’uwanta itama Maryam din ta dauketa tai Mata wasa.

 

Bayan sun gama ya maida su gida dama ita da wata cousin dinta ne Aisha, itace ma ke Mata fada akan kin shiga wajen Maryam din da batai ba..

 

 

Daddy kuwa ya yanke hukuncin sanar da mahaifiyar mommy sbd tana mutunta shi, Kuma ta San halin yarta sarai, tasan iriin zaman hakurin da yayi da ita,ko da suka rabu cewa tai tayi asarar miji bazata Samu kamarsa ba,wnn ne yasa take mutunta shi sosai…

 

 

Ai kuwa haka akayi, takanas ya shirya ya tafi maidugurin Tai masa tarbar mutunci,bayan sun gaigaisa ya kwashe duk abinda ke faruwa ya sanar Mata ranta ya baci,tace wato yadda taiwa kanta sagegeduwa shine take so taiwa yartata..Aiko Bata Isa ba…ta bawa daddy hakuri,sannan tace zata shirya taje har gida ta sameta…yayi godiya yai Mata Akhairi taita godiya sukai sallama ya yafi…

 

Bayan kwana 2 Haj. Babar mummy ta shirya sai gidan mummy, rukayyah ma Tai murna da zuwanta domin itama tana Shirin Kai karar mimny haj.tace ai abinda ya kawoni kenan mahaifinki ne yaje ya Gaya min duk halin da ake ciki..rukayyah Tai ta murna tasan matsalarsu tazo karshe don tasan mommy tana Jin maganar hajiyarta….tana matukar shakkarta.

Bayan Haj. Ta huta ta samu yarta Tai ta Mata fada akan mummunan kudirin da ta sa aranta…tace Kuma ta gaggauta janye wnn ra’ayin tun kafin ranta ya baci…taso musawa mahaifiyartata,Amma sanin halin haj.ta sbd Bata da wasa ko kadan,duk da itama ta zuba mulki a gidan mijinta kafin ya rasu..

Mummy tana ji tana gani aka Sanya ta janye kudurinta, Amma tace ba hannunta a ciki bazata sake shiga sha’aninta ba,ko matsala ta samu karta Fara dumfararta da duk wani Abu da ya shafeta..har kukan bakinciki mommy tayi ga haushin taje ta Kai kararta wajen wadda tasan sai taci galaba akanta…ranta ya baci sosai Anty batulu dama na gidan sai Kara zugata takeyi akan ta zame hannunta akan lamarin rukayyah in ba haka ba sai bakincikin su,ya kasheta…

 

Rukayyah kuwa wnn Rana ko bacci bataiba, don farinciki,har ta bugawa Abbas ta shaida masa yace Allah ya tabbatar Mana da Alkhairi….

 

________________________

Rukayyah kuwa ynx ba abinda ke ranta sai hanyar da zata bi,domin ta Kama shi a hannu ta juya shi son ranta..ta kwace mijinta tun kafin ta koma gidan….

Hakane yasa ta Fara shige da fuce don ganin ta sameshi yadda yake so Kar a samu mtsala kamar yadda ta faru a baya…..

Burinta Kuma ya Fara tasiri,don ynx Abbas jinta yake sosai a ransa,ji yake Yana Mata wani irin so,duk yabi ya damu akan ta dawo …ita Kuma tace ya Kara Mata lokaci…tayi hakan ne don ta gama gudanar da duk wani Shirinta akansa…kuma duk wani shiri da takeyi a Alhajihunsa ne,shi Kuma idonsa ya rufe ko me ta tambayeshi cikin barin jiki yake yi…har wata malama dake yin lecture akan Mata taje ta hada Mata magunguna masu tsadar gaske…

Sai da ta tabbatar da ta gama kamashi a hannu ta ko ina sannan.. aka sa date din daxata tare sai da tasa ya cika Mata akwati biyu da nata da na yarinyarta da Kaya masu kyau…

 

Ranar Asabar itace ranar da rukayyah zata koma gidan Abbas ya rage saura 3days kenan yau….

 

Bangaren Maryam Kuma ko wane shiri take yi…..?

 

Sai min hadu a page na gaba ……

 

 

 

*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
KISHI KO HAUKA
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

 

 

*Story&written*

*By*

*Ummu Ameer* 💃

 

 

 

*Page* 2⃣8⃣

 

 

Bangaren Maryam kuwa ta dage da addu’a Allah yasa hakan ya zame musu Alkhairi gaba daya..ita kanta tana mamakin wnn dokin da yake akan Maryam…don ko lokacin da zai aureta Bai yi haka ba..

Bata wani dorawa kanta mugun kishi ba..sbd ta San za ai haka ballantana an Dade ba’a hadu ba….ita dai kawai addu’a tasa a gaba sbd itace takobin mumuni..

 

Shi yasa bata damu kanta ba, ta wahal da zuciyarta…matsala daya ce ke damunta wato karamin cikin dake jikinta Wanda ko Abbas Bai San da shi ba…Kuma Yana wahal da ita sosai..

Amma duk da haka batai sake da gyara kanta ba, dama Kuma ita ko yaushe cikin gyaran take ..sai dai ba kowanne take amfani da shi ba sbd cikin da ke jikinta,akasari Daman da kanta take hadawa cikin sauki ga Kuma aiki…

Ta fannin jiki da kwalliyarta ma ba abinda ya canza …dama ita ciki Bai hana ta gyaran jiki sai dai kawai canji yanayi na masu juna 2 ..Wanda in ba’a daure ba shi ke kawo kaxantar da rashin gyara..

 

 

___________________

Rukayyah kuwa shiri take kamar wata sabuwar Amarya ta zage sosai ta Sha gyara ..a ganinta abinda Maryam keyi kenan ta gama sace xuciyar Abbas…yake rawar kafa a kanta ..Bata San cewa ba maganin Mata ne kadai ke saka mallaki zuciyar miji ba..in Zaki Sha duniyar Nan matukar Baki da tarbiyyah,ko rashin iya kula da miji,da rashin iya girki,da dai ire-iren wadannan abubuwa da Kuma Mai gaba daya *hakuri* to babu tasirin da Abinda kike Sha zai yi ko da Yana yi to wadannan abubuwan da kika rasa sai sunfi tasiri, shi yasa ynx Mata suke ganin in dai ta Sha gyara to Bata da matsala da miji..

 

Duk wnn shiri da ruky keyi mommy Bata ko shiga harkarta ba, ido kawai ta zuba Mata.

Ranar da za’aje jere ma gidan ba Wanda ta Kira a fanninta sai kawayenta da kanwarta, da ita kanta ne suka je suka shirya abinda zasu iya..sauran Kuma sai Abbas din ne ya karasa shiryawa..kayan ma ba duka ta bayarba,wai a Ina xata aje, taji ance ai daki ne daya sai karamin falo..abinda ya Kara sa tsani auren.

 

Ranar Asabar da daddare aka dawo da rukayyah gidan Abbas,tare da kannen daddy da Kuma matar daddy, sai kanwar rukayyah,mommy cewa Tai ba Wanda zai taka kafarsa xuwa gidan a danginta, ba arziki suka rabu.

 

Bayan sun kaita sun Kara yi musu nasiha akan su dinga hakuri da juna, sannan suka ce akai su wajen Maryam, don su musu nasiha su zauna lfy..har rukayyah akace suje Taki zuwa sai da kanwar daddy Tai Mata fada sannan suka shiga wajen Maryam.

Ko da isarsu ta amshesu hannu biyu cikin sakin fuska,Kuma ta kawo musu abin motsa Baki,Suka gaisa ..Amma rukayyah ko gaisheta batai ba sai harararta take taga want kyau da ta Kara yi Mata akan sanin da Tai mata…and cikin ya Kara mata kyau da haske ta Kara cika..

Tasa hannu tana ta karbi Khadija tana Mata wasa,sai a lokacin ne ta Dan sake taga tana yiwa diyarta wasa..ita ko Bata taba daukar ya’yan ta ba balle Tai musu was..a zuciyarta tace makirci ne da kissa ..

Su gwaggo da Anty nusaiba sukai musu nasiha akan su hade kansu su zauna lfy…Maryam tace insha Allahu … Sukai Mata sallama suka tafi..ta rakasu har waje,sunji dadin yadda ta mutuntasu sukace ai da ganinta Bata da matsala ..suka kara yi Mata fada ta cire kishi a ranta su zauna lfy fa kishiyarta…sukai musu sallama suka tafi…

Ruky kuwa sai rawar Kai ake an dawo gidan Miji…wasu Riga da siket ne ajikinta duk kirjin a waje..shayarwar da take yi ne suka ciko..Amma siket din sai kace an daurawa muciya zani…

Sai faman karairaya ake wa mijin..Shima din sai wani rawar Kai yake Mata..

Bayan sun dawo ya Kira rukayyah wajen Maryam ya Kara yi musu nasiha,akan su zauna lfy..tana sane da yadda yake ta rawar kafa akan rukayyan…bayan ya gama sukai Mata sallama, ya dauki abinda zai dauka a dakinsa yai Mata sai da safe…sai wajen ruky…

 

 

Muje zuwa

*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

*Story&written*

 

By

*Ummu Ameer* 💃

 

 

*Page* 2⃣9⃣

 

 

“””Maryam kuwa tun fitarsa daga wajenta ta kasa samun nutsuwa kishi ya tashi …ya Hana ta sakat,duk yadda taso ta kawar da Abin a ranta ta kasa tana Jin motsin su,dake duk waje daya ne kawai dai hanyar shiga can ne yayi ta baya Amma duk Abinda ake anaji..

Zuciyarta sai faman bugawa take kamar ta fashe..sai addu’a take bacci ya dauketa take ..Amma fir bacci ya dauke a idonta ..data tuna mijinta suna tare da wata ko ta danji wani motsi sai taji wani Abu ya tsaya Mata a rai…tace sanda suna can ba abinda ya dameta…

Haka dai taita juye-juye dake bacci barawo Bata San sanda yai gaba da ita ba..Amma sai kusan 3am na dare..

Can wajensu rukayyah kuwa an kwashi soyayya an Dade ba’a hadu ba..

___________________

Washe gari bayan ya dawo daga masallaci yai karatun qur’ani kamar yadda ya Saba ..wajen 7aam yaje ya bude gidan daga Nan ya wuce wajen Maryam yaji ya suka kwana..A wnn ranar ta kasa danne kishinta da ya shigo ta amsa Masa sallama Bata Kara bi ta kansa ba ..ta shige kitchen don ci gaba da hada break fast..gashi duk gidan ya dumame da kanshin girki ..qamshin ne ya tashi ruky daga bacci..don tun kafin ya fita masallaci yake ta tashinta Taki tashi ..gashi ya tsani wnn lalacin da take da shi Kuma ya lura Bata canja Hali ba..tana farkawa taga ba miji..ta leka ko Ina Bata ganshi ba..sai muryarsa ta jiyo a wajen Maryam..tace kan ubancan.. wnn mutumin Bai daina halinsa ba kenan ..Bari yaxo wlh baxata yiwuba ..matukar Yana San zaman lfy..

Ga haushin ta karade musu gida da qamshi…tana tsaye tana jiran shigowarsa da taji alamun ya shigo Tai saurin shiga toilet..Kar ya sameta har ynx Bata shiga ba.

 

Maryam kuwa a sanda ya shiga wajenta ta gyara ko Ina da wankanta dama ita tun asuba take yin wankanta Tai sallarta,wani lokacin ma ita ke tashinsa daga baccin..

Koda ya dawo bangaren rukayyah kuwa Yana Jin sanda ta shiga toilet sai alokacin ne zatai wankan ,balle ko breakfast da Bata ma Fara Shirin yi ba..tsoki yayi a zuciyarsa yace dama Mai Hali Bai fasawa…

 

 

 

**** ****. *****

Kwana 2 yayi a wajen rukayyah,ya dawo wajen Maryam …

Ranar da ta fita girki kusan zaucewa tayi sbd tsabar kishi..ji tayi dama ta bar gidan in girkinta ya zagayo ta dawo…a ranar kasa yin komai tayi a gidan ko abinci Bata dora ba,wnn Kuma halinta ne in dai ba ta da girki tun acan gidan da ta Fara Zama,batayi sai ranar girkinta ko waye a gidan sai dai asha complex ko indomie kiwar girkin take…

 

Da daddare kuwa da yaje sallama tsiro da wani makirci tayi taki bawa Khadija nono,Kuma tasan shi take bukata ..hakane yasa taita kuka,ko da yazo ya tambayeta Mai ya faru tace itama batasani ba sai faman kuka takeyi..ya karbeta yaita jijjigaya yarinya kuwa yinwa na cinta sai faman ihu take ..sai da ya kusan 1hr daga sallamar da Bata wuci 10mins ba …sai da tasan ta kunna Masa wuta…. tukun ta amsheta tace Bari na Bata Tasha ko tayi shiru..sbd tasan shi akwai kulawa da yara Kuma ya iya rainon..tasan bazai iya tafiya ya barta a wnn halinba shiyasa ta kunno da wnn salon..don ba kowa ne ke son rainon yara ba, wasu mazan ma in suna kuka yaran ficewa suke su bar gidan..

Yai mata sai da safe ya tafi …itako zuciyarta fari Kal…

 

Maryam kuwa da taga shiru Bai dawo ba..a zahiri ranta ya baci..Amma da ta tuno halin ta,ba ynx ta Fara haka ba..sai ta saki ranta ko da ya shigo ma Bata wani nuna Masa komai ba..Kuma dama ita ko laifi yayi Mata Bata nuna Masa a lokacin sai daga baya ta nuna Masa rashin jin dadin abinda yayi..balle Kuma ynx ga kishiya a kusa ta Yaya zata Bari ta jiyo wata baraka daga garesu…duk Tai masa abinda ta Saba..ba tare da nuna Masa komai ba..ga wani kyau da yaga ta karayi Masa ..Wanda Bai lura da hakan ba sai ynx…Nan da Nan wani shaukinta ya kamashi…ga wani cika da ta karayi..sai wani mayataccen kalloh yake binta da shi..sai kace Wanda Bai taba ganinta ba…yace ranki ya Dade wai menene sirrin ne Kinga wani kyau da kike yi kuwa..murmushi kawai tayi.

Don ma a kwanankin nan yana Dan samun matsala daga gareta Bata cika son bashi hakkinsa ba har fushi yayi da ita ..shi Kuma cikin yanayin da yazo Mata da shi kenan duk sauran ciki Bata samu matsalar Nan ba..akasari Kuma Mata sukan fuskanci haka in cikin Yana karami Amma in ya fara girma sukan dawo normal.

A wnn Daren ne Kuma ta Gaya Masa tana da ciki..yaji dadin sosai har Yana cewa ko yara nawa zata haifo Masa bazai gajiya ba..sbd ta iya santalo kyawawan yara ..tai murmushi tace masu Kama da Kai ko..yace wane ni ai ke suke biyowa saidai su dauko wasu abubuwana.

Sai ynx ya gano dalilin da yasa take gudunsa kwana 2, sbd cikin da take da shi…yasan dama masu ciki suna samun wnn matsalar.

Suka kwanta cikin farin ciki da annashuwa Kuma yaji dadin kasancewa da ita a daren..duk da itama rukayya yaji canji a wajenta ..Amma bazai taba hada su daya da Maryam ba,Yana alfahari da ita sbd ita ta daban ce a cikin Mata..tuni ta mantar da shi komai..

Rukayyah kuwa a wnn dare kasa Zama tayi tunda ya dawo wajen Maryam har labe take taji hirar da suke amma ta kasa sbd Maryam Bata daga murya sosai in suna hira da Abbas ko bama shi ba haka take maganarta, sai dariyar Abbas kawai take ji sama-sama ..ranta ya baci wato dama har dariya yake haka Amma ni sai in Dade ban ga dariyarshi ba…lallai ne wato har ynx da saura na kenan,haka taita labenta har sai da taji Shiru …alamun basa falon sannan ta zagaya ta daidai saitin dakin Maryam taji Shiru..ta zagaya ta saitin dakin Abbas sannan Taji motsinsu..tace lalai ita har turaka ne ma da su…haka ta kasa kunne ko xata Dan ji wani abun shiru..Bata ji komai ba sbd an rufe dakin ga karar A.c ta hana ta Jin komai..hakanan ta hakura itama ko barcin kirki Bata samu yi ba..sai kusan asubahi maimakon Tai sallar ta kwanta sai ta yi baccinta..har Abbas din yazo yayi ta kwankwasa kofa Amma shiru ..tayi nisa a baccin…yayi komawarsa can…

 

 

Muje zuwa

*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

 

*Story & written*

*By*

*Ummu Ameer* 💃

 

 

*Page* 3⃣0⃣

*Kuyi hakuri da rashin jina kwana 2, sabgogi ne sukai yawa…ngd sosai da kulawarku* 😘

“””Ko da Rukayyah ta farka taga kusan karfe takwas na safe,Amma Abbas Bai shigo ba, ranta ya baci sosai, hakanan ta tashi jiki a sanyaye ta shiga toilet..sai a lokacin zatai sallah, bayan ta idar ta dawo falo ta zauna ta cika fam da Abinda Abbas yai mata,jiran shigowarsa kawai take ta zazzaga Masa bala’i… sleeping dress ce a jikinta don ko wanka batai ba.

Tana Nan zaune ita Ba ga wankan ba,balle gyaran gida ga shi har ynx Abbas Bai shigo ba…

Sai karfe Tara ya shigo,yai sallama ko amsa masa batai ba, Yana ta magana Tai masa shiru..yace wai lfy na shigo Ina ta magana Baki tanka min ba? Me Kuma ya faru ..ai bazaka San Abinda ya faru ba tunda a tunaninka daidai kayi..wai yaushe ne xaka Fara kamanta adalchi a tsakanin mu..ko yaushe kana kokarin fifita uwargidanka akaina..ta Yaya kuwa kake tunanin samun zaman lfy a gidanka? Idan kana wajena,kana tashi tun kafin gari ya karasa wayewa kake shiga wurinsu,Amma ni sai ynx ne kake shigo min sbd baka damu da mu ba…wlh bazai yiwu ba Ina ji Ina gani na Zama wulakantattiya a gidan Nan ba, ya Zama dole ka canja tsari…

Shi kuwa tsayawa yai Yana kallon ikon Allah na gajen hakurinta…yace na shigo kina bacci shiyasa na tafi kar na katseki ..

Tace meyasa baka tasheni ba?

Yace Am late idan na dawo mayi maganar…yai mata sallama ya tafi,binshi tayi da idanuwa ko Allah kiyaye batai Masa ba…

Yana fita ta durkushe a wajen ziciyarta na tafarfasa, a ziciyarta tace har ynx da saurana akan mutumin nan,tana mamakin irin soyayyar da yake Mata …a tunaninta ita yafi cancanta ta samu wnn soyayyar, tunda itace Amarya .

Nan da Nan wata dabara ta fado mata, akan ta kwantar da Kai ta shigewa Maryam yadda yadda zata saki jiki da ita domin ta gama sanin duk wani sirrinta domin ta gano abubuwan da take Masa da kuma sanin sirrin zamantakewarsu..

 

Cikin sauri tai abubuwan da zatai ta shirya tsaf ta nufi wajen Maryam …

Ko da Maryam ta ganta har sai da gabanta ya Fadi tayi tunanin ko rashin kirki ne ya kawo ta….Amma sai ta ga fuskar ta a sake cikin walwala …..Maryam Tai Mata iso zuwa falo suka gaisa har tana tambayar Ina yara sun tafi sch.ko?

Maryam tace eh!

Amma tana shakkun Anya kuwa babu wani nufi a tattarre da ita …wata zuciyar Kuma tace ki daina wnn tunanin watakila ta gane gaskiya ta dauki hanyar Zama lfy ….Nan da Nan ita ma Maryam ta saki jiki da ita suna ta hira…Amma in Maryam ta kawar da fuska sai ta jefa Mata wata muguwar harara, sbd a hirar da suke tayi iya kokarinta na gano wani aibu ko cikas Bata gano ba,a tare da ita,ta ko Ina Maryam tayi Mata zarra…..

Tana gidan har Azhar a gidan taci abinci, har kitchen din tabi ta wai zata taya ya aeki….tayi haka ne don ta ga irin sinadarin da take amfani da shi a girki…da spices da curry, taga tsantsar tsafta,domin kuwa taga ko tsinke Maryam Bata Bari sai ta dauke ….Bata barin datti ko kadan a waje.

Rukayyah kuwa gani take hakan wahala ne me zaisa mutum ya Kare a wahala ba hutu ko yaushe cikin aiki ….tace wlh bazan iya ba.

 

Ba ita ta bar gidan ba sai da Abbas ya dawo, ya Kuma ganta a gidan …Shima a zuciyarsa ya zargi wani Abu a tare da ita,ya San a kwai abinda ya kawota…tana ganinshi Tai saurin barin sashe don bazata iya jure ganinsu ba…..

 

 

 

Kuyi hakuri da wnn bani da isasshen lokaci ne shiyasa….

 

Taku

*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI ko HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story& written*

*By*

*Ummu Ameer* 💃

 

*Page* 3⃣1⃣

 

 

Haka rukayyah tai ta amfani da wnn damar na shigewa Maryam don samun abinda take nema…ta danne kishinta na dan wani lokaci.

Akwai watarana da Abbas suna hira da Maryam take ce Masa ni Kam Abban mufid Banga wani hali na ki a tare da rukayya ba,domin ynx ta sauke komai ta bada hadin Kai an zauna lfy….yace ki dai bi a hankali,ba komai Zaki sakar Mata ba …. itako xuciyarta ta gama aminta da ita gani take rukayyah bazata sake yin wani abu makamancin na baya ba…*Maryam ta manta ko Bata San da ba’a Aminta da kishiya ba…komai Jin dadin zaman da kuke*

 

‘yanuwanta ma sai da sukai Mata magana akan tabi a hankali don wasu kishiyoyin ba Abin yarda bane…ita dai jinsu kawai take Amma a tunaninta ba abinda zai biyo baya….

 

 

Sai da tayi wata guda a haka, Kuma Bata San cewa Maryam na da ciki ba…

Amma itama Maryam din tana da wayonta domin kuwa ba komai ne ta Bari rukayyan ta sani ba dangane da zamantakewarsu.

Ba Abinda ya fi tsayawa rukayya arai irin yadda taga ya dauki son duniyar Nan ya Dora Akan su mufid sosai yake nuna musu wani irin so da kulawa ….kasancewarsa caring father, ko tari sukai duk sai ya wani kidime ya rikesu Yana musu sannu, Kuma ko a gaban waye baya kunyar nunawa yaransa kulawa …wannan ne yasa rukayya ta Kara tsanar Maryam da yaranta.

Domin ynx ko kula yaran Bata yi..kwanaki kuwa ta danne halinta ta Dan jasu a jiki dama na munafurci ne…

Sai Abu na 2 da ta fahimta a tare da shi kwata-kwata baya nunawa Khadija irin soyyayar da yake ma sauran yaran…wnn Kuma ba laifin shi bane sbd yarinyar akwai kiwa in ba su mommy da ta taso a gidansu ba,Bata yadda da kowa Bata shaku dashi ba tun farko yayi iya kokarinsa ganin ta Saba da shi Amma har ynx Bata Saba da shi ba,Amma Yana iya kokarinsa kawai dai rashin godiyar Allah ne…

Kuma sauran yaran tun suna jarirai kusan shi ke rainonsu in dai Yana gida,sai dai in suna bukatar abinci ne zai kaiwa mahaifiyarsu,sun shaku da shi gaskiya fiye ma da ita mahaifiyarsu.

Wannan dalilin ne yasa rukayyan ta dinga cusa Masa yarinyar ta karfi…da ya shiga gidan in ba girkinta bane sai ta manna Masa ita wai ya tafi da ita aeki takeyi,tun yarinyar na ki, har ta fara sabawa da shi Amma ba kamar sauran ba, sbd yasan takan yara sosai.

 

Ta fannin girki kuwa duk idon da ta Sanya akan yanayin girkin Maryam,in taje zata gwada ba ya taba yin kamar na Maryam din don sau tari ma kasa ci yakeyi ….duk sanda yaki ci kuwa ba zaman lfy kwana kuka wai taga in a gidan Maryam yake zagewa yake ya cinye tana sane da shi,Amma ita ta wuni tana yi don ta faranta Masa yaki ci…a ranar ko bacci gagararsu yake sbd bala’inta.

Har cewa yayi taje Maryam din ta koyawa Mata …tace Allah ya kiyaye tunda ta Kai ga Abincin ma baka Jin dadin na kowa sai nata….

Duk da cewa har ynx tana aiki akansa Kuma Yana tasiri..sai an danyi kwana 2 sai Kuma ya sakeshi…sai a Kara himma.

Cikin wani ikon Allah duk Abinda takeyi akansa baya shafar Maryam din, don har ynx Bai canza Mata ba,a ko yaushe darajar ta karuwa take a wajensa Kuma ko da wasa Bai bata dama ta Raina ta ba.sbd zuciyarta kyakkyawace Bata da mugun nufi…ga Kuma addu’ar da Bata sake da ita. Ta dauketa da zuciya 1.

Hakan da rukayya ta gani abun ya tsaya Mata duk yadda taso ta ga wata baraka ko ta gansu a ruwa Bata gani ba, tana bakin cikin ganinsu cikin nishadi da mutunta juna,ita ba abinda takeso ta gani illa ta ranar da zai Fara wulakanta Maryam ….ta Zama ba komai ba a wajensa ya zamo ita ke iko da shi.

 

****** ***** *******

Akwai wata Rana Abbas zai Kai Maryam Asbiti zata Fara Awo, shine rukayya tace ai itama fita zatayi, dama Kuma girkin rukayya ne, yace ta Bari sai gobe..ba yadda baiyi da ita ba Amma Taki ita a dole sai ta fita, sai da Maryam tace ka kyaleta Mana taje…sannan ya barta Amma ba don yaso ba,. Sbd ya na sane da Abinda take duk ranar da ta fahimci Maryam zata fita sai ta bijiro da ta ta fitar…shikuma ganin akwai Mata 2 a gida Bai dace ace gabadaya sun fita ba.

Sun gama shiryawa tsaf sun fito rukayya Tai hanzarin shiga gaba,har tana tuntube sauran kiris ta Sha kasa, maryam tace hankali dae…shikuwa Abbas tabe Baki yayi….

Ko gaisheta rukayya batai ba,sai Maryam din ce ta gaisheta sai faman wani kimbura take ita a dole an shiga hakkinta ya fita da ita ranar girkinta,Kuma Yana sane da Abinda tayi wnn tasa ko kula ta baiyi ba,sai faman zuba take zancen da ba kan gado sai dai yace eh ko a’a, Aiko ba karamin kuluwa tayi da hakan ba,ya gama kunyatata a gaban kishiya…daga karshe ma Maryam din yace wa mmn mufid lfy kuwa kinyi shiru ko jikin ne, tace a’a .

Haka yaita janta da hira,rukayya kuwa takai kololuwa wajen bacin rai tai danasanin biyosu..kamar tace ya sauketa a wajen, haka dae ta danne Batai Masa magana ba, har akazo hospital din ya fito ya budewa Maryam mota ta fito tace wa rukayya Allah kiyaye ta amsa a dakile ya leka ta window yace Yana zuwa…Tai Masa banza.

 

Tare suka shiga ciki,sai da Maryam din tace ya koma Kar rukayya Tai ta jiransa yace ai ta ga zata iya sai da nace ta Bari gobe ta fita takiji…kinga bani da laifi.

Dake duk yasan likitocin Basu wani Sha wahala ba, anyi duk wani abinda ya dace ayi na masu Awo,suna jiran result ne na text din da akayi ya leka wajen ruky yaga ba ta cikin motar….ya duba ko Ina Bai ganta ba ya Kira Taki dagawa, ya koma wajen Maryam aka Basu suka taho komai normal.

Suna Isa tace ina ruakyya yace Shima Bai sani ba,yazo ya duba Bai ganta ba ya Kira Bata daga ba, tace Abban mufid bansan Ina Zama silar matsalarku naganta cikin damuwa tunda muka taho,rabu da ita … .

Can gida ya kaita wajen ummi yace in ya gama zai zo ya dauketa….

 

 

 

Muje zuwa

*By*

*Ummu Ameer*💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story & written*

 

*By*

 

*Ummu Ameer*💃

 

*Page* 3⃣2⃣

 

“””””Rukayyah kuwa ba inda ta zame sai gidan wata kawarta da sukai school tare, tana zuwa ta hau kuka farida kawar ta ta hau tambayar lfy kike kuka,me ya faru ..?

Ita dai kukanta take sai da tayi Mai isarta sannan ta kwashe komai ta fada Mata da irin zaman da suke ….ai tun kafin ta karasa farida tace Amma kin badani wlh …kina mace tana mace sannan har ki Bari ta fiki tasiri a zuciyarsa …Ashe Baki da wayo ko kadan, Ina ganinki Yar gari Ashe kallon kitse nake wa rogo…..

Rukayya tace to me ake so nayi ? Nayi iya kokarina wajen ganin na janyo hankalinsa gareni Amma kamar ingiza shi akeyi…Kuma duk da haka ba haka na zauna ba, in maganin ya fara tasiri Bai jimawa ajikinsa sai kiga an koma gidan jiya…Ina tunanin malaminta yafi namu karfi….

Wata bazawarar dariya farida ta saki tare da tashi ta karasa kusa da ruky ta dafa kafafarta tana cewa “ke da baki shirya ba kika kwaso Mai Mata haj.ruky?

Ai ya kamata ace kinsan komai akansu kafin ki aureshi, ki San wacece matar kisan wane matsayi take dashi a wajensa kisan irin soyyayar da yake mata, sai ki San irin aikin da ya kamata ki Fara akansu tun kafin ki shiga gidan, Kinga da kinyi haka komai zai zo Miki da sauki Kuma da bakiyi facing ol dis problem ba…at least Kya samu saukin wasu abubuwan.

Ruky tace hakane wlh duk banyi wani tunanin ba,idona ya rufe akansa, banyi tunanin zan samu wata matsala daga gareshi tunda muna son junannmu…kawai matarsa ce ta shiga tsakaninmu.

Yanxu me shawara tunda har ynx Ina da sauran dama…..

Farida tace kinganni nan a cikin gidan nan sai abinda nace wa mijina shi akeyi hatta da provisions na Abinci a bangarena yake sai abinda Naga damar bayarwa ko Bai Isa ba, Basu da damar tambaya….ke hatta da girki in Banga dama ba sai yayi 2-3 wks Bata girki a gidan nan,in banso ba sai yayi kwana da kwanaki baiga fuskarta ba, gashi ni bani da kowa a gidan kinsan matsalata ai tun muna sch. So ynx likita ya tabbatar bazan iya samun ciki ba…Kuma hakan bai canza komai ba daga gareshi…ruky Tai saurin katseta da cewa ke kuwa wajen wa kike zuwa har kika samu wnn nasara haka….murmushi farida tayi tace kin faye gajen hakuri…ruky zan gaya Miki.

Tace ba inda nake zuwa a ynx Amma naje dai kafin na shigo gidan a ynx ba inda nake zuwa sai basirata….ruky tace bangane ba?

Farida ta kwashe duk irin kissa da makirci da Kuma magungunan mallaka da take amfani dasu duk ta fadawa ruky …ruky kuwa mamaki ne ya cika ta Jin irin wanna shedanci na kawarta ….

Nan itama ta karanta mata duk irin Wanda zata Fara Yi a cikin gidanta …Aiko ba karamin farinciki ruky tayi ba tace da Ina dake Amma na tsaya Ina wahalar da kaina….har magungunan ta hada Mata. Tai Mata godiya sosai sukai sallama akan cewa itama farida zata kawo Mata ziyara tazo taga wnn kishiyartata…

 

Farida tare sukai sec.sch.da ruky,dama farida tun suna sch. Bata da kunya gashi Bata tsoron kowa ba wani kyau ne da ita ba, tana da haske shine ma ya fito da ita ga son kwalliya a cika fuska da su eye shadow da eye liner kamar aljana.

Alh Auwal indabawa shine mijin nata Yana zaune da matarsa lfy da yaranmu 4 biyu maza biyu mata, ga matar kyakkyawar gaske bafulatana ce kamar ita Tai kanta, sun taso cikin kaunar juna da mutunta juna.

Kwatsam ya debowa kansa ruwan dafa kansa don farida tun kafin ta aureshi ta gama da shi Kuma gashi mutum ne da yake sake da addu’a da rashin maida hankali ga ibada itama matar Abin Yana damunta tana iya kokarinta wajen ganin yana maida hankali …

Haka akai auren ta shigo gidan da gadara ..cikin kankanin lokaci ta gama da shi,ya zamo tsoron shiga wajen uwar gidan yake kiri-kiri Yana ji Yana gani wajenta ya gagareshi…sai ya tambayi izini a wajenta sai ya tambaya kusan sau 5 take barinshi ya shiga…

Ita Haj.bilkisu (uwar gidan) Bata sake da addu’a tana iya kokarinta da ba don haka ba ma sai Abin yafi haka…kullum cikin tsayuwar dare take Akan Allah ya karya duk wani tuggunta.

 

 

******* **********

Rukayya kuwa da matsanancin farinciki ta koma gida….tare da karfin gwiwa har da kiransa a waya ta bashi hakuri akan tafiyar da tayi yace dama ke kikai kidanki kikai rawar ki …ya wuce sai a kiyaye gaba….tace tnx baby it won’t happen again….sukai sallama tana kashe wa ta saki wani ihun farinciki tana tsalle wai komai yazo karshe…..garin tsallen Bata ankaraba ta takewa Yar tata kafa Tai ta kuka kamar ranta zai fita, Ashe targade tayi…hankalinta kuwa ya tashi sosai ga murna ta koma ciki….

Sai da ya dawo suka kaita wajen Mai gyara yarinyar kuwa Tasha wahala sosai Shima uban sai da ya tausaya mata ruky kuwa kuka shabe-shabe tana taya diyarta ….

Bayan sun dawo yace wai garin yaya kika Bari tai wnn raunin Tai Masa karyar wai tana rarrafe ne Bata San tana bakin kofa ba shine ta taketa….yace Allah ya kiyaye gaba Amma a dinga kula …..

 

 

Jingine duk wani shiri tayi a gefe sai Khadija ta warke sbd tana Jin tausayi yarta sosai ….

 

*To masu karatu muje zuwa shin ruky kuwa zata samu nasarar akan Shirin da takeyi …hausawa dai na cewa in wani yayi rawa an bashi kudi wani duka
zai Sha*

 

Taku

*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story & written*

 

*By*

 

*Ummu Ameer* 💃

*Godiya dubu ga masoya Ina jin dadin comment naku domin shi ke Kara min karfin gwiwa…ngd sosai* ❤

 

 

*Page* 3⃣3⃣

 

 

””’’”’sai da akayi sati guda sannan Khadija ta samu sauki, shiyasa ruky ta jingine komai sbd kulawa da diyarta sbd ba karamin damuwa tayi da ciwon nata ba, tana tausaya mata sosai, tana matukar ji da ita kamar me, Bata son ko kuda ya taba ta…wannan daliline yasa ya aje duk shirinta waje daya tace ba abinda yafi lfyr yarta gudan jininta ….

 

 

 

Ranar Asabar a ranar ta tashi da aiwatar da Abinda suka shirya da farida……

 

Tun wajen 11am aka shiga kitchen ana shirya abinci ta zage iya karfinta ko tasamu ta inganta ya cinye tas kamar yadda yake a wajen Maryam …ta gwada irin na Maryam Amma baiyi irin nata ba…don kin ciyuwa ma yayi Kuma ya gane Sarai na Maryam take son kwaikwaya yai ta dariya a zuciyarsa yace girman Kai ya Hana a koya…

 

Shiyasa yau ta zage ta hada duk wani abinda ke Sanya girki dandano da qamshi…tuwon shinkafa tayi da miyar agushi,kasancewar ta fahimci Yana son kalar Abincin a gidan Maryam in tayi shine ta gwada Amma Ina kwata-kwata tuwon Bai dahu ba aka tuka dama haka take yin tuwanta fa shinkafa batso -batso Bata Bari ta dahu ta tuka ga ruwa aciki Bai tsane ba…sai yayi wani shakakaf, a hakan ma ta gyara ganin yadda na Maryam take nata kamar sakwara, miyar ma haka ayita agushin daban ruwa daban ba kyan gani ….

Sai juice din da ta hada Masa Wanda a ciki me ta Sanya Masa maganin barci Yana Sha zai Fara bacci….

Ta gama komai tana jiran dawowarsa ta gyara ko Ina yau ..itama ta Sanya turaren gidan Yana ta qamshi…Amma da ga turaren ga burner Amma kiwa ta Hana ta kunnawa, yau Kam ta zage don tun safe ake a tsaye Kuma ba karamin jiki taji ba…duk ta gaji abinda Bata Saba ba….

 

Koda ya dawo gidan ya Fara shiga wajen Maryam kamar yadda yadda Saba …wadda cikinta har ya Fara fitowa ya mata kyau …ya sameta tsaf da kwalliyarta hakama gidan tsaf cikin baya Hana ta gyara kanta ko kiwar gyaran gida ta Riga ta Saba ma in batayi ba Bata Jin dadi.

 

Bayan sun gaisa yayi wa yaransa wasa ya danyi mintuna sannan ya wuce wajen ruky….

 

Yana shiga wajenta yaji qamshi Yana tashi an gyare ko Ina tsaf ….Yana shigowa aka wani tafi a guje akai hugging dinshi tana masa shagwabar tayi missing dinshi …shi dai duk ya cika da mamakinta tun a waje ya Fara ganin changes …shi kuwa da Bai shiru da Baki in yaga sabon Abu ko akasin haka yace toh sabon salo kenan yaushe kika canza haka lokaci daya….ta wani langabe Kai tana cewa haba baby! Dama can haka nake …murmushi yayi ya dauki Khadija Yana Mata wasa ba dadewa tayi bacci dama bacci takeji ta kwantar da ita …ita Kuma dama wasu kaya ne ajikinta mini skirt da wata half vest tazo ta zauna kusa da shi ta Fara aiwatar da shirinta sai da ta gama rikirkitashi da salo salo na kissa Wanda Bata taba Yi Masa ba….ai tuni suka Lula duniyar ma’aurata, dama tayi amfani da wnn maganin da farida ta Bata…Aiko ya Mata aiki sbd taga aiki ba kadan ba…

Bayan sun samu nutsuwa ya shiga toilet yayi wank ya Sanya jallabiya ya fesa turare ya fito yace zai shiga wajen Maryam zai kulle gida tace haba baby! Baka ci abinci ba saka fita haba zo na baka kaci ka koshi sai kaje…

Zuwa tayi ta janyo hannunsa ta zaunar da shi ta zuba Masa abinci Yana Kai loma daya …ya furzar da shi kallonsa tayi cike da bacin rai tana cewa bansan ranar da zaka Fara cin girkina ba kullum nayi kace baiyi ma ba…adalchi kenan ?

 

Shiko har da wani janyo ta ta kwanto a kirjinshi Yana wani lallashinta wai tayi hakuri wlh Yana iya kokarinsa wajen ya ga ya ci Amma sai ya kasa….kiyi hakuri ki gyara kinji…

Dagowa tayi daga jikinta ta ce to ga juice din kasha ta zuba Masa cikin glass cup ita ta bashi ma abaki dake yasha sanyi Kuma ba laifi yayi dadi duka ya shanye tas….

Aiko Nan ta saki wani murmushi….Nan take kuwa ya Fara …layi kan kace me bacci ya daukeshi.da dai ta tabbatar da cewa yayi nisa …ta saki dariyar mugunta tace ai sai kaje wajen Maryam din tace Dani kike zancen….

Haka Abbas ya bige da bacci Akan kujera Bai San duniyar da yake ba…shiyasa ta Fara morarsa Yana dawowa sbd tasan zai dauki lokaci kafin ya dawo dai2

 

 

Maryam kuwa ta baza idanuwa Abbas Bai shigo ba…gashi elham tana fama da ciwon ciki…sai kuka take tayi, ta kirashi yafi a kirga Amma ba’a dauka ba…sbd ruky ta Sanya ta a silent Kuma tana ganin Kiran da akeyi

 

Da dai Maryam taji Shiru ta aika mufid ya kirawo Abbansa yace elham ce ba lfy …Amma da ya zo ya Gaya Mata sai tace dallah can tafi ka bani wuri kace bacci yake….

 

Yaro ya fita cike da tsoron tsawar da tayi Masa,yaje ya fadawa mummyn shi, ranta ya baci sosai ga dare yayi tace gashi ba dama in fita ba da izininsa ba…ya zanyi kuka ta Fara Yi tana ya Allah ka taimakeni ya Allah ka kawo min mafita…

 

Itako ruky tana can ya bugawa farida ai aiki yayi tana ta mata godiya …farida tace ba komai kedai kici gaba da kokari zakisha mamaki….

 

 

 

Tofah

Ki biyo ni don Jin yadda zata Kaya….

 

*Taku*

*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

*Story&written*

 

*By*

 

*Ummu Ameer* 💃

 

 

 

*Page* 3⃣4⃣

 

 

 

 

“”””””Maryam taje ta duba
magungunan dake gidan Amma ba na ciwon ciki, ga yarinya na ta murkususu, ta rasa inda zata Sanya kanta, zuwa tayi ta dauko cup da ruwa ta Mata tofi aciki ta Bata ta sha.

Cikin ikon Allah sai bacci ya kwasheta alamun ya lafa Mata.

Sai alokacin ta samu nutsuwa ta Fara tunanin ya akayi Abbas ya kwanta baizo sunyi sallama ba,,,,

Kuma Bai kulle gida ba,,,?
Kuma yaki daukar wayarta ?
Sannan an aika ta koro yaro ,,,,,

Anya kuwa lfy?
Ta tambayi kanta

Tana Nan zaune tana jiran shigowarsa shiru…wata zuciyar tace kije ki gani ko lfy?

Wata zuciyar Kuma na Hana ta sbd ta fahimci tun ranar da suka fita tayi tafiyarta ta daina shigowa gidan Bata kula yaran, shiyasa itama ta fita a harkarta….sai ynx ta gane gaskiyar wadanda ke gayamata ya bi ahankali ta gane kawai zuwa tayi ta bugi hancinta,,,Kuma dake Allah na tare da Mai gaskiya Allah Bai Bata ikon aiki da Shiba ko tayi ma Bai yin tasiri…

Ko da Maryam taga har 12 na dare ya wuce tashi tayi take ta kulle gidan ta rufe ko Ina na bangarensu ,,,cike da fargaba a zuciyarta don zuwa ynx ta Fara tsoron rukayyah Bata son wane abin take kullawa ba kuma.

 

 

******. *******

Washe gari har wajen 7na safe Abbas Bai farka ba da taga Abin yayi yawa Kar asiri ya tonu shine ta tasheshi ya tashi cikin magagi alamun baccin Bai sake shi ba…sai a lokacin ta tuna ta zuba kwayar ne da yawa …a haka dai ta takura ya shiga toilet yayi Alwala yazo Yana sallar Amma kana ganinshi kasan bacci ne Bai ishesba Yana idarwa ya Kara komawa…tace na shiga uku….karfa a gane abinda nayi,,,,

 

 

Maryam kuwa hankalinta ya tashi sosai tana ta tunanin ko lfy?

Gashi ta shirya su mufid zuwa sch.amma shiru har ynx Bai taba irin haka ba…..

Ganin 8 ta kusa tace Bari ta je ta tambaya ko lfy..

Hijab ta Sanya ta nufi bangaren rukayyah …

 

Sallama taitayi Amma shiru kamar ba kowa a ciki…sai da aka kusan 5mint sai gata nan ta fito sanye da wata gown sleeping dress ta barbaza gashni kanta ba ko kunya ta tunkarota a haka..dake Saida ta leka ta ga me sallamar sannan tayi wnn Shirin ..

Ko da Maryam ta ganta ranta ya baci sosai Amma bata Bari ta gane ba, ta gaishe ta amsa mata a yatsine har da cewa wai lfy da sasssfe haka ko tashi masu gidan basuyi ba…

Maryam tace dama naji shiru ne tunjiya banji shi ba na Kira ma ba’a daga ba shiyasa na zo inji ko lfy …

Wani kallon raini Tai Mata tace ai ba kullum ake kwana a gado ba haj.yau da gobe ya Fara gajiya da sintiri wajenki…shiyasa yai kwanciyarsa nima Kuma Naga hakan shiyafi cancanta …Amma lau yake ba wani Abin, sai a Kara gaba ….

 

 

Maryam juyawa tayi cike da takaici zuciyar ta tana Mata radadi….

Lekawa tayi taga makotansu da suke sch. Daya da su mufid tace don Allah su tafi tare daddynsu ne bashi da lfy

Suka shiga motar suka tafi…

Zama tayi akan kujera kalaman rukayyah na dawo mata akai…tana mamakin halin maza Bata taba tunanin haka daga gareshi idan har hakane tabbas yaci amanarta ya karya Alkawarin daya daukar Mata ,,,,,

 

Sai zuwa kusan 10na safe Abbas ya watsake ya farka da salatin ganin lokacin da ya Kai Yana bacci …Wanda Bai taba yin haka na tun kafin yai aure…mamakine ya cika Masa zuciya yadda akai haka t faru ….sai ga ruky ta shigo tana cewa wai me ya faru babynah tun jiya kake ta wnn baccin tun jiya?

Bai tsaya Bata amsa ba yai hanzarin shiga toilet

Itako rufe Baki tayi tana dariyar mugunta…

yayi wanka ya fito ya shirya a gaggauce tace ya kake Shirin fita baka Yi breakfast ba yace na makara me yasa baki tasheni ba kinsan Ina da abubuwa agabana ga Kai yara sch.

Tace nayi iyakar kokarina wlh Amma Ina tashinka sai ka koma bansan me ya sameka ba ..kasa ni cikin damuwa Nima.

Yace sai na dawo kawai ynx dai na makara zuwa tayi ta bashi hot kiss sannan tare da wata irin kissa da saida taso kashe Masa jiki…

Yace kyaleni in tafi sai na dawo ….tace take care baby ,,,,

 

Fita yai da sauri kamar zai tashi sama ya shiga wurin Maryam dake kwance kan 3seater tana ta tunane2 ko breakfast batayiba duk da motsin da cikin ke Mata kamar zai fasa ya fito .don yinwa, Amma hakan baisa ta tashi don cin wani abu ba.

 

Kamar daga sama taji muryarsa yana sallama tare da qamshin turarensa saurin rufe ido tayi don ya dauka bacci take yi .

Key din hannunsa yasa Yana Mata wasa a kunne
Tai saurin razana ta mike, tana ganinshi tai tsaki ta koma ta zauna yace morning wify!
Ta amsa a takaice

 

Yace kiyi hakuri wlh bansan me ya faru ba,tunda na dawo bacci ya daukeni sai kace Wanda yake maye ban farka ba sai kusan after 9

 

 

 

Dagowa tayi ta kalleshi ta ga kwayar idonshi ba karya a zancensa ta gasgata zancensa.

Amma Bata Yi saurin nuna Masa ta yadda ba, tace Allah ya kyauta

Yace Ameen!

Yace Ina su mufid din waya kaisu ?

T
ace tare da su khaleel neighbour dinmu suka tafi

Allah sarki yace!

Sai na dawo ma karasa maganar am late!
Tace Allah ya tsare hanya…
Yace Ameen ya fita

 

 

A mota kuwa yana tuki Yana ta tunani wnn lamari Anya ba wani Abin yasha ba da har yayi ta wnn baccin …Nan ya tuno lemun ya Sha Kuma tun bayan nan Bai sake sanin komai ba…ya tuno duk abubuwan da suka faru bayan dawowar shi daga office, da irin changes din da ya gani a tattarre da ita …

Yace ya Zama dole in Sanya ido akanta domin kuwa Yana zarginta akan faruwan hakan….

Ko da ya Isa office ya tarar da patience jindim suna jiran isowarsa, ya shiga da fara’arsa Yana Basu hakurin late din da yayi.

Cikin hanzari ya shiga ya Fara gudanar da aikinsa .

 

 

 

*Taku*

*Ummu Ameer* 💃

🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

 

*Story & written*

 

*By*

 

*Ummu Ameer* 💃

 

 

*Page* 3⃣5⃣

 

 

 

 

“””” Kasancewar girkinta ne ma yau din haka ta gudanar da komai kamar jiya ta tsaftace ko Ina da dai sauransu yau Kuma zobo tayi Masa bayan ta gama hadawa ta zuba kwayar a ciki Amma kadan …

 

 

Ta gama komai Tai wankanta yau ma wata Riga ta Sanya wadda da ita ma gara babu..sai wani wando iyakar sa gwiwa Bai ma Kai ba …ta yi parking gashin duk da ba wani yawa ne da shi ba sai ribbom da ta cika, haka ta zauna ta Sanya wani turare da farida ta Bata Wanda aka yi shi don mallaka.

 

Ta kosa ya dawo shiru har bayan magrib…ba Abbas ta Kira wayar a kashe hankalinta ya tashi ,tace ko dai yana wajen Maryam ?

Zuwa tayi ta leka ba motarsa a parking space ,ta zagaya ta yadda zata ji magana ta wajen Maryam ko Yana Nan taji ba muryarsa sai yara dake wasa.

 

Haka ta hakura taje tai sallar magrib ta sake gyara make-up din, Khadija kuwa tuni tayi bacci Bata wuce magrib take bacci.

 

Sai karfe 8na dare taji horn dinsa, ta leka ta window taga shine,Kuma ba inda ya zarce sai wajen Maryam Nan ta Kara Jin haushi da dai ta tuna hadin zobonta Kuma sai ta Tai murmushi tace Kai da Kara shiga sai gobe…

Cikin sauri ta zo ta jere Masa Abincin akan dining,yau kawai snacks Tai Masa ganin tana wahal da kanta Kuma ba ci yake ba..

 

Acan kuwa Abbas sai da ya kwashe 1hour sannan. Ya dawo ta Kai kololuwa wajen bacin rai Tai ta kwala Masa Kira “Abban Khadija” Abban Khadija ” Yana jinta yai shiru ….har Maryam na cewa ka tashi kaje Kar hakan ya jawo wata matsalar yace ba inda zani sai na gama Abinda nake …Aiko Bai je ba sai da ya gama wasa da yaransa har Saida sukai bacci ..sbd yai missing insu rabonsa da su tun jiya, itama sun Dan yi Hira sama-sama sbd har ynx Bata sakar Masa fuska ba…yana sane da ita ya kyaleta ne sai zuwa gobe tukun sai su fahimci juna ranar girkinta kenan…yai Mata sallama ya tafi cike da begenta sbd ba karamin kyau tayi Masa yau….haka nan ya tafi cike da shaukinta.

 

Itako rukayyah koda taga ya kusan awa daya acan ai tuni haukanta ya tashi ganin ta Kira Bai amsa ba balle ya dawo, tana ganin ya gama tozarta ta a wajen Maryam ….ai Nan da Nan ta zuciya ta shiga kitchen ta Fara wancakali da kayan dake kitchen din tana fasawa tana kuka kamar mahaukaciya tana ta sambatu “tana fadin ni zaka na wulakantawa don kaga Ina sonka, duk iya kokarin da nakeyi wajen ganin na kyautata na janyo hankalinka Amma a banza…na rabu da kowa sbd da Kai Amma kullum kokarin muzgina min kake …ke Kuma Zaki hadu Dani ki bar ganin Ina kyaleki kina min shisshigi ba wai tsoronki nake jiba ..wlh sai na dauki mataki akanki …haka dai taita sambatu Kuma Bata fasa zubar da kayanba hatta da falon ta hargitsa komai na falon, ga wani irin kuka da take kamar zata hadiyi zuciya ….tana tsaka da haukan taji knocking ta san Kuma shine Tai banza da shi taci gaba da farfasa abubiwan fashewa,

Yana tsaye yaji karar fashewar Abu..yace wnn yarinyar kuwa lfy take …cigaba da kwala Mata kira yayi Amma Bata da niyyar budewa …sai faman jijjiga kofa yake kamar zai balla, Amma ina Taki saurararsa.

Cikin matsananciyar fargaba ya Kira no daddy mahaifinta ya gaya Masa Abinda ke faruwa, daddy ya kirata yafi a kirga, sai daga baya ta dauka cikin kuka tace daddy na gaji da wnn auren kullum bacin rai ya dinga wulakantani a gurin matarsa, komai nayi ban iya ba sai ita…na…kafin ta karasa ya katseta Cikin bacin rai shut up!
Rufe min Baki mutuniyar banza da wofi kina so ki dauki dabi’ar mahaifiyarki ko? To zan zame hannuna a lamarinki matukar Baki canza ba…

Kuka ta Kara fashewa da shi ta aje wayar, tana ta maida numfashi sama sama …karar bugun kofar ne yasa ta tashi a fusace ta je ta bude kofar ta Galla Masa wata hararar da Bai San ta iya ta ba, ganinta da yayi sai da ya tsorata sbd ta wani hargitsa gashin kanta kamar mahaukaciya ga rigar hannu daya ya fita sbd bala’i komawa tayi ta zauna tana cigaba da kuka, yabita da kallon mamaki…

Mamakinsa Bai kare ba sai da ya ga haukan da tayi a falon binta yayi da kallon mamaki itako ko inda yake Bata kallah ba, ya leka ko Ina yaga irin abinda ta aikata…

Bai tanka Mata ba yazo ya Fara tattare na fashewar, ya gyara falon, kitchen dinma ya shiga ya kwashe abubuwan da ta fasa ya zubar ya gyara wadanda zai iya …Amma zuciyarsa a wuya take fa Ashe haukanta ya Kai ga haka dole ya dauki mataki Nan gaba baisan me zata aikata ba, shi yasa yai shiru Bai kula ta sbd in ya biye Mata a yanzu Abin bazai kyauba…

Itako ganin yaki kulata bakinciki ya rufeta takaicinsa ya Kara kamata, wato Bai ma damu da halin data shiga ba, maimakon yazo ya Fara lallshinta a’a shi ta gyara waje yake Nan ta Kara fashewa da kukan bakinciki…

Shi kuwa ko ta kanta baiyiba, daya gama gyara ko Ina yai wankansa yaje ya Dora ruwan tea ya Sha duk tana zaune. Bai kulata ba itako zuwa ynx takai kololuwa wajen bakinciki.

Tashi yayi ya shiga daki da zummar zai kwanta bayan ya kulle ko Ina.

Tana ganinsa ya shiga daki ya rufe kofa zai kwanta …tace bacci ma zaiyi ya barni cikin wnn halin ga asarar shirinta da tayi

Sai da ta Bari ya Dan jima da shiga taje ta bude kofar taji a rufe ta jijjiga da karfi kamar zata balla kofar….Yana jinta yai shiru gashi kansa na Masa wani ciwo kamar zai rabe2 .

Da dai ta ga bashi da niyyar budewa, kitchen ta shiga a guje ta dauko tabarya tazo ta Fara buga kofar kamar zata balla …tana fadin ka bude kofar ko na balla ta ka maidani sakarya bansan me nakeyi ba to ka bude muyita ta Kare eheee..

A lokacin karfe 2na dare …cikin matsananciyar bacin rai ya bude kofar Bai yi wata -wata ba ya kwasheta da Mari har sau 3 yace ke mahaukaciyar Ina ce Zaki dinga yimana hauka tsakar dare?

Itako tunda Taji saukar zafafan mari a kuncinta ta zube kasa a waje ba numfashi…..

 

Cike da tsoro ya kalleta yaga abinda tayi …cikin sauri ya daga hannunta yaji ba motsi ya jijjigata da karfi Yana Kiran sunanta kamat zautacce Amma shiru…

 

 

*Ummu Ameer ce💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

 

*Story& written*

 

*By*

 

*Ummu Ameer* 💃

 

 

 

*Page* 3⃣6⃣

 

 

***** Jin Kiran rukayyan da yake cikin tashin hankali ne ya farkar da Maryam daga daddadan baccin da takeyi, itama a tsorace ta tashi cike da fargaban me yake faruwa cikin wnn Daren haka….

Tashi tayi ta je daidai saitin da take Jin Kiran da yake tace Abban mufid lfy …yace ki zagayo ki shigo ba lfy Maryam

Rukayyah ce!

Ya Fadi cikin mawiyacin Hali ….

Tace me ya faru ne ka Gaya min Mana yace ki shigo kawai xuwa yayi ya bude kofa Maryam ta shiga gidan tana shiga taga rukayyah a kwance kamar matacciya a kasa ..

Innalillahi!

Tace me ya sameta Abban mufid haka ..cike da tsoro yace ba wnn ba Maryam ki diba kiga kamar Bata numfashi….

Tsugunawa tayi akanta ta Sanya yatsa a bakin hancin don Jin ko tana numfashi ..tana sawa taji tana numfashi, tace kawo ruwa da sauri tana numfashi cikin sauri ya je ya debo ruwa a cup har Yana Shirin faduwa ya yayyafa mata Nan take ta sauke wata irin ajiyar zuciya…Amma Bata bude ido ba,,,,,

Shi ko ba abinda yake sai hamdala da Bai Zama sanadiyyar rayuwarta ba…don gabadaya ya gama tsorata ya dauka mutuwa tayi shi yasa ya kasa komai ya Kira Maryam tazo …duk ya wani fita hayyacinsa lokaci daya, tare da nadamar Sanya hannu akanta da yayi dama ba halinsa bane Bai taba dukan matarsa bare wasu ita ma din ta kaishi makura ne duk yadda yaso ya kaucewa hakan sai da ta janyo ya bugeta…yana Kara godewa ubangiji da Allah yasa Abin ya tsaya anan, har ya Fara hango kanshi da laifin Wanda yayi kisan Kai …

Maryam na tsugunne kusa da ita, ruky ta bude idanuwanta ta sauke su kan Maryam ta waiga ta hango Abbas a can gefe Yana maida numfarfashi…🤣 Namiji da tsoro …

Mikewa tayi tsaye ta kalli Maryam sama da kasa kallon raini ta Kai ganinta ga Abbas, ta watsa musu wani mugun kallon Wanda sai da Maryam din ta tsorata, tayi shigewatta daki…

Maryam na ganin haka tace Abban mufid bari na tafi tunda ta farka …kasa magana yayi kawai gyada Mata Kai yayi ta fita cike da mamakin Abinda ya hadasu haka….tace maganinsu kenan suna zaune lfy su janyo ma kansu bala’i .

 

Maryam na fita ya shiga dakin wajen ruky da ya sameta a zaune a kasan carpet din dakin tana kuka ….karasowa yayi kusa da ita yace kiyi hakuri ba son Raina na dakeki ba, na kasa controlling kaina ne a lokacin sbd bacin rai …itako abin nema ya samu har da wani kara sakin kuka Mai ban tausayi…

Sai da ya tabbatar da ta hakura sannan ya tashi ya shiga toilet don dauro Alwala kasancewar har an Fara Kiran sallar asuba …

Tana ganin ya shiga toilet ta tashi ta fashe da dariya tana fadin Ashe zan iya wasan kwaikwayo..

Ashe dama Yana kaunata Bai nuna min ne kawai, ji yadda ya wani rikice sanda na fadi…sai yanzu nasan irin kaunarka garani,,,,,

Nan kuwa Bata San tashin hankaline ba ya dauka kisa yayi shiyasa ya gigice Yana kiranta a haukace….

Tana Jin motsin fitowarsa ta ci gaba da kukan karya …shiko harda Kara wani lallashinta Yana Bata hakuri yace taje tayi Alwala. Ta tashi da kyar irin wadda Tasha wuya dinnnan.

 

Shikuwa tashin hankalin da ya faru ne ya manta duk hukuncin da yaso yi akanta don bazai jure wnn haukan nata ba Bai San Abinda zatayi gaba ba Kuma.

Wnn abinda ya faru ne kawai ya janyo rugujewar shirinsa akanta …

Amma zai Kara Bata damar ko zata canja…Kuma Yana ganin girman mahaifinta sbd Yana iya kokarinsa akanta wajen Bata shawara ta zauna lfy a gidanta …gashi duk sanda ya Kai kararta wajensa ita yake bawa laifi baya goyon bayanta ko kadan.

 

 

Bayan ya fito tai sallah komawa baccin da Bata Sami yi ba tayi.

 

Bayan yayi wanka ya shirya ya tafi Kai su mufid sch.

Amma kana ganinshi kasan Yana cikin damuwa..Yana Mai ganinshi laifinshi wajen kawo wadda take Shirin tarwatsa mishi rayuwa sai ynx ne ma yake nadamar dawo da ita da yayi dama kawai ya musu abinda suke so ita da mahaifiyarta.a wancan lkcin

 

Rukayya kuwa cikin doki da karfin gwiwa ta tashi tana hada break fast, tana tuno yadda plan dinta yai tasiri a wajen Abbas …na sanin irin matsayin da take da shi…a wajensa ynx

Bayan ya dawo ta gama shirya breaakfast dinta suka je suna ci, Amma tana sane da yadda taga ynx ba walwala a fuskarsa…

Tace lfy kuwa naji ka shiru…Ina ta magana ba amsa?

Yace ba komai Amma fuskar har ynx ba walwala

Tace Ina so ka gafarta min Abinda ya faru jiya wlh Nima bacin Raine Kuma na kasa controlling dinsa Amma kayi hakuri ka yafe min insha Allahu bazan sake Yi makamancin haka ba…har da tsugunnawa a kasan kafarsa tana bashi hakuri. Ganin ta dameshi yasa yace “ya wuce!

Ta tashi tana Masa godiya!

Tea kawai ya iya Sha, ya tashi zai wuce aiki, yai Mata sallama ya tafi wajen Maryam itama sukai sallama…

 

Muje xuwa

*Ummu Ameer ce* 💃

🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story& written*

 

*By*

*Ummu Ameer* 💃

 

 

*Page* 3⃣7⃣

 

 

“”””Har yanzu rukayyah Bata San cewa Maryam na da ciki ba,,, sbd Bata da girman ciki, Amma dai duk da haka ya fito…Kuma Shima Bai fada Mata ba.

 

Rukayya kuwa ba farincikinta Bai misaltuwa taji dadin yadda Abbas ya nuna damuwarsa akan halin da ta shiga a gaban maryam,tasan yanxu itama zata gane irin son da yake Mata..don duk tana Jin abinda yake faruwa duk Abinda yayi tana jinsa, sannan ta fahimci mugun matsoraci ne🤣zata Yi amfani da wnn damar….

Har farida ta fadawa abinda ya faru …tace Ashe kema shegiyar kanki ce, ai gara da kika tashi tsaye in kika tsaya Sanya zakiga Sanya hajiya…sukai sallama cike da farinciki a ranta.

 

Abbas kuwa ko da yaje office kusan kasa komai yayi Yana ta tunanin abinda ya faru har ynx ya kasa cire Abin a ransa shi yasa ya wuni ba walwala a tare da shi.

Yana zaune a office friend dinshi ya shigo Dr Yusuf ya shigo daukan ruwa a fridge kasancewar fridge dinshi ya lalace,yai ta sallama shiru Abbas yayi nisa a tunani …sai da ya Dan yarfa Masa ruwa a fuska yayi firgigit …yace Dr. Me kake tunani ne Abokina haka Ina ta magana ka yi nisa a tunani ….ko Mata 2 sun Fara caja maka Kai ne?

Ajiyar zuciya ya sauke yace Kai dai bari Yusuf jiya Naga hauka a gidana …Yusuf yace wane irin hauka Kuma ?

Abbas kwashe duk Abinda ya faru yayi ya fadawa yusuf, har da sauran matsalolin da suka faru kafin wnn.

Yusuf yace ai dama na Gaya maka zaka Yi kuka da wadannan mutanen sbd Basu da kyau akan kishi …ko da yake kaddara ce da Kuma rabo, ni Daman ban goyi bayanka ba akan auren Nan tunda muka je da Kai Naga yadda mum din ta take behaving na San akwai mataala, a lokacin don ka yi nisa ne shiyasa na kyaleka …kana zaune da matarka Mai hankali da hakuri yar gidan manya ka debowa kanka ruwa….

Abbas yace duk wnn ya wuce tunda aikin gama ya gama ni kaina sai ynx nake nadamar Kara auren da nayi gashi nai rashin sa’a, wlh ni auren ya fita a Raina …

 

Yusuf yace ai dole kaganni Nan kwata-kwata bani da ra’ayin mace 2 Kuma kada kayi tunanin wai bani da matsala da matata, da Mai ra’ayin ne da tuni na yiwa safiyya kishiya Amma duk da wnn bantaba sha’awar Kara wata ba, duk da su Haj. Sun so na Mata ko ta shiga hankalinta akan rashin mutuncin da takeyi..Amma fir naki sbd nasan wata matsalar xan karawa kaina in suka zamo su 2 maimakon a samu sauki.

 

Kaidai kawai ka ci gaba da hakuri, Kuma ka dage da addu’a Allah ya hada kansu ita Kuma ya yaye Mata zafin kishi…in Banda ma Abin rukayya, ai Maryam ce ya kamata tayi wnn kishin ba itaba.Allah dai ya kyauta Ameen!
Abbas yace tare da mikewa Yana saka laptop inshi a jaka da sauran tarkardunsa, tare suka fito daga Asibitin Daman Shima Yusuf din ya tashi tun dazu,sukai sallama kowa ya nufi motarsa suka tafi.

 

 

Bayan ya koma gida yaje wajen ruky kamar yadda ya Saba, Fara zuwa wajen wadda Bata da girki ya shiga fuska ba yabo ba fallasa itako sai wani rawar Kai takeyi..bayan wasu mintuna kadan ya wuce wajen Maryam ya sameta a kwance cikin wani mawuyacin Hali…da gudu ya karasa inda take Yana tambayar lfy kike kuwa…Amma Ina ba Baki sai karkarwar zazzabi take har hakoranta na karo da juna,yace Amma me yasa baki gayamin halin da kike ciki ba Maryam?
Kinsan illar zaxxabi ga Mai juna 2 kuwa? Shine kika zauna da shi har haka Yana maganar kamar zaiyi kuka miryarshi na rawa…sbd yasan hatsarin zazzabi ga masu ciki, cikin tashin hankali yace wa kanwarta da tazo gidan tai maza ta dauko Mata hijab su kaita hospital.

Da taimakon hafsa kanwarta suka taimaka Mata ta shiga motar don kuwa tana Jin jiki ga wani zazzafan zaxxabi kamar turirin garwashi ga ciwon Kai kamar kan zai cire don Bata taba ma irin wnn zaxxabin ba.

 

A guje ya figi motar da wani irin gudu kamar zai tashi sama, Kuma motsi kadan zai ce sannu, itako ba Baki don Bata ma San Wanda ke kanta ba…

 

Bai tsaya ko Ina ba sai Asibitin da take Awo da sauri yai Kiran nurses suka taho da wheel chair aka dorata akai tare da hanzarin shiga da ita dakin ganin likita aka dorata akan gadon dake cikin dakin Shi kuwa Abbas Yana rike da hannayenta har da kwallah…sbd tausaya matan da yayi Kuma ga fargabar kar yai affecting din babyn cikin.

Dr. Ya Masa tambayoyi game da cikin ko dama ta Dade tana yin zaxxabin? Yace wlh Bata taba yi ba sai yau, Nima Ina dawowa na ganta a cikin wnn halin, Kuma ga dukkan alamu Bata dade da farawa ba,

Nan da Nan aka Sanya Mata drip sannan aka Debi jininta don gwajin malaria n typoid, shi kuwa Yana rike da hannunta Yana Mata sannu duk da ba iya amsawa take ba.

Rukayya kuwa ta kira ya Kai sau 20 Amma ya kasa picking…

Itako tana gani sanda suka fita daga gidan rike da Maryam din, yanayin da ta ganshi a ciki ya tabbatar Mata da cewa Maryam dince ba lfy..Kuma shine ko ya Gaya min zai fita ga wani irin tashin hankalin da ya shiga sai kace ce Masa akai ta mutu tsaki tayi tace aikin wofi kawai..ga takaicin kin daga wayar ta da baiyiba.

Tace to ma wai me take damunta?Kar dai ace ciki ne da ita? Inko hakane Akwai matsala…tashi tayi tsaye tana ta zagaya dakin tana safa da marwa….

 

 

Muje zuwa

 

*Taku*

*Ummu Amear* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story & written*

 

*By*

 

*Ummu Ameer*💃

 

 

*Page* 3⃣8⃣

 

 

Sai bayan awa 2 sannan Maryam ta dawo hayyacinta, Abbas kuwa cike da farinciki yace sannu maryam, ya jikin?
Tace da sauki!
Ya taba kanta yaji ba zazzabin ma, hamdala yayi tare da godewa ubangiji.

Motsawa tayi alamun tana son tashi zaune taimaka Mata yayi,sannan ya cire Mata robar ruwan da aka Sanya Mata sbd ya kare.

Sai faman Nan -nan yake da ita motsi kadan yace sannu ba dai wani Abu ko?
Tace eh!

Shima Dr. Da ya shigo ya yi murna da ganinta kamar ba ita ba, yayi wa Abbas murna.
Yai Mata tambayoyi ko akwai sauran abinda ke damunta? Tace babu.
Sannan ya nuna Masa result din, malaria ce Tai Mata mugun kamu.

Yace ikon Allah Kuma Bata fashin kwana cikin net.
Dr. Yace hakane Daman sai dai aci gaba da kula sosai kasancewar cikin dake jikinta anyi sa’a ma Bai shafi babyn ba,
Abbas yace Alhamdulillah
Thank you Dr umar!
Insha we shall do as u said!

Dr ya rubuta Mata magunguna masu kyau na malaria, sukai sallama yai musu fatan Allah ya kiyaye gaba, shi Kuma Abbas ya rungumo matarsa ta kishingida jikinta a jikinsa suka tafi, Dr. Kuwa sai murmushi yake sbd a gaskiya sun burgeshi Kuma ya Mata murna samun miji kamar Abbsa ‘caring husband’ gashi sun matukar dacewa da juna..

 

 

Haka suka fita kowa na binsu da kallo, har zuwa inda yai parking ya zaunar da ita sannan ya zagaya ya shiga suka tafi…

A hanya ya tsaya ya saya Mata fresh milk, da shawarma, da carton din maltina.

Sai sannu yake Mata duk hankalinshi na kanta har suka iso gida …

Lokacin karfe 1na dare, ruky kuwa kamar jira aka Bata ta kasa zaune ta kasa tsaye ta Hana kanta bacci, sai taga dawowarsu, kafin isowarsu sai da ta shiga toilet sau uku sbd fargabar ko cikin ne…

Tana Jin karar shigowarsu kuwa ji tayi kamar ta je ta tambayesu me ya sameta sbd gajen hakuri.
Lekawa take ko zata iya gane wani alamu na masu ciki, Amma Ina Bata fahimci komai ba.

Haka ta hakura ta zauna tana jiran shigowarsa ta tambayeshi..

 

Shi kuwa Abbas jinya ta sameshi shi ya hada Mata ruwan wanka ya taimaka mata ta shiga wankan, haka dai yai ta Bata kulawa ta musamman, yara kuwa tuni sun Yi bacci suna ta tambayar hafsa Ina mommynsu tace sunje anguwa zasu dawo ynx.. a haka dai sukai bacci cike da kewar mahaifiyarsu.

Abbas kuwa har zai kwanciyarsa, sai ya tuna da Kiran wayar ruky, ya shiga ya sameta a zaune ba alamun bacci,yace lfy baki bacci ba har ynx?

To wane bacci zanyi baby? Naga ka fita a tashin hankali wai meya faru ne ka fita bako sallama yace Maryam ce ba lfy wlh?

Har da Dan zaro ido cike da kissa tace Allah sarki me ya sameta haka?
Yace malaria ce ta kamata sosai!

Bata San lokacin da ta sauke ajiyar zuciyaba tare da hamdala!
Yace lfy!

Tace har naji dadi ba wani mugun ciwo bane da ya tsaya kan malaria Allah ya sawwake
Yace Ameen !

Ni zan koma sai da safe
Kuma gobe ki shiga ki duba jikinta.

Ta yatsina fuska batare da ya ganta ba, a fili kuwa sai tace Allah ya kaimu…

 

***** ******* ******

Washe gari Abbas Bai fita office da wuri ba, ya tsaya Yana kula da Maryam sbd Bata son shan magani sai ya takura Mata tukun take Sha.

 

Karfe 11 na safe kuwa sai ga ruky ta shigo bangaren Maryam fuska ba yabo ba fallasa Bata Sami kowa a falon ba, taita sallama sai ga hafsa ta fito ta gaisheta ta wani amsa ya wulakance tace Ina matar gidan?
Hafsa tace tana daki Bari na kirata!

Hafsa taje tayi knocking kofar Abbas ya leko tace Anty rukayyah ce tazo yace kice tana zuwa.

Ta dawo ta Gaya Mata tana zuwa ki zauna ..

Sai alokacin ta zauna a kujera sai bin falon take da kallo, dake zuba daddadan qamshi, a zuciyarta tace ko Ina take samun wadannan turaruka masu qamsh oho!

Jin karar kofa ne yasa ta maida hankalinta ga wurin, wani irin razana tayi da Abinda idonta ke gane Mata Maryam ce ta fito sanye da doguwar Riga irin me roba din nan ga ciki a gaba, Wanda akalla zaiyi 7month, Nan take ta rikirkice hankalinta yaso gushewa, har sai day Maryam tace lfy kuwa ?

Sannan ta wayance tace oh! na Dan tafi tunani ne, suka gaisa da Maryam Tai Mata ya jiki, Amma har alokacin ba’a hayyacinta take ba, sai Kara bin cikin take da kallo, a zuciyarta tace lallai ma Abbas ya cika minafiki.

Ko 5mint batayi ba tace zan tafi sukai sallama Maryam ta rakata har bakin kofa,sannan ta koma daki wajen Abbas dake Shirin fita office..

Yace har ta tafi tace eh!
Yace to wify! Ni zan tafi don Allah Kisha magingunan akan lakaci plx! zan dinga kiranki in tym din yayi.
Tace zan Sha wlh.
Kissing din cikin yayi tare da shafa shi yace my baby zan tafi aiki take care !

Dariya tayi tace waya fada maka yanaji?
Yace ai kece Baki sani ba ,Yana jina amsawa ne dai sai ya fito ko my baby ?

Dariya sukai gabadaya ta karbi jakar hannunsa ta rataya ta suka fito falon kana ganinsu kaga masoyan Asali..har bakin kofa ta rakashi yace ya Isa haka Kar a wahal min da baby tace au ni Kuma fah?babyn ka kasani..yace wane ni?
Har da ke ya fada tare da lakuce mata hanci.

Tace husby na Ina godiya da irin kulawarka gareni ba abinda zance sai dai Allah ya saka da Alkhairi ya kare min Kai a duk inda kake ya Kuma barmu tare har Abada!
Yace Ameen uwar ya’yana Kuma Abin Alfaharina.

Ngd sosai da wnn addu’ar.

Sukai sallama cike da kaunar juna .

 

Me zai faru?Ashe ruky idonta da kunnenta akansu, wata Yar bula ta samu take lekawa duk sanda Taji su anan din…

Haukacewa ne kawai batayi ba jikinta sai karkarwa yake sbd tsabar kishi, tsigar jikinta na tashi…idonta ya daina gani ta fita hayyacinta
*Oh su ruky da lekan asiri an lekowa wa Kai da jiyo wa Kai tashin hankali*🤔

 

Abbas sai sallam yake Amma Bata ji ba, Bata a hayyacinta kwata kwata ga tashin hankalin cikin da ta gani Abu goma da ashirin…

 

 

Muje zuwa

 

*Taku*

*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story &written*

*By*

 

*Ummu Ameer* 💃

 

 

*Page* 3⃣9⃣

 

 

 

“”””Sallama yake tayi Amma Bata San ana Yi ba, shi kanshi ta bashi tsoro, ganin lokacin da ya dauka Yana ta sallama Amma Bata ji ba, sai da yazo Yana facing dinta yace “rukayyah”me hakane?sannan tai firgigit, yace meya sameki tun dazu Ina ta sallama bakijini ba?
Tunanin me kike haka?

Kallon shi tayi cike da raini ta buga tsaki Tai shigewatta daki ta barshi Nan tsaye da mamakinta,Yana cewa wanna matar ba’a kwana 2 cikin zaman lfy da ita sai ta bijiro da wani Abin kuma?

Bai bita ba, yasa Kai yai
Ficewarsa da takaicinta…

Tana Jin ya fita wani bakincikin ya sake rufe ta, ta fashe da kuka tare da lalubo wayarta ta Kira daddy tana Gaya Masa wai wulakancin daya ke Mata yai yawa ynx in Bata da girki ko zuwa baya yi wajenta sai ya ga dama sharri iri-iri Tai ta Yi Masa…

Tsakanin uba da ‘da’ sai Allah sai tausayin diyarsa ya kamashi a karo na farko yace tayi hakuri zai Masa magana…sukai sallama .

 

Tana gama kiransa ta Kira farida itama ta Gaya Mata cikin da Maryam ke dashi…dariya farida tayi tace shugabar masu kishi ke Kuma Ina ruwanki da cikinta ba matarsa bace, taitayi Mana ai Nan da Nan zakiga ta tsofe, sai kace akuya..ke in Banda shashanci ma ai dadi Zaki ji…. rukayyah ta katseta da cewa wani irin dadi Kuma ta Riga ta gama zazzago Masa yara ya Riga ta mallakeshi Baki ga yadda yake nuna ma yaran kauna ba, kamar akansu aka fara haihuwa, ko Khadija bata samu wani soyayyarba daga gareshi, hakuri kawai nake Ina kyaleshi sbd ba yadda zaiyi jininsa ce ko Yana so ko baya so….Kuma Baki ga wani irin kulawa da yake Mata ba, kamar me haihuwar fari ko ni bansami wnn gatancin ba, sannan Kuma in zauna Ina kallo ba wani mataki da zan dauka…farida tace wane mataki Zaki dauka ai aikin gama ya gama tunda kince ma ya Kai 7month ko?
Tace zai Kai..
Kuma ga munafurci ko da wasa Bai taba Gaya min ba.

Farida tace Kinga ki bar wnn zancen ni Banga wani abin tada hankali ba anan ai kin Mata zarra ta Nan tunda ke haihuwarki 1 Kuma ba dainawa Zaki ba ynx kika Fara Kila ma ki dinga haifo 2 tinda so kike ki Tara Masa yara…ta karashe maganar da tsokana.tace karki wani dami kanki don wnn ,ke dai kawai ki cigaba da samawa diyarki matsayi na musamman a zuciyarsa.
Haka dai suka dauki lokaci suna waya daga karshe sukai sallama.

Amma ko kadanba haka taso ba, taso ta goya Mata baya su San abinyi akan cikin, sai aka samu akasin haka sbd ita farida Bata dauki haihuwa wani ba, ita a ganinta ai haihuwa ma tsofar da mace takeyi shiyasa dama ita a tsarinta ko da Allah yasa ta haihu to bazata wuce 2 ba, sbd ta morewa rayuwarta ….a nata tunanin.

 

Itako rukayyah Bata dauki shawarar farida ba, sbd idan ta barta tana ta zuba Ya’ya ai ta Riga da ta kwace mijin, shi yasa take ta tunanin wata hanyar Kuma.

 

Daddy kuwa Kiran Abbas yayi yace rukayyah ta Gaya min Abinda ke faruwa don Allah dai kaci gaba da hakuri Kuma kayi kokarin kana kamanta Adalchi tsakaninsu don samun zaman lfy a gidanka…
Yace insha Allah!
Sukai sallama
Yace me Kuma ta hada min wnn munafukar yarinyar, har zai kirata ya fasa sai ya koma gida ya sameta..

 

Sai da yayi kwana 2 a gidan Maryam cikin kwanciyar hankali da kaunar juna, Bai so ba ma zai bar gidan sbd ynx jinta yake kamar me… A bed.

 

Rukayya kuwa tun rannan ba magana suke ba, ita a dole tana Jin haushi yama Maryam cikiiii….karfin hali kenan

Randa zai dawo gidan kuwa Bata wani wahal da kanta ba, wajen gyara shi ba, tunda tace ko tayi ba tasiri yake ba*A tunaninta da gajen hakurinta ya Hana ta cin ribar zaman aurenta*

Amma dai yau ma ta Kara hada Masa zobo ta Sanya Masa kwayarnan Bata mance da ita ba, ita dai tana Jin haushin shigar da yake wajenta ranar girkinta…

 

Ko da ya dawo ba wani fuska ya sakar Mata ba, ya shiga toilet yai wankansa, ya gabatar da sallar isha’i, Bai ko kalli wajen dining din ba, balle yai tunanin ci, ita Kuma girman Kai ya Hana ta kiransa a tunaninta ai shi ya kamata ya bita tunda shi yai Mata laifi…hauka kenan.

Ya wani dauki fushi da ita, bayan ita yaiwa lefi shine yake wani wayancewa da borin kunya Kar tai Masa zancen, da ta kalleshi in ta tuno cikin Maryam sai ta Kara Jin haushinsa …

Ganin Yana Shirin fita wajen Maryam tace mallam ya haka bakaci Abinci ba, kake Shirin fita wani wajen Kuma,ta Sha gabansa ta tare hanyar.

 

Yace sai kin je kin koyi yadda ake Zama da miji da iya yi Masa magana tukun sai in ci …Aiko maganar ta Dakar Mata zuciya, tace ni Kake fadawa haka Abbas?
Yace an Gaya Miki kiyi duk Abinda zakiyi na gaji da wnn halin naki I’m tired.

A take tsoro ya kamata a zuciya tace karfa ya sakeni, don wlh bazan iya jure rashinsa ba, bazan iya rayuwa da wani in ba shi ba, gashi taga ya harzuka matuka shiyasa ta ja bakinta tayi shiru …tana ji tana gani ya fita, Yana fita ta dauki zobon ta zubar a kitchen tace bashi da sauran wani amfani a gareni,in ma yasha ni zai cutar…

Ko da ya shigo ma kasa tunkararsa tayi da wani zancen ya gama duk Abinda zaiyi ya shiga bed room zai kwanta, ranta ya baci sosai da Abinda yayi, bayan ta gama kukanta taga bashi zai fissheta ba,tashi tayi tabi bayansa…ta tura kofar a hankali ta shiga ciki…

Zuwa tayi ta zauna kusa da shi tace ka tashi zamuyi magana da Kai…Yana jinta yai Mata shiru,sai da yaga tana Shirin Hana shi bacci yace Ina jinki, tace ka tashi ka fiskanceni mana,yace kunnene ke ji ai…ta fara magana tana fadin wai don Allah me nayi make kake min irin wnn horon a gidanka?, Ina soyyayar da kake min? Ina Alkawarin da ka daukar min kafin dawowata gidanka,ynx ni na cancanci duk wadannana abubuwan daga gareka?
Rukayyan kace fa Abbas..

Na fahimci kwata kwata baka kaunata, kaunarka tana ga matarka Maryam komai nayi ban iya ba, baka nuna son kamar yadda kake nuna mata, Khadija ma Bata samu soyayyar dakake nuna wa yaranta ba, karka manta yarkace itama, Kuma jininka..

Na fahimci matarka ce take yin asirin da muke samun matsala itace duk ummul aba’insin komai,

Yace dakata karki Kara ambatota da irin wnn kazafin, duk Abinda zamuyi ya tsaya tsakaninmu, ba ruwanki da ita, bana son korafi, tinda nake da ita Bata taba kawo min wani korafinki ba, nasan abinda zatayi,nasan Wanda bazata yi ba.

Nan da Nan wani bakinciki ya turniketa kamar ta hadiyi zuciya.

Sannan ya Kara da cewa batun changes Kuma da kika gani wanna Kuma ke Zaki binciki kanki, ki nutsu ki daina duk wasu halaye da kika son bana so, ki guji abinda bana so, ki fi kowa son Wanda nake so… ki dawo rukayyan da nasani a baya …ki cire wnn mugun kishin da kika saka wa kanki, don bashi ne mafita a gareki ba…..

In kin canza, Zaki ga canji….

Nan take ta fashe da wani irin kuka…tana cewa ita dama ko yaushe Mai laifi ce a gareshi, baya Mata Adalchi ..ganin Bata da niyyar shiru yasa ya janyota ta kwanta ko tasamu ta barshi yai baccin, itako ganin haka yasa tai luf ajikinsa, Abin nema ya samu…

 

 

Muje zuwa

 

*Ummu Ameer ce*💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story & written*

 

*By*

 

*Ummu Ameer* 💃

 

 

*Page* 4⃣0⃣

 

 

 

Hakanan rukayyah ta hakura ta saduda ta kwantar da hankali, Amma har ynx bata taba yi Masa zancen ko Maryam na da ciki ba, hasalima Bata son tuna hakan sbd tana dadewa cikin bakincikin hakan…sai dai itama ta dauki aniyar daukan cikin , dama tana allura Amma shi kanshi Bai sani ba, a boye takeyi, sbd ta nuna tana son Yi yace a’a Yana da illah, Amma Taki Jin maganarsa sbd a lokacin tana cin karenta babu babbaka, a lokacin Bata da niyyar sake haihuwa kusa sai ta huta, ta mori rayuwa, Amma tunda ta kyallara idanuwa akan cikin maryam, ta sake tunani..

Shiyasa ynx tace bazata Kara zuwa ayimata ba…

 

Maryam kuwa ciki ya Kara girma sosai don a yadda take cikinta baya wani girma sosai, Amma wnn tunda ya Kai 7month sai kace kafin gobe ta haihu, yayi girma ba kadan ba, gashi yayi Mata nauyin da Bata taba Jin irinsa ba, wani zubin har kirjinta take Jin cikin, gashi ko tafiya da kyar take yi don nauyin cikin gashi Sam Bata iya rike fitsari don in Bata hanzarta ba ma kafin ta Kai toilet ya zubo mata.

 

Har scanning suka Kara yi don tabbatar da lfyr cikin aka tabbatar da lfy shi normal, har sex din ya fada musu cewa baby girl ce…..hakane yasa tun daga hospital din suka biya sayen kayan baby girl, komai pink suka siya takalma ne, bandana har da gown masu kyau da tsada, haka suka dawo da Kaya niki -niki, ko da suka dawo rukayyah na leken su ta window ana ta shigar da Kaya, anan ta tabbatar da lalai ta kusa haihuwa …ga bakin cikin kayan da aka dinga shiga dasu …tace ko Khadija Bata samu haka…duk da itace dama tace a basu da kansu zasu siya,suka je sukai son ransu suka saya masu arha, shi kuwa baya sayan Abu Mai arha sai ya duba tsadaddu masu kyau sannan ya dauka, shiyasa in yaran suka Sanya Kaya kowa sai ya dinga Santinsu wai Ina suke samun kaya haka masu kyau…

 

Sai da taga wucewarsu har da Maryam taga katon cikin take gabanta gashi tayi wani haske kamar baturiya..Bata karasa kallonta ba don bakinciki ta koma ta zauna…

 

*******. ******. ******

Yanxu Kam ruky ta shiga hankalinta sbd ynx Abbas baya raga Mata ko kadan, sbd yaga haukanta bana karewa bane, ta dauka tsoronta yake ji..ynx Kam baya daukan shashanci…shi yasa ta nutsu ta rage haukan nata, ta nuna Masa cewa shine gatanta shine rayuwarta bazata taba rayuwa bashi ba, ta Saba da kulawarsa…

 

Maryam kuwa wani irin ciwon kafa take fama dashi in ya Fara yi kamar ranta zai fita don azaba, ko da suka je hospital aka ce nauyin babyn ne ya danne Mata cikin, sai dai tayi hakuri har Allah yasa ta haihu lfy…Amma tana Shan wahala sosai …

 

Ranar wata laraba ciwon kafar ya takura Mata kamar me, gashi Yana gidan ruky…maryam kuwa ta kasa jure azabar ciwon sai wani irin nishi take kamar me nakuda duk ta fita hayyacinta don ana Jin saitin shi har waje …kamar a mafarki Abbas yaji sautin ya farka a firgice ya kasa kunnenshi Yana jiyowa kasancewar a falo take ta kasa kwanciyar a daki, itama hafsa Jin motsi. Maryam din ne ya fito da ita,dake tana gidan tinda cikin ya tsufa dama ba iya wasu aikin take yi ba…tana kusa da Maryam din tana Mata sannu, sai ganin Abbas sukai ya shigo a firgice yace lfy hafsa me ya sameta tace wlh kafar ce ta matsa Mata da ciwo tun dazu ganin halin da Maryam ke ciki yace bari in fita da mota kawai muje Asibiti, cikin sauri ya fito da motar, ya dawo suka kaita mota tare da hafsa…Jin karar motar Abbas ne ya farkar da ruky, ta duba taga bashi a gadon Aiko ta mulmulo wani katon ashariya tace ni za’a ci wa Amana haka ta fito harabar wajen daga ita sai Riga da wandon bacci, wando iya gwiwa sai karamar rigar baccin kanta ba dankwali, kafin ta fito ya figi motar da gudu…

Nan ta tsaya tana takaici, tare da cixon yatsa….dubanta takai ga kofar shiga gidan Maryam ta ga hafsa tsaye a bakin kofar cikin matsananciyar damuwa…karasawa tayi wajenta kamarabin arziki tace ke Ina yayarki sai da hafsa ta dau mintina kafin ta amsa Mata tace sun je asibiti, maimakon ta jajanta sai cewa tayi Ashe za’a ga tashin hankali a gidan nan, ta nan Kuma ta bullo da makircin nata tsakar dare zata dauke min miji tsabar makirci to wlh sai na nuna mata ko ni wacece munafukar banxa masu bin bokaye…

Hafsa sbd takaicin shirmenta komawa ciki tayi ta maida kofa ta rufe cike da tausaya yar’uwarta wnn mahaukaciyar kishiyartata ….

 

 

Haka ta karaci shirmenta ta koma ciki taga ba maijinta, ta zauna zaman jiran dawowarsu…taso ta kirashi a waya sai Kuma ta ga wayar tasa a gida ya manta …

duk a karfe 3na dare….

Koda isarsu hospital Dr. Ya tambaya watannin cikin suka Gaya Masa 8m da kwananki, yace a shiga da ita metron zasu duba ta, ko haihuwa don wani lokacin ta kanzo a haka da ciwon kafa, yace haka ma wata patient tayi Kuma ana dubawa akaga haihuwace.

Bayan an duba aka tabbatar da cewa ba haihuwa bace, Dr. Yace sai dai ya basu magingunan da zasu taimaka Mata wajen rage Mata radadin ciwon, haka akayi har allura akai mata, suka taho Kuma cikin ikon Allah ta samu relief, don ynx ma da kanta take takawa, daxu kuwa ko tafiyar Bata iyayi sai daya riketa tana dingishi…

 

 

Suna Isa gida yace ta danci wani abu tasha maganin, ya Bata tea Tasha kadan ya Bata magunguna, yace ta shiga wanka ko taji dadin jikin nata…daga Nan ya wuce wajen rukayyah lokacin assalatu tayi…

Yana shiga yaci karo da mutuniyar a zaune ta cika fam kamar ta fashe don haushi don idonta kaf akan dawowarsu….

Yana shigowa ta tashi ta Sha gabansa tana yau dubunku ta cika munafukai Azzalumai kawai maciya amana….a fusace ya daga hannu zai zabga Mata mari sai Kuma ya tuna baya ….ya fasa Amma ya dinkule hannu Yana huci kamar Zaki….ita Kuma ganin hakan sai ta samu karfin gwiwar ci gaba da rashin kunyar tana fadin dake ni tana tura Masa jikinta ka dakeni nace in ka Isa Dan halak ne kai, shi kuwa ranshi ya gama baci karshe da munanan kalamanta, ta cigaba wlh yau da ka Kara tabani sai na kullah maka sharrin da bazaka iya fita ba, wlh sai kotu ta rabamu da Kai.. jaka aka kawo maka ko tinkiya ..aikin banza kawai Kuma itama sai na nuna Mata cewa ruwa ba sa’an kwando bane kawai ka goya Mata baya tana yiwa mutane Abinda taga dama…ganin ya wuce tuni ya barta a wajen yasa ta bishi dakin tana bugawa ya bude ya Sanya key, yai Mata banza, sallah yayi ya kwanta domin bacci ne a idonsa sosai.

Itakuma gajiya tayi da bugawa ta zame kasa ta zaman dirshan a wajen tana kuka …ta fara tuno mommy tace nasan da Baki tsame hannunki a kaina ba da ban Zama wukantata ba a gidannan, Nan ta Fara kuka tana Kiran mommy kiyi hakuri ki yafeni na gane kuskurena wlh na tuba…

Nan ta karaci kukanta har gari ya karasa wayewa, yai wankansa ya shirya tsaf ya fito zai wuce aiki, itama data ga uwar Bari tashi tayi tai wankanta Amma batayi break fast ba, ita a dole an Mata laifi, shi Kuma ganin tana bacci ne yasa Bai tasheta ba, Kuma Bai dauka Abin ya Kai haka ba, shiyasa ma ko wayarsa bai dauka ba.

Yana fitowa Bai saurareta ba, Khadija kawai yaiwa wasa yai fice, tana ji tana kalloh, tace lallai wannn shine karfin hali ga duka ga Hana kuka …

 

**********************
Bayan kwana 2 da faruwar haka, basa mgn da Abbas baya cin girkinta itama Kuma ta Dena yi, wai harda fadin ka hutassheni.

 

Ranar daya koma gidan Maryam a wnn Daren ma kafar ta Kara tsananta Mata Batai bacci ba, ita da shi, yace ta tashi suje hospital tace ka kyaleta kawai tunda sunce sai na haihu zan daina ji ciwon….haka suka kwana zaune zuwa asuba Kuma sai ciwo ya koma Mara ta Fara Jin ciwo kadan kadan, Amma ba sosai ba, ganin hakan yasa tace suje Asibitin ko wani abun ne , Amma Bata kawo haihuwa ba, sbd ciwon ba Mai tsanani bane.

Ta shirya da kanta suka fita zuwa asibiti, Kuma a lokacin sai ciwon kafar ya dauke, suna Isa Asibitin suka ce zasu duba ko ta Fara labour, Aiko ana duba ta suka ce ai ga kan baby nan..haihuwace, ita kanta abin ya Bata mamaki sbd bata Jin ciwo a lokacin ko kadan.
Ta saba ita data ke dogon labour,inko hakane ta godewa ubangiji.

Nan da Nan aka fada Masa ai haihuwa ne maza a kawo kayan haihuwa…Shima mamaki yayi don baiga alamun nakuda ba.

Cikin sauri ya koma inda ya aje motar ya fito da akwatin kayan dama tuntuni an shiryasu, indai ta shigar watan haihuwa komai kintsa shi take sai su aje a motar shall incase sai gashi kuwa hakan yai tasiri…ai kafin ya kawo kayan sai Jin kukan baby yayi,Yana kaiwa akace ta haihu ta haifi baby boy…yai murna sosai yace ikon Allah, sbd ya tunaa scanning ance mace ce, gashi komai na Mata ne sai wani set, na overoll unisex, ai mamaki Bai gama shi ba, yaji guda ana ‘yan2 ne twins ol boys, Nan aka dinga rige rigen Masa Albishir ai twins ne maza kyawawa inji wata nurse take fada masa, hmm farin cikin a gurinsa ba’a magana, Baki yaki rufuwa kamar gonar audiga, baisan sanda ya nufi dakin da gudu ba, akai saurin dakatar da shi ..yace don Allah ki barni inje ingansu plz ..akace kayi hakuri in an gyarasu sai ka shiga kaga abinka, tunda duk suna cikin koshin dasu da mahaifiyarsu….

Haka ya hakura ya kyalesu, farncikinsa kuwa yaki boyuwa mutane sai taya shi murna suke yi..Shima har ya bugawa yan’uwa da su ummi kowa sai murna yake bare da suka ji ance lfy suke gabadayansu.

 

Amma Bai fada was ruky ba…

*To ruky hassada ga Mai tabo Taki*🤷🏻‍♀

 

 

To reader’s ku biyoni don Jin Yaya ruky zatayi idan ta samu labari..

 

Muje zuwa

*Ummu Ameer* 💃.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

.
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story & written*

 

*By*

 

*Ummu Ameer* 💃

 

 

*Page* 4⃣1⃣

 

* I really appreciate ur comments masoyana Allah ya bar kauna*😘

 

 

””””’ cikin kankanin lokaci lbrn haihuwar Maryam yaje kunnen ‘yan’uwa da abokan arziki…ruky kuwa ba labari….sbd ko da taga sun fita Bai Gaya Mata ta Kara Jin haushi wai ya fita Bai sanar da ita ba shiyasa Taki kiransa, Shima Kuma Bai Kira ba, Yana sane da Kiyayyar da take da cikin Daman shiyasa yaga Bata cancanci taji ba…

 

Shiko Abbas Yana makale da yaransa ya dauki Hassan din Hussain din Kuma na kwance kusa da Maryam, sai kallon yaran yake cike da kauna Yana yiwa Allah godiya da wnn kyauta da ya masu, yaran jajir dasu kamar larabawa gasu lafiyyayu dasu, sai faman sannu yake mata ganin haihuwa yara 2 a lokaci daya, Yana kuma jinjina Mata tare da godewa ubangiji da ya Basu kyautar da basuyi zato ba…

Sai daukansu hoto yake har da ita mejegon sbd in ka ganta bazakai tunanin ma itace ta haihu ba, garau da ita…sbd Bata ma taba Jin karfin jikinta ba a haihuwarta ba kamar wnn, har tana cewa Abban mufid kaga ikon Allah ko?
A scanning suka ce baby girl, sai ga twins boys…yace ikon Allah ne kawai sai kiga wani lokacin Allah bai Basu ikon ganin dai-dai ba, hasashe ne kawai.

Tace to kayan fa? Na baby girl da muka kwaso? Yace anjima zan canzo masu.

 

Kan kace me yan’uwa da abokan arziki da suka ji lbr duk sunxo asibitin, har su ummi da Abba sunxo ganin jikokinsu, murna a cikinsu kamar me…

 

 

Sai wajen karfe 5na yamma aka sallamesu suka taho gida…tare da yayar Maryam da ta dauki Hussain Maryam Kuma na dauke da Hassan.

 

 

Ruky na zaune jiran dawowarsu don ko kadan batai tunanin haihuwa bace, tana zaune taji karar motarsa ta tashi don yin leken da ya zame Mata jiki…

 

Me zata gani…?

Maryam ta haihu? Mamakinta Bai kare ba,sai da ta ga yara 2 daya a hannun sis din Maryam 1 Kuma Abbas ya dauka, kara goge idonta tayi Wanda take tunanin yana Mata gizo, Amma hakan dai take Kara gani…wata zuciyar tace to ko dayan na waccan ne tana nufin Yayar maryam.

Sai tace Anya Kuwa…. tana Nan tsaye cike da wasi-wasi a zuciyarta har suka shige suka barta cikin duhu…

Kasa zaune tayi tana ta so ya shigo ta tambayeshi…zuciyarta sai dukan 3 take yi.

Ba jimawa kuwa sai ga Abbas ya shigo dauke da wani irin farincikin da ta mDade Bata ganshi a ciki ba, Nan ciki ya Kara durar ruwa, sbd son Jin gulma ko gaisheshi bata Yi ba ta hau tambayar haihuwa tayine me ta Haifa? Ta tambaya cike fa fargaba,
Yace wlh kuwa mun samu karuwa Maryam ta haifi twins Kuma duk maza lafiyyayu, ya fada cike da doki da farinciki Mara misaltuwa..

Wani irin zare ido tayi tana cewa me? Ya Kara maimaita Mata..Bata San lokacin data saki wata Kara ba, tana cewa No! Tare da zubewa kan kujera shirif jiki a mace.

Ta mance shaf Yana wurin…yace No what!

Sai a lokacin ta dawo hankalinta ta wayance da rike ciki tana cikina Abbas ciwo Wayyoh cikina….sai ta kwasa a guje ta shige toilet cike da tsoron Allah yasa bai ganoni ba….

Shiko tana shiga yai murmushi ya ganota tsaf ba tun yanzu ba, ficewa yayi ya koma can wajen Maryam.

 

Ruky kuwa bata fito ba, sai da ta tabbatar da baya Nan ta fito tana goge xufar data cika Mata fuska kamar wadda Tai wasan dambe, tana fadin yau na Banu ni ruky Yan 2 ta Haifa …tabdijan ai shikenan Kashi na ya bushe mun gama Zama Bora ni da diyata, Maryam ta gama samun wuri a zuciyarsa….yadda nake masifar son twins Amma ace matar da nafi tsana itace ta Haifa masa su…shikenan ynx Kuma sai abinda yayi gaba….

Har ta janyo waya zata Gaya wa mommy sai ta fasa sbd har ynx mommy Bata Bata fuska ko xuwa tayi daga gaisuwa Bata Kara shiga sabgarta, saidai suyi ta hirarsu da kanwarta Aisha.

Sai tai dialing no. Farida tana dauka ta Fara Bata labarin kishiyarta ta haifi twins duk maza…cike da mamaki farida tace da gaske? Tace wlh ynx Nan suka dawo daga asibiti, ruky tace wlh danaji lbr kusan zaucewa nayi don bakin ciki…farida tace name Kuma Kinga gara ma ki saduda ki dauke kishinki akan haihuwarta gashinan kinxo kina kyashi tana d ciki sai gashi Allah ya Bata kyautar 2, tace kawai kema ki addu’a Allah ya baki twins din tunda so kike ki Zama mama…ta karashe maganar da dariya.

Tace wlh Nima Ina bala’in son twins da Allah zai bani a haihuwar farko Kinga shi kenan na gama…ruky tace dakata da Allah na fuskanci ynx kin canza tunaninki akaina in ba haka ba, nakiraki ki tayani jaje kina min wani soki burutsu.. .

Farida tace kamarya …so kike nace ki kashe su ko me? Ni Banga dalilin d zaisa ki damu kanki akan haihuwarta ba, sbd matarsa ce, in Kinga kema kin shirya zazzago Masa ne bissimillah Mana waya Hana ki…ni wlh bana dorawa kaina wnn wahalar ba abinda zaisa ni damuwa da haihuwar kishiyata…ni dai barni da Kama miji da kuma makirci na, don ni bama zan Bari har yaje gareta ba, balle haka ta faru, in ma ta faru to ko ajikina tunda bani zan haifar Mata ba, ita zata ji ajikinta ..

To gara ma ki cire wnn a ranki kici gaba da gudanar da Abinda kika fara,in kuma kema kin shirya haihuwar ne to Allah ya baki Yan 4.

Rukayya tace bazaki ganeba, shikenan kawai …farida tace sai munxo suna ta fadi da zolaya . Ruky ta kashe wayar tana tsaki…

 

 

Tunda akai haihuwar ruky Bata je taga twins ba, ba yadda baiyi da ita ba, sai tace to zan shiga, sai lokacin shigar yayi sai tace wai cikinta na ciwo..har akai kwana4 da haihuwar, Kuma kullum a gidan yake kwana, sbd tunda Maryam ta haihu ta nemi alfarmar ya koma wajen rukayyah har Allah yasa yaran sun dan kwana 2, sbd abubuwan suna mata yawa duk da hafsa tana gidan ga Kuma wata da aka kawo Mata don taimaka Mata da rainon yaran, ga kuka in wnn ya Fara sai wnn Shima ya kama, sai duk ta rikirkice.

Haka Nan ya hakura ba don yaso ba, itakuma ruky da farko kin yarda tayi tace sai ynx da tasan Bata da mamora ne zata turoka, to bazan yarda ba, nima aikin yawa yake min, har ya zuciya zai koma Kuma sai ta lallabashi ya dawo tace ai dama ce na samu da zan gama kamashi kafin ta warke…

 

Sai ana gobe suna ta shiga gidan Jin ance Yan danbatta zasu xo yau, Kar azo a Dora Mata laifi yasa ta shiga, ko da ta shiga ma ko daukan yaran Bata yi ba, har an dauko Mata sai tace barsu kawai na gansu daga Nan…duk da Bata daukesu ba Amma ta hango su yaran tubarkallah son kowa..Bata jima ba ta tashi ta tafi…Maryam batai mamaki ba da Abinda ruky tayi tasan zatai fiye da haka ma..sai sis dinta dake dakin ce tace haka kishiyartaki ke da bakin kishi haka, bako Kara..take bayyana shi a fili?
Maryam tace haka take wlh kinsan kowa da irin nashi kishin…sis din nata tace wane irin kishi hauka dai..waye bashi da kishin? Ai dannewa ake musamman ma agaban kishiyar, Amma ita shine nata ya fito fili a bayyane…

Maryam murmushi kawai tayi tace hmm Allah dai ya kyauta Aunty..tace ameen dai.

 

Zuwa yamma gida ya cika da yan’uwa Yan danbatta, har da su Yaya babba tace ita ai a wajen ruky zata kwana…bayan an gaisa din wnn karon ta rage Kiyayyar Maryam a ranta ko don taga ta haifi Yan 2 ne oho! Don da farinciki ta shigo…tana manne da yaran.

Bayan sun gama gaisawa ta tafi wajen ruky ita datawagarta su biyar…suna shiga gidan ruky ta karbe su hannu 2, kasancewar Yaya babba mutuniyarta ce..

Tana ji sunce ai anan zasu kwana Nan take ta dauke wuta Tai dif duk sun fahimci hakan, sai ta Fara inda inda tana cewa ba isasshen waje ai Anty…eh ba komai ai sai muyi kwanciyarmu anan. Ruky na Jin haka ta tashi ta shiga daki tana kunkuni wai wlh bazasu sani wahala ba, ni ba da haihuwa ba, sai a barni da wahala wlh bazan iyaba . Tana cikin maganar sai ga Abbas ya shigo Yana lfy na ji kina magana ke kadai ?

Sai tace wai su Yaya ne zasu kwana anan shine Naga kuma ba wadatataccen waje….yace badai ki Fadi masu hakan ba ko?

Sai Tai karyar eh!

Yace kyalesu Mana yau dai 1 tunda ba anan zasu dawwama ba, haka Nan ta hakura Amma bata so ba, don ma kawai suna dasawa da yayan ne inba hakaba wlh ba Wanda zata Bari ya kwanar Mata. Abincin data kawo masu plate 1 ko mutum 2 bazai Isa ba.

Hakanan suka hakura sai daga baya wata daga cikinsu ta amso musu a wajen Maryam….Aiko ta Sha zagi wajen su, suka ce wnn matar da ita kadai ce wajen Abbas ba Wanda ze ziyarceta, gaskiya baiyi dace da matar kwarai ba wlh…itama Yaya taji haushi domin kuwa harda kawayenta daga ciki ta taho dasu, Kuma ta kunyatata a gabansu…Amma dake har ynx Bata cika ganin laifinta sai ta basar kawai…2 daga ciki kuwa fir kin kwana sukai suka koma wajen Maryam, suna ai ga Yar mutunci anan…

 

*******************

Washe gari ranar suna gida tun safe ya cika da mutane, sunyi shawara akan a bar musu sunansu wato Hassan da Hussain. mejego ta sha kwalliya kamar ba me jego ba, sai kace amarya don musamman aka dauko Mai make -up tazo tana Yi mata, Shima ango ba baya ba, anyi order abinci kala-kala kamar gidan biki, duk inda mejego tayi sai wani kyalli take,..ruky kuwa kasa shigowa tayi don bakinciki, sai leke …sai da farida tazo ta takura Mata akan su shiga itama don taga me jego da yaran, kwalliya farida Tai Mata itama ta Sanya wata super Riga da siket.ta yafa mayafin kayan orange, suka shiga gidan…ai Bata Kara sirewa ba sai da taga Maryam cikin wani dankararren lace Wanda kana gani yasha kudi ba kadan ba, ya amshi jikinta sosai tayi parking din kanta a tsakiya an Masa doughnut, an daura Mata dankwali irin me Hawa Hawa din Nan kamar amarya tayi kyau sosai…da ruky ta ganta kasa magana tayi, sai farida ce ta gaisheta Tai Mata barka dake ita tafi ruky iya duniyanci ta wani saki jiki kamar tasan Maryam har da daukan baby’s din tana fadin Masha Allah, yara kyawawa, Aiko ruky ta wani balla Mata harara.

Ruky dai ba magana don ko gaisheta batai ba, sai daga baya Maryam ta tuna basu gaisa ba, sannan ta gaisheta, ta amsa da kyar fuskar Nan ba annuri, ga kishin kashe kudin da akai kamar yau aka Fara haihuwa a gidan, a zuciyarta tace lallai Abbas ya Raina min hankali Amma zamu hadu…ganin farida ta zake da yawa yasa ruky tace tashi mu tafi…suka Mika Maryam ta cikawa farida take away aleda Tai Mata godiya suka tafi….suna fita farida tace Kai Amma gaskiya yaran nan Masha Allah kamar in sace su. …wlh sun bani sha’awa, harara ruky ta bata, tace wlh kin bada ni kawai kina shiga sai ki zake ki hau surutu ..mtsss tayi tace ni ban ma fahimceki ba? Meye amfanin yin hakan …farida dariya tayi tace wlh kina bani dariya Baki iya zaman duniya ba, so kike in biye Miki agaban kishiyar in nuna kishina don HAUKA ?
Lallai da sauranki shiyasa har ynx Baki nasara akansu ba, sbd gajen hakuri da rashin iya danne kishinki tabdi wlh da sauranki ruky …

Ruky a fusace tace ba wani nan gsky ni banji dadin abinda kikai ba …tace to kiyi hakuri bazaki Kara ganina ma agudanki balle kimin haka..ta fasa rain bace.

Ganin ran farida ya baci ta janyota tana fadin yi hakuri besty nah, muje ba haka nake nufi ba, hannunta ta riko suka shiga cikin gidan tace muje ki yi min wata lecture….

 

 

Muje zuwa

*Ummu Ameer ce* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story& written*

 

*By*

*Ummu Ameer* 💃

 

 

*Page* 4⃣2⃣

 

 

Suna shiga cikin gidan ta jata daki ta Sanya key gudun Kar wani ya shigo ya shammace su…

Dukansu Zama sukayi a gefen gadon suna fuskantar juna, farida tace wlh kin bani haushi har na Fara tunanin fita harkarki tunda baki daukan shawara…ruky tace kiyi hakuri kawata wlh idona ne ya rufe kinsan ni akan kishi…

 

Murmushi farida tayi tace Banga laifinshi ba, akan abinda yake Miki..ko kinsan Namiji ba abinda ya tsana ga mace kamar nuna tsantsar kishi akansa, ko zakiyi ma to karki Bari ya gane hakan sbd matukar ya fahinci haka akwai matsala….kinganni nan duk zafin kishina Ina iya controlling dinshi ban taba nuna Masa shi ba, bantaba nuna Masa Kiyayyar matarsa a fili ba..inkinga yadda nake nuna kauna agabansa akanta Abin sai ya Baki mamaki ..shi yasa shi Kuma ya dauki yadda da Amana y doramin ynx ko wani ne yace Masa zan Yi abinda nake a bayan idonsa bazai yarda ba, ke wani lokacin ma Nike bashi shawara akan ya Dan gyara halinsa akan matarsa Nan ko Bai San nice silar komai ba, shiyasa nace Miki ni ba boka ba mallam kawai basirata ce ke aiki.

Amma ke na fahimci kina da gajen hakuri ga shi Baki iya danne kishinki ako ina, kinje wajen Mata ko magana Baki Mata ba, kin nuna kiri-kiri kishin yaran kike, kuma na tabbatar Shima kin nuna Masa hakan,sannan kike tunanin har ki samu matsuguni a Zuciyarsa, sannan Nima kike so in biye Miki mu Zama mahaukatan gabadaya…

In Zaki canza taku ki canza tun wuri kafin lokaci ya kure Miki ki daina nuna tsanarta a gaban mutane duk da dama ba zancen so ga kishiya Amma ki iya takunki sai kiyi galaba, itama din ai ba sonki take ba, Amma na tabbatar Bata taba nuna Miki a fili ba, sbd iya kissa kin zauna yarinya karama tafiki wayo….

Hmmmmm doguwar ajiyar zuciya ruky tayi tace zan jarraba Amma Abin da kamar wuya …wai gurguwa da auren nesa .

 

Farida ta tashi tare da fadin atoh! Ya rage naki inkin bi shawara kanki …ni dai Kinga tafiyata, ruky Tai Mata godiya ta rakata har gate din gidan sannan ta dawo tana dawowa ta hangi Abbas ya rungumo Maryam suna picture, ba yaran ahannunsu ma sbd sunyi tare dasu tun dazu. Har wani style suke sai kace masu pre-wedding pictures sunyi matuakar kyau ba kadan ba, hakanne ya Kara tunxura ruky ta kwasa a guje don bazata iya kallah ba….tana shiga Tai kacibus da Yaya babba tace lfy kuwa Yar Nan?

Ruky ko kallaonta batai ba, ta shiga dakin ta Sanya key sai faman huci take kamar wacce taga wani bala’i, don kukan ma kasa yinsa tayi duk da ta maida shi sana’a don kusan ko yaushe acikin yinsa take , Yaya babba tabe Baki tayi tace wnn yarinyar fa na fahimci ba diyar arxiki bace, kaji Ina Mata mgana ma ko ta kaina Bata bi ba, tabdijan !

 

Sum-sum ta fice ta koma can bangaren Maryam.

Mejego Kam da kyar ta samu ta zille da wnn pic da ake tayi yaki karewa, ga Baki na jiranta aciki, sai da wata abokiyar wasansa tace Kai kyaleta haka Nan da hoton Nan kabi ka nanike Mata tun dazu ka fakaice da hoto…yace to sa’idinawa Ina ruwanki? A barni in Sha iska…ya fice sumi-sumi dashi.

 

Taro Kam Alhamdulillah ansha Baki gida ya cika da mutane, wadanda ma Basu taba xuwa ba sunxo sunan twins, sunsha kayan barka, Kuma anci an sha, an tashi taro lfy.

 

Ruky tana can ta kulle kanta a daki ana ta bugawa Amma shiru Taki budewa, sai kusan magriba ta fito idon Nan yayi jajir kowa ya fahimci kishine ke addabarta, kowa sai fadin albarkacn bakinsa yake akanta…Basu Kara sirewa da ita ba sai da ta tazo falon cike da tsiwa ta tsaya agabansu tana fadin wlh aje a gyaran bandaki tayaya zaku shiga ku Bata min sannan ku barni da gyrara . .ta fada cike da rashin kunyar…kuma a lokacin harda Yaya babba da sauran yan’uwa , har wata daga cikinsu ta tashi zata zazzago Mata rashin mutunci Yaya babba ta ruko ta, yi hakuri bazamu biye Mata ba, kuruciya ce. …kuruciya fa kika ce inji me Shirin yin masifar wane kuruciya ce anan bayan Saida ta gama girmanta a gida ta rasa mashinshini, shine ta makale wa Abbas, sannan zata zo tana yiwa mutane hauka. Don nasan rufarsa sukai Don a hankalinsa bazai kwaso Mana wnn shirgin ba…ruky kuwa naji an Mata tatas ta fashe da kuka ta shige daki, Yaya babba tace me yasa ba kyajin magana ne Asabe sai da nace ki kyaleta kika ki, tace kyaleni in nuna Mata ba tsoransu ake ba, Ina sane da Abinda suke yi mana, cin kashin ya Isa haka

Yaya babba janyo su tayi tace su wuce su tafi wajen Maryam mu bar Mata gidan, Asabe tace akan me gidanta ne, ko kuwa da shi aka kawo ta, Yaya babba tace ki dai taho nace ko, suka dunguma suka koma wajen Maryam,, sannan suka dunguma sai gidan yayah suka ce sai da safe don acan zasu kwana.

 

Abbas kuwa bayan sun tafi ya shiga wajen ruky, Yana ta buga kofa, tana ji Taki budewa ya gaji ya koma wajen Maryam.dakinsa ya shiga ya kirata sukai ta hirarsu Yana yabon kyan datai kamar sabuwar amarya…

Yace Masha Allah gaskiya anyi taro sosai don ba’a taba cika kamar haka ba, ko don sbd Yan 2 ne kinsansu da farinjini, tace lallai Kam Masha Allah, an Yi taro sosai, Kuma an Kare lfy.

 

Yace Allah ya kawo wasu twins din Mata, wata shekarar..ya fada da zolaya….

Tace haba dai ai na gama, haihuwa fa ba sauki …

Yace to meye nee haihuwar, ba gashinan ba, kamar Baki Yi ba, wazece ma kece mejegon sai faman kyalli kike kina haskawa kamar zahra a cikin taurari…

Hmmmmm tace tare da tashi ta zuba Mai sauran snacks din da drinks da kuma naman da aka soya sannan ta zuba wa Maryam ta bashi in zai tafi ya Kai mata.

Sai da yayi kusan awa 2 suna ta hirarsu, sai itace ma ke tuna Masa akan ya tafi kar ruky Tai fushi…Amma sai ya basar sbd Bata San ma ynx rufe gdn tayi ba,sbd shi bashi a cikin mazan dake kawo zancen kishiya kamar yadda wasu mazan suke duk Abinda ya hada su, da daya sai ya fadawa daya, sbd a ganinshi hakan Bai kamata.

Sallama yai Mata kamar Kar ya tafi har Yana cewa shifa gaskiya ta barshi ya dinga kwana da yaransa Yana Jin duminsu a jikinsa gaskiya.

 

Ko da ya koma wajen ruky zuwa yayi ya tarar da gidan a hangame alamun Bata ko ina a bude yake yai mamakin hakan, shiga yai ya duba ko Ina Amma Bai ganta ba, ya Kira wayarta Bata dauka ba, yace Ina Kuma taje cikin Daren Nan haka, ya bugawa anti Salma y tambayeta ko taje tace batazo ba.

Itama Anty Salman ta tambayi mommy tace Bata zo ba, Kuma tace ko tazo ba dai gidana ba wlh, tunda na kafa Mata sharadi, Kuma ta Amince taje tunda mijinta ya finiii.

Janyo kofar yayi ya rufo gidan ya shiga yai wanka yai kwanciyarsa.

*****************

Tun asuba text dinta ya shigo tace masa na fuskanci Kora kake min da hali a gidanka, don na fahimci wani Abin ma da gayya kake yinshi, to ka sani duk halin da na fada Kai ne sanadi, Abbas bakin cikinka ya kusa sa zuciyata ta buga, duk Abinda ya faru da ni kasani Kaine sila, sbd haka Naga ya dace in baku waje kasha iska….

 

Yana gama karantawa Kuma sai jikinsa yai sanyi, duk da yasan ita take Sanya kanta a ciki, Abu Bai taka Kara ya karya ba, ta maida shi babba.

Reply yai Mata Yana tambayarta tana ina?

Ta bashi amsa da cewa tana gidan wata kawarta farida, shi Bai ma San gidan ba, balle farida.yace Tai Masa kwatance zai zo su tafi anjima..

Gidan farida taje tun jiya Amma Bata gaya mata gaskiyar rashin hakurinta ne ya fito da ita ba, sai tace wai ji tayi gidan ya gundure ta, gashi ba kowa shine tace zata zo ta kwana gb sai ta wuce,farida kam Sam Bata yarda da Abinda ta fada Mata ba, don tasan halin ruky rashin hakurinta ne ya Hana ta Zama, binta tayi a haka itama, suka Sha hirarsu..kasancewar mijinta Bai kasar..ita kadaice a gidan…

 

Kasancewar wkend ne ranar lahadi bayan Abbas ya tashi ya shirya ya shiga wajen Maryam Bai nuna Mata Bata Nan ba, daga bisani yace zaije ya dawo.

Tace Allah ya tsare hanya .

Tace Ameen.

 

Kwatancen da Tai Masa ya bi har xuwa gidan farida baisha wani wahala ba, kasancewar mijinta sananne ne a unguwar,. Yana Isa y kirata a waya yace y iso, tace y shigo yace a”a kawai ki fito sauri nake.

 

Sai ga ta sunfito da farida, tazo suka gaisa da Abbas, Amma tunda ya ganta kawai yaji Bata kwanta Masa a rai ba, vaison alakarsu da ita, Kuma Bata taba bashi lbr ta ba.

Sallama sukai Mata suka tafi, a hanya yake tambayarta Ina ta samo wnn Kuma, tace kawata ce tare mukai sch. Da ita yace Kuma ki rasa inda zakije sai gidan kawa ki kwana?

Yace karki sake plx bana so…

Tun a hanya suka sulhunta kansu bazakace ma wani Abin ya faru tsakaninsu ba.

 

Kuma ba Wanda yasan ma tayi yajin sbd tun jiya ba Wanda ya kuma shiga wajenta.

Ganin haka yasa ruky Kai ya fasu …
Sai kuma aka bude sabuwar soyayyah .

*To Anya kuwa ruky zata Bari ta dore*

 

Muje xuwa

 

*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story & written*

 

*By*

*Ummu Ameer* 💃

 

 

*Page* 4⃣3⃣

 

 

 

Su ruky kwana 2 shiru an Sami yanda ake so…shiru kake ji, duk da cewa Bata Jin dadin zuwan da yake wajen Maryam ya dade, gani take tunda ta Bata girki ai ashikenan,haka dai taita dannewa, data ga Abin ba sauki, sai ta sameshi Tai Masa magana, Abban Khadija a gaskiya fa bana Jin dadin abinda kake min, tace ta bani girki, ya kuma za ai ka dinga shiga tana rike ka, da kisisina gaskiya banso, in Kuma girkin take so ai bissimillah, Amma bazata barni da wahala ba Kuma ita da rike miji ba…

Shiru yayi na wasu seconds ya dubeta da mamakin kalamanta a zuciyarsa yace ashe Bata canza halinta ba, dubanta yayi Rai a bace yace kina nufin don ta Baki girki bazan zanje ni in duba lafiyarsu ba, kawai don Kar ranki ya baci…in kin gaji da girkin ba matsala sai na koma can din ai ba wani abu bane…

Tana jin ya Fadi haka ta Fara a’ a ni bance na gaji ba, a zuciyarta tace yadda nake jin dadin kasancewar sa tare Dani b zanso ya koma can ba ynx..ai Kaine sai ka shafe awowi acan kamar bazaka dawo ba,

Yace na dauka kin gaji ne da sai in barki ki huta…

Murmushin karfin hali tayi a zuciyarta tace ai sai na gama kamashi a hannu ya mance da wata Maryam tukunna…

 

Haka ta tsara cewa zata bi duk wata hanya domin ta ga Abbas ya dawo gareta sannan ya mance da duk wani Jin dadin dayake samu daga gareta..

*Anya kuwa*?

 

itama ba azaune take ba, Daman sai da aka Mata dinki, Yana warkewa ko ta Fara shiga ruwan magarya da bagaruwa, da ta fito Kuma Tai tsuguna kan garwashi à na kanumfari, ga shi tana kokarin cin duk wani abinda zai dawo Mata da Abinda ta rasa, dama ita ko ba kishiya Bata wasa da kanta, balle Kuma ynx ai sai abinda yai gaba, shi kansa aduk sanda ya koma mata sai ya mata jinjina Yana fadin ita din dabance a cikin mata, domin ko yaushe zam-zam yake jinta, shi yasa Bata wasa ko kadan da kanta, gashi ko hakan ya janyo Mata daraja ta musamman.

Yau kwananta goma Sha daya da haihuwa, Hassan ya tashi da wani irin zazzabi sai kuka yake, Abbas cikin tashin hankali yace ta shirya su yi maza su je asibiti, sbd yaga ma idon yaron ya canza kala zuwa dorawa, cikin tashin hankali ta Sanya hijab suka tafi…

Kasancewar sa likitan yara, Shima Kuma a bangaren yake direct ya wuce da su can S.C.B .U dake cikin Asibitin mallam, Da taimakon wani abokin aikinsa Dr.mahmud ya taimaka Masa wajen gwaje -gwajen Don a tabbatar da matsalar tashi, Nan da Nan akai sun gano joundice ne, yai masa karfi a jiki, sbd haka dole sai an canza jini…

Koda Maryam taji labari kuka ta Sanya tace shikenan Hassan don Allah karka tafi …kuka take sosai Mai ban tausayi gashi ta shaku da yaron don kuwa har yafi Hussain kuzari,ita gani take bazai tashi ba,ta Yaya za ai wa jariri wani canjin jini…

Sai da Abbas ya fahimtar da ita tukun yace aikinsu ne arana sai suyi ma yara kusan goma Kuma duk su tashi garau ai juyen jinin shine samawa yaron lfy, ki kwantar da hankalinki ba abinda zai Sami Hassan dinki kinji mmn twins ya shafa Mata habarta tare da goge Mata hawayen fuskarta, ya lallabata ta samu nutsuwa ya kaita office dinshi ta zauna acan bayan an dauki jininta za’a tantance blood group dinta. Kuma sungano 0+ne shima nashi Hassan din haka.

Nan da Nan aka Basu gado Kuma don tuni an Fara Masa aikin, ita Kuma aka kaita can amenity ita da Matar dake taimaka Mata da rainon, Koda taje dakin kasa komai tayi duk jikinta yai sanyi sai addu’a take Allah ya bashi lfy ya tashi kafadunsa.

Sai wajen 11 na dare Abbas ya shigo dakin yace har anyi ba wata matsala insha Allah zuwa gobe ma, zasu tafi gida.. Alhamdulillah tace Tai wa Allah godiya.

Yace Bari ya koma gida yaje ya dauko musu abubuwan bukata da Abinci, tace to Allah ya kaika lfy, ya tafi.

 

Can kuwa ruky ta Kai kololuwa wajan bacin rai duk da ya sanar da ita inda zasu Amma sai ya je ya zauna, nufinsa acan zai kwana sbd akanshi aka fara haihuwa kenan, ganin har 1 na dare Bai dawo ba, gashi wayarsa a kashe…tana ta ita wlh bazai yiwu ba, ya za ai su dinga Raina Mata hankali.

Tana zaune tana mita sai gashi ya dawo don sai da ya Fara Kai duk abinda za a bukata cikin boot din motar sannan ya shigo y Gaya mata, halin da ake ciki…

Yana shigowa tace lfy sai ynx, ya fada Mata lalurar yaron Amma ko ajikinta Bata nuna damuwa ba, sai ma cewa tayi ynx to me kake nufi? Yace zan koma na Kai musu kayan da suke bukata ne, sai na dawo…zare idanuwa tayi cike da mamakin zancen nasa tace kana nufin cikin Daren Nan zaka koma, tace gskya ka Bari kawai da safe ka Kai musu ynx dare yayi….wani banzan kallo ya bita da shi ya juya yai ficewarsa ya barta Nan gurin a tsaye.

Wani takaici ne y lullubeta ta ciji yatsanta Tai kwafa ta shige daki tare da fadin zaka dawo ka sameni, sai dai ayita ta Kare yau na gaji haka ..

 

Koda ya koma Asibitin sai da ya Fara zuwa wajen Hassan yaga yanayin shi Kuma Alhamdulillah aiki Yana kyau sannan ya wuce ya kaiwa Maryam kayan sai da ya sa ta agaba taci Abincin sannan ya tafi yace ta dinga lekawa wajen Hassan lokaci zuwa lokaci, sannan sukai sallama yace da safe in ya Kai su mufid sch.zai taho.tace Allah ya kaimu.

 

Sai karfe 3na dare ya koma gida yaje wajenta zai Gaya Mata zai kwana da yaran tunda mommynsu Bata nan, duk da akwai hafsa Amma gara ya kwana da yaransa, dama haushinsa take ji kamar me, tabe Baki tayi taja tsaki, tayi komawarta daki, shi Kuma ya koma can wajen yaran duk da sun yi bacci, adakin shima wanka yayi ya kwanta bacci.

 

Washe gari sai da ya kusa makara sbd Bai Sami isasshen bacci ba, a gurguje ya shirya yaran shi ya masu wanka da kanshi ya shirya su tsaf, hafsa kawai break fast tayi musu, ya tafi kaisu sai tanbayarsa suke Ina mommy da su Hassan yace suna asibiti in sun dawo daga sch. Zai kaisu su gansu.

 

Ko da ya dawo ya shirya yaci abinci, sbd ita bayi ta yi ba, ta Hana kanta sukuni tun jiya, shi yasa tace ba zatayi ba, yaje can Maryam din ta bashi.

Ko da ya shirya zai tafi ya shiga yai Mata sallama, tace ai wlh kafarka kafata duk inda zaka Ina biye da Kai ta fada tana Shirin Sanya hijabin ma duk ba a goge ba,ko wanka ma batayi ba, ta Suri takalmin zaman gida ta Sanya ta Riga shi fita da yarinya a hannu ko wanka itama Bata Yi Mata ba, tana fadin haka kawai kun Raina min wayo ka dinga fita da ita Kuna Shan soyyayrku, ni Nan kun barni jiran gida,

Magana yake Mata Yana ki dawo, ki Bari ki shirya in zan Kai su mufid sai muje, gaba tayi ta Riga shi shiga motar, ta zauna tana surutai kamar tababbiya

Mamakinta kawai yake Anya kuwa tana d cikakken hankali? Ana ta Mara lfy tana wani shirmenta banza, ta Sanya zargin wofi a ranta, a fusace ya shiga motar ya figeta da wani mahaukacin gudu, kamar zai tashi sama, ko kallaonta Bai yi ba, bare ya tanka mata.ta gama kular da shi, ga haushin shigar da tayi don tsaf za ace house girl ce….kawai don ta tozarta shi ta shirya hakan , kwafa yayi yace in kinsan wata, ai Baki San wata ba….

 

 

Muje zuwa

*Ummu Ameer ce*💃💃

🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

 

*Story & written*

 

*By*

 

*Ummu Ameer*💃

 

 

*Page* 4⃣4⃣

 

 

*Addu oin ku sun iso gareni masoyana nagode kwarai Allah ya bar kauna* 💓💓💓

 

“”””” Ko da isarsu Asibitin,bayan yai parking, shammatar ta yayi, yai saurin fita daga motar ya Danna security na motar yai fita ya barta a wajen, sai faman buga glass din take,shiko ko a jikinsa, direct wajen Hassan ya wuce kasancewar ba guri daya suke ba, da Maryam dinba da Dan tazara.

Yana shiga ya sameshi sai wutsil- wutsil, yake gashi garau baka ce shi akai wa juyen jini ba, zuwa yayi ya dauko shi yayi duk binciken da zai yi na tabbatar da yasamu lfy, kuma Alhamdulillah ba sauran wata matsala, yace zuwa yamma ma kawai zasu tafi.

 

Bayan ya gama da Hassan ya koma motar ya dauko musu breakfast ya kunna motar Yana kunnawa Tai saurin fitowa sai faman hararar shi take, tana fadin ai kome zaka min sai na bika …. Ko saurarta Bai yi ya fito da Abincin da sauran wasu ledoji ya rufe motar ya wuce can Amenity inda take, itako tana biye da shi a baya…

Shiko godiya yai ga Allah, da Bata Sami binshi cikin s.c.b.u dinba, sbd abokanan aikinshi suna wurin.

Sai sauri yake Kar ta cimma shi ta ga room din da zai shiga, Don yadda take dinnnan yasan zata iya komai a gaban mutane, sauri yayi ya shiga dakin ya rufe, dake shine ba farko, itama sai gata sai faman diri- diri take tana kokarin shiga, sai security tace ya lfy madam? Ina Zaki ta Fadi tare da tokare hanyar shiga, sbd ka’idarsu ce ba’a Bari a shiga sai 4na yamma, sai Mai jinyar kawai ko mijin.

Ruky kallonta tayi da raini tace kamarya? Sbd ita Bata San ka’dar Asibitin ba, sbd Bata zuwa Nan din, Wanda take zuwa daban.

Security ta taso pa hasile ganin irin kallon rainin da ruky take mata, tace who are you ana Miki mgn kina kokarin shiga wajen wa zaki? Na Gaya miki ba Wanda zai shiga wurin Nan sai 4 tayi aha!

Ruky tace ai sai ki Hana ni in gani kinsan ko ni wacece Zaki hanani shiga wajan mijina, ko Zaki ce baki San Dr. Abbas danbatta ba?

Security ta kalleta ta jefeta da wani kallon raini, tana tunanin Bata san matar Dr. Ba, Zatai mata karya, Kila ma house girl ce, tace a Ina kika Zama matar Dr. Bayan matarsa na ciki, babynsu ba lfy.

Ruky tasowa tayi zata shiga tana kokarin bangaje security, ita ba abinda yafi Bata haushi ganin tana Bata Mata lokaci, Bata shiga ta ga uwar da suke ba, ganin haka yasa ta zuciya, tana kokarin hambare security, itako tana ganin haka ta tattaro karfinta, ta wullah ta gefe.

Abbas tunda ya jiyo sautin muryar ruky ya garzayo d sauri gudun karta jawo Masa Abin magana, Yana zuwa ya taradda sai zagin security take, itako Tai shiru bazata biye Mata ba, sbd intace zata biye Mata sai ta ballah ta, shiyasa tai shiru ta kyaleta, shikuwa Yana ganin haka yai hanzarin karasowa yace wa security ai tare suke, tace kayi hakuri sir! Kasan dokar wurin shiyasa ban barta t shiga ba, yace no problem.

 

Yayi gaba tana biye da shi yasan dama bazasu barta ba, shiyasa yai saurin shiga, ya barta a baya, ynz Kuma ganin zata Tara Masa mutane yasa ya shigo da ita tunda ta Zama jaraba….Abin nata ma ya wuce hauka .

Suna shiga dakin itama ta shiga, ganin Maryam Tai ta Kara wani kyau kana ganinta kasan tana cikin kulawa d kwanciyar hankali, hakan ya sosa Mata Rai, ta dauka zata ganta cikin wani hali, shiyasa itama, Bata damu da shigar da tayi ba, sbd taga yawanci Mata in suna jinya a asibiti, shikenan sai su maida kansu marasa lfyr, wasu ko wanka ma gagarar su yake, maigida yazo ya taradda su kacha-kacha wai sbd tashin hankalin rashin lfyr…

Ita kanta sai ynx ta Fara Jin kunyar kanta akan shigar da tayi danasanin shigowa… Itako Maryam sanda taga ta shigo dariya ce, taso kufce Mata Tai saurin kawar da Kai gefe ta rufe Baki,

Mutuniyar kuwa ana hakince akan kujerar da aka tanada don Baki cike da takaici ta shigo bako sallama balle ta Gaishe su, Tai kicin-kicin da fuska, sai Maryam dince ta gaisheta, tace Khadija ammata, tana Mata wasa, ganin da tayi kamar in taci gaba da Zama zata kara wulakanta yasa tace ka tashi mu tafi, tai hanzarin fita a dakin.

Abbas yana fita yace Bari in maida matar can gida Kar ta jawo min wani Abin,don Naga ta Fara fita hayyacinta.

Tace Allah ya kiyaye hanya, yace ameen ynx xan dawo insh allah, ya fita itakuma tuni har ta Isa ga motar tun kan y iso ya bude motar ta shiga, suka dauki hanyar gida,tace kana nufin wait gida zaka maida ni, wlh nifa duk inda kasa kafa sai na saka, bazaka bige da rashin lfy Kai ta cin amanata ba…ganin Abin nata da gaske ne, yasa wata dabara ta fado Masa yace to muje in kaiki gida ki wanka sai in jira ki mu tafi ko kuwa, tace yayi! A takaice.

 

Suna Isa gidan ta shiga da saurin don ta hanzarta ta shirya karta Bata Masa lokaci, shikuwa mukullan gidan ya diba, tsaf ya saka Aljihu, Yana ganin ta shiga wankan ya saurin fita ya kalleta ta baya….ya shiga mota ya tafiiiii

 

 

Muje zuwa

 

*Ummu Ameer ce* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

 

*Story & written*

 

*By*

*Ummu Ameer*💃

 

*Page* 4⃣5⃣

 

“”””A hanya kuwa tunanin wnn halin na rukayya yake, Yana tambayar kansa Anya kuwa Bata da wani matsala akanta kanta ko kuwa tsabar kishi ne yai Mata yawa? Haka dai yaita sake-sake akanta har ya Isa Asibitin. Bayan ya huta Daga bisani ya koma kan aikinsa.

 

Ruky kuwa ko da ta fito a toilet ta duba Bata ganshi ba, ta ga ya kulleta ta baya…wani irin ashar ta mulmulo, tace ni zai rainawa hankali,ni zai mayar shashasha? Lallai yau zan tabbatar Masa da bani da hankali a KISHI…

Haka dai taita buga kofar kamar zata balla daga baya Kuma ta shiga kitchen ta hau farfasa abubuwa, tana fasawa tana kuka, haka ta farfasa kayanta ta hargitsa komai na gidan kamar wancan Karan. Data gaji da haukan taga ba Mai jinta, ga yarta sai kuka take Taki sauraranta, da kanta Kuma ta natsu sbd gajiyar da jikinta yayi ga baccin da batai ba, tun jiya, daukan Khadijan tayi suka shiga daki suka kwanta.

 

 

Acan Asibitin kuwa tun karfe 4 aka sallamesu har ta dauki hassan din zuwa can inda take, suna jiran Abbas ya tashi aiki su tafi.

 

Sai karfe 7na yamma suka dawo gida, hakan kuwa yayi dai- dai da farkawar ruky daga baccin daya saceta, aiko da dai ta tabbatar da sune suka dawo Kuma har da Maryam, Nan ta Dora daga inda ta tsaya sai faman ashariya take binsu dashi sannan Kuma tace wlh indai Bai bude ta ba, sai Tai Masa danyen aiki, shiko Yana jinta sai da ya gama duk Abinda zai yi, sannan ya nufo wajenta, duk da cewa har ynx Bata fasa abinda take ba, na ashariya da farfasa abubuwa, Yana dumfaro wajen ya ji abinda take a zuciyarsa yace ikon Allah ita Kuma irin nata kalar bacin Rai kenan, Aiko in Bata shiga taitayinta yau za’ayita ta kare, na gaji da wnn haukan, bazai yiwuba ya fada cike da bacin Rai….

 

Yana Isa ya bude da mukullin dake jikinsa, tana ganinshi ta cafko shi ta cakumi wuyansa tana faman bugun kirjinshi, tana fadin na tsaneka Abbas na tsaneka, ka cuceni , ka rabani da yan’uwana, da iyayena, na biye maka kaci amanata, sai Allah ya saka min,. Bazan yafe maka ba, shidai Yana tsaye Yana ganin ikon Allah runtse idanuwa shi yayi yana ambaton ubangiji, wai yau shine yake auren irin wnn matar wadda Bata da tarbiyyah, Bata San daraajar aureba, A fili ya furta Allah kaine ka jarabceni ya Allah ka bani ikon cin jarabawarka….

A lokacin kuwa ita ta nufi kitchen tana wasa wuka, wai gara ta kashe kanta ma ta huta da wnn bakin cikin…Jin karar wukar ne ya maida hankalinshi ga Abinda yake ji a guje ya karasa ya sameta ta hakinkance tana wasa wukar ta dauka kenan zata aza bisa cikinta, yai saurin cimmata, ya anshe wukar da karfi,ya zabga Mata Mari a kumatu, Nan suka hau kokawa, tana kokarin amsar wukar tana kabani na kashe kaina sai ka huta da jarabata, tunda na zame maka jaraba, ganin ta gama fita hayyacinta yasa ya janyota ta karfi ya jefata cikin daki ya kulle dakin ya dauki khadija, ya kaita can wajen Maryam, sai faman huci yake Maryam na tambayarsa lfy? Amma ya kasa ma magana, sai faman safa da marwa yake a dakin.

Sai da nutsuwarsa ta samu sannan ya dauki wayarsa ya Kira daddy ya shaida masa Abinda rukayyah ke Shirin yi, yace daddy Ina ganin ko za’a kaita ai Mata rukiyya ko tana da wasu mutanen akanta, Amma a gaskiya lamarinta ya Fara bani tsoro, Abu Bai taka Kara ya karya ba, Amma ta dauki zafi ta Hana kanta sakat…daddy shiru yayi don yasan ba wani abinda take dasu, kawai zafin Raine irin na uwarta, in ransu ya baci su maida kansu mahaukata, har illata kansu sukeyi, Amma in haka ne ko Bata gadawa yaranta Abin arxikiba, ya fada a zuciyarsa, dogon ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya ce, kayi min Alhlfarma kayi hakuri, nasan irin hakurin dakakeyi Amma don Allah Kara min wani, gobe in Allah ya kaimu zanzo in sameta zan yi maganin haukanta, kayi hakuri kaji…

Abbas yace Allah ya kaimu..sai ka zo, Amma a zuciyarsa baiyi niyyar barinta ta Kara kwana a gidan ba.

 

Zamanshi yayi Bai Kara komawa wajenta ba, ya rufe gidan ya shiga wanka, ya Dan sake samun nutsuwa, sannan ya kwashe abinda ya faru ya Gaya wa Maryam, tace kayi Kara hakuri Abban mufid jarabawarka kenan kayi kokarin cinyeta kaji …

Gyada Kai kawai yayi haka taita Masa kalamai masu kwantar da hankali, har sai da taga ta kawar Masa da damuwarsa…

Ruky kuwa kokari take ta ballah kofar ta fito bacin ran ya kalleta ya tafi can wajen matarsa ne yasanyata ta tattaro karfin da take dashi ta buga kofar Aiko sai ga kofa a kasa dake Bata karfe bace, ta fito kamar wata zakanyar dake farautar nama…ta nufi wnn tsakanin da ya raba tsakaninta da gidan Maryam, ta nufi wajen a guje…..

 

 

*Muje zuwa*

 

Taku

 

*Ummu Ameer ce* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story&written*

*By*

 

*Ummu Ameer* 💃

 

*Page* 4⃣6⃣

 

 

“”””Tana zuwa wurin ta hau buga wajen tana kazo ka bude ni, wlh ko nai na tayar da hankaiin Yan unguwar Nan gaba daya, bugawa take ba kakkautawa, dama tsakanin da akai musu kofa ce Amma ba karfe ba, Kuma ba’a shiga ko fita ta wajen sai dai a zagaya ta can baya…da ta daddage ta saki karfinta ga kofar sai ga kofar a akasa…

Suna jin karar balla kofar ya tashi a fusace kafin ya iso gareta, ta dauki wani katako ta rafka Masa a goshi, kan kace me jinin ya Fara malala a gurin, Maryam na ganin haka ta zuciya ta nufeta a kufule, Abbas yai saurin fizgota, ya rike ta Yana fadin me zaisa ki tunkari wnn mahaukaciyar so kike ta illata kine, so take Daman ta samu damar illataki tunda ke kika tsole Mata ido…Cike da bacin rai tace ka barni in nuna Mata ba tsoranta nake ba, haka kawai taga ana kyaleta ne, shiyasa take wnn iskancin.

Ganin jinin dake xuba a goshinsa yasa ta Kara zuciya zata koma wajen ruky, ya Kara riko ta, yace me hakane bansanki fa da wnn halin ba, karkice Zaki biyewa wnn karyar…Jin sunan da ya kirata ne yasa ta Kara yunkurin Kara zuba Masa katakon, hannunsa yasa ya fixge katakon ya wurga ta gefe guda, da alama kuwa taji jiki don kasa yinkura tayi ta zube tana rige kwankwaso, Amma bakinta Bai rifu ba, sai binsa take da Allah ya Isa mugu kawai, so kake ka kasheni ka huta ko, to wlh sai na dauki fansar abinda kaimin..

Tazo ta wuce ta gabansu ta shiga ta dauki yarta a gidan tace wlh, ba Wanda zai bacci a gidan nan, in Kuma ka musa mu zuba.ta fada tana jijjiga jiki,kamar farin shigar hauka…

Jan Maryam yayi suka koma wajensu, har sun yi nisa ta jefo musu wnn katakon Allah yasa Bai samesu ba….

A zuciye ya dawo ya fixgo ta Yana fadin ke mahaukaciya ki barmin gidana ynx Nan kafin nai danyen aiki akanki ya fada don bacin rai har karkarwa hannunsa yake, idonsa ya birkice ita kanta sai da ta tsorata da yanayin nasa, tana tsoron karya furta saki, Amma dake zuciyarta ta bushe alokacin sai cewa tayi ba inda zani, Zama daram wlh, ni da Kai mutu ka raba….ya katseta da fadin ki fita nace ai ba da gidan kika zo ba….

Tace wlh ba inda zanje in ma kana tunanin haka to gara ka daina Batawa kanka lokaci…juyawa tayi ta janyo rigarsa ta baya tana wlh fa ba inda zakaje sai dai mu kwana anan dukanmu Amma ba Wanda zai runtsa.. a lokacin 12saura na dare,

Da dai yaga Bata da niyyar fasa haukan Kuma Taki fita a gidan sai ya damkota yana Shirin fitar da ita ta karfi, amma ta tirje Taki motsawa, shi kanshi Yana mamakin wnn karfinta haka shiyasa wani lokacin yake tunanin ko ba ita kadai bace.

Amma duk da haka dake karfin Namiji ba daya da mace ba, sai da yayi nasarar janta zuwa bakin gate ya bude kofar kenan Yana Shirin wurgata wajen sai ga makocinsu ya fito sbd Jin hayaniyar dake tashi tun dazu a gidan makocin naci, shiyasa ya fito sbd hakkin makotaka.

Yace subhanallahi Dr .lfy me ke faruwa haka? Shi bacin rai ma da kunyar Abin kunyar da ta janyo Masa ya Hana shi cewa komai ita Kuma sai ta fara kuka tana fadin kagan shi Nan wlh ba abinda yake min sai musgunawa da rashin Adalchi tsakaninmu, yayi ta wulakantani a gaban matarsa, ya raba ni da iyayena na biye Masa sannan Kuma ynx yake son juya baya, kawai don na nemi in kwaci yancina a gidan, tunda na shigo gidannan kullum da bacin rai nake kwana, in nai Masa magana yace in bazan iyaba, in tafi ai ba rikeni yayi ba, yaje yasa an toshe min mahaifa, ya bar matarsa tana haihuwa ni baison hada zuriya Dani….

*Kaji sharri irin na ruky*

Makocin najin haka yace ya Isa haka baiwar Allah, kiyi hakuri ki koma cikin gidanki, zamuyi magana da maigidan naki…tataso Tai saurin komawa ciki…ba inda ta dosa sai bakin kofar data karya tana fadin to bakar munafuka fito, maganin naki baici ba, Ina Nan daran Zama ynx na Fara, ni da shi mutu ka raba, ba inda zanje sai dai ke ki fita ki barni, so kike in fita in bar Miki shi, dama hakan kike so, to ki canza batu don Abu kazakazanki Yar masu bin bokaye, haka taita shirmenta Amma Maryam Bata tanka Mata ba, Sanya key tayi a kofar ta rufe tana ambaton ubangiji ya yaye musu wnn bala’in….

 

A can kuwa Abbas kwashe duk Abinda ya faru yayi ya Gaya masa, Kuma ya tausaya Masa don yasan halinsu na mugun kishi, hakuri ya bashi akan don Allah Kar ka yanke hukaunci cikin bacin rai ka jira mahaifinta ya zo goben tukun Kar yace baka ji maganarsa ba, Abbas yace na gaji da halinta ne wlh, shiyasa naso in yarda kwallon mangoro in huta da kuda, makocin yace kayi hakuri munsan kanayi ka Bata dama mahaifinta yazo goben.

Abbas yai Masa sallama ya koma ciki, tana Jin shi ya taho Tai saurin shiga daya dakin da Bata balla kofar ba, ko kallon inda take baiyi ba, ya wuce wajen uwargidansa, ya sameta itama a cikin damuwa na abinda ya faru, ya Bata hkauri akan ta yafe masa shi ya jefa su cikin wnn halin, har Yana xubda hawaye, tasowa tayi tazo kusa da shi tana fadin don Allah ka daina zubda hawayenka akan wnn matar kayi hakuri da jarabtar da Allah yayi ma, kaita addu’a Allah ya kawar d dikkan sharrin dake cikinsa.

Haka dai taita lallashinsa daga bisani, yai treating din wajen, da ta fasa Masa,kusan a zaune kuwa suka kwana sbd Yana tsoron kar ta shigo musu da wani makamin, shiyasa ko runtsawa Bai yi ba sai da har garin Allah ya waye….

 

 

Muje zuwa

 

Taku

*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story &written*

 

*By*

*Ummu Ameer*💃

 

 

*Page*4⃣7⃣

 

 

“”””Washe gari, Ruky tashi tayi da nadamar Abinda ta aikata, kamar ba ita Tai hauka ba jiya, a zahiri in ka ganta bazai Kai tunanin cewa zata iya aikata abinda take yi ba, Nan kuwa zuciyar kafirai gareta, tashi tayi ta hau gyaran gidanta da kanta duk ta gyara abinda ta hargitsa na fashewar Kuma ta kwashe ta xubar ,ta zage tukuru tana aikin gidan ko don taji daddyn nata zaizo ne oho!

 

Har wajen karfe 9na safe Abbas Bai shigo ba, hakan kuwa Bai Mata dadi ba, anata wautar…

Da ta ji shiru sai ta dauki waya ta kirashi Bai dauka ba, har ta gaji ta hakaura, taci gaba da aikinta, kamar gaske, bayan ta gyara ko Ina tai wankanta Tai ma Khadija.

 

Bai shigo gidan ba, sai da ya tabbatar da isowar mahaifinta wajen karfe 10:30 na safe, ko da daddyn ya Isa gidan shima yayi mamakin ganinta kamar ba ita akace ta aikata wani abinba, tai murna sosai da ganin mahaifinta, sai rawar jiki take wajen kawo Masa abubuwan ci da na Sha, shi kuwa sai kallon ta yake da mamaki, har Yana zargin ko dai ba gaskiya ya fada Masa ba, Abbas din, Yana Nan cike da mamakinta sai ga Abbas din ya shigo, ya tsugunna ya gaisheshi ya masa ya hanya.

Shima kanshi yayi mamakin yadda yaga rukyn, kamar ba ita Tai rashin mutumci jiya ba, gashi yaga ko Ina tsaf ta gyara gidan kamar ba Abinda ya faru….haka dai ya samu wuri ya zauna a kasan carpet din itama tazo ta zauna ta daya gefen, tana satar kallon shi ta kasa-kasa, kamar wata mumina.

Bayan shiru ya ratsa na Dan wani lokaci, daddy ya Fara magana yace

Rukayyah bana Jin dadin Abinda kike aikatawa a gidan mijinki, kinki kwanatar da hankalinki ki zauna lfy, kullu yaumin cikin hayaniya, haba ban tsammanin haka daga gareki ba, sbd ada, na sanki da kyamatar irin wnn halin, Amma gashi ynz kin tsunduma kanki tsundum a ciki, nasiha yai Mata Mai ratsa jiki, daga karshe yace Kuma matukar ta sake aikata haka zai zare hannunsa akanta tunda ya fahimci taurin Kai ne da ita.

Itakuwa harda fashewa da kuka Mai shiga rai tazo ta tsuguuna gaban shi tana Mai neman ya yafe Mata bazata Kara yi, ba, shi dai Abbas binta yai da kallon mamaki.

Shima Nan ta zo gabansa akan ya yafe Mata bazata sake yin makamncin haka ba.

Shiru yai Bai amsa Mata ba, ganin idon daddy akansa yasa yace Allah ya kiyaye gaba. Har da cewa ngd baby!

Shikuwa fakar ido yayi ya wullah mata harara, don har ynx haushinta yake ji, Koda ma sun ci gaba, da Zama baya Jin zai Kara sakin jiki da ita, girmanta da kimarta duk babu su wajensa.

Daddy kuwa yaji dadin yadda suka sulhunta kansu, da Kuma nadamar da tayi, yai musu sallama ya tafi, tare da Addu’ar samun zaman lfy.

Har waje suka rakashi, bayan sun shigo taga Yana kokarin komawa wajen Maryam, hannunsa ta riko, ta sakalo shi ta hade da nata, tana cewa don Allah ka gafarta min, wlh nayi nadama, dama bacin Raine Kuma na kasa controlling dinshi, Amma ynx na gane kuskurena, kayi hakuri ka Kara bani wata damar…plxxxxx ta fada har da wani kwantar da Kai a kafadnshi, shi kuwa da dai ya tuna Abinda tayi jiya,sai ya fixge hannunsa yayi tafiyarshi ciki, ya barta Nan a tsaye.

 

Haka ta dauki jiki ta koma ciki, jiki ba kwari, zuciyarta na Gaya Mata cewa tayaya za ai ki aikata irin wnn mummunar Abin, sannan ki yi tunanin samun kansa ta sauki, ai sai kin zage..

Wata dabara ce ta fado Mata, ta dauko mayafinta ta shiga wajen Maryam, taita sallama taji Shiru sai ga Abbas din ya fito, yace lfy?
Murmushi tayi tace nazo na bawa Maryam hakuri akan abinda ya faru…

Wani kallo ya bita da shi na raini, ya Koma ciki, ya fada Mata wai rukayyah ce tazo Baki hakuri… ita kanta tayi mamaki da Jin hakan, sai Kuma ta Dan yi dummm na wani lokaci, sai ta yunkura ta tashi, yace Ina Zaki?tace zanje wajenta mana.

Yace kyaleta kawai…tace in mun kayi haka bamu kyauta ba, tunda har ta gane kurenta ai sai muyi mata afuwa, mu zamo masu saurin yafiya, tunda itama har tayi saurin nadama, kaima ina rokon Alfarma ka yafe Mata, shiru yayi na wasu lokuta, a zuciyarsa yace lallai Maryam na da kyakkyawan hali, na rashin rike mutum a ranta, tabbas shine shaida domin kuwa ko akansa ya Isa ya gane wnn kyakkywan halin nata.

Tashi tayi ta fita, ta sameta zaune akan kujera, yau ita ne ta gaisheta, bayan gaisuwar tace nazo ne in Baki hakuri akan Abinda ya faru jiya, wlh bacin Raine da sharrin shaidan,kiyi hakuri insha Allahu haka bazai sake faruwa ba…

Maryam tace lah ba komai, Allah ya yafe Mana Baki daya, tace Ameen.

Daga bisani sukai sallama, ta koma wajenta.

Koda Maryam ta shiga daki ta Gaya Masa yadda sukai, shidai kawai jikinshi Bai bashi ba, Yana tunanin ko wani makirci take so ta kullah, Amma sai ya barshi a zuciyarshi, yace Allah ya kyauta, yai Mata sallama ya wuce office.

To wnn tuban da ruky tayi ko me dorewane???

 

Taku

*Ummu Ameer*💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story&written*

 

*By*

 

*Ummu Ameer*💃

*Page* 4⃣8⃣

 

 

“”””Bayan kwana 2 da faruwar haka, rukayya ta karbi girki, duk da har yanzu ba wani sakewa da ita yai ba, ita kuwa ta dage wajen ganin ta janyo ra’ayinsa, ya yafe Mata, Amma Ina yadda take tunanin Abin ba haka bane, wnn karon Abbas ya dau zafi..

 

Kwata-kwata ya canza Mata ita kanta da ta San haka ne zai biyo baya da batai ba…a haka yai kwana 2 a gidan Amma ba wani walwala ko sakin fuska daga gareshi.

 

********. *********

Bayan 2wks da faruwar hakan har ynx zaman nasu ba dadi…ba Abinda batai Masa ba ganin ya sauko Amma ina.

 

To tsakanin miji da Mata sai Allah, sai da ruky tasan yadda tayi amfani da kissa yaudara ta janyo hankalinshi ya sauko daga fushin da yake da ita. Sun shirya an bude sabuwar rayuwa.

Maryam kuwa na can ta dage wajen Kara gyara kanta fiye da na da, ba yadda baiyi ba, a koma ruwa Taki yadda, ta ci burin sai tayi arba,’in tunda ynx ba ita kadai bace, har fushi yake da ita, sai dai ta kwantar Mai da hankali ta wani fannin.

 

Su ruky kuwa ynx ta dage wajen kokarin ganin tana danne wnn zaxxafan kishin, shiyasa kwana 2 shiru..gashi ynx ba kwayar Hana shi zuwa wajen Maryam, sbd akwai wata Rana Yana neman wata takarda ya gano shi, ko da ya gani daukewa yayi ya zubar, sannan yayi tirrr da halinta ya gane nufinta akan kwayar..Kuma yai shiru Bai Gaya Mata ba.

Shiyasa ya Sanya ido akan duk abinda take yi a gidan, Kuma ya daina Shan duk wani drinks da zata hada da kanta. Tun daga lokacin ta Sha jinin jikinta ta San tabbas ya gano wani abin,,,

 

Mummy kuwa tun da taji labarin wai ana neman rukayya, tayi yaji…sai jikinta yai sanyi, ta Fara ganin kuskuren zare hannunta da tayi a kan diyarta, duk da cewa itama ta watsa mata kasa a ido, Amma duk da haka ya kamata ta San halin da yarta take ciki.

Kanwar rukyn ta tura gidan ta je ta bugi cikin rukyn ta fada Mata damuwarta…

Aisha ta shirya ta tafi gidan rukayyah, rukyn kuwa ba karamin dadi taji ba da ganin yar’uwarta, sbd tana son zuwa Amma mommy ta Hana su.

Sai dai ba wani Abin aje a fada da Aisha ta gani ko taji daga gareta, ba yadda Aisha batayi ba, ganin taji damuwar Amma Taki fadan komai, tana tsoron kar ta guntule Mata igiyar aurenta.

A wnn lokacin ne Kuma yai dai-dai da arba’in din Maryam yara sunyi kyau gasu da kibarsu Abin sha’wa ga kamar da suke sai ka kula sosai zaka iya gane su…

Ranar da ya Kama arba’in din kuwa kada kuso kuga gyara ta ko Ina wajen maryam, ansha Jan kunshi ga kitso an Mata shi ya zubo gadon bayanta, ga wani fresh da fatarta ta Kara sai sheki take ga taushi kamar fatar jarirai, ga Abubuwan saukar da ni’ima ta tsumu sosai,ita kanta tasan ta gama hadewa.

Ranar kuwa yai dai dai da ranar da zata karbi girki, hatta da Abincin da aka shirya Masa na musamman ne, gidan ma ya Sha gyara na musamman, bed room dinsu kuwa yasha turaruka masu sanyaya rai da saukar da nutsuwa, an Sanya new sheet, tare da fesheshi da turarukan qamshi.

Wasu kananan Kaya ta Sanya wanda suka amshi jikinta sukai Mata das, kamar don ita akai kayan,Riga da wandon ne rigar ja, sai wandon bluei Wanda yasha adon stones ta gefe amma Bai sauko kasa ba, hakan ya Kara bayyanar da kyawun kunshin kafarta, ta saki gashinta har bayanta, ta Sanya sarka Mai beads Mai ratsin ja da blue haka ma Abin hannunta, ansha make up Wanda yai dai dai da tsarin shigar da tayi, in ka ganta ma bazakai tunanin ta haifo yara haka ba.ga wasu shedanun turaruka da ta shafa kala-kala bazaka iya tantance ma qamshin ba,
Haka ma madarar turare shafe ko Ina tayi na jikinta da shi tun kafin ta Sanya kayan..

 

Ruky kuwa dama kamar ita ta haihu tana irgen kwanakin, ga qamshi girki da na gida ya budade ta, tun daga lokacin ta kasa samun nutsuwa, har shiga gidan tayi ta ga irin kwalliyar da tayi, lokacin Abbas ya fita masallaci ta saci kafa ta shiga, ta fake da cewa wai tazo Mata murna, lokacin tana daki Maryam har zata fito ta koma ta Sanya xumbulelen hijabi baka iya ganin me ke jikinta, sai kunshin da kwalliyar fuska, hakan kuwa ya sosa ran ruky, tace don bakin Hali ma bazata Bari a ga me ta Sanya ba, ganin hakan yasa tace zan koma. Maryam Tai Mata godiya ta rakata kofar fita.

Ruky kuwa ta dawo da takaicin rashin ganin shigar da Maryam tayi.

 

Shi kuwa gogan tunda ya kyallara ido akanta ya gagara samun nutsuwa sai wani Nan -nan yake da ita kamar wata sabuwar Amarya, Yana manne da ita Yana shakar qamshin da ya gama rikirkita shi, A ranar dai komai santin shi ya dinga yi…

A Daren ranar kuwa abin ba magana domin kuwa jinta yayi kamar wata sabuwar Amarya, yasa mata Albarka yafi akirga.

Ruky kuwa Abin ya tashi kasa bacci Tai a wnn Daren, har labe tayi ko zataji wani Abin Amma ba Abinda ta iya ji.

Dan wahala ko bacci kasa yi tayi, kishin ya tashi ta kasa samun nutsuwa,,,,,

Washe gari kuwa Bai shiga wajen ruky ba da wuri, Maryam ta gama sukurkuta shi, sai da zai fita office ne ya biya, ya sameta ta cika fam gaisuwar ma Bai Samu ba, yai ma Khadija wasa wacce a lokacin tana dabo koyon tafiya, Sam Bai damu da rashin kulashin da batai ba, har yazo zai fita tace Ina da magana da kai, yace tin shigowa ta, Baki tashi yi min magana ba, sai ynx da nazo fita ki Bari idan na dawo mayi maganar, tace Sam Bata yarda ba, ynx take son suyi maganar,,,

Ganin ta hakikance tana Bata Masa lokaci, gashi ya Riga ya makara yau, kawai yasa Kai yai tafiyarshi, ya barta Nan tsaye da bakin cikin rashin saurarrarta, mayafi tai saurin daukowa ta rufe gidan ta bishi har bakin motar Yana Shirin tayar da ita, tace tunda kaki saurarata, muje ka saukeni a gida bana jin dadi, banson kadaici yace a’a ba inda zakije ba ke kike da ikon fita aduk lokacin da kika so ba, ki Bari sai na Baki izini tukun, ya fada tare da Shirin Jan motar tace nace maka bani da lfy, Amma bazaka iya tsayawa ka tambayi abinda ke damuna ba, kake Shirin tafiya, tunda ba damuwar ka bace ko?

Tace tun jiya ban yi bacci ba, sbd zazzabi da ciwon Kai ….yace Allah ya sawwake zan taho Miki da magani in na dawo, ya tashi motar ya tafi, ta tsaya Nan gurin da takaicin rashin samun nasarar Abinda taso yi, wai ita a dole sai ta ja ra’ayinsa sun dauki wani lokaci, don hakan ya sosa ran Maryam, ko ta bishi su fita, don tasan matukar Tai hakan Maryam bazata ji dadi ba, tunda tasan girkinta ne, shi Kuma kamar yasan kudurinta, shiyasa baya biye Mata.

Haka dai ta koma gidan kafa ba kwari, Amma duk ta bi ta damu kanta, tunda ya fita take doka Masa Kira wai zazzabin ya dameta, Bata iya Abu kaza, tun Yana dauka har ya gaji ya daina daukar ita kuwa Bata fasa Kiran ba.

Shi kuwa tunda yaje office ba abinda yake tunani sai abinda ya wakana a Daren jiya tsakanin shi da maryam, jinta yake sosai a ransa, har Allah Allah yake ya koma gidan ….itama sai turo Masa zafafan text take wadanda suke Kara rikirkita shi.

Hakane ya Sanya ya koma gida da wuri..Koda ruky taga dawowarsa murna taitayi ai ya dawo ne sbd rashin lafiyarta, Yana shigowa wajen rukyn yaje da murnarta ta tare shi, ansha make-up an matse cikin kananan Kaya, sai wani kirsa take yi, Koda ya ganta a zuciyarsa yace to wacce Bata lfy ce da irin wnn iyayin, shikuwa ko Zama ma bashi da niyyar yi, ya tambayi yarinyarsa tace tana bacci, yace Bari na wuce wlh a gajiye na dawo zanje na Dan huta…a take annurin fuskarta ya dauke Tai kicin-kicin da fuska ya Mika Mata ledar magungunan yace sai anjima, a fusace tace Abban Khadija ba kace in ka dawo zamuyi magana ba, yace kinji abinda nace a gajiye na dawo, why not mu Bari gobe in kin karbi girki sai mu tattauna, tace Sam Bata yarda ba, ganin tana Bata Masa lokaci yasa shi ficewarsa, tace wlh bazan yarda ba, ita in tana da matsalar baka tsayawa ka saurareta ne, sai ni da ban Isa ba, sau nawa kake shiga Kai zamanka ran girkina Amma ynz ni zaka kasa sauraran nawa izunin, har waje ta leko tana Abban Khadija! Sai kwala Masa Kira take Bai saurareta ba, ya shige ya gane tsaf kishin ne ya tashi, yace ai Daman Mai Hali Bai canza shi…

Ko da ya shiga ciki a falo ya taddasu suna wasa da yaranta, har da ita, suna wasan buya, sai a rufe ma daya ido in ya Kama mutum to yaci, a haka ya samesu wasan kuwa ya birgeshi, don Basu ma San ya shigo ba, sai da suka ji tafi raf-raf, sbd itama ta buya a bayan kujera, sai suka Fara ihun ganin Abbansu suna daddy oyoyoh, shi kuma ya hau daukan kowa daya bayan daya, Yana ajewa sai akazo kan madam, yace kema taho in daga ki, ta noke Kai Tai Masa nuni da yaran, tunda idonsa ya Kai kanta ya kasa saukeshi, yau shigar Riga da siket na lace tayi Tai daurin dankwali Wanda ya zauna daram kamar gwaggwaro, tayi kyau nesa ba kusa ba,Tai Masa sannu da zuwa ta amshi jakar hannunsa ta Kai daki shima Yana biye da ita a baya Yana yaba irin kyawun surarta, Yana godiya ga Allah da yabashi mace kamar Maryam….ruky kuwa idonta akai tana lekowa ta wata Yar kofa….

Har sai da taga shigarsu daki ta dawo ta zauna tana ta sauke ajiyar zauciya kamar zata hadiyeta, wayarta ta dauka ta Kira no shi alokacin har ya shiga wanka, Koda maryam taga ruky ce sai ta dauka, tace ya shiga wanka Tsaki ruky Tai ta katse wayar tana Allah Allah ya fito ta Kara kiranshi….

 

To ko Kiran me take Masa oho….???

 

 

Muje zuwa

*Taku*

*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story & written*

 

*By*

 

*Ummu Ameer* 💃

 

*Page* 4⃣9⃣

 

 

 

 

 

“””””Kiranshi take ba kakkautawa shi Kuma baya tare da wayar suna can dining suna cin Abinci, baiji Kiran ba, Kuma Yana fitowa daga wankan Maryam ta Gaya Masa, yace zai kira, sai Kuma ya mance shaf da zancen wayar.

Sai knocking suka ji anayi, ya tashi ya je ya bude, Yar aikinta ta turo da Bata wuce shekara 11ba wai yazo inji Rukayyah yace kije gani Nan zuwa.sai da ta Aiko sau 2 kafin yaje.

Komawa yayi ya gayawa Maryam zai je yaji ko meye, tace toh!

yana Isa ya sameta tayi wani Afujajan lokaci daya..duk ta sanyawa kanta damuwa tayi wani iri kamar wacce ta shekara tana jinya, dama ita jiki ba jiki ba, ga rashin kwantar da hankali, shima kanshi daya karemata kalloh sai da ya tausaya mata, Yana shiga ta fashe da kuka wai ka kaini asibiti numfashina ne yake sama-sama, kamar zai dauke, yace tun yaushe?tace tun bayan tafiyarka, yace ta ta shirya su tafi Asibitin.

Komawa yai wajen Maryam ya shaida Mata zai kaita asibiti Bata da lfy,tace Allah ya sawwake ,sai kun dawo!

Ya shirya ya fito da motar tare suka tafi da Yar aikin ta rike Mata yarinyar, suka wuce Asibitin da take zuwa.

Kasancewar Asibitin bashi da Wanda ya sani shiyasa suka dauki lokaci kafin a dubasu, ko da aka dubata sun gano jininta ne ya hau sosai har Dr, na tambayarta me ta Sanya a rai har ya janyo Mata jininta yai irin wnn hawan gashi ba wani shekaru ne da ita masu yawa ba, fada yai Mata akan ta rage tunane-tunane, shima yai wa Abbas din fada akan a dinga kiyayewa don Allah, sannan suka saya magunguna suka kama hanyar gida, shima a hanya har nasiha yai Mata akan ta rage Sanya wa kanta damuwa, ba komai ne yake Zama damuwa a rayuwa ba, Amma ke Abu Bai Kai ya kawo ba, ki maida shi gagarumi a wajenki, ki daina plx, ki dinga yin hakuri da rayuwa ki daina wahalar da zuciyarki.

Tace duk abinda ya sameni Abbas kaine, kullum kokarin cuxguna min kake, yace a’a kike dai cuxguna ma kanki, duk yadda zanyi in kaucewa abinda zai shiga hakkinki Ina yi, Amma bakya gani…

 

Tace ai shikenan Basu koma gida ba, sai 3:30 na dare, Koda suka Isa ma Bata barshi ya koma can ba, sai wani Nishi take tana langabewa, ga patient, hakan yasa ya bita gidan yaita kwantar Mata da hankali, da Kuma sanyata Tasha magungunan, sannan yai Mata sai da safe, a lokacin har 4na asuba tayi.

Itakuwa Yana fita ta tashi tana murnar yau tayi nasarar ruguxa musu wnn daren, Daman a zahiri rashin lfyr karya take, sai Kuma gashi an aunata jini ya hau, tace Daman indai a irin wnn lokacin ne, zan dinga auna b.p ai wataran ma sai zuciyar ta buga..sbd ba abinda yake tayar Mata da hankali kamar Daren da ba na girkinta ba, tana dorawa kanta wahala….

Tace yau nai wining, Maryam you missed Dix night…ta fada tana murmushin mugunta.

Koda ya Isa Daman ya rufe gidan ta baya, shiyasa ma Bai tsaya knocking ba, ya bude ya shiga, har an fara Kiran assalatu, Yana shiga dakin ya tarar tayi nisa a bacci, Bai tasheta ba, ya shigo toilet yai wanka, sbd shi ka’ida ne inda ya dawo daga asibiti, Wala inda yake aiki ko wani sai ya yi wanka yake samun nutsuwa ya dauro Alwala ya Fara gabatar da nafilfili, sannan daga bisani ya wuce masallaci.

Itako tin shigowarshi tana ji, Tai pretend kamar tana bacci..

Yana fita ta tashi Tai wankanta Tai Alwala, tazo Tai kwalliyar cikin doguwar Riga na material , ta shiga gudanar da Ayyukan data Saba yi..Koda ya dawo Tai Masa sannu da zuwa yace shine kikai baccin ki Baki jira na dawo ba, tace na jiraka kasan bacci barawo bansan sanda ya saceni ba, Bata nuna Masa damuwarta ba, na Daren da ya Kai basu dawo ba, har ma tanbayarsa tayi ya Mai jikin yace da sauki, yace b.p dinta tane yai high, tace Allah ya sawwake…

Tace in na Bari ya gane Raina ya baci,. Ai ta samu abinda take so, don tasan da gayya ta bijiro da fitar, tuni ta gane nufinta.

Shiko sai cizon yatsa yake na missing din wnn Daren gashi yau a gidan ruky yake, zuwa lokacin kuwa yara tuni sun tashi daga bacci, itako ruky ta sanya idanuwa da kunne taji bala’in maryam, kamar yadda ita ta Saba, amma shiru kake ji, Abin Bai Mata dadi ba, ba haka taso ba, da safe ma ya shiga ya duba ya jikin tana Jin shigowarsa ta Kara wani langabew tana Nishi sama-sama, yai Mata sannu sannan yace tayi breakfast ta Sha magungunan tace tohh!

Komawa yayi breakfasat ya shirya fita office, har kofar ta rakashi kamar yadda ta Saba, har zai tafi ya dawo yai Mata rada a kunne, duk yadda Nima naso inji banji ba…sai dariya kawai Naga tayi shikuma ya kanne Mata ido, tai Masa Allah ya kiyaye!
Yace ameen my sweet wify..

Ta koma cike da nishadi a ranta,da alama taji dadin radar da yai mata.

 

Shima zuciyarsa fal da nishadi, har yayi nisa ya mance Bai shiga yai wa Yar rigima, sallama ba, sai kawai ya dauki waya ya kirata ta yace Tai hakuri ya makara shiyasa Bai shigo ba..bataji Dadi ba Amma ba yadda ta iya tunda yau itace ma da girki, tace Allah tsare sai ka dawo.yace Ameen.

 

Duk da ba yadda taso abin ya kasance ba, Amma duk da haka taji Dadi sosai, wnn ne yasa ta ware tana cike da farinciki a ranta, ga shi Kuma yau oga nata ne!

Hakane yasa ta zage tana ta shirye-shiryen tarbarsa, don itama yau shiri take na musamman tayi koyi da Maryam, an gama shiryawa tsaf ana jiran dawowar yallabai…

 

 

 

Muje

*By*

*Immu Ameer* 💃

🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story & written*

 

*By*

*Ummu Ameer* 💃

 

 

*Page* 5⃣0⃣

 

 

“””””Sai bayan magriba ya dawo ya shiga wajen Maryam daga bisani ya dawo gidan ruky, da fara’arta ta tarbeshi, yace ya jikin tace da sauki yace kin Sha maganin tace eh!

 

Bayan ya gudanar da duk abinda ya Saba yi, ta kawo shi dining, ya Dan tsafura Abincin yace ta kawo Masa tea yasha, Yana Sha suna taba Hira, Khadija na hannunsa ita Kuma sai sai daukansu take pictures , sbd ta samu ta Dora akan dp dinsa don Maryam ta gani, ta zata tata kawai ake wa haka…

 

A wnn ranar dae sun kasance cikin walwala da farinciki dama ita ke Bata zaman, sai ana zaman lfy ta bujuro da rigimarta,

Amma a zahirin gaskiya hankalin shi na kan Maryam duk kewarta ta dameshi, bare da yaje sallama kusan kasa controlling din kansa yayi, haka Nan ya dawo da matsanacin kewarta…

*********** **********

*UNFORGATABLE DAY*😭

 

 

Washe gari ma sun tashi cikin farinciki, ya gama duk Abinda zaiyi ya mata sallama yace zai fita daga nan zai Kai Maryam gida yawon arba’in

Zare idanuwa tayi tace what,?
Yace yes!

Tace wlh bazai yiwu ba, ta Bari sai ranar girkinta yace sbd me, tace abd yau girkina ne ko ka manta ne in tunasar da Kai?

Yace Ina sane, yace Amma rukayyah wlh kin faye son kanki da yawa, kin manta Randa na kaiki Asibiti muka kusan kwana acan, amma Maryam ko daga Kai batai ba, Amma shine kike fadin haka…

Tace wnn ai larura ne, kaima gashi ka fada asibiti…ita kuwa fitar nishadi ne, sbd haka kawai ta bari ranar girkinta, ganin ta hakikance da gaske take yace ke Bari kiji, wlh ba abinda zai Hana ni fita da ita, tace ni Kuma nace baka Isa ba, yace to zamuga wai zai nasara, yasa kafa zai fita Tasha gabansa tace, sai ka canza magana zaka fita a gidannan, ganin haka yasa shi ya wancakalar da ita gefe yace Allah ya wadan wnn halin naki,, nonsense!

Kuka ta Fara Yi da karfi kamar karamar yarinyar da aka duka, tana wlh indai ka fita da ita ban yafe ba, Allah ya Isa!

Tana gani suka fitan, Kuma Bata fasa kukan ba, har suka fice daga gidan, sai da tayi Mai isarsa tukun sannan ta tashi ta shiga, kamar ta Kira no mummy Kuma sai ta fasa, kawai sai ta Kira kanwarta, Aisha tazo gidan, ta Gaya Mata abinda ya faru, dake kanwar ma ta fita zafi akan rukyn sai ta shiga zugata wai wlh an Raina Miki hankali, in Banda ma kin maida kanki wata iri har yaushe zasu Fara Miki haka, ai wlh Anty ruky idan nice Basu Isa sumin haka, kece ma da kika nace masa, sai da mummy taso ta hadaki da Dan gidan Alh.dala, inda Zaki je kiyi abinda kika ga dama Amma kika ki, kika nacewa wnn da ba shi da wani arxikin azo a gani, ni ki tsaya kiga Wanda zan kawo a matsayin miji…ruky tace ya Isa haka Nan ke kanki kinsan Ina son Abbas kuma son da nake masa ne yasa nake zaune da shi, Kuma ni a gaskiya bazan iya rabuwa da shi ba, sbd mijin da kowacce mace zata so mallaka ne , ga kulawa, ga kyautatawa iya gwargwado gashi ya iya soyayyah, matarsa ce kawai take Mana katsalandan, sbd haka wlh nasha Alwashin sai ta bar gidan Nan..😳

 

 

Haka dai yar’uwarta taita zugata har tana cewa in suka dawo kizo mu shiga muyi Mata dukan tsiya muga uban da zai tsaya Mata shegiya kawai..ruky tace ke so kike ya koreni kenan,ki dai kawo wata shawarar…

Nan sukai ta saka wancen kunce wancen, har bayan magriba shiru basu dawo ba, itama Maryam duk ta damu Kar ya jawo matsala tunda ba girkinta bane, data Kira shi sai yace wlh abokinsa ne yaxo daga ibadan zai kaishi masauki sai ya dawo, yace kinsan Kuma an Dade ba’a hadu ba, muna Nan muna ta kwasar hira.

Tace to ka dai hanzarta don Allah kasan yadda muka barota a gidan.yace insha Allah zan taho ynx tace Allah ya tsare hanya…

Acan kuwa ruky ranta ya gama baci, tun tana sa ran karfe 7 har 8 tayi ga kuma 9…

Aisha tace kawai ki debo kayanki kizo mu tafi, ki barmasa gidansa, yaga kin nace Masa shi yasa yake wahal dake, ruky tace ba inda zani, wato ta samu ma Abinda take so,ai so take na bar Mata gidan, ni kuma Zama daram, ba inda zani…

Aisha tace ai shikenan Kinga Zaki iya ne….wlh da nice …hmmmmm ta girgiza Kai Tai kwafa da sai sun gane kurensu…haka suka zuba idanuwa suna jiran dawowarsu, Kuma Aisha ta Hana ta buga Masa waya, wai ai shi ya kamata ya nemeta..

Karfe 9:30 na dare suka iso, suna ganin haka Aisha tace wlh ko barazana ce ki Masa kice tafiya zakiyi, sai ta bi shawarar ta, suka shirya Kaya a akwati Yana shigowa tace abinda kake so kenan yau zan bar maka gidanka, yace me yayi zafi haka, ya Kai dubansa ga Aisha wacce sai jifanshi take da harara, sai yai maza ya fita ya rufe kofar don Kar ta fito, tana ganin haka ta Fara bubbugawa ita da yar’uwarta da dai suka fuskanta baya wurin sai ta zagaya ta dauki jug na glass ta jefa ta wajen Maryam tana fadin wlh in baka bude min ba, sai na yi muku danyen aiki, tana fada tana Kara jefa kofunan glass, su Maryam suna neman hanyar kaucewa jifan nata, Aiko tana jefo na karshen saura kiris ya fada kan mufid…Abbas na ganin haka ya fita bangaren a guje cikin matsanancin bacin ran da Bai misaltuwa, ita kanta Maryam sai da ta tsorata da ganin yanayinsa, ya bude kofar ya shiga a fusace zai zabga Mata Mari kenan Aisha tace kul wlh kasake ka tabamin yar’uwa sai mun kulleka jaka aka maka? Ruky kuwa ta dauki wani kofin zata kwala Masa yai saurin bige hannun ya janyota yace ki barmin gidana ynx nan,tirjewa tayi tace ba inda zani ta fada da karaji, wlh ba inda zani fita, ganin ta hakikance har kanwar na fadin ki bar Masa gidan meye acikin gidan. .tace bazan fita ba….

Aiko sai cewa yayi kije na sake k…Bai karasa fada ba, tai wata irin Kara tare da ashariya kan ubancan ni ka saka ? Hahhhhhhh Ashe yau za ai gawa uku a gidan nan, ta fada tare da wullar da dankawalinta ta ruga kitchen a guje da zummar dauko wuka…tana fadin wlh tunda ka sakeni babu wata Yar iskar da ta Isa ta zauna a gidan Nan wlh sai na kasheka na kashe kaina sannan… ..Maryam kuwa na can kafafuwa suna rawa 😂Jin ance za ai gawa uku…shi kuwa tana shiga kitchen din yai saurin kulle gidan ya koma ya cewa Maryam ta shiga daki karsu fito, zai San Abin yi…tace mun shiga uku Abban mufid wata irin mace ka kwaso Mana ta fada cikin tashin hankali, shi dai sai cewa yake kiyi hakuri komai yaxo karshe, ki kwantar da hankalinki karki fito kinji, tace Abban mufid don Allah karka fita karta kashe min Kai ta fada tana kuka ta riko shi, yace ba abinda zai sameni ki koma kawai, Yana shiga ya sameta da wukar a hannu ta dumfaro shi gadan-gadan, yai saurin rike hannunta suka hau kokawa tana wlh tunda ka sake ni sai na kashe ka,ka rabani da kowa bani da kowa sai Kai sannan kace ka sake Nan ta Kara wani yinkurin…Maryam dake jiyo Abinda ke faruwa jin dif anyi shiru yasa ta kurma ihu Wayyoh Allah ta kasheshi …….

 

To Nima dai hannuna karkarwar yake, tashin hankali ya Hana ni karasawa…ku biyoni don Jin yadda ta kasance….

 

 

*By*

*Ummu Ameer*💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Story & written*

 

*By*

*Ummu Ameer* 💃

 

*Page* 5⃣1⃣

 

 

“”””” Shirun da Maryam taji shiya tabbatar Mata da cewa lallai ta kashe shi ko Tai Masa wata illar, kuka ta dinga yi ta nufi kofar fita,duk da taji a kulle take, Amma tana gwada sa’ar ta ko Allah zai sa ta bude….Amma Ina ko alama, haka dai taita kuka tana Allah ya kareshi daga sharrin wnn mahaukaciyar matar..Allah yasa ba wani abin Tai Masa ba.

Ganin haka yasa baba sa’a (Mai taya ta renon su Hassan) ta kamota ta zaunar da ita tana lallashinta, tace Haj. Kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki, insha Allah ba Abinda zai sameshi…tace Allah yasa…Bata rufe Baki ba kawai sai ganin ruky sukai akansu kamar Aljana Maryam na ganinta ta tashi zata gudu sbd Bata da maraba da mahaukaciya
Kai a bude ta barbaza gashi, kafar duk tayi Kura daga ita sai vest iya cibi.. da wando..Maryam daga nesa da ita, take fadin me kikai wa mijinah?, Ina kika kaimin shi…?ruky wani banzan kalloh Tai Mata ta dumfareta a fusace wai saita Gaya Mata dalilin daya sa, ta shiga tsakaninsu da Abbas har ya sake ta, don tasan ba yin kansa bane ita take haddasa duk Abinda yake faruwa…Maryam tace kije na barki da Allah Kuma in nice na zalunceki Allah ya saka Miki, dama alokacin ba komai a hannun rukyn, Maryam na gama fadin haka ruky tace haka kika ce? Sai kuma ta kwasa a guje kamar wadda Tai mantuwa taje dauko abinda ta manta, ita da baba sa’a suka bita da kalloh,suna mamakin wai ya akayi ma ta shigo bayan ko Ina a rufe yake,,,

Ashe wnn kofar da Tai musu tsakani wadda ta ballah kwanaki, duk da dai an gyara Ashe ba’a saka key ba, Maryam na ganin haka Tai maza ta dauko key ta murda, jiki na rawa don bata aminta da fitar da Tai ba, da kyar in ba wani makamin ta je daukowa ba…

Baba sa’a tace haj, gara kije ki sanar wa makotanku, abinda ke faruwa sbd ba’a San me take Shirin aikatawa ba Kuma ynx, Bai kamata muyi shiru ba, ko sa taimaka mana, tace haka ne baba, Bari nai saurin barin gidan…spare key din gidan taje ta lalubo taxo ta bude kofar ta baya wacce ita kanta rukyn Bata San da ita ba, tai hanzarin fita ba tare da ta dauki yaro ko daya ba, sbd tasan ita take Hari don ta tasan ita ta tsolewa ido, cikin sanda ta bar gidan ta shiga makotansu tana buga kofa alokacin 12 na dare sai faman buga kofar take tana waige ko rukyn ta biyo ta, sai da akai kusan 5min sannan maigidan ya fito shima cike da tsoron Mai buga musu gida a wnn lokaci, sai da ya Dan leka ta wata kofa ya ga Mai bugawar sannan ya bude Yana tambayar Maryam din lfy kuwa?

Tace ba lfy Amaryar Dr. Ce ta kasheshi tana fada tana kuka tace ynz haka ni take bi, wai sai anyi gawa uku..don Allah baban Khalil ka taimaka ka duba min halin da yake ciki…shi kanshi ya tsorata da jin haka, yace shiga ciki Bari naje naga Abinda ke faruwa , amma wnn wace irin mace ce haka, Allah ya kyauta…cikin hanzari ta fada gidan ta samu matar gidan a falo itama Tai jugum domin duk Taji abinda Maryam din ke fada …tace zo mushiga ciki Maryam ta janyota suka shiga daki, ta koma ta Sanya key a kofar falon gudun Kar su ganta kwatsam a gidan..ita dai Maryam sai kuka take tace ni wlh tashin hankali na shine bansan halin da Abbas yake ciki ba, don wnn matar ba abinda bazata iya yi ba…matar tace insha Allahu ba abinda zai sameshi, tace maza ne da kwashe -kwashe Kuna zaman lfy su kwasowa kansu bala’i ynx Ina amfanin wnn don Allah..

Ashe wnn shirun da Maryam taji, yankarsa tayi a hannu ganin zata Kara wani yunkurin, yai saurin kaucewa tare da barin wurin a guje ya fita daga gidan tabi bayanshi itama a guje, ganin ta hakikance kisan take son yi, ya tsorata matuka, yace kafa me naci banbaki ba, itama ta kure gudu, Yana gudu tana binshi, daga ita sai wnn rigar iya cibi da wando, ba dankwali, Yana gudu Yana Fadi a xuciyarsa lalle ba makawa wnn Bata da hankali, ganin ya Mata nisa sosai yasa ta tsaya tana haki tace wlh duk inda kaje sai na bika na hallaka ka, ba abinda zai canza kudurina, Kuma wlh ba wata nadamar da zanyi, juyawa tayi ta koma hanyar gida, sai ga kanwarta da ta biyo bayanta ta rike ta suka koma, duk Yan unguwa na kallonsu don ma wasu sun yi bacci, wasu Kuma hayaniya ce ta fito da su, su ganewa idonsu abinda ke faruwa, wasu har video suka Fara dauka don tabbatar da shaida idan har ta aikata kudurinta, sai faman tsinewa halinta ake.

Shiko Abbas Bai tsaya ko Ina ba, sai division dake basu da nisa ya shiga Afujajan ya Kai musu report din abinda yake son faruwa, suka shigar da case din, Daman sun sanshi, Suma sun jajanta masa, suka ce ya Dan samu nutsuwa sai suje gidan,yace na samu yallabai kawai muje a fitar min da ita a gidana na Riga na saketa ba wani sauran Abu tsakanina da ita, ga iyalina bansan halin da suke ciki ba, karta je ta far musu.

Bayan dawowarta daga bin Abbas din data yi shine ta afka wa maryam tana tuhumarta da cewa ita ce silar faruwar komai, wnn fitar da tayi aguje kuwa komawa tayi ta dauko wukar ta afkawa Maryam, Amma tana zuwa ta tarar kofar a rufe gam, an kulle sai jijjigata take iya karfin ta, ganin an kusa ballah kofar baba sa’a ta fashe da kuka tana fadin shikenan kashinmu ya bushe ..a guje taje ta dauki Hassan ta goya ta dauki usaini a hannu ta fita ta inda Maryam ta fita a guje tana la’ila ha’illallahu jama’a ku taimaka zatai kisan Kai, kicibus sukayi da baban su Khalil Wanda ynz ya gama waya da Abbas ya shaida masa Yana Raye police station yaje ya Kai report gasu Nan ma a hanya zuwa gidan.

Yana ganinta a wnn halin yace baba lfy? Gata can tana can tana Shirin ballah kofar Kuma wlh wukar ce hannunta ta fada a gigice, yace me ?
Shima ya tsorata ainin, yace kiyi sauri ki Kai yaran ciki mamansu tana gidana, ni Bari nai hanzarin debo sauran yaran, … haka baba sa’a taita bugawa su Kuma sun daukan rukyn CE Basu bude ba Saida tace Haj. Nice kuyi hanzarin budewa yara na kawo miki tana can tana Shirin ballah kofar da wuka a hannunta cikin hanzari suka bude suka karbi yaran tana kukan wnn bala’i ko a film Bata taba ganin irin haka ba, tana Basu ta koma cikin hanzari don debo sauran yaran, sai ga Abban su Khalil ya dauko mufid, yace kiyi hanzari ki dauki macen ta kusa ballah kofar..ta dauko ta kenan sai ga kofa kasa ta shigo a fusace da wuka a hannu… Baba sa’a Tai hanzarin buya jikinta sai rawa yake sauran kiris fitsari ya zubo Mata don tsoro, ruky kuwa ba inda tayi da wukar sai dakin Maryam, ta bankada kofar da karfi, ta shiga tana waige waige Bata ga kowa a dakin ba, har wardrob da karkashin gado Bata ganta, ba yaran ko daya a ciki…

Baba sa’a kuwa tana gani ta shiga dakin Tai saurin barin gidan cike da tsoron karta cimma su, Tai saurin shiga can gidan tana fadin wlh hajiya ke take nema, tana ballah kofar dakin ki tayi da wukar tana dubaki, tace wlh da tasamu daya ayaran Nan sai ta hallaka wani, karbar elham din Maryam tayi tana kuka tace na sani ai tinda ni take zargin na rabata da mijinta..

Makociyar tata tace oh wnn masifa Dame tayi Kama…Amma gsky wnn ba Imani a tattare da ita ko kadan…

Anan baba sa’ar take shaida musu Abbas Yana Nan da ranshi, police station yaje sun taho ma gidan ynx. .hamdala Maryam tayi tare da godewa ubangiji daya tserar dasu daga gareta.

 

Acan gidan kuwa ba inda Bata duba ba, Bata ga kowa ba, tace tabbas guduwa sukayi, Amma ta ina? Ta tambayi kanta, ganin Bata samu kowa ba, yasa ta fito waje tana dubawa ko zata ga inda sukai Amma ba Wanda ta gani, A haka bbn su Khalil din ya cimma ta yace haba baiwar Allah me yayi zafi haka kike Shirin aikata irin wnn danyen aikin? Wanda zai saka ki nadama daga baya..tace wlh ba nadamar da zanyi bayan na kashe shi..mutumin daya rabani da kowa, na bashi dukkan kaunata Amma ya saka min da saki, wlh ba abinda zai hanani kashe shi…A’uxubillahi sai kace ba Yar musulma ba kike wnn kirarin …yace ki taimakawa kanki ki aje wnn wukar ta hannunki domin matukar hukuma ta kamaki da ita kin kade…tana Jin hukuma sai Kuma ta tsorata sbd ta tsani Yan sanda balle kwanan prison..ni ko nace Ashe haukan nata na karya ne..Amma sai ta dake Bata nuna Masa tsioronta ba har taci gaba da fadin bazan fasa kudirin da na dauka ba…hango mutanen da suka dumfaro su Tai saurin wulla wukar bayanta, ta danne da kafa, shiko Abbas karasowa yayi da sauri Yana fadin gata Nan yallabai ku tafi da ita, bana bukatar ta Kara koda mintuna a gidana…

 

Muje zuwa

 

*Ummu Ameer ce*💃

🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

*Story & written*

*By*

*Ummu Ameer* 💃

 

 

*Page* 5⃣2⃣

 

*** Kuri-kuri Tai ta idanuwa tunda taji ance wai a tafi da ita, ganin suna Shirin arresting dinta yasa makwabcin sa ya Dan ja Abbas din gefe yace Masa, kayi hakuri kar ka Bari su tafi da ita can,kayi hakuri zuwa safiya sai su kwashe kayansu su tafi, kaga ko ba komai da yarinya tsakaninku Bai kamata ba, kamar tozarci ne ko ya kagani..

Abbas zaro ido yayi yace in barwa zuwa safe ai Banga Abinda zaisa ta kwana a gidan Nan ba, bakasab kudurin da take da shi ba ne akaina, sai kuma in kyaleta don bansan ciwon kaina ba…

Ruky kuwa ganin sun dumfarota ta xube kasa a gurin tana kuka, wai wlh nayi nadama, dama bacin raine ..kuka take sosai sai kace ba ita ta gama kirarin kisa ba, har tana Basu hakuri tace, kunga ba komai a hannuna, tun daxu nayi nadamar Abinda nayi, ta juya kan Abbas ta hade hannu biyu tana rokonsa ya gafarta mata, tayi nadama, tana rokon ya gafarta Mata Kar ya Bari su tafi da ita…shiko ko ajikinsa yace dolenki ki bisu ba abinda zai hanaki kwanan cell!

Kuka take sosai ganin haka daya daga cikin masu tafiya da ita yace oga Ina son magana da Kai..Abbas yabishi suka yi gefe yace oga Ina ganin tunda bamu da hujjar kamata bamuga wani makami a hannunta ba, Kuma Naga alamun nadama a gareta Ina ga kawai gara ka barta zuwa safiya sai su tafi, kaga shi kanshi case din zai iya Kara zama wani Abu daban ga tonon asiri kowa sai yasan me ya faru, Kuma a matsayinka na babban mutum Bai kamata ai ta yawo da maganar ba, in yaso zan bar mutum 1 Wanda zai zauna har gari ya waye gudun Kar wani Abu ya biyo baya…ko ya kagani?

Dogon azuciyar zuciya ya sauke yace amma Sam ban yi niyyar barin ta, ta kwana anan ba, da kyar dai ya Amince da hakan da taimakon makocinsa,, sannan suka ce Maryam din Tai kwanciyar ta, acan din xuwa safiya…

 

Nan suka Mata fada sosai ita kuwa a lokacin ta Fara dawowa hayyacinta ga matsananciyar nadamar Abinda tayi…suka ce ta koma gidan gobe sai su tafi…jiki a sanyaye kanwarta ta kamata suka shiga cikin gidan.

 

Shima Abbas din daki ya shiga, Amma Yana fargabar Kar haukan nata ya Kara tashi, da ya tuna Kuma akwai Mai tsaro a waje sai ya Dan sake…ya zauna yai dressing din wajen data yankeshi Yana yi, Yana tunano abinda ya faru, yace da tuni ta sheka ni lahira, Allah ya kubutar Dani.

Nan dai ya zauna don ba tunanin bacci a wnn Daren abinda ya faru ne ke ta Masa yawo akai ga wani matsanancin ciwon Kai kamar zai fashe, sai Allah wadai da irin wnn zafin kishi nasu yake, sai ynx ya tabbatar da Abinda ake fada akan Yan garinsu masu kashe miji har lahira akan kishi..

 

Can kuwa ruky kuka take kamar ranta zai fita ganin ynx ba wani sauran Zama tsakaninsu da Abbas rashin hakuri da bakin kishinta ya jawo mata nadama, da danasani, tana fadin ynx me zan cewa mummy da wane idon zan kalleta…

 

Aisha ce ke lallahinta tana fadin ki daina kuka don kin rabu da wnn Mara mutuncin ke Baki ga tozarta ki da ya yayi ba, har kike bakin cikin rabuwa da shi, tace wlh Ina son shi, Ina sonshi, tayaya zan iya rayuwa ba tare da shi ba ..Aisha cika ta tayi don takaicin maganar rukyn tace wlh kin bada Mata…Kuma ynx xan Kira mummy in Gaya Mata duk Abinda ya faru, tace karki kirata don nasan Abbas zai yafe min zai barni muci gaba da rayuwa, nasan Yana sona shima bacin raine, Bari naje na Kara bashi hakuri …Aisha ce ta kulle dakin tace wlh ba inda Zaki kina fita zan Kira mommy…ba yadda ta iya haka ta koma ta zauna tana kukan nadama, ta dauki Khadija ta rungume ta, tana fadin kiyi hakuri ‘yata nice na janyo miki rabuwa da Abbanki sbd zafin kishina, na rabaki da Abbanki domin kuwa matukar na bar gidannan ba yadda za ai na barki a gidan, sbd kece farincikina bazan iya Koda kwana 1 ba tare dake a kusa Dani ba, sai Kuma ta fashe da kuka, itama Yar uwartata sai da tayi musu kwallah, ta janyo yayarta ta rungumesu suna kuka.

 

Can Maryam kuwa itama ta kasa runtsawa ko kadan, taso ganin Abbas din Amma akace Tai hakuri xuwa safiya, tunda qlau yake …ba yadda ta iya haka ta hakura,tana Mai tausaya Masa halin da ya shiga, gashi ta mance wayar a gidanta, ita batace ma ga inda take ba, tunda aka Fara wnn tashin hankali…a zaune ta kwana cike da fargabar ko wani abun zai biyo baya, duk da an Gaya Mata duk yadda ta kasance …

 

Tun asubahi ruky taje tana ta buga dakin Abbas da dai ya tabbatar ita ce sai yaki budewa har ta gaji ta Fara cewa Abban Khadija kayi hakuri ka gafarta min wlh nayi nadama abinda nai, kayi hakuri ka bani dama ta karshe …shikuwa cewa yayi axuciyarsa lallai tana da karfin halin tunkararsa da wnn maganar, tsabar rashin kunya ne ma.

Bai saurareta ba, ta karaci surutunta ta koma wajenta, tana shiga taga Aisha ta gama hada Kaya a akwati, tai wa Khadija wanka, ta hada musu duk abubuwan bukata, Zama tayi shirif jiki ba kwari ta kalli Aisha tace nifa ba inda zani, nasan zamu sasanta kanmu, ki daina wnn Shirin …Aisha dubanta tayi da mamaki tace kinsan mekike cewa kuwa tace nasani…

A take Aisha ta Kira no mummy ta Gaya mata duk Abinda ya faru…mummy tace yayi kyau ga abinda nake jiye Mata nan, Kuma ba dai gidana ba wlh..Aisha tace ai tace ba inda zataje wai zasu sasanta ,mummy tace Bata wayar, ta Mika mata Nan ta hau ruwan Bala’i tace in kika Bari gari y waye Baki bar gidan Nan ba, zakiga abinda zani Miki wawiya shashasha kawai…ruky ta cillah wayar tana kuka tana fadin ni ba inda zanje.

Ganin ta dage bazata bar gidan ba, yasa aka sanar da yan’ uwanta abinda ya faru, aka ce suje su taho da ita daga gidan…

Daddy ma Koda yaji labari ransa ya baci sosai na yadda Saida ta kashe auren sannan taji Dadi, cewa yai ba ruwanshi shima ya zare hannunsa akanta.

Koda gari ya waye Abbas fita yayi ya bar gidan, ya gayawa Maryam karta dawo sai sun tafi rukyn.

 

Wajen 8na safe anty Salma da mijinta da wata yaruwarsu suka zo gidan, suka tambayi Aisha abinda ya faru..ta kwashe komai ta fada musu, Anty Salma tace kinga abinda nake Gaya Miki ko gashi Nan ai kin yiwa kanki akan banzan kishi da Bai da amfani, kin guntule auren naki kin huta, tana jin Anty Salma ta Fadi haka ta Kara fashewa da kuka tana fadin don Allah anty ki sa Baki ya maida ni, wlh bazan iya Zama da kowa ba sai shi, ki bashi hakuri ya maida ni, Anty Salma tace ni bazan iya ba, ba dai haka kike so ba, kinsanu kuma ai shikenan.

 

Nan mijin Antyn Salman yace a Kira Abbas din aji ta bakinsa, ko Allah zai sa a dace. …Anty Salma tace wlh ba wanda zai zauna da Mai irin halin wnn kisan Kai fa Tai niyyar yi, sannan Kuma mu tikasta Masa Zama da ita, ni ba hannuna a ciki, in zaka gwada bissimillah, shiko Kiran Abbas din yayi, yace shi baya kusa ,sai da kyar ya bashi hakuri akan yaxo, sannan ya taho ba don yaso ba, donshi ya fita ne har sai ta bar gidan ya dawo.

 

Koda rukyn taji zaizo Dadi taji..har da Kara kintsa kanta

 

Bayan isowarshi ne, ya gaishesu, mijin Antyn ya bukaci ya Gaya Masa Abinda ya faru, ya Gaya Masa komai, suka ce gaskiya rukyn CE da laifi, Bata kyautaba, sannan yace Amma Abbas tunda har tayi nadama muna rokon ka Kara Bata dama, insha Allah zata canxa….Abbas yace ai ynx aure ya Kare tsakanina da ita domin kuwa saki uku 3 nai Mata..ruky najin haka ta kwallah wani irin Kara ta tashi ta nufi Abbas din kamar zakanya…

 

 

 

 

*True lyf story*

 

Muje xuwa

*Ummu Ameer* 💃
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

 

*Stiry& written*

*By*

*Ummu Ameer*💃

 

 

*Page* 5⃣3⃣

 

“””””Cakumarsa tayi tana fadin wlh baka Isa ba, tunda ka tsinke igiyar aurena da Kai wlh da Kai da Matar taka sai na hallaka ku, wlh muddin Ina Raye kuda farinciki har Abada…

Anty Salma ce ta daka Mata tsawa tare da janyo ta daga wajen Abbas tana fada Baki da hankali ne, Zaki dinga wnn furuci, ta wurga ta kan kujera tace koma me ya faru dake kekika jawo, yaro Mai hakuri, in ba ma Shiba a wnn zamanin waye zai kyaleki ki ta wnn haukan ai da tuni ma ya koreki, Amma duk da haka sai da kika kaishi makura, ai kinji Dadi, ki tashi mu tafi tunda ba sauran Zama tsakninku, tana Jin haka tace Anty ba inda zani wlh..ji kake tasss ta shharara Mata Mari tace lallai na yarda ciwon hauka ya sameki, wawiya kawai..ruky najin haka ta shige kitchen ta kulle kanta ta kunna gas wai zata kona kanta, akai akai t bude taki har warin gas din ya Fara fita sosai ta kyassa kenan mijin Anty Salma d Abbas din suka ballah kofar anty Salma ta hau dukanta tana fadin ah lalle dole Abbas ya samawa kansa lfy wa zai jure wnn isakancin naki, tana fitowa Kuma sai tayi toilet Nan ma ta kulle ta kyassa ashanar a soso wai in ya Kama sai ta Dora a jikinta, Nan ma da kyar aka bude, ba Kuma a fasa dukannata ba, Amma ko ajikinta kayan ta dik sun yayyage, tana fadin wlh saina jaza maka bala’in da sai ka Kare rayuwarka a prison…Anty Salma ta riko ta tace ku Kama ta mu Sanya ta a mota wnn tayi nisa karta ballo wa kanta bala’i, mutum 4 ne suka kamata 4,maza 2 Mata 2, Amma yadda kasan ingarman doki, kasa janta sukai ta tirje a lallai bazata bar gidannan.

Shidai Abbas Yana bakin kofa ya tsaya ya harde hannuwansa waje daya Yana godewa Allah da yasa take zuba haukan a gaban yanuwanta…su tabbatar da halinta.

Ruky dai hauka tuburan wani karfi daya zo mata tai wancakali da su, ta nufi gurin Abbas shiko Yana ganin haka yai hanzarin barin gidan ta bishi a hakan duk Kaya a barke yai hanzarin shiga motarsa da yai parking dinta can nesa da gidan.

Tana ganin haka ta juyo ta dawo, ba inda ta nufa sai bangaren Maryam Allah yaso dakunan a kulle suke da kitchen, ta falon ta Fara farfasa abubuwa, tana wullar da komai na wajen, data gama da nan Tai toilet, Nan ma ta fasa na fasawa ta zubar da na zubarwa sai da Tai kacha-kacha da gidan sannan ta fito, Aiko Anty Salma wata sharbebiyar bulala ta je ta samo a waje ta afkawa ruky Amma dake zuciyar ta bushe ko ajikinta, Abin ma ya Fara Basu tsoro ko dai tana da mutanen Nan, zuba Mata ido sukai suna mamakin ikon Allah , Itakuwa wata kwalba ta glass din data fasa ne ta dauko ta yanki hannunta yankar kuwa ba karama ba, Nan jini ya fara bulbulowa sai Kuma ta Fadi ta xube a kasa a sume…kanwarta Tai kanta a guje tana Kiran sunanta, tana jijjiga ta, a haka aka kwasheta sai asibiti…wnn shine silar barinta gidan.

 

Shikuwa Abbas ba nisa yai ba, can bayan layinsu ya samu ya fake, anan ake gayamasa Abinda ya faru da rukyn yace Allah kyauta.sai da ya tabbatar da sun bar unguwar sannan ya dawo gidan yaga irin barnan da ta Masa a gidan, yace tunda ba wani kika hallaka ba, Allah tsayar Anan.

Nan ya Kira Maryam yace ta dawo sun tafi, shiyaje har kofar gidan ya debo yaransa, suna yiwa juna jajen Abinda ya faru…

Nan suka zage suna aikin harda Baba sa’a suna gyaran gidan, cikin kankanin lokaci suka kimtsa gidan, na gyara ya kirawo masu gyara suka gyara, na zubarwa aka zubar.

A ranar ba inda Abbas yaje Yana gida, masu zuwa jaje na zuwa, Yan gulma na xuwa ganin kwaf..

 

Rukyn kuwa a Asibitin, tana farfadowa ta ganta a hospital, tana tambayar waya kawo ni Nan, ba Wanda ya kulata,sbd kowa Jin haushin ta yake ,

Ganin haka yasa ta tambayi Aisha wayarta ta Mika Mata, ba Wanda ta Kira sai no Abbas, Tai ta Kira kusan sau goma Bai dauka ba, daga karshe ya tura mata yace Kiran me take wa mutumin da taso hallakawa, kiyi hakuri ki daina kirana, ba wani sauran Abu tsakanina da ke…yarinyata ma zan zo in dauki yata.
Allah ya kaddara saduwa…a take yai blocking no.

 

Tai ta Kira Amma Taki shiga, haka ta hakura ta Fara zubda kwallar nadamar da Bata da amfani..ita ciwon ma Bai dameta Bata shi take ba.

Su anty Salma kuwa sun gane Wanda take kokarin kira, suna mamakin wnn halin nata, kowa ta bashi haushi a wajen.zuwa can sai ga mommy Afujajan taji ance yarta na asiniti, kasancewar Basu fada Mata Abinda ya faru ba…

 

 

Muje xuwa

*Ummu Ameer* 💃

🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

*Story & written*

*By*

*Ummu Ameer* 💃

*Jinjina Mai yawa a gareki MRS ABUBAKAR Ina godiya da kulawarki a gareni Allah ya bar zumunci*🤝🏻

 

 

*Page* 5⃣4⃣

 

“””Mummy kuwa na Isa Asibitin ganin yarta a wani hali, duk ta lalace kamar ba ita ba, ta Kara Baki..yasa mummy fadin ohhhh! Irin gashin K’umar da yake Miki kenan Amma kikai shiru Kika kasa fada?

To wlh ya saurari sammaci,bazan yarda da wannan rashin mutumcin ba, haka na bashi y’artawa?

Anty Salma tace “Yaya me ya kawo batun sammaci, kawai don tayar da fitina tsaye, kin binciki yartaki da har kike Shirin yanke hukuncin..ai ba shine ya cancanci yaji sammaci ku ya kamata yaiwa haka, Amma sbd sirikin arziki ne da ke, ya kyale maganar, kinsan irin danyen aikin data so janyowa ma kanta kuwa?
Allah ne ya taimaketa da tuni tana “gidan kaso”.

Budar bakin mummy kuwa sai cewa tayi and so wahat inta kasheshi, shi din ma ynx ai kiris ya rage ya karasa ta…

Anty salmah kuwa tace haka Kika ce? Mummy tace yes of course!

Mijinta taiwa umarni da ya tashi su tafi, tace na barki lfy..kuyi duk yadda kuka so, tasa Kai Tai ficewarta a dakin.

Ruky kuwa fashewa tayi da kukan nadama, ta fada jikin mummy tana fadin Mummy Abbas bashi da laifin komai, rashin hakurina da rashin bin maganar iyaye ne ya jawo min, ta Kara tsananta kukanta da fadin don Allah mummy kiyi hakuri ki yafemin nayi nadama, Nan itama mummyn kwallah ta cika idanuwanta tana cewa na yafe miki, Kuma nima da laifina Akan zare hannuna da nayi akanki Nima ki yafe min.

Nan sukai ta nemawa juna yafiya akan kurakuran da suka aikata.

Ruky kuwa wata iri ta koma duk ta fita hayyacinta cikin kankanin lokaci, tare da matsananciyar nadama, har tana fadin Ina ma baya zata dawo da tayi amfani da ita wajen gyara kura-kuranta, Amma Ina bakin Alkalami ya bushe, duk Wanda ya ganta a halin da take ynx sai ya tausaya mata.

Zuwa dare aka sallamesu tare da Bata magunguna suka kama hanyar gida.ita Khadija kuwa dama Aisha ta wuce da ita gida tun dazu.

***** *********** *******
Acan gidan su Abbas kuwa sai ynx yaje jinsa free, tunda ya sawwake mata yake Jin kamar ya sauke wani nauyi ne akansa…cikin kankanin lokaci har ya dawo hayyacinsa, a baya kuwa jinsa yake bashi da wata nutsuwa sbd kullum cikin korafi, da kawo fargabar abinda zaije ya tarar a wajenta,.

A Daren ranar ne suna zaune suna hira, tare da jajantawa juna wanna masifar da ta auko gidansu, har Yana Bata hakuri akan ta yafe Masa akan kawo musu tashin hankali da yayi a gidan suna zaman lafiya.

Tace tace ai mutum baya wuce kaddararsa Allah ya Kara kiyaye gaba ya Kuma Kara karemu da kariyarsa.
Yace “Ameen”

Yace ai Allah ya auna arziki da sai dai kuji mummunan labari.

Nan ya Bata labarin gudun da suka rinka Yi, har Saida taga nayi mata nisa sannan ta hakura…Maryam kuwa ta kwashe da dariya har da rike ciki, yace ok! Dariya ma na Baki ko?hmmm ba Dole na ceci kaina ba, Kuma kinsan ni kaina bansan zan iya wnn gudun ba, kinsan mutum in Yana bazai iya ba, to Bata kamashi bane.

Itako har da tsugunnawa kasa don dariya, tace ka bada maza gaskiya Ina jarumtar mazan? Tace ta gane kafa matsoracine.
Shiyasa.

Yace kedai abar zancen kawai.
Yace shine ke kuma Kika gudu Kika barmun yara, to da ta samesu Baki tunanin komai zai iya faruwa..tace to ai Naga nice danuwarta ba yara ba, shiyasa na bar gidan.

Yace gaskiya hakan kuskurene ki daina..

Bayan sun gama maida zance suka je suka kwanta Amma Saida ya tabbatar da ya kulle ko ina yadda ya kamata, don ya tsorata ainin da halin ruky.

 

Ruky kuwa acan ta kasa Koda runtsawa Taki cI, Taki Sha sbd tashin hankalin data ke ciki, ga matsananciyar kewar gidanta, in ta kalli Khadija kuwa sai taji wani irin tausayin yarinyar ya shigeta, tace yanxu shikenan zata taso ba tare da mahaifinta ba, Zatai irin rayuwar da tayi na rashin mahaifi a kusa.

Ga wani irin son Abbas din data keji Yana Kara Shigarta, sosai tayi nadama, sai dai nadamar tata Bata da wani amfani a yanxu…

A zaune ta kwana don ko tayi yunkurin kwanciyar Jin zuciyarta take kamar
zata fashe ga wani irin nauyi da kirjinta yai, Bata iya koda kwakkwaran motsi.

A haka ta kwana a zaune,duk da kokarin da Aisha ke Mata na ganin ta cire Mata damuwarta, Amma ko kusa kamar ma karuwa take.

Haka dai ta shiga cikin wani kunci, kowa ya tausaya Mata halin da take ciki, wasu Kuma na halinta ne ya janyo mata, ita kanta sai yanzu ne ta Fara tirr da wannan bakar zuciyartata, da bakin kishin da Tai gado..

Ta dawo silent, kamar ba ruky ba, dama can haka halin nata yake don Bata cika son magana ba.kishi ne ya canza ta.

 

Muje zuwa

Taku

*Ummu Ameer*💃

🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻
*KISHI KO HAUKA*
🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

 

*Story&written*

*By*

*Ummu Ameer*💃

 

*INA MATUKAR GODIYA GA BUMBUN MASOYANA ADDU’OINKU SUN ISO GARENI BA ABINDA ZANCE SAI DAI ALLAH YA SAKA DA MAFIFICIN ALKHAIRI ALLAH YA BAR KAUNA*❣❣❣

*NIMA INA ALFAHARI DA KU AKO YAUSHE BURINA A KO YAUSHE IN FARANTA MUKU*

*NAGODE KWARAI*
*ANA TAREE*🤝🏻

*MRS ABUBAKAR ina Taya ki murnar fara sabon novel dinKI(*KUN CUNCENI*) ALLAH YASA AN FARA A SA’A AMEEN.

*Page* 5⃣5⃣
*END*

“””Su Yaya babba kuwa da aka ji labari ruky ta Sha tsinuwa wai kaga shedaniyar yarinya, dan’uwanna mu kenan da yake kula da mu take son hallaka mana shi, ja’irar banza kawai ai da an kulleta ta koyi hankali, Ina ganinta kamar mutuniyar arziki Ashe ta iya ta’addanci.

Har gida taxo tai musu jaje, tace ka kyauta da Kai mata saki 3, ai ko a hanya bazan fatan Allah ya hadani da ita ba.

Nan ta roki Maryam gafarar akan halayen da ta nuna Mata, tace Ashe kece yarinyar arziki, tun a sunan Yan biyu ta Fara yin tsiyar ai, to Allah ya raka taki gona, Allah ya Kara hada kawunanku.
Tace Ameen!!!

Nan tace Masa ya je ya karbo yarinyarsa, shikenan ba wani sauran alaka tsakaninsu.

Kwananta 2 ta tafi Maryam ta hada Mata shatara na arziki sai godiya take.

____________________

Bayan sati guda da rabuwarsu ya tura Mata text Akan ta shirya wa Khadija kayanta zaizo ya dauketa…Nan fa ta buga tsalle tace Bata yarda ba, wlh ba Wanda ya Isa ya rabata da yarta, yace aikuwa Baki Isa ba, shine mahaifinta Yana da iko da y’arsa. Tace wlh ko kotu Bata Isa ta rabani da gudan jinina ba.

Rigima akai sosai akan yarinyar, sun hakikance ita da mummy akan bazasu bayar da ita, duk inda zaije ya kaisu ya je.
Hakanan ya hakura ya bar musu.

Sannan suka yanka Masa wasu makudan kudi da zai dinga Basu na yarinyar duk wata, yace Nan fa daya iya karfina zanyi, in sun Raina su maido Masa diyarsa.

Anan ma ba karamin artabu akai ba, ba yadda suka iya suka hakura, saboda yarinyar ce bazasu bayar ba.

Bayan kwana 2 kuwa yace suxo su kwashe kayansu Yana da bukatar dakunan….

Ruky kuwa naji ance a kwashe Kaya Nan hankali ya Kara tashi, sai kiransa take Amma Sam wayar Taki shiga, sai text ta tura Masa wai don Allah Kar yai Mata haka, ya Bata lokaci su Dan fahimci juna, yace wane sauran faahimta kin manta babu wata sauran alaka tsakanina dake?

Yace zuwa next week kuzo ku kwashe Kaya zanyi amfani da dakuna..hankalinta sosai ya tashi.

Mummy kuwa da Anty batulu da wasu mutane 4 suka je gidan ranar Asabar da Shirin kwashe Kaya itama rukyn tace sai tazo yace karta soma tako Masa gida, mummyn tace tunda ga mahaukaciya ba, kartazo Tai maka hauka ko?

A zuciyar sa yace ai gara ma mahaukaciya tunda ansan itace…Nan ya tsaya ya kasa yana kula da duk abinda sukeyi, ya kulle bangaren Maryam gudun karsu soma shigar mata, don Yana jin suna cewa sai sun Mata dukan tsiya.

 

Nan dai suka hau parking din Kaya suna yi, suna zaginsu, harda mummy don itace ma kan gaba, wai har tana tunda ka maida diyata bazawara kaima in Allah y yarda sai an wa naka haka, duk Yana jinsu Bai ko tanka musu ba, abinda ya Kara Bata musu rai kenan.

Itama Maryam din ta saitin kofar ta sukai ta binta da munanan zagi suna to Yar masu bin bokaye maganinku yai tasiri sai aje a biya shi, shegiya Yar abukaza kaza Kuma uwar ce da wnn aikin da kanwarta Aisha, girma dai ya Fadi…

Maryam kuwa ko kula su batai ba, itama suna tare da wata yayarta har tana cewa ya za ai ku zuba musu ido suzo har gida suna zaginku, Maryam tace ai in mun biye musu muma min Zama su kenan ki barsu da halinsu kawai,

Haka dai suka kwashe kayan tsaf, bayan sun gama suka hau farfasa wasu abubuwan, suka yi gaba tare da takaicin rashin dukan Maryam ga haushin Bata tanka musu ba, suna fita Abbas ya rufe gate din gidan, ya koma ciki yaga irin barnar da sukai yace tunda ba wani kuka taba ba da sauki, yai tirrr da halinsu na rashin dattako, yai wa Allah godiya da ya raba shi da Kaya..

 

Ruky kuwa tunda aka kwaso Kaya wani sabon kuka ta bude, zuwa ynx ma sun Fara Jin haushinta, Akan wahal da kanta da take Akan Wanda Bai San tana Yi ba, shiyasa ynx kowa ya fita a harkarta.

Ga daddy shima ya zare hannunsa akanta,yace Kar ta soma xuwa inda yake, haka rayuwa Tai Mata kunci, ta shiga wani hali..ita kanta mummyn Taji zafin rabuwar tasu, sbd tana sane da cewa samun mutum kamar Abbas da wuya, gashi mutum ne Mai kulawa da gidansa akan komai..baya wasa da gidansa.tunda tasan cewa ba abinda zaka nema ka rasa a gidansa na Jin dadin rayuwa..mutum ne Mai zuciya.

Amma sai ta bar Abin a zuciyarta Bata bari an fahimceta ba.

Ganin yarinyarta na Shirin shiga wani Hali yasa ta tattara duk wata kulawa ga yartata don ganin ta dawo Mata da farincikinta. Amma Ina Abin na ruky babba ne har rashin lfy ta kwanta a asibiti tsawon wata guda, kamar bazata yi ba.

Sai da aka hada Mata da addu’oi ta Dan fara marmarowa, aka sallamesu suka dawo gida, ga babban tashin hankalinta hatta takardar da Abbas ya bayar ta sakin da ya rubuta ya Sanya yunkurin kisan kan da take son yine dalilin sakin..domin a zahirin gaskiya da ya furta Mata sakin ba uku yai niyyah ba, ganin irin haukan da ya biyo bayan sakin yasa shi yin ukun yace da ana fiye da haka da yayi..

To ynx shine damuwarta, domin xuwa ynx ta Riga tasan Abbas yai Mata nisa, ta hakura ta rage damuwarta akansa, Amma soyyayar sa kullum Kara karfi take a zuciyarta.kuma tasan duk Wanda yai yinkurin auranta yaji abinda Tai niyyar aikatawa bazasu yadda su kwasarwa kansu ba, ita kanta tasan har yarta ta janyowa domin za’a ce yarinyar Mai yinkurin kashe mijinta ne, ita kanta Yar za:a yi shakkun auranta.

 

Haka rayuwa ta juyawa ruky baya, ta shiga kunci Mara misaltuwa, ganin haka yasa mahaifinnata ya yafe Mata yace ta dawo wajensa da zama ko ta nesanta da shi…

Haka kuwa akai ta koma can wajen daddyn da Zama, Kuma ba laifi ta Dan samu saukin damuwa, da taimakon Anty nasiba,matar daddyn kullum cikin nasiha take Mata. Kuma Alhamdulillah ta dauka.
Domin ynx ta Fara cire shi a xuciyarta.

Ganin haka daddy ya Sami Mata aiki teaching, tana koyarwa a wata government sch, ko ta Kara samun saukin damuwarta, haka ta Fara koyarwa a makarantar hakan kuwa ya rage Mata damuwa sosai, saidai duk sanda ta tuno Abbas din tana kuka Mai isarta, shi kuwa ba abinda ya shafesshi don baima San halin da take ciki ba.saidai duk wata Yana Mata transfer na Khadija, wani lokacinma, har shopping yake mata ya aika gidansu, shi baima San ta koma wajen daddyn ba.

 

_____________

Acan kuwa gidan Abbas wata sabuwar rayuwa suka bude Mai cike da so da kaunar juna, ga wata kulawa ta musamman da suke ma juna, sai kacee sabbin amare, ga su Hassan sun girma har suna yawo ko Ina kyawun yaran ya Kara fitowa dik inda suka je sai anyi sha’awar su, shima abbnsu Yana gatanta su, Yana ji da yaran sosai..

Haka rayuwa taita shudawa, suna zaune cikin kwanciyar hankali, Abbas kuwa cewa yai ai shida Karin aure har abada…Maryam kuwa tace hmmmm Allah yasa….

Tuni Maryam ta koma makaranta, inda take masters dinta ynx, sbd Bata da wani nauyin yara domin su hassan ma an Sanya su amakaranta, domin wayo ne da su ga Baki radau sai kace wasu manya, Nan kuwa shekararsu 2.

Baba, sa’a itace har ynx ke kular Mata da yaran don sun Saba da ita, zata barsu a gida ta je ko Ina ba tare da fargaba ba.

Maryam an Kara zama babbar Mata, Kuma duk da haka bazaka ce ta haifi yara 4 ba.sbd kula da kanta da takeyi ko yaushe, kwalliyarta ma, sai abinda ya Karu, shiyasa ko yaushe cikin dokin junansu suke.

 

Bayan ya kammala gidansa da ya ke ginawa a wata unguwar suka koma, gidan babba ne sosai sama da kasa, tabbas gidan ya Sha kudi.. duk wani abin more rayuwa an Sanya shi, sai zuwa musu murna akeyi, harda wajen shakatawa da aka kayatashi, da furanni masu kyau ga wasu kujeru da ba ako Ina zaka gansu ba.

Gida Kam sai son barka, sai fatan Allah yasa a kashe lfy…

Khadija tuni an Sanya ta a sch.kuma shima Abbas yana kokarin kula da yarinyar gwargwado.

.ruky kuwa in masu son aurenta suka zo, tun Bata saurararsu har ta Fara ganin shekaru na ja…Amma da sun tsananta, binciken akanta sai su janye suna gudun Kar ta hallaka su, sbd Suma suna da aure da ya”ya.

Tun Abin Bai damunta har ya Fara sanyata damuwa, sbd a halin ynx ta fara gajiya da zaman gida, so take itama ta samu yancinta.

Aikuwa dai tana ji tana gani auren ya gagareta, sai a lokacin ta Fara ganin illar Abinda ta aikata, gashi Nan Yana bibiyarta….sosai ta shiga damuwa har ta fidda ran auren kwata-kwata.

 

 

Sai daga baya wani yarensu yazo shima Yana da Mata da yara 5, Nan da Nan ta Amince Masa akai komai cikin kankanin lokaci…aka Kai amarya can maiduguri.

Saidai kishiyar ta tattaka ruky rashin mutumci, itako a lokacin ta saduda, ta cire wnn bakin kishin a ranta, ganin ba abinda ya janyo Mata sai asarar mijin data fi kauna duk duniya…don shi kanshi wnn din ba wai sonshi take ba, kawai ita dai gajiya tayi da zawarcin.

Amma zuciyarta na ga Abbas, Khadija kuwa tana wajen mummy tana makaranta.

Haka ta fara sabuwar rayuwa a gidan, ga kishiyarta ta Hana ta sakat, a gidan ta Riga ta gama Kama mijinta a hannu, sai abinda tace Bata Jin dadin rayuwar gidan ko kadan, ga shi ba wata soyayya da ya., Bai San kula da mace ba, ba kyautatawa sai sai dai kawai ya biyawa kansa bikata ta karfi in hakan ta taso. .ruky kuwa ai ynx ya Fara kukan nadama, tayi rashin miji, ynx har ta Kai sai ya dauki tsawon sati guda ko fiye da haka Bata da girki, kuma Bata Isa Tai magana ba, ya hau jibgarta kamar jaka, gashi ta kasa fadin halin da take ciki…

Sai wata Rana da aka kaimata ziyara suka tarar Yana ta dukanta, ganinsu ma Bai Sa ya daina ba, dama halinsa ne dukan mace ita waccan har ta Saba.

Aikuwa suna ganin haka suka ce bazasu yarda ba, sai ya saketa shikuwa yace ba Wanda ya Isa yasa shi ya saketa, harda zaginsu wai kwadayi ne yasa suka manna masa ita Daman, to Zama ynx ya fara da ita, ganin haka yasa suka shigar da shi Kara, akai ta case daga karshe dai sai da sukayi nasarar raba auren.

Ga cikin wata shida, haka ta koma gidan Tai ta renon cikin Kuma yaki saurararta, baya musu aike ko kadan, haka Allah yasa ta haihu saidai yaron baizo da Rai ba….

Tayi kuka sosai sannan taita neman gafarar ubangiji..ya sassauta Mata halin datake ciki.

Bayan ta yi arba:in da haihuwar ta koma gidan mommy da Zama auren ya fita akanta kwata-kwata, harda turawa Abbas text akan ya yafe Mata Abinda Tai masa, taga abubuwa iri-iri bayan rabuwarsu…yace ban rike ki araina ba, Allah ya yafe Mana Baki daya Ameen….

MU HADU A KASHI NA 2
Amma ba yanzu ba.

*ALHAMDULILLAH*

 

*Komai yai farko zaiyi karshe, ayau na kawo karshen wnn littafi kishi ko hauka Allah ya bamu ladan Abinda muka fadakar, kurakuran dake ciki Allah ya yafe Mana*

*Masu Hali irin na ruky Kuma sai su farga suga abinda ya janyo Mata, shi zafin kishi ba inda zai kaiki sai ga nadama komai na rayuwa Dan hakuri ne, yau ko ke kadai kike zaune da mijinki sai kinyi hakuri balle kuma ku 2 ko fiye da haka, Ina fatan hakan ya Zama iznah ga masu wnn halin*
I

 

Ina godiya da karfin gwiwar da kuka bani akan wnn novel,, Ina godiya sosai da sosai..

*Sai kunjini a sabon novel dina very soon*

 

 

 

*NAGODE*

Taku

*Ummu Ameer* 💃

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button