Hausa Novels

Sumbatar Masoyi Na Ƙara Tsawon Rai Da Sheƙin Fuska Musamman Ga Mace

WATA SABUWA: Sumbatar Masoyi Na Ƙara Tsawon Rai Da Sheƙin Fuska Musamman Ga Mace – Binciken Ƙwararru

Sumba hanya ce da masoya ke amfani da shi wajen nuna soyayyar su ga waɗanda suke so.

Ba ya ga masoya iyaye ma kan yi amfani da wannan hanya domin nuna soyayyar su ga ƴaƴan su.

Wata marubuciya da masaniyar abincin dake inganta garkuwar jiki dake ƙasar Amurka Jeena Schreck ta bayyana wasu hanyoyin da Sumba ke inganta lafiyar mutane.

 

Ga Hanyoyin

1. Sumbata Na Ƙara Danƙon Soyayya a Tsakanin Masoya:

Sumbata musamman tsakanin masoya na cikin hanyoyin dake taimaka wa mata wajen amincewa da namiji wajen yin jima’i ko aure.

2. Faranta Rai:

Sumbata hanya ce dake faranta wa mutum rai yana kuma taimakawa wajen rage gajiya a jiki.

An ce gamsuwar da ake samu a lokacin da ake sumbatar masoyi kusan dai-dai yake da irin daɗin da wanda ke maskewa da Heroin.

3. Inganta Gatar Mutum:

Musamman ga mata sumbatar masoyi na ƙara haske da annuri a fuskar mace ta riƙa sheƙi.

4. Sumbata na taimaka wa mutane da dama wajen samun gamsuwa kafin jima’i. Sannan yana taimakawa wajen inganta sha’awar yin jima’i ga masoyi da masoyiya.

5. Sumbata Na Ƙara Tsawon Rayuwa:

Wani sakamakon bincike da Arthur Szabo ya gudanar ya nuna cewa sumba na ƙara tsawon rayuwar mutane a duniya.

Sakamakon binciken ya nuna cewa muddin namiji na sumbar matarsa da safe kafin ya tafi wurin aiki yana ƙara tsawon rayuwarsa domin zai tafi aiki cikin jin dadi da anashuwa.

Duk da haka akwai wasu hanyoyi da suka nuna cewa sumba na cutar da lafiyar mutane inda haka ya zama dole mutane su riƙa yin hattara da irin mutanen da suke Sumba.

 

Cututtuka Shida Da Ake Kamuwa Da Su Ta Hanyar Sumba

1. Tarin fuka

2. Mura da tari

3. Ƙwayoyin ‘Bacteria’ dake kama hakora da saka warin baki.

4. Hepatitis B

5. Cututtukan sanyi kamar ‘Herpes’, ‘Gonorrhea’, Syphilis da sauran su.

6. Cutar ‘Meningococcal’: Cutar na kama da cutar sanƙarau domin yana kama ƙwaƙwalwa da ƙashin baya sannan ana kamuwa da shi ta hanyar yin Sumba.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button