Education

Hadarin Soyayya a Facebook

๐‡๐€๐ƒ๐€๐‘๐ˆ๐ ๐’๐Ž๐˜๐€๐˜๐˜๐€๐‘๐‡ ๐…๐€๐‚๐„๐๐Ž๐Ž๐Š
(๐ฒ๐š๐ซ ๐ฎ๐ฐ๐š ๐ค๐ข ๐ค๐š๐ซ๐š๐ง๐ญ๐š ๐ณ๐š๐ข ๐š๐ฆ๐Ÿ๐š๐ง๐ž๐ค๐ข)

Duk imaninki, duk iliminki, duk wayonki, duk tsoron Allanki namiji zai iya cin galaba akanki da taimakon shaidan ta hanyar
soyayyar kafar sadarwar zamani, ki gujeshi baki daya kawai domin baki iya gane wanene zaizo da gaskiya baah..

Wallahi sai kin kiyaye kanki sannan Allah zai kiyayeki.

Yar uwa ta yaya wanda bai sanki ba, bai San asalinki ba, baisan yanayin halittarki ba yace
yanasonki kuma har ki yarda???

Karya namiji yake, yace wai sonki yake saboda addininki ko iliminki zallah batare da bukatar wasu abubuwa daya kamata ace
kin mallaka don dorewar zaman aure ba…

 

1__Wani burinshi kawai mutane su jinjina
masa cewar yayi soyayya dake, amma baya
bukatar ki zama matarsa.

2__Wani kuma so yake yasamu wacce zata
dinga fada masa kalaman soyayya idan yana
online dazaran yabar Facebook ya manta
dake.

3__Zaki iya sallama zuciyarki ga wani sai kinyi
nisa a sonsa kudau shekaru tare da tunin zai aureki ,sai ya gama jin dadadan
kalamanki, ya Riga yasan sirrikanki ya gudu
ya barki, yar uwa yaya zakiyi tunda haduwar
Facebook ne? Ina zaki gano shi bayan kin
kamu da sansa?

4__Wani kuma dama karya yake ba sonki
yake ba hotonki kawai yake son samu, dama
aikinsa kenan kullum tara pics din ‘yan mata.

 

5__Wani zai iya amfani da hanyoyi da zaki
kamu da sonsa, wanda daga karshe zaiyi
amfani da son da kike masa yajaki zuwa
aikata abinda zakiyi nadama, abinda ke
kanki zaki kasa yafewa kanki.

6__Da zarar kin fara bude zuciyarki wajen
karban soyayyar wani, to akwai yiyuwar
idan wani yasake zuwa ki amsa mashi,
kenan kin zama YAR YAUDARA.

Bawae nace soyayyar facebook Karya bace. Ana samun masoyan gaskia har aure anayi ta sana diyyar SOCIAL NETWORK. amma shawara itace Kufara Haduwa da Juna tukunna, idan kaga juna wannan ba matsala bane. Intayi maka kaima kayimata saiku daidaita Kanku

SHAWARA CE KYAUTA

๐ฆ๐ข๐ฃ๐ข๐ง ๐Ÿ๐š๐ฅ๐ฆ๐š๐ญ๐š
Pharouq khalakhala

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button