Kalaman soyayya ga budurwa
NA MAZA
Ke ce hasken ranar da ke haska min dare na san safiya ta yi a duniyata, ke ce iskar da nake shaka domin na rayu, ke tamkar igiyar ruwa ce a cikin kogin da nake ninkaya, ke ce bugun zuciyata da yake bambance rayuwa da mutuwata. Ina Son Ki.
Son da nake yi miki tamkar madubi ne a cikin zuciyata. Ko da a ce ya fashe, idan kika sanya idanuwanki a kansa za ki tarar da ke a cikinsa. Son ki ya zamo jini a jikina ya bi ta jijiyoyin jikina ya narke a cikin zuciyata. Ina Son Ki Sarauniyata.
Ranar da za a ce ga ki a kusa da ni, a wannan ranar zan ji ni a matsayin cikakken mutum mai sa’ar da babu irin sa, a wannan rana zan yi takun kasaita tamkar na sarkin da ke da daular da babu irin ta a duniya, saboda na mallaki mai kyawun da babu kamar ta, wadda nake fatan mu rayu tare rayuwa ta har abada. Ina hango mana rayuwa mai tsawo cikin shekaru masu ɗauke da ranaku masu ban mamaki a nan gaba. Ina Son Ki Gimbiyata.
A dukkan lokacin da tinanin kyakkyawar fuskarki ya bujuro a cikin zuciyata, sai na ji zuciyata ta kara narkewa a cikin soyayyarki, na ji na kamu da matsanancin begenki, kewarki mara misaltuwa ta dabaibaye ni ta yadda nake kasa tsaida zuciyata daga tinaninki. Ina Son Ki.
A lokacin da taurari suka kasance suna haska saman duniya da haskensu, mu kuma mu kasance tare a kasanta muna masu haska cikinta, wannan abu ne da zuciyata tini ta aminta da shi tare da kaguwa wajen ganin mun kasance tare tamkar jini da tsoka, zan so a kullum ke ma kamar ni burin son ganin faruwar hakan ya kasance a cikin zuciyarki. Ina Son Ki. Fatan Kina Nan Lafiya?
Macen da murmushinta ke haska duhun dare, macen da sautin muryarta ke sanya nutsuwa a zuciyar mai sauraro. Kin samar da farin-ciki a cikin zuciyata, kin zamo mace ɗaya tilo da babu kamar ta a cikin idanuwana. Ina Son Ki.
Amincin Allah ya tabbata a gare ki, mace ta farko da ganin kyawunta a karon farko ya hana ni bacci a tsawon dare, ya hana ni sukuni a tsawon yini, macen da ta tsaida zuciyata daga tinanin komai sai nata, macen da nake so kuma zan cigaba da so har karshen rayuwata. Ina Son Ki.
Ke ce babbar kyautar da a tarihin rayuwata na taɓa samu wadda ba zan taɓa mantawa da ita ba. Ina son ki. Ina fatan tabbatuwar murmushi a saman fuskarki tare da kasancewarki cikin walwala da farin-ciki a ko da yaushe.
A lokacin da na ga hoton kyakkyawar surarki na kan yi murmushi ko da ina cikin damuwa, na kan faɗa cikin tinanin kyawawan idanuwanki da tattausan murmushinki. Ya kan gusar da hankalina daga sauraren komai da tinanin komai sai naki, ya kuma iza wutar begenki a cikin zuciyata. Ina son ki masoyiyata, abar tinanina.
Ke ce mai kawata baccina a duk cikin dare, a lokacin da kike bayyana a cikin mafarkina kina mai haske ni da hasken murmushinki mai taushi. Zan so ki kasance a tare da ni a rayuwarmu ta zahiri kamar haka, na tabbata jama’a zasu koma kirana da Yarima ko Dangata, saboda na mallake ki. Ina son ki.
♡
Son da kike yi min, shi ne abu mafi girman dukkan wata kyauta da na taɓa samu a rayuwata. Kamar yadda na sha sanar da ke a baya ina son ki ni ma so mara iyaka da lokacin yankewa. Ki kula min da kanki.
Ba na yin nadama ko da na sani da zaɓenki a matsayin masoyiyata, saboda ke ce zaɓin raina kuma ke ce mahaɗin rayuwata, ke ce wadda na jima ina nema. Fatana na rayu tare da ke a matsayin uwar ‘ya’yana, na kuma mutu ina mai fatan sake haɗuwa da ke a gida mafi soyuwa ga kowane mutum wato Aljanna. Ina Son Ki.
Barka da safiya masoyiyata, kyakkyawar macen da babu kamar ta, mai sanyin muryar da ta zarce sarewa, mai kyawun ido da kyawun kallo, ina fatan kin tashi lafiya kyakkyawar zinariyata.
Son ki ya shiga zuciyata ta yadda ba zan iya wuni ba tare da tinaninki ba. Yadda nake ji a cikin zuciyata a kanki ya sanya ni jin cewa ina son ki ne fiye da yadda kowa yake nuna hakan a kanki. Idan har kika tambaye ni me ya sa, ba zan iya sanar da ke dalili ba. Zan ci gaba da son ki har na tsawan rayuwata, zan kasance a tare da ke ba zan bari ki kuɓuce min ba. Ke tawa ce ni naki ne, fatan zaki amince mu rayu tare rayuwa ta har abada? Ina Son Ki.
Son ki na bayyana kullum a cikin zuciyata, tamkar yadda rana ke futowa a sararin samaniya, ya yaɗu a cikinta ya kawata ta, fiye da yadda taurari ke kawata sararin samaniya a cikin dare. Ina son ki kuma zan cigaba da son ki har zuwa fitar numfashina