Minene Yakamata ayi da Facebook Account din Mamaci, bayan mutuwa ta dauke shi?
Me ya kamata ayi da Facebook Account din Mamaci, bayan mutuwa ta dauke shi?
___________________________________
Akwai sauka (Going Offline) daga Facebook da in muka yi shike nan mun sauka kenan, babu Wanda zai sake ganin mu Online, mun fita daga duniya Kuma munyi logout din karshe daga kafar sadarwar Facebook.
~ Idan ‘dan uwan ku ya rasu yaya za kuyi da Facebook Account din sa?
Abu na farko shine, kuyi login zuwa Account din, kuyi sanarwa kamar haka:
~ “Yan uwa Musulmi sunana (wane) ‘dan uwan (wane) Mai wannan Account, Ina sanar daku rasuwar sa, Kuma an binne shi a Makabartar gari kaza, rana kaza”.
~ “Bayan haka mu ‘yan uwan sa muna rokon yafiya daku yafe masa, Kuma don Allah duk Wanda yake binsa bashi, Rance, idan bai yafe ba ga number wayar mu, ya kira ya tabbatar da hakkin sa dake kan mamacin, idan kuma ya yafe muna godiya”.
~ “Idan kuma wasu kayayyaki ne aka bashi (shi mamacin) azo ayi bayani, za’a same mu ta wannan number……”.
Sa’annan Kuma ku ‘yan uwan mamacin kada ku yarda ku bude Inbox dinsa, chatting dinsa da mutane, sai dai wajen neman Hujja, idan mutum yace mamacin ya karbi kudi a waje na, Kuma ta Facebook muka tattauna batun karban kudin”.
~ Sai kuje Inbox kan Account din wanda yace ya bayar da kudin ku duba chatting dinsu domin ku tabbatar da abinda yayi Da’awa, saboda akwai wadanda idan sun mutu akan ga sun rubuta (Wane yana bina Bashin kudi Naira kaza da kaza) zaku gani a littafin dake rubuta basussukan da ake binsa.
~ To amma baza ku San wanene ba, kuma a ina za’a same shi, zaku ga cewa baku sanshi a garin ku ba, baku sanshi acikin abokan sa na zahiri a gida ba, toh kuyi posting a Facebook dinsa, zasu bayyana muku.
~ Saboda Facebook ya hada abota da yawa, zumunci Mai karfi, ya hada aure da soyayya sosai fiye da yadda baka tsammani. So, abubuwan ta Facebook mutane suke tattauna su a rubuce ko Facebook Voice Note.
~ Idan ba irin wadannan dalilan ba haka kawai ku bude Chatting din da mamacin yayi don kalli wane irin chatting mamacin yayi, wannan kuskure ne, neman sanin sirrin mamacin ne Wanda yin irin wannan bincike binciken zai iya fito wasu abubuwan da ake bukatan rufe su.
~ Domin Manzon Allah yayi wata magana game da wankan Gawar mamaci, Wanda nake ganin maganar bata tsaya a wajen wankan Gawa ba kawai, zata iya shiga har cikin abubuwan da suka shafi irin wadannan kafofi na Sadarwa bayan mutum ya tafi.
~ Manzon Allah yace:
“Duk Wanda yaje wankan Gawa, zai yi wanka wa mamaci, sai yaga abinda ya gani, sai ya rufa sirrin mamacin, Allah zai yafe masa manya manyan zunuban sa guda Arba’in”.
A cikin wata Riwaya yace “Allah zai bashi Ladan shiga Aljannah da kaso 40”.
Wato marking din da ake so Kaci ko samu kafin ka shiga Aljannah, marking 100, to za’a baka 40 daga ciki, idan ka rufe Asirin mamaci daka gani yayin wankan Gawar sa.
~ Shin akwai abinda ake gani ne a tattare da mamaci yayin wankan Gawar sa?
Eh, akwai.
~ Wani lokaci idan aka je wankan Gawa akan ga Gawar mamacin ta canza daga yadda aka sanshi, kamar aga yayi bakikkirin, fatar sa tayi baki fiye da yadda aka sani, ko kuma aga idon sa sun zubo kan hancin sa, ko aga harshen sa ya zazzago yayi tsawo har kan ruwan cikin sa, ko zuwan kan Cibiyar sa, harshe kawai.
~ Ko aji Gawar sa tana wari, Kuma warin daga jikin sa ne, to duk Wanda yaga irin wannan a tattare da Gawar Musulmi sai yayi shiru bai gaya wa kowa ba har Shima ya rasu, to za’a yafe masa manyan manyan zunubbai har guda 40.
~ To Ina Kuma ga Wanda yaje yayi ta bude Chatting din mamaci yana bi, yana so yaga irin chatting din da Marigayin yake yi, watakil zuciyar sa ta saka masa son yaga ko mamacin yana chatting din batsa da mata, ko wasu abubuwan da ba za’a so aga Musulmi ya tafi ya bar su ba.
~ Idan kaga Gawar mamaci tayi muni, ko kaga wasu daga cikin abubuwan da muka ambata a sama, hakan ba yana nufin mamacin ‘dan wuta bane, hakan ba dalili ne akan mutumin banza ne ba, sai dai Gawar batai kyau ba.
~ Sau da yawa hakan tana bayyana ne akan gawan Fasikai na bayyane ko na boye, idan Mala’ikun mutuwa sunyi musu duka kafin su cire ransu. To idan za’a Shari’a zata ce kayi shiru idan kaga wani aibi a Gawar Musulmi bayan Shari’ar ce tace kaje kayi masa wankan, Amma tace kayi shiru, toh ina Kuma ga bude Chatting din mamacin da Shari’a bata ce ka bude ba?
~ Daga karshe, sharwari guda biyu game da Facebook Account din Mamaci zuwa ga ‘yan uwan mamacin:
1. Kada a goge Account din gaba daya (Permanent Deletion), idan mutum ne da yake saka abubuwa na addini da fadakarwa da wayar da kan mutane akan lamuran rayuwa da Ibada.
Ku bar masa Facebook din da Account din, domin ya cigaba da samun Ladan wadannan posting din da yayi game da rayuwa da addini, watakil wadannan posting din su samar masa da Ladan da zai samu Rahama daga wajen Ubangijin sa.
2. Abu na biyu, babu laifi kuje ku bibiyi Public Post dinsa, ku ‘yan uwan mamacin ku goge duk wani posting din da kuke ganin bai dace ba, kamar hotunan mata, videos din kida da Waka, videon din rawa, posting din da yake nuna kiyayya ga wasu ko wani.
~ Bayan kun goge sai ku roki Allah ya yafe masa, ya gafarta masa, ya karbe shi a matsayin bawa Mai neman taimakon Rahama da Yafiya daga Ubangiji.
Sai shawara gare mu wadanda muke Raye a yanzu akan Facebook.
1. Muyi kokari mu dinga posting din da ko yau muka kwanta a Kabari ba zamu bar baya da kura ba, haka chatting din mu.
(Allah kada kasa sai bayan mun mutu mu tuna cewa akwai abinda ya kamata mu goge a Social Media kafin Ajali ya sauka).
Kuma Muji tsoron Allah kada muga mutum Mai kudi ya mutu muje mu kirki karya muce muna binsa Bashin kudi.
2. Abu na biyu, kada mu manta da wannan Ayar a duk lokacin da za muyi rubutu ko Posting a Facebook, Ayar Suratul Israa’ (C-17) V-53, Allah yace:
وقل لعبادي يقولوا التي هي أحسن إن الشيطان ينزغ بينهم إن الشيطان كان للإنسان عدوا مبينا
“Kuma ka gaya wa bayi na su fadi magana Mai kyau (da harshe ko da abin rubutu), saboda tabbas Shedan yana rural Wutar fitina a tsakanin su, tabbas Shedan makiyin bayyane ne ga ‘dan Adam”.
Allah yasa mu dace…
Abdul-Hadi Isah Ibrahim.