Hausa Novels

Matar Shege Hausa Novel Part 2

P*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

Related Articles

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 1

 

Ranar bakwai,ga watan d’aya,shekara ta dubu biyu da goma sha shida,ita ce ranar da littafin k’addarata ya fara bud’ewa,ranar da na shiga cikin damuwar da ba na tunanin zan fita har abada!

Zaune na ke a cikin adaidaita sahu,kan hanyata ta komawa briged daga gidan yayata da ke unguwar hotoro,kaf hankali na ya na kan wayar da na ke amsawa ta masoyina,wanda yau watanni biyu ya rage auren mu.

“Y’an mata don Allah zan shiga nan,na kar’bawa maigidana sak’o”

Na ji muryar mai adaidata sahuna

Sai na kai duba na ga laundry (wurin wanki)d’in da ya ke nuna min,na ce”ok”

Tsautsayi ba ya wuce ranar sa,da na san zan ga abin da na gani yanzu me zai fito da ni yau? Wata bak’ar mota ce ta ke k’ok’arin fakin a wurin,duk da ban san tsadar motoci ba na san wannan dai ba k’arama bace,ya yi minti uku da fakin ga shi dai ya bud’e murfin motar amma bai fito ba,haka ne ya sa ni sake tattara duk hankali na wurin ganin wannan mashahurin.

A kan idona ya fito daga cikin motar,gabana ya fad’i daga yi masa kallo d’aya tak!

Fari ne tass,mai manyan idanuwa ,farare tas kamar bai ta’ba yin kuka ba,ba wani dogon hanci ne da shi ba,madaidaicin bakinsa ya hau sosai da zagayayyiyar fuskarsa,
Bak’ar riga ce a jikinsa da bak’in wando iya k’wauri,ga wani bak’in agogo da ya yi wa farin hannunsa kyau sosai

Ba k’aramin tafiya da imanina ya yi ba,nan take na ji wani irin yanayi a zuciya da gangar jikina,na yi wata kasalalliyar ajiyar zuciya,ina kuma k’are masa kalllo

Yamutse fuska na ga ya yi,tare da kai hannunsa kan gashin kansa da ke ta shek’i da alama ya sha gyara har ya gaji,ya wani hautsina sumar wanda na ji kamar da gayya ya yi,don kuwa wani irin kyau na ga ya k’ara,kai ka ce ba d’an Nijeria ba ne,wallahi ban ta’ba zaton a kwai irin kyawawan nan a garin Kano ba

Mota ya koma,ko shiga ciki bai yi ba hannu kawai na ga ya mik’a ya ciro wata jar facing cap ya saka.

Wanda ya yi daidai da dawowar mai  adaidata sahu na,hannunsa d’auke da wata jaka

Ina kallo matashin ya shiga wurin,ya na ta b’ata rai.

“Yi hak’uri hajiya,na ‘bata miki lokaci” Mai adaidaitar ya fad’a

Na yi guntun murmushi lokacin da mu ke wuce wurin na ce”babu komai”

Sai da mu ka d’an yi tafiya,na ji muryarsa”sunan shi Salim,shi ne mai wurin wankin nan,kuma shi ne me wurin cin abincin nan na sabin sati(seven thirty) ba shi da kirki,kuma ya na shan sigari,an ce ya na da kamfani a sharad’a,wanda da kan shi ya ke kula da shi,kuma gidan su ma a can ya ke”

Ban yi mamakin maganganun sa ba,don na san ba ya rasa nasaba da irin kallon da ya ga ina yi wa wanda ya kira da Salim d’in

“Hmm!” Na sauke ajiyar zuciya kafin na ce

“Ba ka san wani abun ba game da shi bayan wannan?”

“Abin da na sani kenan” Ya fad’a

“Ba ka da number shi?” Na tambaya zuciyata na bugu

Ya yi dariya ya ce”tabb! Wane ni?”

Cikin zak’uwa na ce”to don Allah maida ni wurin, idan ya fito ka bi min bayan sa”

Mai adaidaita ya yi wata irin juyowa ya zaro ido kafin ya ce”ki rufa min asiri,ban shirya mutuwa ba,y’an mata ina da iyali”

Ni ma y’ar dariya na yi na ce”don ka bi bayan shi sai ka mutu?”

Ya ce”to me zai hana? Ko ban mutu ba na san zan sha wuya,ke watak’il ma na k’are rayuwata a gidan yari”

Dariya kawai na yi na ce”hakane”.

“Amm…ka ce ya na shan sigari? Ta ya ka san da hakan?”

Na yi tambayar da zumud’in jin amsar da zai bani.

Mai adaidaita ya ce”eh,sau biyu ina ganin shi a wurin nan ya na zuk’a,da alama ta bi jikinsa don ya na sha a gaban kowa”

Na jinjina kai kafin na ce”Allah ya shirye sa”.

Har mu ka k’araso unguwar mu ban kuma magana ba,na fad’a duniyar tunanin Salim.

Da sallama na shiga gidan,na tadda Mama Saude ta na tsintar shinkafa,ga wutar murhun da ta kunna sai hayak’i ta ke yi,gidan duk ya kaure da k’auri
.Mama Saude matar mahaifina ce,bai jima da auro ta ba,sakamakon rabuwar su da mahaifiya ta,wanda ni ce silar rabuwar,a duk lokaci da na tuna da haka na kan shiga damuwa,wata rana ma har hawaye na ke yi.

Mama Saude ba ta da kirki,sam ba ta k’auna ta kullum cikin ganin ta had’a ni da mahaifina ta ke,gashi shi kuma duk abin da ta fad’a masa yarda ya ke yi,ya hau kai ya zauna ya yi ta surfa min masifa. Ko da ya ke ban cika ganin laifin sa ba,tun da nawa laifin ya fi yawa,ba na jin magana ko kad’an,shi ya sa ma a k’a k’agauta na yi auren kowa ya huta.
Hmm! Nan gaba dai za ku ji ko wacece ni.

Ban ko kula Mama ba,na shige d’akina da ba wani tarkace ne a ciki ba,wulli na yi da jakata ina fad’awa kan katifa ta.

Kiran sallar la’asar ne ya tashe ni daga guntun baccin da na tafi,kai tsaye wanka na shiga na fito na d’aura alwala,ina dab da shiga d’aki na ji sallamar Mama ta shigo cikin gidan,ban amsa ba sai tsaki da na ja,ina mamakin irin halin Mama Saude,wai ta san sarai bacci na ke yi amma sai ta yi ficewar ta,ba ta ko karo k’ofar gidan ba,yanzu idan wani ya shigo ya yi min sata kuma fa?

“Allah ya kyauta” Na fad’a ina k’ok’arin shigewa d’aki

Ban kai ga shiga ba na jiyo muryar ta”ke! Uban wa ki ke fad’a wa hakan?”

Banza na bawa ajiyar ta na shige d’aki,don idan na kula ta sai mu kai magriba mu na yi,ko kad’an ba ta gani ta kyale,kuma ba ta gajiya da mita ni ma yau d’in Allah ya sa ba y’an rashin kunya bane a kaina,da haka zan biye mata mu yi ta yi,wannan ya zama jiki kusan kullum sai mun yi,kamar kishiyoyi ko facaloli haka mu ke ni da ita,shi ya sa ma ban fiya zaman gidan ba na gwammace na fita yawona,idan na dawo na sha fad’a a wurin mahaifina.

*Zinatu* kenan,matashiyar budurwa mai ji da kanta,y’ar kimanin shekara ashirin cif,ta kammala secondary tun shekaru uku da su ka wuce,islamiyya kuwa tun tuni ta ajiye ta a gefe,babu yanda ba ta yi da Baban ta ba kan ya bar ta,ta cigaba da karatu ko y’ar digiri ta samu,amma ya ce sam ba zai yi wu ba,a rashin jin maganar ta bai ga dalilin da zai sa ta je makarantar gaba da sakandari ba,don kuwa ya na jin tsoron had’uwar ta da maza,da kuma gogaggun mata,saboda Zinatu ba ta jin magana.Allah ya yi wa Zinatu farinjinin masoya,don duk inda ta shiga sai wani ya k’yasa,ita kuma mutum ko kad’an ba ta sauraron maza,don duka ma ba ta yarda da soyayya ba,wahala kawai ta d’auke ta,haka ne ya sa ta dad’e ba ta tsaida mijin aure ba.

Ba ta da k’awa ko d’aya,sai abokai maza sun fi a k’irga,ita kowa nata ne in dai namiji ne,hakan ne ya sa mutane su ke yi mata kallon ballagaza,wasu ma har su na zargin ta da wani mummunan halin.

Ban gama tsinkewa da lamarin Salim ba,sai da dare ya yi na zo bacci,don kuwa yau duk saurin bacci na sai na neme shi na rasa,hoton fuskar Salim ya yi ta dawo min kamar dai maza bak’ina ne? Sai da na tashi na d’akko k’ur’ani na fara karatu,kafin na fara jin baccin.

Kiran sallar asuba a kunnena,na tashi na yi sallah na koma na kwanta,don baccin yau bai is he ni ba.Shuuu! Na ji Baba ya kunna rediyon sa me hanani komawa baccin safe,na ja tsaki ina shirin sake yin juyi na jiyo muryarsa

“Zinatu! Ke Zinatu!”.

“To fa! Babu lafiya,Allah ya yi dare gari ya waye”. Na fad’a a bayyane ina tashi na saka hijjabi na fito

Zaune na tadda shi a k’ofar d’aki,Mama kuma ta na ta gyare-gyaren wurin sana’arta,da ya ke ta na saida wainar shinkafa da k’uli kullum da safe.Na gaisheta ta amsa a d’ak’ile,na kalli Baba da ya ke nuna min gefen sa,alamar na zauna.

“To ni Zinatu! Allah ya fitar da ni!”. Na fad’a a zuciyata,don kuwa in dai ka ga Baba ya min irin kiran nan da zai bani wurin zama to akwai magana,ko dai zai min fad’a ko kuma nasiha,ille kuwa! Ban gama tunanin laifin da na yi ba,na tsinkayi muryarsa

“Yanzu Zinatu irin rayuwar da ki ka za’bawa kanki ki na ganin za ta kai ki tudun tsira?”

“Subhanallah! Baba me na yi kuma? Ko dai an sake had’ani da kai ne?”. Na yi maganar ina yiwa Mama kallon gefen ido.

Tuni Baba ya tsuke fuska,ya fara magana” yanzu a masallaci a ke fad’a min an ganki jiya wai maza su na koya miki keke,haba Zinatu! Ke me yasa ba kya gudun bakin duniya wai? Kullum burinki ki jawo min abin magana ko,a yi ta nuna ni a gari a na ga mahaifinki ko? Don Allah ki rufa min asiri na aurar da ke lafiya,sauran y’anuwanki dai ba mu yi haka da su ba”.

Yanda ya k’are maganar da sanyin murya sai ya bani tausayi,don ni kaina ina tausayin Baban yanda ya ke ta k’ok’arin ganin na nutsu

“Ka yi hak’uri Baba,zan daina in sha Allah, sai a yi ta saka ni cikin addu’a”.
Na fad’a ina tashi na koma d’akina,ba tare da na jira abin da zai ce ba.

“Kar ma ki daina! Ni kam shi ya sa na matsu ki bar gidan nan ko na huta,da ganin takaicinki”

Mama Saude ta yi maganar ta na jan tsaki.

Katifa na fad’a ina murmushi,tunowa da Anas da ya ke fad’a min tunda na fad’i sau uku ba zan ta’ba iya keken ba.

“Allah ya shiryi y’an gulma” Na fad’a ina rufe idona,tuni bacci ya sureni.
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 2

Ringing d’in wayata ne ya tasheni,na wartsake da hayaniyar masu siyan waina,ban fara kawo tunanin komai a raina ba sai na Salim,rintse idona na yi ina sake tuno yanda na ganshi,na d’an jima a kwancen ina sak’e-sak’e kafin na tashi,ban kalli wayar ba bare na duba me kiran,na saka k’aramin hijjabi na fita don shiga wanka.

Karin kumallo bai dameni ba,to ina ma na ke da gatan da za a bani? Mahaifiyata ce kawai me min tilas na ci abinci,ko na rana ma ni ce na ke yin girkina,don tuni na samawa kaina y’anci daga wulak’ancin Mama akan abinci,idan na rage kuma na mik’a mata,babu kunya ta ke kar’ba ta ci,don babu laifi ta na da kwad’ayi.

Hoda kawai na shafa,bayan na shirya cikin doguwar riga ta atamfa,na yafa wadataccen mayafi,na saka takalmi, na d’auki jaka,ina dab da fita na sake jin ringing d’in wayata

“Y’ar wahala,har na manta da ke”. Na fad’a ina d’akko ta,kamar yanda na zata Habib ne me kiran

“Wahala ta aure ka,tunda ka nace”. Na yi maganar kafin na daga kiran.

“Hmmm!”. Ya sauke ajiyar zuciya,kafin ya ce,
“Saura k’iris zuciyata ta fashe Zinatu”.

“Har dagargajewa sai ta yi” Na fad’a k’asa-k’asa.

“Me ki ka ce?” Ya tambaya

Na yi guntun murmushi na ce”me ya hana ka zuwa jiya…?”

“Wane ni da taka umarnin ki? Na kira ba ki d’aga ba, kuma kin gargad’e ni na daina zuwa sai na sanar miki”.

Na yi murmushi na ce”hakane fa! To ya kake?”

“To gani nan dai,lafiya ba lau ba,wallahi Zinatu ba na jin nutsuwata za ta dawo idan ban mallake ki ba,wata biyun nan jin sa na ke kamar shekara biyu,kuma…”

Na yi saurin katse shi da fad’in”kai! Dakata,na ga ka d’ebo fira,ni kuma wani uzurin na ke ka katseni,ka zo yau da daddare sai mu yi zancen ko?”
Ban ma jira cewar sa ba na katse kiran,na jefa wayar a jaka,na fito na na rufe d’akina da mukulli.

“To sai ina kuma?” Mama ta yi maganar daga y’ar rumfar da ta ke suya.

“Inda Allah ya nufa”. Na bata amsa ina ficewa daga gidan.

Kai tsaye gidan su mahaifiyata na nufa,a d’aki na tadda ta ta na shara,na zauna ina gaishe ta bayan na kar’bi sharar na k’arasa mata.

“Zinatu!” Ta kira sunana a nutse

“Na’am Ummi” Na amsa ina maida hankalina wurin ta.

Sai ta ce min”anya da gaske za ki yi auren kuwa?”

Na yi d’an murmushi na ce”me ki ka gani Ummi?”

“Na ga kamar ba kya shiri,ga abu sai matsowa ya ke”. Ta fad’a ta na tashi ta d’akko min leda wai tukwane ne ta siya min,za ta had’a da wancan kayan.

Sai na yi murmushi na ce”Na gode Ummi,Allah ya saka”.

Ba ta amsa min ba ta tashi ta had’a min shayi,ta mik’o min,na sha fin rabin kofin,sannan na tashi ina yi mata sallama.

“Ba za ki gaida kakar ki ba?” Ummi ta tambaye ni.

Na d’an cukume,don ba ma shiri da mahifiyar Ummi,ni fa duk wanda zai fad’a min gaskiya bayan mahaifiyata,to fushi nake yi da shi.Labulen d’akin na d’aga ko sallama ban yi ba,zaune na ganta ta na linkin kaya,na saki labulen kawai na juya,duk da mun yi ido hud’u da ita,sai na d’an d’aga murya ina fad’a wa Ummi bacci take yi.

Na d’an jima tsaye a bakin titi,ba wai abin hawar na rasa ba,a’a kawai ina jinjina wurin da zuciyata take bani umarnin zuwa ne,daga baya dai na yi shahada na tari adaidaita na antaya,ina fad’a masa inda zai kai ni.

Daidai wurin da na ga Salim ya faka motar sa jiya na tsaya ina waige-waige,amma ban ga ko mai kama da motar ba,cikin k’arfin hali na shiga wurin ina had’e gira,don kar ma wani ya kawo min raini.Ma’aikacin da na fara cinkaro da shi na tambaya”don Allah Salim ya shigo?”

Sai ya zaro ido ya ce”waye ya ce miki kullum ya ke zuwa?”

Na sake had’e rai na ce”mun yi da shi ne za mu had’u a nan,na yi mamakin rashin zuwan shi”

Na yi maganar ina daddana wayata,na kara a kunne,tsaki na ja na ce”ka gani ko? Tun d’azun na ke kiran shi a kashe,kuma shi ma yau ya na son ganina dole,kai Salim matsala ne!”.

“Mu ga lambar?” Ya tambayeni.

Na d’an ji dam,amma ban nuna ba,na maze na ce”mu ga ta wayarka?”

Babu musu ya mik’o min wayar bayan ya nemo lambar,na ji wani farinciki na kalli lambar na ce”ka ga kuwa ba ita bace a wayata,shi dai ban san adadin lambobin shi ba,kamar d’an kidnapping”.

Tass! Na kwafe lambar,na bashi wayarsa ina yi masa godiya.Cikin farinciki na fita daga wurin kamar an yi min albishir d’in cikar wani babban burina.

Saving d’in lambar na yi da Salim na jefa wayar a jaka ina murmushi.

Kai tsaye kasuwa na nufa,na yi siyayyar abin da ba ni da shi na kayan abinci,na yi cefane na har da kaza,saboda yau ina cikin farinciki.A tsakargida na tadda Mama ta na tsintar shinkafa,duk sallamar da na yi ta rangad’awa ba ta kalle ni ba,bare ta amsa,da alama dai yau tambotsen take ji,murmushi na yi na shige d’akina,ba tare da na yi mata magana ba.

Tunda na fara aikin girkin Mama ba ta kalli inda nake ba,ta na ta fama da hura murhu,ga shi bakinta ya k’i mutuwa sai mita take yi,wai ita ta gaji da wannan bala’in na girki a murhu,na gama abin da zan yi na shige d’aki,don risho d’ina a d’aki yake saboda gudun satar kalanzir da Mama take yi min.Dab da kammala soya miyar na ji Mama ta na k’wala min kira “Zinatu! Zinatu!”

“Ya aka yi?” Na tambaya daga inda nake.

Sai gata ta bankad’o rik’e da roba ta na fad’in”wai da na ga kin fita ba ki karya ba…shi ne na ce to bari na rage miki waina”

Ta min maganar ta na ajiye min wata sandararriyar waina,had’i da lek’a tukunyar miyar da ke kan risho.

Na yi wata dariyar rainin hankali na ce”kin ga Mama…to ina ruwanki da cikina? Yau na saba fita ban ci komai ba?”

Sai ta gyara d’aurin d’ankwali irin na marasa gaskiya ta ce”ai wai da na ga yanzun aure za ki yi…”

“Idan ba na karyawa auren ba zai yiwu ba ko?” Na katse ta.

Sai ko ta had’e rai ta ce”ke ba fa na son raini,don ma kin ga ina lalla’ba ki? To kar ki ci d’in!”

Na yi murmushi ina d’aukar kwano na zuba mata abincin,na mik’a mata”k’amshi dai ki ka jiyo,shi ne ba za ki iya fad’a kai tsaye ba”

Ta k’ar’ba,ta fice ba tare da ta tankani ba.

Bayan na gama cin abinci na yi sallah,sai na kwanta na janyo wayata,wadda ta fara yi min kwarjini saboda bak’uncin lambar Salim da ta samu.Na jima ina kallon lambar kafin na yi k’undunbala na danna kira.

Har ta katse bai d’auka ba,hakan ya sa na sake kira a karo na biyu,nan ma dai amsar d’aya ce,aikuwa aiki ya ce min muje! Nan na yi ta jera masa kira,kamar ba gobe,sai kace wani game aka bani,ina jira in yi over.

Sai da na yi guda tara cif! Ina shirin yin na goma na ga shigowar sak’on shi.

Da hanzari na duba don na ji ko wani uzurin zai bani na rashin d’agawar shi

_”Waye ne?”_ Abin da ya ke rubuce a sak’on kenan.

Na yi saurin mayar masa da amsa kamar ya sanni na ce _”Zinatu ce”_.

_”Wace kuma haka? Daga ina?”_ Ya sake tambaya ta.

Tsaki na yi na sake kiran lambar ko zai d’aga,na yi sa’a kuwa ya d’aga,na wani kashe murya don gaskiya ba ni da zak’in murya na ce”Assalamu alaikum”.

Tsaki na ji ya ja,a maimakon amsawa ya ce”malama tafi kai tsaye ba ni da lokacin shirme!”.

“Subhanallah!” Na fad’a a zuciyata,da alama dai zai yi wulak’anci.

Sai da na yi gyaran murya sannan na ce”Zinatu ce”.

Ya sake jan wani tsakin ya ce”kin kirani ne don ki koya min sunanki? To na haddace,menene wai?”

Gabana ya d’an fad’i,na shiga tunanin abin da zan fad’a masa,don ni kaina na san ba ni da wani dalili me k’arfi,na yi ta maza na ce”amm…jiya na ganka za ka shiga laundry,sai na ga ka burgeni,na so na yi maka magana ban samu dama ba,to kuma da daddare…”

K’itt! Na ji ya kashe wayar,tun kafin na k’arasa,na yi saurin sake kira amma sai na ji ta k’i shiga,ina dai zargin a blacklist ya sakani.

Na yi shiru ina nazarin yanda zan yi,kamar wadda aka min umarni, na fara rubuta masa sak’o kamar haka,

_”Idan ba ka ji dad’in maganata ba ka yi hak’uri don Allah,in sha Allah ba zan sake yi maka makamanciyar wannan maganar ba”_.

Ina ta jiran amsar shi amma shiru,kamar an aiki bawa garinsu,ina nan zaune ina nazari har aka kira la’asar ,na tashi na gabatar sannan na yi wanka na saka hijjabina har k’asa na fita waje,kai tsaye gidan su Hamza na yi,na tsaya a k’ofar gida na yi sallama da shi,a nan dakalin k’ofar gidan mu ka zauna mu na ta fira kamar abokai,sai magriba na tafi gida,don Habib ya fad’a min ana sallar isha’i zai shigo.
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 3

 

Habib d’an’uwana ne,mahaifinsa da mahaifina uwa d’aya uba d’aya suke,a unguwar Tudun wada gidansu ya ke,kuma shi ne babba a gidansu,ya na da k’annai mata harda sa’anni na,amma ba ni da wata mu’amula da su,sai dai idan mun had’u a sabga ta y’an’uwa mu gaisa.Ya na so na tun ina cakuikuya ta,tsananin son da ya ke min ne ma ya sa ya fara bani tausayi har na ke sauraron shi,don idan na ce ina son Habib na yi k’arya,sai dai zan iya cewa ya na burgeni da kuma k’auna ta jini.Shi likitan ido ne a asibitin Nasarawa,ba k’aramar wuya ya ci ba wurin shawo kaina har na amince da auren shi,kuma sosai ya ke bin duk wani sharad’in da na gindaya masa kamar mahifiyarsa,duk wata sai ya k’irga dubu goma ya bani,ya ce na yi k’ananun buk’atuna,duk dan kar abun hannun wani ya hure min ido,nasiha ba ranar banza sai dai idan bai zo ba.

Tun ranar da aka saka ranar auren mu,ya tare abokaina Anas da Hamza,wanda na fi shak’uwa da su duk cikin abokaina,ya yi musu gargad’in babu su babu ni,kar ya sake ganin sun kula ni.

Anas ne ya zo har gida ya ke fad’a min,aikuwa nan take na yi wa Habib kiran gaggawa.Aikuwa ya sha madarar bala’i ranar,sosai na nuna masa muhimmancin abokaina,na gargad’e shi kan ko kallon banza ya yi wa wani daga cikin su,to a bakin auren shi,don wallahi a ranar zai kar’bi kud’in auren shi.Nan ya yi ta bani hak’uri, duk ya rikice,har ya so bani tausayi ya ce ya ji,ya yarda,babu ruwan shi da su.

Bayan isha’i ya zo,mun d’an jima muna fira har ya ke sanar min wani satin za a kawo kayan lefe,shirin sa kawai ya ke cikin zumud’i,da farinciki.Ni kuwa tsakanin farinciki da akasin sa ban san wanda zan ce ina ji ba.

K’arfe goma na dare na sake gwada lambar Salim amma har yanzu ba ta shiga, ni sai yanzu na ga ragon azanci na,da ban tambayi wurin da aka ce ya ke aiki ba, sak’o na aika masa kamar haka _”Amincin Allah ya tabbata a gareka,ina yi maka fatan alkhairi,da kuma fatan dawwamar farinciki a zuciyarka,murmushi ya tabbata a kyakkyawar fuskarka har abada”_,
_”Daga Zinatu”_.

Na yi murmushi kamar ina da tabbacin ya gani,na yi addu’a na kwanta da tunanin sa.

Salim ya na zaune ya na chatting sak’on ya shigo wayarsa,ta’be baki ya yi bayan ya gama karantawa,ya na jinjina haukan wasu matan.

Washegari tun da safe na aika masa sak’on fatan alkhairi,kuma na sake gwada kiran layin nashi bai shiga ba,don haka na fita na siyo sabon layi, ina saka shi a waya,ban yi sanya ba na loda kati nadoka wa Salim kira,lokacin k’arfe goma da rabi na safe,har ta katse bai d’auka ba,hakan ya sa na sake danna wani kiran,sai ya d’aga da sallama, na tashi zaune k’irjina yana bugu,don ban shirya abin da zan fad’a masa ba,tunda ban yi zaton zai d’aga ba,haka na daure na amsa sallamar sannan na gaishe shi,ya amsa kafin ya ce”da wa nake magana?”

“Zinatu ce,don Allah ka saurareni”. Na fad’a ina fargabar zai saurareni ko zai kashe wayar?

Guntun tsaki ya yi kafin ya ce”to ya aka yi? Ki na ta takura min fa,za ki fara shiga hakkina!”.

Da d’an fad’a ya yi maganar,hakan ya sa ni nutsuwa,na d’an yi nazari na y’an sakanni,can na tuna me adaidaita sahun nan… ya fad’a min shi ne yake kula da kamfanin su na Sharad’a,sai na yi saurin fad’in”e… dama akan kamfanin ku ne,na Sharad’a…”

Na d’an dakata don na ji yanda zai d’auki zancen,amma sai na ji ya yi shiru,alamar ya na jira na cigaba

Cikin in’inar da ban san ina da ita ba sai ranar na ce”e da dama, shi ne na ke son…na yi siyayya”.

“Siyayya ta me?” Ya tambayeni.

Nan fa k’irjina ya bada ras! Na rasa abin fad’a, tunda ban san sunan kamfanin bama,bare na san abin da ake siyarwa,wannan fa shi ne ga k’oshi ga kwanan yunwa,ga shi ya bani lokacin sa,kuma damata ta na neman kufce min,to aiki ne na fara shi sama ta ka babu shawara…

“Ina da abin yi fa” Muryarsa ta katse min tunani.

Dabara ta fad’o min na ce”idan babu damuwa mu had’u a office mana?”

Ya ce min”ai dole sai na ji yanayin cinikin naki,idan babu yawa ba sai kin ganni ba ma,don yau ina hutu ba na zuwa kamfani”.

Na d’an tsorata,don ba na son ya taro jirgina,hakan yasa na yi ta maza na ce”gaskiya da yawa,don za mu yi wajan mota uku”.

Sai da na kai k’arshe kuma na ji tsoro,yanzu idan gwalagwalai suke siyarwa fa? Shi ne zan siyi mota ukun? Lallai na iya tarar aradu da ka!

“Zan iya ganinka?” Na fad’a, jin ya yi shiru.

“Ok,gobe litinin sai ki shigo k’arfe d’aya na rana”

Ya katse kiran,bai jira amsata ba.

Hmmm! Na sauke ajiyar zuciya,ina tunanin yanda goben za ta kasance,can kuma sai na zaro ido da na tuna ai ban ma san kamfanin ba,ya ilahi! Yanzu kuma idan na tambaye shi adreshin kamfanin ai na kwafsa,sai ma ya d’agoni,na san dai Sharad’a da girma take,ta ina zan fara neman wani kamfani? Phase 1 zan je,ko phase 2,ko kuma 3 d’in zan yi? Da na san sunan wurin ne ma to da sauk’i,amma gaskiya ba zan tambaye shi ba,don wannan babbar damar da na samu ba zan bari ta kufce min ba.

Da tunanin mafita na yi wunin ranar,ko k’ofar gida ban fita ba,jikina duk ya yi sanyi,ina jiran zuwan gobe.
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 4

K’arfe goma sha biyu na kammala shirina tsaf,har da kwalliya na yi,na baza turare,na yi kyau sosai kuwa,da kuzarina na yi shirin,duk da idan aka kira tafiyar tawa da sauri ba wurin zuwa ba a yi k’arya ba.Ko girki ban tsaya yi ba,don haka na fara biyawa ta gidan Ummi ko zan samu wani abun

Girki na tarar ta na yi,na gaisheta ya amsa ta na tambaya ta inda zan je,na ce mata babu inda zan je,na zo gaisheta ne kawai

Ta ce”to tashi ki daka min yaji,dama ba son dakan nake ba”.

Na d’an kalli agogo,na tashi na ajiye mayafina na hau dakan,ina ta sauri kar lokaci ya yi ban k’arasa ba,bayan na gama ma sai da ta bani yankan salak,abincin ma kad’an na ci,saboda sauri,na ce mata gida zan koma akwai aikin da zan yi.

“Sharad’a” Na fad’a bayan na shiga adaidata sahu

Sai da muka d’au hanya na ji ya ce”phase 1?”

Na ce”ka san wani kamfani a can? Sunan me kamfanin Salim”

Ya ce”na meye kamfanin?”

Na furzar da iska na ce”wallahi ban sani ba”

Ya ce”ai dole sai na san ko na meye,kafin na san sunan me wurin.Yanzu ina za mu yi?”

Na yi jim,kafin na ce”kai ni Sharad’an kawai”

Ya ce”to bari na kaiki phase 1 don ya fi yawan kamfani”

“Na gode” Na fad’a ina duba wayata,da agogo ya nuna d’aya saura kwata.

A daidai wani babban kamfani ya saukeni,na ba shi kud’insa ina kallon wurin da aka rubuta ALBARKA FOOD’S LTD da manyan bak’i,har ya ja mashin d’insa zai tafi na yi saurin tambayar shi na ce”don Allah nan d’in me da me su ke yi?”

Ya ce”kema kamar ba y’ar Nigeria ba? Ai duk wani nau’in kayan abinci taliya,macaroni, couscous, shinkafa,da kika ga an saka ALBARKA to a nan ake had’a shi”

Na sake kallon wurin,ina jinjina kai alamar gamsuwa,sannan na ce”kuma baka san sunan me kamfanin ba?”

Ya ce”ai sananne ne,na san shi,sunan shi Muhammad, amma am fi ce masa Oga Js”.

Na d’an tab’e baki na ce”gaskiya ba shi bane,na gode”.

Gaba na k’ara,ina ta kalle-kalle kamar y’ar k’auyen da ta fara zuwa birni a ranar,duk kamfanin da na gani komai girman sa ko k’ankantar sa sai na tambayi me kamfanin,ni dai ban ji kamfanin Salim ba,ban yi aune ba na ji kiran sallar azhar,na yi saurin duba wayata na ga k’arfe d’aya da rabi

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Na furta,ina jin bak’inciki,yanzu ya na can ya na cewa na yi masa African time. Na yi ta zagaye a Sharad’a har biyu da rabi,ganin zan yi asarar lokacin sallah na hak’ura na tari adaidaita na koma gida,takaici kamar zan yi kuka

A gajiye lik’is na shiga gidan,ko sallama ban yi ma,don gani nake da na bud’e baki da nufin magana to kuka ne zai biyo baya,sai dai ina shiga na ga abin da ya k’arasa d’ugunzuma zuciyata

Hauwa ce y’ar Mama tsaye a k’ofar d’akina,sanye da doguwar rigata ta yi rolling da mayafina ta na ta d’aukar kanta a hoto,na daskare ina kallon yanda ta ke malkwad’e-malkwad’e kamar musaka,takaici ya rufeni,cikin k’araji na ce”bura’uban nan!”

“Hauwa! d’akina,kika shiga ki ka d’akko kayana,kika saka?”

Ta juyo da sauri,cikin rashin gaskiya ta kalleni,sai kuma ta had’e rai ta zo za ta shigeni,na funcukota na wanke ta da mari,ta d’aga hannu za ta rama na murd’e hannun,aikuwa ta cakumeni mu ka shiga bawa hammata iska,kamar y’an dambe,na yi mata matsiyacin duka don na fita k’arfi,kuma na girmeta,na yi mamakin rashin fitowar Mama,har muka gama,na shige d’aki,Hauwa ta na ta zagina,ni dai ban sake kulata ba,na yi wanka na yi alwala,na tada sallah

Ina sallamewa na ji shigowar Mama gidan,ashe duk budurin da muka yi ba ta nan “Hauwa! Kin gama shirin kuwa? Ko sai ta dawo kina shashanci?”

Ni dai ban fito ba,ban kuma san amsar da ta bata ba,sai can Mama ta shigo d’akina cikin kwantar da murya ta ce”haba Zinatu,Hauwa ai k’anwarki ce,meye kuma don ta rab’i arzik’inki? Wannan ma ai wani girman ne,saurayin ta ne ya ce zai zo su je gaida hajiyarsa,to sai naga tunda masu hali ne bai dace ta je a tsiyace ba,shiyasa na ce ta ari kayanki ta sa,idan ta dawo sai ta wanke miki”

“Na ji!” Na fad’a a tak’aice.

Ta tashi ta fita,ta na min godiya,sai kuma na ji ban kyauta ba,na ma rasa meyasa na harzuk’a haka,kodayake dama a k’ufule nake,kuma ta k’ara b’atan rai da ta shareni

Kwanciya na yi,ina jin yanda k’afafuna suke amsawa,saboda yawon da na sha,na yi zaton ma Salim zai kirani ya tambayi dalilin rashin zuwana,amma sai na ji shiru,ni kuma ban kira shi ba,don ban san abin da zan fad’a masa ba

Zuciya duk a jagule na yi wunin ranar.Na yi ta nazari kafin na samu mafita,wadda nake fatan ita ce kawai za ta sadani da Salim idan na samu dama.

Washegari goma na safe a laundry d’in su Salim ta min,ko gidan Ummi ban je ba,don kar yau ma ta zaunar da ni.Kai tsaye na shiga,na yi ta dube-dube kafin na ga wanda ya bani lambar Salim,sai na yafito shi da hannu,na ja gefe na tsaya,ya zo muka gaisa,na d’an yi jim kafin na ce,
“Magana nake son yi da kai me muhimmanci”

“Ina jinki” Ya fad’a ya na min kallon sama da k’asa.

Na ce”don Allah ina son duk wani bayani akan Salim da rayuwarsa”.

Ya d’age gira alamar nazari sannan ya ce”ke d’in wacece? Kuma meyasa ki ke son sanin Oga Salim?”

Na furzar da iska na ce”ba ina shirin cutar da shi bane,kawai ya na burgeni ne,kuma ina son shiga rayuwar shi”.

“Ko gwamnati ba ta aikin banza”. Ya fad’a ya na yiwa jakata kallon gefen ido.

Duk da na fahimta amma na ce”ban gane ba”

Ya ce”a nawa zan baki bayanan?”

Na ce”dubu biyu ne a jakata”

Ya ce”tabb! Aikuwa y’anmata Salim ya fi 2k,k’ara ki sha bayani”

Na zuge jaka,na zaro dubu uku na ba shi.Ya je ya d’akko kujeru guda biyu ya zauna a d’aya,nima na ja d’ayar na zauna,sannan ya fara kwararo bayani…

“Sunan shi Muhammad Ibrahim Muhammad,an fi kiransa da Salim,wasu kuma su na ce masa Oga Js.Shi kad’ai ne namiji a gidansu,ya na da k’anwa sunan ta Baby,ban san sauran y’an gidansu ba,ita d’in ma na ga su na zuwa nan ne wataran,da alama dai akwai shak’uwa sosai a tsakaninsu”

Na jinjina kai, alamar gamsuwa,ina sake sauraron shi,ya d’ora”wannan wurin wankin nashi ne,J.S shop ma na shi ne,kuma ya na zama sosai a wurin,musamman da daddare,kuma wurin cin abinci na 7:30 ma na shi ne,don an ce yawanci ma da daddare a can yake zuwa ya ci abinci.Akwai kamfanin mahaifin shi a Sharad’a phase I,sunan shi ALBARKA LTD,kuma Salim d’in ma a can yake aiki,a haka za ki ganshi kamar d’an wulak’anci,amma kuma ba haka bane,yana kirki,shi dai kawai ba ya son rainin hankali,kuma ba kowa yake sakarwa fuska ba,a iya sanin da na yi masa,da kuma yanda nake jin labari ba shi da buduruwa ko d’aya,kuma ya na shaye-shaye”

“A yanda na ji duk gidansu babu me zaman banza,ance ita ma Babyn ta na da wani wurin gyaran jiki a nan Sharad’an,na dai manta sunan wurin”.

Na jinjina kai,ina tunanin ashe jiya kamfanin na shi aka kaini,na wuce shi a rashin sani

Na ce”na gode sosai, na ji dad’in bayanan ka,ba wani abun kuma?”

Ya ce”e to,zan iya baki hotunan shi,ina da su kala uku,biyun a ranar birthday d’insa na ga ya d’ora a dp,ya na girmama birthday sosai,d’ayan kuma drivern sa ne ya tura min,da yake abokina ne”

Da sauri na bud’e xenda ya tura min,sannan na rok’e shi lambar abokin na shi,da ya ce drivern shi ne,ya saka min,na yi masa godiya,na bar wurin da mad’aukacin farinciki.
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 5

 

Gaskiya na ji dad’in had’uwa da wannan ma’aikacin,ni sai bayan na tafi ma na tuna ko sunan shi ban tambaya ba,bare lambarsa.Tun a adaidaita sahu nake ta kallon hoton Salim kamar an min dole na haddace kamannin sa kafin cikar mintuna,ya yi kyau sosai fiye da yanda bakina zai iya fad’a, gaskiya shi kyakkyawa ne,sai na ji ya k’ara burgeni fiye da da,na d’aura hoton a fuskar wayata,yanda da na danna zan ganshi,ba sai na sha wuyar shiga wurin hituna ba.

Ranar fa na samu assignment,haka na wuni ina k’are masa kallo,ga wani abu da ya ke ta azazzalar zuciyata,wanda na rasa gane ko na mene,kuma gabana ya na d’an fad’uwa idan na tuna da shi.

Gidan Ummi na wuce don na fad’a mata zancen kawo lefe ranar Juma’a,ina shiga na ci karo da Kawu Ummaru k’anin Ummi,ya na shirin fita daga gidan,na d’an rusuna na gaishe shi,ya amsa har ya wuce ya juyo ya ce”ke Zinatu,kamar ke na gani jiya a cikin adaidaita sahu wajan Sharad’a?”

Na ji fad’uwar gaba,don shaf na manta a wajejen yake aiki,na yi saurin fad’in”a’a Kawu,sai dai ko kama”.

Ya gyad’a kai ya wuce,na sauke ajiyar zuciya na shige.Bayan mun gaisa da Ummi na fad’a mata Habib ya ce ranar Juma’a za a kawo lefe,Ummi ta ce”too! Ikon Allah,to Allah ya kaimu”

Na amsa da”amin”.

Na ce”Ummi ai dai nan za a kawo shi ko?”

Ta ce”a’a,gwara dai akai gidan babanki Zinatu,y’an’uwana duk za su je,daga baya sai a dawo da shi nan d’in ko?”

Na ce”to”

Sai ta ce”kira min Halima a wayarki,sai na sanar musu gobe su zo mu yi d’an soye-soyen tarar bak’i”

Na kira na mik’a mata,su na fara wayar Umma ta k’wala min kira,na fita ina had’e gira.Nasihar ce dai take ta min,ga shi dole na zauna na ji,tunda Ummi ta na nan,haka dai na yi ta kallon bakinta don ba komai ma nake fahimta ba, hankalina ya rabu biyu,ina ta tunanin da ya ke shirin aurena

“Zinatu!” Na ji muryar Ummi

“Na’am” Na amsa,ina saurin tashi,don dama Umma ta isheni

Sai dai ina shiga wurin Ummi, na yi saranda ganin yanda ta k’urawa fuskar wayata ido,na ji wata fad’uwar gaba,tuni na fara tunanin amsar tambayar da ba a kai ga jefo min ba

“Zinatu wannan kuma waye?”. Ummi ta tambayeni

Na yi murmushi na ce”kai Ummi! Saif Ali Khan ne fa,wannan na fiml d’in indiyan,ba ki gane shi ba?”

Na fad’a ne ba don suna kama da Salim ba,sai dan shi d’in ne kawai sunan shi ya zo kaina

Ummi ta ce”to ni da kallo bai dameni ba? Yanzu kalle-kalle ki ka koma kenan,maimakon k’arfafa ibadarki,tunda ba islamiyya kike zuwa ba?”

Na ji dad’in yanda ta yarda da ni,ina kwanciya a katifa na ce”a’a fa Ummi,kawai burgeni ya ke yi wallahi”.

Ummi ta rik’e hab’a ta ce”e lallai! Ke da za ki yi aure nan da wani lokaci,shi ne har wani ya ke burgeki?”

“Uhm! Inji me ciwon baki” Na fad’a yanda ba za ta ji ba.

 

“Abba,ka d’an k’ara min lokaci zan zab’a nan ba da jimawa ba in sha Allah!” Salim ne ke yiwa mahaifin shi maganar cikin son kwantar masa da hankali.

Abba ya ce”yawwa yaron kirki! Ba wai ina son takura maka bane ba fa,amma ina son ka fahimci shi auren zai k’ara maka nutsuwa da hankali,kuma kamalarka za ta k’ara cika,babu mamaki ma ka daina wannan d’abi’ar taka…”

Salim ya sunkuyar da kai ya ce”Abba na daina fa…”

“Za dai ka daina,tashi ka tafi Allah ya yi maka albarka”. Mahaifin nashi ya fad’a ya na murmushi.

Bai jima da shiga d’aki ba Baby ta shigo da sallamarta,bakin gadon da ya ke kwance ta zauna,ta rik’o hannunsa ta matse kafin ta ce” Bros tashi mu yi magana,na san ba bacci ka ke yi ba”.

Ya bud’e ido,ba tare da ya kalleta ba don kar ta fahimci halin da ya shiga,ya ce”Baby! Ina lafiya,ki je ki huta,za ki rakani J.S anjima”.

“Ba zan je ba!” Ta fad’a da k’arfi.

“Dama na sani,matsalarka kenan Bros,haba! Kai fa namiji ne cikakke,son kowa k’in wanda ya rasa,akan me za ka na wahalar da kanka akan wacce ba ta da imani? Ta na neman lalata rayuwarka,amma ka k’i fahimta,na tsaneta!”

Sai ta fashe da kuka,ta tashi ta bar d’akin a guje.Ya yi saurin durowa daga gadon ya bi bayanta.

 

Ranar Juma’a aka kawo kayan lefena,akwati shida da manyan jakankuna guda biyu,cike da kaya kowa ya yaba da k’ok’arin Habib,kuma aka tsayar da rana sati shida masu zuwa

Hmmm! Sati shidan da suka zame min kamar shekara shida,a cikin sati shidan nan komai ya faru,idan na ce komai ina nufin komai da komai,a cikin wa’innan satuttukan ne na aikata kurakurai da dama,wanda su ka jefani halin da nake ciki a yanzu,ko ma na ce k’addara.

To k’addara mana! Duk wanda ya ce so ba k’addara bane,to bai tsinci kanshi a irin halin da so ya sakani ba

Kallo d’aya tak! Ya jefani a manyan matsaloli.

A daren juma’ar su Anti Halima suka kwashi kayan,su ka maida shi wurin Ummi,ni kam ko kallon tsanaki ma ban tsaya na yi musu ba.Bayan sallar isha’i Baba ya kirani,ya ke tambaya ta wasu irin kayan d’aki nake so?

Sai na ji duk jikina ya yi sanyi,tunda na fara gane da gaske dai auren zan yi,kuma da Habib,na kwantar da murya na ce”Baba ba ni da wani zab’i,duk wanda aka samu na gode”.

Baba ya ce”to ma sha Allah! Zinatu kin ga dai ni ba me k’arfi bane,sai dai rufin asiri,don haka zan yi miki iya k’arfina.Kuma don Allah ki k’ara nutsuwa,ba na son na sake jin wani ya kawo min k’ararki,ki nutsu mu samu mu rabu lafiya,kema auren shi ne kwanciyar hankalinki”.

Na amsa da to, sannan na tashi na koma d’akina,kwanciya na yi rigingine haka kawai na ji saukar hawayen da ban san ko na meye ba.Na d’akko wayata cikin rashin sanin abun yi na kira layin Salim,har ta katse bai d’aga ba, sai na yi masa sak’on fatan alkhairi,nan ma dai bai dawo min da shi ba.

Washegari da misalin k’arfe goma na shirya tsaf,cikin dogon hijjabina har k’asa,na fita na tari adaidaita sahu,ban tsaya ko’ina ba sai ALBARKA

Ban samu matsalar shiga wurin ba,don na sanar musu Salim ya san da zuwa na,sai dai ina zuwa k’ofar office d’in na tarar da wata matashiya,kuma ta ce min sai ya bada izini ake shiga,don haka na dakata ta yi min iso

Na jinjina kai,ina fad’a mata sunana Zinatu,ba ta jima ba ta fito ta ce min na shiga

Gabana ya yi fad’uwar da ban tantace ko ta meye ba,na san dai ba ta rasa nasaba da rashin k’wakkwaran dalilina na zuwa wurin,da kuma yanda Salim zai yi idan na fad’a masa k’arya nake ba kaya zan siya ba,sai kuma uwa uba yanda zai karb’i maganar da zan yi masa yanzun

Da sallama na shiga a nutse, kai sai ka rantse ba ni bace,na tadda shi zaune a kujera ya na danna waya,da jarkar coca cola a kan teburin,sai d’an k’aramin kofi

Ya yi masifar kyau,yau sanye yake da manyan kaya,wani yadi ne dak bulu da bak’ar hula a kanshi,ga bak’in agogo sanye a hannunsa

Idona ya sauka a bayan wayarsa,me d’auki da hoton wata budurwa me kyau,ban san ko wace ba,amma na fi kyautata zaton ita ce Baby

“Wa alaikissalam” Ya amsa da muryarsa me dad’i,ya na min nuni da kujerar da take fuskantarsa alamar na zauna.

“Na gode” Na fad’a bayan na zauna d’in.

Shiru na d’an lokaci kafin na ce”Zinatu ce”.

“Na gane” Ya fad’a ya na ajiye wayar.

Na d’an yi jim,na sauke ajiyar zuciya,ina jin wani sanyi da ya ke shiga kowace kafa ta jikina,kar fa ku ce ko sanyin Ac ne,a’a,wani irin sanyi ne da rasa yanda zan yi muku bayanin sa,ni dai na san k’alau na shigo wurin da sai na ce zazzab’i nake yi

Na d’an yi gyaran murya,wai ko za ta k’ara dad’in sauraro na fara magana”da farko dai zan fara baka hak’uri na rashin zuwa na jiya…”

Ya katseni”ai shiyasa nake son ki hanzarta,don yau ba ni da appointment dake”

“Hakane,na gode da bani dama” Na fad’a ina muskutawa,sai gyara zama nake kamar me nak’uda.

“To a gaskiya ba zan b’oye maka ba Salim…ba da gaske na ke ba, da na ce maka zan yi siyayya a kamfanin ku…”

Ya katseni”e na sani,kuma ba na neman dalilin k’aryarki,dalilin zuwan ki yanzu na ke buk’ata”.

Na kalle shi,na ga ni ya ke kallo,irin kallon nan na ido cikin ido,nan da nan ya yi min kwarjini,sai na ji duk na muzanta,na ji dama ban zo ba ma,To wai ma me ya ke damuna ne? Meye hakan na ke ta yi? Me zai sa na zubar da ajina na zo har wurin shi? To ko dai son shi na ke yi? Kai ba haka ake so ba,so ba rana d’aya ake fara shi ba,kamar yanda Habib ya fad’a min,na dai fi yarda Salim burgeni kawai ya ke yi…

K’was! K’was! Ya buga teburin gaban shi,da wani had’addan zobe dake yatsan shi na tsakiya.Ban gama dawowa cikin nutsuwata ba na ji ya ce”kar ki min k’arya,don ita ce abin da na fi tsana,kuma idan ki ka min k’arya ba zan sake sauraron kalma d’aya daga bakinki ba.Meye dalilinki na bibiyata?”

Dum! Dum! In ji k’irjina,na sanyaya murya kamar marainiya na ce”wallahi Salim haka kawai na ji ka burgeni,idan ba damuwa ina son k’ulla alak’a da kai,ko da ta abota ce,ka zama abokina don Allah”

K’urr! Ya tsaya ya na kallona,sai kuma ya dafe kanshi da duka hannunsa biyu,ya lumshe ido,ina ta fargabar yanda zai d’auki zance na,har tsawon mintuna ya na haka sannan ya d’ago ya zube idonsa akina.
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 6

 

“Ban amince ba”. Ya fad’a a sanyaye

Na ji zuciyata ta motsa,na kalle shi,sai ya lumshe ido ya na nuna min k’ofar fita daga office d’in

“Don Allah Salim”. Na fad’a a kasalance,idona su ka ciko da k’walla

“Tashi ki fita” Ya fad’a,ya na janyo lokar dake jikin teburin.Ban fita ba,sai ma kallon sa da na tsaya yi,ina son ganin abin da zai d’akko

Wata kwalba ya fito da ita,ta maganin tari ya janyo robar coca cola ya bud’e ya juye maganin a ciki duka,ya jijjiga ya kafa kai ya na kwankwad’a ya na kallona

Ko wani bai fahimtar da ni ba,na san hakan ya na nufin shaye-shaye kenan,cikin inda-inda na ce”Salim! Me hakan ya ke nufi? Me kake sha?”

Ya ajiye robar ya ce”yanayin ku d’aya! Kalaman ku ma iri d’aya ne,ko ita ta turoki ki gwadani?”

Gabana ya fad’i,to ba dai giya ya sha ba,bare na ce har ya fita daga hayyacinsa,ina cikin nazarin na ga ya d’auki waya ya yi kira”zo office d’ina”. Abin da ya fad’a kenan

Ba a jima ba kuwa sai ga wani ma’aikaci ya shigo,tun kafin ya k’araso ya yi masa nuni da ni ya na fad’in”fita da ita,kuma ka fad’awa Godiya kar a sake bari ta shigo!”

Na bugawa ma’aikacin wata kafirar harara,ganin ya na shirin tab’ani,sannan na tashi a sanyaye na fita,ina waiwayen Salim idona taf k’walla.

Ina fitowa daga office d’in na ji na kasa rik’e hawayen,ina jinsu su na ta zuba amma ban damu da gogewa ba,ko kuma na tsaida su

Sai dai dab da zan fita daga wurin na gamu da Kawu Ummaru zai shigo,gabana ya yi mummunar fad’uwa,na yi wani wawan ribas na juya don komawa ciki,ashe na makara don kuwa ko taku uku ban yi ba na ji ya kira sunana da alamaun mamaki

Duk k’ok’arin da na yi na ganin na tsaida hawayena kafin na juyo abu ya ci tura,har sai da ya sake kiran sunana sannan na juyo ina share hawaye

“Zinatu me kika zo yi a nan?” Ya tambayeni har yanzu da mamaki a fuskarsa.

Dabara ta zo min na ce “Aiki na zo nema”.

Sai ya bud’e baki da mamaki ya ce” aiki kuma? To an d’auke ki?”

Na girgiza kai alamar a’a

Ya ce”banda shirme ki taho neman aiki ba tare da shawara ba? Kuma ba jiya na ji ana zancen kayan lefenki ba? Ko kuma shi Habib d’in ne ya ce ki nemi aikin yi kafin auren?”

Na cigaba da hawayena,ba tare da na ba shi amsa ba. Sai ya wuce ya barni tsaye ina goge hawayen

To bayan na fita daga wurin a maimakon na yi gida,sai na yi 7:30 restaurant,ina ta rarraba ido bayan na shiga wurin,sai na je wurin wani da nake kyautata zaton ma’aikaci ne,tunda ga shi da uniform me d’auke da sunan wurin,na yi masa sallama ya amsa

Sannan na ce”don Allah zan iya ganin manager?”

Ya ce”e ba matsala,ga office d’in shi can”.

Na shiga k’ofar da ya nuna min da sallama,aka amsa ana yi min izinin shigowa,wani matashi na gani kwance akan doguwar kujerar dake office d’in

“Hajiya barka da zuwa” Ya fad’a ya na tashi zaune

“Barka” Na ce,ina zama a wata kujerar

Na ce”alfarma na zo nema”

Ya ce”to,ta mene?”

Na d’an cije baki kafin na ce”don Allah aiki nake nema a wurin nan”.

Ya ce”tabb! Aikuwa baiwar Allah, ba mu jima da k’ara ma’aikata ba,yanzu dai sun wadata gaskiya ba ma buk’atar k’ari”.

Na yi saurin fad’in”don Allah ka taimakeni,ko da shara ce ko wanke-wanke”

Ya ce”zancen kike so”

Na tausasa murya na ce”don Allah ko kyauta ne ni zan dinga aiki,idan ya so duk wata ka dinga rik’e albashina,na bar maka…”.

Ban k’arasa ba ya tareni”ok, ba sai ta kai nan ba,zan iya baki aiki,amma fa ba wanda kike zato bane idan za ki iya duk wata za ki samu kud’i fiye da zaton ki,amma nima za ki na bani wani abun k’arshen wata”

Na yi saurin fad’in”e na yarda, in dai a wurin nan ne”.

Ya ce”a anan ne ba matsala.Wurin namu b’angare biyu ne,akwai wurin da masu kud’i suka fi zama idan sun zo cin abinci,to za mu saka ki a cikin wa’inda za ki na kai musu abinci,wasu kuma sukan buk’aci wata ta zauna ta tayasu fira,ke wani ma idan firar ta yi dad’i har ya buk’aci ki raka shi wani wurin,to ta nan ne ake samun kud’i daga hannunsu,ga kuma albashinki me tsoka,dad’in dad’awa ma ku da kayan gida za kuna zuwa,amma fa sai kin kula da kwalliya mai d’aukar hankali”.

Na jinjina kai bayan na gama sauraron sa,na ce”babu matsala zan yi”.

Ya ce”yawwa! Amma dutyn dare za ki na yi,saboda na ga kina da kyau sosai,Allah yasa dai za ki iya aikin”.

Na yi murmushi na ce”kar ka damu zan iya.Yaushe zan fara zuwa?”

“Tun daga yau” Ya bani amsa,sannan ya tambayi cikakken sunana,na fad’a masa,ya tashi ya rubuta a wani littafi,mu ka yi musayar lambar waya sannan ya ce zan iya tafiya.

Na yi masa godiya,na fito daga wurin ina jin wani farinciki sosai.

Yanzun ma ba gida na yi ba,kasuwar sabongari na wuce na yi siyayyar kayan kwalliya kala-kala da turaruka masu k’amshi,domin inganta aikina.Gidan Ummi na wuce kai tsaye,bayan na gaisheta na tashi na yi alwala na yi sallar azhar,don lokacin k’arfe d’aya saura kwata, ta zubo min abinci na ci kad’an na tashi zan tafi,ta ce min”kin ga kayan naki kuwa?”

Na gyad’a mata kai,alamar e,ta na murmushi ta ce”Habib ya yi k’ok’ari sosai,Allah dai ya baku zaman lafiya”.

Ban amsa ba na fice ina yi mata sai gobe.

To daga nan kuma gidansu Kamisu na wuce,wani a k’asan layinmu da mu ke mutunci da shi,na yi sa’a kuwa ya na nan,zaune akan benci na tadda shi a k’ofar gida,na zauna a bencin nesa da shi,ina tambayarsa ya garin

Ya ce”normal wallahi,kin yi wuyar gani, sai jiya nake jin ashe auren ya kusa?”

Na yi murmushi na ce”haka aka ce”.

Ya ce”a,ban gane haka aka ce ba?”

Na yi y’ar dariya na ce”share kawai,kamar na ji ance k’anwarka ta na yin lalle ko?”

Ya tab’e baki ya ce”wai Nana? Ko yanzu ma shi na fito na barta ta na yi”

Na ce”yawwa! So nake don Allah, d’an kad’an za ta yi min”

Ya ce”ok,mu shiga to”

“A’a,ta fito dai ta min,sauri nake”.

Na fad’a ina d’akko wayata da ta fara ringing. Habib ne me kiran,na d’aga,bayan mun gaisa ya ke ce min yau zai shigo da daddare,na ce masa a’a sai dai da yamma,don ina da abin yi da daddare,ya amince muka yi sallama

Na kalli Nana dake tsaye na ce” yawwa Nana,kinga ba me yawa bane,da na iya rik’e lallen ma da kaina zan yi, harafin (S) kawai za ki zana min babba a nan”

Na yi maganar ina nuna mata bayan hannuna.Nana ta zauna a benci nima na zauna,ta zana min kamar yanda na buk’ata,sannan ta cike tsakiya da jan rani,hannun ya yi kyau sosai kuwa,na mik’a mata d’ayan na ce shi kuma ta zana min J.S,nan ma ta zana min,sannan ta saka min a y’an yatsuna ,na yi mata godiya na ce ta zuge jakata ta d’auki d’ari biyar,ta ce a’a na bar shi,ta shige gida.

Kamisu ya kalli lallen ya ce”amma Zinatu na ga dai sunanki daga Z ya fara”.

Na yi murmushi ina kallon hannun da na shanya shi s titi na ce”hmm! Share kawai Kamisu,wai ka ji y’an drugs sun k’wamushe Salisu ko?”. Daga haka mu ka shiga wata firar.

 

Da yamma Habib ya zo kamar yanda na ba shi lokaci,ya kwashi surutun sa ya k’ara gaba,don ni kam duk rabin hankalina ya na ga yanda aikina zai kasance,ya ce dai da daddare amma ban san ko k’arfe nawa ake tashi ba,yanzu idan za a kai dare sosai wace k’aryar zan yi wa Baba akan fita ta kullum? Wannan tunanin ya d’an sanyaya jikina,amma fa bai canza min k’udirina ba.

Ana fara kiran sallar isha’i,ina kammala shirina,doguwar riga na saka dama duk ta fi burgeni cikin kayana,na zauna na rangwad’a kwalliya,na nad’e kaina da mayafi kalar takalmin da zan saka,na baza turare bayan humrar da na yi wankanta,lokaci-lokaci nake kallon k’unshin hannuna na yi murmushi, kamar dai an bani tabbacin yau zan had’u da shi,na saka takalmina me tudu,na rayata jaka y’ar k’arama na fito

Mama Saude da ke kwashe tuwo ta bud’e baki ta na kallona,na tsuke fuska ina shirin wuceta na ji ta ce”Allah me iko! Zinatu wannan kwalliyar fa? To ko dai dawo da bikin yau aka yi bani da labari?”

“Wurin dinner k’awata zan je” Na fad’a don kar ta had’ani da Baba,na fice daga gidan cikin sauri-sauri.
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 7

 

Ina zuwa manager ya had’ani da wani,ya kaini b’angaren da aikina ya ke,ya na ta yaba kyauna,ni dai binsa kawai nake ina k’arewa wurin kallo,wani holl ya kaini,na ga y’an mata wasu na girmesu wasu sun girmeni,ga kuma sa’annina duk sun ci kwalliya su na zaune,wasu na fira,wasu na danna waya. Wata ya nunawa ni ya ce ta koya min yanda zan gudanar da aiki.Ta matso kusa da ni ta na murmushi ta fad’a min komai,sannan ta d’ora da fad’in”akwai Oga Salim,shi ne me wurin,shi ma ya na zuwa wataran,kuma be cika cin abinci ba idan ya zo,shi ya fi yin shaye-shayen shi,da yake d’an shaye-shaye ne”.

Sai na ji kalmar shaye-shayen har cikin raina,na ji ban ji dad’i ba a ganina Salim ya wuce ana danganta shi da wannan kalmar mara dad’in ji,to amma ya zan yi? Tun da halinsa ne dole a fad’a

“Allah ya shirya shi dai” Na fad’a ina sauke numfashi

Ta ce”hmm! Ai ni idan ya zo har na tsani a turani kula da shi wallahi”

“Kula da shi,sai kace wani jinjiri?” Na fad’a a zuciyata

A fili kuma na ce”to ya ake kula da shi?”

Ta ce”ai idan mutum ya shiga ba ya barin d’akin har ya tafi,saboda kai za ka rik’e masa d’an farantin da zai dinga karkad’e tokar sigarin da zai sha,kuma kai za ka had’a masa lemo da maganin tarin nan,idan zai ci abinci sai ya fad’i wanda yake so,ka kawo masa,ga shi ba ya son kallo,sai dai ka duk’ar da kai,ga warin taba shiyasa duk muka tsani a tura mu idan ya zo”

Na jinjina kai,ina mamakin wannan mulki irin na Salim,sai dai sosai hakan ya min dad’i,ko banza zan jima ina ganin shi,kuma zan samu hanyar shigar da kaina cikin sauk’i,na yi farinciki da ba sa son zuwa,ni kam ba warin sigari ba ko na giya ne zan jure.

Muna nan zaune aka yi kiran mutum uku,ni dai ina ta raba ido da fargaba,tunda na ga abun zab’a ake yi,kuma na ga kwalliyata duk ta fi tasu kyau,hakan ya b’ata min rai kad’an.Me kiran mutanen ya na sake shigowa kiran wata na yi sauri na tashi ina fad’in”kai! Ni ce zan je”

Ya ce”ai ke da Oga na yiwa tanadi,amma taho idan kin matsu”

Na yi saurin komawa na zauna na ce”a’a,shikenan zan je wurin ogan”

Ba a jima ba kuwa ya ce na fito,Oga ya k’araso.Na tashi na bi bayansa,sai kuma na ji wata fargaba ta dira a zuciyata,na fara hasashen watak’il Salim ya na ganina zai koreni daga aikin,wannan tunanin ya sanyaya min jiki,haka dai mu ka k’arasa har wani d’aki,ma’aikacin ya ce na shiga yanzu zai shigo

Na hau bin d’akin da kallo bayan na shiga, kujera ce zaman mutum uku,sai wani k’aramin firji da kuma wata loka y’ar k’ara,ga tebur a gaban kujerar me d’auke da k’aramin faranti me kyau sai walwali ya ke,wanda na ke kyautata zaton shi ne na zuba tokar tabar,sai da na kalli teburin da kyau sannan na lura da zanen harafin (J) me kyau sai k’yalli ya ke yi,na kai hannu na tab’a ina tunanin abin da J d’in take nufi.

Ina jin motsin bud’e k’ofa na yi saurin zama a k’asa,nan gaban teburin ina sauraron yanda zuciyata take bugu.

“Assalamu alaikum” Ya yi sallama ya na shigowa,na amsa cikin kashe murya wai ko zan burgeshi

Bai kalli inda na ke ba ya zo ya kwanta rigingine a kujerar,ya fara danna waya

“Ina wuni” Na gaishe shi.

Sai ya juyo ya na kallona,ko so ya ke ya ganeni oho,ya min kallon sakanni ya juya ga wayarsa sannan ya ce”lafiya k’alau”.

“Za a kawo wani abun?” Na tambaye shi a d’arare.

Ya yi shiru kamar bai ji ba,sai can kuma ya ce”ina zuwa”.

Ganin ya bawa banza ajiyata ya na ta harkar wayarsa sai nima na zuge jakata,na d’akko wayata,na tank’washe k’afa na shiga y’an danne-danne na

Wajan minti talatin mu na haka,sannan ya tashi zaune ya ajiye wayar ya kalleni ya ce”bud’e lokar can ki d’akko min sigari”

Na tashi tsam,na je na bud’e sigarin ce a ciki da yawa,da maganin tari suma kala-kala,sai wasu k’ananun robobi masu murfi,wanda ban fahimci abin da yake ciki ba,gida d’aya na d’akko,na duk’a na ajiye a teburin cike da ladabi

Ya d’auka ya zaro d’aya,ya kunna ya fara zuk’a,ni kuma na d’auki farantin na matso kusa da tebur d’in sosai,sannan na sunkuyar da kai. Ni sai na ji kamar hannuna ya ke ta kallo,ko tsarguwa na yi oho!

Sai da ya shanye su duka,ya na kad’e tokar a farantin,hannuna duk ya sage amma hakan bai sa na ji ina son barin kusa da shi ba

Kamar daga sama na ji muryarsa”Zinatu ki ke ko?”

Gabana ya fad’i,don da na yi zaton bai ganeni ba,ashe ya gane.Na d’ago na kalle shi a d’an tsorace na ce”na’am”.

Sai ya kalmashe yatsun sa wuri d’aya sannan ya ce”me yasa ki ke bibiya ta?”

Na yi saurin fad’in”na rantse da Allah ba bibiyarka na ke yi ba Salim,ka fahimceni”.

Ya kalleni na y’an sakanni,sannan ya ce”ta ya zan yarda ba Junaina ce ta turoki ba?”

Na ji dam! Na fara nazarin wacece Junaina? Sai kawai sunan na shi ya fad’o min (J.S) to ko dai J d’in ta na nufin Junaina,amma wace ita d’in? Kuma meye alak’ara su?

“Ki na shirya k’aryar da za ki fad’a kenan…”. Ya katse min tunani

Bai rufe baki ba na yi saurin fad’in” a’a wallahi,ni ban san wata Junaina ba, kuma ba ni da wata alak’a da ita,babu wanda ya turo ni”.

Ya jinjina kai sannan ya ce”ok! To ko dai so na ki ke yi?”

Na ji wani dam! Har numfashina sai da ya tsaya na sakan d’aya,to meyasa zai min wannan tambayar haka kai tssye? wannan ai k’ure ne kuma wace amsa ya kamata na ba shi? Na fad’a masa an kusa aurena,ko kuma na ce masa son shi na ke yi? Kai! Ba zan yi masa k’arya ba,ni dai burgeni ya ke kawai,amma ban sani ba fa ko ya ya kamu da so na ne,kar na je na yi abin da zan yi danasani

Muryarsa ta katseni
“Da ke na ke magana”

“Eh” Na fad’a a tak’aice.

Sai na kalle shi, jin ya yi shiru,na ga hannuna kawai ya zuba wa ido,ban ankara ba na ji ya rik’o hannun nawa me d’auke da zanen J.S,ya k’ura ido ya na kallo na y’an sakanni sannan ya wurgar da hannun ya fara magana

“Me yasa d’azu kika yi min k’aryar burgeki kawai na ke yi? Ba ke ce kika fara furta min kalmar so ba,amma na yi mamakin salonki,kin san meyasa?”

Ni dai na yi shiru kaina a k’asa,na kasa ba shi amsa

Ya ce”ok! Shikenan,ba sai kin ji ba”.

Na yi saurin d’agowa na kalle shi,saboda har ga Allah na so na ji dalilin,amma kamar an d’aure bakina na kasa yin magana

Ya tashi tsaye ya na jan d’an bak’in gemunsa da ya k’ara masa kyau ya fara magana”ba na sonki,kuma ba zan tab’a son ki ba”

Na ji wani dum! A k’irjina

Ya d’ora”ke ba ma ke ba,duk duniya babu wata mace da zan so bayan Junaina,ita kawai na ke so kuma ita kad’ai ce matata in sha Allah! Ko na auri wata macen sab’anin ta to fa sai dai ta yi zaman amsa sunan matar aure kawai,don ko gangar jikina ba za ta samu ba bare kuma zuciyata”.

Ban san lokacin da na fara kuka ba,sai da na ji d’and’anon gishiri a bakina,na ji wani dunk’ulallen abu ya zo ya tare min mak’oshi,raina ya b’aci sosai,zuciyata ta yi bak’a k’irin,cikin y’an sakannin na fahimci tabbas son Salim na ke yi,da kuma kishin sa me k’arfi.

“Kin gama aikin ki,za ki iya tafiya”

Ya fad’a ya na d’aukar wayarsa,ya saka a aljihu zai fice

Da k’yar na tattaro yawon bakina na had’iya,wai ko zan iya had’iye abun da ya tokare mak’oshi na,sai na samu damar magana.
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 8

“Na yarda zan yi zaman amsa sunan matar auren,in dai aurenka ne!”. Na fad’a kamar wanda ya bani zab’i

Sai ya juyo ya min wani kallo me kama da harara,ban damu ba na d’ora da fad’in” ban damu da gangar jikinka ba,ko ban samu zuciyarka ba babu matsala,ganinka ma kawai zai wadatar da ni”.

“Don Allah!” Na fad’a ganin ya tsaya kallona.

Sai kawai ya buga tsaki ya bar d’akin.Na jima zaune a wurin ina hawayen rashin gaskiya,to rashin gaskiya mana,idan ba haka ba har yaushe na fara son Salim da zan ji yanda na ji yau don ya fad’a min ba zai tab’a so na ba? Duka fa ban dad’e da sanin shi ba, ko gidansu ban sani ba bare iyayenshi.Kuma ni da na ke shirin yin aure nan da sati shida me ya kaini jefa kaina a irin wannan matsalar?

“K’addara!” Zuciyata ta ba ni amsar da ta gamsar da ni

Ina nan zaune a wurin manager ya turo k’ofar ya shigo d’akin,ya buga min wata kafirar harara kafin ya ce”wallahi yau da kin sa an kore mu daga aiki sai mun sa an rushe gidan ubanki! Shegiya me bak’ar k’afa,daga zuwanki yau kin b’ata ran Oga,har ya na zancen zai rufe gidan…”

Bai k’arasa ba na zabura na mik’e,hankad’ani aka yi? Tsalle na yi,iska na bi,duk ban sani ba amma ni dai idan na ce k’arasawa ta wurin shi na yi sakan d’aya na yi k’arya,na wanke shi da wani zazzafan mari,don har hannuna sai da ya d’auka,ina huci kamar zakanya na ce”k’arya ka ke yi wallahi! Ubana ya fi k’arfin ka,kuma kai k’aramin d’an iska ne,iskancin lungu ka ke yi,ka biyo ni eriyata ka gani don ubanka!”.

Ina gama maganar na fice daga office d’in,zuciyata na tafarfasa,ni na yi zaton ma zai biyoni wallahi,amma sai na ji shiru,watak’il hak’uri ne da shi,ko kuma ya ji tsorona ne oho! Shi dai ya sani

Adaidaita sahu na tare na shiga na fad’a masa inda zai kaini,duk da hasken da ke titi tarwai bai hanani gane dare ya yi ba,na share hawayen da suka zubo min,na kifa kaina da guiwa ban d’ago ba har sai da me adaidaita ya ce min an k’araso

Sauka na yi,ina shirin duba jaka na d’akko masa kud’insa,jaka ta ce d’aukeni inda ki ka ajiyeni,sai yanzu na tuna ko jakata ban tsaya d’auka ba,tana office d’in Salim,takaici ya rufeni kamar na saka kuka na kalli me adaidaita na ce”ka ga na manto jakata a inda na je,don Allah ka yi hak’uri na tsallaka,naje gida sai na d’akko maka”.

“Kutt! Amma dai kin san ko yaro ba zai yarda da wayon ki ba ko? Malama sallameni tun ranki bai b’aci ba!” Ya yi maganar ya na fitowa daga ciki ya murtuke fuska

Muna tsaye muna jayayya sai ga hannu d’aya ya zo wucewa.Hannu d’aya abokina ne,tsabar k’arfin sa ne yasa ake ce masa hannu d’aya,don ance duka d’aya yake wa mutum ya baje

Na yi farinciki kuwa,na k’wala masa kira daga inda muke,ya k’araso cikin takunsa na masu k’arfi ya na k’ara bubbud’ewa ya ce”kai! Zinatu tamu,me ki ke yi a ta nan da daddare?”

Na kwashe duk yanda muka yi na fad’a masa

Ya yi wa me adaidaita wata dank’a,ya matse wuyansa ya ce”kai! Har ance maka za a kawo maka kud’inka amma ka tsaya ja da ta wajanmu?”

Ya fizge daga rik’on ya ce”ai hakki na ne,dole ta ba ni,ba wani shege wallahi!”

Hannu d’aya ya ce”kai! To da alama ba ka da iyalai,idan kuma akwai to maza ka musu waya ka sanar da su inda za su zo su kwashe ka”

Sai ya karkace ya zaro wuk’a y’ar k’arama ya cakumo shi

“Na shiga uku! Ni fa ban saka ba don Allah kar ka sa caka masa”

Na fad’a cikin rud’ewa,don har rik’e hannunsa na yi.

Mai adaidaita ya rud’e ya shiga ba shi hak’uri, sai ya hankad’a shi kusa da ni ya ce”au! Ka ce kai shege ne? To duk’a ka bata hak’uri”.

Ba shiri ya zube a gabana ya na bani hak’uri, har abun ya bani dariya,na shiga yinta

Hannu d’aya ya ce”za ka ware ko sai na maka d’ayan? Don dai hakkin ka ne da yau babarka ba za ta ganeka ba,k’aramin d’an iska!”

Shi dai bai tanka ba ya shiga mashin d’in ya ja shi a miliyar.Wannan abun shi ya d’an wanke min zuciya ya rage min damuwa,muka jero da Hannu d’aya ina fad’a masa inda na je.

Na yi mamakin ganin gidanmu a bud’e,tunda na san Baba da wuri ya ke rufe k’ofa,na tura na shiga da fargaba.A tsakar gida na tadda Baban ya na zaune ya zuba tagumi,na yi sallama na zo zan wuce shi sum-sum

“Zinatu!” Ya kira sunana da alamun fushi

Na dawo ina d’an rage tsayina na ce”na’am Baba”.

Ya ce”daga ina kike?”

Na yi shiru kaina a k’asa

Ya nisa can ya ce”wata rayuwar kuma ki ke shirin shiga ko Zinatu?”

Lokaci d’aya na gane inda zancen sa ya dosa,kuma na ji babu dad’i a raina,da k’yar na bud’e baki na ce”a’a Baba,daga wurin aiki na ke wallahi”.

Bai kulani ba ya shige ya je ya rufe gidan,ya dawo ya shiga d’aki.Ni ma na yi d’akina,ko kaya ban canza ba na kwanta ina tunanin ta yanda zan samu jakata da wayata.

Ni dai ba zan koma wurin ba,musamman yanda na mari manager, sai dai na tura Hannu d’aya ya amso min,amma kuma ina tsoron manager ya sa a kama shi fa,da dai wannan zulumin bacci ya kwasheni.

Da asuba bayan na idar da sallah,na je na gaida Babana,ya amsa babu yabo babu fallasa,har zan tashi ya na ji muryarsa ya na cewa”Zinatu! In dai na isa da ke,to daga yau kar ki sake fita ko k’ofar gida,har sai ranar aurenki,ko Habibu ne ya zo ya shigo cikin gida”.

Gabana ya yanke ya fad’i,nan take zuciyata ta shiga bugu don kuwa na ji Baba ya na bani umarnin da ba zan iya yi masa biyayya ba

“Amma Baba jiya na manta wayata a wurin aiki,yau zan je na karb’o”. Na fad’a kaina a k’asa.

Baba ya min shiru kamar bai jini ba,har tsawon lokaci,ganin haka na san ba zai yi maganar ba,watak’il ya amince ne ko kuma ya yi fushi da maganata,ni dai na tashi na koma d’akina na kwanta ina ta nazari.

Salim gida ya wuce kai tsaye,zuciyarsa na tafarfasa,ya kwana biyu bai shiga irin wannan halin ba,ya na takatsantsan da duk wani abu da zai sa ya tuna farkon had’uwar shi da Junaina,shi yasa ko kad’an ba ya shiga sabgar wata macen.Duk da Junaina ta na cikin rayuwar shi har yau,har gobe ma amma ba ya son tuna farkon k’ulluwar alak’ar shi da ita

Baby ce ta shigo d’akin,kallo d’aya ta yi masa ta san ya na cikin damuwa,ta k’araso ta zauna a kujera ta ce” akwai matsala ne Bros? Me ya ke damun ka?”

Ya yi shiru ya na kallonta,sai ta d’age kafad’a ta ce”ai na sani,wannan yarinyar ba za ta tab’a barinka ka ji dad’in rayuwa ba,ta hana ka aure,kuma ita ta k’i ta aureka! Ka duba fa ka ga yanda ta maida kai,ta na son haukata ka,ta maida kai d’an maye,amma ka k’i rabuwa da ita,meyasa?”

Ya sauke numfashi da k’arfi ya ce”a’a Baby,da gaske na rabu da Junaina,farincikin ki shi ne nawa.Wata ce yanzu ba ita bace”.

Baby ta share hawayen da ya zubo mata ta ce”da ka damu da farinciki na da tuni ka yi aure Bros.Ka fito Ammi ta na kiranka”.

Daga haka ta bar d’akin ta na hawaye,ya tashi ya bi bayanta ya na jin damuwa sosai da hawayen y’ar’uwar tasa.

K’arfe takwas na safe Ummi ta aiko wata y’ar mak’otan su,na zo ta na kirana,na d’an tsorata da kiran,ina tunanin watak’ila an fad’a mata an ganni jiya da daddare,haka dai na shirya wajan k’arfe goma na tafi gidan

Tun zuwana jikina ya yi sanyi,ganin damuwa a fuskar Ummi,na gaisheta ta amsa babu yabo babu fallasa,na tashi na je d’akin Umma na gaishe ta,wai ko zan d’an y’antu a wurin Ummi,na dawo na zauna na sunkui da kai kamar a gaban malamina na ke.

Shiru na d’an lokaci,sannan Ummi ta ce”wai ke Zinatu me yasa ba kya jin magana? Ni fa gabad’aya na rasa inda ki ka sa gaba,ban san me ki ka d’auki rayuwa,ki fad’a min abin da ya ke ranki!”

Na yi shiru,idona ya ciko da k’walla.Ta d’ora da fad’in”jiya Ummaru ya ke fad’a min ya ganki a kamfani wai kin je neman aiki,da wa ki ka yi shawara Zinatu? Ko mahaifinki ne ya tura ki?”

Sai na ji sanyi a raina,tunda ba laifin jiya da daddare bane,ni har na manta ma mun had’u da Kawu Ummaru,dama na san bakinsa ba zai yi shiru ba,na tausasa murya na fara magana

“Don Allah Ummi ki yi hak’uri, ban yi da wata manufa ba,ni na je neman aikin ne saboda na rage muku wani nauyin akan auren nan,amma tunda ba ko so ba,na bari in sha Allah”.

Ummi ta ce” haba Zinatu! Waye ya fad’a miki ba za a yi miki komai ba? Kuma ko za ki nema da kanki tun da ba ki yi ba sai yanzu da aski ya zo gaban goshi? To ki kiyayeni Zinatu,abun naki ya isheni haka!”.

Tuni hawaye su ka zubo min,na dinga ba ta hak’uri, har sai da na ga alamar ta hak’ura sannan na ce mata zan tafi, ba ta bari na tafi ba sai da ta bani abin kari na ci na k’oshi.

Mai hali dai ba ya fasa halinsa,ina fitowa daga gidan su Ummi kai tsaye laundry d’in Salim na wuce,yau ma da na je ban sha wuyar ganin wannan ma’aikacin da ya bani bayanan Salim ba,mu ka gaisa na rok’e shi ya kwatanta min wurin gyaran jikin Baby k’anwar Salim

Tiryan-tiryan ya kwatanta min,na yi masa godiya na kama hanya.
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 9

K’arfe goma sha d’aya a shagon Baby ta yi min,na shiga wurin da sallama,ba wani girma ne da shi sosai ba,akwai ma’aikata su na ta aikin su,da tsirarun mutane da ake yiwa gyaran jiki,na ja kujera na kame ina raba idon ta inda zan ga k’anwar Salim d’in,duk da dai ban tab’a ganinta ba, amma na san idan na ganta zan ganeta,tunda jini ba ya b’uya

“Hajiya me za a yi miki? Gyara,ko kwalliya?”. Wata ma’aikaciya ta tambayeni

Na d’an ji dam! Don kuwa dubu d’aya da d’ari biyu ne a jakata,don duka kud’ina su na cikin jakata da na manta ta a d’akin Salim,don haka ban shirya wani gyaran jiki ba

“Amm…Baby ba ta shigo ba?” Na tambaye ta,don ni dai burina na ga yarinyar

Ta ce”ai ba ta zuwa da wuri,da yake ita kwalliya kawai take yi,kin ga kwalliyar an fi yin ta da yamma,sai k’arfe uku take zuwa.Mu mu na yin kitso,k’unshi,wankin kai,da kuma gyaran jiki”.

Na sauke numfashi na ce”ga shi kuma kwalliyar na ke so,unguwa zan je kuma sauri na ke yi,don Allah ko za ki kirata ta yi min?”

Ta ce”to bari na gwada,Allah yasa ta na free”

Ta d’auki waya ta kirata,ta yi mata bayani,sai ta kalleni bayan ta gama wayar ta ce”lallai kin yi sa’a,ta ce ga ta nan zuwa”.

Na ji sanyi a raina,na yi mata godiya ina gyara zama

Babu jimawa ta zo wurin,aikuwa kallo d’aya na mata na yarda k’anwar shi ce,su na kama sosai,sai dai ita ba fara bace,kuma da alama za ta yi kirki,don sai gaisawa suke da y’an wurin cikin wasa da dariya.

Na gaisheta,duk da dai ba na jin za ta girmeni,ta maido min da gaisuwar ta na murmushi ta ce”ke ce za a yi wa kwalliya?”

Na ce”e ni ce”.

Tace”ok,bismillah”.

Na matso inda take zaune akan kafet,ta na shirya kayan kwalliyar,ta kalleni ta ce”to,ta nawa za a yi miki?”

Gabana ya fad’i,na dai dake na ce”ta d’ari biyar”.

Ba ta yi magana ba ta hau yi min,ni dai ina ta kallon ta, sai can cikin son janta da fira na ce”uhm! Ni fa zan yi kwalliyar ne kawai! Amma ba ni da wayar da zan d’an yi hoto idan an gama”

Ta yi murmushi ta ce”ba ki da waya,da girmanki?”

Na ce”ina da waya,jiya ne na manta ta a d’akin saurayi na,kuma bai kawo min ba”.

Sai na ga ta d’an yi damm,sannan ta ce”aikuwa da ya kawo miki”.

Ta gama yi min kwalliyar,ta kalleni ta na murmushi ta ce”wow! Gaskiya kin yi kyau,ki na da kyau sosai”.

Na yi murmushi na ce”kai Baby! Duk kyauna ai dai ban kai ku ba,ke da kayan ki”.

Na yi zaton ma za ta tambayeni inda na san yayanta sai na ga kawai ta yi y’ar dariya,ta d’auki wayarta ta ce na tsaya ta min hoto

Na yi murmushi me kyau,ta d’aukeni,sannan na rok’eta mu yi tare,mu ka yi,mun yi kyau kuwa

Ta na shirin barin wurin na ce”don Allah zan rok’e ki wata alfarma”

Ta ce”ok,ina jinki”.

Na ce”lambata zan baki,idan na karb’o wayata daga wurin Salim sai ki tura min hoton”.

“Salim?” Ta fad’a da mamaki

Na yi murmushi na ce”e sunan saurayin nawa ne haka”.

Sai ta yi murmushi ta ce”nice! Ni ma sunan Bros d’ina ne,kuma ina son shi sosai.Kar ki damu,ki saka min lambar,in sha Allah zan tura miki”

Ta k’arashe maganar ta na mik’o min wayarta,na saka mata lambar na fad’a mata sunana,na yi mata sallama,sannan na je wurin wadda ake bawa kud’in na bata na fito daga wurin da farinciki.

Shabiyu da mintuna na koma gida,na tambayi Mama ko Baba ya shigo da na fita? Ta maka min harara ta ce”ban sani ba! Ko tsoron shi ki ka fara yi yau d’in? Na ga dai ba yau kika saba taka umarninsa ba, shi ma ai da gangan ya ke yi,bai yi miki mari a k’afa ba kuma ya saka ran za ki zauna a gida? Aikin banza…”

Ni dai ban tanka ta ba na shige d’aki,na barta ta na ta yi.Y’an tsirarun kayana na had’a na wanke,na yi kwalimar d’akina,haka dai na yi ta k’irk’irar aiki duk dan kar na gaji da zaman na yi sha’awar fita,don ba a son raina na taka dokar Baba ba,dole ce kawai.

 

Fess! Ya fito cikin shirin sa na k’ananun kaya,jar riga da bak’in wando,sai k’amshi ya ke zubawa. “Sannun ku Mami,ke da autarki ne ku ke fira?”. Ya fad’a ya na murmushi.

Mami ta kalle shi ta ce”Salim ba ka ci komai ba fa,tun safe”.

Ya ce”e,yanzu zan je na ci”.

Ya kalli Baby da take zaune ta na danne-danne a waya ya ce”my Baby,zan fita”.

“A dawo lafiya” Ta fad’a ba tare da ta kalli inda ya ke ba.

Sai ya dafe kai,ya zauna kusa da ita ya ce”na fasa fitar ma,ta ya zan iya fita ki na fushi da ni y’ar’uwa?”

Ta juya kai gefe ta ce”ni fa babu ruwana da kai Yaya Salim,ka je kawai”.

Ya ji babu d’adi sosai,ga Mami da take yi masa kallon tuhuma,don ba ta k’aunar duk wani abu da zai b’ata ran autar ta.Khadija(Baby) ita ce auta a gidan,akwai yayyun Salim guda biyu mata,wanda duk sun yi aure da y’ay’ansu,Baby da larurar ciwon zuciya aka haifeta,shi yasa duk gidan kowa ya ke tausayin ta,ake k’ok’arin faranta mata,ko kad’an ba a bari ranta ya b’aci don kar ciwon ta ya tashi,duk cikin gidan sun fi shak’uwa da Salim,kamar ya fi kowa son faranta mata rai,za ta iya cewa bai tab’a saka ta damuwa ba sai bayan had’uwar shi da Junaina.

“Don Allah ki zo ki rakani,zan yi miki wani abun mamaki,kuma na san zai faranta miki sosai”.

Sai ta yi murmushi ta ce”ka tabbata?”

Ya na kamo hannunta ya ce”e mana”.

Ta tashi ta shiga d’aki ta d’akko mayafinta su ka fita.Ta d’an b’ata rai ganin sun nufi restaurant ta ce”anan za a nuna min wani abun mamaki?”

Ya ce”yunwa na ke ji,mu fara cin abinci tukunna”.

Ta yi shiru har su ka k’arasa,sai da ya ja Manager gefe ya fad’a masa kar a turo kowace yarinya sannan ya dawo wurin Baby su ka shiga d’akinsa.

Ta bi d’akin da kallo ta na d’age gira,don ta yi zaton za ta ga hoton Junaina,caraf idanunta su ka fad’a kan jakar mata y’ar k’arama,ta yi saurin k’arasawa ta d’auki jakar

Salim ya ce”ke yanzu daga ganin abu sai ki tab’a ba ki san me shi ba?” Cikin dauriya kawai ya yi maganar,don ya yi mamakin ganin jakar,kuma ya gane tabbas ta Zinatu ce.

Baby ba ta kula shi ba,ta bud’e jakar kud’i ne a ciki sai turare da waya,ta d’akko wayar ta danna aikuwa hoton Salim ya bayyana a fuskar wayar,sai ta juyo ta yi masa kallon tuhuma ta ce”Yaya,wannan jakar waye?”

Ya ji wani takaici,da haushin Zinatu ya rufe shi,ya ma rasa ta yanda zai yi mata bayani,ganin har ta fara hawaye ya ce”zauna don Allah,wallahi jakar me aiki ce,ina jin mantuwa ta yi a d’akina”.

Baby ta yi tsaye da jaka a hannu ta na kallon shi,lokaci d’aya tunanin kalaman sa su ka dawo kanta da ya ke cewa’A’a Baby,da gaske na rabu da Junaina,farincikin ki shi ne nawa.Wata ce yanzu ba ita bace’

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Ta furta cikin sanyin murya,ta tsaya kallon shi na d’an lokaci,sai kawai ta saka wayar a jakar ta rataya,ta nufi k’ofar fita.Ya yi saurin bin bayanta ya rik’ota ya ce “Baby! Wai ki na nufin ba ki yarda da ni ba? Wallahi da gaske ba ni da alak’a da me jakar nan”.

“Amma me ya kawo hotonka a fuskar wayarta? Duka ma me zai kawo ta d’akinka bare har ta yi mantuwa? Haba Yaya,me ya sa za ka fara haka?”

Ta kai k’arshen maganar da sanyi sosai,kamar za ta yi kuka.

Ya dawo da ita,ya zaunar akan kujera ya ce”ki yarda da ni Baby,da gaske ba ni da alak’a da me jakar nan,ni fa ban ma santa ba,kuma ban san yanda aka yi aka samu jakar a d’akina ba, ina tunanin wani tarkon ne dai ake shirin yi min”.

Ta yi saurin katse shi da fad’in”don a had’ani da kai? Ko kuma don a had’a ka da matan da ka ke kawowa?”

Ya ji kalmar kawo matan har cikin ransa,ba dan ya na gudun ciwon ta ya tashi ba,da yau sai ya wanka mata mari,ya cije baki ya ce”haba Baby! Ke fa k’anwata ce ba yayata ba,ya zan dinga yi miki bayani ki na neman jifana da wata manufar mara kyau? Oya tashi na maida ki gida”.

Ya yi maganar ya na mik’a mata hannu,alamar ta ba shi jakar.Ta maida jakar baya ta ce”ba zan bayar ba,wallahi Yaya sai na ga me jakar nan ido da ido,sai na ji alak’ar ku da har take zuwar maka d’aki,ta yi zaman da za ta yi mantuwar jaka…”

Cak! Ta tsaya,ta yi shiru baki bud’e ba tare da ta k’arasa maganar ba,tunanin kalaman Zinatu na d’azu su ka shiga dawo mata,ta ce ta manta jakarta da wayarta a ciki,a d’akin saurayin ta,kuma sunan saurayin Salim,tabbas Salim d’inta ne buduruwarsa ce

Ta zauna hannunta har karkarwa ya ke,ta dubo lambar da Zinatu ta bata,ta danna kira.K’irjinta ya bada dum! Ganin ga shi a zahiri hasashen ta ya tabbata,don kuwa bugu d’aya wayar dake hannunta ta soma ringing.

Sai ta nuna masa wayar ta ce”Ashe ita ce? To ita ta fad’a min gaskiya, d’azu ta fad’a min ta manta wayarta a d’akin saurayin ta,ashe kai ne Yaya? Yaushe ka fara soyayya da wata bayan Junaina?”

Ya zauna shi ma ya na mamakin ta inda ta samu lambar Zinatu ya ce”ba ni wayar nan Baby”.

“Na ce fa ba zan bayar ba,ni zan maida mata da kaina,kawai ka kaini gidansu”. Ta yi maganar ta na hawaye

Hankalin sa ya d’an fara tashi,don ba ya son ciwon ta ya tashi,ya sassauta murya ya ce”sister ki tsaya ki fahimceni…”

“Wallahi Yaya ba zan fahimce ka ba,ta ya zan fahimce ka alhalin idona ya nuna min komai? Ba alak’ar gaskiya ku ke yi ba,shi ya sa tun farkon had’uwar ku ba ka bani labari ba ko?”

Ya yi shiru ya na kallon ta.Ta d’ora da fad’in”zan yi maka wata alfarma guda d’aya,ba zan sanarwa da kowa ba,amma fa idan ka min alk’awarin za ka kaini gidansu”.

Ya ce”subhanallah! Ba ki yarda ba kenan? Wallahi ban san gidan su Zinatu ba,hasashen ki ba gaskiya bane”.

Ta ce”ba abun mamaki bane,na yarda ba ka san gidansu ba,tunda ba ka da niyyar aurenta,shikenan Bros na fahimce ka,amma ni zan nemo gidansu zuwa gobe,zan je za mu yi magana da ita”

Daga haka ta fice daga d’akin cikin sauri ta na rik’e da jakar
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 10

 

A cikin kwana biyun da suka wuce na yarda da lallai Salim ba iya burgeni ya ke ba,har da so mai tsanani ma kuwa,don kuwa tunaninsa ya hanani sakat,komai na ke yi ya na raina,hotonsa ba ya b’ace min daga idon zuciyata,burina kawai na ganshi,ko na ji muryarsa, amma na yi alk’awarin ba zan koma kamfanin su ba,don gaskiya ina jin tsoron mu sake had’uwa da kawu Ummaru,kuma ba wai kawun na ke tsoro ba,b’acin ran Ummi ne kawai ba na so,kuma ba na son komawa gidan cin abincin nan a samu matsala,shi ya sa ma na hak’ura,na zubawa sarautar Allah ido,don na san dai idan Salim ya koma d’akinsa dole zai ga jakata,kuma idan da imani ai ko bai nemeni ba zai sa wani ya kawo min.

K’arfe goma na safe Habib ya zo gidanmu,bayan mun gaisa ya ke tambaya ta ina wayata,wai ya na ta kira ba na d’agawa,ya shiga damuwa ya yi zaton ko akwai matsala.Na tab’e baki kawai na ce masa “hutun amsa kira na tafi”

Habib ya yi murmushi ya ce”kirana ko?”

Na turo baki na ce”zancen ya isheni haka fa,ko dama shi ya kawo ka?”

Ya ce”a’a,shikenan an bar shi”. Mu ka d’an yi fira,har ya nuna min gidanshi,wanda za mu zauna a ciki,na kalla na ce ya yi kyau,ya tambayeni komai ya yi min,ko da wani gyaran? Na ce ai gidanshi ne,kar ya biyewa ra’ayina,bai jima ba ya tafi,don dama daga wurin aiki ya zo gidan namu.

Ya na tafiya nima na k’ara gaba,wurin Anas na je na ari wayarsa,na saka lambata a ciki na danna kira,ban yi zaton za a d’aga ba,don duk a zatona har yanzu ta na d’akin babu wanda ganta,ga mamaki na sai na ji muryar mace ta d’aga da sallama, na amsa ina nazarin muryar,mu ka yi shiru na y’an sakanni kafin ta ce”waye me magana?”

“Me wayar ce” Na bata amsa

Ta ce”Zinatu ce?”

Na ce”e,sai na ji muryar kamar ta Baby”

Ta ce”e ni ce,wayarki ta na hannuna,ki kwatanta min gidanku zan zo na kawo miki yanzu”.

Na d’an yi jim! Ina tunanin ta yanda wayar ta je hannunta,sannan na kwatanta mata tiryan-tiryan,ta yi min godiya ta ce ga ta nan zuwa.

Na bawa Anas wayarsa,sai da na siyi ruwa da lemo sannan na koma gida,na d’an k’ara kimtsa d’akina na kunna turaren tsinke,har tsakar gidan nan share,duk da na ga Mama ta share da safe,Allah ma ya taimakeni ma su siyan waina sun watse,na koma d’akina ina zaman jiranta

Ina kwance ina sak’a da warwara na ji muryarta ta na rangad’a sallama na tashi na tareta da fara’a,Allah ya taimaka Mama ba ta nan,bare ta sa mana ido,bayan ta zauna mu ka gaisa,na ba ta ruwa

Ba ta sha ba ma,ta mik’o min jakata sannan ta nisa ta ce”Zinatu zan tambayeki,ki fad’a min gaskiya don Allah”.

Na d’an ji dam! Na ce”to in sha Allah”.

Ta ce”menene ya had’aku da Salim har ki ka je d’akinsa ki ka manta jaka?”

Na yi shiru ina tunanin na fad’a mata gaskiya,ko na yi k’aryar da za ta shigar da ni rayuwar Salim.Ban gama yanke shawara ba na ji muryarta “don Allah ke ki fad’a min gaskiya, shi ina kokwanto akan abin da ya fad’a min”.

Cikin y’an sakanni dabara ta zo min,na ce” zan fad’a miki gaskiya, amma da sharad’i”.

Da d’an mamaki ta ce”sharad’i kuma? Na meye?”

Na gyara zama na ce”ina son ki ba ni labarin soyayyar Salim da Junaina,da kuma abin da ya rabasu,sannan ki samo min lambar ita Junainan,ko kuma adireshin ta”.

Baby ta tsaya kallona kamar me nazari,cikin so tabbatar mata na ce”wannan shi ne sharad’in,amma idan ba zai yiwu ba babu dole fa,za ki iya auna k’aryar da Salim ya yi miki”.

Ta nisa kafin ta ce”amma ke me yasa ki ke son jin labarin?”

Na ce”ina da babban dalili,ke dai ki sanar min daga baya kya ji dalilin”

Ta ce”to shikenan,amma dai kin san ba zai yiwu na san komai ba,saboda haka iya wanda na sani zan sanar dake”.

Na gyad’a kai alamar gamsuwa.Ta fara ba ni labari “Junaina y’ar jihar Katsina ce,a Manumfashi,gidansu su na da yawa,amma ita k’ad’aice mace,ta na da kyau babu laifi,ina tunanin za ta kai shekara ashirin da biyar.Wani yayanta ne abokin Salim,wanda su ka yi makaranta tare a Egypt.Wata rana Salim ya kai masa ziyara Katsina,saboda ya duba shi,sakamakon rashin lafiya da ya ke yi,a ranar ne suka had’u da Junaina,Yaya ya ce ya na ganinta ya ji k’aunar ta,amma ya dake har ya baro garin bai nuna ba,ashe ita ma haka ta kamu da son shi,ta samu lambar shi a wurin yayanta,ta yi ta damunsa da kira da sak’onni har dai ta bayyana masa son shi take,ya amince da ita,ya na mugun son ta sosai,lokaci d’aya duka dangi kowa ya sani saboda yawan zuwa Katsina da yake yi,in dai ka na son ganin Salim a farinciki to ka yi masa firar Junaina.Ganin da gaske suke soyayyar, ya sa Abbanmu ya ce ai kawai gwara ayi auren kowa ya samu nutsuwa,sai dai ana zuwa da zancen aure Junaina ta ce ta amince,amma ba yanzu ba,sai ta yi digiri”

Baby ta sauke numfashi,ta tab’e baki ta ce”saboda babu gaskiya, tun da me take yi ba ta yi digirin ba?”

“Gaskiya kam!” Na fad’a ina gyara zama.

Ta cigaba “kuma ta ce ita a Kano take son yin karatun,Yaya ya fi kowa jin dad’in hakan,saboda ya dinga ganinta akai-akai,admission ma shi ne ya sama mata,kuma ya d’auki nauyin karatun ta da duk wasu buk’atun ta,mahaifinta shi dai godiya ce kawai aikinsa,B U K ta fara zuwa,da farko ta na karatun kamar abin arzik’i,Salim ya na ta hidima da ita,sai daga baya wasu mazan suka fara d’auke mata hankali,mutane da yawa sun so ankarar da Salim,amma ya k’i yarda,saboda tsabar k’aunarta.Haka ake ta tafiya,abun Junaina ya na k’ara gaba,shi kuma ya na k’ara rufe idonsa,har dai ta kai ga ta daina b’oye masa komai, ta na kula samari a gabansa,ya sha zuwa ya tarar da ita da saurayi sai ta ce masa abokinta ne,idan ya ga abun bai yi masa ba zai iya canza shek’a,haka ya yi ta hak’uri ya na daurewa,saboda ba ya so ya rasa ta”

“Kin san wani abun takaici?”. Ta dakata,tare da tambaya ta.

Na girgiza kai alamar a’a.Ta d’ora” daga k’arshe dai Junaina sai da ta yarda da samarin shaho,suka d’auke mata hankali,tun ta na yiwa makaranta asha ruwan tsuntsaye har ta daina karatun duka,wani saurayin ta ya kama mata gida a ‘Dorayi,yanzu haka ta na can da zama”.

“Subhanallah! Zaman kanta take yi kenan?” Na tambaye ta da mamaki.

Ba ta bani amsa ba ta d’ora”lokacin da ya ankara kar ki so ki ga yanda ya shiga tashin hankali,sai da ya kusa shafe wata d’aya a kwance,ya na daga kwancen yana kiran wayarta,amma wallahi ba ta zo ta duba shi ba.Da k’yar mu ka samo kan shi,ya dawo cikin hayyacin sa,amma duk da haka sai ya cigaba da bibiyarta,ita kuma ta na yi masa wulak’anci son ranta,amma wai a hakan ta ce masa shi za ta aura idan zai jirata,kuma kud’i ko nawa ne idan tana bukata shi take tambaya ya tura mata ko ya kai mata”.

Na jinjina kai na ce”tabb! Amma wannan ta cika y’ar rainin hankali!”.

Baby ta ce”ai duk ba ma wannan bane abin haushin,kin san kuwa y’an’uwanta shi suke zargi da lalata musu y’arsu?”

Na zaro ido cikin mamaki na ce”rainin hankali! Ai sai su zo su gani”

Baby ta ce”su ga me!? Shi fa suka kira,kuma ya tabbatar musu da shi ne ,kawai saboda ya kareta. Ke so fa k’addara ne!”

Na ce “tabbas! Lallai wannan Junaina ta cika mara rabo”.

Ta cigaba”to daga baya ta dawo ta ce masa ta daina komai,ya ba ta jari za ta fara sana’a,saboda mahaifinta ya gargad’e ta k’ar ta kuskura ta koma Katsina,jiki na rawa ya d’auki kud’i masu yawa ya bata,ta bud’e wani wurin sai da kayan sawa,na maza da mata,amma duk da haka dai ta k’i yarda da auren su.Ba mu san lokacin da ya fara shaye-shaye ba,ba mu san dalili ba,amma gaskiya duk mun fi danganta abun da halin da Junaina ta saka shi ne ya jefa shi a harkar”.

Ta d’ora ” kuma ya ce shi zai jira har lokacin da za ta nutsu,ta amince da aurensa,ba zai tab’a yin aure ba,saboda ta ce muddin ya yi aure to ta rabu da shi har abada! A cewar shi dai yanzu ya rabu da ita,amma duk ba mu yarda ba,sai dai daga lokacin da na ga jakarki a d’akinsa na fara zargin wani abun kuma na da ban.Wannan shi ne labarin Junaina,sai ki cika alk’awari ki fad’a min gaskiyar tsakanin ki da Yaya”.

Hawayen da ban tantance ko na meye ba suka shiga zubo min,tun ina gogewa har na fashe da kuka sosai.Wata k’aunar Salim da tausayin shi suka yiwa zuciyata dirar mikiya,har na ji idan ba shi na aura ba ni ma har abada ba zan yi auren ba.

Baby ta tsaya ta na kallona da alamun mamaki,sannan ta ce”Allah yasa dai ba zatona bane ya ke shirin tabbata!”.

Na yi shiru ina saita kaina,na ce”ko kad’an,Baby kar ki zargeni ko d’an’uwanki,yanda ya fad’a miki d’in na san gaskiya ne…”. Na kwashe labarin tun farkon had’uwarmu har izuwa ranar da na bar jakata na fad’a mata.

Ta yi shiru kamar me tunani,sannan ta kalleni ta ce”Zinatu tsakanin ki da Allah da gaske ki ke son Salim?”

Na yi saurin fad’in”wallahi har zuciyata nake k’aunar Salim,tunda na yi masa kallo d’aya,idan so ya na zama k’addara to son Salim shi ne tawa k’addarar”. Na fashe da kuka

Cikin sanyin murya ta ce”ayya! Ki bar kukan haka,ba zan yi miki alk’awarin auren Salim ba,amma zan yi iya yi na ganin na had’a alak’ar ku,ke ma sai ki had’a da addu’a, da kuma y’an dabarun ki”.

Na ce”na gode sosai y’ar’uwa,amma a ganina me zai hana na shiga jikin Junaina,na karanci halaye da d’abi’unta,ko koyi da ita zai sa Salim ya maye gurbinta da ni?”

Baby ta yi murmushi ta ce”Zinatu gurbin ido ba ido bane,kuma shi so babu ruwan shi da halayya,tunda ita d’in yake so,to fa ko za ki yi birgima a tab’o ki koma kamarta sak,bai zama lallai ya so ki ba”.

Na jinjina kai na ce”hakane,amma duk da haka ina son ganin ta dai,ki taimakeni da lambarta don Allah”.

Ta ce”wa!? Ni kam me zan yi da lambarta,kin san yanda na tsaneta kuwa? Zan dai kwatanta miki wurin sana’arta idan ki na so”.

“Ina so!” Na fad’a da sauri.

Ta kwatanta min,babu nisa ma sosai,a zoo road ne wurin,kuma siffanta min kamannin ta

Na rakata har bakin titi ina ta kwarara mata godiya kamar ba gobe.
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 11

Ina dawowa daga rakiyar Baby,na zauna na kira lambar Salim,har ta katse bai d’auka ba,sai da na kira sau uku sannan ya d’aga cikin fushi ya ce”ke! Lafiya kike kira na?”

Na d’an ji fad’uwar gaba,amma na dake na ce”lafiya lau,na kira ne kawai na gaishe ka,kuma na ji lafiyarka”.

Bai bani amsa ba,kawai ya kashe wayar.Na had’a kai da gwuiwa,hawaye suka min sallama,na jima a haka ina nazari kafin na tashi cikin sauri,kamar an tsikare ni

Wanka na yi,na shirya cikin dogon hijjabina har k’asa,na zari jaka da wayata na fice.Sai dai ina tsayawa a bakin titi don jiran abin hawa,kawai na ga Baba ya sakko daga adaidaita,na d’an ji fargaba da kunyar sab’a umarnin sa sun kama ni,amma na dake cikin zuciyata na ce”sai dai ka yi hak’uri Baba,addu’ar ce dai za ka yi ta min”.

Kafin ma ya k’araso inda nake,har na fad’a adaidaita,ban zarce ko’ina ba sai Zoo road, Allah ma ya taimake ni me mashin d’in ya san wurin,don haka ban sha wata wahala ba aka kaini har k’ofar shagon Junaina.Babu laifi wurin da girman sa,ya burgeni tun daga k’ofar,na saita kaina na k’ara nutsuwa ina kallon kaina daga sama har k’asa,wai na tabbatar babu wata makusa,kamar dai wadda zan gana da shugaban k’asa ko wani sarki

Tun kafin na k’arasa ta glass na hango wani matashi daga ciki,ya kafeni da ido kamar ya sanni,na tura k’ofar na shiga sallama d’auke a bakina,shi kad’ai ne a ciki don iya hange na ban ga alamar Junaina ba,ko kuma masu siyan kaya,matashin ya tashi da sauri ya amsa sallamar,ya fara washe baki ya na min sannu da zuwa,da alama dai ya na da rawar kai kuma sam bai burgeni ba,don haka na had’e gira na ce”Junaina nake nema”.

Ya turo min kujera tare da fad’in”wallahi yanzu ta fita,amma ba za ta jima ba,ki zauna bari na kira ta a waya”.

“Na gode” Na fad’a bayan na d’osana na zauna a kujerar,sannan ya d’auki waya ya kirata.Ya dinga k’ok’arin ja na da fira ni dai kawai ina bin sa da e,a’a,a haka har kusan minti ashirin,ni dai har na fara k’osawa sai ga ta ta shigo da sallama

Na yi saurin d’agowa daga kallon wayata,na zube idona a kanta,fara ce tass,ba don kar ace kishi nake ba ma da na ce har da k’arin mai a hasken,ba ta da wani dogon hanci,sai manyan idanu kamar k’wai,bakinta d’an k’arami don nawa ya fi nata girma,wando ne a jikinta da riga iya gwuiwa,ta nad’e kanta da mayafi,sai wani uban glass da ta maida shi goshinta,y’ar siririya ce kamar yanda Baby ta fad’a min

“Wa alaikumus salam” Na amsa ina yi mata murmushi

Ta k’araso ta ja kujera ta zauna,ta na kallo na ta ce”ke ce me nema na?”

Na ce”ni ce”.

Ta ce”to Allah yasa dai lafiya”

Na yi murmushi na ce”in sha Allah “.

Ta jinjina kai ta na sake kallo na daga sama har k’asa ta ce”to ina sauraron ki”

Na d’an kalli matashin nan,na ga mu ya ke kallo, sai na ji nauyin yin magana a gabansa,don haka na kalle shi na ce”bawan Allah ko za ka iya bamu wuri?”

Junaina ta ce”Sani jira mu a waje mana”. Ya tashi ya fita ya na waige na.

Na maida hankalina kan Junaina na ce”sunana Zinatu,don Allah wata tambaya na ke son yi miki da farko”.

“Uhm” Ta ce kawai.

Na ce”na san duk tarihin soyayyarku da Salim.Don Allah me yasa kika k’i amincewa da auren shi har yanzu? Ko ba ki san yanda yake k’aunar ki ba?”

Sai ta yi shiru na y’an sakanni ta na kallo na,sannan ta yi murmushi ta ce”shi ne ya turo ki da wannan tambayar?”

Na ce”a’a,Salim ba shi da masaniyar zan zo wurin ki,kuma ba a bakinsa na ji tarihin soyayyarku ba”.

Sai ta jinjina kai ta ce”ina son Salim, amma ni ban shirya yin aure yanzu ba,shi ne kawai dalili”

“To me yasa?” Na yi saurin tambayar ta

Ta ce”saboda ban shirya kashe rayuwata ba”.

“Kisa kuma?” Na tambaye ta da mamaki

Ta yi y’ar dariya ta ce”e mana! Ai ita mace da zarar ta yi aure to rayuwarta ta zo k’arshe,shi ya sa nake son na gama cin duniyata da tsinke kafin aure,tunda ina da dahir d’in me yi min son gaskiya,kuma zai jirani duk tsawon lokaci”.

Na yi shiru ina mamakin kalaman ta.Ta d’ora”menene dalilin zuwanki wurina?”

Kai tsaye na ce”son Salim nake,kuma na zo ne na rok’eki ki bani wasu shawarwari don na samu kan Salim cikin sauk’i”.

“Me!?” Ta fad’a da d’an k’arfi ta na zaro ido.

“Shi Salim d’in ya san ki?” Ta tambaye ni

Na sauke numfashi na ce”ki nutsu don Allah, Salim ya san ni,amma bai amince da ni ba.Ni ki yanke kud’in da zan biya ki kawai ki fad’a min abin da ki ke yi masa ya ke k’aunar ki don Allah”.

Sai ta jinjina kai,amma da alama dai hankalin ta ya tashi,ta ce min”ok! Gobe bayan magriba ki dawo,kafin nan na yi shawara”.

Na yi mata godiya na fito daga wurin,kaina duk a d’aure,ni dai ban yi zaton Junaina ta na son Salim ba,amma a yanda na gani a idonta kam tabbas tana kishin Salim sosai.Na hau mashin na koma gida,gidan Ummi ma na wuce,don ina jin tsoron had’uwata da Baba, na yi sallahr azhar na ci abinci,na kwanta sai bacci.

 

Yau da wuri ya dawo daga kamfani,ransa duk a b’ace ya ke, don ya san Baby ce ta je ta kaiwa Zinatu wayarta,yau da wani ne ta yi masa haka ba ita ba,babu abin da zai hana ya yankar masa tikitin rashin mutunci,fuska a murtuke ya shigo gidan,bai tadda kowa a falo ba,ya fi zaton suna kitchen, don haka ya shiga kai tsaye da sallama,a zaune ya ga Baby ita kuma Ammi ta na tuk’a tuwo,ya d’an saki ransa bayan sun amsa sallamar ya ce”Hajiya Ammi,ke da y’arki ne ku ke yin tuwo?”

Ammi ta yi murmushi ta ce”na ke yin tuwo dai,fira kawai take taya ni,kuma ni na ce ta zauna ta huta”.

“Aaaa,lallai y’ar gatan Amminta” Salim ya fad’a da d’an murmushi.

Baby ta kalle shi,ta na nazartar sa ta ce”sannu da dawowa Bros,ya aiki?”

“Aiki babu dad’i,zo mana sister mu yi sirri” Ya fad’a ya na shirin fita daga kitchen d’in.

Ammi ta ce”lallai fa sirri,idan ta yi tsami dai za mu ji”.

Baby ta tashi ta na dariya ta ce”ai Ammi babu abin da zai yi tsami,indai tsakanina da my bro ne”. Daga haka ta fito ta yi hanyar d’akinsa,kamar yanda ta ga ya yi can.

A zaune ta tadda shi,ya had’e rai ba kamar d’azu ba,ta k’araso jiki a sanyaye ta zauna nesa da shi,don ta lura da yanayin sa tun shigowar sa gidan,ta share ne kawai

“Akwai matsala ne bros?” Ta tambaye shi

Ya ce”ina wannan jakar?”

“Na kai mata abun ta” Ta yi maganar ta na bud’e hannu alamun ko a jikinta.

Ya sauke numfashi ya ce”haba Baby! Me yasa za ki kai mata da kanki? Kuma idan ma dole sai kin je da kanki ai sai ki takura min na kaiki”

Ta turo baki ta ce”to ba kai ka ce ba ka san gidansu ba?”

Ya yi shiru ya na kallon ta,ya na shirin magana ta riga shi “don Allah Yaya zan rok’e ka wata alfarma,duk da na san ba zan samu ba ma”. Ta k’arasa a sanyaye

Salim ya ce”ina jinki”

Ta tashi ta dawo kusa da shi ta zauna,don nuna masa muhimmancin maganar,ta fara”ni dai a yanzu burina kayi aure,ka samu nutsuwa,ka manta da Junaina.Yaya! Zinatu ta na matuk’ar k’aunar ka,wallahi irin wannan macen ya dace ka aura,don na san a yanda take son ka ko ka auri Junaina daga baya za ta jure komai,Yaya Junaina fa ba son ka take ba,wallahi cutar da kai kawai take yi,da za ka bawa wata macen dama ta hanyar auren ta za ka tabbatar da hakan…”.

“Baby kin san yanda nake ji a zuciyata kuwa? Ke ba ki san so k’addara bane ko?” Ya katse ta

Ta yi murmushi ta ce”alhamdulillah! Tunda har ka riga ni sanin k’addara ne,to kamar yanda ka ke ji d’in nan,ita ma Zinatu haka take ji fa,yanda Junaina ta zama k’addarar ka,haka itama ka ke k’ok’arin zama tata k’addarar…”

Ya katse ta da fad’in”a’a,ban yarda ba,ita ce ta d’orawa kanta!”

Ta yi saurin fad’in “kenan kai ma kai ka d’orawa kanka? Idan amsar e ce kenan mutum shi yake zab’arwa kansa k’addara ko? Kai me yasa ka zab’o wadda za ta wahalar da kai?”

Ya yi shiru, ya rasa abin fad’a,sai ta cigaba”wallahi Yaya na ga k’aunar ka k’arara a idon Zinatu,har kuka ta dinga yi duka saboda kai,me zai hana ka gwada saka ta a rayuwarka ko na d’an lokaci ne ka gani?”

“Na riga ki wannan tunanin” Ya katse ta.

Da mamaki ta ce”to amma me ya sa ba ka aiwatar ba?”

Ya ce”na gwada aiwatarwa,sai na tadda matsala,yarinyar ba ta dace da ni ba gaskiya, ba ta da hali”.

Baby ta ce”subhanallah! Wane hali ne da ita? Kuma Yaya kai da ka ce ba ka san ko gidansu ba,ta ya ka san halinta?”

Ya yi guntun murmushi ya ce”bari na fad’a miki gaskiya, yarinyar nan akan gab’a ta zo min,dama ina son in yi aure, ba don ina buk’atarsa ba,sai dan na farantawa Abba rai,yanda yake ta lallab’a ni akan zancen auren nan,shi yasa na yanke shawarar zan yi,amma sai na samu me so na sosai,yanda bayan auren za ta iya jure kowane irin k’alubale,don Junaina ko cewa ta yi na saki matata zan saketa”.

Ya nisa,sannan ya cigaba”a ranar da ta bar jakarta a d’akina,a ranar na yanke hukuncin auren ta,kuma ta na barin wurin bayan ta mari manager na shiga adaidaita sahu na bi bayanta,a gabana ta kira d’an daba ya zare wuk’a zai cakawa me mashin d’in,Allah ya taimake sa suka k’yale shi,kuma dama marin da ta yi ma ya sa ni kokwanto akan tarbiyyar ta.Washegari na dawo unguwar,na yi bincike akan yarinyar,na farko da na tambayi manyan unguwa mutum biyu,suka tabbatar min da yarinyar ba ta da tarbiyya,ta na mu’amala da maza…”

Baby ta katse shi”maza kamar ya?”

Ya ce”maza dai wanda kika sani,kuma na tambayi wasu samari su ma sun tabbatar min da hakan,to tun lokacin na san yarinyar ba matar aure bace,shi yasa na fasa”. Baby ta yi shiru ta na nazari,sannan ta ce,
“Amma Yaya babu wani taimako ko nace uzuri da za ka yi mata? Ta na son ka”

Ya ce”ni kuwa na yi mata taimako,kin san matakin da managerna ya so d’auka kuwa? Da na samu labari,na gargad’e shi indai ya sake na ji wani abu ya same ta,sai na yi shari’a da shi”.

Sai ta rasa abin cewa,ta ce”Yaya sallar magriba”. Ta bar d’akin jiki a sanyaye,amma sam ba ta yarda da zancen yayan nata ba,kuma za ta yi bincike.

 

Sai bayan la’asar na koma gida,na tadda Baba a k’ofar gida shi da wani mak’ocinmu,na gaishe su,kaina a k’asa na shige gida,na zauna ina ta tunanin k’aryar da zan yi masa idan ya ritsa ni.Ga mamaki na,sai na ga Baba ya bawa banza ajiya ta,aikuwa na ji dad’i sosai na ce watak’il ya sassauta hukuncin ne.

Washegari ko minti biyar ban k’ara ba akan lokacin da Junaina ta bani,yau ta na nan kuma ita kad’ai ce a wurin babu wannan matashin,bayan mun gaisa ta kawo min lemo da ruwa,ni dai ban sha ba,burina kawai na ji ta bakinta.

Ta nisa ta ce”ke dai yanzu idan na fahimce ki,ki na son sanin duk abin da Salim ya ke so,da kuma wanda ba ya so,abin da yake burge shi,da wanda ba sa burge shi ko?”

Na ce”e hakane,idan da dama ma har kalar abincin da ya fi so,da wanda ba ya so”.

Ta yi wani murmushi ta ce”za ki ji komai,amma fa akwai sharad’i”.

Na ce”na amince da sharad’in ki,fad’a min kawai”.

Sai ta yi y’ar dariya ta ce”y’an mata da sauri haka?”

“Zan iya yin komai don Salim ya aureni” Na fad’a ina murmushi

Ta gyara zama ta ce”kin ga yaron da ki ka gani jiya anan? Abokina ne, shi yake taya ni jire wurin nan,kuma gidanmu d’aya da shi,to jiya ya fad’a min ya na son ki,kallo d’aya ya yi miki ya ji sha’awar ki ta kama shi”

Sai ta yi murmushi ta ce”ai ban ga laifin sa ba,kin had’u Zinatu.To a tak’aice dai ya na son kwanciya dake ko sau d’aya ne,wannan shi ne sharad’in idan kin amince ko yau a shirye yake,ni kuma da kun kammala zan ba ki bayanai”.

Tunda ta fara magana wani abu ya zo ya tokare k’irjina,na ji kamar na tashi na yi ta fesa mata mari.Ni kam ko da wasa ban tab’a sha’awar aikata wannan mummunan abun ba, to ta zarge ni ne ma wai da take kawo min wannan tayin?

“Ki bani lambar ki,idan na yi shawara zan kira ki” Na fad’a ina mik’a mata wayata.

Ta saka min lambar na karb’a na yi mata godiya na tafi.
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 12

Lokacin da na k’arasa gida har an yi sallar isha’i,tun daga nesa na hango Habib zaune a bencin k’ofar gidanmu,na rage sauri na dinga d’aga k’afa kamar ba na so,kallon shi kawai nake yi cikin tausayawa,indai abin da na ke ji a zuciyata game da Salim,shi ma Habib haka ya ke ji game da ni,to kuwa tabbas zan tausaya masa,sai dai ba zan iya sadaukar da farincikina akan na wani ba.

“Barka da zuwa gimbiyata”. Ya fad’a bayan na zo dab da shi

Na zauna a bencin nesa da shi na ce”daga ina haka?”

“Daga gida nake” Ya bani amsa

“A yi hak’uri dai a min uzuri,na karya dokar sarauniya,ina fatan za a tausayawa raunanniyar zuciyata wurin yi mata hukunci. Na ji kin ce kin tafi hutun amsa kira,kuma ban sani ba ko har yau ba ki dawo ba,shi yasa ban kira ki ba na yi gaban kaina na zo”. Ya k’arashe maganar a raunane,wai a dole na ji tausayin shi

Na k’ura masa ido tun daga kanshi,har yatsun k’afarsa,har yau na kasa gano makusar Habib,ya na so na sosai ga shi d’an’uwana,ko bai b’ata bakinsa ya fad’a min ba,na san zai kula da ni da soyayya idan ya aureni,ya na da hak’uri sosai duk wani laifi da nake yi masa da gangan ya na sani ya ke sharewa,ko wani bai fad’a min ba na san idan na aure shi zan ji dad’i.Amma sai dai kash! Kwata-kwata Allah bai d’iga min son shi a zuciyata ba,a da na amince da shi ne saboda ina ganin ni fa duk duniya babu wani namiji da zan so da aure,ashe lokaci ne bai yi ba,ni kuma GAJEN HAK’URI na ya sa ni saurin zab’ar Habib, ashe sarkin zuciyar tawa ya na dab da bayyana,gaskiya na yi garaje.

Ban san hawaye na ke yi ba sai da na ji muryarsa ya na fad’in “subhanallah! Zinatu lafiya kuwa? Me ya ke damun ki? Ko ba ki da lafiya ne?”

Na share hawayen cikin dakiya da jarumta na ce”Yaya Habib, ina son magana da kai ta fahimta,Allah yasa za ka fahimce ni”.

Ya sake tattara hankalin sa wurina,alamun damuwa k’arara sun bayyana a fuskarsa ya ce”me zai hana? Zan fahimce ki Zinatu, ki fad’a min don Allah”

“Idan na tambaye ka,ka na so na ban yi maka adalci ba, na san duk duniya babu wani namiji da ya ke so na sama da kai Yaya Habib,amma a wane mataki ka ajiye so na a zuciyarka?”

Ya sauke numfashi har yanzu dai da alama bai nutsu na ya ce”Zinatu,ba iya son ki nake ba,har da k’aunarki,k’auna me tsanani ma kuwa,kuma kin kai mataki na k’arshen k’arshe a zuciyata”.

Na d’auke kaina daga kallon sa na ce “idan na fasa auren ka ya za ka ji? Ma’ana idan k’adddara ta sa na auri wanin ka…”

Ban k’arasa ba ya katse ni,a sanyaye”amma me ya kawo wannan maganar?”

“Ka fara bani amsa kafin ka ji dalili” Na fad’a har yanzu ban kalle shi ba.

Cikin raunin murya ya ce”Zinatu ni musulmi ne,na yarda da k’addara me kyau da akasin ta,wallahi ina tunanin irin yanda zan ji,da kuma yanda rayuwata za ta kasance idan ban aure ki ba, saboda ke kad’ai nake so.Amma hakan ba zai sa na kasa yarda da k’addara ba,tunda na sani wani ba ya auren matar wani,kuma duk da ke kad’ai ce a zuciyata,amma a kullum ina sake neman zab’in Allah”.

Jikina ya yi wani mugun sanyi,gaskiya Habib ya na da hankali,kuma na san har da ilimin addini a wannan kyaun zuciyar nasa,ina ma ace shi ne Salim! Da zan bugi k’irji cikin dubunnan mata na ce na fi kowace mace dacen miji,sai dai kash! Zanen k’addara ba ya gogewa,don kuwa har yanzu ban ji son Habib a raina ba,sai dai tausayin shi,kuma wallahi ba zan iya sadaukar da farincikina ba akan shi,sai dai ya yi hak’uri ya d’auki tasa k’addarar kamar yanda nake shirin rungumar tawa

“Akwai wata matsala akan maganar aurenmu ne Zinatu?” Ya tambaye ni

Kamar na yi masa k’arya sai dai na daure na ce”Yaya Habib ko a cikin maza kai namiji ne,ka had’a abubuwa da dama wanda duk mace me hankali za ta so ta same ka a matsayin abokin rayuwa,sai dai ni har yau na kasa jin son ka a zuciyata saboda ba ni da hankali…”

Ya yi saurin katse ni da fad’in”a’a Zinatu,kar na sake jin haka daga bakinki,ki na da hankali,wannan ba laifinki bane laifin zuciyarki ne,shi ya sa ake son mutum ya dinga addu’ar Allah yasa ya fi k’arfin zuciyarsa,zuciyarki ta fi k’arfin ki,da ace kin fi k’arfin ta za ki iya yi mata tilas ta so abin da hankalin ki ya ke baki daidai ne”.

Wasu hawaye suka zubo min,na share na ce”wallahi har zuciyata,na so na yi wa mahaifana biyayya don na faranta musu,su yi alfahari da ni ko da sau d’aya ne a rayuwa,amma rafkananniyar zuciyata ta gaza bani had’in kai.Ka yi hak’uri Yaya Habib na fasa auren ka,saboda ko da na aure ka ba zan tab’a iya baka farincikin da ya dace namiji nagartacce irin ka ya samu daga matarsa ba”.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Ya furta kawai

Shiru na tsawon lokaci sannan ya ce”Zinatu na sani dama can ba kya so na,amma na tabbata yanzu akwai dalilin ki na fasa aurena,me ya sa? Don Allah kar ki b’oye min”.

Gaskiya ban ji zan iya ba shi labarin Salim ba,don haka na girgiza masa kai alamar a’a sannan na ce”ka d’auka hakan k’addara ce kamar yanda ka sanar da ni ka yarda da ita.Ni dai yanzy alfarma d’aya nake nema a wurin ka, wannan alfarmar idan ka yi min ita ce kawai za ta sani na tabbatar da k’aunar da kake yi min,kuma zan rik’e ka a zuciyata masoyi na gaskiya,na yi maka alk’awarin duk sallolina biyar na kowace rana zan yi maka addu’ar Allah ya baka mace ta gari,kuma Allah ya cire maka so na a zuciyarka”.

“Wace alfarma ce wannan?” Ya tambaye ni,jikinsa duk ya yi sanyi

Na gyara zama ina fuskantar sa na ce”Yaya Habib so na ke ka fad’awa manya ka janye maganar aure na,don Allah ka yi min wannan”.

Ya saka yatsan sa a baki ya ciza kafin ya ce”haba Zinatu! Me yasa ki ke da son kanki da yawa? So ki ke ni aga laifina fa kenan,ki na so a saka ni a jeren masu sab’a alk’awari kenan? Kuma da wane idon kike so na kalli mahaifanki?”

“Ka na nufin ba za ka iya yi min wannan alfarmar ba,a matsayina na wadda ka ke kira farincikin ka?” Na tambaye shi muryata na rawa.

Ya tashi tsaye ya ce”e,ban yi miki k’arya ba Zinatu,ke ce farincikina,amma ba zan iya yi miki wannan abun da kika nema ba,gaskiya sai dai ki yi da kanki.Kuma ki yi tunani kafin ki yanke hukunci,so da yawa mutane su na son abu kuma abun ba alkhairi bane a rayuwarsu,kuma sai su k’i abun da shi ne alkhairi a duniyarsu da lahirarsu,shi ya sa istihara take da amfani,ki je ki yi ta istihara ki nemi zab’in ubangiji,idan still kin ji ba za ki iya aurena ba,sai ki sanar musu da abin da kika yanke,ni ma zan saka ki cikin addu’o’ina in sha Allah, Allah ya mana zab’in alkhairi”.

Ya na gama maganar ya buga mashin d’insa ya tafi,ni kuma na tashi na shiga gida ina kukan rashin gaskiya.

‘Dakina na shiga na fad’a a katifa,na fashe da kuka sosai,ni ma na san ban yi wa Habib adalci ba,to amma ya zan yi? Haka k’addarar mu ta zo mu duka ukun,da ni, da shi da Kuma Salim,duk Allah ya jarabce mu da son maso wani.

Bayan na gama kuka na sai tunanin sharad’in Junaina ya dawo min,a gaskiya ina son Salim kuma ko da na ke ganin zan iya yin komai a kansa abun bai kai na aikata zina ba,to na saida mutunci na don ya aure ni,na je masa fanko kuma na saka ran zan yi wata daraja a idonsa? Ai idan na yi hakan na yaudari kaina,kamar an ba ni umarni na d’akko wayata na dubo lambar Junaina na doka mata kira

Ta d’aga da sallama ta na kiran sunana,ban amsa ba na fara magana”Junaina wannan sharad’in ya yi min girma,gaskiya ba zan iya ba,idan akwai wani ki fad’a”.

“Za ki yarda da romance? Ina nufin ki yarda ya biya buk’atarsa ba tare da ya kusance ki ba”. Ta fad’a kai tsaye kamar me bani shawarar na yi azumi ko sallah

Na yi shiru,ina tunani duk zina ai sunan ta d’aya ne,ko ta ido ma an ce ana zina bare kuma wannan babban abun

“Idan fa kin ga ba za ki iya ba,babu dole” Muryarta ta katse ni.

Mu na cikin wayar kiran Baby ya shigo,na yi saurin ce mata”zan kira ki anjima”.

Na katse kiran,na d’auki na Baby na k’irk’iri murmushi me sauti na yi mata sallama.

Ta amsa sannan ta ce”da fatan kina lafiya matar Yaya Salim”

Na ji zuciyata ta motsa,na yi y’ar dariya na ce”Baby kenan,to Allah ya tabbatar”.

Ta ce “Amin”.
Sannan ta yi jim ta ce” amm…Zinatu ina son ganin ki gobe,akwai magana me muhimmanci da za mu yi da ke akan Salim,ina tunanin na samo mafitar da za ta shigar da ke wurin shi ta hanya me sauk’i”.

“Da gaske kike!?” Na fad’a da d’an k’arfi,farinciki ya mamaye zuciyata

Ta ce”e,goben ki zo shagon gyaran jikina da yamma”

Na yi mata godiya na ce zan zo mu ka yi sallama.Tun kafin na ajiye wayar na ji muryar Baba ya na k’wala min kira

Gabana ya fad’i,don na san yau dama tara ni ya ke yi,na saka hijjabi na fita kaina a k’asa kamar malama,na je na tsugunna nesa da shi a tsakar gida na ce”Baba ga ni”.

Ya ce”Zinatu da gaske dai ban isa da ke ba ko?”

Muryata na rawa na ce”a’a,wallahi ka isa da ni Baba”.

Ya ce”to indai kin yarda ni ne na haifeki,daga yau kada ki sake fita ko k’ofar gida sai da izinina!”

Ban ce komai ba,sai gyad’a kai da na yi alamar na amince,na tashi na koma d’ak’i na fashe da kuka.

 

HABIB😥
Babu me son Habib don Allah?
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 13

 

Bacci kad’an na samu a daren,ina ta tunanin yanda zan yi na yiwa Baba biyayya,ba na son b’ata masa rai,amma kuma Baby ta buk’aci gani na goben,kuma na san ba zai yiwu na ce ita ta zo ba,tunda k’aruwa ta ce ba tata ba,na so ma na ce ta fad’a min ta waya sai kuma na ga rashin dacewar hakan,ta na ta k’ok’ari a kaina,ai sai ta ga kamar ma ban damu ba,itama ta janye jikinta.Ga tunanin yanayin da na saka Habib a ciki,watak’il ya na can a cikin damuwa ta dalili na.Ita dai Junaina na ajiye buk’atar su a gefe,don ta yi kad’an ta saka ni aikata zina,ta dad’e ba ta bani bayanan Salim d’in ba don uwarta!.

Washegari da ciwon kai na tashi,ina d’aki tun safe,na kira Salim har sau biyar bai d’aga ba,na tura masa sak’on fatan alkhairi,ina nan kwance ina ta juye-juye da sak’a da warwara na ji sallamar yayata anti Na’ima,na yi farinciki da zuwanta sosai kuwa,na fito tsakar gida inda suke zaune da Mama Saude ni ma na zauna mu ka shiga shan fira,don babu laifi anti Na’ima su na shiri da Mama,cikin firar take fad’a min alfarma ta zo nema a wurin Baba

Da mamaki na ce”alfarma kuma anti?”

Ta ce”e mana,so na ke ya bani ke mu tafi gidana,na fara yi miki gyaran jiki”.

“Kuma tun yanzu ake yi?” Na tambaye ta.

Ta ce”to Zinatu sai yaushe? Sati biyar ne fa ya rage,sai na miki na sati hud’u,ki dawo idan bikin ya rage sati d’aya”.

Jikina ya d’an yi sanyi na ce”to Allah yasa ya yarda”.

Mama ta ce”zai ma yarda,ai ko ni sai na saka baki ya amince,to wa ya k’i gyara?”

Anti ta ce”a to! Idan ma Habib d’in kike ji ai ya san hanyar gidana,sai ya dinga zuwa kuna gaisawa”.

“Uhm!” Kawai na ce,don ni fa ganin lamarin aurena da Habib na ke kamar almara.Na rasa ta yanda zan sanar da su na fasa,kowa na kalla sai na ga ya yi min kwarjinin da ban isa na tunkare sa da wannan batun ba,to amma fa na ga hakan ba mafita bace,tunda abu ya na ta k’ara matsowa,ya zama dole na samu mafita kafin sati biyun.

Bayan la’asar ta koma gidan Ummi, ta ce idan Baba ya dawo na kira ta a waya,kuma na shirya idan ya amince a yau za mu tafi Hotoro,k’arfe hud’u da rabi Baby ta yi min waya ta na tambayar zan shigo kuwa? Na ce mata ina nan tafe.

Da na gama shiri ma na jima ina nuk’u-nuk’u a d’aki,don ina shakkar taka umarnin Baba yau d’in,sai da na ga Mama ta shiga band’aki,sannan na zo na fice sad’af-sad’af,ba tare da na rufe k’ofar d’akina ba,na je na hau adaidaita,sai Sharad’a.

Muka gaisa da Baby cikin fara’a,ta bani wurin zama ta na tsokana ta da matar Yaya,ni kuwa sai murmushi nake ina jin kamar ya tabbata.

“Zinatu kin je wurin Junaina?” Ta tambaye ni

Kamar na yi mata k’aryar ban je ba sai na ga rashin dacewar hakan, “e na je” Na bata amsa

Ta gyad’a kai ta ce”to ya ku ka yi? ”
Na yi jimm! Don ba na jin zan fad’a mata irin sharad’in da Junaina ta bani,don haka kawai na ce”cewa ta yi na je na tambaye shi,shi ya san dalilin da yasa ya ke son ta”.

Baby ta tab’e baki ta ce”ai dama na fad’a miki kar ki je”.

“Kin san mafitar da na samo miki?” Ta tambaye ni,na girgiza kai alamar ban sani ba

Ta ce”kin ganni nan! Duk gidanmu an fi so na,ana ji da ni,kuma ana gudun b’acin raina sosai, musamman Yaya,don ni kad’ai Allah ya jarabta da ciwon zuciya,idan ya tashi ina shan wahala sosai,su na mugun lallab’a ni don kar ciwon ya tashi,to kin ga kuwa idan na so za ki iya shigowa rayuwar Salim ta dalilin ciwona”.

Na yi jim! Na y’an sakanni,kafin na ce”amma Baby ki na ganin hakan zai yiwu? Kuma ke d’in tada ciwon naki za ki yi saboda ni?”

Ta yi murmushi ta ce”Zinatu,ina son Yayana sosai,ina yi masa sha’awar ya auri macen da take mugun son shi kamar ke,saboda ban San lokacin da zai daina shaye-shaye ba,kuma kin San zama da me shaye-shaye sai wanda ya jure,sai mace me mugun hak’uri, ko kuma wadda take bala’in k’aunar mijin”.

Na jinjina kai alamar gamsuwa,ina dai sauraron ta,amma ni har mantawa nake da shaye-shayen Salim,don a ganina ba komai bane,wannan k’aramar matsala ce.Hmmm! Ashe na yi kuskuren fahimtar da ya kusa jefa ni a rijiya gaba dubu,nan gaba dai za ku ji…

Baby ta d’ora da fad’in”zan nuna masa kawai indai yana son farinciki na to ya aure ki,idan ya k’i amincewa sai na fara nuna ina cikin damuwa,na daina walwala a gaban kowa,hakan zai tashi hankalin kowa na gidan,har su nemi jin ba’asi,to a sannan ne zan sanar musu da na zab’a mishi ke kuma idan bai aureki ba mutuwa zan yi…”

Ta na kawowa nan na tuntsure da dariya,ta saki baki ta na kallo na,sai da na yi me isa ta sannan ta rik’e hab’a ta ce”mene ya sa ki dariya?”

Na ce”haba Baby! Na ji ki na zance ne sai kace a shirin films, yanzu kawai sai ki cewa iyayenku kin yiwa Salim zab’in matar aure? Kuma don kin ce za ki mutu idan bai amince ba sai su yi masa dole?”

Baby ta yi murmushi ta ce”ki na mamaki ne? Da ace yau zan bawa Abba da Ammi labarin ki,na ce musu na yi k’awa ina son ta sosai,wallahi gobe idan ki ka zo gidanmu sai kin yi mamakin yanda za su karb’e ki,don har Abba ba zai fita aiki ba saboda ku gaisa”.

Na jinjina kai na ce”a lallai na yarda ke y’ar gata ce”.

Ta yi dariya ta ce”yanzu kin san yanda za a yi? Zan cewa Ammi na samu k’awa,na san za ta yi farinciki sosai”

Na katse ta da fad’in”to wai ke d’in ba ki da k’awaye?”

Ta yi wani murmushi ta ce”yanzu ba ni da k’awa ko d’aya,da dai ina da k’awa,sai ta ci amanata, na yarda da ita sosai ina son ta,amma ta cuceni,ta raba ni da wanda na ke masifar so,da tuni shi zan aura,yanzu haka har an yi auren su.Tun daga lokacin ban kuma sha’awar yin wata k’awa ba,kowa sai dai mu gaisa sama-sama,amma banda k’awance”.

Cikin tausaya mata na ce”Allah sarki,Allah ya saka miki cin amanar da suka yi miki”.

Ta yi murmushi ta ce”manta da su kawai.Za ki fara zuwa gidanmu as mun shak’u da juna,ni ma zan dinga zuwa gidanku,to daga nan sai na fara nuna wa Ammi kyaun halinki,idan na ga ba ta gane inda na dosa ba,sai na yiwa Salim zancen kai tsaye,tunda ya san komai,idan bai amince ba sai na yi plan d’in da na shirya”

Na ce”amma ki na ganin hakan zai yiwu kuwa?”

Ta ce”yes! Abu me sauk’i,amma fa gaskiya sai nan da sati uku”.

Gabana ya fad’i da na tuna saura sati biyar bikina,ga shi ta ce sai nan da sati uku za a fara wasan,kuma ban san sati nawa game d’in zai d’auke mu ba.

“Me yasa sai nan da sati uku?” Na tambaye ta

Ta ce”e,saboda nan da sati uku Salim zai yi birthday, ya na girmama birthday d’insa,shi ya sa ba na son rage masa farinciki kafin zuwan ranar,don indai ina cikin damuwa shi ma ba ya tab’a walwala”.

Hmmm! Na sauke ajiyar zuciya na ce”to shikenan Baby,na gode sosai da kulawarki”.

Ta ce”kar ki damu,ai yi wa kai ne”.

Ta rakoni har bakin titi na shiga adaidaita sahu na kama hanyar gida.Na yi ta tunanin halin da na jefa rayuwata a ciki,gefe guda kuma na gamsu da mafitar da Baby ta kawo d’ari bisa d’ari,sai dai ina gudun k’urewar lokaci,ace sai aurena ya rage sati biyu za a fara wasan? Yanzu idan komai bai yi daidai ba a sati biyun ya zan yi? Don ban ga alamar Habib zai sanar musu da na fasa auren shi ba,ni kuma gaskiya ina jin tsoron abin da zai biyo baya idan na furta na fasa auren.Kuma ita kanta Baby ban yi kuskuren k’in sanar mata an kusa aurena ba kuwa? Amma gaskiya ba zan fad’a mata ba,don ina jin tsoron ta janye taimakon ta,ta ce na hak’ura da Salim

Da wannan tunane-tanayen na k’arasa gida,lokacin ana shirin sallar magriba,don haka ina shiga gida na d’aura alwala na shiga d’aki,aikuwa Baba ya na dawowa ni ya fara k’wallawa kira,ina jin muryar Mama ta na fad’in,

“Wai wace Zinatu ka ke kira? Ai ba ta gidan nan tun d’azu”.

Baba ya ce” Zinatun ce ta fita yau? Amma ai ga d’akinta a bud’e ko?”

Mama ta ce”zancen kake so,ai sai ka shiga d’akin ka d’akko ta”.

Ina jin haka na kwanta akan sallayar kamar me bacci,don na san Baba akwai ganin k’wak’waf!

Aikuwa sai da ya zo ya d’aga labulen kamar yanda na zata
“Ke Zinatu!” Ya kirani da k’arfi

Na tashi firgigit kamar wadda aka tasa daga bacci na ce”uhm!”

Ya ce”wane irin shashanci ne haka bacci da magriba?”

Na tashi zaune na ce”kaina ne ya ke ciwo”

Ya ce”to Allah ya sawak’e,yanzu Na’ima ta kirani a waya,wai kun yi zancen za ki je gidanta ki kwana biyu,ta jirani kuma sai mijinta ya mata waya ga shi nan a hanyar shigowa garin,to yanzu dai ta riga ta tafi gidan,ke kuma gobe sai ki shirya ki je”.

Na ce”to Baba”.

“Ai ba to ba,saura ki je ki yi ta yawon naki a can,wallahi na ji ba daidai ba sai ranki ya b’aci”.

Na sunkuyar da kai na yi shiru,ya wuce ya na fad’awa Mama ai ina ciki bacci nake yi.

Wajan k’arfe goma na dare ina kwance,kamar a mafarki sai ga kiran Salim,hannuna na rawa na d’aga har da in’ina wurin gaishe shi.Bai amsa ba ya ce”ke nutsu dalla,tambayar ki zan yi”

Na ce”to,ina jinka”

Ya ce”me ya kai ki shagon k’anwata yau?”

Gabana ya fad’i,na yi saurin fad’in”kitso na je”.

Ya yi wata y’ar dariya ya ce”kitso ko? To ke da ita d’in ku iya takun ku,don duk abin da kuke yi a tafin hannuna yake”.

Ya katse kiran,ba tare da ya bani damar wata maganar ba.

Na dafe k’irjina da har yanzu bai daina bugu ba,maimakon na yi nazarin maganar sa,da kuma tunanin yanda ya san na je wurin Baby,ina! Sai na fad’a wani shauk’in son shi,na ji kamar ba ni da wata damuwa a duniya,muryarsa ta mantar da ni duk wata matsala da take tunkaro ni.

 

 

KU NA GANIN MAFITAR DA BABY TA KAWO ZA TA SAMU SHIGA KUWA?

AKWAI WANI K’ALUBALE BABBA A KOMAWAR ZINATU GIDAN ANTI NA’IMA.

Ku dai ku biyo ni🥰
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 14

K’arfe goma na safe na kammala shirin tafiya gidan anti Na’ima,na yiwa Mama sallama ta amsa kamar gaske.Sai da na biya ta gidan Ummi na gaishe ta,ta kwaso min kayan kitchen da zannuwan gado,labulaye da dai sauran tarkace wai duka nawa ne,a to tarkace mana! Tunda su suke ta shirin su,watak’il dai sun tanadi wata matar da za su aura wa Habib,don ni Zinatu na yi masa nisa

Ban jima ba na yi mata sallama na tafi,bayan ta yi min nasiha sosai wadda ba ta fashi indai zan zo gaishe ta.

Fuska babu yabo babu fallasa na shiga gidan Antin,don ina tunanin yanda zaman gidan zai zo min,indai za ta hana ni fita harka ta to fa tabbas tafiyar mu ba za ta yi nisan zango ba,domin kuwa ba na jin zan iya yin sati hud’u ban bawa idona hakk’insa ba,wato kallon Salim

Gidan nata b’angare biyu ne,don ta na da abokiyar zama,ita ce amarya,uwargidan babba ce har ta na da manyan y’ay’a guda uku,Nazifi shi ne babba,kuma mu na shiri da shi sosai,kun dai sanni da maza…sai k’annen sa Hafiz da Umar.Ita Anti Na’ima Allah bai bata haihuwa ba har yanzu,su na zaune lafiya babu wata matsala,shiyasa idan na je ma muddin Nazifi ya na nan,to na fi zama a shahen su,mu yi ta shan firar mu ta duniya.

Don haka yau d’in da na je,bayan ta nuna min kayan gyaran da yanda za ta yi min,na ce mata sai gobe a fara,na tashi na yi sashen su Nazifi,na yi sa’a kuwa ya na nan,a can muka zauna mu ka sha firar mu har la’asar

Na yi zaton ma Anti za ta min fad’an zama na a can, sai na ji ta yi shiru,na taya ta girkin dare muna yi ta na yi min bayanin wasu dabarun girkin,ni dai jinta kawai na ke,ina bin ta da ido.Washegari aka fara yi min gyaran jiki,tun daga ranar kuwa fatata ta fara kyau, cikin sati d’aya na zama kamar ba ni ba,kullum mu na waya da Baby, ko ba ta kira ni ba,ni zan kira ta mu gaisa,haka ma ta b’angaren Salim ba ta canza zani ba,domin kuwa kullum sai na jera masa kira,amma ba ya d’agawa.Lokaci zuwa lokaci bawan Allah Habib ya na fad’o min a rai,don tun ranar da muka yi wannan maganar…bai sake kiran wayata ba, bare ya zo,har Anti sai da ta yi min maganar sa,na ce mata mu na yin waya kullum,ba ni da matsala a zaman gidan,sai dai na fara k’osawa da rashin fita ko k’ofar gida,tunda ko aike na ba a yi,sau d’aya ma na ce zan raka Nazifi kasuwa,maman su ta ce na yi zama na,idan ana gyara ba a shiga rana.

Ranar da na cika kwana goma sha biyu a gidan, wata rana da yamma ina zaune sai ga kiran Salim,Allah ya sa ni kad’ai ce a wurin,don haka na d’aga da hanzari ina yi masa sallama.

“Wa alaikissalam” Ba saban ba yau ya amsa sallamata.

“Da fatan ka na cikin k’oshin lafiya?” Na fad’a,ina dafe k’irjina da ya ke ta bugu kamar na ga abin tsoro

“Kwatanta min gidanku” Ya fad’a, ba tare da ya amsa ni ba.

Sai na ji kamar a mafarki ne ba zahiri ba,yau Salim ke cewa na kwatanta masa gidanmu? Aikuwa sai zuciyata ta fara ayyana min watak’il ya yarda da soyayyata ne,har zai zo mu fara fahimtar juna.

Cikin zumud’i na ce”e…am…yanzu ba na gidanmu”

“Ki na ina? Koma ina ne ki kwatanta min,ga ni nan zuwa yanzu” Ya fad’a cikin d’an fad’a-fad’a.

Jikina ya yi sanyi,na fara tunanin zuwan na shi na lafiya ne ko akasin haka? Amma na fi kyautata zaton alkhairi ne, tunda na san ban yi masa wata kwab’a ba a y’an kwanakin nan.Don haka tiryan-tiryan na kwatanta masa gidan Anti,bai ce komai ba ya katse kiran,ni kuwa na tashi da sauri na shiga band’aki na yi wanka,duk da na yi d’azu na yi kwalliya,na saka doguwar riga,na yafa k’aramin mayafi,na yi zaman jiran shi.

Anti da ke ta hada-hadar girkin dare ta kalleni ta ce”to! Ke kuma ina zuwa haka,ki ka yi shiri ki ka kame a falo?”

Na ce”Anti Habib ne zai zo”.

Ta ce”to! Ai da sai ki ce ya shigo,ku yi firar ku a cikin gida ko?”

Na ce”a’a,sauri ya ke yi,abu zai bani ya wuce”.

Ta ce”to ai shikenan,ki gaishe shi”.

“Zai ji” Na fad’a ina tashi don Salim ya k’ara kira,na san ya k’araso ne.

Sai da na fita na d’aga kiran,ban ma kai ga yin sallama ba na hango shi tsaye a kusa da motarsa,ya na sanye da farar shadda da bak’in glass,ya yi kyau sosai, sai na ji kamar na je na rungume shi na bud’e zuciyata,ya ga irin k’aunar da na ke yi masa, da kuwa babu shakka sai ya tausaya min ko da ba zai karb’i soyayyata ba.

A slow na dinga taku,har na k’araso inda ya ke a tsaye,na yi masa sallama na sunkuyar da kai,ganin yanda ya kafeni da ido tunda na taho

Bai amsa sallamar ba ya fara magana”Zinatu sunanki ko?”

Na ce”e,haka ne”

Ya ce”me ya sa kike son shiga rayuwata?”

Na d’ago na kalle shi,sai na ga tsakanin sa da Alllah ya ke tambayata, na maida kaina k’asa na ce”Allah ne ya jarabceni da son ka,wallahi ba yin kaina bane,kuma da alkhairi nake son ka ba sharri ba”

Ya ja dogon tsaki ya ce”me ya kaiki wurin Junaina?”

Gabana ya fad’i,don ban shirya k’aryar da zan yi ba,tunda ban tsammaci tambayar ba,don haka na ce”ni? Yaushe na je?”

Sai ya ciro wayarsa a aljihu ya yi y’an danne-danne,ya nuno min fuskar wayar, gabana ya fad’i ganin hotona a wayar,ina zaune a shagon Junaina.Na shiga mamaki da tunanin yanda a ka yi har ta min hoto ban lura ba,da kuma tunanin yi min hoton ma duka,lallai wannan Junainar makira ce ashe.

“Me za ki ce game da wannan hoton?” Ya tambaye ni,bayan ya maida wayar aljihu.

“Duk sanadin ka ne Salim,kai fa musulmi ne,don Allah ka tausaya min,ina son ka”. Na yi maganar hawaye na zubo min

Ya ce”saboda ki na so na sai ki nemi cin mutuncin macen da na ke k’auna? Kin san matsayin ta a wurina kuwa?”

Na dafe k’irji,cikin firgici na ce”na shiga uku! Cin mutunci kuma? Ni d’in? To wallahi sharrin ta yi min,Allah ya isa tsakani na da ita!”

Ya daka min tsawa”ke! Kin ga dakata,ni ban zo don ki min rantse-rantse ba,na zo yi miki gargad’i ne da jan kunne,don wallahi ko ta waya ki ka sake zagin ta sai kin yi kwanan prison!”

Na saki baki ina kallon shi da mamaki,Allah ne kad’ai ya san irin k’aryar da ta had’a masa.To amma me yasa Junaina ta yi min haka?

“Idan kunne ya ji…!” Ya fad’a, ya shige motarsa ya tafi,ya bar ni tsaye,ko k’wak’kwaran motsi na kasa yi,kamar na had’iyi tab’arya.

 

“Zinatu!” Nazifi ya kira sunana da alamun mamaki

Na yi saurin kallon shi,sai na ga fuskarsa sam babu walwala,na ja k’afa,na k’arasa inda ya ke tsaye a k’ofar gida.

Ya kalleni da kyau ya ce “kukan me ki ke yi?”

Oho! Ni ban ma san ina hawaye ba sai da ya fad’a, na kai hannu na share na ce”babu komai”.

Ya ce”ban yarda ba! Waye wannan d’in Zinatu?”

Na ce”yayan k’awata ne fa,ya zo ya ke fad’a min ta rasu tun wancen satin”.

“Kuma kun shak’u da k’awar sosai ko?” Ya tambaye ni,ya na maida fuskarsa kalar tausayi

Na share wasu hawayen,ina shirin yin magana ya rigani

“K’aryar ki ba ta samu shiga ba.Me ya had’a ki da J.S har ya zo wurinki? Ba ma wannan ba,me ya fad’a miki da ya saka ki kuka?”

Na ce”a ina ka san shi?”

Ya ce”fara ba ni amsa,kafin ki tambaye ni”.

Haka kawai na ji na yiwa Nazifi yardar da zan ba shi labarin gaskiyar abin da ya had’ani da Salim.Ashe rabon ayi ne ya ja ni…

Mu ka shiga ciki,a tsakar gida mu ka zauna kamar an jona min batir haka na zayyane wa Nazifi tun had’uwata da Salim har izuwa abin da ya kawo shi wurina yanzu.Ya sauke ajiyar zuciya ya na murmushi ya ce”lallai ke ma Zinatu sai a barki! Yanzu ana ta shirye-shiryen aurenki,ke ashe ki na can ki na naki d’an bikin? To wallahi ki na ruwa!” Ya kwashe da dariya

Takaici ya rufeni,na ji dama ban sanar masa ba,na ce”dama don ka yi min dariya ka so jin sirrina?”

Ya daina dariyar ya ce”to ai ki na bada labarin tun kafin ki k’arasa,mafita ta zo min raina,wannan dariyar da kika ga ina yi,har da ta mugunta”

“Mugunta kuma?” Na tambaye shi,ina had’e gira.

Ya ce”yes! Salim na ke yiwa dariya,don kuwa muddin ki ka yarda da sharad’ina to fa ki sa a ranki kawai kin zama matar Salim,ko da za a kira ki da MATAR SHIGE…
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 15

“Zan amince da sharad’in ka kowane iri ne,muddin babu sab’awa Allah a ciki” Na fad’a jikina na d’an yin sanyi,don na tsorata da jin kalmar sharad’i,tunda ga dai yanda mu ka yi da Junaina

Nazifi ya yi murmushi ya ce”babu wani sab’on Allah a ciki,zance ake yi na kud’i muddin ki na da kud’i to kuwa ni zan shige miki gaba har sai kin samu shiga.Ke ni fa ban ga laifinki ba,wallahi yaron ya had’u ga kyau ga kud’i”.

Na d’an fara fargaba,don ban san ko nawa zai buk’ata ba,kuma ni yanzu kud’in hannuna ba su haura dubu takwas ba,na ce”kamar nawa kenan?”

Ya ce”ki tanadi dubu hamsin,kafin nan da kwana takwas”.

“Dubu hamsin!?” Na fad’a ina zare ido,saboda na yi mamaki,kuma uwa-uba ban ga ta inda zan samu dubu hamsin ba.

Ya yi y’ar dariya ya ce”e,dubu hamsin kuma a hakan ma fa bai zama lallai ta isa ba,kin ga ba ni kad’ai zan yi aikin ba,dole sai mun siyi wani na kusa da Salim,wanda zai taimaka mu samu damar gudanar da komai cikin sauk’i,sannan dole na sai get fast…”

Na yi saurin katse shi da fad’in”dakata! Wai wane irin aiki ka ke magana akai? Kuma get fas na meye?”

Ya ce”aiki ne mai wahala kuma me hatsari,amma muddin aka yi sa’a ya wakana babu tangard’a,to ni na tattabar miki kin samu Salim kin gama,sai dai idan ba ki so ba.Shi kuma get fas na shiga wurin da zai yi birthday na ke nufi,nan da sati d’aya ne,haka na ji a bakin wani abokin sa”.

Na jinjina kai na ce”na san da maganar birthday d’in,amma ban san ya kusa ba,zan yi wa Baby zancen na ji ko zan samu get fas d’in”.

Ya ce”to indai za ta ba ki,kawai idan ki ka karb’a ki bani saboda ke ba sai kin shiga wurin ba”.

“Kamar ya!?” Na fad’a ina b’ata rai.

Ya ce”kin ga dai yanzu ki fara tanadin kud’in kafin mu gama tsara komai,amma in sha Allah komai zai zo da sauk’i”.

Na ce”Allah yasa”.

Jikina duk ya yi sanyi, ina tunanin ta inda zan samu dubu hamsin,ya fita daga gidan ni kuma na shiga sashen Anti

A falo na tadda ita ta na kallo,ta kalle ni ta ce”har ya tafi?”

Ni sai yanzu ma na tuna da k’aryar da na yi kafin na fita,na ce”e ya tafi”

Ta ce “ai da ya shigo mun gaisa,yaushe za a bugo invitation?”

Ina shegewa d’akin da aka bani a gidan na ce”kai Anti,ai da saura”.

Zama na yi na kira lambar Baby,ta d’auka,bayan mun gaisa na ke ce mata”ashe birthday d’in mutumin nawa ya zo,ko gayyata ko?”

Ta yi dariya ta ce”ya ma zama naki ko? Ai ban yi zaton za ki je ba,in dai za ki je gobe ki zo ki karb’i katin,jiya ya bani guda uku”

Na ce”me zai hana ni zuwa? Wani ma ya yi rawa bare d’an makad’a? To amma sauran biyun na waye?”

Ta ce”a’a,ai dama ya bani ne kawai ko da wanda zan gayyata,tunda kin ga ni ba sai da get fas ba,tare za mu shiga da shi”.

Na ce”kuma Junaina ta na zuwa?”

Ta yi guntun tsaki ta ce”wai ke meye damuwarki da wannan banzar? Me zai kawo ta?”

Na yi dariya na ce”ke dai kawai ba kya son ta,abu nasu me zai hana ta zuwa?”

Ta ce”ai sai ta zo mu gani”.

Na ce”to suwa za ki bawa? Guda biyu nake so,ina son gayyatar wata k’awata ne”.

Ta ce”ok! Ba matsala,ko gobe sai ki zo ki karb’a ai,don dai yau yamma ta yi ne ma”.

Daga haka na yi mata godiya muka yi sallama.

Washegari da safe Nazifi ya kira ni a waya,ya ce min sun riga sun shirya komai da yanda abun zai kasance,amma fa babu yanda za a yi dubu hamsin ta isa,don haka dole na samo hanyar da kud’i za su shigo.

Gabana ya fad’i cikin sauri na ce “yanzu kana ina?”

Ya ce”ina d’akina,amma yanzu zan fita”.

Na ce”to idan ka fita ka jirani a k’ofar gida,sai na fito mu yi magana”.

Haka kuwa aka yi,ya na fita ni ma na fita,na yi sa’a ma Anti ba ta falo. “Wai Nazifi dubu hamsin d’in ma ka san da yanda zan samu,da har ake neman k’ari?”

Ya ce”to Zinatu me zai hana a hak’ura? Tunda babu dole, wai ni dama taimakon ki zan yi,ganin halin da kike ciki,kuma da ina da kud’i wallahi ni me iya biya ne ayi miki komai ba tare da ko sisinki ba”.

Na sauke ajiyar zuciya na ce”to yanzu nawa ake buk’ata?”

“Dubu d’ari biyu” Ya fad’a kai tsaye.

Na dafe k’irji tare da zaro ido na ce”haba Nazifi! Ko sata na fara ai ba na jin zan had’a dubu d’ari biyu nan da kwana bakwai”.

Ya yi dariya ya ce”wa ma zai aike ki sata? Ki na mace,macen ma buduruwa,buruwar ma me kyaun suffa irinki Zinatu amma ki dinga tunanin ta inda za ki samu dubu d’ari biyu acikin kwana bakwai? Wallahi sai dai rashin niyya!”

Cikin son gano inda zancen sa ya dosa na ce”ban fa gane ba,ka yi min dalla-dalla”.

Bai yi magana ba ya d’akko wayarsa a aljihu,kafin na ankara ya k’yasta min hoto,sannan ya ce”ba ni minti biyar ki gani”.

Ya cigaba da danne-danne a waya,kafin ya kalle ni ya ce”na fad’a miki ba ni kad’ai zan yi aikin ba,dole sai mun had’a da direban sa,duk da ma na ji ance bai fiya son tafiya da direban ba,sai in mahaifinsa ya matsa masa.Sannan wanda zai kula da abinci da kuma abun sha a wurin,shi ma dole sai mun biya shi,ke megadin gidansu ma sai mun biya shi,sannan shi ma abokina da za a yi aikin tare da shi sai an biya shi,ni kuma na yafe, na miki saboda Allah”.

Na ce”ni fa duk ba wannan ba,so na ke na fara jin yanda aikin zai wakana,idan na ji ba mai yiwuwa bane gwara na hak’ura kawai”.

Sai ya duba wayarsa da na ji shigowar sak’o ya ce”kin gani ko!? Dama na fad’a miki ai ki na da kadara” Ya yi maganar ya na murmushi

Cikin rashin fahimta na ce”wai mene?”

Ya ce”yanzu na turawa wani gaye hotonki,na ce masa haja ce sabuwa dal,nawa zai siya? Shi ne ya ce ya siya dubu d’ari biyar kwana biyu”.

“Nazifi ni ce hajar!?” Na fad’a da k’arfi,zuciyata na zafi

Ya yi shiru ya na kallo na. Na d’ora”tun farko sai da na fad’a maka zan yarda da sharad’in ka ne kawai idan babu sab’on Allah a ciki…”

Ya katse ni”wannan ba ya cikin sharad’i ai,idan ki na da hanyar samun kud’in an wuce wurin”.

Na ce”Nazifi,ban tab’a Zina ba,kuma ba zan fara ta ba saboda Salim,idan na bada kaina ka na da tabbacin abun da za mu shirya d’in zai yiwu? Idan ba mu yi nasara ba fa? Na yi biyu babu kenan fa,ko kud’in za su siyo min wani mutuncin? Idan ma aikin ya yi kyau,da wane ido zan kalli Salim bayan ya aureni? Me zan fad’a masa?”

“Gaskiya ne!” Ya fad’a da d’an rauni a muryarsa

Sannan ya ce”ni dama na yi tunanin ba ki da hanyar samun kud’in ne,shi ya sa na yi hakan”.

Na yi huci me zafi na ce”tabbas! Ba ni da wata hanya da zan samu dubu d’ari biyu,amma hakan ba zai sa ni aikata zina ba.Mutuncina na mijina ne in sha Allah, ba ma Salim ba,duk wani namiji da ya aureni ko da ba na son shi shi kawai zan mallakawa kaina.Zan dai nemi wata hanyar ba wannan ba,zan yi shawara”.

Ya ce”to,amma ki yi da wuri,kin ga lokaci ya na k’urewa”

Na ce”in sha Allah! Sannan maganar get fas,na samu guda biyu, anjima zan k’arb’o a wurin Baby”.

Ya ce”yawwa! Ya yi kyau,idan na dawo da daddare sai ki taho min da shi sashenmu”.

Ranar haka na wuni ina ta tunanin ta inda zan samu wannan kud’in,to ni kam indai ba kayan lefena zan siyar ba ta ina kud’in za su fito? Ga shi sai hanya-hanya ya ke min,ya k’i sanar min yanda aikin ya ke,da dubu hamsin ne ma da tsaf zan shafawa idona toka na tambayi Habib,don na tabbata zai bani,amma gaskiya dubu d’ari biyu ya yi yawa,da me zai ji? Ga duka ga tsinka jaka!

Dab da magriba na tambayi Anti zan je gida na d’akko wasu kayana,sai da ta yi min fad’a kafin ta bar ni,wai meyasa tun safe ban je ba sai da magriba? Haka dai na shirya na tafi shagon Baby,sai dai ina zuwa na tarar ba ta nan,wai lokacin tafiyarta gida ya yi.Na kirata a waya na sanar mata na zo mata nan,ta ce sai dai na k’araso gidansu tunda babu nisa,ta kwatanta min na kama hanya.

WANI KUSKURE…

Ban san zuwa na gidan su Salim a lokacin kuskure bane sai daga baya,da na je na tarar da megadi,amma bai hana ni shiga ba,ina dai tunanin Baby ta sanar masa za ta yi bak’uwa,lokacin har an shiga masallaci ana sallar magriba,a tsakar gida na tadda Baby,ta tareni da farinciki,mu ka k’arasa ciki,ta na ta murna

Mu na zama sai ga wata matashiya ta zo ta kawo min abun motsa baki,na tambayi Baby wace ita? Ta fad’a min me taya su aiki ce,sunanta Habiba.

Na sha lemon da ta kawo min,sannan mu ka gaisa da Baby na ce”yi sauri ki d’akko min,kin ga magriba ta yi”.

Ta ce”Tabb! Ai ki tashi ki yi sallarki,yau sai kin ci abincin dare a gidan nan”.

Na ce”rufa min asiri Baby,kunyar Ammi na ke ji wallahi”.

Ta kwashe da dariya,har da rik’e ciki ta ce”wato ga surukarki ko? Aikuwa dole sai kun gaisa,don ta san da zuwanki,sallah take yi shiyasa ba ta fito ba”

Na tashi tsaye na ce”don Allah Baby ki rufa min asiri,wallahi sauri na ke yi”.

Ta yi murmushi ta ce”to bari na nuna miki abun d’ebe kewa”.

Kafin na yi magana ta ja hannuna,ta nufi wani d’aki da ni,ta tura k’ofar ta bud’e mu ka shiga,ni na yi zaton ma d’akinta ne,amma ina shiga sai na ji irin k’amshin da nake ji a jikin Salim ya daki hanci na,ga wani k’aton hotonsa a bangon d’akin,ya yi kyau sosai yana sanye da k’ananun kaya,a d’ayan bangon kuma na shi ne,shi da Baby,ta rirrik’e shi su na dariya,sun yi kyau sosai,kamar rak’umi da akala haka ta ja ni har kan gadonsa.

Ta ce”ga d’akin angon ki nan,na san ba za ki gaji da jiran Ammi ba “.
Na zauna a bakin gadon,kamar wata amarya,tuni na ji wata kasala ta rufeni,k’amshin sa duk ya cika d’akin,har na fara zargin ko dai ya na ciki?

Na kalli Baby na ce” k’amshin Salim duka ya cika d’akin,ko dai ya na nan?”

Ta yi dariya ta ce”turarukan shi dai su na nan,ko na ba ki d’aya?”

Na zare ido na ce”rufa min asiri,idan ya tambaye ki Wanda ya d’auka fa?”

“Sai na ce ke ce” Ta fad’a ta na d’age kafad’a.Na yi murmushi na tashi, na ce,
“Don Allah mu fita,ni dai gida zan koma”.

Ta d’akko wani turare a gaban mudubi ta damk’a min a hannu ta ce” ni ce na ba ki kyauta”.

Na karb’a na ce”na gode”.

Da mu ka fito ba Ammi ba ta dawi falon ba,sai ta ce bari ta kira ta mu gaisa,ni dai duk sai na ji kunyar matar tun kafin na ganta,haka dai na zauna don kar Baby ta ji babu dad’i

Wayata ta fara ringing na ga Nazifi ne me kira,kamar kar na d’aga sai dai na d’aga,get fas ne ya ke tambaya ta,na ce ya ba ni mintuna ina cikin gidan

Ina gama wayar Ammi ta na k’arasowa tare da Baby,babbar mace ce y’ar gayu,fara ce tass! Don da gani ma hasken ta Salim ya yi

Ta k’araso da murumushi a fuskarta ta zauna a d’aya daga cikin kujerun

Na ji ta yi min wani kwarjini,na sakko na zauna a k’asa,kaina a duk’e na gaishe ta

“Lafiya lau Zinatu,ta shi ki koma kujerar” Ammin ta fad’a

Bam koma ba,kuma ban d’ago na kalle ta ba

Baby ta ce”Ammi sauri take yi,bari na raka ta”.

Ta ce”to! Rowa za ki ma k’awar taki,ba za ta ci abinci ba?”

Na yi saurin fad’in”na k’oshi Ammi,na gode”. Na tashi na yi hanyar fita,ina ta wasa da kwalbar turaren ta cikin hijjabina.

Kafin Baby ta fito daga d’akinta har na fice tsakar gida,bayan na yi wa Ammi sai da safe.Baby ta fito hannunta rik’e da leda,ta mik’o min,sannan ta ba ni get fas d’in guda biyu.

Na amsa na ce”ke! Wannan ledar ta meye?”

Ta ce”Ammi ta ba ki”.

Na ce”to ki taya ni godiya,Allah ya saka”.

“Ameen” Ta fad’a, ta na murmushi.Sai da ta raka ni har k’ofar gida sannan ta koma

Ina tsaye a bakin titi ina jiran adaidaita sahu,na ga hango wani mashin tun daga nesa ya dalle min fuska da hanke,ni ma shi na ke kallo don ina son sanin ko waye,amma hasken ya kashe min ido har na kasa gane shi,ya zo ya wuce ni.Na shiga adaidaita,bayan na zauna na bud’e ledar,da kud’i na fara cin karo,na yi mamaki don haka na yi saurin d’akko su,na k’irga dubu biyar ne cif,sai wata atamfa me kyau,da mayafi,sai wani saitin turare a kwali,na ji dad’in kyautar sosai,na kai kwalbar turaren Salim hancina,na shak’a har da lumshe idona,sai na ji kamar ina tare da shi ne,na jefa shi jakata tare da kud’in,na kuma fara tunanin yanda zan yi idan Anti ta tambaye ni wanda ya ba ni.

Ina shiga gida mu ka had’u da Nazifi,ya tare ni da fad’in”yawwa kin samu abun?”

Na ce”an samu” Na d’akko get fas d’in na ba shi duka,sannan na yi masa bayanin kayan da Ammi ta ba ni
Ya ce”tab! Aikuwa Anti ta na falo, don yanzu haka daga can na ke”.

Na ce”yanzu me zan ce mata?”

Ya yi dariya ya ce”ai kawai ki bar min,dama yau zan je zance,kin ga sai ayi kyauta akan kyauta,ita ta ba ki,ke kin ba ni,ni kuma na bawa wata”.

Na harare shi na ce”kyautar surukar tawa? Ina so ni ma”

Allah ya taimake ni hijjabi ne a jikina,na saka saitin turaren cikin jakata,na soke sauran kayan a jikina,na shiga d’akin.

Washegari da safe sai ga sak’on Salim a wayata,hannu na rawa na bud’e,duk da na san ba ya nema na sai na yi masa wani laifin,ko sallama babu a sak’on,tambaya ta kawai ya ke yi,wai da fatan dai jiya ba gidansu na je ba.

Na maida masa da amsa _”idan na je gidanku zai zama matsaka ne?_

Ina ta jiran amsa na ji shiru,na tashi na d’akko turaren da daga jiya zuwa yau na shinshina shi ya fi sau shurin masak’i.
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 16

*O’o! Fans😂,ni fa ba matar shege sunan littafin nan ba🤦🏻‍♀️Matar shige ne,(shi)na ke sakawa ba (she) ba,matar shige ba ta daraja,ni na isa na ce matar shege ba ta daraja? Shi ma shegen ai ba shi ya zab’awa kansa kasancewa a haka ba*

Yau kwanaki uku kawai suka rage min na biyan kud’in da za a yi min aikin nan,kuma har yanzu dubu goma sha uku ne a hannuna,ni da nake buk’atar dubu d’ari biyu,duk iya tunanina na kasa gano ta yanda wannan kud’i za su shigo min,har wata rama na yi a y’an kwanakin.Tun Nazifi na yi min magiyar na kawo har ya gaji ya daina yi min zancen

Kuma har yanzu Habib bai kira ni ba,bai kuma zo gidan Antin ba,bare na saka ran wani abun daga wurin sa.Kullum sai na yi sana’ar tawa,ta kiran Salim amma sam! Ba ya d’agawa.Junaina ta kira ni jiya take tambaya ta ya batun bayanan Salim d’in? Don haushi ban san lokacin da na k’unduma mata zagi ba,na dinga surfa mata ruwan ashar kamar zan ari baki,kuma na ce idan ba ta yi recoding ta kunnawa Salim ba, ba ta haifu ba! Ba ta tanka ni ba dai, ta katse kiran,na danna shegiya a blacklist na yi wurgi da wayar.

Ranar Asabar ne ya kama birthday d’in,don haka ranar Juma’ar nan duk wanda ya kalleni sai ya gane ina cikin damuwa,Anti kuwa tun kwana biyu da suka wuce ta zaunar da ni ta tambaye ni,na yi mata k’aryar babu komai,ko d’azu mun yi waya da Baby ta sake tambaya ta,na tabbatar mata da zuwa na goben.

Da yamma mu ka keb’e da Nazifi a k’ofar gida,ya kalle ni da kyau ya ce “Zinatu! Yau ce fa rana ta k’arshe da ya kamata a kammala duk wani shiri! Kuma kin ga dole sai da kud’i, wanda za mu yi aikin tare ya na da wasu uzururrukan fa”.

Na yi huci me zafi,ina kalmashe hannayena a k’irji,na ma rasa abun fad’a

Ya ce”kin yi shiru”.

Na yi jim! Sannan cikin sanyi na ce” Nazifi a bar shi kawai na hak’ura,idan Salim rabo na ne zai aure ni”.

“Wai duk saboda kud’in ki ka hak’ura?” Ya tambaye ni

Na ce”e! Tunda na yi duk yi na,ban samu hanyar samu ba,kuma lokaci ya k’ure”.

Nazifi ya yi shiru kamar me nazari,can ya jinjina kai ya ce”ina zuwa”. Ya ja gefe can nesa da ni,ya ciro wayarsa a aljihu ya kara a kunne

Wallahi ban san da wanda ya yi waya ba,ba na jiyo muryarsa bare na fahimci wayar,kuma ya juya baya bare motsin bakinsa ya d’an yi min k’arin haske,wajan minti biyar ya na waya,sannan ya dawo inda nake ya na fara’a,har abun ya so bani mamaki.

Na ce”kuma murmushin na meye?”

Ya washe baki ya ce”ke na ke tayawa”.

“Ni kuma?” Na tambaye shi

Ya gyara wuyan rigarsa ya ce”wanda za mu yi aikin tare ne ya ce ki bar kud’in kawai,dayake na yi masa bayanin ba ki da kud’i, shi ne ya ce tunda ya na da shi kawai zai taimake ki.Yanzu dai aiki zai yiwu gobe in sha Allah!”.

Ban san dalili ba,amma sam ban ji farincikin maganar ba,duk da ina ta fatan me bani wannan kud’in,na k’agi murmushi na ce”na gode sosai Nazifi,Allah ya saka da alkairi,ka yi masa godiya”.

Ya ce”kar ki damu,goben k’arfe takwas za a fara fatin nasa,ke kuma sai ki shirya k’arfe biyar na yamma,za mu zo mu tafi da ke,inda za mu fake kafin lokacin ya yi”.

“Kai Nazifi! Ya fa kamata ace kun yi min bayanin aikin nan,ya za a yi min abu kuma ayi ta yi min dabaibayi,na rasa gane inda kuka dosa”.

Ya yi murmushi ya ce”to me kike ci na baka na zuba? Gobe ne fa”.

“Ni dai kawai ka fad’a min malam” Na yi maganar ina had’e gira.

Ya ce”to gaskiya wani zarge za mu yi wa Salim,ko dai na ce tuggu za mu had’a masa,mu yi masa d’aurin goro,yanda bai isa ya ware ba,kawai dole ya aureki”.

Na yi jim sannan na ce”ina jinka,wane irin tuggu kenan? Ya za mu yi?”

“Ya za ku yi za ki ce,ke aikin ki sai mun kammala namu,mu ne masu aiki ba ke ba”. Ya fad’a ya na dariya.

Na ce”duk da haka ka sanar min yanda abun zai kasance”

Ya ce”d’akin Salim za mu kai ki,a wani irin yanayin da duk wanda ya gan ki zai ce ya yi miki fyad’e…”

Na yi saurin katse shi “ban gane wani yanayi ba!”.

Ya ce”za ki gane bayan komai ya tafi daidai.Idan muka yi nasarar shigar da ke,ke kuma sai ki yi k’ok’arin tabbar wa iyayensa abun gaskiya ne,ki nuna musu Salim sato ki ya yi,don ya miki fyad’e”.

“Amma idan na yi masa haka anya na yi masa adalci kuwa?” Na fad’a, jikina duk ya yi sanyi

Ya ce”idan ba za ki iya ba babu dole,sai ki hak’ura,ko kuma ki samo wata hanyar da ki ke ganin za ta tilasta masa aurenki”.

Na kama baki ina nazari,don gaskiya na san idan na yi wa Salim sharri,ban yi daidai ba,yanzu ko darajar Baby ai bai dace na yi hakan ba,da wane ido zan kalle ta? Kuma ko kowa ya yarda Salim zai sato ni ya min fyad’e banda Baby,tunda ta san duka tsakaninmu da shi,amma na yarda hakan ne kawai zai sa ya aureni a y’an tsakanin nan,ina jin tsoron jinkirtawa har a d’aura aurena da Habib ban ankara ba,sai dai na san ko na yi nasara ya aureni ba lallai na samu wata daraja daga gare shi ba,saboda MATAR SHIGE BA TA DARAJA!
Amma na yarda ni mace ce, don haka na saka a raina shiga gidan nashi ne babban aiki,karkato da hankalin sa gareni,da cusa masa soyayyata shan ruwa ma zai fi shi sauk’i,matuk’ar na zama matarsa.Don haka na yarda da wannan aikin na su Nazifi,amma na saka a raina zan yi ta istigfari daga baya,kuma bayan komai ya zama normal zan nemi yafiyar Salim

Idan aikin ya yiwu fa kenan!

Nan na fad’a wa Nazifi na amince,kuma goben zan shirya kamar yanda ya ce d’in,na yi masa godiya ya tafi,ni kuma na shiga gida. Ashe wani babban kuskuren na sake tafkawa! Idan banda ragon tunani irin nawa,ta ya zan yarda da zancen wai wanda zai min aikin,ya biya min kud’in? Shi da ya na da kud’in da zai yi kyautar dubu d’ari biyu,amma ya tsaya a wannan aikin wanda idan aka kacaccala kud’in bai fi ya samu hamsin ba? Na sake kuskuren da ya hanani zaman lafiya. Nan gaba dai za ku ji…

Bacci na kad’an ne a wannan daren,ina ta tunanin yanda wannan wasan mara kyau zai kasance gobe,yanzu idan abun ya b’aci ai na tabbata ni da su Nazifin duka sai mun yi zaman gidan d’an Kande.Gefe guda kuma ina tunanin irin halin da zan jefa gogan nawa a ciki,idan aikin ya yi kyau,ai zan b’ata masa suna a idon danginsa,kuma ba ni da tabbacin Baby za ta rufa min asiri a yanda take k’aunar d’an’uwanta.Sannan ina tunanin irin yanayin da iyayena za su shiga,idan suka ji wannan babban lamari,da kuma yanda Habib zai ji.Amma fa hakan ba zai sa na janye ba,saboda ina son Salim gaskiya

Na janyo turaren shi,na kafa hancina na lumshe ido,ina neman bacci.

Washegari da safe duk a sanyaye na tashi,har Anti ma sai da ta gane hakan,ta kalle ni da kyau ta ce”wai ni kam Zinatu meye damuwarki a y’an kwanakin nan? Har fa kin fara ramewa,ko tunanin auren ki ke yi?”

Haka nan na ji saukar hawaye,na share ina gyad’a mata kai alamar e tunanin ne

Ta ce”ki kwantar da hankalin ki,za ki auri namiji me hankali kamar Habib shi ne har ki ke tada hankalin ki? Maza ba su da tabbas,amma ina kyautata zaton Habib ba zai sa ki kuka ba Zinatu,ki kwantar da hankalin ki”.

Na gyad’a mata kai,ina share hawaye,sannan na sanar mata da yamma zan je gidan k’awata,don mu tattauna akan bikin.

Wajan azhar ina zaune kamar a mafarki sai ga kiran Habib,kamar ma kar na d’aga,don sharenin da ya yi ya ba ni haushi,na d’aga ina sallama murya a dak’ile

Shi ma ba kamar yanda ya saba yi min wasa da kalamai masu dad’i ba,yau kai tsaye ya ke yi min magana “Zinatu zan shigo da yamma za mu yi magana”.

“Ni fa bana gidanmu” Na fad’a,cikin jin haushi

Ya ce”e na sani,kuma gidan Na’imar zan zo dama”.

“Ban baka dama ba” Na fad’a cikin ba shi umarni

“Dama ban nemi izininki ba ai” Ya fad’a,kuma ya datse kiran bai jira cewa ta ba.

Na bi wayar da kallon mamaki,a bayyane na ce”e lallai Habibu ka samu dama,ka dad’e ba ka zo ba kuwa!”.

 

“Yanzu Baby ki na ganin wad’annan kayan sun yi?” Salim ya fad’a ya na kallon kayan da ta zab’a masa,na zuwa wurin birthday

Baby ta narkar da kai ta ce”oh! Bros Allah sun fi wanda ka zab’a kyau fa,ni na fi son na gan ka da manyan kaya ne”.

Ya yi murmushi ya ce”to shikenan,zab’inki shi ne nawa sisi”.

Ta juyar da kai ta yi shiru,alamun ta shiga damuwa da tuna wani abun.

Ya ce”to y’ar rigima,me kuma ya faru?”

Ta ce”rok’on ka zan yi alfarma Yaya”.

“Zan yi miki ko ta mene” Ya fad’a.

Ta ce”don Allah kar ka sha wani kayan maye,kamar yanda ka yi waccan shekarar,ka ga wannan karon Abba ya na nan,kuma zai je wurin”.

Ya kama hannunta ya ce”wannan shi ne damuwarki?”

Ta gyad’a kai. Ya ce”na yi miki alk’awarin ba zan sha komai ba in sha Allah”.

“Na gode” Ta fad’a ta na ficewa daga d’akin.

K’arfe shida daidai na kammala shirina,kuma ya yi daidai da kiran wayar Nazifi,ya na jirana a waje,doguwar riga na saka ta atamfa da wadataccen mayafina,na yi kyau sosai,na zabga turaren Salim kamar zan k’arar da shi,na yiwa Anti sallama na fita.

Sai dai ina fita na ga Habib ya na k’ok’arin gyara packing, zai fito daga motarsa,na yi saurin shigewa motar abokin Nazifi da suke ciki suna jira na,amma kafin ya ja mu tafi,Habib ya yi saurin zuwa inda muke,fuska babu walwala ya ce da abokin Nazifi “kai bud’e yarinyar nan ta fito”.

Na bud’e,ba tare da na fito ba na ce”unguwa za su kai ni”.

Ya ce”e,ki fito ni na kai ki”.

“A’a, na gode” Na fad’a ina shirin rufe k’ofar.

Ya rik’e murfin ya ce”to ki zo,ina son magana da ke ko ta minti biyar ce”.

“Ba zan samu dama ba gaskiya, idan na dawo sai ka dawo mu yi”. Na fad’a ina rufe murfin motar,su ka ja mu ka tafi,mu ka bar Habib tsaye kamar an dasa shi.

Sharad’an mu ka dosa,can wajejen su Salim d’in,don kuwa gidan da na ga sun faka motar babu nisa da gidansu Salim.

Mu ka fito muka shiga,amma banda abokin Nazifi,na dinga bin matsakaicin gidan da kallo, d’akuna uku ne a ciki,sai band’aki,da wani wuri da nake kyautata zaton kitchen ne,ya shiga wani d’aki ya ce na shigo, na shiga da sallama

Babu komai a ciki sai katifa da kayan kallo,da wasu akwatunan kaya a gefe,da alama dai d’akin saurayi ne.Na rab’a gefe na zauna duk a tsarge nake

Muna nan zaune da Nazifi ya na yi min bayanin yanda aikin zai kasance,sai ga abokin nashi da na ji ya na ce masa Sabi’u ya dawo rik’e da ledoji.

Ya zube su a gabana,ya kalli Nazifi ya ce”to ta so mu wuce ko?”

Nazifi ya kalle ni ya ce”to Zinatu,bari mu je,anjima za mu dawo d’aukarki,kafin nan an fara fatin,ga abinci nan ko za ki ji yunwa”.

Na ce “to,sai anjima”.

Bayan sun fita na bud’e ledar,na ga abinci ne a takeaway, sai lemuka har kala uku, ba na jin yunwa amma sai na ji sha’awar shan lemon

Na bud’e d’aya,na sha kusan rabi,na matsar gefe,na d’akko wayata ina kallon hotunan Salim da sak’e-sak’e,ko minti goma sha biyar ban yi ba,na fara jin bacci-bacci,abu kamar wasa tun ina daddaurewa har dai abun ya rinjaye ni,na kwanta a nan k’asa,na yi fulo da gefen katifa tuni wani bacci me shegen dad’i ya sure ni muka tafi…
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 17

 

Saukar ruwa me sanyi da na ji a fuskata shi ne ya farkar dani daga nannauyen baccin da na yi,na farka a firgice ina k’ok’arin bud’e idanuna da nake jinsu kamar ba nawa ba,wani irin yanayi nake jin jikina kamar dai wata ce aka saka zuciya da tunanina a jikinta

“Ke! Uban waye ya kawo ki d’akina!?”

Duk da ban gama wartsakewa ba,amma ba na jin akwai halin da zan shiga wanda zai mantar da ni muryar Salim,na bud’e idona sosai na kalle shi,sai na ga kamar ba Salim d’ina bane,don kuwa gani na yi kamar an canza idanunsa,ta idonsa kawai za ka fahimci ya na cikin tashin hankali mara misali.Lokaci d’aya na fara tunanin ta yanda su Nazifi suka kawo ni d’akin Salim,a iya sani na bacci na kwanta a d’akin da suka ajiye ni,kuma ban farka ba sai yanzu,kenan hakan ya na nufin cak suka d’auke ni? Kuma har ta ya ma suka shigo da ni nan d’in wani bai gan su ba?

Ban gama tunanin ba na ji muryarsa cikin hargagi,kamar mak’ogoronsa zai fice “me ya kawo ki nan? Kuma waye ya miki haka!?” Ya yi maganar ya na nuni da kayan jikina

Sai na kai duba ga jikina,gabana ya yi wata mummunar fad’uwa ganin alamun jini a farin yadin jikina,na doguwar rigar da ta kwanta a jikina,kasancewar ta roba.Nan take na tuna ni fa atamfa na saka daga gida,kuma duka ma ba ni da irin rigar nan,hankalina ya yi matuk’ar tashi fiye da yanda za ku yi tsammani,k’irjina ya dinga lugude kamar ana daka a ciki

Sai da na maimaita innalillahi wa inna ilaihiraji’un kusan sau biyar sannan Salim ya sake katse ni,ta hanyar buga min wata gigitacciyar tsawa ya ce”ke Zinatu! Kar fa ki raina min hankali,tambayarki nake yi waye ya kawo ki nan!?”

Da k’yar na bud’e baki na ce”don Allah waye ya yi min haka? Allah yasa kai ne ka min fyad’e ba su ba,kai ne?” Na fashe da kuka.

Sai dai na yi saurin dakatar da kukan jin ana buga k’ofar d’akinsa da k’arfi.Ya zaro ido had’i da d’ora hannunsa a kai,alamar ya shiga tashin hankali,murya k’asa-k’asa kamar zai yi kuka ya ce”na shiga uku! Zinatu me na yi miki za ki yi min haka?”

Ni ma hawayen nake yi,amma ba na tausayin shi ko nadamar abin da na yi masa ba,ni kukan nawa na tunanin wanda ya yi min fyad’e ne

Aka sake buga k’ofar,wannan karon har da kiran sunan shi,muryar namiji ne,ina dai zargin mahaifinshi ne.Ya zo da sauri ya ja hannuna ya na fad’in “don Allah tashi ki b’uya,ki rufa min asiri kar wani ya ganki,wallahi ba zan iya wanke kaina ba,tashi don Allah!” Ya kai k’arshen maganar ya na k’ok’arin d’agani

Sai ya ba ni tausayi don haka na fara tunanin janye wannan mummunan k’udurin nawa,na yi masa sharrin fyad’e, na yunk’ura da nufin tashi,amma me? Sai na ji na kasa tashi,jikina kamar ba nawa ba nake ji,aka sake buga k’ofar ana kiran sunan shi,ban yi aune ba sai gani na yi ya sungume ni cak ya yi wata k’ofa da ni,band’aki ne kamar yanda na zata,cikin hanzari ya shiga ya wurga ni cikin bahon wanka,har k’uguna ya bugu,ya rufe k’ofar ya fita

Ban san yanda suka yi da me buga k’ofar ba,can dai na ga ya sake dawowa,har yanzu ba ya cikin nutsuwarsa,sai zare ido ya ke ya na huci

“Zinatu Allah ya isa tsakani na dake! Me na yi miki wai? Ta ya kika zo d’akina?” Ya fad’a ya na d’ora duka hannuwansa a ka.

Tausayin shi ya kama ni sosai,na yunk’ura na tashi zaune na fashe da kuka sosai kamar ya min umarni da kukan.Sai ya zaro duka idanunsa kamar za su fito ya ce”kuuut! Wai har damar kuka ma ki ka samu? Ni da zan yi kuka ban yi ba,sai ke? Zo ki fice daga gidan nan tun ban yi miki dukan mutuwa ba!”. Ya kai k’arshen maganar muryarsa na rawa kuma cikin fad’a.

“Ina wayata?” Na tambaye shi.

“Ta na gidan ubanki!” Ya fad’a,sannan ya fusgoni daga cikin bahon ya warb’ar da ni a k’asa,k’afata ta bugu har na ji kamar babban yatsana ya karye

Da k’yar na tashi tsaye don fita na tafi gidan kamar yanda ya ce,amma da k’yar na samu na iya taku uku,wani irin juyi na ga garin ya na yi min,haka na yi ta layi ina dafa bango a k’ok’arina na fita daga band’akin,kallo d’aya dai za ka min ka san ba na cikin hayyaci na,ina fitowa daga band’akin na zube a k’ofar cikin mutuwar jiki,don k’arfina ya k’are duka,ba na jin zan iya wani takun

Salim ya zube shi ma a inda na fad’i murya na rawa ya fara jijjigani ya na fad’in”na shiga uku! Zinatu ki rufa min asiri kar ki mutu a d’akina don Allah!”

Ya tashi a guje ya d’akko robar ruwa ya watsa min,don shi a zaton sa suma na yi,na bud’e idona da suka yi jawur na ce”Salim… Don Allah Salim ka ji?”

“Uban me zan ji? Me za ki fad’a min? Ai har gani ma na yi ba ji ba,wannan shi ne sakamakon son da kika ce ki na yi min? Allah ya isa!”

Kawai sai ya jingina da bango ya fara share hawaye.Na daddafa na tashi da k’yar,idona ya na rufewa saboda har yanzu da sauran bacci a ciki na fara takawa a hankali nima ina share hawayen,ni dai hawayen tausayin kaina da nadama nake yi, shi kuma ban san ko na meye ba.

Har na kai bakin k’ofa na ji ya daka min tsawa ya ce”dawo!”.

A maimakon na dawo sai na zauna a bakin k’ofar,idona ya na lumshewa,ya tashi ya fita daga d’akin.

Babu wani zafi ko zugi da nake ji daga k’asana,wanda zai tabbatar min da fyad’en da aka yi min,amma ko ban ji zafi ba dole na yarda tunda ga jini nan ya zama shaida,da kuma canza min kayan da aka yi,ni yanzu babbar damuwata na ga wayata kawai,don na kira Nazifi na ji wanda ya yi min fyad’e da kuma dalilinsa na yi d’in.

Bai jima ba ya dawo d’akin,ya bud’e sif ya d’akko kayan shi,ya buga min harara ya shige band’aki,ya fito sanye da k’ananun kaya ba na d’azu ba,ya zo ya tsugunna a gabana har ina jin hucin numfashin sa,ya ce”Zinatu! Don girman Allah waye ya kawo ki d’akina?”

Na kalli k’wayar idonsa da na ke karantar damuwa k’arara na ce”son ka ne Salim! Wallahi son ka ne k’addarata…”.

“Ni ma kin zama k’addarata Zinatu,kuma ban yafe miki ba” Ya katseni

Na share hawaye ina lumshe ido,wata sabuwar k’aunar shi na dagargazar zuciyata wallahi burina kawai na ganni a kwance ina bacci,da ya san yanda nake ji a halin yanzu da tuni ya rungumeni na yi bacci a jikinsa.

“Da ki ka zo d’akin nan kin d’auki wata k’wayar kin sha ne?” Ya tambaye ni,ya na nuna min lokarsa

Na girgiza masa kai,alamar ban sha ba. Ya ce “ok dama can ki na shaye-shaye kenan?”

Na yi banza da shi

“Ki tashi na kai ki gidanku,gobe zan zo mu yi magana”. Ya fad’a ya na d’akko mukullin mota.

Na tashi da k’yar, ina tangad’i idona na lumshewa,amma duk iya k’ok’arina sai na kasa tafiya,saboda tsabar jirin da nake ji

“Wuce mana!” Ya daka min tsawa

Ina d’aga k’afata na tafi luuu,na fad’a kanshi gabad’aya

“Bura’uba!” Ya fad’a da k’arfi,sannan ya hankad’e ni,Allah ya taimake ni a gado na fad’a, sai kuwa na gyara kwanciyata na lumshe ido.

“Yau na shiga uku ni Muhammad!” Na ji muryarsa sama-sama

Babu zato na ji ya shek’a min ruwa a jikina,Ina bud’e ido na gan shi tsaye da bokiti ya na huci,na tashi a firgice na ce”ka yi hak’uri don Allah, zo ka raka ni gida,ko kuma ka bar ni,na kwana anan wallahi gobe zan tafi”.

Ya dafe goshinsa ya na wani irin huci.Can dai kamar wanda aka yiwa umarni kawai ya zo ya sungume ni,ya sab’a a kafad’a,dama ba wata k’iba ce da ni ba,bare na yi nauyi,ya yi waje da ni.Don dole na wartsake saboda wani sanyi da nake ji,sakamakon rigar jikina da ta jik’e jak’ab,sad’af-sad’af haka ya dinga tafiya da ni a kafad’a,ya na jera min Allah ya isa,har mu ka kusa fita daga falon.

“Salim!” Ya tsaya cak! Jin muryar mahaifinsa.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Ya furta a sanyaye,sannan ya dawo ya ajiye ni a kujera ya durk’usa,ya saka gwuiwowinsa a k’asa. Taku d’aya bayan d’aya mutumin ya k’araso har gaban shi, murya a sanyaye ya ce”Salim yaushe ka fara satar mutane a cikin gidana?”

Salim ya runtse ido bai yi magana ba. Ya daka masa tsawar da ni kaina sai da na firgita na wartsake sosai,na gyara zamana, ya ce “da kai na ke magana!”

Salim ma ya firgita ya ce”na rantse da Allah Abba…”

Bai k’arasa ba ya katse shi da fad’in”rantsuwa na tambaye ka?”

Ya sunkuyar da kai ya ce”wallahi Abba ban san wanda ya kawo yarinyar nan d’akina ba,ai ka ga dai tare muka shigo gidan da ku,ina zuwa na tadda ita a kwance,na rantse da Allah Abba”.

Abba ya ce”to to to, wato aljanu ne su ka kawo ta ko? Idan gaskiya ne ai tun lokacin da ka ganta za ka zo a guje ka sanar mana,ba ka yi tunanin ko aljana bace yanzu da ka kinkime ta? To ina ma za ka kai ta da ban fito ba?”

Kafin Salim ya kai ga magana Ammi ta fito ta na fad’in “wai hayaniyar me nake ji cikin dare?”

Sai ta zaro ido ta na kallona ta ce”wacece wannan?”

“Amsar wanda ya kawo ta na ke jira!” Abba ya fad’a, ya na zama a kujera

Ammi ta kalle ni da kyau,sannan ta dafe k’irji ta ce”mun shiga uku! Wannan ai k’awar Baby ce,Nuratu ko?”

“A’a Zinatu,ita ce,k’awar Baby ce” Cewar Salim da rawar murya.

Abba ya ce”zance ya fara fitowa,ashe har sunanta ka sani?”

Ammi ta koma da sauri,sai ga ta sun fito tare da Baby,ta na murtsuke ido,alamar ta fara bacci.Turus! Ta ja ta tsaya,ba tare da ta k’araso inda muke ba, ta nuna ni da yatsa ta na fad’in “Zi zinatu?”

Na runtse idona hawaye suka zubo,sannan na sunkuyar da kai

“Tambayar ka mu ke yi,me ya kawo mace d’akinka?” Cewar Abba

Salim ya ce”wallahi Abba ba ni na kawo ta ba,kuma ban san wanda ya kawo ta ba”.

Sai Abba ya juyo da kallonsa gareni ya ce”ke maganar da ya fad’a gaskiya ce?”

Na d’ago,mu ka yi ido hud’u da Baby,da ta k’ank’ance ido ta na kallona,na maida duba na ga Salim,na ga idanunsa taf da k’walla

Na sunkuyar da kaina k’asa na ce”ba gaskiya bane,shi…shi ne ya kawo ni” Na fashe da kuka

Wallahi da na san haka abun zai kasance babu yanda za a yi na yarda da wannan aikin,ban gama tunani ba na ji muryar Abba “to kidnapping d’inki ya yi?”

Salim ya kalle shi da sauri ya ce”haba Abba!”

“Yi min shiru!” Cewar Abban

Sannan ya kalle ni ya ce”biyan kud’in fansar aka yi,shi ne zai maida ki gida ko?”

Na girgiza kai alamar ba haka bane.

Abba ya ce”to me ya yi miki?”

Na kalli Baby,na ga sai share hawaye take yi,na kalli Ammi na ga ta rik’e k’ugu,fuskar nan murtuk kamar kunun kanwa,na kai duba ga gogan nawa,shi ma ni ya ke kallo kamar idanunsa za su fito

Sai kawai na maida kaina k’asa,gabana na tsananta fad’uwa.

Ammi ta ce”tambayarki fa ake yi!”

Sai da na yi wasu huci masu zafi har uku a jere sannan na ce”Fyad’e ya yi min”.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Duka suka d’auki salati,har da Salim d’in.

 

 

#Team Salim
#Team Zinatu

Waye abin tausayi wai?😥
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 18

 

“K’arya take,wallahi ban yarda ba!” Cewar Ammi ta na nuna ni da yatsa.

K’irjina ya dinga lugude,tuni nadama ta rufe ni, kai gaskiya ranar na yi danasani,na ji haushin kaina sosai. Salim ya kalle ni ya ce”Zinatu ki ji tsoron Allah! Yanzu saboda na k’i karbar soyayyarki sai ki saka min da wannan?”

“Kai!” Abba ya daka tsawa ya kalli Salim ya ce”Salim! Ka san ni dai ba sa’anka bane,bare ka tsaya yin wasan kwaikwayo a gabana,don haka ka fad’a min gaskiyar yanda abin ya kasance”.

Salim ya cije leb’e da alama dai ya na jin zafi a zuciyarsa,ya ce”wallahi tallahi Abba ban yi mata komai ba,sharri ta yi min kawai!”.

Ammi ta ce”amma lallai yarinyar nan ke makira ce! Kenan saboda ya ce ba ya son ki sai ki nemi jifansa da sharri? To plan d’inki bai samu shiga ba!”.

Abba ya d’aga mata hannu ya ce”kin ga Rahma! Ba a shaidar d’an yau,kuma ki yi tunani idan Khadija aka yiwa haka ya za ki ji? To wallahi ba zan bar maganar nan haka ba,dole na tabbatar da adalci a ciki”.

Ni dai hawaye kawai nake sharewa,yanzu kam na fi tausayin Salim fiye da kaina.Baby dai har yanzu ba ta ce komai ba,ban kuma san abin da shurunta ya ke nufi ba,jikina ya mutu murus nadama ta haifar min da kasala sosai.

“Don Allah Abba ka yi bincike,wallahi wannan yarinyar sharri ta yi min, ban san wanda ya kawo ta d’akina ba,kuma tun farko fargabar yanda za ku d’auki zancen ne yasa na kasa fad’a muku,na yi yunk’urin fitar da ita daga gidan nan”. Salim ya fad’a murya na rawa.

Abba ya ce”alfarma d’aya zan yi maka! Gobe za mu je asibiti da yarinyar nan,likitoci su duba ta muddin aka tabbatar an yi mata fyad’e to na yarda da zancen ta,na watsar da naka,don kai ne ka yi kenan. Idan kuma aka tabbatar da babu wani fyad’e da aka yi mata,to zan yarda da zancen ka,kuma ba zan bar duk wani me hannu a sharrin da aka k’ulla maka ba”.

Salim ya ce”amma Abba…”

“Na gama magana,kuma ban buk’aci jin komai daga bakin kowa ba”. Ya katse shi da fad’in haka.

Gabana ya fad’i da jin furucinsa,nan take na fara tunanin anya kuwa na yiwa Salim adalci? Ni dai a halin yanzu ban san a wane hali nake ciki ba,an yi min fyad’e? Ba a yi min? Wallahi ba ni da masaniya,idan aka je asibiti ya tabbata anyi min,shikenan fa na had’a Salim da mahaifinsa,kuma bani da tabbacin hukuncin da zai yanke min zai yi daidai da burina,hukuncin tilastawa Salim aurena na ke nufi.Idan kuma ba a yi min fyad’en ba duk cikin plan d’in su Nazifi ne fa? Wane irin hukunci zai yanke akan mu,bayan asiri ya tono? Na dinga jero salati a zuciyata, da na tuna yanzu duk inda hankalin Anti Na’ima ya ke ya tashi,na rashin dawowa ta,watak’il har Ummi da Baba duk sun ji.

Abba ya kalli Baby da ke share hawaye ya ce” Khadija,je ki bata d’akin da za ta kwanta kafin goben”.

“Ki biyo ni” Baby ta fad’a, ba tare da ta kalli inda nake ba.Shi kuma Salim har yanzu ya na nan a durk’ushe kamar me neman gafara,kodayake kusan hakan ne ma ai

Na tashi jiki ba k’wari na bi bayan Baby,tun ban yi nisa ba na ji Abba ya saki salati,na yi saurin juyowa sai ya juyar da kai ya ce”sannu kin ji? Khadija ki bata kayanki ta canza wad’annan”.

“Salim ka na da imani kuwa? Da har ciwo ka ji mata haka,amma shi ne za ka fita da ita a haka?” Na ji muryar Abba, hakan ya tabbatar min ya ga jinin jikin rigata ne.

Ban ji amsar da Salim ya ba shi ba na shiga d’akin da na ga Baby ta shiga,ta kunna haske sannan ta fita.Na bi d’akin da kallo,fess yake,babu wani shirgi daga katifa madaidaiciya,sai mudubi lik’e a jikin bango,na samu gefen katifar na rab’a,sanyi ya na ratsa sassan jikina

Ba a jima ba Babyn ta dawo,da sallama na amsa ina son ganin cikin idonta,amma ba ta bani dama ba,ta ajiye min riga da sket na atamfa,ta juya ta na shirin fita na ce”zan samu hijjabi don Allah? ”

Ba ta juyo ba ta fice kamar ba ta ji ni ba,amma kuma ba ta dad’e ba ta dawo ta jefo min hijjabin ta koma

Na tashi na shiga band’akin cikin d’akin,don dama fitsari nake ji sosai ya d’aure min mara.Sai dai na yi mamakin rashin ganin jini a jikina,don a iya rigar kawai ya tsaya,na jima a tsugunne ina son na gano halin da nake ciki,da gaske anyi min fyad’e ko a’a? Amma na kasa ganewa,don haka na hak’ura na tashi na yi wankan tsarki,tunda ban gama yarda da kaina ba,na wanke farar rigar,ko nace na d’auraye ta tunda ban ga clean ba,haka dai na cukuikuye ta na barta a band’akin,na fito na saka kayan da ta kawo min na saka hijjabin na tada sallah,margiba da isha’i na yi don su ake bi na,haka na zauna na yi ta istigfari tun kafin na san yanda za ta kaya goben.Wata yunwa ma nake ji sosai,amma sanin a yanzu ba ni da gatan samun abinci na kwanta a haka na lullab’a da hijjabi,tuni bacci ya kwashe ni.

Washegari da na farka har an idar da sallar asuba,gari ya fara haske,kuma a hakan ma fa baccin bai isheni ba,na tashi na yi sallah na kwanta a kafet d’in ina jin yanda babban yatsana na k’afa yake zugi,wani baccin ya sake kwasa ta.

“Zinatu,Zinatu” Na ji muryar Baby cikin baccin nawa

Na farka na ganta tsaye a bakin k’ofa. “Ki fito inji Abba” Ta fad’a, sannan ta fice

Na tashi,na saka hijjabin na fito cikin jin kunya,kaina a k’asa,a falo na tadda su duka har da Salim d’in,na saci kallonsa ta gefen ido,sanye ya ke da bak’ar shadda da kofin shayi a hannunsa,ya na juyawa da cokali,sai na ga ya yi min kyau sosai.

Na k’arasa na duk’a na gaida Abba,ya amsa ya na yi min ya jiki,ban amsa ba saboda kunya,na juya wurin Ammi na gaisheta,ita kam ba ta ma nuna ta san da halitta ta a wurin ba,na juyo kan gogan nawa na ga ni ya ke kallo, na ce “ina kwana?”

“Lafiya lau” Ya amsa min,ban yi zato ba. Na koma gefe na rakub’e kamar yajin k’osai

Habiba y’ar aikin gidan ta shigo falo ta kalleni ta ce”ki zo ki karya”.

Na tashi na bi bayanta da d’an d’ingishi,don har na fara zaton na yi targad’e ne a jefoni da ya yi,daga cikin bahon wanka.A nan dinning d’in na tadda Baby ta na karyawa,na kalle ta na ga hankalinta na kan farantin dankalin dake gabanta

“Baby,an tashi lafiya?” Na fad’a ina k’irk’iro murmushi.

Sai ta yi kamar ba ta ji ba, ta tashi ta bar wurin.Cikin d’ari-d’ari na had’a shayi,don ba dan ina jin yunwa ba ma ba zan ci komai ba,na zuba dankalin kad’an na karya,sai na yi zama na a wurin,don duka kunyar su nake ji wallahi, na dinga tunanin halin da gidanmu yake ciki a yanzu,watak’il ana can ana ta nema na,na fara fargabar kada Habib ya ji labari,tunda shi ne kawai ya ga lokacin da aka d’aukeni a mota,kuma babbar matsalar ma ya ga wanda ya d’auke ni d’in.

Ina nan zaune Baby ta dawo cikin shirinta,har da hijjabi,ta kalle ni ta ce”ki taso muje asibiti.Kuma ki sani ko kin auri Salim ba za ki tab’a samun wani farincikin rayuwar aure ba,saboda Ammi ba za ta tab’a k’aunarki ba,ta san tsakaninku da Salim,tun ranar da kuka gaisa a gidan nan,na bata labarinki duka.Sannan ko da kin yi nasarar shigowa dangin mu,za ki yi rayuwa ne ke da mijinki kawai,saboda har ni ma ba na tare da ke!”. Ba ta jira cewata ba ta bar wurin

Ba ni da zab’in da ya wuce na bi bayanta,don haka na tashi jikina duk ya yi sanyi,na nufi falon,har Abba ya so bani tausayi,yanda yake kallo na cikin kulawa da tausayi a idonsa,na fita kamar yanda na ga sun yi.

Muka shiga mota,Salim ne a mazaunin direba,Abba a gaba,sai ni da Baby muka shiga baya,sai da na ga an tada motar na gane banda Ammi za a je.

“Ina ne gidanku?” Abba ya tambaye ni.

“Hotoro ne” Na fad’a a sanyaye.

“Wace unguwa?” Ya sake tambaya ta.

“Abba na fa san gidan” Ya fad’a da murya ciki-ciki.

Abba ya ce”to ka ga Salim,in har ka san da gaske ka yaudari yarinyar nan ka fad’a min,ba sai mun je asibiti mun tonawa kanmu asiri ba”.

Salim ya ce”wallahi Abba gaskiya na fad’a maka,ni ban yi mata komai ba”.

“To amma ta ya ka san gidansu?” Ya tambaye shi.

Salim ya yi shiru,kamar bai ji shi ba.Motar ta yi shiru,har muka k’arasa k’ofar gidan Anti Na’ima,bugun zuciyata fa sai ya k’ara tsananta,Abba ya ce na shiga na yi masa sallama da Babana,na yi masa bayanin nan d’in gidan Yayata ne,sai ya ce na kira yayar tawa,ko mijinta.

Na fito daga motar jiki a sanyaye na shiga gidan,ina shiga na tadda Anti a falo,ta tashi tsaye ta ce”Zinatu a ina ki ka kwana? Hankalinmu duka ya tashi muna ta nemanki,kuma kin bar wayarki a gida!”

“Ina wayar tawa?” Na tambaye ta.

Ta ce”ban sani ba! Na ce a ina ki ka kwana?”

Na sunkuyar da kai ban bata amsa ba na ce”ana sallama da ke a waje”.

Cikin mamaki ta ce”sallama kuma? Waye?”

“Mahaifin Salim ne” Na bata amsa.

Ta ce”waye kuma Salim?”

“Anti suna jiranki,ba fa k’ananun mutane bane” Na fad’a cikin k’osawa da tambayoyin ta.

Sai ta d’akko hijjabi ta saka ta ce na ce su shigo ciki kawai. Su ka shigo,amma banda Baby da ta zauna a motar,bayan sun gaisa Abba ya tsara mata yanda komai ya faru,sannan ya shaida mata yanzu wani nasu ya shirya aje asibitin tare.

Anti Na’ima ta dinga jera salati babu k’akk’autawa,sannan ta fara k’walla ta ce”wallahi Alhaji aurenta saura sati biyu,ashe ita yarinyar nan shirin ta da ban!”

Abba ya jinjina kai ya ce”duk abar maganar,aje asibitin kawai”.

Anti ta ce ta na zuwa,ta shiga d’aki.Ba ta jima ba ta fito,ta mik’o min wayata,tana min wata kafirar harara, mu ka tafi. Hanyar asibitin Aminu Kano muka d’auka,Anti ta ce gwara aje Nasarawa akwai likitoci mata ta wannan fannin,Salim ya juya kan motar muka yi Nasarawa,ni dai gabana sai fad’uwa ya ke yi,shi kuwa Salim ban san abin da yake ransa ba.

Muka shiga asibitin,Anti ta ce ta san b’angaren da ya kamata mu je,kamar an san da zuwanmu mu na zuwa aka nuna mana inda za mu shiga,Anti ce ta yiwa wata nurse bayani a tak’aice,sai aka yankan min kati,babu jimawa aka nuna min d’akin da zan shiga a dubani.

K’irjina fa ya tsananta bugu,na dinga taku d’aya bayan d’aya kamar wahainiya,fargaba fal raina

Da na shiga d’akin kusan fad’uwa na yi,saboda wani tuntub’en bazata da na yi,sakamakon ganin Habib sanye cikin uniform d’insa na asibiti,ya hard’e hannu a k’irji,fuskar nan babu walwala,shi kad’ai ne a d’akin,da alama dai shi ne likitan da zai duba ni.
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 19

*Ni fa na san so,kuma na yarda k’addara ne.Don haka ina team d’in Zinatu,idan kuna zaginta Allah zan tafi hutun typing na sati biyu,kafin nan zuciyarku ta yi sanyi,sai mu d’ora😉*

 

Habib ya yi min wani firgitaccen kallo,da alama dai bai tsammaci gani na ba.Ni kuwa kusan mutuwar tsaye na yi,ganin wannan tonon sililin da ya tunkaro ni,ko kuma na ce na jefa kaina a ciki,amma sosai na yi mamakin ganin shi a b’angaren,don a iya sani na Habib likitan ido ne,to me zai kawo shi nan b’angaren? Ban gama raba d’ayan biyu ba na ji muryarsa

“Zinatu! Kar dai ki fad’a min ke ce wadda za a duba yanzu!” Ya yi maganar ya na k’ank’ance ido da alamun b’acin rai.

Na ji wata kunyarsa ta rufto min,na kasa magana,kawai sai na fara zub da hawaye ba tare da na shiya ba. Ya yi huci me zafi ya nemi kujera ya zauna,sannan ya d’akko wayarsa a aljihu ya yi danne-danne ya kara a kunne

Na yi shiru ina sauraron wayar tashi,ban san da wanda yake wayar ba,na dai ji ya na cewa”ka ga doctor, ka k’arasa a tsanake,ni ma na ari office d’in naka na y’an mintuna,idan na kammala zan kira ka”.

Ya ajiye wayar ya kalle ni fuskar nan murtuk kamar ba shi ba ya ce”maganar fyad’en da ake tantama a kansa,ina so ki fad’a min gaskiya anyi miki,ko ba a yi miki ba?”

Na yi shiru,kaina a k’asa.Ya buga teburin da k’arfi ya ce”ke! Ina tamabayarki ne fa as your doctor, ba Habibun da kika sani ba,ki d’auka ban ma tab’a ganin ki ba sai yau,saboda haka idan kin shirya ganin likita sai ki bud’e bakinki,idan ba ki shirya ba ki fice min daga office!”

Na d’ago na kalle shi, sai na ga tabbas wannan ba Habib d’ina bane,da gaske ya ke yau a gaban doctor Habib nake,sai na saka a raina ban san shi ba d’in,don haka na ce”ni ma ban sani ba”.

“Kamar ya ba ki sani ba? Shekarunki nawa?” Ya tambaye ni,idonsa a kaina

“Ashirin” Na ba shi amsa.

Ya ce”ko y’ar shekara biyar aka yi mata fyad’e dole ta sani,bare ke da kin isa zaman aure! Ki na kokwanton anyi miki fyad’e,ta ya ki ka tsaida wanda kike zargi?”

Na lura dai da gaske Habib ya ke son k’ure ni,gwara ni ma na dawo masa Zinatu,don ya na shirin canza min suna da wata banzar barazanar sa,wai shi likita!

Na had’e rai na gyara zama na ce”kafin na shigo wurin nan ce min aka yi likita zai duba ni,ba lauya ba,kuma a zatona da doctor Habib na ke magana,ba barrister Habib ba”.

“E hakane,amma wannan tambayar duka cikin aikina ne”. Ya fad’a ya na had’e gira.

Na ce”tunda ka ga har sun kawo ni nan,ai ka san an zo gab’ar raba gardama kenan.Idan za ka duba ni bismillah kawai”. Na k’arasa maganar zuciyata na bugu,don ina fargaba da takaicin wani gardi ya ga tsaraicina,musamman ma Habib d’in,wannan rashin darajar ina zan kai shi? Amma a fili ba za ka tab’a kawo haka nake tunani a raina ba.

Ya yi shiru ya na kallo na,tsawon sakanni,sannan ya jinjina kai ya ce” bismillah! Ga gado can je ki hau”.

Gabana ya fad’i,duk da har yanzu zuciyata ba ta amince da zai iya duba ni d’in ba,ban nuna ba na dake na tashi na yi inda gadon ya ke,sai dai zama na yi ba kwanciya ba

Na d’an jima da zama,har na fara k’aguwa sannan ya k’araso wurin,ya janyo kujera ya zauna ya fuskance ni,ni kuma na sunkuyar da kai, don ba na son ya kalli k’wayar idona.

Tun kafin ya fara magana wani likita ya shigo,wanda na ke kyautata zaton shi ne me office d’in.

“Doctor ka kammala?” Ya tambaye shi,idonsa a kaina

Habib ya yi wani huci ya dafe kansa da duka hannayensa biyu.

Likitan ya janyo wata kujerar ya zauna a kusa da shi,ya ce”na fa kasa fahimta,a iya sani na ba ka harka da mata,wacece wannan?”

Kamar ba zai ba shi amsa ba,sai can ya ce”ita ce Zinatu”.

Ko idona ne oho! Sai na ga kamar lokaci d’aya yanayin likitan ya canza,zuwa ga b’acin rai,ya yi min wani kallon da na kasa fassra shi a lokacin,sai daga baya,sannan ya kalli Habib ya ce”to me ya kawo ta nan d’in?”

Habib ya tashi ya je kan teburin ya d’akko masa takarda ya ba shi.Ko me aka rubuta a takarda tawa oho! Na dai ga ya kalle ni da sauri,kuma da alamun b’acin rai

Ya kalli Habib ya ce”yanzu ka duba ta d’in?”

Ya girgiza masa kai alamar a’a.Sai ya ce”ok,ka je kawai zan saita komai”.

Habib ya yi masa wani kallo me wuyar fassrawa ya ce”kai! Matar da zan aura d’in za ka duba!?”

“Ai cikin aikina ne” Ya ba shi amsa ya na d’age kafad’a.

Habib ya kalle ni ya ce”ke tashi ki fita! Sai dai ku canza wani asibitin wallahi,ta ya wanda na sani zai duba min mata?”

Likitan ya dafa kafad’arsa ya ce”ok! Na fahimce ka Habib,amma ka sani ko wani asibitin aka kai ta ba ka da tabbacin mace ce za ta duba ta.Na yi maka alk’awarin ba zan duba ta ba,zan lallab’a ta ta sanar da ni gaskiya”.

Habib ya yi shiru kamar me nazari. “Ka yarda da ni abokina,ka je d’in”.

Habib ya kalle ni,sannan ya maida facemask d’insa ya fice.Na sauke ajiyar zuciya a b’oye,har yanzu zaune nake a bakin gadon

Likitan ya kalle ni da kyau ya ce” ke anyi miki fyd’en ko ba a miki ba?”

“Ni ma na kasa tantancewa fa” Na fad’a, ina juyar da kai gefe

Sai ya tab’e baki ya ce”yanzu ya kike jin jikinki?”

Na ce”ya na yi min ciwo kad’an,sai bacci da nake ji”.

“Tun yaushe abun ya faru?”

“Jiya da daddare” Na ba shi amsa.

“Waye wanda ake zargi” Ya tambaye ni.

“Wani ne” Na fad’a

Ya ce”ko Salim da na gani a waje?”

“Shi” Na fad’a a tak’aice.

Ya ce”ok! To yanzu zan canza miki d’aki,sai na saka miki drip,idan ya k’are za a sallame ki”.

Ina shirin yin magana ya tashi,ya na cewa na biyo shi.

Ba ni da zab’in da ya wuce bin umarnin shi.Zazzaune muka tadda su Abba,da alama har sun k’osa da jira,na tsaya daga d’an nesa,yayinda likitan ya k’arasa wurin su,Abba ya tashi da sauri ya mik’a mishi hannu suka gaisa ya na tambayar sa ya ake ciki?

Likitan ya kalli Salim sannan ya maida duban shi wurin Abban ya ce”fyad’en dai ya tabbata,sai dai Allah ya rufa asiri”.

“Ban yarda ba! Wallahi akwai k’ulla-k’ulla a wannan abun!” Muryar Salim ta karad’e kunnuwanmu.

Gabana ya fad’i. Likitan cikin nuna rashin damuwa ya ce”me ye ya ba ka tabbacin hakan?”

Salim ya ce”duba yarinya ba sai likitoci biyu ba,likitan farko da ya dace ya duba ta ya jima a ciki,sannan ya fito kuma ina kallon shi,sam ban yarda da yanayinsa ba,kai ma kuma da ka shiga ka jima a ciki,to meye dalilin dad’ewarku a duba mutum d’aya kawai?”

Likitan ya kalle shi na y’an sakanni,har na fara fargaba sai ji na yi ya ce”amma dai ina tunanin ka san irin b’arnar da ka yi mata ko?”

“Ban gane ba!” Salim ya fad’a a hasale.

Likitan ya ce”likitan farko da ka ga ya fita,shi ne ya fara duba ta,kuma ya ga b’arnar da ka yi mata,shi yasa ya kira ni saboda na fi shi k’warewa a fannin d’inki,yanzu dai an gama gyarata,za mu saka mata ruwa,idan ya k’are kuma sai a sallame ta.Akwai magungunan da zan rubuta”.

“Dank’ari!” Na fad’a a zuciyata.Amma lallai wannan likitan idan ya shiga wasan kwaikawayo zai samu abinci sosai, na ji wani farinciki ya rufe ni,sai dai fa na yi mamakin abin da ya sa shi wannan k’aryar har haka,kuma na sa a raina ba sai na ji dalili ba,ko ma menene ni kam ya taimake ni.

Salim ya ce”kai ka ga! Kada ka sake danganta ni da wannan,can za ta nemi wanda ya yi mata b’arna ba…”.

“Kai!” Abba ya daka masa tsawa,Salim ya koma ya zauna fuskar nan kamar bai tab’a murmushi ba.

Abba ya ja likitan gefe,ban san dai me suka tattauna ba,ni kuma wata nurse ta zo ta rik’e hannuna muka shiga wani d’akin. Aka bani gado,ta saka min drip,ta ba ni magani na sha,har da lulllub’e ni da bargo,aikuwa bacci ya ce min mu je.

Ba ni na tashi ba sai bayan azhar,na duba wayata dake kusa da ni,na ga k’arfe biyu da minti ashirin,na tashi zaune,yanzu kam na ji dad’in jikina sosai,babu wani sauran bacci a idona,na tashi na shiga band’aki na d’auro alwala.

Ina fitowa na tadda Mama Saude a d’akin,ta dinga kallon k’afata kamar wadda aka ba ta aikin k’irga taku na,na san dai tsabar gulma ce take cinta,na had’e rai na k’araso na gaishe ta.

Ba ta amsa ba ta ce”oh! Zinatu ashe haka abu ya faru?”

“Uhm!” Kawai na ce,na d’auki d’ankwalina na shimfid’a a k’asa,na tada sallah

“To kin yi wankan tsarki ne?” Na ji tambayar tata a bazata.

Na juyo na kalle ta na sakan uku,sannan na tada sallata.Kafin na idar ta fita ta shigo da kwando me d’auke da kuloli,ta had’a shayi kofi biyu, ta ja d’aya gabanta,ta mik’o min d’aya,haka abincin ma ta zuba faranti biyu, ta gyara zama ta fara antayawa ba tare da ta min magana ba.

“Mama a ina aka samu wannan abincin?” Na tambaye ta,ina d’aukar kofin shayin

Ta ce”daga gidansu yaron aka kawo.Ai ya na nan ma,ya na jira a sallame ki, ya maida mu gida,wallahi yaro kyakkyawa me hankali da kirki,ni na san k’addara ce kawai kifta”.

Na ce”Baba da Ummi sun sani?”

Ta na yagar naman kaza ta ce”yo kema dai zancen ki ke so,idan ba su sani ba ni taya zan ji har na zo jinya? Ai har da mahaifin yaron ma baban naki sun zauna,ban dai ji abin da suka tattauna ba tukun,sai mun koma gida”.

“Ummi ta zo?” Na tambaye ta.

Sai ta tab’e baki ta ce”ta zo ina? A gabana Na’ima ta kira ta ta sanar mata,amma wallahi bud’ar bakin matar nan,sai cewa ta yi Allah ya ba ki lafiya.To dama waye dolenki idan ba ni ba? Wallahi na san na fi mahaifiyarki shiga tashin hankali,ke ni yanzu fargabata d’aya ,kar Habibu ya ji labari”.

Ni dai na yi shiru ban sake tanka mata ba,ta na ta surutun ta,ni kuwa tunanin yanda za mu yi da mahaifana kawai na ke yi. So na ke ma ta bani space na samu damar kiran Nazifi a waya,amma ta zaune min.

Mu na nan zaune Salim ya shigo da sallama,Mama ta amsa ta na yi masa sannu,ni kuwa binsa da kallo kawai na yi,ina jin wata k’aunar shi, Kai! Gaskiya ina son Salim fiye da zaton ku.

Kallo d’aya ya yi min ya kauda kai,ya kalli Mama ya ce”kun ci abincin kuwa?”

Ta washe baki ta ce”mun ci abinci mun k’oshi”.

“Ok! Za mu wuce gidan”. Ya fad’a ya na d’aukar kwandon kayan abincin.

Ya fita,muka bi bayansa,sai kallon shi nake yi.Muna shirin shiga motar wannan likitan ya dakatar da mu,ta hanyar k’walla min kira,na dakata,shi kuwa Salim ya shige motar bayan ya bud’ewa Mama ta shiga gidan baya.

Likitan ya ce” kin ba ni mamaki”.

“Na me kenan?” Na tambaye shi.

Ya ce”akan irin yanda na fad’i abin da ba haka bane,kuma ba ki nemi jin dalili ba”.

Na ce”to meye dalilin?”

Ya ce”saboda ba na son tarayyarku da Habib”. Na yi masa kallon mamaki

Ya d’ora”Sam! Habib bai dace da mace irinki na,ya na da hak’uri da halaye masu kyau,mace me hankali da hak’uri ce kawai ta dace da shi.Ya na yawan ba ni labarin irin yanda ya ke son ki,ke kuma ba ki damu da shi ba…”.

“Kai dakata malam! Idan ka yi ne don ka raba ni da shi,to ka sani shi ka cuta ba ni ba,kuma tunda ka ga tun farko ban nemi jin dalili ba,idan da tunani ai za ka gane hakan dad’i ya yi min.Ba ni da lokacin ku!”.

Ina gama maganar na wuce wurin motar na bud’e gidan gaba na shiga, ya ja muka tafi.

Gidan Babana mu ka je,na ji wata sabuwar fargaba ta kamani,Mama ta bud’e ta fita,ina shirin bud’ewa na fita,babu zato kawai na ji Salim ya…
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 20

 

Na ji ya kira sunana a sanyaye,na juyo na kalle shi ina jiran abin da zai fad’a,sai kawai ya tsaya ya na kallo na,ni ma na zuba masa ido son shin na ratsa duk wasu jijiyoyin jikina,wajan minti biyu muna a haka,sannan ya jinjina kai ya d’auke idonsa a kaina ya ce”je ki”.

“Na gode” Na fad’a,sannan na fice na rufo masa motarsa,tsaye na yi ina kallon motar har sai da ya b’acewa gani na,na sauke ajiyar zuciya na shiga gida da fargaba.

A tsakar gida na tadda Mama,anti Na’ima,anti Halima,da kuma yayata ta Rijiyar lemo anti Maimuna,na yi sallama na k’arasa inda suke a sanyaye,da na gaishe su ma babu wanda ya amsa,ni dai na d’auki buta na shige band’aki,ina shiga na duba wayata,na dannawa Nazifi kira,bugu biyu ya d’auka ko sallama ban jira ya yi ba,na fara magana
“Nazifi me kuka yi min?”

Ya ce”ya ya? Da fatan komai ya tafi daidai,ban kira ki bane saboda kar a samu matsala”.

“Wai da gaske an yi min fyad’e?” Na tambaye shi,cikin zafi-zafi.

Ya yi dariya ya ce”haba Zinatu! Zargi na kike yi?”

Na ce”ka ga kawai ka sanar min!”

Ya ce”wallahi Zinatu babu wani fyad’e da aka yi miki,kuma cikin mu babu wanda ya tab’a ki”.

Na d’an ji dama-dama a raina, na ce”ta ya zan yarda da kai,bayan na ga kun canza min kaya?”

“Wallahi mace ce ta canza miki kaya,ba mu ba”. Ya fad’a

Sai na yi mamaki,na ce” to wace ita? A ina kuka samo ta? Kuma jinin jikin rigar fa!?”

Ya ce”k’anwar abokina ce,kuma ta ina za mu samu jini? Zob’o ne muka zuba”.

Har raina na yarda da zancen sa,ashe ya b’oye min wani babban abu,sai nan gaba za ku ji illar da suka yi min!

Na ce”to amma meyesa duka jikina yake ciwo? Kuma maganin bacci kuka bani ko?”

Ya yi dariya ya ce”ai dole jikinki ya yi ciwo,tunda ba ki tab’a shan irin k’wayar ba,ke ta ma fa sake ki da wuri”.

Na ce”amma Nazifi meyasa kuka ba ni k’waya?”

Ya ce”to Zinatu gani na yi idan idonki biyu za ki iya kawo cikas wurin gudanar da aikin,ko kuma bayan mun kai ki,ki ji tsoro daga baya ki lalata aikin,amma wallahi babu abin da aka yi miki”.

Na sauke ajiyar zuciya na ce”to shi ke nan,Nazifi na gode sosai, Allah ya biya ku”.

“Amin matar oga J.S” Ya fad’a yana dariya. Na yi murmushi na kashe kiran.

Bayan na fito aka tisa ni a gaba,da fad’a kamar za a min ciki da hak’ora,ni dai ban wani damu da hayaniyar su ba,tunda dama na san ta zama wajibi,kuma ko dukana za a yi tunda burina zai cika ba zan damu ba.Bayan sun gama bambamin su,sai kuma suka sakko suna tambaya ta a inda na had’u da Salim har ya min fyad’e,na fad’a musu dama can saurayina ne,kuma ba halinsa bane,shi ma tsautsayi ne ya afka masa.

Anti ta katse ni da fad’in”to idan ma halinsa ne cutar y’ay’an mutane ai yanzu ya yi wanda ba zai kub’uta ba,don kuwa yanzu sati d’aya aka tsayar auren ku”.

Na ji zuciyata ta motsa,sai na rasa farinciki zan ji ko akasin sa? Ni dai abu d’aya da na tsana yanzu bai wuce yanda y’an’uwana su ke yiwa Salim kallon macuci ba,na san alhaki a kaina,sai dai na kan ji dama-dama idan na tuna da anyi auren komai zai wuce…

Na tashi na shige d’aki,na kwanta,ina jiyo tattaunawar su,har aka kira la’asar.

Ina idar da sallar la’asar Baba ya shigo,ya kira ni,na zo na tsugunna kaina a k’asa,to shima dai fad’an ne babu k’akk’autawa,kuma ya tabbatar min ranar Asabar za a d’aura aurenmu da Salim, kamar yanda mahaifinsa ya tsara, ya ce min shi ma kuma ya amince don shi ne kawai mafita a gareni.

Washegari da safe Anti Maimuna yi min waya, ta ce na je gidan Ummi yanzu, na shirya na tafi ina ta fargaba.A d’akin Umma na same ta,na zauna na gaishe su suka amsa babu yabo babu fallasa,na yi shiru ina jiran ta inda za su fara tasu tijarar,jin shirun ya yi yawa na ce”Ummi ga ni”.

Ta ce”ai na gan ki, me zan yi miki? Ko na kira ki ne?”

Na ce”Anti Maimuna ta ce na zo”.

Ta ce”to ki kira ta ki tambayi wurin wanda za ki je,ni dai ban kira ki ba”.

Na sunkuyar da kai na ce”don Allah Ummi ki yi hak’uri”.

Ta ce”hak’uri ai ke ya kama Zinatu,ke da za ki zama MATAR SHIGE…”.

Babu wanda ya sake yi min magana, har dai na gaji da zama na,na tashi na koma gida. Tun daga nesa na hango Habib a k’ofar gidanmu,na k’araso na yi masa kallo d’aya,ina niyyar shigewa ya zo ya tare hanya,sannan ya ce”Zinatu zan yi magana da ke”.

Ban ce komai ba,na tsaya sauraron shi

Ya ce”yaushe ku ka had’u da J.S,har kuka yi nisa a soyayya ban sani ba?”

“Ba mu dad’e ba” Na ba shi amsa.

Ya ce”kuma da gaske ne ya yi miki fyad’e?”

Na ce”to kai meye matsalar ka da hakan?”

Ya ce”amma ai kin san ya kamata na sani ko?”

Na ce”saboda me?”

Ya ce”saboda ni zan aureki,kin ga kuwa ya dace na san komai game da matsalar”.

Na yi shiru ina mamakin sa.

Ya d’ora da fad’in”saura fa sati biyu ya rage,zuwa gobe na ke son a buga invitation,sai ki lissafi abin da ki ke buk’ata,na baki kud’in,lokaci ya na k’urewa”.

Daga haka ya tafi,ya bar ni tsaye da mamakin sa.

SALIM

Tunda ya maida su Zinatu ,gida ya dawo ya kwanta,zuciyarsa fal bak’inciki,ya san dai ko giyar wake ya sha bai isa ya kalli Abba ya ce masa ba zai auri Zinatu ba,shi a yanzu ba ma auren nata ne damuwarsa ba,yanda Junaina za ta d’auki lamarin kawai ya ke ji,ace aure nan da sati d’aya? Anya kuwa za ta yarda da shi?

Ya tashi zaune jin k’irjinsa ya yi masa nauyi,ya je ya d’akko lemo a fridge ya yi had’in k’wayoyin sa,ya fara kwankwad’a.

Ya na cikin wannan yanayin Baby ta zo ta same shi,kasa ajiye jarkar ya yi,saboda burinsa kawai ya shanye ya samu bacci ko zai samu nutsuwa.

Ta na k’araso wa,ta warce jarkar ta jefar,ta zauna ta fashe da kuka, ya dafe kansa ya na furzar da iska. Ta ce”Yaya…”

Ba ta k’arasa ba ya katse ta”wallahi Baby Zinatu sharri ta yi min,ban san komai ba”.

Ta ce”na sani,kuma ko na sakan d’aya ban tab’a zarginka ba Yaya,wallahi na yarda shiri ne kawai,saboda son da take yi maka,ga shi har son ya na nema ya zama k’iyayya”.

Ta d’ora da fad’in”Yaya shaye-shaye ba mafita bane,da wannan abun da ka zauna ka na sha da alwala ka yi,ka tada sallah ki ka yi ta karatun k’ur’ani,idan ma ba ka da nutsuwar karaton ka kunna ka yi ta saurara,za ka ji sauk’i a zuciyarka”.

Haka ta yi ta kwantar masa da hankali har sai da ya nutsu.

HABIB
Da daddare Baba ya kira Habib,ya zo gidanmu,bayan sun gaisa Baba bai b’oye masa komai ba,ya zayyane masa halin da ake ciki,tunda a zaton sa shi bai sani ba,ya d’ora da fad’in “Habib na san ka na son Zinatu,amma a irin yanayin da ta shiga yanzu ya zama dole ka hak’ura da ita,shi wanda ya yi b’arnar shi ya dace ya aure ta,ya zauna da ita”.

Habib ya ce” Baba,son da na ke yiwa Zinatu na tsakani da Allah ne,ba gangar jikinta na ke so ba,kuma idan ni d’an’uwanta bai yarda da aurenta a halin da ta shiga ba,waye zai yarda?”

Baba ya ce”ai shi mahaifin yaron ya tilasta masa auren ta,don haka babu wata sauran matsala”.

“Shi ne ma babbar matsalar Baba” Habib ya fad’a.

Ya d’ora “wallahi Baba ina jin tsoron kar ayi masa tilas ya aure ta,ba da son ransa ba,kuma ya zo ya na k’untata mata daga baya.Ni fa na ce,na ji na yarda,zan aure ta a hakan kuma mu zauna lafiya ba tare da na nuna mata alamar na sani ba”.

Baba ya sauke numfashi ya ce” wata sabuwa! To a gaskiya da farko na yi zaton idan ka ji haka za ka fasa aurenta,shi ya sa ma har na amincewa mahaifin yaron,amma yanzu zan sanar masa da na janye maganar,shikenan komai ya wuce,tunda itama ai da nata laifin”.

Habib ya ce”to Baba na gode,Allah ya saka”

“Amin Habibu,ni ne da godiya, ka je ka cigaba da shiri” Baba ya fad’a.

Ina kwance na ji shigowar sak’o wayata,na duba da sauri ganin sak’on Habib ne

_”Zinatu son gaske nake yi miki ba na k’arya ba,don haka ba na jin wannan k’aramar matsalar za ta sa na fasa aurenki.Ki kwantar da hankalin ki,har yanzu akwai maganar aurenmu”_.

_”Habibu! Ba na son ka,kuma ba zan aure ka,Salim zan aura in sha Allah!”_ Na maida masa da amsa.

_”Wallahi sai kin aureni Zinatu,ko kuma ki yi danasani, da nadama mabayyabiya!”_

Ya maido min da amsa.
*MATAR SHIGE…!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION☀️*

Page 21

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
10GB@===2,600
15GB@===3850
20GB@===5000
40GB@===9900
Dial *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*

 

Na tashi zaune ina sake kallon sak’on da d’umbin mamaki,lallai Habib ya na son wargaza min shirina,aikuwa yanzu ne zan d’aura d’amarar zabga masa madarar rashin mutunci,don wallahi ba zai sani na yi wahalar banza akan Salim ba,na kira shi bai d’auka ba,sai sak’on da ya sake turo min me d’auke da kalamar _”I love you “_. Ban samu bacci ba a daren har sai da na samawa kaina mafitar da ta dace.

Washegari da sassafe na tafi gidan su Ummi,na samu dai yau ta kula ni,ta yi ta min nasiha a tsanake,na tambaye ta Kawu Sabi’u,ta ce ya na d’akinsa ba ya jin dad’i,ta ce jiya ma shi ya yi ta tausar Kawu Ummaru,don cewa ya yi sai ya zaneni,na yi farinciki kuwa don dama wurin sa na zo,na ce mata zan shiga na duba shi.

Ina fitowa tsakar gidan na ga Kawu Ummaru ya na shirin fita,ya zabga min wata kafirar harara,na sunkuyar da kai na gaishe shi,bai amsa ba sai k’wafa da ya yi ya fice,na tab’e baki ina bin bayansa da harara sannan na yi sallama a d’akin da Kawu Sabi’u ya ke.

Ya amsa,ya min izinin shiga,na shiga da sallama kaina a k’asa,ko fuskata ba na son ya gani,saboda nauyin zancen da na zo masa da shi, kamar amarya haka na nemi wuri na rakub’e,ina sake jawo hijjabina,na gaishe sa na yi masa ya jiki,ya amsa,na yi shiru na d’an lokaci kafin na ce” Kawu dama wata magana ce nake son yi maka”

Ya ce”to Zinatu,ina jinki”.

Na ce”dama akan zancen aurenmu da Habib ne”.

Ya ce”to,wani abun ne kuma ya taso? Ba an ce ya yarda zai aureki a hakan ba?”

Na ce”e,amma ni Kawu wallahi na fi son na auri shi Salim d’in”.

Ya ce”meyasa?”

Na yi kalar tausayi na ce”wallahi Kawu ni ina tsoron wulak’ancin da zai biyo baya,wannan abun da ya faru k’addara ce,kuma ni a yanda nake gani Habibu zai aureni ne kawai saboda mugunta,wallahi yanzu ba so na ya ke ba…”.

Sai na ga ya had’e rai,ya ce”shi ya fad’a miki yanzu ya daina son ki?” Na girgiza kai,alamar a’a.

Ya ce”to kul! Na sake jin haka daga bakinki,babban rufin asirinki shi ne ki auri Habibu,don kuwa shi ne kawai zai iya zama da ke ba tare da wata tsangwama ba,saboda irin yanda ya ke son ki,kuma ke ma sai bayan auren za ki fahimci abin da ake fad’a miki”.

“Ba za ku gane ba!” Na fad’a a zuciyata.Wani takaici ya rufeni,nan take kuma wata dabarar ta fad’o min,wadda nake kyautata zaton ita ce ma babbar mafita,amma ni da na tsaya duhun kai ban aiwatar ba.

Na tashi na fita daga d’akin,ina jin takaicin su na rashin fahimtata,sallama na yi wa Ummi,na tafi,kai tsaye bakin titi na yi,na siyi sabon sim na saka a wayata,na yi gida.

Ina zuwa k’ofar gida na tadda motar Salim ta na k’ok’arin tsayawa a k’ofar gidanmu.Na ji irin abinda na ke ji idan na gan shi a y’an kwanakin nan,tsayawa na yi har ya daidaita fakin ya fito,mu ka tsaya muna kallon kallo na tsawon minti biyu kafin na k’arasa inda yake,na gaishe shi ina sunne kai,ya amsa fuska babu yabo babu fallasa,sannan ya mik’o min y’ar jakar da take hannunsa ya ce”congratulation Mrs Muhammad Salim!”.

Na karb’a ina mamakin maganar sa,tun kafin na bud’e jakar ya shige mota ya bar unguwar. Na shiga gida,har ina tuntub’e saboda sauri,ina shiga d’aki na bud’e jakar,wani abu ya caki zuciyata ganin abin da yake ciki,invitation ne me kyaun gaske,d’auke da sunana da na shi,na duba date d’in na ga kwanaki biyar ya rage aurenmu.

Na fad’a katifata ina yin siririyar dariyar farinciki,can kuma na rungume katin na fara hawaye.

Na jima a haka,sannan na zabura kamar an tsikare ni,na d’auki wayata na saka sabon sim d’in,na nemo lambar mahaifiyar Habib,sai dai duk rashin kunyata sai na ji ba zan iya aiwatar da abin da na yi niyya ba,na yi shiru ina nazari,kafin na d’auki jakar invitation d’in na fice daga gidan.

Kai tsaye wurin da na san zan samu Anas na yi,na yi sa’a kuwa ya na nan,sai na ja shi gefe,bayan mun gaisa na yi tsara masa duk abin da ya faru tun daga farko har k’arshe, sannan na fad’a masa abin da na ke so ya yi min yanzu.

Tunda na fara jawabi ya ke jinjina kai,ina kai aya ya ce”lallai Zinatu ke ma fa babban kai ce”.

Ya d’ora”yanzu da gaske wannan gayen ne zai aureki?”

Na yi wani murmushi na ce”har ka ga invitation ai ya raba tantama”.

Ya gyad’a kai ya ce”kawo wayas!”.

Na mik’a masa wayata bayan na kira lambar mahaifiyar Habibu,bugu biyu ta d’auka Anas ya k’aro k’arar wayar ta yanda har na ke iya jin muryarta

Bayan ya gaishe ta ta tambaye shi me magana,ya yi gyaran murya ya ce”abokin Habibu ne”.

Ta ce”to ya aka yi? Ai Habibun ma yau bai fita ba,ba ya jin dad’i “.

Anas ya ce” kin san kuwa Zinatu ce dalilin rashin lafiyarsa?”

Ta ce”kamar ya?”

Nan fa ya kwashe k’arya da gaskiyar da muka had’a ya zayyane mata tsaf,tun kafin ya kammala take jero salati da sallallami,sannan ta yi masa godiya,ya katse kiran ya mik’o min wayar,na yi masa godiya sosai ba shi invitation d’in har da na samarin unguwa,na koma gida,zuciyata fal da farinciki.

Ashe na yi wani kuskuren ban sani ba,za ku ji nan gaba…

Ban jima da komawa ba,yaro ya shigo wai ana sallama da ni,duk a zato na Habib ne,amma ina fita na yi saranda ganin Junaina tsaye a kusa da motarta

Na ji wani kishi ya rufe ni,na had’e rai na k’arasa inda take na ce”lafiya dai ko”.

“Ita ce ta kawo ni” Ta fad’a,sannan ta zuge jakarta ta fito da wani envelope ta mik’o min.

Na kalle shi a k’yamace ina tab’e baki na ce”wannan kuma fa?”

Ta ce”me ki ke jin tsoro? Tunda har ki ka samu nasarar sace zuciyar Salim ai kin cika jaruma,ba na jin akwai abin da kanki ba zai iya d’auka ba”.

Na karb’a,ina yi mata kallon daidai nake da ke.

Ta na k’ok’arin shiga mota ta ce”wancen tsohon layin nawa fa ya daina tafiya,idan ki ka buk’aci gani na sai dai ki zo wurin sana’ata”.

Ba ta jira cewa ta ba ta shige mota ta tafi,na shiga gida,ina auna maganganunta,to uban me zai sa na nemi ganinta? “Mahaukaciya!” Na furta ina k’ok’arin bud’ewa,don ta lik’e da gam

“Innalillahi wa inna ilaihi ra’jiun!” Na furta ina fito da duka idanuna waje,wani tashin hankali me bugar da zuciya ya rikito min,ganin abin da ya ke ciki.

Jagwab! Na zube a wurin,ina dafe k’irjina,ba dan na san ba ni da ciwon zuciya ba da zan ce yanzu tashi zai yi,to ta yaya?

Gaskiyar Junaina,dole na neme ta!.

*LAST FREE PAGES*

KADA KU MANTA ZINATU TA CE TAYI KUSKUREN RASHIN GANIN SHAYE-SHAYEN SALIM A MATSAYIN MATSALA!

KUN SAN WACE IRIN ILLA SU NAZIFI SUKA YI MATA?

KUN SAN WANE IRIN KUSKURE TA YI,NA FADAWA ANAS SIRRINTA?

KUN SAN ABINDA JUNAINA TA KAWO MATA?🙆🏻‍♀️

Duka wannan amsoshin suna wurina,kudai ku biyo ni don jin yanda za ta kaya,na tabbatar ba za ku yi kukan kud’in ku ba, don yanzu aka fara wasan.

Ku dai ku hanzarta,don babu jira,gobe za mu d’ora💃

*ME SON CIGABAN SA 200 NE KACAL!*

_KATIN MTN, NA 200 TA WANNAN LAMBAR_
08028966015

MASU TUROWA TA ACCOUNT ZA KU TURO TA NAN
HADIZA ABDALLAH ZENETH BANK
2217944522

SAI KU TURO SHAIDAR BIYA TA NAN
08028966015

Y’AN Niger za ku turo katin Airtel 300f ta wannan lambar
08028966015

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button