Hausa Novels

Rabo Ajali Complete Hausa Novel

[◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣
By Aysha Ya’u Kurah

بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين والصلاة والسلام على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه وسلم. …..

Related Articles

Affan… Affan… Affan..
sau uku saurayin dake tsaye a kanshi ya kira sunanshi amma ko waiwayowa baiyi ba bare ya amsa,, hankalinshi na kan ruwan dake malale cikin wani katon ramin kiwon kifin dake cikin gidansu yana kallon yadda suke wuntsil wuntsil ciki yana girgiza kanshi da jikinshi hakoranshi waje yana dariya da karfi,
duk wanda ya ganshi yasan hankali sam bai isheshi ba, dafashi saurayin yayi hade da zama gefenshi ya watsa ma kifin abincinsu nan take suka kara hautsinewa suna yawo cikin ruwan gwanin ban sha’awa, ihuu Affan yasa yana kaďa kanshi yana kokarin kai hannunshi cikin ramin kuma yana nokesu alamar tsoro, saurayin yayi murmushi ya kara watsa abincin,,, affan ya cikwikwiyeshi cikin murna yana fadin yeeehhh Jabeer kara zuba musu yunwa suke ji dama,
jabeer ya shafa fuskarshi cikin tausayin halin da amininshi yake ciki yace affan lokacin sallah yayi muje muyi sallah mu dawo sai in cigaba da basu abincin,
affan ya no’ke wuyanshi kamar karamin yaro yace um um ba yanzu zanyi sallah ba mummy tace ko da yaushe nayi sallah dai2 ne saboda ni ba a rubuta min zunubi, Jabeer da idonshi ya fara canza kala dan ya riga ya saba da jin hakan a bakin affan kullum in yayi mishi maganar sallah,
cikin dabara yace waya fada maka ba a rubuta maka zunubi Affan,
to bari kaji kasan wutar nan da ake kunnawa mai zafin nan?
Affan cikin firgici yace eh na santa wanda ake dafa min indomie mai zafi ko,
jabeer yace of course ita ay kasan tafi indomie zafi ma ko, affan ya gyada kanshi, jabeer yace to wutar da Allah ke kona waďanda basa sallah tafi wannan zafi sau “dubu malala gashin tinkiya”
affan ya mike a firgice idonshi zuru2 yace tafi wutar dake dafa ruwan toilet heater ma wanda yake kona ni in zanyi wanka,
jabeer yace sosai ma ay wannan ruwan kamar ruwan sanyi ne akan wutar Allah,
affan ya fara ja baya yace karya kakeyi sai naje na tambayi mummy,
jabeer ya mike da sauri dan yasan yana zuwa ya tambayi mummy to fa bazata taba bari yayi sallah ba,
da sauri ya rike hannunshi yace affan ni ke karya,
ya fizge hannunshi yace eh mana kaine kake karya ya juya ya ruga cikin gida da gudu jabeer na kiranshi yayi banza dashi,
dafe kai jabeer yayi cikin damuwa sai da yafi minti 5 tsaye sannan ya wuce ya tafi masallaci,,,,

Jabeer ďinne ya fada maka haka,
affan ya gyada kanshi yana daďa kwanciya jikinta alamun tsoro yakeji kar wuta ta kona shi,
mummy tace rabu dashi makaryaci ne na fada maka ka daina kulashi kullum burinshi ya tirsasa maka yin abinda da bakayi niyya ba kuma ko a musulunce babu takura a addini,
rabu dashi kaji affan din daddy tashi kaje kaci abinci kayi wasanka kaji,
ya daga kanshi ya mike yana tsalle har ya karasa gurin cin abinci yana kiran sunan Hansa’u mai aikinsu tazo ta zuba mishi abinci,

murmushi mummy tayi hade da ajiyar zuciya,
Salma babar diyarta ta ajiye laptop dinta tace mummy wannan tsinannan jabir din so kawai yake ya ruguza miki plan dinki, kullum shi kenan maganar sallah sai kace wani sallau,
mummy tayi dariyar mugunta ta kalli gurin da affan ke cin abinci duk yayi kaca2 da gurin amma ko digo bai diga a rigarshi ba saboda tsananin tsaftarshi,
tace barni dashi ummu, jabeer yana wuce gona da iri tabbas zan san duk yadda zanyi in rabasu da affan in ba haka ba wata rana zai sa kwaba ta tayi ruwa,
Fareedah tace wallhy I so much hate him sai ya dinga wani ďadďaga kai kamar kadangare shi a dole ga kyakykyawa mtsww taja tsaki,
mummy tace ku barni dashi dani yake magana in yasan wata ay bai san wata ba…..

Mrs tijjani shattima……
[15/12 09:32] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣
By Aysha Ya’u Kurah

Da gudu ta shigo gida ta tarar da jarababbiyar kishiyar uwarta a tsakar gida tana fiffita,
sannu da gida kawai tace bata jira amsa ba ta wuce ďakin kakarta Hajja Giďe,
fadawa dakin tayi babu ko sallama ta cire skul Bag ďinta tayi wurgi da ita a kan gado sam bata kula da mutum a kan gadon ba ta fita da sauri ta shiga toilet,
Hajja ta idar da sallah tayi tsaki tace wannan yarinya saidai Allah ya shirya yi hakuri jabeer, ya mike zaune yana murmushi yace zata sani ay bari ta dawo, hajja tace ay kai baka iya yi mata faďa sai dai kullum kace zata sani kullum kai ke kara sangarta ta,
kafin yayi magana ta shigo ta ďane kan cinyar hajja tace hajjanah” sannu da gida,
hajja ta tureta tace dalla ni sauka karki karya ni,
sai a sannan idonta yakai kan jabeer dake kallonta baya ko kiftawa, da sauri ta mike tana murmushin jindadi ta zauna kusa dashi kamar zata shige jikinshi tace dama kana cikin dakin nan,
ta shagwabe fuska tace shine kana kallon hajja tana tureni ko kayi mata magana kalli fa hannu na saura kaďan taji min ciwo,
Hajja tace Allah ya kiyaye dai banji miki ciwon ba ko, ta turo baki tace kinso kiji min mana inaga ma dan kinsan yaya jabeer na nan ne shiyasa baki ji min ciwon ba,
hajja ta kwashe da dariya tace to yau dai sharrin kaďan ne ko Allah nagode maka ma yana cikin dakin da yana zuwa nasan ce mishi zakiyi yau da kyar na barki da rai,
jabeer ya kwashe da dariya,
ta kwabe baki ta fashe da kukan shagwabe harda buga kai a gado,
jabeer yace subhallahi me kuma akayi miki, hajja ta mike tace tabarar fa,
ni bari kaga in fita dan in ina dakin nan zane yarinya zanyi, cikin kuka tace kaji ko wallhy bulala takemin kullum yauma dan ta ganka ne,
jabeer ya haďe rai yace gaskiya hajja zamu kai kararki can kotun karshe a yanke miki hukunci,
hajja tayi dariya tace mu fara shariar daga yau ma in dai akan AFEEYAH ne,
afiyah ta dago kai ta harareta,
jabeer yayi murmushi ya ciro hndky dinshi yana share mata hawaye, yace so sorry babynah, ya dago fuskarta ya kalli cikin idonta yace baki san kin girma da kuka ba, ta kara marairaicewa kamar karamar yarinya tace to baka ganin abinda takemin, yace to nace kiyi hakuri kinji, ki daina yarda suna saki kuka kinaso a dinga ce miki ruwa2,
ta noke wuyanta tace ah’ah, yace to sai kin zama mai hakuri kin daina yawan kuka kinji,
tace tam zan daina, yace yauwa wifey nah,, ya dakko ledar gefenshi ya fito dasu biscuits da chocolates, rungumeshi tayi cikin murna ta mishi peck a kumatu tace I love u so much hubbynah, wani abu yaji yana mishi yawo cikin kwanyarshi,
a hankali cikin rashin kuzari yace more than u do babynah,, ta sakeshi tana dariya, nan suka cigaba da hirah cikin jindadi tana shan chocolates,
sai da aka kira la’asar sannan ya fito zai tafi, rakoshi ta fito yi bayan yayi sallama da hajja, a dai2 kofar dakin inna suwaiba kausar ke zaune tana ganinsu ta shiga wakar habaici tana fadin Allah wadai da halin yan iska sai a shige daki afi karfin awa wai da sunan ana hira,
ran Afiya ya baci matuka jabeer ya lura da hakan ya rike hannunta gam ta fisge, tace da uban wa kike , kausar ta mike tace da ubanki nake kinji na kira sunanki, in ba tsarguwa kikayi ba meye na jin haushi shegiya marar kunyar banza,
Afeeya ta kuma hassala tayi kanta da sauri jabeer ya riketa da iya karfinshi ya jata da kyar suka fita,
kukan bakin ciki ta fashe mishi dashi tana ta tirje hannunta, murmushi yayi dan yasan in bata tsaya ta mayar da martani ba bazata taba hucewa ba,
hakuri ya shiga bata amma ko kalma daya bata iya rikewa ba saboda zuciyarta cike take da bakin ciki gani take idan basuyi fada da kausar ba yau sai tayi ciwo mai tsanani,
matsowa sosai yayi kusa da ita yace haba afee nah, ba nace kiyi hakuri ba, kinaso inyi fushi ne, ta turo baki tana kuka tace ko zaka fashe yau bazanyi hakuri ba,
ya hade rai yace to ni kuma in bakiyi hakuri ba mun bata garin ma zan bari gaba daya, cikin dakewar zuciya tace ka tafi gaba da birnin sin ma dan wallhy bazan hakura ba,
sakin hannunta yayi yace ni ko? Ta juya mishi baya tace eh ďin,
yace to shikenan bye yasa kai ya fita,
ko ajikinta a lokacin saboda zuciyarta na azalzalarta taje gurin kausar…….

Mrs tijjani shattima…..
[15/12 09:32] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣
By Aysha Ya’u Kurah

Tana shiga ta tarar da kausar na buga k’ullun alale, sam kausar bata kula da shigowarta ba sai saukar wata sanda taji akanta da karfi, zafin ya gigita ta sosai tasa ihun da ya fito da inna suwaiba da hajja daga ďaki,
cikin rudewa inna suwaiba ta kama kausar tace kausar meya faru, kausar ta kasa magana sai kuka takeyi hannunta rike da gurin jini na fita,
hajja ta kwace sandar hannun Afiya tace yanzu ke saboda tsabar mugunta wannan murďaďďiyar sandar kika buga mata,
Afiya ta turo baki tace hajja fa baki san abinda tayi min bane shiyasa,
inna suwaiba cikin fushi ta saki kausar tace uban me ta miki, Afiya ta murguďa baki tace gata nan ki tambayeta,
inna suwaiba tace lallai yau za’a haifi ďa mara ido a gidannan wallhy,
Afiya tace a haďa harda mara hanci ma a haifa,
hajja ta bige bakinta tace ke wai wace irin yarinya ce da baki jin maganar kowa,
Afiya tace to wai hajja ita baki tambayeta me tace mana ba, ce mana fa tayi yan iska, inna suwaiba tace ay kunfi karfin ya’yan iska saidai na guguwa, wallhy yau saina miki shegen duka a gidan nan sai na tabbatar wannan tsinannan bakin naki yayi laushi,
Afiya tace Allahn da halicci baki na shi kadai zai iya sashi yayi laushi ba wata ca— hajja ta toshe mata baki tace na shiga uku ni Giďe, yanzu ke Afiya bazan miki magana kiji ba, inna suwaiba tace hajja ki wuce daki ki barni da yarinyar nan wallhy yau sai na mata lahani a gidannan, Hajja tace kiyi hakuri suwai— karki bani hakuri ki cuceni hajja kullum mu kenan a cuce mu a taushe mu, to wallahi bazan dauka ba,
ji yadda jini ke zuba a kan kausar ay dan tasan kuna daure mata gindi ne ke da malam shiyasa take abinda takeso, in ba ta raina mutane ba ay kausar ba sa’arta bace,
hajja tace kiyi hakuri dai nace suwaiba, Afiya ta harari hajja tace wai hajja hakuri kike basu ni baki bani hakuri ba sai su da babu abin ma da nayi musu,
inna suwaiba ta hassala sosai tayi kan Afiya ta cakumota, hajja ta riketa tace wallhy suwaiba karki taba min marainiyar Allahn nan,
wallhy kika kuskura kika sata kuka sai ranki yayi matukar baci,
inna suwaiba tace ay ko sai dai ya baci ta kaima Afiya duka ta goce tana kicikicin kwacewa,
kausar dake jin kanta kamar dutse ta mike tazo ta bayan Afiya ta kai mata duka, Afiya tayi kukan kura ta kwace jikinta a gurin inna suwaiba ta haye kan kausar inna suwaiba na jibgarta ita kuma tana jibgar kausar, hajja na gefe tana kuka ita sam bata ma ga dukan da afiya kema kausar ba ita dai tafi jin dukan da akema Afiya,
dakyar da taimakon shigowar malam faďan ya rabu kowa na maida numfashi, kausar bayan inna taje ta boye tana kuka sosai saboda taji jiki, Malam Atiku cikin bacin rai yake ma inna faďa itama cikin fushi take mayar mishi,
yace yanzu in banda ke babbar kwabo ce meye na shiga faďan yara, wai ke in an barki ga mai ýa ko, kin gama zubar da mutuncinki a idon karamar yarinya, inna cikin fushi tace faďa min mai mutunci a idon wannan shegiyar yarinyar,
hajja ta fashe da kuka tace wallhy ba shegiya bace, Danbaba ni na gaji da zaman gidan nan kullum sai sun tsokani yarinyar nan ita kuma Allah bai ďiga mata hakuri a ranta ba gara muyi nesa dasu su zauna su kadai a gidan,
malam Atiku yace babu inda zaku hajja, baku da inda yafi nan, zan dauki tsatstsauran mataki akan wannan alamarin,
inna suwaiba tayi tsaki ta hararesu tace ka daďe baka ďau mataki ba, wannan yarinyar wata rana saita dauko muku na barin gari, ta kama hannun kausar suka wuce ciki tana masifa zuciyarta na ķuna saboda Afiya, ta rasa dalilin da yasa ta kasa samun nasara akan Afiya,
zama tayi bakin gado idonta yayi jajur dan ba karamin caza mata kwakwalwa Afiya keyi ba,

Can kuma dakin hajja fada sosai suke ma Afiya akan rashin hakuri, malam atiku yace ni wallhy na rasa inda yarinyar nan tayi gadon wannan halin hajja ko kadan bata da hakuri komai aka mata tace saita rama kuma rayuwa bazata taba tafiya haka ba,
Allah na tuba kayi hakurin ma ya ka kare a wannan zamanin bare kuma bakayi ba, hajja tace ay ni yanzu inaga nawa ido tsakanina da Afiya dan gani sukeyi kamar goyon bayanta nakeyi ni take ďaura ma bakin jini dan kawai taga banason abinda zai bata mata rai shiyasa takeson a dinga ci min mutunci,
Afiya ta fashe da kuka tace dan Allah hajja kuyi hakuri in shaa Allahu ko duka na zasuyi bazan kara tanka musu ba,
hajja tayi tsaki tace ke ďin ce zaki faďi magana in yarda, malam atiku yace hajja muyi mata addua babu mamaki bazata kara ba,
Afiya tace Allah abba bazan kara ba,
hajja tace to Allah yasa da gaske kikeyi, duk suka ce ameen, nan suka cigaba da yi mata nasiha akan rayuwar duniya cikin dabara suke mata nuni da illar rashin hakuri,
Afiya jinsu kawai takeyi dan ita bataga rashin hakurin da aketa ikirarin tana dashi ba ita dai tasan ko manzon Allah s.a.w yace in aka bata maka ka rama dai2 yadda akayi maka, to ita kuwa akan me zata yarda tanaji tana gani a taka ta, bazai yiwu ba,, har suka gama nasiharsu Afiya tana gyada kai kamar taji abinda suka ce sai gab da magriba malam atiku ya fita suma suka tashi suka je yin alwala…

Tun daren ranar take zuba idon ganin jabeer shiru har kofar gida ta fito ta tsaya tana kallon kofar gidansu ko zata ga fitowarshi amma ko giftawarshi bata gani,
kullum ta dawo skull sai ta tambayi hajja ko yazo, in hajja tace bai zo ba nan zata fara sababi tace hajja kawai ki fadamin ko kin fita yazo baki nan ko kuma kina baccinki bakisan yazo ba,
hajja saidai tayi tsaki tayi banza da ita ta cigaba da abin da takeyi,
Afiya ta damu sosai da rashin ganin jabeer ji takeyi kamar ta mutu saboda rashin ganinshi haka kawai zata zauna taki cin abinci tayi ta kuka hajja bata ko kallonta bare ta rarrasheta..

Yauma kamar kullum a cikin sati biyun da tayi bata ga jabeer ba tana zaune ta haďa kai da gwiwa tana rero kuka hajja ta ajiye mata abinci a kusa da ita ta zauna gefenta ta kira sunanta, bata dago ta kalleta ba ta cigaba da kukan da takeyi, hajja tace to shikenan tunda bazaki saurareni ba dama jabeer ne,,, ta ďago kanta da sauri tace me ya sameshi hajja,
hajja tace yana nan cikin koshin lafiya baki ga yadda yayi kyau ba, dazu kina makaranta yazo yace in faďa miki yana gaisheki in ya samu lokaci nan da wata daya bayan kin gama jarabawa zai zo ku gaisa,
idonta ya ciko da kwalla tace hajja wata daya? Hajja tace eh mana, ba yace kince ya tafi gaba da birnin sin ba,
to ba wasa nake mishi ba afiya ta faďi haďe da fashewa da kuka, hajja tace ay ko shi da gaske ya ďauka,
Afiya ta maida kanta cikin gwiwoyinta cikin kuka tace shikenan kar ma yazo din dama nasan so kawai yakeyi ya kasheni,
hajja ta gimtse dariyarta tace kull kar na kara ji, duk laifinki ne meyasa in yayi miki magana bakya ji,
Afiya tace to ba nace na daina ba kema shaidace yau sati biyu kenan banyi fada da kowa a gidan nan ba kuma suna tsokanata meyasa baki faďa mishi haka ba, da wani abun nayi da yana zuwa zaki fada mishi amma saboda nayi abun kirki shine kika ki fada mishi,
Hajja dariya taci karfinta sosai ta mike ta fita tana dariya ita kaďai,
Afiya ranta ya kara baci ta kwanta tanata kuka harda sheshsheka tana tausayin kanta dan tasan in bata ga jabeer ba nan da kwana biyu to tabbas zata iya mutuwa,,,
muryar hajja taji tana kwalawa Mahmud kanin kausar kira,
ya taho da gudu yana buga ball yace hajja gani, tace Gidan Alh Bara’u zan aikeka,
Afiya ta mike zubur ta dakko hijab dinta ta fito tace zanje hajja, hajja ta kalleta tace da wannan kumburarren idon zaki shigar musu gida,
Afiya tace eh dashi zan shiga ni dai ki fada min sakon,
hajja tace to ay sai kije ki shiga din mu gani zonan mamu kaji ta miko mishi kullin magani tace kace a aikawa Asiyah nayi mata bayanin amfaninsu,
ya karba yace to hajja, bin bayanshi Afiya tayi ta hađe rai tace bani, jikinshi na rawa ya mika mata hajja tace Afiya karki fita gidannan haka ko uniform baki cire ba, bata saurari hajja ba ta fita dan so kawai takeyi yau ko ta halin k’ak’a taga jabeer….

Mrs tijjani shattima…
[15/12 09:32] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣
By Aysha Ya’u Kurah

Tana fitowa tayi tafiya kadan ta fada gidansu jabeer,
gaisawa tayi da Ado mai gadi, yace yar lelen jabeer kwana biyu kinyi wuyar gani, tace wallhy baba ado mun kusa fara jarabawa ne,
yace au too to Allah ya bada sa’a, tace Ameen ta wuce ciki idonta kan motar jabeer tasan tabbas yana ciki,
kai tsaye ta wuce dakin Ummi ta murda ta shiga hade da sallama,
amsa sallamar yayi haďe da ďago kanshi suka haďa ido,
kallonshi ta tsaya yi idonta cike da kwalla shi kuwa murmushi yake mata yana mai jin dadin ganinta,
girgiza kanta tayi ta wuce kitchen inda taji buruntun ummi,
ummi na ganinta ta fadada fara’arta tace Afee yan matana,
Afiya ta tsuguna ta gaisheta, ummi ta amsa haďe da ďagota tace kin gujeni kwana biyu ko ďan girki kin daina zuwa tayani, afee ta sunne kanta tace wallhy ummi jarabawa zamu fara yanzu bana fita amma ay nazo ran Saturday bakya nan,
ummi tace eh kwarai naje daura, ya hajja, afiya tace tana gida ita ta aikoni wai gashi a kaima anty Asiyah,
ummi ta karbi maganin tace Allah sarki kice mata an gode sosai kinji,
afiya ta gyaďa kanta sannan tace bari in tayaki wanke wanken, ummi tace aiko nagode kamar kinsan na gaji, ga dayyaba har yanzu bata dawo ba, Afee ta fara wanke2 tace ummi Amirah fa, ummi ta wanke hannunta tace tana can kaduna gidan Asiyah har yanzu bata dawo ba,
Afeeyah tace Allah ya dawo da ita lafiya, ummi tace Ameen yar albarka ta fita ta tarar da jabeer zaune yana latsa waya tace au ashe baka fita ba,
yace walhy ummi nagaji ne sosai,
tace ay da gajiya ni bari in ďan kwanta kafin la’asar,
yace to ummi Allah huta gajiya tace Ameen ta wuce ciki,,
saida ya tabbatar ummi ta kwanta sannan ya mike ya shiga kitchen ďin,
tana tsaye tana goge kwanukan da ta wanke tana mita tana girgiza kai,
dariya ta bashi a zuciyarshi yace yau ya shiga uku da masifarta,
karasawa kusa da ita yayi ya dauki plates din da ta goge zai jera tayi saurin rikesu tace malam ka ajiye ni ban sa ka ba, yace ay nasan baki sani ba tayaki kawai zanyi, tace to banaso ko dole ne,
yayi murmushi yace dole ne mana in ban tayaki aiki ba wa zan taya,
tayi tsaki tace wacce ka samu a cikin sati biyu nidai ka fita kawai, da nasan ma zan sameka a gida da ban shigo ba,
yayi dariya haďe da rike kafadunta yace makaryaciya dan ki ganni ne ma kika yarda aka aiko ki,
tace God forbid, in ganka inyi maka me, yace kiji daďi mana in kuma bakiji dadin ganina ba kalli cikin idona ki faďa min,
ta ďago a tsiwace zatayi masifa suka haďa ido tayi saurin sauke kanta saboda wani abu da ta gani a cikin kwayar idonshi, yayi murmushi yace nasan kinyi missing ďina,
cikin muryar shagwaba tace ni banyi missn dinka ba, yace um um fa karki sani in tafi gurin da bazaki kara ganina ba, muryarta ta fara rawa tace me ya rage kuma tunda har ka iya yin sati biyu baka neme ni ba, ya dago kanta ya kalli idonta da hawaye ya fara zuba a cikinsu yace bake kikace in tafi ba,
ta dunkule hannunta ta buga a kirjinshi da karfi tace to ba wasa nakeyi ba, shine ka daina bari in ganka baka ma damu da halin da zan shiga ba kasan ko kwana ďaya ne in ban ganka ba banajin daďi ni nasan yanzu ka daina sona tunda har ka iya yin sati biyu baka ganni ba kuma ka zauna la-fiya ta karasa fadi cikin kuka mai tsanani,
kwantar da kanta yayi kan kirjinshi dake bugawa da sauri yace am so sorry Afee nah kece bakya ji in na miki magana,
tace wallhy na daina kaje ma ka tambayi hajja Allah ko sun tsokaneni bana tanka musu,
jabeer yace to yi shuru na yadda ki daina kuka kinji,
ta gyada kanta tace promise me bazaka kara yin bacci baka ganni ba,
yace I promise baby in dai da rai da lafiya bazan kara ba kinji, tayi murmushi tace Allah ya kara maka tsawon rai da kuma lafiya in dinga ganinka har karshen rayuwata,
ya ja kumatunta yana murmushi yace Ameen my queen,
tayi dariyar jindadi suka cigaba da kife kwanukan suna hira har suka gama,
a parlor suka zauna yake tambayarta karatun jarabawa, tace tanayi sosai saidai maths ke dan bata wahala, yace baki da matsala zamu dinga yi kullum kafin ku fara exams tashi ki rakani gidansu Affan,
ta turo baki tace nidai bazan shiga ba,
ya harareta yace yau sai kinzo munje kin gaisheshi rabonki da shiga gidan tun kafin ya fara ciwo saboda haka yau sai kin shiga, ta marairaice tace ni fa ba ruwana in wadannan masu kama da iyamuran sukayi min wllhy ramawa zanyi saidai kace bani da hakuri,
ya murďe bakinta har saida tayi kara yace suwaye masu kama da inyamurai,
tace oho ni nasan sunansu ne,
yayi dariya yace bazaki taba canzawa ba afee sai dai addu’a, tace wallhy zan canza amma fa baza a dakeni a hanani kuka ba,
yace to naji tashi muje bazamu daďe ba, tace too ta mike suka fita suka shiga gidan Alhj Basheer,,

Cigaban na 4..

Yana zaune as usual a gurin kifaye yayi kasake yana kallonsu kamar me nazarin wani abu,
jabeer ya dafashi ya juyo a firgice ganin jabeer yasa shi washe hakori sosai yana kaďa kanshi cikin murna,
jabeer yace Affan abokin jabeer kuma abokin kifi,
Affan yayi dariya cikin maganar dolaye yace jiya baka zo ba inata kallon can kofar mota har dare baka zo ba, jabeer yace kayi hakuri na danyi wata tafiya ne,
Afiya dake tsaye fuskarta dauke da tausayin halin da affan ke ciki tace ina wuni, ya ďago kanshi dake rawa yana washe hakori yana kallonta baya ko kiftawa, duk maganar da jabeer ke mishi bai kalleshi ba idonshi na kan Afeeya kanshi yaki tsayawa guri daya,
jabeer ya kalli afeeya da ta rabe tana jin tsoron kallon da Affan ke mata yayi murmushi yace affan baka gane Afeeyah ba, affan ya girgiza kanshi ya runtse idonshi kamar yana son tuno wani abu can ya bude idonshi yace na ganeta amma na manta a wani cartoon na taba ganinta,
jabeer ya kwashe da dariya haka shima affan suka dinga dariya tare saida jabeer yayi shuru sannan affan ma yayi,
jabeer ya kalli afeeya da ta cika tayi fam ya maza ya mike yace Affan ka jamin bala’i,
affan ya mike shima ya matso kusa da afiya sosai kamar zai shige jikinta yasa hannu ya shafi fuskarta wani irin laushi yaji haďe da sanyi mai fisgar zuciya ya maza ya cire hannunshi yana tsalle yace bari inje in fada ma mummy yau na taba fuskar cartoon, jabeer ya janyoshi yace karka kara ce mata cartoon,
Affan ya bata fuska yace to mecece in ba cartoon ba kalli fa idonta kato irin nasu, kuma ka taba fuskarta kaji,
jabeer yace idonka ne ya ga cartoon wannan Afeeya ta ce,
ka tuna ta, Afeeya mai kyuiya mai kukan banza ya faďi yana mata kallon tsokana,,,
affan ya kara rufe idonshi ya bude yace mai kuka irin na mage, Afiya tayi tsaki cikin fushi ta fara tafiya, affan yace jabeer kace ma cartoon ta dawo dama bani da barbie din wasa,
jabeer yabi bayan afeeya yana cema affan jeka kace ma mummy ta siyo maka wannan barbie din tawa ce,
Affan ya bata rai yace sai na fadama daddy in ya dawo ince kaki bani barbie,
jabeer bai kulashi ba shidai hakuri kawai yake bawa afeeya, suna kaiwa gate zasu fita shima affan yasa kafa zai bisu yaji wani irin tsawa mai firgitarwa sannan gabanshi yaga kamar namun daji suna so su biyoshi,
a sittin ya ruga ciki yana ihu yana kiran sunan mummy,
jabeer sam bai lura da yanayinshi ba ya ďauka shirmenshi ne dan baya taba wuce kofar mai gadi yauma yayi mamakin da ya biyosu har gate saboda barbie,,

Har cikin gida ya
rakata yana rarrashinta da kyar ta sauka da alwashin ta gama shiga gidan Alhj basheer har ta koma ga Allah dama sam jininta bai haďu da flowers din kofar gidan ba ma bare a kai ga mutanen cikinshi gara ma daddy da shi affan din suna gaisawa in jabeer ya kaita gidan, ta saki ajiyar zuciya tace yaya jabeer haka Yaya affan ya dawo rabona da ganinshi tun ina js3,
Amma wai wane irin ciwo ne wannan,
hajja dake gefensu tace au ke yau kin shiga kin ganshi,, ay a unguwar nan babu wanda ake bari yaje dubashi ko meye dalili oho,
jabeer yace hmm babu wani dalili hajja kawai dai matar gidan ce bata yarda a ganshi ni ma dan ta rasa yadda zatayi dani ne shiyasa ta barni,, ga daddy ba mazauni ba dan sai yafi wata bayanan,
hajja tace to Allah dai—- sai bakinta ya sar’ke kamar a datseshi da gum…

wannan itace babbar jarabawar da Allah ya daurawa AFFAN ta hanyar kishiyar uwa babu wani mahaluki a doron kasa da zai iya yi mishi addu’ar samun sauki,
jabeer shi ne kadai yake iya ganinshi har yayi yunkurin sanyashi a hanya amma saboda karfin iko da lokacin da Allah ya ara ma mummy, daga affan ya fara jin maganar jabeer kamar kiftawar walkiya sai ya mance abinda yace ya bijire mishi,
duk yadda taso rabasu ta kasa saboda amintar su mai karfi ce wacce zaiyi wuya kasamu labarinta a kasar hausa,

Bari in baku takaitaccen tarihin gidaje ukun…

Mrs tijjani shattima…
[15/12 09:32] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣
By Aysha Ya’u Kurah

A unguwar “zoo road” dake cikin garin “kano” ta dabo tumbin giwa nan zan ďan tsakuro muku tarihin gidajen makota ukun,

Alhaji Basheer Balarabe dan asalin k’asar Cameroon ne, sana’ar Gwal ita ta shigo dashi kasar nigeria tun yana saro kaďan2 yana siyarwa har Allah ya sanya wa abin albarka ya koma sarinsu da yawa yana shigowa dasu yana siyarwa,
a duk cikar kasuwar gwal dake cikin garin kano babu wani wanda yakai Alhj Basheer kawo ingantattun gwalagwalan da babu mixed a cikinsu, wannan dalilin ne yasa duk wanda ya tashi siyan gwal to fa a gurinshi zai siya dan shagunanshi sun fi karfin goma a cikin kasuwar,
Alhj Basheer ya auri matarshi ta farko kuma yar uwarshi Zeenatu,
auran zumunci akayi musu wanda ganin girma da kuma karamcin rik’on da iyayen zeenatu sukayi mishi yasa ya yarda da auren amma badan yanaso ba,
shekararsu uku da aure suna zaman lafiya saboda irin biyayyar da take mishi, a cikin wannan shekarun ne ya dakko ta suka dawo Nigeria da zama kwata2 sai dai suje cameroon hutu,
a shekararsu ta biyar da aure ne hankalinsu yayi matukar tashi saboda rashin haihuwa,
babu ma kamar alhj basheer da yake ganin madarar kuďi babu maciyansu sai dai yan uwa da makota,
ya kosa matuka yaga yana da ya’ya barin ma ďa namiji dan wani lokaci har mafarkin gashi nan an haifa mishi ďa kuma namiji yakeyi,
a wannan yan lokutan ne ya fara tunanin k’aro aure duk da a lokacin ba mazauni bane saboda bai fi yayi sati a nigeria ba sauran kwanakin duk a kasar waje yake yinsu yana turo kaya,

Wata ranar asabar ya baro airport cikin tsananin jin yunwar da ta bashi mamaki, nan ya tsinci kanshi da tsayawa a wani restaurant dake Jabi dan bazai iya matsawa ko’ina ba tare da yaci abinci ba,

cikin karairaya wata farar ingarmar budurwa ta matso kusa dashi tace alhj me kake bukata,
cikin ruďewar ganin jar fata gata a cike gaba da baya ko’ina sai rawa yakeyi a jikinta yace anytn special yanmata dan yunwa nakeji sosai,
ta ďan tsuguno kadan tace an gama ranka ya dade,
tayi gaba jikinta na girgiza alhj basheer ya bita da ido baki sake yana kallonta har ta bace ma ganinshi, ajiyar zuciya mai karfi yayi sannan ya gyara zamanshi dan ba karamin tafiya da imanin shi tayi ba, cikin yan dak’ik’u ta dawo dauke da plate din fried rice da pepper chicken sai peprsoup din kayan ciki a gefe da drinks,
alhj basheer da bai cika cin abincin restaurant ba sai gashi ya tsinci kanshi da cin abincin nan sosai, takardar bill ta kawo mishi yabi kirjinta da ya cika kamar zai faso cikin rigarta da kallo yace yanmata duk wadannan kudin ni zan biya,
tayi walll da ido tace alhj yayi kaďan ko, yayi wata kasaitacciyar dariya yasa hannu a aljihu ya ciro rafar dari biyar yace ya daiyi yawa ni kinga abinda zan iya biya nan,
tayi murmushi tasa hannu ta karba haďe tsugunawa, tace to an gode yallabai,
tayi gaba ya bita da kallo yana lasar baki kamar tsohon maye,
tashi yayi bayan ya gama goge bakinshi da tissue yana sakace ya yafito wani yaron da yaji an kirashi da John, da sauri yaron yazo ya tsuguna yace alhj any problm,
alhj basheer ya ďagoshi yace no young man ina bukatar taimakon ka ne,,
john cikin mamaki yace taimakon me alhj, alhj basheer ya jashi waje yace wannan yarinyar da take kawo abinci nake son sanin sunanta,
john yayi dariya yace OYIZA kake nufi,
alhj basheer yace ban sani ba wata fara kakkaura,
yace yes itace alhj sunanta “Safiya” Oyiza ake ce mata ita y’ar mai restaurant din nan ce,
bata cika zuwa nan ba sai in tazo daga lagos kuma I think gobe ma zata koma saboda tafi 1wk anan gurin,
ya fara waige2 ya ďan rage murya cikin gulma yace amma fa alhj bat— maganarshi ta katse sakamakon kiranshi da yaji madam dinshi nayi,
da sauri yace alhj bari in tafi sai anjima ya ruga ciki da gudu,
alhj basheer a zuciyarshi yace ko bata dame ya ke so ya fada mishi oho? ya ďaga kafadarshi kawai ya dawo ciki dan yayi magana da mahaifiyar oyiza,

Guri na musamman maman oyiza ta bawa alhj basheer ya zauna tana yashe hakori cikin murna dan taga gurin ďana tarko,
cikin girmamawa suka gaisa, saida shuru ya đan ratsa na kusan 2mins sannan alhj basheer ya fara magana yace madam naga yarinya a gurinki ne kuma inaso,
wallhy da aure nake sonta ba yaudararku zanyi ba, ni in kin amince ma a cikin sati biyu a gama komai na maganar aure,
maman oyiza tayi ajiyar zuciya cikin gurbatacciyar hausarta tana girgiza kai tace anya kuwa gaskiya bazan iya ba bahaushe oyiza ba, kaiii bazan iya ba alhj hausawa basu cika rik’e mata ba,
yayi murmushi yace wasu dai madam ai ba duka aka taru aka zama daya ba,
tace ummm haka ne amma gaskiya— alhj basheer ya katseta yace madam na barki kije kiyi tunani, zan dawo nan da 2days sai inji abin da kika yanke ya ajiye mata wasu kudin a gabanta sannan ya tashi ya tafi….

Mrs tijjani shattima…..
[15/12 09:32] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣
By Aysha Ya’u Kurah

Jujjuya kuďin maman oyiza takeyi cikin fargaba dan ita a tunaninta harka kawai zaiyi da ďiyarta su tatsi kudi su bar banza,
sai kuma gashi da aure yazo musu, ita kuwa sam bazata iya aurawa ďiyarta bahaushe ba tafi son kabilarta kuma dan garinsu wato OKENE, mikewa tayi ta shiga wani ďan lungu da oyiza ke yawan zama kullum in tazo abuja, waya takeyi tana dariya cikin murnar da uwarta ta kasa gane daga inda murnar ta samo asali,
zama tayi kusa da ita tana mata magana, oyiza tayi saurin katse wayar da takeyi ta kalli mamanta,
maman oyiza ta dafa ta tace sofy mun shiga cikin matsala,
oyiza ta haďe rai tace matsalar me mum, maman oyiza ta share gumin da ya tsatstsafo mata ta labarta ma oyiza duk yadda sukayi da alhj basheer, cikin damuwa tace ni bansan me yasa kika fito har kika kai mishi abinci ba, ke da ko ruwa bakya kai ma customers in kina gurin nan,
oyiza tayi dariyar farin ciki a zuciyarta tace thank uu “Chummy lord” ta kalli mamanta tace mum wannan shine matsala? ay wannan is a blessn to us,
kinsan irin dukiyar da yake dashi ne,
kuma kinsan abun dadin bai taba haihuwa ba,
maman oyiza ta saki baki tace a ina kika san bai taba haihuwa ba,
gaban oyiza ya fadi amma ta dake tace john ne ya fada min, mamanta tace koma dai menene ni bana son auren bahaushe, oyiza ta dafa mamanta tace mum karki fara wannan maganar ma saboda bazai yiwu ba, kawai in yazo kice mishi eh mun shirya yazo ayi maganar aure,
maman oyiza cikin bacin rai tace kina hauka ne,
oyiza cikin fushi tace yess am mad in dai akan kuďi ne, kuma duk wanda ya nemi shiga tsakanina da samun kuďi ko waye wil fc d consequences,..
Maman oyiza ta mike tace to zanga yadda za’ayi ki aureshi tunda ke baki da hankali kina zuwa 1yr ya koroki in dai bahaushe ne ki ma cire a ranki dan I swear bazan bari ya shigo ko gate din restaurant dinnan ba bare yazo jin wani feedbk ta wuce tana masifa,

Idon oyiza yayi jawur nan da nan fuskarta ma ta rikiďa ta zama jawur gunin ban tsoro, ta mike kamar walkiya ta wuce motarta taja tayi gida,
wani jan akwati ta bude ta dakko wani farin kyalle da wata jar baby kamar sassakar laka,
wani kirari tayi mai karfi da ya girgiza gidan da take ciki, cikin second uku wata mace ta bayyana a gabanta cikin jajayen kaya,
“fitsarin tsoro na saki ganin halittar wannan matar jikina take ya fara rawa idona ya ciko da kwalla a zuciyata nace duk “Badiyya” ce ta sani wannan bin diddigin gashi na kawo kaina inda zan halaka” dakewa nayi na fara karanto adduoin neman tsari, nan na samu kwarin gwiwar kai kunnena da idona gurin abun da sukeyi, oyiza na hango tayi ma matar da naji ta kira da “Chummy lord” sujjada (wa’iyazubillah) chummy tasa ma oyiza wani nannaďaďďen farin yadi a kanta tace “u are safe wit me by ur side”,
oyiza ta ďago kanta zuciyarta a dake tace I found him my lord, amma mum naso ta kawo min matsala, chummy tayi dariya mai karfi tace ur mum ko kuma gvn mum,
kin manta u sacrifice her sannan kika samu alhj basheer yasan inda kike,
cikin faduwar gaba oyiza tayi kasa da kanta tace I love my mum my lord,
chummy tace I knws dat amma in har kinason jin dadi dole ki katse numfashin mahaifiyarki, kuma bari in fada miki kina shiga gidanshi zaki samu ciki so u will be d apple of d house saboda u bring air to d family, ,
mum dinki ta fara tsufa so let her go ke kuma ki fara rayuwarki mai daďi,
haka tayita convincn dinta har ta gamsu ta fitar da uwarta a ranta tayi alkawarin yau da dare zata bada uwarta saboda komai ya tafi mata daidai,
sun kusa awa suna tattaunawa kafin Chummy ta bace, oyiza ta mayar da komai na tsafinta ta fito ta shiga kitchen dan tayi ma innocent mum dinta girki, tsayawa tayi a kitchen ta kasa komai tana tunano rayuwar da tayi da mahaifiyarta da irin wahalar da mahaifiyarta tasha akanta da karatunta, tayi tsaki a zuciyarta tace kuďi yafi min komai ciki harda ke mum,
am so srry mum u have to go,
ina son sunana ya shiga jerin mata masu arzikin duniya,
girki ta farayi duk da jikinta a mace yake amma ta dake saboda zuciyarta ta daďe da kangarewa da shan jinin bil adama,

Oyiza ta shiga cikin kungiyar asiri ne tun shekararta ta farko a jamiar lagos,
wata kawarta esther Babajo ita tasata lokacin tana shan wahalar rashin kuďi da abinci saboda mahaifiyarta bata da kuđi, sannan kuma sun shiga ne dan su dinga samun first class result a set dinsu,
haka kuwa yake faruwa dasu dan su biyun nan saida ya zamana babu wanda yake iya bugesu, kuma kuďi ma babu macen da zata nuna musu shanawa a cikin skull, duk irin gulmarsu da akeyi babu wanda ko wacce ta isa tazo gabansu tayi saboda tsabar tsoronsu da ake ji,
jini kuwa su kansu basu san adadin na mutanen da suka sha ba,
oyiza ta hadu da alhj basheer ne a airport lokacin sun dawo daga Italy ita da esther, tunda ta daura idonta akanshi da suka sakko daga jirgi taji sonshi mai tsanani ya kamata,
tun a airport suke bin bayan motar da ta daukeshi har zuwa hotel din da zai kwana kafin safiya ya wuce kano,
Saida suka bari ya shiga ciki sannan suka samu drivern da ya daukoshi suka tambayeshi sunanshi, da kyar da kuma kuďi da suka bashi ya sanar dasu sunanshi da kuma garin da yake, godiya sukayi mishi sannan suka wuce,
tun daga ranar Chummy ta fara mata aiki akanshi, nan ta gano irin kudin da yake dashi da kuma wanda zaiyi nan gaba, ta kuma gano matsalar da yake ciki na rashin haihuwa ,
jin yunwarshi da tsayuwa a restaurant dinsu 4d first tym duk aikinsu ne..
dariya oyiza tayi bayan ta gama tunano wadannan abubuwan sannan ta sauke abincin da ta daura ta kwashe ta haďa juice ta jere su akan dining ta zauna zaman jiran mamanta dan suyi hirar karshe….

Allahu akbar,,,
tabbas mun tsinci kanmu a zamanin da kuďi suka fi wadanda suka kawo mu duniya daraja,
kuďi sunfi ďan da ka tsuguna ka haifa saboda a cikin 100% 85% zasu iya bada komai nasu dan su samu kuďi dattin duniya,,,
tabbas a wannan zamanin da muke ciki masu karancin imani da tawakkali zasu iya aikata komai saboda kudi,
Ya Allah ka tsarkake mana zuciyarmu da ta yan uwa musulmi baki ďaya,
Allah ka azurta mu da baye bayenka kayi mana rowar talaucin da zai kaimu ya baro mu,, ameen thumma ameen….

Mrs tijjani shattima…..
[15/12 09:32] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 7⃣
By Aysha Ya’u Kurah

Daren ranar bayan sun gama hirah da mamanta ta nuna mata ta hakura da maganar alhj basheer, mum ta yi murna sosai dajin hakan daga bakin oyiza,
sai gurin sha ďaya taga mum na hamma ta dafata tace mum bacci kike ji, mum tace eh bacci sosai nakeji bari inje in kwanta, oyiza ta mike tace bari in kara gyara miki ďaki saboda kiji dadin bacci da kyau,
mum tayi murmushin jin dadin ganin yadda yarta ke tarairayarta, dakinta oyiza ta wuce ta yaye shimfiďar zanin gadon tasanya mata wani fari kall a kasa sannan ta ďaura nata akai,
idonta yayi ja lokacin da ta dauko wata kwalbar farin magani zata yayyafa a gadon, sai da ta ďan zubar da hawaye sannan ta yayyafa maganin ta fita taje ta taso mum da ta fara bacci,
har ďaki ta rakata ta rufo kofar ta koma ďakinta tayi tagumi tana jiran dare ya raba ta tafi gurin meeting, ,,

2:45am

Tsugune suke gaban “CHUMMY LORD” cikin jajayen kaya su kusan goma sha biyar maza da mata masu neman arziki da mulki,
jini ne a kwarya wani bakin mutum ya ďauko ya mika ma wacce take gaba ta sha ta mika ma sauran duk suka sha sannan suka ajiye kwaryar, wani irin kirari haďe da ihu “chummy” tayi akan wani farin kyalle sai ga wasu yara yanmata basu wuce shekara 14 ba sun bayyana a gabanta cikin night gown, yara ne farare kyawawa masu kama da juna da ganinsu yan biyu ne,
a firgice yaran suka fara waige2 suna kankame junansu, chummy tayi dariya sosai tace Alhaji Sambo aikinka yayi kyau lallai ka tabbatar kana son cin wannan kujerar,
da sauri yaran suka fara kallon mutanen gurin ko zasu ga wanda aka kira da sunan mahaifinsu, jikinsu ya kara rawa lokacin da idonsu ya sauka akan babansu mai kaunarsu dare da rana wanda a wannan daren kafin su kwanta bacci saida yayi yawo dasu cikin garin abuja da kewayenta ya kashe musu makudan kudi na ban mamaki, cikin rawar murya suka ce PA–PA,
alhj sambo ya sunkuyar da kanshi kasa,
daya daga cikinsu tayi karfin halin zuwa gabanshi ta dafashi dan gani takeyi kamar mafarki takeyi,
jin da gaske shi ďinne yasa ta rusa ihu ta kalli yar uwarta tace “Fanne” ba mafarki nakeyi ba wallhy papa ne, meyasa zaka mana haka, yanzu ashe neman duniya zai iya saka ka bayar da ya’yanka na cikinka,
papa sanda zaka bada damu bakayi tunanin bazaka kara ganin mu ba,
cikin fushi dayar tace “Fanna” meye a ciki dan ya bada mu an kashe,
kika san iya adadin mutanen da ya kashe saboda neman duniyarshi,
kukan me kikeyi? Saboda bazaki kara shakar iskar duniya ba kome?
Inda zamu tafi nan zai zo yau ko gobe ko jibi in kwananshi ya kare shima,
gara ma su kashemu da zama karkashin zalunci da cin kudin haram da na kawunan mutane,
wani mugun mari aka dauketa dashi ta waiga ta kalli bakin mutumin zuciyarta ta kara zafi tace ba mari nake bukata ba kashemu zakayi mu huta,
“chummy” tayi dariyar kusan minti uku sannan tace ai dama kun mutu ruhinku ne anan,
in naso zan iya barin ruhinku yayita yawo shi kadai a duniya gangar jikinku kuma tana rami,
Fanna tace ki so din,
fanne tayi saurin cewa dan Allah dan annabi ku maida mu gurin mammi ta waiga ta kalli mahaifinta tace papa kaji tsoron Allah,
Oyiza cikin Fushi tace chummy lord yaran nan na bata mana lokaci gashi har asuba ta gabato ga kuma mum can daure gara ayi mata abinda za’ayi in wuce gida,
Fanne ta waigo ta kalleta a hankali tace mum? U mean mum dinki kika bayar saboda— wannan karan chummy ce da kanta ta kai mata duka a baki,
chummy tace bazan kashe yaranka yanzu ba alhj sambo dey wl be under my control, zan watsasu duniya saboda naga za’a dama dasu,
fanne tace karya kikeyi jininmu ne yafi karfin ki,,,
chummy tayi murmushi tana girgiza kai,,
Alhj sambo cikin tsoro yace my lord ina tsoron kar suyi min illa, chummy tace babu kai babu su saboda zaku binne gangar jikinsu a grave so ka kwantar da hankalinka, yayi ajiyar zuciya yana kallon hararar da fanne take musu shi da oyiza,,,
dafa kansu chummy tayi da wata sanda mai kyalli nan da nan suka bace,,

Mum din oyiza kuwa kuka ta dingayi ganin ďiyarta ce ta bada ita, gaba daya magana ma kasa fita tayi a bakinta sai girgiza kai kawai takeyi tana tunano rayuwar da tayi da yarta,
cikin minti goma aka gama da maman oyiza suka gama shaye shayensu sannan kowa ya bace, ,,

Kuka oyiza takeyi a bakin gadon da mum ke kwance tana ihu makotan da ta aika mai gadinsu ya faďa musu suna kanta suna bata hakuri,
ta kira can kauyensu ta fada musu suma suka dinga ihu suka shirya suka kamo hanyar abuja,
Guraren karfe biyu akayi mata sutura da kyar dan yan uwanta sunce saidai su kaita can okene a binneta ita kuma oyiza ta kafe saidai a binneta anan saboda tsoron kar asirinta ya tonu dan tasan kakarta na ganinta zata san abin da ya kasheta dan itama mayyar kanta ce,
saida malamai sukayi ma yanuwanta nasiha sannan suka yarda akayi mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya…

Washe gari ta kira john a waya tace yaje ya buďe shago in alhj basheer yazo ya kawoshi gidansu,
haka kuwa akayi yaje ya bude shago amma har dare babu alhj basheer, washe gari ma haka,
oyiza hankalinta in yayi dubu ya tashi tana ta kai kawo saboda rashin zuwan alhj basheer gashi har an kusa sati daya,
a daren ranar ta bayyana gaban chummy da matsalolinta, chummy ta gama incantation dinta tana girgiza kai tace yana karkashin kulawar matarshi,
ta nuna mata wata kwarya,
bakar mace ta gani a ciki sanye da hijab tsaye gefen gadon mijinta dake bacci tana sallar dare in ta idar sai tayi adduoi ta tofeshi dashi sannan ta mike ta kara tada kabbara,
chummy tace kin gani da idonki ko? Oyiza ta haďe rai tace na gani amma ay ni babu ruwana da wannan, mum na bayar saboda haka so kisan duk yadda zakiyi,
chummy tayi dariya tace dadina dake wutar ciki, trust me Oyee cikin satin nan za’a daura miki aure da alhj basheer,
cikin farin ciki oyiza tace yanzu naji magana…..

Mrs tijjani shattima…..
[15/12 09:32] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 8⃣
By Aysha Ya’u Kurah

Alhaji basheer tsugune yana gyara canvas din kafarshi cikin shigar blue nd white track suit,
mikewa yayi bayan ya gama ya kalli matarshi zeenatu dake gyaran gadon da ya tashi yace to ni na fita training, tace to a dawo lafiya yallabai,
yace Allah yasa sannan yasa kai ya fita,
Zagaye ya dinga yi yana jogging cikin farin ciki saboda yadda sanyin safiyya ke kaďashi,
yayi zagaye na tara yana yi yana hutawa, a zagaye na goma ne ya hango wani shima jogging din yakeyi dai2 gurin wata katuwar kwata kafarshi ta gurďe ya tafi zai faďa alhj basheer yayi saurin rikoshi yana fadin subhanallah sannu,
mutumin ya ďago yana gyara kafarshi yace yauwa nagode sosai gaskiya ka taimake ni, alhj basheer yayi murmushi yace mu gode ma Allah, mutumin ya mika ma alhj basheer hannu yace sunana Bara’u ina nan zoo road, “BB close” opp gidan alhj Basheer Balarabe,
Alhj basheer yayi dariya yace ni kuma sunana Basheer Balarabe (BB) nima ina zaune a zoo rd BB close cikin gidan Alhj Basheer balarabe,
Alhj Bara’u yayi dariya sosai yace ikon Allah alhj basheer, kaga yadda Allah ke abunshi ko, .
alhj basheer yayi dariya yace kai gaskiya bamu fitar da hakkin makobtaka in ba haka ba ga gida ga gida ace bamu san juna ba,,
Alhj bara’u yace ko 1week banyi da tarewa ba kuma nasa ayi min magana da duk makota na kai kaďai ne Allah baiyi zamu hadu ba saboda ance min baka gari,
alhj basheer yace kwarai kuwa ban daďe da dawowa ba, to ya unguwar tamu da fatan dai baka samun matsala,
Alhj bara’u yace walhy babu matsala unguwar cike take da mutanen kwarai naji dadin kasancewata cikin ku, Alhj basheer yayi murmushi suka fara tafiya yace to ya iyalin fa, Alhj bara’u yace tukunna dai har ansa rana jiranta nakeyi ta karasa skull zuwa nan da 3monts sai ayi in shaa Allah,
Alhj basheer yace Allah ya nuna mana kai kadai ne a cikin gidan kenan, alhj bara’u yace eh ni kadai ne amma weekends a daura nakeyi saboda rashin iyali, alhj basheer yace hakan yayi Allah ya taimaka yace ameen har suka karaso gida suna hira cikin kankanin lokaci suka saba da juna, a dai2 kofar gida sukayi sallama kowa ya shiga gida,
kanshi tsaye yake tafiya cikin gidanshi yana amsa gaisuwar masu musu hidima, yazo gab da shiga parlo yaji wata muguwar faďuwar gaba,
juyawa kanshi ya fara yi sosai ya dafeshi ya karasa parlon dakyar ya zauna kan kujera, zeenatu na can kitchen bata san halin da mijinta yake ciki ba,
runtse idonshi yayi siffar Oyiza ta dinga mishi yawo a cikin kwakwalwar kanshi, buďe idonshi yayi da sauri da ya tuno da oyiza gaba daya yaji wani abu ya tokare mishi kahon zuciyarshi, ga wutar son ganinta da ta ruru a zuciyarshi kamar wacce aka iza da petur,
mikewa yayi da sauri ya shiga bayi yayi wanka sharp2 ya fito ya shirya da gaggawa ya feshe jikinshi da turare ya debi kudi a sv dinshi na gida masu yawan gaske sannan ya wuce kitchen ya sami zeenatu,
Cikin rashin fahimta tace tafiya weekend kaiko ina zaka, yace abuja zeena alheri ne yake kirana,
tayi murmushi tace to Allah ya kawo mana alkhairin tare,
yace ameen yar matata sai na dawo, tace to Allah ya tsare ya kuma kiyaye hanya, yace ameen ya fita da sauri,
biyoshi tayi da gudu tace na manta ban fada maka ba, dan Allah zan shiga gidan Malam atiku gurin Ma’u tayi min kitso, yace to adawo lafiya tayi miki mai kyau fa, tace karka ji komai in dai kitson ma’u ne, yayi murmushi ya fita ya tafi…

Da kyar ya gane restaurant din, yana isa ya fito cikin farin ciki,,
tsayawa yayi turus saboda ganin gurin da yayi a rufe, jingina jikin motarshi yayi ya rasa me ke mishi daďi yanzu wa zai fara tambaya inda take anan gurin, ya kusa 30mins kafin ya shiga motarshi da niyyar tafiya,
kamar daga sama ya hango john yana bude gurin,
fitowa yayi da sauri kamar wanda akayi ma albishir da gidan aljanna, karasawa yayi yana kiran yaron, john ya juyo rai a bace saboda yadda yaji ana kiranshi ganin alhj basheer yasa john jindadi ya fito da gudu ya tsuguna a gabanshi ya gaishe shi,
alhj basheer ya amsa suka shiga ciki,
ya kalli john yace ina madam dinku, john ya raunana fuska yace madam is no more alhj tun ranar da kazo washe gari ta mutu, alhj basheer ya girgiza kanshi cikin tausayin oyiza yace Allah ya jikanta to ina yarta oyiza,
john yace tana gida dama tace idan kazo in kaika can gida, alhj basheer yaji dadi sosai a ranshi dan a tunaninshi kafin mahaifiyarta ta rasu tayi mata bayanin komai, tashi yayi suka fito shi da john suka shiga mota suka wuce gidansu oyiza…

Bayan ya gama yi mata gaisuwa yana rarrashinta saboda kukan munafurcin da take yi ita a dole tayi rashin uwa,
tausayinta sosai ne ya ratsashi ya tambayeta ko mahaifiyarta tayi mata bayaninshi,
tayi kasa da murya tace eh a daren ranar ta fada min komai kuma tace in ka dawo zata yarda ka aureni, ta fashe da kuka tace ashe bazata ga auren ba,
alhj basheer zuciyarshi ta kara narkewa yace kin yarda to zaki aureni, tayi kasa da kanta tace ko banaso zan yarda tunda shine last will din mahaifiyata, alhj basheer yace haka ne naji dadi sosai da kuka amince dani, yanzu ina son cikin satin nan a gama magnar komai muyi aure in tafi dake,
wani daďi ya ratsata tace to ba matsala bari in turo maka kanin babana kuyi magana, mikewa tayi ta shiga ciki ta turo mishi kanin babanta da wan mamanta,

Kudin da alhj basheer ya wankesu dashi da kuma nuna yanason ya auri oyiza saboda yana tausayinta shi kadai yasa suka yarda da auren suka sa rana ya biya sadaki da komai, sannan ya tafi cikin farin ciki,
A daren ranar ya fita da oyiza yawo ya siyo mata duk wani abu da mace zata bukata na aure,, sun daďe tare har suka saba sosai kafin su rabu,
Tana shiga gida ta dinga tsalle tana murna nan ta shirya ta wuce gurin chummy yin godiya….

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:32] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 9⃣
By Aysha Ya’u Kurah

Cikin satin aka ďaura auren alhj basheer da Safiya oyiza a okene, shiri na musamman chummy tayi ma oyiza ta haďata da special kayan tsafi a cewarta su zasu taimaketa ta zauna lafiya saboda wannan matar tashi mai yawan addu’a,

Washe garin daurin auren ne ya dauki matarshi da kawayenta biyu suka kamo hanyar kano, tunaninshi ďaya shine yadda zai fara tinkarar zeenatu da maganar ya auri oyiza saboda sam duk wainar da ake toyawa bata sani ba, ita dai taga ana ta aikin gyaran part din gefenta sama da kasa amma sam bata kawo aure yayi a ranta ba, sai gurin bakwai suka shigo garin kano, kallon garin oyiza da esther keyi har suka kawo kofar dankareran gidan alhj basheer dake zoo road,
a kofar gidan alhj bara’u ya hango su tsaye shi da malam atiku suna hira, ganin motarshi yasa suka mike suka karaso gurinshi da saurinsu, ya leko ta cikin glass cikin fara’a suka gaisa, yace ga amarya fa ku gaisa,
alhj bara’u yayi dariya yace wace amaryar kuma, alhj basheer yace amaryata da aka ďaura min aure da ita jiya,
malam atiku yace shine ko labari ranka ya daďe to Allah ya sanya alkhairi sannu amarya,
oyiza ta gyara gyalenta tace yauwa, alhj bara’u ma yayi mishi addu’a suka ja suka tsaya shi kuma ya danna kai cikin gida kirjinshi na duka sosai, parking yayi suka fito duka su ukun suna mika gasu ďirka2, sannu alhj basheer yace musu sannan ya fara tafiya suna binshi a baya,
yana buďe kofar main parlon yayi arba da zeenatu cikin kyakykyawar shigar material dinkin stone work fatar nan tata sai kyalli takeyi ga wani kamshi da sanyin dadi ko’ina a cikin parlon, da sauri ta karaso tana mishi sannu da zuwa,, gabanta ya faďi sosai da ta hango su oyiza amma sai ta kara fadada fara’arta tana musu sannu da zuwa, karasawa sukayi cikin parlon suna yabawa da kyau da tsarin parlon ga kuma kula da yake samu ta musamman,
zeenatu ta nuna musu guri suka zauna ta wuce kitchen cike da tambayoyi a zuciyarta, kayan shaye2 ta kawo musu da snacks tanata yake,
ta kalli alhj basheer da ya dafe kanshi tace yallabai gajiyar ne, tashi muje ciki kayi wanka,
oyiza cikin kishi ta watso ma zeenatu harara,
alhj basheer yace zauna zeena akwai maganar da nakeso muyi dake,
ta nemi guri kusa dashi ta zauna,
a hankali ya fara magana yace sai kuma kika ganni da baki,
tayi murmushi tace eh,,
yace dafatan zaki fahimceni zeenah, kinsan komai nufi ne na Allah kuma matar mutum duk inda take sai ya aureta,
ya nuna oyiza yace wannan matata ce jiya aka ďaura min aure da ita bawai dan inci mutuncinki ko kuma dan bana sonki ba, “a’a” wannan auren ki ďaukeshi kaddararre ne daga Allah kuma babu mamaki safiyya na tafe da alkhairai masu yawa cikin gidan nan,
zeenatu da tayi mutuwar zaune tayi maza ta saita kanta ta kirkiri murmushi tace kaii barka Allah ya sanya alkhairi nayi maka murnar samun karuwa,
ay aure cigaba ne yallabai Allah ubangiji ya bayyana alkhairan dake cikin wannan auren kuma alkhairan ya wanzu a tsakaninmu,
yace ameen yar albarka zeenatu nagode sosai da kika fahimceni,
tace ba komai yallabai bana jayayya da abin da Allah ya kaddara Allah ya bamu zaman lafiya,
yace ameen, nan yayi introducn zeenah a gurin oyiza da irin muhimmacin da take dashi a gurinshi,
oyiza ranta ya baci da irin praisn zeenah da yakeyi a gabanta da kawayenta,
bayan ya gama maganganun da zaiyi yace ma oyiza su tashi ya nuna mata part dinta, suka mike kamar samudawa suka rataya jakunkunansu suka wuce,
zeenah da kiris ya rage ta fashi da kuka ta danne kishinta ta shiga kitchen ta hado musu abinci ta kai musu dakinsu ta fito tayi nata dakin ta rufeshi da key ta faďa gado tanata rusa kuka,

Can dakin oyiza kuwa bin ko’ina sukeyi ita da kawayenta suna tsalle suna murna ganin irin dukiyar da alhj basheer ya zuba a ciki, zama sukayi a kan gado esther tace oyee baby sai kinyi da gaske da wannan matar dan da ganinta ta iya munafurci, evelyn tace green snake kenan, gata very pretty, gaskiya akan matar nan na kara yarda black is beauty kuma suna kama da bash,
oyiza tayi tsaki tace trust mee mana ai matar nan sai mai aikina ta fita daraja bari dai in haihu, kunsan bata haihuwa kuma na riga na gano abinda alhj yafi so a rayuwarshi kenan haihuwa,
ta shafa cikinta tace baby boy zan haifa maka alhj a lokacin ne zan nuna karfin ikona a gidanka,,
duk suka kwashe da dariya evelyn tace shegiya a ina kika san baby boy zaki haifa, oyiza tace bansani ba amma dat’s wat I want kuma zan samu kinsan ni duk abinda nake so sai na samu, suka kara kwashewa da dariya suka cigaba da hira har dare ya raba sannan sukayi bacci oyiza batai maganar sallar magrib da isha ba,
wa ma yasani ko tayi na safe da rana ohooo……

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:33] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣1⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Tun daga ranar suwaiba ta samu gurin zuwa su zauna suyita hira suna shewa suna kulle kullensu dan ta kuntatawa zeenatu, anan suwaiba ke yini In ba ranar girkinta bane,
ko kallon zeenatu ta daina yi, saboda ita a ganinta tayi kawa wacce zata ci arziki da ita kamar yadda ma’u ke ci da zeenatu,
(bata san bomb ta samu a madadin kawa ba)..

Watansu uku da aure oyiza bata fara nuna komai na halin tsafinta ba,
sai dai abinda ke bawa alhj basheer mamaki game da ita shine rashin sallarta, ko ya matsa mata tayi sallah to fa zata san yadda tayi ta zille dan baza tayi ba,
gurin zeenatu kuwa mugun kyankyamin cin abincin oyiza takeyi saboda sam bata yarda da musuluncinta ba, ko sun haďu a dinning ana cin abinci sai tace ita yanxu abinci mai nauyi bata mata cikinta yakeyi,,

a cikin wannan lokacin ne oyiza ta fara laulayi mai zafin gaske,
komai bata iya ci, haka ta tsani kamshin gidan gaba ďaya, tunda alhj basheer yasan ciki ne makale jikin oyiza shikenan duk wani kula da soyayya ta duniya ya ďauka ya daura mata,
babu dama zeenatu tayi abu in oyiza tace bata son kamshin shi to fa shikenan zai hauta da faďa sosai kamar tababbe,
suwaiba ce ke shigowa ta kula da ita suyita yada habaici dan zeenatu taji haushi, duk da zeenatu na jin haushin abin amma sai ta danne ta dinga tambayar oyiza ko akwai abin da takeso, ko kallonta oyiza batayi bare ta bata amsa,
abubuwa suka hadu sukayi ma zeenatu yawa, gashi sam mijinta ya juya akalarshi gurin kula da oyiza a cewarshi,
gurin Ma’u da amaryar da Alhj bara’u yayi kadai zeenatu ke samun sauki,

Kayan baby babu wanda alhj basheer bai siyo ba a nan nigeria da waje, kuma duk kayan maza ya siya dan a scaninng an tabbatar mishi namiji ne, itama chummy ta tabbatar mata namiji zata haifa, gaba daya oyiza ta gama wasa wukarta dan ta gama hada plan din yadda zata mallake gidan da duk wasu kadarori na alhj basheer,

Cikin oyiza ya kusa wata tara alhj basheer ya ďauketa suka tafi india acewarshi zasu fi samun kula ita da babynshi,
tafiyarsu ita tasa zeenatu tasamu sauki take bacci da adduointa cikin kwanciyar hankali, da rana su ma’u da Abida amaryar Alhj bara’u su shigo su ďebe mata kewa da bata shawarwari duk da Abida itama ba isashshen lafiya gareta ba saboda cikin dake makale jikinta na wata hudu,

A daren ranar talata ta idar da sallar tana shirin kwanciya taji ringing din waya, daukar wayar tayi taga alhj basheer ta dauka cikin mamaki dan rabonshi da ya kirata har ta manta,
sallama ta mishi ya amsa murya babu walwala tace ya mai jiki, yace da sauki ta sauka lafiya,
zeenatu ta washe baki tace Allah ya raya ya kuma bata lafiya, me muka samu,
kukan da oyiza ke yi ya hana shi bata amsa, kuka takeyi sosai tana fadin ya za’ayi ace ya’ mace ta haifa,
tsawa ya daka mata yace to ubanwa kike tunanin ya canza miki, ko wannan din ke kika bawa kanki,
ki rufe min baki kar ranki ya baci,
zeenatu ta kashe wayar da sauri ta hau gado ta dukunkune (nidai bansan me ke ranta ba a wannan lokacin, farin ciki ne ko kuma tausayin oyiza,, masu kishiya su bamu amsa plss..)..

Satinsu biyu a india suka dawo gida cikin koshin lafiya,,
tun acan ya raďa mata sunan mahaifiyar oyiza wato Salamatu (ummu Salma) tunda suka dawo makota ke shigowa yi mata barka, suwaiba sai tausarta takeyi akan gara ita tana haihuwa ba juya bace,
wannan kalaman na suwaiba suna matukar sosa ran zeenatu su ke sata kuka a kullum dare da rana tana rokon Allah akan ya bata farin cikin rayuwa itama,
dan haihuwa farin cikin rayuwa ne, in ka haihu ka wuce bakin cikin duniya da lahira,
ya Allah ka azurta wadanda basu haihu ba da ya’ya masu albarka cikin gaggawarka bata shaidan ba,
wadanda suke dashi kuma Allah ka shiryar mana kuma ka tayamu raino ameen thumma ameen…..

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣2⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Shekarar ummu salma uku, in ka ganta sak uwarta gata katuwa kamar renon agric, tana matukar samun kulawa gurin mahaifinta dan ba kananan kudi yake kashe mata ba,
a wadannan shekarun banda karfin imani da salatin annabi da tuni zuciyar zeenatu ta buga saboda ko kallo kwakwkwara tayi ma ummu salma to fah zata fashe da kuka ta dinga nunata, shi kuwa alhaji basheer babu bincike babu komai zai hauta masifa wani lokaci harda gorin haihuwa,
zeenatu sam ta kasa gane kan mijinta saboda kullum alamuranshi kara tabarbarewa sukeyi sam babu sauki a tare dashi game da ita dan ko hanyar dakinta baya bi, ta ma manta rabon da su kebe tare a matsayin mata da miji,

Oyiza kuwa yanzu burinta ta samu ciki amma kafin ta samu sai ta shirya tsaff saboda wannan karan bazata taba yin sakacin haihuwar ya mace ba, sai kace ita zata bawa kanta haihuwar,,
( kaii Rashin ilimin addini shine babbar cuta a rayuwar dan adam)

A cikin kwanakin kullum dare suna gurin meeting duk dan saboda ta samu haihuwar ďa namiji, chummy ce ta kalleta bayan ta gama duk abinda zatayi na tsafi, tace oyee zaki haifi ďa namiji amma sai kin bamu jinin yaro karami namiji kar ya wuce 2yrs,
oyiza ta dafe kanta tana tunanin inda zata samu ďa namiji, chummy tace ki kokarta oyee wannan bazai miki wahala ba in kikayi la’akari da yanzu iyaye na sakin yan 1 nd half year a titi da sunan wasa,, sweet kadai zaki bawa yaro shikenan,,,
kije ki kawo zuwa jibi sai muyi aiki mu gama cikin satin nan..

Munafurci dodo ne tabbas mai shi ya kan ci,,
Oyiza ce zaune a tsakar gida tana kallon salma na wasa cikin motarta da a kiyasi zata kai 350k dan har petur ana zuba mata ta fita yawo da ita cikin unguwa,
suwaiba ce ta shigo rike da Abulbait tana ma ummu wasa,
zama tayi a kasa kusa da kafar oyiza ta fara mata kirari, nan da nan oyiza ta saki fuska suna hira tana bin Abulbait da kallo,
oyiza ta kalli suwaiba tace wai ni ko yanzu abul ya kai shekara uku, suwaiba tayi dariya tace wane uku, shekararshi 1 da wata takwas,
oyiza ta haďiye miyau ta shafa kanshi tace naga yayi saurin girma ne, suwaiba cike da murnar an yabi ďanta tace a hakan, ay ko ni ganinshi nakeyi a motse kamar fara, oyiza tace aiko ya girma wallhy bari in bashi sweet kema akwai wata yar kyautar da zan miki, suwaiba cikin murna ta mike tana godiya ta bi bayan oyiza jiki na rawa,
dubu ashirin oyiza ta bata tace ta kara jari sannan ta bare sweet ta bawa Abulbait tace shanye kar ka bawa kowa kaji,
bakin suwaiba ya kasa rufuwa tanata godiya kamar wacce akayi ma kyautar aljanna,
oyiza tace haba ba komai ay zaman tare ya wuce komai nima kin min abinda ya fi wannan,
har gate ta raka suwaiba tana kallon Abulbait saida ya shanye tass sannan ta juya gida,

Suwaiba da rawa ta shiga gida tanata ďaga kuďin sama tana nunawa ma’u dake ma Asiya yar Abida kitso, rawa takeyi tana habaici wai wata saidai bauta amma bata samun kudi, kullum aikinta renon yayan da ba nata ba daga a bata ragowar abinci sai a bata na batarwa,
Ma’u ko kallonta batayi ba ta karasa ma asiya kitso tayi mata wanka ta bata abinci ta goyata kafin mamanta ta dawo daga gurin aiki,,,

Tun bayan isha’i Abulbait ke kakarin amai kamar zai amayar da yayan hanjinshi,
jike jike suwaiba ke tayi mishi tana bashi amma ina amai yaki tsayawa,
kudin da oyiza ta bata ta kalla a zuciyarta tace nasan yanzu in nace zan kaishi asibiti zan kashe fin dubu biyu, ta maxa ta mayar dasu tace inaa a gida zaka zauna bari in jiķa maka tazargade dan da gani aman hakori ne,
tashi tayi tana bincika tazargade bata gani ba, ta duba ko ina na dakin amma bata ganshi ba kuma tasan tana dashi ko dazu ta ganshi,
mikewa tayi ta fita da gudu ta shiga gurin hajja dan bata rabo dashi, hajja ta dubo ta mika mata tace Allah ya bashi lafiya, tace ameen ta fita da gudu,
tana shiga ďaki ta tarar da gawarshi bakinshi duk ya baci da jini,
wani irin ihu ta saki tana jijjigashi tana kiran sunanshi, da gudu hajja da ma’u suka shigo cikin dakin, ganin Abulbait ya daga musu hankali hajja ta daukeshi tana dubashi ko da sauran numfashi, girgiza kanta tayi tace saidai kiyi hakuri suwaiba Allah ya karbi abinshi, ta kara sa ihu tana kuka tana birgima kamar tababbiya, dakyar aka lallasheta tayi shuru akayi mishi wanka aka suturceshi malam atiku ya daukeshi ya kaishi dakinshi yayi kwanan keso acan…

Aiki sosai chummy takeyi ma oyiza akan ta samu cikin ďa namiji,
tace mata ta nesanci alhj basheer har tsawon kwana uku, a ranar na hudun ne zata bata magani sai tasa ya kusance ta,
haka kuwa akayi oyiza ta kauracewa shimfidar alhj basheer gashi mabukaci gashi kuma ta hanashi kusantar zeenatu, abin na damunshi amma haka ya daure dan kar ya bata mata rai..

Suna zaune a kofar gidanshi shi da alhj bara’u suna hirar rayuwa, alhj bara’u ya tuno da wani tsumi a motarshi ya shiga ya dakko ya mikawa alhj basheer daya, alhj basheer yace na menene wannan, alhj bara’u yayi dariya yace goggo ta aikomin shi daga daura maganin basir ne,
alhj basheer ya fara sha yace lallai wannan irin bauri haka da basu sa zuma ba dakyar zai shawu,
sai gurin sha ďaya suka rabu kowa ya shiga gidanshi,
a parlor ya tarar da oyiza cikin wata matsiyaciyar shiga mai tada sha’awa, karasowa yayi kusa da ita ya zauna,
matsawa tayi sosai tace meye haka kuma, idonshi yayi ja yace ki taimakeni safiyya,
, tayi tsaki ta mike tace in taimakeka akan me, nifa banason jaraba na fada maka kayi min hakuri na tsawon 3dys jibi ne fa
, ni banason gajen hakuri walhy, ta wuce ciki ya bita da sauri tayi maza tasa keyy ta datse dakin,,
ya koma ya zauna cikin tashin hankali,
mararshi yaji tana murďa mishi sosai ya rasa yadda zaiyi sai juyi yakeyi,
kamar an mintsileshi ya mike rike da mararshi ya wuce dakin zeenatu, tana zaune tana addua tana kai kukanta gurin Allah ya murda kofar ya shigo,
waigowa tayi ta kalleshi ta mike da sauri saboda yadda taga idonshi yayi ja, karasawa tayi kusa dashi cikin damuwa ta rikeshi tace lafy me ya sameka,
kankameta yayi yana fitar da wani wahalallen numfashi yace ki taimakeni zeenatu, dan Allah ki taimakeni in sauke nauyin da rataya a wuyana akanki saboda ina cikin mawuyacin hali,
ta rikeshi sosai itama tace babu taimako tsakanin mata da miji, duk lokacin da kake bukatata a shirye nake in amsa kiranka,
ya sauke ajiyar zuciya yace Allah ya miki albarka zeenatu,
nan suka shiga faranta ran junansu,
tabbas zuciyarshi tayi missing zeenatu ta ko wane bangare amma ya rasa meye ya tokare wani shashi nata har baya iya kyautata mata,
Alhj basheer ya ji dadin wannan daren saboda yayi gamsuwar da ya dade baiyi ba,
ga zeenatu ma haka abin yake domin ganin daren tayi kamar duk yafi sauran darurruka amma ta dangantashi da missing din mijinta da tayi,
sai da yayi wanka a dakinta yana sa mata albarka sannan ya fita cikin tsananin ciwon kan da yarasa dalilinshi,
a daren ranar Alhj basheer da zazzabi mai zafi ya kwana saukinta ma ya sauke wani nauyin, sai kawai yaji da na zazzabin…..

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣3⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Satin Alhj basheer daya yana zazzabi har saida yasha allurai, zeenatu ke kula dashi dan oyiza na fushi dashi tun da ta ganshi ya fito daga dakin zeenatu a ranar,
Ga kuma maganin da chummy ta bata ya wuce ka’idar amfaninshi saboda ciwon da yakeyi,
a ranar da taga alamun yaji sauki ne ta fara neman hanyar da zatayi amfani da maganin har ya kusanceta,
haka kuwa akayi sai da tasan duk yadda tayi da kissa da yaudara har ya kusanceta,,
oyiza ta kasance cikin farin ciki a wannan dare dan gani take ma har ta haifi ďan komai ya dawo under her…

4mnts ltr

Zeenatu ce zaune suna hirah da Abida dake da tsohon ciki,
Abida ta kalli zeenatu tace matar nan fa ni ban gane miki ba, tun wata biyu da suka wuce kika wani canza kikayi fresh, yanzu kuma gaba daya kin cika famm sai kace me ciki,
zeenatu ta shafa cikinta tace sai kace yin cikin wasan yara ne, ko sign fa ban taba ji ba,
Abida tace ji ki da wata magana, akwai cikin da haka yake ba’a taba ganeshi sai in ya fito da kanshi kuma wallhy alamu sun nuna cikin nan ya dan dade a jikinki, zeenatu tayi dariya sosai tace to doctr Abida naji bayaninki, dama ana jini in ana da ciki,
Abida tace nawa akayi kedai ina zuwa, gida ta shiga ta dauko ragowar “pt strip” din da tayi amfani dashi farkon cikinta sannan ta dawo ta bata kwalba tace taje tayi fitsari,
zeenatu ta mike tana dariya tace Abida kenan wahala kawai zaki bawa kanki,
Abida tace tunda ba ke zaki wahala ba meye na compln, ta yi dariya hade da shiga bayi tayi fitsari ta fito ta mika mata kwalbar,

Wani irin ihun murna Abida tayi da taga postive, ta kalli zeenatu tace wallhy nayi tunanin hakan, wayyo dadi kasheni, zeenatu a ruďe ta shafa cikinta tace kina nufin ciki gareni, u mean akwai halitta mai rai a cikina,
Abida tace sosai ma kuwa in baki yarda ki shirya gobe kafin na tafi karbar hutun haihuwa muje asibiti, zeenatu idonta ya ciko da kwallar farin ciki tace Abida bansan irin farin cikin da zanyi ba in har wannan maganar taki ta tabbata,
Allah ka tabbatar da wannan maganar kasa Abida ta faďi a bakin mala’iku,
Abida tace ameen zeenah,
tashi zeenah tayi ta shige ďaki ta cire rigarta tana kallon kanta a mudubi, kirjinta ne kadai ya ciko amma mararta a shafe take, maida rigarta tayi tana adduar Allah ya tabbatar da wannan abun,,

Washe gari tun asuba ta gama shiri dama bata rintsa ba tana ta addua,
karfe takwass dai2 ta fito suka wuce dan mai gidan baya gari sunyi tafiya shi da oyiza mai laulayi wai batasan warin gidan da nigeriar gaba ďaya, (samun guri),
AKTH suka nufa, basu wani sha wahala ba saboda akwai kawar Abida a asibitin,
test din jini akayi mata aka tabbatar da tana da ciki,
scanning ppr aka bata suka je tayi scanning inda ya nuna makalallen ciki na wata hudu, ‘”HAMDAN KASIRAN DAYYIBAN MUBARAKAN FIHI,”” abinda zeenatu ke fadi kenan hade da kuka, saida suka gama komai a asibitin Abida ta maidata gida cike da murna ta tsaya tayi wa su Ma’u albishir sannan ta wuce aiki,
Hajja da ma’u a lokacin suka shigo taya ta murna,
har ta ďaga waya zata kira alhj basheer ta fada mishi sai wata zuciyar ta haneta, haka gida ma so takeyi ta musu surprise,

Kula sosai take bawa cikinta da ya kai wata biyar har ta fara zuwa awo alhj basheer da oyiza basu dawo ba, gidan Abida take zama suyi hirarsu lokacin ta haifi ďanta namiji mai suna JABEER,

Cikin zeenatu na wata bakwai su oyiza suka dawo itama da nata cikin watanshi bakwai, fitowa tayi cikin hijab tana musu sannu da zuwa,
alhj basheer ne kadai ya amsa babu yabo babu fallasa, ta kalli salma tace ummu ya hanya,
salma tayi banza da ita suka wuce daki ita da mamanta, saida alhj basheer yayi wanka ya huta sannan ya fito cin abinci, zeenatu ce tayi serving dinshi tana mishi hira yana amsawa jefi2, bayan ya gama cin abincin ne ta fara mishi magana cikin hikima,
tace ranka ya dade kudi nakeso,
ya yatsuna fuska yace me zakiyi da kudi, ta sunkuyar da kanta kasa tace siyayya nakeso inyi ma kyautar da Allah ya bani,
cikin rashin fahimta yace ban gane ba, ta daga hijab din jikinta ta dauko hannunshi ta ďaura kan cikinta tace Allah ya azurtani da ciki har na tsawon wata bakwai,
“karaf a kunnen oyiza da ta fito cin abinci,”
fuskar alhj basheer ta kasa boye farin cikin da yake ciki a wannan lokacin, janyota yayi ya zaunar da ita kan jikinshi sam bai kula da oyiza ba, ya kalleta yana shafa cikin da ya dan taso yace da gaske zeenah,
ta gyada mishi kai, yayi murmushin jindadi ji yakeyi kamar wannan ce haihuwar da zaiyi ta fari, yace Allah ya fito min da abinda ke cikin nan kuma yasa namiji— ta maza ta toshe mishi baki tace namiji da mace duk Allah ke hallitarsu,
muyi fatan samun masu albarka shine kawai yallabai,
yaji wani nutsuwa ta ratsashi yace hakane Allah ya bamu masu albarka, “mtswwwwwww” sukaji an ja tsaki mai karfi suka waiga suka ga oyiza tayi gaba tana huci kamar zakanya,
kau da kanshi yayi ya cigaba da kallon cikin zeenatu yace gobe ta shirya suje siyayya da asibiti a kara duba lafiyarta,
sun dade suna hira cikin jin dadi ya ma manta da wata oyiza a rayuwarshi…

Oyiza kuwa tana shiga ďaki ta maida salma ďakinta, ta hau kan buzun tsafinta sai gata ta bayyana gaban “chummy” idonta jawur take fada ma chummy halin da take ciki, chummy tayi iya yinta da duk wasu siddabarun da zatayi tace oyee wannan cikin bazai zube ba, cikin jikinta na tare da kariyar adduoi sosai sai dai ki bari in ta haifeshi sai kisan abun yi,
cikin tashin hankali tace “my lord” to idan ta haifi namiji fa, chummy tace sai kinso ya rayu in ya fito duniya,
oyiza hankalinta ya ďan kwanta tayi sallama da chummy ta bace ta nufi gida….

Ciwo takeji sosai amma hakan bai hanata ci gaba da aikinta da tasbihi a bakinta ba,
wani irin Murďawa mararta tayi ta tsuguna da sauri tana faďin “YA HAYYU YA KAYYUMU BI RAHMATIKHA ASTAGITHU ASLIHLI SHA’ANI KULLAHU WALA TAKILNI ILA NAFSEE ĎARFATU AYNUN” da dai taga abun kamar gaba yakeyi ta mike tayi hanyar parlo tana maimaita adduoi a bakinta,
oyiza na zaune tana cin abinci zeenatu ta shigo da kyar, tace dan Allah safiya ki taimak— ta kasa karasawa saboda wani irin nishi mai karfi da yazo mata,
oyiza tayi tsaki ta juya tana adduar Allah yasa ki mutu ke da ďan cikinki,
zeenatu kuka sosai takeyi ga wani ruwa dake bin kafarta, sallamar Abida taji nan taji kamar an sauke mata zafin wani bangaran, da sauri Abida ta karaso ta ajiye jabeer tace haba zeenatu ay da sai ki kirani a waya, zeenatu ta runtse bakinta ta rike hannun Abida dake kiran Ma’u a waya,
da sauri ma’u ta shigo suka kamata,
Abida ta kalli oyiza tace dadin abin nakuda Allah bai ďauke wa uban kowa ba, kowacce yar iska zata dandani nata in lokaci yazo,
oyiza ta harzuka matuka ta mike tana bala’i suka fita sukayi banza da ita, drivrn gidan ya karaso da sauri suka wuce asibiti,
Suna shiga Allah ya taimaketa batayi wata doguwar nakuda ba ta haifo ďanta namiji kyakykyawa mai kama da iyayenshi,
likitoci suka shirya baby suka kimtsa mamanshi suka kwashe mata jini suka turota dakin hutu, murna a gurin su ma’u ba’a cewa komai, Abida ta kira Alhj basheer tayi mishi albishir,
murnar da yayi a lokacin ba mai faďuwa bace, saida yaje gida ya shirya sannan ya fito zai tafi asibitin, oyiza ta fito rike da kugu tace ina zaka je, ya fadada fara’arshi yace hospital zeenatu ta haihu,
oyiza ta kauda kanta tace Allah ya raya, yace ameen, har yayi gaba, ta tuna ta kwala mishi kira ya tsaya tace me ta haifa, yace baby boy,
wani irin murdawa mararta tayi cikin ruďewa tace namiji kenan ta haifa,, yace eh mana,
ya shiga mota cikin farin ciki ya wuce ya barta tsaye kamar an dasata hawaye masu zafi suna kwaranya a idonta….

ayshakurah.mywapblog.com

Mrs tijjani shattima…..
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣4⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Ciki ta juya tana tafiya da kyar, ga bakin ciki ga kullewar mara,
a gado ta kwanta tana kuka sosai kamar wacce akayi ma mutuwa,
sai da tayi kuka ma’ishi sannan tayi shuru da tunanin itama fa cikin gareta kuma chummy ta bata assurance din namiji zata haifa,
yanzu kawai abinda ya rage mata shine tasan yadda zatayi ta kashe jaririn nan tun kafin ya girma yasan kanshi, da wannan tunanin zuciyarta tayi wasai ta mike ta shiga wanka..

Kwanan zeenatu huďu da haihuwa kullum da daddare alhj basheer na makale a ďakinsu, duk wanda ya ganshi a kwanakin yasan farin ciki ne cike da zuciyarshi, haka mai jego na samun kulawa daga gurin makotanta da kanwar kakarsu Yadikko da tazo daga cameroon,
a ranar da suka cika kwana shida da yamma sunyi wanka ita da baby yadikko ta debo rushi tasa garin “habbatis sauda” a ciki tana sa hannunta a hayakin in ya dau zafi saita daura a kan cibiya da marar jaririn tana karanto adduoi tana tofa mishi, juyawa oyiza tayi da sauri da ta tunkaro dakin da wasu magungunan tsafinta wanda chummy tace in har ta shafi babyn da maganin a hannunta to tabbas jininshi zai kafe ya mutu,
jin hayakin tayi kamar zai tafi da ranta, ta shiga daki da sauri ta datso kofa tana haki haďe da kakarin amai, ta dade sosai a haka kafin wani irin murdaddan ciwon mara ya dawo da ita daga duniyar azabar shakar hayakin habbatis sauda,
ciwon da oyiza taji ne yasata sakin ihu tana karawa kamar zararriya, babu wanda yajita dan su yadikko suna can suna hira dasu hajja da suka shigo a lokacin sunata preparation din suna washe gari,

sai da ta galabaita sosai tana ihu tana faďin “ohh my lord” “chummy wr are u,”
Ma’u ce ta fara jin ihun saboda zagayawa baya da tayi dan kwaso shanyar baby, da sauri ta zagayo ta faďa musu suka mike sukayi dakinta suka murďa sunata bugawa yaki buduwa saboda tasa key,
kiran alhj basheer zeenatu tayi lokacin har oyiza ta suma saboda azaba,
cikin yan dakiku ya baro inda yake ya dawo gida ya dauko spare key ya bude dakinta,
kwance cikin jini suka sameta, da sauri suka karasa suka kamata suka sata a mota sai asibiti,
dakin theater aka wuce da oyiza, cikin gaggawa likitoci suka shiga ceton ransu ita da babyn,
cikin nasara suka samu fitowa da baby mai kyan gaske gata katuwa dan da sukayi wghn dinta ta kai 6.2kg, doctor yayi ma oyiza “PS” nurses suka shirya baby suka fito ma alhj basheer da ita, cikin murna ya karbeta yana kallonta yana mata addua,
ita kuwa oyiza sai can cikin dare ta farfado tana ihun kuka dakyar,,,,
wata nurse ce a gefenta da yadikko suka matso suka riketa suna fadin sannu,
ta kwanta lamoo tana shafa cikinta dakyar tace na haihu ne, yadikko ta daga mata kai tace eh kin haihu, tayi murmushin da bata san ya fito ba saboda azabar ciwo tace ina yaron yake, yadikko ta fito da babyn cikin gadon jarirai tace gata nan, oyiza cikin rashin fahimta ta gwalo dasassun idanuwanta tace gashi nan ko gata nan,
yadikko tace gata nan dai inaga bakiji da kyau bane,
oyiza ta waigo a hankali ta kalli babyn ta juyar da kanta tana kuka sosai tace “why chummy” why? Meyasa zan haifi mace, kin manta alkawarin da kikayi min,
meyasa zeenatu zata haifi namiji ni mace,
meyasa zanyita haihuwar mata, magana oyiza takeyi cikin zaucewa tama manta da wata yadikko a kusa da ita, saida tayi kuka sosai nurse tazo tayi mata allura sannan ta samu bacci,
Yadikko komawa tayi ta zauna tana kallon oyiza tana mamakin furucinta, tabbas sai sun mike tsaye akan zeenatu da ďanta saboda wannan furucin na oyiza ba karamin ďaga hankalin yadikko yayi ba, ‘”CHUMMY” kalmar da ta dinga maimaitawa kenan a ranta, wacece kuma chummy? tambayar da yadikko tayi ta ma kanta kenan ta kasa samo amsa daga karshe ta mike ta shiga tayi alwala ta fara nafilar nemawa jikokinta tsari daga sharrin makiya…

Ranar suna jariri yaci suna AFFAN, anyi taron suna na gani na fada mutane sunzo sosai tayasu murna, faďin farin cikin da duka su biyun suke ciki bata lokaci ne domin bazai taba misaltuwa ba, oyiza kuwa tana can cikin bakin ciki dan tunda ta farka anyi anyi ta bawa baby nono taki, kuka kawai takeyi tana tufka da warwara, maimakon isharar da Allah ya nuna mata yasa ta saduda tasan babu wani mai yi sai shi taki ta gane, sam batayi gv up ba sai ma wani karin mugunta da zuciyarta ta naďo, babu abinda yafi daga mata hankali sai cewa da doctor yayi mahaifarta bazata kara rike kwai ba saboda ta samu gagarumar matsala,
a wannan lokcin likitoci sunga bori saboda tsine musu kawai takeyi tana zaginsu, dakyar alhj basheer ya lallabata da kalamai masu kwantar da hankali,,,

Kwananta hudu a asibiti aka sallameta ta dawo gida da muggan kudirai a cikin ranta, a zuciyarta tace wannan karan ita zata zama shaidaniyar kanta dan taga yanzu aikin chummy baya tafiya mata yadda ya kamata,
haka ta cigaba da jinyar jikinta da kula da yarta wacce taci suna FAREEDAH,

oyiza kullum idonta na kan side din zeenatu taga ko sun bar Affan shi kaďai amma bata samun wannan damar saboda yadda yadikko ke manne dashi a ko dayaushe,
sai da yadikko tayi wata biyu a gidan tana kula da zeenatu,
tun ana saura sati ďaya ta tafi kullum dare bata aikin da ya wuce yi ma zeenatu faďa akan ta kula da kanta da ďanta da kuma adduoi,
zeenatu saidai tayi dariya dan abin na yadikko ya zame mata kamar waka tunda kullum sai anyi maimaicinshi..

Cont 14

Salma ta kalli mahaifiyarta tace mummy kika ce wannan nawa wannan na affan ko,
oyiza tace a’a wannan ne naki, ki kula fa sosai, ta gyaďa kanta ta fita da gudu fareeda na binta a baya,
Affan zaune suna bin karatun lptp din yara na “alifun ba’un” shi da jabeer lokacin shekararsu biyu da rabi shi da fareeda ita kuma salma ta kusa 6, dafashi salma tayi yayi saurin ďago kanshi, a razane ya matsa dan mugun tsoronta yake ji saboda dukkan da take mishi,
zama tayi kusa dashi ta kara duba ice cream din dan ta tabbatar da wanda mummy tace na affan din ne, mika mishi tayi tana murmushi tace gashi inji mummy,
farida cikin gwaranci tace “wanshan ne naci,” salma ta harareta tace wannan ne, farida ta dage akan dayan ne saboda tafi salma wayau, kuka ta fashe dashi da taga alamar salma bazata bashi wanda mummyn tace ta bashi ba,
da sauri zeenatu ta fito tace lafiya me aka miki farida,
salma tace ice cream mummy ta bani in kawo ma affan kuma wannan ne nashi wai ita dole sai dai in bashi Nawa, farida cikin kuka tace “wanshan ne mummy ta kaya mici sugar” kuma “cha kiji” ,
gaban zeenatu ya faďi sosai tace to duk bari in raba muku gardama ke salma je ki kara tambayota wanne ne na affan din,
da gudu suka fita suka bar zeenatu cikin jimamin maganar farida,
innalillahi kadai take fada tana kara rokon Allah ya tsare mata ďanta da a kullum sai an kawo mishi harin kisa tun yana karaminshi,
shafa kansu tayi shi da jabeer tace ma jabeer tashi kuje gidan Antie Ma’u kafin umminka ta dawo kaji,
ya gyada mata kai ya kama hannun affan dan yafi affan wayau, har sun fita ta tuna da kar su hadu da su salma ta bashi ice cream din yasha,
binsu tayi da sauri tace ku dawo bari Gaje ta dawo daga kasuwa sai ta kaiku kunji, ta kamo hannunsu suka shigo ciki dai2 lokacin su salma suka dawo da ice cream daya suka ce gashi wannan ne nashi,
zeenatu ta amsa tace to kuce ya gode sosai, salma tace mummy tace yasha a gaban mu sai mu tafi, zeenatu tace to an gama yaran kirki bari in raba musu shi da jabeer,
ta mike ta shiga kitchen, Allah ya taimaketa akwai nashi na jiya a fridge, daukowa tayi ta raba musu shi da jabeer ta fito ta mika musu tace gashi maza ku sha ku tafi gidan anty ma’u wanda bai shanye ba a gida zai zauna, suka karba suka fara rige rigen sha,
salma da farida suka fita da gudu tun kafin su kai ďaki suke rige rigen faďin mummy yasha,
suna karasawa ta toshe bakinsu tace ku rufemin baki ku wuce ku bani guri, suka wuce ciki suka dau nasu suna sha,
zama oyiza tayi cikin farin ciki dan tasan yau babu makawa aikinta yaci tunda har sun tabbatar mata yasha,,
har bayan isha tana kasa kunne taji ihu, amma shuru takeji hankalinta ya fara tashi,,
karfe 9 lokacin taji dawowar alhj basheer ta mike ta fito ita da yaranta,
zaune ta taddashi affan na kan ruwan cikinshi suna hira suna kyalkyace dariya kamar da sa’anshi yakeyi,
wani abu ne ya tokare mata wuya wanda ta kasa controlling dinshi har ya kaita ga jan razanannan tsaki, taja hannun farida dake kokarin zuwa gurin babanta tace dalla wuce kuje ďaki, an faďa muku ta taku yakeyi, ai ku muna ya’ya ne a gidan nan amma ba ya’ya ba,
alhj basheer ya dago da sauri yace haba safiya,
me yasa kike faďin haka, da affan da su salma duk daya ne agurina,
da karfi tace biyu ne, karka kara cewa ďaya ne, ka riga ka nuna musu tun yanzu basu da wata daraja a idonka saboda sun zo a ya’ya mata,
nan ta shiga masifa kamar zata tsaga gidan, bakin ciki ne dankare a zuciyarta saboda yadda in tayi abu akan affan baya kamashi,
alhj basheer bai kalleta ba ya kara rungume affan da ya tsorata ya mike ya wuce ciki ya barta anan tana bala’i……

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣5⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a gidan alhj basheer,
kullum da sabon makirci da muguntar da oyiza ke fitowa dashi na tsafi da kuma na magunguna amma dayake rayuwarmu da mutuwarmu tana gurin rabbil izzati babu abinda ya faru da zeenatu da affan duk da wani lokacin in tayi tana cin nasara saboda ance tsafi gaskiyar maishi sai dai duk tsafin mutum in har ka dogara da Allah to ko ya kamaka na ďan lokaci ne zai sake ka,
a yan shekarun da suka wuce oyiza ta kara karfi cikin kungiyar asiri dan yanzu haka tana cikin kungiyoyi masu karfin gaske guda hudu, zeenatu kuwa addua takeyi ba dare ba rana akan Allah ya kare su ita ďanta ya ďaurasu akan makiyansu…

Affan da jabeer zaune ďakin hajja suna cin danwake,
jabeer ya kalli affan yace kaii yau banga su anty salma a skool ba, affan ya juyar da kanshi yace ohoo musu wai dan daddy yace shi zai kaini zana C.E exams su su jira driver shine sukayi fushi mummynsu tace bazasu ba,
Hajja dake gefe tana saka suwaitar kulu tace ca nakeyi ajinku daya da farida kenan bata rubuta jarabawar ba,
jabeer yayi dariyar shakiyanci yace dondi kenan hajja, ay anyi mata repeating yanzu p4 take,
Affan yace p4 din ma da ya aka bari ta kai,
ni ay ban taba ganin wacce brain dinta baya ďaukar karatu irin farida ba cewar jabeer,
Affan yace tabb ay wallhy gara farida a haka, dan anty salma knws nottn banda mugunta,
ma’u ta ďeko dakin hajja da tsohon cikinta da kullum suke adduar Allah yasa zaunanne ne tace ashe baku wuce gida ba, na ďauka ma kun tsufa a gida,
jabeer yace eh “Mama” sunan da yake kiranta dashi kenan saboda a gurinta ya girma bacci kadai ke maidashi gida”, yanzu zamu tafi muna nan muna cin ďanwaken tsohuwa,
Ma’u ta juya tace ai ya kamata kuje gida ku faďa musu kun gama jarabawar sai kuma a ďan fita yawo tunda ba mata bane ku,
suka rufe kwanon danwaken suka mike sukayi sallama da hajja da ma’u,, sun kusa da kofar fita kausar yar suwaiba tana rarrafe a tsakar gida tsirara ta mike ta rike wani abu tana dabo ta fetso kashi saura kaďan ya taba wandon Affan,
da gudu suka fita jabeer na mishi dariya harda rike ciki yana tayashi dubawa ko ya taba wandonshi, dakyar ya karasa gida yana masifa ya wuce bayi saida yayi wanka ya canza kaya sannan ya fito ya shiga ďakin mahaifiyarshi,
zaune ya sameta tana waya ya zauna kusa da ita, sai da ta gama wayar ta juyo ta kalleshi tana murmushi tace daga ina haka,
yace gidan maman jabeer, tace ya jarabawar kun gama ko, yace mun gama umma sai dai ayi mana adduar samun nasara,
tace addua kullum yinta akeyi Affan, saidai a ďaura, ni dai ina kara jaddada maka ka rike ibada da karatun qur’ani da tsoron Allah wadannan abubuwan in ka rikesu sun isheka duniya da lahira,
yace in shaa Allah umma, Allah ya kara mana karfin imani, tace ameen,
ya mike zai fita kenan Asiya ta shigo da sauri,
tace ina wuni umma, zeenatu tace lfy lau dan asy, ya na ganki haka,
tace ummi ce tace in zo in fada miki anty ma’u ta haihu yanzun nan tana can gidan ma,
da sauri zeenatu ta mike cike da murna tace me muka samu, asiya tace nima ban sani ba,
ta dauko hijab ďinta suka fita da sauri a ranta tana adduar Allah yasa zaunanne ne abin da ta haifa,
tun kafin su shiga ciki kukan yarinyar ke musu kuwwa cikin kunne,
kuka takeyi irin na jarirai da iya karfinta wata nurse a unguwar tana gyarata,
Affan a kofar gida ya tsaya dan yana tsoron ya shiga ya kara arba da kausar dan bai sani ba ko wannan karan a jikinshi zatayi kashin,

A cikin gida kuwa murna sukeyi lokacin an gama kimtsasu anyi ma mai jego allura tana kwance tana hutawa,
duk makota anata shigowa tayata murna banda suwaiba da tace meye na barka a gurin gawa, mudai je zuwa nan da anjima itama zata bi layin yan uwanta su cike su bakwai,
karaf wannan furucin na suwaiba ya shiga kunnen jabeer, hararta yayi ya mikama mamanshi babyn suka fita shida Asiya, a kofar gida suka hadu da affan suka wuce gidansu..

Anyi suna dai2 na masu rufin asiri,
mai jego ta samu kaya da kudi masu yawan gaske haka mahaifinta ya samu kudi sosai haihuwar tazo mishi da goshi, jaririya taci sunan Hajja “Hajara” Abida tace a dinga kiranta da “AFEEYAH”, suwaiba kuwa bakin ciki kamar zai kasheta da taga har kwana bakwai jinjira na raye ga kaya da kudi da uwarta ta samu kamar za’a bude shago dasu, sam ta kasa boye bakin cikinta har saida sukayi fada da Abida ta gaggaya mata bakaken maganganun da yasata shigewa ďaki ba shiri dan Abida ba kanwar lasa bace itama…

Tun daga lokacin kullum sai suwaiba ta kasa kunne ko zataji kururwar mutuwar jinjinra amma shuru takeji ga jinjira har ta wuce wata bakwai kullum cikin koshin lafiya,
Afeeya ta taso cikin kulawar mahaifiyarta da kakarta hajja, yarinyar duk wanda ya ganta sai yayi sha’awarta saboda kullum a tsaftace take kan nan nata baya rabo da kitso da ribbons saboda tana da yalwar gashi, gata yar lutuya goyonta gunin ban sha’awa, saidai fa akwai azabar kuka da masifaffen kwuiya, banda mamarta da hajja babu wanda take yarda ya ďauketa a duniya sai jabeer, shima dan tana ganinshi kullum a dakinsu kuma yana fita da ita yawo,
sam bata yarda da affan dan ko ya miko hannu zai ďauketa in ta soma tsala ihu bata taba yin shuru har sai taga baya gurin, wannan dalilin yasa kullum ya shiga gidan sai yasan yadda akayi yasa ta kuka ta hanyar daukanta ta karfin tsiya,,
Afeeya na da shekara biyu jabeer yasa babanshi yasata a makarantar da suke zuwa lokacin suna js2, dakyar ma’u ta yarda dan gani takeyi kamar wata hidimar ta ďaura musu,
tare suke zuwa makaranta in sun dawo ya wuce gidansu da ita sai can yamma yake mayar da ita gida, duk wani kuďin break da ake bawa jabeer akan afeeya yake karewa,
gata sosai takesha gurin yan samarin biyu duk da har lokacin bata cika yarda da affan ba,
salma da farida ba karamin tsanarta sukayi ba, in suna cikin mota ta kallesu sai su sakar mata harara,
turo baki takeyi a tsiwace irin na yara itama ta rama sai tayi lamoo a jikin jabeer ta runtse idonta dan kar su daketa,
haka a skul ko takata yaro yayi bai sani ba ko yafi karfinta sai ta bishi ta rama in ya daketa taje ta faďa ma jabeer, in kuma tafi karfinshi to ta samu nama dan sam bazata raga mishi ba….

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣6⃣ By Aysha Ya’u Kurah

★ bayan shekara 6★

Jabeer ne ya fito daga makarantar (buk) cikin motarshi “vibe pontiac” da L a jikinta saboda har lokacin bai kware sosai ba,
waya sukeyi da Affan da ya tafi karatu egypt wata uku da suka wuce, hira sukeyi sosai cikin jin dadi da kewar juna,
saida yayi parking dai2 skool din su Afeeyah sannan sukayi sallama,
can ya hangota cikin yara suna dambe ita da wata yarinya yara na ihu suna musu waka,
da sauri ya karasa gurin ya raba fadan ya riketa tana kuka saboda yarinyar tafi karfinta karfin hali ne kawai irin nata,
fisge2 ta shiga yi ita dole sai an barta ta buga ma yarinyar dutse,
tsawa jabeer ya daka mata ya rike hannunta da karfi yace wuce mu tafi ko in zaneki a gurin nan,
ta kalleshi cikin mamaki dan bai taba mata magana mai karfi ba bare tsawa, yace baki ji abinda nace bane,
ta saki wani razanannen ihu tana buga kafa tana kuka sosai kamar wacce ake yanka ta,
tsaki yayi ya ďauketa tana tirjewa ya turata cikin mota, Safna kawarta ta miko mishi school bag da L.B dinta yasa aciki ya zagaya ya shiga,
dago kanta tayi tana kuka ta hango wasu yara suna mata gwaloo,
haba nan ta fara kicin kicin bude kofar tana bugawa tana ihu kamar zata tsaga motar,
kashe motar yayi ya janyota jikinshi yana rarrashinta tana zillewa,.
dakyar ya rarrasheta yace ta faďa mishi abin da ya haďa su, kumburo baki tayi tace dukana tayi wai dan ban sani ba na yaga mata littafi shine har da cire min beets din da mama tasa min, kuma taja min gashi da karfi,
murmushi jabeer yayi dan yasan tana sane ta yaga littafin yace banason karya fadamin gaskiya tsokanarki tayi kika yaga mata ko? ta turo baki ta gyaďa kanta, yace nasani ay,
kuma shine dan rashin gaskiya kika fito kuna dambe ko, bana hanaki faďa ba? idonta ya fito waje tace to ay sune suke fara neman fada na,
ya zaunar da ita kan kujera ya tada mota yace munyi faďa yau babu ruwana dake, dama na siyo miki cake kuma na fasa baki,
ta rike mishi hannu tana kuka tace zan daina,
yace bazaki daina ba kullum haka kike faďa, ta kwantar da kanta kan hannunshi tace Allah zan daina gobe, yayi dariya yace to naji in kika kara me zan miki, ta boye fuskarta tana dariya tace hakuri zakayi mana,
ya kwashe da dariya yace yarinyar nan kin raina ni da yawa, yaja motar suka wuce..
Tsayawa yayi ya siyo ma Ma’u dake fama da ciwon ‘koda’ tun wata biyar da suka “fruits da rake” dan shi take yawan sha ance yana wanke infection din ‘koda’, sannan suka wuce gida,
Tun kafin ya kai kofar gidan ya hango cikowar mutane, karasowa yayi jikinshi a mace yayi parking a gefe can ya hango maza sunata alwala ana jimami,
bai bi takan fruits din da ya siyo ba ya dauko schl bag da lunch box din Afeeyah ya kama hannunta zasu shiga ciki, ta dinga waige2 tana cewa yaya jabeer baka dakko ma mama raken ba,.
bai kulata ba ya jata suka shiga ciki, a tsakar gida ya tarar da taron mata cikin hijab kowacce tayi tagumi, dakin Ma’u ya shiga nan ya tarar da tashin hankali,
kallon mutanen dakin yakeyi ya karasa kusa da mamanshi yace ummi me ya faru, ina mama,?
Abida ta share hawayenta ta nuna mishi ma’u kwance cikin likkafani, matsawa kusa da ita yayi da sauri ya bude fuskarta ya fashe da kuka sosai yana kiran sunanta,
Afeeya ta matso kusa dashi jikinta a sanyaye ta rikeshi itama tana kuka, rungumeta yayi sunata kukan da ya kara sa mutanen gurin kuka, Abida cikin kuka tace ya tashi ya wuce gida,
kin tafiya yayi ya haďa Asiya da Afeeya suka wuce gidansu shi kuma ya zauna akayi mata sallah tare dashi aka kaita gidanta na gaskiya,,
mutuwar ma’u ta girgiza jabeer sosai saboda ba karamin shakuwa sukayi ba, ita taci kashin shi tun yana karaminshi har yasan kanshi saboda mahaifiyarshi ba mazauniya bace..

Tun daga lokacin rikon Afeeyah ya koma gurin hajja dama acan take rabin zamanta ko sanda mamanta ke da rai,
jabeer kuwa wata sabuwar kulawa yake bawa Afeeyah wacce take mantar da ita rashin uwa,
gaba ďaya ya daina mata faďa kuma ya hana kowa yi mata faďa,
ko an kawo kararta saidai ya basu hakuri yace ay yarinyace, sosai ya shagwabata, basu rabuwa ko da na kwana ďaya ne in kuwa tafiya ta kamashi in har ya tafi to ranar ba cin abinci babu bacci, wani lokaci ma har ciwo takeyi, shiyasa yake tsoron duk wani abu da zai sa yayi tafiya ya barta,
haka su zeenatu da Abida ba karamin kula sukeyi da ita ba dan sun ďauke mata komai duk da malam atiku shima yana iya kokarinshi yaga ya debe mata kewa, suwaiba kuwa mutuwar ranar ne ya taba ta amma anayin uku shikenan ta sake tama manta da wata ma’u a rayuwarta, ganin Afeeyah da kuma jarabar rashin hakurinta su kadai suke tuna mata da ta taba yin kishiya…

Mrs tijjani shattima..
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣7⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Yar Kyakyawar budurwa ce zaune cikin bakar doguwar riga mai adon jaa a parlon ummi,
duka shekarunta baza su wuce 14 ba amma in ka ganta zaka rantse ta kai 16 saboda kayataccen jikin da makerin yammata ya fara kerashi,
bazan iya fadin kyawun fatarta ba saboda ya zarce misali, ita dai ba fara bace kuma sam bata dauko hanyar bakake ba,
wani irin colour ne mai daukar hankali wanda yake shan gyara da mayuka masu tsada, manyan idanuwanta da ďan hancinta da bai cika tsawo ba su suka kara ma fuskarta kyau, bakinta dan dai2 mai cike da masifar tsiwa,
gefenta Amirah ce yar shekara 11 zaune sun maida hankali kan TV suna kallon series a mbc bollywood,

kwala kiran Amirah ummi tayi zata aiketa gurin zeenatu (umma), Amirah ta fara kunkuni kamar zatayi kuka dan bata so film din ya wuceta,
gwalo Afeeya tayi mata ta cigaba da kallo,
Amirah taja tsaki tace wallhy zan kashe kowa ya huta kuma in gudu da remote din,
Afeeya tace yi hakuri meerah je ki dawo zan baki labari, ki gaisar min da masu suffar samudawa,
ummi na kitchen dariya ta kufce mata da karfi tace su waye kuma masu suffar samudawa,?
Afeeya ta toshe baki tace ummi Amirah ce ta faďa,
Amirah tace nagode Allah da ya banbanta muryata da taki da ba karamin bomb zaki dinga haďa min ba,
Afeeya tace ummi taki tafiya fa tana tsaye tana kallo,
ummi tace to ke amsa kikai kinji yar albarka, kice wai ina gaisheta,
Amirah ta fara rawa tana mata gwaloo, Afeeya tace dan Allah rakani muje,
Amirah tace wallhy ke kadai zaki tafi,
ummi tace bana fa son iskanci in bazaku ba ku bani in shiga da kaina,
Afeeya ta ďaďa ma Amirah duka taja gyalenta ta ďaura kan gashinta da yayi tutsu a tsakiya,

Da bisimillah ta shiga gidan dan Allah yasan ta tsani ganin su fareeda dan basa ga maciji ko kadan,
parlon ta wuce ta dinga sallama taji shuru ta wuce ciki ta murďa kofar dakin umma haďe da sallama, tana sa kai ciki sukayi karo sosai da Affan wayarshi ta faďi kasa,
baya taja da sauri rike da kanta tace washhh Allah kaina,
kai baka san mutum zai shigo bane,
ya tsuguna ya ďauki wayarshi yace saboda idon mudubi gareni da ke hasko min abinda ke waje ko,
ta turo baki tabi ta gefenshi zata wuce ya tare kofar yana kallon cikin idonta yace baki iya bada hakuri ba ko, ta sakar mishi harara tace kai zan tambaya wannan tunda ni ka bige ma kai kuma har yanzu zafi yakemin,
yayi murmushi yace lallai yarinya zaki kwana anan dan bazaki taba wucewa ba sai kin bani hakuri, tayi dan guntun tsaki ta juya ya maza ya janyo hannunta ya matseta sosai numfashinsu na gaurayuwa,
runtse idonta tayi tace ka sakeni in tafi, bin ko’ina na fuskarta yakeyi da kallo yace ina zaki,
a tsiwace tace ina ruwanka dalla ni ka sakeni ko inyi maka ihu,
yayi dariya yace bakinki a bude yake ay go ahead, ya ďauka wasa takeyi yaji ta saki ihu da karfi,
da sauri ya saketa ya koma baya a zuciyar shi yace wannan wace irin yarinyace,
da gudu zeenatu ta fito tana waige tace Afeeya me ya sameki, ta ruga bayanta tace wancan ne ya bige min kaina kuma wai sai na bashi hakuri,
zeenatu ta kalleshi tace zanci maka Affan ba gurin jabeer kace zaka ba,
yace wallhy umma karya takeyi sai yanzu ma na gane afeeyah ce, ya harareta yace jarababbiya kawai, yasa kai ya fita yana mamakin irin girman da afeeya tayi,
gurin aikin jabeer ya wuce dan ya kosa ya ganshi rabon da su ga juna tun da ya tafi egypt dan ummanshi ta hanashi dawowa hutu saboda lafiyarshi dan ita kanta a ďarare take a gidan saboda yadda oyiza ke hurda da wasu mutane a cikin gidan da kuma yawan mafarke mafarken da takeyi akan oyizar da ďanta, ga alhj basheer ma sai yadda tayi dashi,

Sunyi matukar farin cikin ganin junansu dan jabeer ma gurin aikin ya bari suka fita yawo sunata hirar yaushe gamo,
sai gurin karfe 5 na yamma suka dawo gida,
gidansu afeeya jabeer ya sauka dan tun safe bai ganta ba kuma yasan tana can ta damu……

Mrs tijjani shattima…
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣8⃣ By Aysha Ya’u Kurah

A daren ranar da Affan ya dawo suna zaune a parlon dukkansu har su salma da suka ri’ka a gida ba aure,
zeenatu dai na ďakinta dan ko tazo ta zauna cikinsu to fa takaici zai sa ta tashi ta koma daki saboda alhj basheer ko kallonta bayayi,
hira sukeyi shi da Affan saboda farin cikin ganinshi, duk irin hararar da oyiza take mishi baisa ya daina hira da ďanshi da yakejin kamar shine ma ranshi gaba daya, mikewa yayi yace ina zuwa affan je ka ce ma ummanka tazo,
Affan ya tashi yaje ya kira zeenatu, dakyar ta yarda tazo dan bata san dalilin kiran ba, wasu takardu ya fito dasu masu yawa yana mikama affan daya baya,
yana gama mika mishi yace kasan takardun menene wannan,
Affan ya girgiza kanshi, alhj basheer yayi dariya ya kalli zeenatu da oyiza yace ku zama shaida na malakkawa Affan company na na lagos dana nan kano,
sai kuma estate dina na Abuja da gidana dake nan Nasarawa, wannan kyautar da nayi wa Affan ba wai dan yafi sauran ya’ya na bane, a’a sai dai dan shine namiji kuma nasan ko bayan raina zuri’ata bazata taba shiga cikin kunci ba in dai Allah ya tayashi riko da duba dukiyar, ya kalli salma da farida yace ku mata ne, kuma aure zakuyi, dan haka duk wata kyauta da zan muku bazata yi wani tasiri a gurinku ba saboda karkashin wani zaku tafi,
wata rana Affan shi zai zama uba a gareku,,
wayyo zan so ku hango min oyiza a wannan lokcin,
kiriss ya rage zuciyar ta buga saboda alhj basheer ya kyautar da duk wata muhimmiyar kadararshi ga affan, shuru kawai tayi jikinta na fitar da zufa, a zuciyarta tace hmmm maiyi baya faďa wannan karan ka kaini bango alhj,
mikewa tayi tace ma su salma ku tashi mu tafi, suka mike suka wuce fuuu cikin bacin rai,
zeenatu ta sauke ajiyar zuciya tace dan Allah ka rufa mana asiri, wallhy Allah kadai yasan abinda kyautar nan zata haifar,
yace ta haifar da komai zeenatu, Affan ďana ne ko bayan raina shi ne magaji na, dan haka ki bishi da adduoin neman tsari kawai,
tace to Allah ya tsaremu da tsarewarshi, ameen yace sannan suka cigaba da hira yace ma affan ya tashi yaje ya adana takardun, Affan ya mike yana jujjya takardun ya wuce ďaki ya bar iyayenshi na hirar da suka daďe basuyi ba…

Tun safe jabeer ya fita da Afeeyah da Ameerah yawo, duk guraren shakatawa da wasannin dake cikin garin kano saida suka je, a shop rite suka tsaya yayi musu siyayya suka fito a gajiye zasu shiga mota,
wata kyakyawar farar yarinya suka hango ta tunkaro su tana dariya,, rufe mota jabeer yayi yana dariya ya karasa kusa da ita yace “Nadiya Lameeďo” idonki kenan, tayi dariya tace kai zan ma wannan tambayar Jabeer, ya kake?, yace am cool walhy, ya skull ko aiki, tace duka, bani cntct dinka zamuyi magana a waya dan naga sauri kakeyi,, ya ciro card dinshi ya bata itama ta bashi nata sukayi sallama ta wuce,
mota ya shiga ya kalli Amirah dake gaba ya waiga ya kalli Afeeyah da ta cika tayi famm yace juyin mulki akayi kenan,
ke Amirah koma gurinki itama ta dawo gurinta,
Amirah ta buďe kofar zata fita Afeeya tace saidai fa mu zauna tare a baya, amirah tace kaji ko yaya, wallhy tun ďazu nake ce mata ta dawo nan taki,
kallonta yayi ta mudubi yayi dariya yace amirah shigo muje,
suna isa kofar gida ta buďe motar ta shige ba tare da tabi takan kayan da ya siyo musu ba,
Amirah ta kwashi nata kayan ta shige gida itama, jabeer ya gyara parking ya kwaso kayan ya fito dasu ya shiga gidansu,
kwance ya sameta can karshen gadon hajja tayi ruf da ciki hajja na mata magana tayi banza da ita,
jabeer ya zauna bakin gadon ya gaida hajja ta amsa tace yau kuma me kayi ma mutuniyar taka,
jabeer yayi dariya yace wallhy babu abinda nayi mata rigima ce kawai, Afeeya ta ďago idonta a kankance tace har kana wallhy,
ya kalleta yace to me akayi,
tace nima bansani ba, ta mayar da kanta kan katifar ita kanta bata san me zata ce ya mata ba ita dai tasan taji masifaffan zafin ganinshi da tayi da wata,
juyin duniya yayi ta faďa mishi abinda yayi mata amma sam taki ďago kai ma bare ta bashi amsa,
hajja taja tsaki tace tashi ka tafi ka rabu da ja’ira da kanta zata nemeka, in ba iskanci ba babu abin da aka ma mutum ya hau fushi, to in kin ga dama ki fashe,,
jabeer zaiyi magana ya ji wayarshi na ringing, ya mike da sauri yace hajja dan Allah ki rarrasheta kafin na dawo tun dazu Affan ke jira na, hajja tayi tsaki tace ni ban iya wacce ka iya ba, ya fita yana dariya. ..

Sai bayan isha suka rabu Affan ya wuce gida,
ya na sa kafarshi cikin gidansu yaji muguwar faduwar gaba,
wucewa ciki yayi a hankali jikinshi a mace ya shiga dakin mahaifiyarshi,
zama yayi ya dafe kanshi yana jiranta dan a tunaninshi tana bayi ne,,
wani irin ihu yaji mai firgitarwa ya mike da sauri yana kasa kunne yaji daga inda ihun ya fito,
kafa kunnenshi yayi a jikin toilet yaji ba alamar mutum a ciki, umma… umma.. ya kira sunanta sau biyu yaji shuru ya tura bayin,
juyawa yayi da sauri da yaga bata yana kwala kiranta,
muryoyin mutane ya dinga ji a can saman gidansu gurin shan iska,
a hankali ya karasa gurin yana leke a tsorace saboda muryoyin da yaji harda ta maza a ciki,

wani razanannan ihu ya saki haďe da faduwa kasa sumamme sakamakon abinda idanuwanshi suka gani…..

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣9⃣ By Aysha Ya’u Kurah

A gigice oyiza da wasu maza suka saki zeenatu da babu alamar numfashi a tare da ita ta faďi timm a kasa,
kan Affan sukayi da gudu oyizah ta ďago shi cikin tashin hankali tana faďin shikenan asirina ya tonu, na shiga uku na lalace, wani bakin kato ya yarda wuka da farin kyallen hannunshi yace yanzu ya zamuyi kenan, dayan cikin dakewa yace mu gama da mamanshi sai mu dawo kanshi,
oyiza ta girgiza kanta tace Nooo mu fara dashi tukunna saboda kar ya farfaďo ya tona min asiri,
bakin katon da naji sun kira da “BULADUNA” yace yanzu me kike so mu mishi, oyizah ta runtse idonta a zuciyarta tace “help me my lord”, cikin mintina uku dabara tazo mata ta mike da sauri tace ku kama min shi,
cikin rashin fahimta sukace ina zaki kaishi, ta nuna kasa da hannunta tace anan zai karasa, kunga babu wanda zai zargeni za’a ayi tunanin faďowa yayi by mistk,,
A tare suka haďa baki sukace Good idea, gaskiya oyee u are very sharp shiyasa kungiya take ji dake, tayi murmushi tace “Lts make it snppy”, kar wani yazo ya cim mana thou nasan ba kowa a gida,
cikin rashin imani da rashin ganin tsawon ginin bene hawa huďu suka wurgo Affan ta kai,,
su kansu saida suka runtse idonsu saboda ganin tsayin gurin amma dayake zuciyarsu a kangare take nan da nan suka sake suka juyo gurin farin kyallen da zeenatu take,
a firgice suka haďa baki suka ce ina ta shiga,
oyizah ta kwalalo ido tana duba ko ina a gurin amma basuga koda sawun kafar zeenatu ba bare ita,, hankalinsu yayi masifar tashi suka shiga duba ko’ina na cikin gidan amma basuga zeenatu ba, oyizah ta buga tagumi tace to ina ta shiga, bana tunanin da kafarta ta tashi saboda ko sanda Affan ya ganmu Kurwarta na gurin chummy,
to waye zai dauke gangar jikinta? Buladuna yace oyee kin tabbatar babu kowa a gidannan,
tace babu kowa,
su farida sun fita sannan na aiki mai aikinta guri mai nisa I don’t think ta dawo kuma ko ta dawo ay baza ta hawo nan ba, dayan cikin kosawa yace mu tafi kawai tunda mun samu abinda mukeso me zamuyi da gangar jiki, buladuna yace hakane, lets go oyee,
cikin rashin kuzari ta bisu kan buzun tsafinsu suka bace daga gidan..

Ba karamin tashin hankali suka shiga ba da chummy tace kurwar zeenatu ko 5mints baiyi ba ta nemeshi ta rasa, oyizah idonta yayi jawur tace to ina yaje,? kodai ya koma jikinta ne, shikenan asiri na ya tonu,,,
Chummy tace calm down oyee, duk inda take yanzu hankalinta baya jikinta, saidai tana tare da wacce take mata addua yanxu haka, wannan dalilin ne kadai ya hanani dawo da ita, amma zansa suyi nesa sosai kuma zanyi mata abin da har ta mutu bazata taba motsi ba bare ta tashi ta dawo ta tona mana asiri,
oyizah ta dafe kanta tace my lord wacece wacce suke tare yanzu ďin,
chummy tace na kasa gane ko wacece, but koma wacece tanada kusanci da gidan,
oyizah ta shiga kogin tunani, a zuciyarta tace to wacece wannan za ta dauke zeenatu, ita dai tasan babu wacce keda kusanci da zeenatu sai Abida to ko Abida ce ta dauke ta, wata zuciyar tace to ta ina abida ta shigo gidan da daddare, ta dinga tunanin da baida amsa ta kara kallon chummy cikin tsananin damuwa tace my lord ya akayi har ta samu damar guduwa,,
Chummy bata iya bata amsa ba ta kalli wani katon glass din da ta tura Fanne da Fanna tayi kwafa cikin takaicin abinda sukayi mata,
dariya fanne tayi tace munci dubu sai ceto, sai dai ki rufemu anan dan wallhy indai muna bude babu wani rai da zai kara salwanta a gurinku,
oyizah taji kamar zata shakesu sabo takaici amma babu hali,
ta kalli chummy tace my lord ya kamata a gama da yarannan if not zasu dinga bata mana aiki,
chummy tayi murmushin mugunta tace very soon oyee,,,

saida suka gama tsaface tsafacensu sannan kowa ya bace itama ‘”chummy” ta tafi gurin jigajigan matsafa na gaba da ita dan samo sababin lakanin tsafi…

Mrs tijjani shattima…
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣0⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Tsaye take cikin zauren gidansu tana leken kofar gidansu jabeer ko zata hango shi,
tun bayan magriba take tsaye a gurin amma har bayan isha’i bata hango inuwarshi ba,
juyawa tayi zata koma ciki kamar zatayi kuka taji an rike hannunta ta baya, tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba hawayen da ya gama taruwa a idonta ya fara zubowa,
a hankali ya juyota ya ciro wayarshi yana haska fuskarta,
murmushi yayi da yaga hawaye akan kumatunta yasa hannu ya fara share mata a hankali yace shikenan ke kuka bashi da wuya a gurinki,
da abun kuka da wanda ba na kuka ba duk sai kin musu kuka, yanzu faďa min abinda aka miki,
ta kara fashewa da kukan da daga ji na shagwaba ne tace ba kai bane— sai kuma tayi shuru,
yayi dariya yace ba ni bane mee? Ta kauda kanta tace ban sani ba, ya juyo da kanta yana kallon cikin idonta yace fadamin laifin da nayi in hukunta kaina yanzun nan,
ta turo baki tace tun ďazu nake jiranka anan kuma kasan zan jiraka shine ka tafi gurin wannan kawar taka mai kama da nunar rana,
jabeer ya kwashe da dariya yace wacece me kama da nunar rana?
Afeeya ta kara turo baki tace ohoo ka fini saninta,
jabeer ya kasa tsayar da dariyarshi ya kamo hannuwanta ya hadesu guri ďaya ya sa bakinshi ya sumbace su a hankali haďe da lumshe idonshi, magana ya fara yi ba tare da ya bude idanuwanshi ba yace gurin Affan naje Afee, kinsan babu abinda da zai hanani zuwa gurinki da wuri sai ganin Affan,
ta zare hannunta daya ta kai saman idonshi ta fara jan zara zaran gashin idonshi tace ni dai ban yadda ba ka fada min gaskiya ko in tura hannuna cikin idonka,
ya buďe manyan idanuwanshi da sauri yace ki makantar dani kenan,
tace eh mana sai inga da idon da zaka dinga zuwa yawo,
yace haba Afee nah yanzu in kika makantar dani wacece zata aureni,
ko bakya so ki samu anty wacce zata dinga kula dake,
Afeeya tayi narai narai mayatattun idanuwanta tace yaya jabeer in kayi aure shikenan zan daina ganinka, zaka daina zuwa gurina,? zaka daina kulawa dani ko?,
ya janyota jikinshi yace babu abinda zai hana jabeer kula da Afeeyah in dai yana raye,
bana fatan abinda zaisa rana ta faďi har inyi bacci batare da nasaki a idona ba,
ta kara narkewa a jikinshi kamar karamar yarinya tace to ay in kayi aure zan daina ganinka haka hajja ta ke cemin kullum, da karfi yace inji hajjan, afeeyah ta gyaďa kanta tace eh mana kullum sai ta faďa min da daddare wai in rage sabon da nayi da kai saboda zan sha wahala in kayi aure, ay nasan bazaka bari in sha wahala ba ko?
ya gyaďa mata kanshi zuciyarshi na kara zurfi a cikin soyayyar afee,
da afeeya tafi haka da babu abinda zai hanashi faďa mata abinda yakeji game da ita,
girgizashi tayi yayi firgigit, tace to karkayi aure ko kuma ka aureni sai mu zauna gida ďaya ka dinga goyani muyi bacci tare ko,
ya kalleta sosai yace kina sona?
ta rufe fuskarta tace sosai ma,
yayi dariya ya buďe fuskarta yace da gaske kikeyi, tace dagaske yayana, to in ban soka ba wa zan so, kaima ay kana sona ko?,
yace fiye da yadda nake son kaina wifey na,
ta daka tsalle tace bari inje In faďa ma hajja ta daina min gori, yace muje dai mu faďa mata tare ko,
tace eh hakane ta kamo hannunshi cike da murna suka shiga ciki…

Sai goma saura ya fito daga gidansu afeeyah, zama yayi kan dakalin gidansu yana kiran wayar Affan dan ya fito su ďan rage dare,
sau huďu yana kirah ba’a ďauka ba,
mikewa yayi a ranshi yace may be yayi bacci ko kuma yana can suna hira da umma,
dakinshi ya wuce ya kwanta yana tunanin Afeeyah,
Allah ya sani yana matukar kaunar afeeya, hakuri kawai zaiyi ya jirata ta gama sec skool ya aureta ya maida ita mallakinshi ya bata duk wasu nau’in kulawa da gata marasa yankewa,
da wannan tunanin bacci mai cike da mafarkai yayi awon gaba dashi….

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣1⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Karfe 6 na asuba Alhaji basheer ya iso gida a gajiye,
bacci sosai yakeji dan haka ya wuce ďakinshi don ya kwanta ya samu isashshen bacci, ya yi matukar mamakin rashin ganin zeenatu ta fito tarbarshi kamar yadda ta saba, amma sai ya share da tunanin ko itama bacci ne yayi gaba da ita ko kuma dai wani abun daban amma haka nan zeenatu bazata taba kin fitowa tarbarshi ba ko da kuwa bazaii kulata ba, da wannan tunanin bacci ya ďaukeshi…

Ihu ya dinga ji kamar a cikin mafarki,
a hankali ya buďe idonshi yaji bugun kofar da ake ma ďakinshi yaki tsagaitawa, da sauri ya diro daga kan gado jikinshi na rawa ya bude kofar,
Salma da farida ya gani tsaye suna ihu suna kuka suka ce daddy Affan– Da sauri ya katsesu yace me yasamu Affan din, kasa bashi amsa sukayi sunata nuna hannunsu saitin kofa, da gudu ya fita waje ya’yan hanjinshi sai kaďawa sukeyi,
turus ya tsaya ganin masu aikin gidan da oyizah tsaye kan affan suna kuka jini ko ta’ina a kasa da kanshi,
wani irin ihu alhj basheer yayi haďe da karasawa yana girgizashi yana kuka, da kyar yake iya hado sunan Affan ya kira saboda tashin hankali, daukarshi yayi bai kula da jini da fashewar da tsakiyar kanshi yayi ba ya turashi cikin mota, binshi oyizah tayi tana kuka tace alhj ina zaka kaishi, ya riga fa ya mutu,
alhj basheer ya watso mata ashariyar da baisan yadda akayi ya fadeta ba ya shiga mota yayi asibiti da affan,
likitoci kansu sun tsorata da ganin Affan, wani a cikinsu yace ranka ya dade wannan ay ya mutu,
alhj basheer yayi kanshi yace ubanka ne ya kasheshi? Doctorn yayi baya yace sorry alhj,
nan likitoci sukayi caa akan Affan duk da bawai sun sa ran yana raye ba saidai dan bala’in da alhj basheer ke musu,
Cikin ikon Allah karfe 2 na rana Affan ya fara motsa hannunshi, cikin mamaki doctor musa ya kura ma hannun ido ko gizau yake mishi, ganin ba gizau bane yasa shi fita kiran sauran likitocin cikin murna,
alhj basheer dai binsu yakeyi kamar zararre yana fadin bai mutu ba ko, dr musa ya gyada mishi kai kawai suka wuce dakin da Affan yake,
sai hudu suka fito kowa yayi hanyar office dinshi,
doctr musa ya kalli alhj basheer yace ka kwantar da hankalinka alhj muje office inyi maka bayani,,
alhj basheer ya bishi office din ba tare da ya ce uffan ba,,

Doctor musah ya kalli alhj basheer cikin damuwa yace alhj ka saurareni da kyau kuma duk abinda zan faďa maka kasani bani nayi ba kuma ba wani bane yayi Allah subhanahu wa ta’ala shine ya jarabceka kuma ya jarabci danka, saboda haka dan Allah alhj kayi tawakkali saboda cuta ba mutuwa bace,
alhj basheer ya share hawayen da ya zubo a idonshi yace faďamin komai doctor, fadamin abin da ya sami Affan,, doctor musah ya mika mishi takardun hotunan kwakwalwar da sukayi ma Affan,
ya karba hannunshi na rawa yace bazan gane komai a ciki ba doctor kayi min bayanin komai da baki,
doctor musah yayi ajiyar zuciya yace alhj, Affan ya samu “brain disorder” abin da yabamu mamakin anan shine duk girman ciwo da karfin buguwar nan bashi ya taba kwakwalwar shi ba har yasamu “mental illness” sai wani abun daban,,,,
ya mika mishi wata takarda yace wadannan sune ciwukan da kwakwalwar shi ta samu

“Psychological trauma”:
wannan cutar may be triggered by P.T suffered as a child, kamar “severe emotional”, physical, or sexual abuse;” abinda ke kawoshi kuma shine, “a significant early loss”, kamar the loss of a parent; and neglect…

sai kuma
“Environmental stressors”:
“itama ana samunta ne a shock din mutuwa ko macen da aka saka, ko kuma dysfunctional family life,
sacking 4rm jobs or schools, and substance abuse — it can trigger a disorder in a person who may be at risk for developing a mental illness.”
Kaga kenan akwai abinda ya gani ko kuma ya sameshi cikin waďannan abubuwan amma sam ciwon kanshi bai da alaka da cutar,
Alhj basheer cikin tashin hankali yace yanzu doctor kana ganin Affan zai samu lafiya nan kusa,?
doctr musah cikin tausayawa yace sauki na gurin Allah alhj, in yazo yanzu baiyi gaggawa ba sannan in baizo yanzu ba baiyi jinkiri ba saboda Allah ne kadai yake iya bada sauki a lokacin da yaso,
sannan ina tsoron sanar dakai mostly mental illnesses irin wannan are caused by a combination of factors and cannot be prevented so easily, saidai a dage da addu’a saboda babu abin da ya gagari Allah kuma babu wanda yasan gaibu sai Shi..,
da sauri oyizah da tun shigewar su office din doctor ta iso ta juya cikin jin dadin ciwon da taji ya sami Affan da kuma firgicin jin affan nada rai kuma zai iya samun sauki a koda yaushe,
kuma tasan yanzu alhj na dawowa zai fara tambayarta ina zeenatu? Kuma me ya samu Affan me ya gani har ya haddasa mishi wannan cutar,
fita tayi daga asibitin da sauri cikin tsananin tsoron abinda zai je yazo, bata zame ko ina ba sai gurin tsafinsu…..

Mrs tijjani shattima…..
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣2⃣ By Aysha Ya’u kurah

Alhj basheer ya fito daga office din doctor Musah idonshi jajur saboda kukan da yaci, dakin da aka kwantar da Affan ya shiga ya zauna gefenshi yana zubar da hawaye yana ta tunanin yadda akayi har Affan ya faďo daga wannan saman nisan gaske, to wai ma me Affan ya gani da har ya firgita shi haka,
da sauri ya mike da ya tuno da tun asuba baisa zeenatu a idonshi ba, kuma ace har Affan baida lafiya batazo inda yake ba, girgiza kanshi yayi a fili ko dai wani abu ne ya samu zeenatu, gabanshi ya faďi sosai da ya tuno da kalaman doctor,
jikinshi ya fara rawa ya murda kofar dakin da affan yake ya fita da sauri yana fadin innalillahi a zuciyarshi,
da taimakon Allah ya isa gida, a waje yayi parking motar saboda tashin hankali,
yana shiga ya wuce dakinta,
babu inda bai duba ba a ďakin bai ganta ba, cikin kiďima ya fito yana haďa sunayen mutanen gidan yana kirah da karfi,
da gudu suka firfito, oyizah da bata fi minti 5 da dawowa daga gurin tsafinsu ba ta matso kusa dashi tace lafiya alhj,
ya nuna dakin zeenatu yace ina zeenatu take, fareeda da salma suka ce daddy tun jiya bamu ganta ba,
oyizah tace ni rabona da zeenatu ma ay tun ranar da zaka tafi mukayi maka rakiya,
cikin karaji yace to ina ta shiga,
oyizah ta dafashi tace calm down my dear muje ka huta ka kira can gida kaji ko tana can,
cikin damuwa ya kalli fuskar oyizah, nan ya tsinci kanshi da kasa yi mata musu ya bi bayanta suka wuce gurin dinning,
saida ta bashi abincin da ta haďasu da sinadaran asiri sannan ta zauna gefenshi tana matsa mishi kafa, kallonta yayi har lokacin fuskarshi dauke da damuwa yace safiya ya akayi Affan ya faďo daga wannan saman mai nisa,
sannan me ya faru a gidannan da har ya haddasa tabuwar kwakwalwarshi,
oyizah ta fara share hawayen karya tace alhj nima ban sani ba, kowa na bangarenshi ya za’ayi insan abinda ya faru,
Allah sarki Affan yanzu brain dinshi ya samu matsala,
murya a dashe alhj basheer yace eh safiya, kuma bawai fadowar da yayi bane ya taba brain dinshi, hankali tashe kamar gaske tace to me ya sameshi,
nan ya kwashe abinda doctor ya faďa mishi ya fada mata,
wani irin kuka ta fashe dashi harda zama a dirshan a kasa tana faďin mun shiga uku, yanzu shikenan Affan ya haukace,
alhj basheer ya shiga rarrashinta yana faďin addu’a zamuyi mishi safiya,
dakyar oyizah tayi shuru tace ni alhj babban tashin hankalina shine rashin ganin zeenatu,
Allah yasa ba wasu mugayen bane suka saceta suka wurgo Affan daga sama, hankalin alhj basheer ya tashi da jin furucin oyiza,
ya kalleta yace da zeenatu tayi musu me zasu saceta,
oyizah tace Alhj ka manta muna cikin zamanin da ba sai kayi ma wani komai ba zai maka mugun illah, nidai gobe kabi jirgin safe kabar kulawar Affan a gurina kaje can cameroon ka dubata dan wannan abun yafi karfin waya,
alhj basheer ya share zufar goshinshi yace kin kawo shawara mai kyau safiya, amma— ta katseshi da sauri tace na fada maka zan kula da Affan fiye da yadda zaka kula dashi, kai dai ka tafi nemanta dan hakkinta na wuyanka,
cikin jindadin tsararrun kalaman oyizah alhj basheer yace nagode sosai safiya, Allah ya kaimu goben, tace ameen yanzu kaje ka kwanta ni zan tafi gurin Affan din in ta kama ma sai in kwana, alhj basheer yaji dadi sosai a ranshi ya dinga shi mata albarka..

Ďaki oyiza ta wuce zuciyarta wasai yanzu gida zai dawo karkashin ikonta,
wani kulli mai kyalli ta kwance ta fito da babyn “Mutum mutumi” an soke kanshi da mashi, Kallon babyn tayi hade da kwashewa da dariya tace Affan kai da warkewa har abada, haka zaka dawwama cikin hauka har ka mutu kamar yadda babyn nan take haka zaka kasance sai yadda nayi dakai,
ta mike ta daga karkashin gadonta inda ta dade da haka wani ramin sihiri ta kara tona gefen ramin ta kira sunan Affan sau uku sannan ta tura babyn ciki tana dariyar mugunta,
ta kalli wata laya ta kara saka wata dariyar tace wannan naki ne zeenatu, ba yanzu zanyi aikin ba sai an gaji da nemanki, ta mayar da layar cikin daurinta sannan ta loda magunguna hade da turarukan tsafi a jakarta ta shirya wucewa asibitin..

Tun asuba jabeer ke neman wayar Affan ba’a dauka ba,
daga karshe ma jin wayar yayi akashe,
gurin karfe 8 yaso shiga ya dubashi sai wani muhimmin aiki ya taso mishi a office ya wuce,
bai dawo gida ba sai bayan magriba, saida ya fara shiga gurin Afeeyah suka dan taba hirah sama2 sukaci abinci tare kamar yadda suka saba sannan ya mike jikinshi a sanyaye saboda rashin jin muryar amininshi yau tru out,
abinda bai taba faruwa ba tun tasowarsu dan ko tafiya daya yayi to suna manne a waya, sallama yayi ma hajja da afeeyah ya fita ya isa kofar gidan su Affan,
tun a gate mai gadi ya sanar dashi abinda yake faruwa,
kiriss ya rage jabeer ya faďi saboda tashin hankali, da kyar ya daidaita kanshi ya karasa cikin gidan, babu wanda ya samu a ciki sai farida dake waya tana kyakyata dariya,
murya na rawa yace Fa-re-da- wani asibiti aka kwantar da Affan, sai da ta kalleshi sama da kasa sannan ta ajiye wayarta, cikin masifa tace haddar sunan asibitoci aka kawo ni yi duniya,
cikin bacin rai jabeer yace “oops” na manta fa da’kikiya kamarki wacce bazata iya haddar sunanta ba bare asibitin da aka rubuta shi da turanci saboda masu ilimi su gane, farida ta mike a fusace zata fara bala’i karar bugun kofa ya hanata,
jabeer ya kalli daddy suka gaisa sama2 yace daddy wani asibiti affan yake, daddy yace muje jabeer nima can zanje nan “Arewa surgery” ne,
jabeer ya harari fareeda ta gefen ido yayi kwafa ya bi bayan daddy….

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣3⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Kuka sosai jabeer yayi da yaga yadda Affan ya koma,
zama yayi gefenshi yasa hannunshi cikin nashi yana karanto adduo’i yana tofa mishi,
oyizah ta harareshi tace dan Allah malam ya isa haka kar miyan ka ya jikashi ya farka lokacin farkawarshi baiyi ba,
daddy yace addu’a fa yake mishi safiya,
oyizah ta marairaice tace doctors ne suka hana alhj nima dazu ina mishi addu’a suka hana ni,
jabeer ya waigo ya kalli daddy idonshi a kumbure yace daddy ina umma,?
alhj basheer yayi jugum sannan ya fada ma jabeer komai game da zeenatu,
a rude jabeer ya mike yace daddy shine ba’a dauki mataki ba tun dazu,
innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
alhj basheer yace nasan bazata wuce gida ba gobe da sassafe zan tafi,
jabeer yace da nan ya kamata a fara daddy, in har bata nan sai a tafi can,
oyizah ta harareshi ta wutsiyar ido sannan tace hakane alhj kai kaje cameroon din mu sai mu fara nemanta anan ko jabeer,
jabeer bai kalleta ba yasa kai ya fita zuciyarshi kamar zata buga saboda tashin hankali..

Washe gari tun asuba jabeer ya bar asibitin ya isa gida,
nan suka shiga binciken duk gidajen aminansu na kusa da na nesa shi da Abida da tun jiya bata runtsa ba da jabeer ya faďa mata wannan mummunan labarin,
babu inda basu shiga ba amma babu labari,
jabeer ya zarce gurin yan sanda ya sanar musu sannan ya koma asibiti,,

yana shiga ya tarar da oyizah zaune gefen Affan tana shaka mishi turare a hancinshi, tana ganin jabeer ta mike da sauri tace jabeer ka dawo,
kaga turare ne aka bani ance yana healing ciwon kwakwalwa in ana shakawa mutum shine nake gwada mishi,
jabeer yace uhum kawai ya zauna gefenshi yana kallonshi yana mishi addu’ar da oyizah ta tsani ganin ana mishi,
a zuciyarta tace tabbas in bata katange Affan daga adduo’in mutane ba wata rana tana zaune adduar zatayi tasiri akanshi,, ta kalli Affan tayi kwafa ta maida turaren jaka ta fita daga asibitin..

A can cameroon kuwa tashin hankalin da suka shiga bazai misaltu ba,
dan kuka sunci shi da aka gama duba guraren dangi ba’a sameta ba,
alhj basheer kanshi kasa tsayar da kukanshi yayi yanata kiran sunanta kamar zautacce yana fađin ina kika shiga ne zeenatu,
da kyar Baffan zeenatu ya rarrasheshi da bashi baki akan suyi ta addu’a, ko gawarta ne Allah ya bayyana,

Washe gari tare da su yadikko aka taho duba Affan,
sun jima tsaye akanshi cikin tausayawa amma fa babu wanda a cikinsu ya iya budar baki yayi mishi addu’a,
“saidai kawai suce sannu Affan cuta ba mutuwa bane, wata rana sai labari sai kuga kamar baiyi ciwon ba,”
wadannan kalmomin su kadai duk wanda yaji Affan baida lafiya yake iya faďi,
JABEER BARA’U DAURA shi kaďaine yake yin addu’a sosai akan Affan,
hakan ba karamin ďaga hankalin oyizah yakeyi ba dan tayi duk wani abun da zatayi na tsafi akan jabeer amma ta kasa,
tabbas tasan jinin jabeer ya fi karfinta dan haka ta kudira a ranta Affan na komawa gida zata hana duk wani mahaluki zuwa dubashi bare har ya samu damar yi mishi addu’a,
sannan shima Affan din zata san yadda zatayi ta daure kafarshi a cikin gida ya zamana ko wajen gate bazai iya taka kafarshi ba,
da wannan tunanin oyizah ta ďan samu relief…

Sati biyu suka wuce babu zeenatu babu labarinta,
haka Affan bai farfaďo ba kullum yana kwance cikin oxygen,

Oyizah ta kalli alhj basheer da yake cikin damuwa har yanxu, tace ranka ya ďade ya kamata ka cire duk wata damuwa aranka, duk inda zeenatu take— yayi saurin katseta yace na manta da batun zeenatu a wayewar garin yau saboda zeenatu ba yarinya bace duk inda take zata iya kula da kanta koda kuwa saceta akayi,
ni yanzu ciwon Affan ne kaďai ke damuna day nd nyt,
oyizah tayi murmushi a zuciyarta tace aiki yayi, ta tuno sanda zata tura layar cikin bakin gawar “Damo” saida ta tsorata taso ta bar aikin, ashe nasara ne ya hanata barinshi,,
ta kalli alhj basheer idonta ya ciko da kwalla, tace karka damu alhj Affan zai samu sauki tunda yana karkashin kulawar likitoci, zeenatu fa babu wanda yasan inda take,
tsawa mai karfi ya daka mata yace nace ki daina kawo min maganar zeenatu nan gurin,
oyizah ta mike sum2 ta wuce ďaki tana kukan munafurci..

Tsalle ta dingayi da ta shiga ďaki murna kamar zai kasheta, yanzu abinda ya rage mata shine tasan inda Affan ya ajiye kadarorin da alhj ya mallaka mishi….

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣4⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Ranar wata jumma’a bayan an sauko daga sallah jabeer asibiti ya wuce saboda nan ne gurin zama da kwananshi,
duk da irin kyarar da oyizah ke mishi hakan bai hanashi zuwa ba,, addu’a sosai yayi ma Affan a masallaci,
yana shiga cikin asibitin ya tarar babu kowa gurinshi kuma yaga kamar bakinshi na motsawa,
da sauri jabeer ya naďe carbin hannunshi ya karasa kusa dashi, ya rike hannunshi yasa kunnenshi saitin bakinshi,
R-u-w-a yaji yana fada muryarshi na rawa,
jabeer ya mike da azama yaje ya kira doctor suka shigo tare da sauri,
doctor ya gama duba Affan sannan ya kalli jabeer yace dan bashi ruwa kaďan,
jabeer jiki na rawa ya balle murfin Faro ya tsiyaya kadan a ciki saida yayi addu’a sosai a cikin ruwan sannan ya matsa kusa da Affan da har lokacin bai bude ido ba sai kiran ruwa da yakeyi, buďe bakinshi yayi zai fara zuba ruwan aciki oyizah ta shigo da sauri ta kabe glass cup din ya fadi ya fashe,
cikin masifa tace baka da hankali ne zaka bashi wannan ruwan daga cewa a bashi,
doctr musah yace hajiya ruwan is pure ni nace ya bashi,
oyizah ta fito da wani ruwa a cikin gora tace wannan ruwan alhj ya bani kafin ya tafi yace duk sanda ya farfaďo a tabbatar shi ya fara sha saboda ruwan addu’a ne da ya amsoshi daga cameroon,
jabeer da ya cika yayi famm yaja dogon tsaki ya fita ya bar asibitin gaba ďaya,
doctr musa ya ba oyizah da ke sharar kwallar munafurci hakuri yace bamu san akwai adduar da za’a bashi bane da bamuyi gangancin bashi ruwa ba,
tace babu komai doctor, yanzu zan iya bashi kenan,
doctr musah yace eh hajiya, nan oyizah tayi murmushi ta gefe ta zauna ta bude bakin Affan ta tsirara mishi ruwan da yasa shi sakin razananen ihu, da sauri ta mike da ta tabbatar da ya hadiye ta matsa baya tana kuka tana fadin doctr dubashi,
da kyar doctor musah ya samu yayi mishi allurar da tasashi bacci ihun ya lafa,
ya waigo ya kalli oyizah yace hajiya I think ruwan adduar nan yasashi ya farfado gaba daya saidai kuma yanzu ne za’a fara jinyar, yasa kai ya fita..

Oyizah tayi dariya sosai tace ba dole ya farfado ba, na daďe ina jiran wannan ranar, ta kalli ruwan sosai tace nasan har yakai inda nakeso yakai,
ta harari affan ta fara shafa mishi ruwan a fuska tace kai da samun sauki har abada Affan..

Tun daga ranar ciwo ya dawo sabo, saboda kullum da ihu yake farkawa sai an mishi allurah ake samun saukin abun,
ciwon kanshi kuwa ya fara warkewa, dan gurin da yayi rami ya ciko sosai,
saida yayi sati ďaya kullum ya farka da ihu yake farkawa, daga ya farka kafin ayi mishi allura oyizah zata bashi maganin da tace ruwan addu’a ne,

Watanshi ďaya a asibiti ana fama da lalura ďaya,
saidai a kawo babban likitan mahaukata gurinshi ya dinga mishi treatment saboda ciwon da ke kanshi,
yanzu kam ciwon yayi sauki sosai dan haka doctor musa ya bada shawarar a kaishi “psychiatric” alhj basheer sam yaki yarda yace saidai ya fita dashi waje,
doctor musah yace hakan ma zaifi Alhj, gara ka kaishi wajen, akwai wani asibiti a “New Toronto, Canada” sunanshi “LAKESHORE PSYCHIATRIC HOSPITAL” asibitin sun kware sosai alhj, in dai waje zaka fita dashi gara ka kaishi can,
kuma anan nigeria ma fa akwai psychiatric masu kyau kuma ana kula sosai, kamar su “FEDERAL NEURO PSYCHIATRIC” dake kaduna da kuma na Lagos, da ma sauransu, amma tunda hankalinka yafi ga fita dashi din gara ka fita dashi, mudai fatanmu a koda yaushe shine ya samu lfy,
, alhj basheer yace hakane doctor, nagode sosai in shaa Allah gobe zamu fara processing tafiyar,, doctor musah yace to Allah ya kaimu alhj shi kuma Allah ya——- doctor musa ya kasa karasawa saboda datse harshenshi da yayi, ya kalli alhj basheer ya mika mishi takardun sallama da reports din ciwon Affan tare da magunguna…

Watan Affan biyu a canada, oyizah ke zaune dashi saboda yawan tafiye tafiyen da alhj basheer keyi, jikinshi yayi kyau sosai saidai duk wanda ya ganshi yaga mai tabin hankali, komai na yara yakeyi, ga yawan son wasa, kallon ruwa da kifaye da sauransu,
a cikin wata biyun nan oyizah ta mallake Affan sai abinda tace yayi, sam bata nuna mishi hanyar kwarai saidai ta nuna mishi mara billewa, magungunan tsafi kuwa su ke ďawainiya dashi tun zuwansu canada,
doctors sunyi mamakin yadda akayi magungunan da suke bawa Affan bai mishi aiki ba,
sudai sunsan larura indai ta haukace to wacce tafi ta affan ma sun warkar bare tashi da suke ganinta minor, basu san duk magungunan da suke zuwa bashi oyizah ta karba tace zata bashi zubar dasu takeyi ba,
wani lokacin ne ma take bashi ba bisa ka’ida ba,

A ranar da suka cika wata biyu da sati biyu aka sallamesu saboda haukar affan ba ta barna bace kuma sunga in oyizah tace ya zauna nan to bazai tashi ba har sai tace ya tashi,
wannan dalilin yasa suke ganin kamar in suka basu isassun magunguna nan da wasu yan watanni zai samu sauki..

Ranar oyizah tayi murna saboda dama ta kosa ta koma gida,
yawo ta fita da Affan tayi mishi siyayyar kayan wasa da uban yawa tana zaba tana mishi dariyar mugunta shi kuwa banda murna da tsalle babu abinda yakeyi,
a daren ranar suka hawo jirgi tare da alhj basheer sai kasar mu ta gado…

Cikin dare suka iso gida a gajiye, kowanne daki yaje ya kwanta banda Affan da shi a gurinshi ma safiya ce,
zama yayi a parlor yana wasa sosai gaba daya ya hargitsa parlon,
in ya kalli hanyar dakin zeenatu sai ya runtse idonshi wasu abubuwa su dinga gifta mishi kamar rayuwar cartoon,
kuma sai yaga kamar harda shi a cikin cartoon din,
tashi yayi yana kokarin zuwa kofar dakin yaji muryar oyizah ta daka mishi tsawa,
da sauri ya dawo bayanta ya tsaya yace mummy wannan kofar wanene,
kamar na taba zama a ďakin, kin gani kofar ma kamar ta drawing ko,
oyizah ta shafa kanshi tace my baby kasan meye a kofar nan, ya girgiza mata kai, ta ja hannunshi ta fara nuna mishi kofar har zuwa hanyar steps din can saman da ya faďo tace duk nan gurin zaman macizai, da namun daji ne, kana son su cinye ka, ya noke wuyanshi ya make a bayanta,
tace to karka kara zuwa arean gurin kaji, yace to mummy,
ta kama hannunshi ta wuce side dinta dashi ta sashi a wani daki ta rufe tana kyakyata dariyar mugunta da jindadi..

Tun karfe 12 jabeer keta fama da masu gadin gidan akan su bude mishi kofa sunki, dan oyizah tace kar a kara barin kowa ya shigo saida izininta, ran jabeer ya baci sosai idonshi yayi jawur,
yace yanzu Halilu har ni ma sai ku hana shiga in an saku,
halilu yace kwarai kuwa saboda ina mutunta aikina,
jabeer yayi kwafa kamar zai juya sai ya dawo da karfinshi ya tura halilu ya ruga ciki da gudu suna binshi a baya,
da sauri alhj basheer ya fito jin hayaniyar tayi yawa,
tsawa ya daka ma su halilu yace lafiya kuke binshi kamar wani barawo,
halilu yace ranka ya dade madam ce tace kar abar kowa ya shigo,
alhj basheer yace jabeer ne kowa, baku san matsayinshi a gidannan bane,
oyizah ta fito da sauri tace yi hakuri alhj mantawa nayi in ce musu kar su hana jabeer shigowa,
alhj basheer yace to su sauran mutanen kuma fa meye dalilin hanasu shigowa,
ta fara matsar kwallah tace bana son a shigo a dinga yi ma affan dariya na fi son sai ya warke mutane su ganshi,
alhj basheer ya jinjina kai cikin damuwa yace na gamsu da bayananki, share hawayenki Allah yayi miki abinda kikayi mana na alkhairi, tace ameen haďe da hararar jabeer,
alhj basheer yace jabeer ka shiga ciki mana abokin naka yana ciki ai,
jabeer yasa kai ya shiga cikin parlon da sallama,

Zaune ya tarar da Affan da wasu kayan wasa a hannunshi, wuyanshi yasha hoda idonshi kuma kwalli, kallon jabeer yakeyi sosai wasu abubuwa na mishi yawo a kwakwalwarshi,
sai da yayi minti biyar yana kallonshi sannan ya zubar da kayan wasan ya rungumeshi yace daddy wannan abokina ne sosai tare muke wasa dashi, kaga fuskarshi ma shima drawing dinshi akayi kamar waccan kofar,
Salma da fareeda suka kwashe da dariya harda rike ciki, yayin da jabeer ya fashe da kuka haďe da kankameshi……

Mrs tijjani shattima…
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣5⃣ By Aysha Ya’u Kurah

A hankali Affan ya saki jabeer yana mishi wani irin kallo,
fuskarshi ya fara shafawa yana share mishi hawaye yace naji maka ciwo ne, ya ďaura hannunshi a kan jabeer yace yi hakuri kadaina kuka zo muje kaga kayan wasa na, kaima kana so ko?
jabeer ya gyada mishi kai hawaye na fita a idonshi,
Affan ya ďan bata fuska yace to ka daina kuka zan baka wasu sai ka tafi dasu kaji, Jabeer ya kasa daurewa ya saki hannun Affan ya fita daga gidan da gudu yana kuka sosai,
Affan ya bata rai sosai kamar zaiyi kuka ya kalli daddy yace daddy kaga ya tafi yana kuka ko,
kuma ay na bashi hakuri bansan zaiji ciwo ba, ka bishi ka dawo min dashi muyi wasa kaji,,
alhj basheer ya share kwallar da ta zubo mishi yace zai dawo yanzu affan yaje ya siyo maka abin dadi ne,
Affan ya daka tsalle yace daddy kace mishi ya taho min da sweets dinnan masu dadi,
alhj basheer yace karka damu affan je ka cigaba da wasanka, Affan ya gyaďa kai cike da murna ya koma gurin kayan wasanshi..

Salma da fareeda suka mike kunshe da dariya suka wuce daki,
suna shiga suka saketa kamar tababbu, fareeda tace salma kiga yadda affan ya koma kamar dan yaye, salma tace ni ba karamin dariya yake bani ba, ji wani kwallin da mummy tasa mishi a ido dan Allah, fareeda tace ay ni yanzu na samu film din kallo wanda zai dinga sani nishadi, salma tace ke ko ni, suka kara kwashewa da dariya…

Jabeer bai dawo gidansu affan ba sai can da yamma, idonshi a kode saboda tsabar kukan da yaci,
a waje ya sameshi yana buga kwallo, affan na ganinshi ya rungumi kwallonshi ya rugo da gudu zai rungume jabeer sai kuma yaja ya tsaya saboda tunanin kar ya kara sashi kuka irin na dazu,
jabeer yayi murmushi ya buďe hannunshi, affan ya kwashe da dariya sosai ya shige jikinshi yace yanzu banji maka ciwo ba ko, jabeer yace ehh friend, Affan ya ďago kanshi yace ina abin dadin da daddy yace zaka siyomin,
jabeer yasa hannu a aljihu ya fito da chocolates ya mika mishi,
tsalle yayi ya dane jikin jabeer yana murna ya karba yace bari in nuna ma mummy dan tace duk wanda ya bani abu in nuna mata kafin in ci, bai jira jin abinda jabeer zaice ba ya ruga ciki da gudu,
jabeer ya rungume hannunshi yana girgiza kanshi a zuciyarshi yana kara jin tsoron Allah mai maida bawanshi yadda yaso a kuma lokacin da yaso,,,

Tun daga ranar kullum jabeer ya taso aiki zai tsaya a gurin affan suyi hirarsu yayi ta mishi shirme, in lokacin sallah yayi duk yadda zai buga ya raya affan yazo suje zaiki yace sai ya tambayi mummy, daga yaje ya tambayeta zata hanashi ta tsoratar dashi sosai, da taga kullum jabeer na matsama affan akan sallah sai ta bijiro da kokarin rabasu,
da farko tayi nasara dan kuwa ko jabeer yazo bata barin affan ya ganshi, da affan yaga har sati daya baiga abokinshi ba ya ďaga musu hankali sosai a gidan duk irin tsoron da mummy ta bashi bai shigeshi ba shidai kawai a kira mishi abokinshi abinda yake fadi kenan,
da taga kullum bashi da aiki sai kuka kuma baya cin abinci sai tasa masu gadi su nemo mata jabeer dan in alhj ya dawo ya tarar dashi a haka to bazai mata da kyau ba..

Duk irin tururuwar da mutanen unguwa keyi a kofar gidan zuwa gaida affan basu samu shiga ba dan ko kofar masu gadi basu buďe musu,
hakan yasa mutane suka hakura da zuwa gaisheshi saidai in sun hadu da alhj basheer suyi mishi jaje a waje, maganar zeenatu kuwa banda yan’uwanta da su Abida babu wanda ke tunawa da ita addu’a kuwa kullum yinta sukeyi akan Allah ya bayyana ko gawarta ne..
Oyizah kuwa likkafa taci gaba don ba kananan kudi takeci da ciwon affan a guri alhj ba ,
duk bayan sati daya da kudin da yake bata da sunan ana ma Affan saukar alqur’ani da rubutu, amma bai taba maida hankali gurin ganin affan yasha rubutun a gabanshi ba saboda ya yarda da oyizah 100%,
haka in malam Atiku ya bashi rubutu a bawa affan ko jabeer ya amso mishi sai dai daddy ya bata yace ta bashi yana fita zata zubar dasu tayi ta musu tofin Allah tsine…
Abinda yafi ďaga mata hankali yanzu shine ta rasa inda Affan ya ajiye takardun kadarorin da alhj ya bashi,
kullum zata zaunar dashi a siyasance tace ya dauko mata takardun da alhj ya bashi, cikin rashin fahimtar abinda take nufi zai tashi yaje ya tattaro duk takardun dakinshi ya kawo mata,
babu irin duban da batayi ma dakinshi da na zeenatu ba amma sam bata gansu ba,, gashi tana tsoron tambayar alhj basheer dan kar ya harbo jirginta, haka ta saduda da tunanin in alhj ya mutu dukiyar duk nata ne da ya’yanta dan ko Affan ma mallakinta ne….

Wannan shine mafarin ciwon Affan da yanzu yake cikin shekara ta uku cikinshi, a wannan shekarun ko sau ďaya affan bai taba fita da kafafuwanshi ba sai dai a kaishi checkup a mota tare da oyizah amma fita shi kadai sam bata yarda dashi ba dan ba karamin kafi tayi mishi ba,
Salma da farida kuwa maidashi sukayi kamar toy haka zasu tasashi a gaba suyita dariya in yana shirmenshi…

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣6⃣ By Aysha Ya’u Kurah

☆ cigaban labari ☆

Gida jabeer ya tafi bayan sun gama hira da hajja da Afee akan lalurar Affan, yana shiga ya wuce parlon mahaifinshi, zaune ya samesu da ummi ya gaisar da babanshi ya amsa fuskarshi dauke da fara’a yace ya jikin abokin naka, jabeer yace alhmdullih baba, Abida ta kalleshi tace ina Afeeyar take shine ta tafi babu ko sallama, jabeer yace ai ummi taga kina bacci ne shine muka shiga gurin affan tare,
Alhj bara’u ya kalleshi sosai yace jabeer yaushe Afeeya zata fara jarabawa,
Jabeer yace next uppr week zasu fara, alhj Bara’u yace hasashena ya zama gaskiya kenan, mun zauna da malam atiku mun tattauna game da maganar aurenku ni in sona ne ma ayi kafin ta zana jarabawar, Abida tace haba alhj ay gaggawa ba namu bane ina laifin in sun gama da sati ďaya, alhj bara’u yace to koma yaushe ne Allah ya kaimu dan na kosa in aurar da jabeer, Abida tace kace dai ka kosa kaga yan jikokinka,
alhj bara’u ya kwashe da dariya yace ma jabeer ya tashi ya tafi, jabeer ya fita shima yana dariya..

Cikin ikon Allah aka tsayar da ranar Afeeyah da jabeer kamar yadda Abida tace,
murna a gurinsu ba’a cewa komai babu wanda zai iya gane wanda yafi murna a cikinsu,
shiri jabeer yakeyi sosai da planning din yadda zasuyi rayuwarsu da Sweet Afee dinshi da ya’yan da zasu haifa tare, duk shirin da yakeyi bai hanashi zuwa gurin Affan ba kullum suna tare da yamma kuma kullum sai Affan ya tambayeshi ina barbie dinshi,
jabeer shirme yake maida abin saboda yasan bayi da isashen hankali, da jabeer yaga abin na Affan bana karewa bane sai yake zuwa ya dauko Afee dakyar suzo gurin Affan, in Affan ya ganta to fa aranar murnarshi ta karu kenan saboda ya dinga mata shirme kenan yana kwaso kayayyaki yana bata wai ta tafi dasu gida,
a cikin yan kwanakin suka dan fara sabawa kadan2, dakyar jabeer ya fahimtar dashi cewa an kusa daura mishi aure da Afeeya, dariya kawai yayi yace to in kukayi aure zaka barmin ita anan gidan, jabeer yace sosai ma ai anan zata zauna, Affan yayi dariya ya kalli afeeyah yace wai haka, ta gyaďa mishi kai tace eh,
wani irin ihu yasa ya mike wai zaije ya fadama mummy,
da sauri Afeeyah ta riko hannunshi ya tsaya chakk yana jin wani irin abu a rikon da tayi mishi,
juyowa yayi kamar me hankali ya kalleta itama shi take kallo haka jabeer kallonsu kawai yakeyi,
jikinta ne ya bata jabeer na kallonta tayi saurin sakin hannun Affan tace karka faďa ma mummy zatace kar abaka ni ko yaya jabeer,
jabeer ya gyada kanshi yana kallon Affan, zama Affan yayi yana murza hannun da Afeeyah ta rike yace to babu abinda zatamin in ta sani,
Afeeya ta gyada mishi kai tace baza ma tasani ba,
jabeer yayi mamakin yadda affan yaji maganar afeeya, mutumin da magana in dai akan mummy ne to babu wanda ya isa ya tsayar dashi, kallonsu ya cigaba dayi yadda yake mata hira tana biye mishi suna kyakyata dariya sai yaji daďi a ranshi dan ko ba komai zai yi amfani da Afeeyah ta dinga dawo dashi hanya,
sam baiji kishin komai a ranshi ba dan yasan Affan baida hankali kuma ko yanada hankali ma bazaiyi kishi ba saboda yasan irin son da afeeyah take mishi..

Safiyyar monday jabeer ya shirya da wuri saboda zai kai Afeeyah makaranta ranar zasu fara jarabawa,
a kofar gidansu ya sameta tsaye tayi kyau sosai tana jiranshi, kusa da ita ya kai motar ta bude ta shiga suka gaisa,
yace da fatan kinyi karatu ko, tace sosai ma banyi bacci sosai ba,
yace kedai fadi gaskiya kodai kin boyo xpo, ta turo baki tace kaima kasan wuce nan duk da bana zuwa 1st kasan dai ban taba wuce 10th ba,
yayi dariya yace 3rd term ss2 dakyar na roka fa aka barki a 10th din shine zaki wani cika min baki a faďa da dambe ne dai ake baki A1,
ta harareshi tace eh naji ďin, yayi dariya ya tada motar suka wuce yana cigaba da tsokarta, kan titin “hausawa” ya hango motar gidansu Affan, bai bi takanta ba bare yasan su waye a ciki, ya wuce ya sauke Afeeyah a skool haďe da yi mata adduoin samun nasara..

Yana fitowa daga layin skull dinsu ya kuma hango motar, wannan karan Affan ya hango a gaba da baloon a hannunshi yana dariya mummy ta hakimce a baya,
bin motar yayi dan yanason yaga Affan kafin ya tafi aiki, asibitin da ake mishi check up suka tsaya, saida suka shiga ciki Jabeer yayi parking, saida ya gaisa da wani abokinshi da suka dade basu haďu ba sannan ya shiga,
sam oyizah bata ganeshi ba saboda hankalinta a tashe yake da result din check up din,
jabeer yaji doctor na cewa gaskiya an gode Allah dan zai iya dawowa normal cikin kwanakin nan saboda mun samu improvement sosai, ya mika mata magani yace wannan maganin shine maganinshi na karshe in shaa Allah in ya kare komai zai zama normal,
jabeer saboda murna zaiyi magana ya bugi wata nurse kayanta suka zube ya durkusa ya kwashe mata yana bata hakuri,
yana ďagowa yaga har sun fita sun shiga mota,
binsu yayi a baya har gida,
a waje yayi parking motarshi saida ya tsaya a waje ya kirah office ya dau excuse sannan ya shiga ciki da sauri,
babu kowa a parlon gidan hakan yasashi hawa sama saboda tsananin murna, tsayawa yayi jikin wata kofar da yakejin magana da karfi haďe da huci kamar zakanya,
lekawa ya fara yi ta gurin mukulli, ya hango Affan zaune kan wani jan kyalle,
da sauri ya dago kanshi jikinshi na rawa ya ďeka ta window, oyizah ya hango da wata halitta suna magana suna zagaye Affan,
suna gamawa yaga an bawa oyiza wani ruwa ance ta bawa affan muddin yasha to bashi ba samun sauki kuma haukarshi zata fi ta da,
oyizah tayi dariyar jindadi tayi sujjada ga wannan halittar nan da nan yaga ta bace,, jabeer sai mutsike idonshi yakeyi a tsorace kamar a mafarki,
muryar oyizah ce ta dawo dashi hayyacinshi waya takeyi da esther tana faďa mata duk yadda tayi ta mayar da Affan haka har abin da tayi ma zeenatu,
a kidime jabeer ya fara fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
jin tayi shuru ne yasa ya leka da sauri ya hangota ta mike zata bawa Affan wannan ruwan,
cikin zafin nama ya murda kofar ya kabe ruwan ya zube a kasa, oyizah ta kalleshi a firgice tace j-a-b-e-e-r, ya dago Affan ya rikeshi yana mata wani mugun kallo yace asirinki ya tonu, muguwa azzaluma, matsafiya mai shan jinin alumma,
naga duk abinda kikeyi yau in shaa Allahu karshenki yazo, yaja hannun Affan zasu fita oyiza tace jabeer ka dawo, ka rufa ma kanka asiri dan wallhy babu wanda ya isa yaga karshena,
ka dawo ka fadi nawa zan biyaka ka rufa min asiri,
jabeer bai saurareta ba ya fita dan a tsorace sosai yake,
suna zuwa gate Affan ya fisge hannunshi yasa ihu yana faďin mummy kizo ga su lion nan zasu kamani, ihu yakeyi yana ja baya ya ruga ciki da gudu,
jabeer ya kalli gate din cikin mamaki dan shi baiga komai ba,
har zai koma ciki sai kuma ya fasa ya fita a fusace,
Police station ya nufa yana zuwa kofar gurin ya fara tunanin to ina evidence yake,
Affan shi kadai ne evidence kuma bashi da hankalin da za”a saurareshi,
shuru ya zauna a motar yana tunanin mafita, can ya fara tunanin yadda zaiyi affan ya samu sauki, a zuciyarshi yace malamai zan tara suyi ta mishi addu’a ita kuma oyizah zan mata lamfa in nuna mata kamar bazan fadama kowa ba har sai nasan yadda nayi har Allah ya bawa Affan lafiya,…

Mrs tijjani shattima…
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣7⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Juya kan motarshi yayi ya nufi gurin wani babban malami dake zaune a Tarauni,
saida ya jira malamin ya gama da almajirai sannan ya shiga suka fara zantawa,
Bayan malamin ya gama jin bayanin jabeer sai ya jinjina kai yace tabbas imani yayi karanci a wannan zamanin, na dade banji rashin imanin da har yakai wannan ba,
ya kalli jabeer yace in shaa Allahu zamu hadu mu fadawa Allah nan da kwana uku zuwa hudu komai zai dai2ta kai dai ka dauke kafarka daga gidan ka barta cikin tunanin baka fadama kowa dinba sannan kayi taka tsan tsan da ita, jabeer yace to malam nagode sosai ya ajiye musu kudin sadaka sannan ya mike ya fita,
Gurin malamai uku yaje a ranar duk yayi musu bayani suma sun dauki alkawarin yi mishi addua ba dare ba rana,,
ranar jabeer ya yini cikin bakin ciki babu yadda ummi da Afeeya da hajja basuyi ya faďa musu abinda ke damunshi ba amma yaki fadi,
Afeeya har kuka tayi mishi duk dan ya fadi amma bata samu nasarar ya fada din ba,

Oyiza kuwa rasa yadda zatayi tayi, ya akayi wannan mayen yaron ya shigo gidannan ya hayo har sama yaji sirrina, kallon affan tayi da ya fara bacci saboda tsoron abinda ya gani a gate,
wani dogon tsaki taja a zuciyarta tana tunanin yadda zatayi da jabeer, yanxu tasan yama gama tona mata asiri saboda haka in ta dau mataki akanshi jama’a zasu zargeta gara tabi komai a hankali..

Kwana biyar da faruwar wannan alamari oyiza taji shuru babu Wanda ya tinkareta,
sannan alhj basheer bai canza mata ba kamar yadda tayi tsammani,
hakan ya bata karfin gwiwar fara aiwatar da duk wani mugun nufinta saboda a tunaninta tsafinta ne ya toshe ma jabeer baki ya ki fadawa mutane,

Shi ko jabeer hankalinshi a tashe yake dan duk malaman da yasa su addu’a kowanne larura ta faďa mishi, daga wanda ya rasa ďanshi sai wanda yayi paralys sai kuma wanda ya rasa mata,

cikin tashin hankali ya dawo gida yayi tagumi yana tunanin mafita,
“Kaka liman” ne faďo mishi a rai nan da nan ya kira wayarshi,
kaka liman yasa wayar a kunnenshi ba tare da ya duba wanda ya kirashi ba yace “malam dan boko dan Bara’u jikan limamin Daura ya ta dabo,”
jabeer yayi dariya yace lafiya lau kakan dan boko ta dabo na gaida Daura, ya kuma tsufa da tsohuwa,
kaka liman yace tsohuwa tana can tana damun hura kasan bata son ayi mata kishiya,
jabeer yace kai ka isa kayi ma Goggo kishiya, kaka liman yace kaji ja’iri kaima fa naga auren nan zakayi nima ina ga cikin satin nan zan nemo wata a cikin nan nijar auro,
jabeer ya kwashe da dariya yace gara dai ka tafi can dan matan nigeria sun fi karfinka, kaka liman yace lallai baka san wanene Abdullahi ba,
a gobe in matarka nakeson aure tana ganina shikenan kai kuma taka ta kare, jabeer cikin dariya yace dan Allah karka kasheni da sauran raina, bari in fada maka dalilin kiran da nayi maka,
kaka liman yace inajinka,
jabeer ya kwashe komai ya faďa mishi har larurar malamn duk ya faďa mishi, kaka liman ya ajiye goron hannunshi yace wannan ta shahara matuka jabeer, ka kirani zuwa karfe takwas na dare zanyi binciken duk wani kullin da sukayi dan sai an fara takanshi kafin a tsunduma cikin addua,
a wannan karan bada malami zata gwabza ba da ni “liman dan Baba” zata gwabza jinina da duk na wani nawa ya fi karfin matsafa saidai idan abun yazo da karar kwana,
jabeer yace to zan kiraka kaka nagode sosai,
kaka liman yace ďan nema rike godiyarka in zaka taho ka siyomin shaddoji da kayan mata in haďa a lefe in auro sabuwar amarya, jabeer yayi saurin kashe wayar yana dariya…

Duk wasu abubuwan tsafi da kulle kulle babu wanda kaka liman bai gani ba, abinda ya kasa ganewa shine na zeenatu gata nan dai an nuna mishi ita a baccinshi bata motsi kuma an nuna mishi tana nan kusa dashi saidai baisan takaimai gurin ba,
ko da yayi ma jabeer bayani yace dole akwai hake haken da sai an haka sannan za’a warware abubuwa sai hayaki da wasu magungunan da zai haďa mishi, dan haka ya bashi kwana uku yazo ya sameshi sai suyi wanda zasuyi a daura sauran ya tafi dashi ya karasa a kano,
jabeer yaji daďi sosai ya dinga ma kaka godiya saboda yasan ko ba komai abokinshi zai samu lafiya kuma zaayi punishing oyiza 4 her deeds,

Tun daga ranar kaka liman yake aiki babu dare ba rana duk da ana yawan kawo mishi farmaki cikin dare haka suke gwabzawa har su hakura su tafi su barshi,
ranar kuwa da ya gama haďa magungunan saida gidanshi ya kusa rushewa saboda girgiza,
bai wani tsorata ba saboda shima hatsabibin bafulatani ne, a cewarshi shi a duniyar nan baiga abin tsoro ba banda Allah shi kadai yake tsoro a ko dayaushe amma mutum dan adam wanda Allah ya ara ma lokacin tsafi ko wani abu to ba abun tsoro bane dan idan Allah ya tashi tarwatsasuu a lokaci daya zaiyi ba tare da bata lokaci ba…

Mrs tijjani shattima…
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣8⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Sati ďaya ya rage bikinsu,
lokacin yayi daidai da kammala jarabawar su Afee,
Fitowarsu kenan daga exam hall ita da safnah kowannensu sai share zufa yakeyi, skul mosque suka wuce sukayi sallah suka zauna bin inuwar gurin saboda gajiya, hira sukeyi duk akan jarabawar da suka zana yau kuma ta karshe,
sai da suka fi minti talatin sannan suka mike da niyyar tafiya gida,
a dai2 gate din fita makaranta suka tsaya ganin anyi cincirundo kan wani yaro ďan ss2, Afeeyah tayi tsaki tace dadina da skool dinnan son gulma dan Allah ji yadda aka wani zagaye yaron can kowa so yakeyi yaji abinda ya sameshi, safnah tace may be abin da ya sameshi babba ne dan kuka yakeyi sosai gunin ban tausayi,
Afeeyah tace to Allah ya kyauta muje ko, safna tace ga “Zulaikha Sambo” can tahowa bari tazo muji me ya faru,
Afeeya tayi tsaki tace dan Allah safnah mu tafi wato kema kin fara son jin abinda bai shafeki ba ko,
kafin safnah tayi magana zulaikha ta karaso gurin su, safnah tace Zully me ke faruwa a can gurin, zully tayi fuskar tausayi tace wallhy mahaifiyar waccan yaron ce ta rasu yanzu aka zo aka faďa mishi, safnah tace ayyah Allah ya jikanta mutuwar mahaifiya ay babbar cuta ce tanada zafi sosai walhy,
Afeeya da jikinta yayi sanyi tace Allah ya rahamsheta mu kuma yasa mu cika da imani, suka amsa da ameen,
safnah tace ay mune abin tausayi Afee, gara ke tun kina karama kika rasa taki yanzu zaiyi wuya wata mutuwa ta girgiza ki,
zully tace kwarai kuwa,,
Afeeyah tayi murmushi tace har gobe ina tunawa da mamana duk da bawani daďewa mukayi tare da ita ba, wallhy kullum na kalli hotonta sai na zubar da hawaye,
mutumin dake debe min kewar tunaninta tun ina karama shine wanda bana fatar rasa shi har karshen rayuwata,
ta kalli safnah tace kikace babu mutuwar da zata girgiza ni, to wallhy kinji na rantse da Allah bana fatan mutuwa akan yaya Jabeer amma ni nasan duk ranar da aka ce min ya mutu to nima binshi zanyi in kuwa lokacina baiyi ba to walhy ko in haukace ko in zama marar amfani,
dariya suka saka sosai safnah tace ay ke baki da hankali,
da in mutum na mutuwa ana binshi kuma Allah baya sa dangana da duk wadanda suka rasa makusantansu suma sun dade da mutuwa,

Afeeyah tayi tsaki tace dan Allah ya isa haka maganar mutuwar Allah yasa mu cika da imani,
suka amsa da ameen sannan suka wuce zuciyar Afeeyah a dagule dan ta tsani zancen mutuwa…

Ranar haka Afeeyah ta wuni sukuku,
wasu irin muggan tunanin mutuwa takeyi, da taga abin bazai fishsheta ba sai ta ďauki qur’ani ta fara karantawa,
a haka jabeer ya tadda ita,
gaisheshi tayi haďe da ajiye alqur’anin a mazauninshi,
kusa dashi ta dawo ta zauna ta zuba mishi ruwan da hajja ta ajiye mishi ta mika mishi tana kallonshi, kallonta yayi shima da ya karbi ruwan yace yau naga duk kin wani natsu ne ko wani ne ya taba min ke,
ta gyada mishi kai,
ya ajiye ruwan hannunshi yace to menene, ko kina son wani abu ne,
ta kara girgiza kanta,
ya bata rai sosai yace akwai damuwa a fuskar nan kinada wanda zaki faďawa da ya wuce ni,
tace um um,
yace to fada min da sauri kinji, idonta ya ciko da kwalla muryarta na rawa tace ba komai,
hajja tace iskanci ne kawai fa da shagwabar banza yau ko abinci bata ci ba saboda abin ya motsa,
jabeer yace dan Allah hajja kiyi shuru karki kara bata min ranta, tashi muje waje ki faďa min kinji,
ta mike jiki a sanyaye suka fita,
a zaure suka tsaya ya kalleta yace ki mayar da kukan nan kar ki bari ya zubo, in naji abinda ke damunki ya cancanci kuka sai in tayaki muyi tare kinji,
ta gyada kai har lokacin kwallah na makale a cikin idonta, yace to inajinki waye ya taba min ke,
ta shagwabe fuska tace ni ba abinda ke damuna kawai dai ina tunanin mutuwa ne,
ta shige jikinshi sosai tace yaya jabeer ay bazaka mutu ka barni ba ko,
ya sa hannunshi ya kankameta hade da lumshe idonshi yace mutuwa lokaci ne Afee babu wanda yasan ranar mutuwarshi,
ta dago kanta tace ni nasan lokacina yaya jabeer,
jabeer ya tallabi fuskarta yace wace irin magana kikeyi,
tace ni nasan duk ranar da ka mutu to nima zan mutu,
yace to ke waye yace miki zan mutu, tace ba kowa ina dai fada maka ne,
yayi dariya sosai yace to naji,
ta marairaice tace dan Allah yaya jabeer karka mutu kabarni kai kadai nake dashi a duk duniyar nan,
kai kadai kake understanding dina, kuma kai kadai kake tolerating dina, kai kake sani dariya kuma ka hanani kuka,
dan Allah ka dinga yi mana adduar in mutuwa tazo ta daukemu lokaci ďaya kaji,
yayi murmushi ya share kwallar da ta zubo daga idonta a zuciyarshi yace yaro yaro ne, ya kalleta yace naji amma ki daina kawo mana maganar mutuwa ke da zaki zama amaryata ranar Saturday,
kar in kara ganin hawayen nan kinji, tace too,
yace yauwa babynah, kin san meye, ta girgiza kai tace a’a,
yace banaso in faďa miki sai kin min alkawari,
tace alkawarin me, yace alkawarin bazaki yi kuka ba, kuma bazaki damu ba, kuma zaki min addu’a,
tace umm nayi alkawari Allah ya bani ikon cikawa,
yace ameen baby,
ina zanje daura gobe amma fa gobe zan dawo in shaa Allah,
Afeeyah ta karkatar da kanta gefe tace ni um umm wayau kamin wallahi na kwance alkawarin,
yayi dariya sosai yace ba’a kwance alkawari yarinya, dan Allah kimin hakuri gobe kawai akwai abinda zanyi mai muhimmaci, kuka ta fara yi tana bubbuga kafa tace wallhy ni bazan yadda ba saidai mu tafi tare, ya rike baki yace ina zamu tafi tare, tace daura mana,
yace haba Afee nah yanzu kinaso in ďaukeki mu tafi gurin su kaka liman tare, ay sai suce amaryar ma bata da kunya,
ta turo baki tace naji ay sau ďaya zasu ce, ya daura hancinshi kan nata yana gogawa a hankali yace haka zasu dinga faďa kullum,
jikin Afeeya ya mutu sosai saboda yadda yakeyi da hancinshi kan fuskarta, ta kalli idonshi dake lumshe ta fara kokarin kauda fuskarta,
hanata yayi ta hanyar daura bakinshi kan nata a hankali yace I love uu to d moon nd bck baby,
ta sunkuyar da kanta kasa tace I love u too yayana,
yace to tunda u love me ki barni inje I promise you komin dare in na shigo gari zanzo in ganki kinji,
ta kalli cikin idonshi tace ko biyu na dare ne fa zan jira ka,
yace na yarda baby kiyi fatan Allah ya kaini lafiya,
tace to Allah ya kaimun kai lafiya ya dawo min da kai lafiya, yace ameen Afee nah,
sun daďe tare a ranar suna hira kamar kar su rabu,
Da kyar suka rabu gurin 11 ya tabbatar mata zai shigo ya ganta kafin ya tafi,.
rakiyar kura suka dingayi har saida ya gaji ya kaita har cikin daki ya tabbatar ta kwanta sannan ya tafi gida cike da nishadi, ya yi matukar kosawa Afeeya ta zama mallakinshi, shi yasan auren Afeeyah shine lst dream dinshi, yasan yana aurenta ya gama samun komai a rayuwarshi,
da wadannan tunaninkan masu dadi bacci yayi gaba da jabeer da gidan Bara’u…

Mrs tijjani shattima…
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣9⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Tun 5 saura na asuba jabeer ya farka jikinshi duk da ya jike da zufa, duk sanyin a.c dana damuna basu hanashi yawan jin zafi a yan kwanakin nan,
bayi ya shiga yayi wanka da ruwan sanyi ya ďauro alwala ya fito yayi nafila ya zauna jiran a kira sallah..

Yana idar da sallah ya zauna kan kujera ya lumshe idonshi kanshi na kallon sama,
Allah kaďai yasan tunanin da yakeyi a wannan lokacin,
sai 8 ya mike jikinshi a sanyaye ya gama shiri cikin farar shadda, yayi matukar kyan da bai taba yin irinshi ba shi kanshi saida ya faďi da ya kalli madubi,,,
saida ya gama shiryawa tsaff har zai fita daga ďakin sai kuma ya dawo ya dinga kallon ko ina ko akwai abin da ya manta bai dauka ba, drawer ya buďe ya dauko driving licences dinshi har zai rufe drawer sai yaga wasu takardu,
daukosu yayi ya dubasu yayi murmushi ya mayar dasu mazauninsu ya rufe drawer yasa kai ya fita daga ďakin,

A parlor ya tadda babanshi zaune yana karyawa ya tsuguna ya gaisheshi, ya amsa da fara’a yace sammako zakayi kenan,
jabeer yace eh baba ina son in dawo da wuri ne shiyasa,
Abida ta fito rike da cup din kunun gyaďa da plate din alale ta zauna kusa da mijinta, jabeer yace ina kwana ummi,
tace lafy lau jabeer yau dai kaka liman yayi kira irin wannan sammako hka,
jabeer yayi dariya yace na kosa inje in ga uwargidana sarautar gida shiyasa,
ta gutsiri alalen ta kai bakinta tace kace ka kosa kaje kuyi faďa har ku gaji,
yayi dariya yace kamar kin sani,
dai2 lokacin Amirah ta shigo parlorn cikin uniform itama rike da break dinta a hannu ta gaisheshi ya amsa yace miko min naki kije ki zubo wani, Amirah ta turo baki tace yaya fa nayi latti dan Allah kasa Dayyaba ta zubo maka,
alhj bara’u yayi mata dakuwa yace gidanku, zubo abincin ne zai hana ayi miki dukan latti, ajiye mishi kije ki zubo wani,
Amirah ta ajiye tana kunkuni ta wuce kitchen ta zauna ta zuba wani kunun tana sha tana mita,
shima jabeer kaďan yasha kunun ko alalen ma bai taba ba ya mike yayi sallama da iyayenshi sukayi mishi fatan Allah ya tsare hanya,
har ya shiga mota yaji kamar ana kwala mishi kirah,
fitowa yayi ya nufi parlon yace gani baba, alhj bara’u yace ban kira ka ba jabeer saidai ko umminka,
Abida tayi dariya tace muna tare a zaune zan kirashi baka ji ba,
ta kalli jabeer dake tsaye yana kallonsu yana murmushi tace ni wai me ma zakayi a daura ne ka kirkiri tafiyar gaggawa,
alhj bara’u yayi dariya yace zuciyarki ce ta kirashi kenan dan tayi mishi wannan tambayar,
jabeer yayi dariya kamar zai faďa musu sai kuma ya fasa yace ziyara kawai zanje yi ummi,
tace to Allah ya bamu ladan tare, duk sukayi dariya haďe da cewa ameen,
kallon babanshi yayi yace baba akwai maganar da zamuyi dakai akan wasu takardu suna nan a ďaki na in na dawo in shaa Allahu zamu tattauna, alhj bara’u yace Allahumma yashaa ka gaida Baba da Goggo,
yace zasu ji sosai ya fita Amirah ta biyoshi da gudu tana mishi bye bye,
hararta yayi yace Allah yasa a fasa miki jiki da dukan latti,
tayi mishi gwalo ta shige mota tana dariya tana daga mishi hannu,
shima motarshi ya shiga ya tada ya fita yana gaisawa da baba ado da sauran masu aikin gidan..

Hanyar daura ya ďauka ba tare da ya tsaya yaga Afeeyah ba saboda yana gudun bata mishi lokaci da zatayi dan yasan in har ya shiga to bazai taba tafiya da wuri ba,,
Karfe 10 da mintina ya isa gidan kaka liman, bayan ya huta yaci abinci da furah suka dinga hira dasu Goggo, basu fara aiwatar da komai ba sai da sukayi sallar azahar sannan suka fita shi da kaka liman,
suna tafe yana mishi bayanin irin mugayen tsafin da akayi ma Affan wadanda aka binnesu a cikin gidan, kaka limann yace saboda rashin imani irin na matar nan har kafin fita gida tayi mishi dan kar ma ya fita wani ya ganshi yayi mishi addu’a ko ya taimaka mishi, sannan ta katangeshi daga dukkan adduar mutane ta mantar da mutane ciwonshi in ba waďanda suke kusa dashi ba,
jabeer ya jinjina kai yace ay ni ban ďauka zaluncinta har ya kai haka ba walhy kaka, amma in shaa Allahu karshenta yazo,

wani kauye suka je a cikin kasar Nigar mai suna “Tsatsunburum (s Burum)”
kauyen bashi da nisa da zangon daura, gaba da gidan sarki sukaje kaka liman yace ya tsaya anan,
jabeer ya kalli gurin,
a katange yake da wata katuwar bishiya a ciki, kaka liman ya fito ya shiga gurin jabeer na binshi a baya, ashe wata katuwar rijiyace a cikin gurin mai cike da tarihi,
kaka liman ya kwance ledar da ya zo da ita ya fito da wasu layu da magunguna ya fara haka rami ya binnesu sannan ya ďauko wata gora a cikin jakarshi da magunguna a ciki yasa hannu a cikakkiyar rijiyar ya debo ruwan cikinta sannan suka fito daga gurin,
jabeer dai kallon gurin yakeyi ga rubutu a jikinshi amma rubutun ya fara gogewa,
ya kalli kaka yace kaka amma wannan rijiyar tana kunshe da tarihi ko,
kaka liman yace kwarai kuwa,
abin al’ajabi ya taba faruwa a gurin nan,
ya nuna mishi wata bishi dake dan nesa kaďan da gurin yace kaga waccan bishiyar, jabeer yace eh kaka, yace to daidai saitinta da gurin kiwon shanu ne, shanaye da yawa ake kiwo a gurin, “akwai wata saniya guda ďaya kullum aka bata abinci sai taki ci haka ruwa, saidai a ganta kullum da yamma tazo nan gurin da muka shiga kafin a katange shi ta daďe a gurin har sai dare take komawa cikin yan uwanta, kullum haka takeyi sam bata cin abincin da ake basu, ana cikin haka rannan sai mai shanun ya dinga binta a baya dan ganin abinda takeyi a gurin, yana zuwa gurin yaga ta kafa kanta a wani ďan tsukukun rami tana shan ruwa, tana gamawa yaga ta kwanta karkashin bishiyar nan lokacin tana karama sosai a gurin take bacci har dare sannan ta koma cikin yan uwanta, in takaice maka dai wannan saniyar tunda ake kiwonta bata taba cin abinci ba wannan ruwan shine ya zamo ruwa da kuma abincinta sannan wannan bishiyar ta zamo gurin hutu a gareta har ta mutu a gurin, bayan ta mutu ne mutane suka haka wannan ramin ya zamo rijiyar da bata taba kafewa ba duk wahalar ruwan da akeyi a garin tofa wannan rijiyar na nan da ruwanta sannan wannan bishiyar tana nan bata taba fadi ba shekaru fin 100 dan nima labari aka bani,
jabeer yace ikon Allah shine aka katange ta, kaka liman yace kwarai kuwa kuma cikin ikon Allah ruwan cikinta yana zama waraka ga duk wanda ya yarda da Allah kamar yadda ta kusugu take,
jabeer yace Allah ya kara ma Annabi daraja, kaka yace ameen jabeer shiga muje dan zan ga Aminina “Maina dogon yaro” shima akwai abin da zai bani daga nan mu wuce cikin daura mu karasa,
jabeer yace to kaka, suka shiga mota suka wuce jabeer na kallon girman bishiyar yana tasbihi ga Allah…

Sai bayan magriba suka gama komai suka dawo gida a gajiye,
dakyar jabeer ya iya taba abincin da Goggo ta kawo mishi sauri2 dan yana son ya dauki hanyar gida komin dare,
babu yadda basuyi dashi ba akan ya kwana yace samm bazai kwana ba dan gobe da wuri yake so fara aiwatar da aikin cikin gidansu Affan wanda shine mataki na karshe na aikin,,
sai da yayi isha’ sannan kaka liman ya fito yayi mishi rakiya yana kara nuna mishi yadda zaiyi amfanin da maganin yana kuma mishi faďa akan yayi taka tsantsan da oyizah,
jabeer ya shiga mota yace in shaa Allahu kaka zanyi duk yadda kace, mun gode sosai, kaka liman yace to Allah ya tsare kayi tuki a hankali ďan boko, jabeer ya tada motar yace baka da matsala tsoho, yaja motar suna ďaga ma juna hannu, saida yaga kulewar motarshi sannan ya juya gida,
haka kawai ya tsinci gabanshi da tsananin faďuwa,
a waje ya zauna yana bin sawun motar jabeer da kallo yana mishi adduar Allah ya kiyaye hanya…
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣0⃣ By Aysha Ya’u Kurah

★ 9:54pm ★

Tun bayan magriba hadari mai tsananin duhu ya taso yana kokarin haduwa a gabas,
iska ce mai dadi taketa kaďawa a wannan lokacin har zuwa karfe 9:32pm, lokacin ne hadarin yamma ya kusa haďuwa da na gabas, iska mai karfin gaske haďe da guguwa da walkiya su keta tashi ta ko’ina kamar zasu tashi gidaje da motocin biladama,
yaf yaf ruwan feshi ke busawa a cikin iskar,

A wannan lokacin gudu jabeer yakeyi cikin motarshi yana Allah Allah ya isa kano kafin goma ko kuma goma daidai,
wuce motoci yakeyi yana tafiyarshi cikin kwanciyar hankali yana wiping yayyafin dake sauka a kan glass din motarshi, karfe 9:50 ya rage saura k.m baifi 15 ba ya shigo garin kano, murna ya dinga yi dan yasan in shaa Allahu kafin 10:30 zaiga Afeenshi,
har ya dauko wayarshi zai kirata sai ya fasa so yakeyi kawai ta ganshi kafin lokacin da ya daukar mata..

Wani haske ya gani ya gifta gabanshi hade da girgiza mai karfi wacce tayi sanadiyyar fitar tayar motarshi ta gaba,
runtse idonshi yayi sosai yana kalmar shahada saboda yadda yaji shi a sama motar na juyawa sosai, wasu masu trailer sukayi parking gefen hanya suna salati cikin tsoro saboda yadda motar ke wulwulawa a sama,
saida tayi minti uku a haka sannan ta daki wani katon dutse ta tarwatse a kasa dai2 lokacin ruwa mai karfi ya tsuge haďe tsawa, mutanen gurin kowa ya kunna full light dinshi suka karasa kusa da motar jiki na rawa saboda basu taba ganin accident irin wannan ba,
ba karamin dagargajewa motar tayi ba, nan da nan suka fara kokarin ciro mutumin da suka gani a gaban motar, da kyar suka iya ciro jabeer saboda wani karfe da ya shige cikin hancinshi ya bullo ta kanshi,
kuka mutanen gurin sukeyi suna salati saboda sun tabbatar da wanda suka ciro a cikin motar nan bashi da sauran rai,
da sauri suka soma bincika aljihunshi dan motar babu abin dauka a cikinta, driving licences suka gani sai kudin da ya baci da jini ko ta ina,
farar shaddar jikinshi ma babu wanda zaice fara ce dan duk ta koma ja, basu samu adress dinshi jikin d.l din ba sai dai sunanshi,
daukarshi sukayi cikin mota suka shigo cikin garin kano suka zarce police station dashi,, (innalillahi wa inna ilahir rajiun)

A kuma dai2 wannan lokacin Affan na zaune kusa da daddynshi suna dan taba hira duk da rabin hirar tasu shirme ce,
a hankali ya karkatar da kanshi yana kallon daddy idonshi ya ciko da kwalla yace daddy yau ma kaga har dare yayi abokina baizo ba, ya kalli inda ya tara wasu fararen duwatsu guda 8 na kirga yace daddy kagani yau kwana 8 kenan,
alhj basheer ya shafa kanshi yace kayi hakuri Affan kasan yanata shirye shiryen biki dole ka rage ganinshi,
Affan ya marairaice fuska yace to daddy ni yaushe zaka min aure, alhj basheer yayi dariya yace duk ranar da ka shirya Affan,
Affan yayi dariya shima yace daddy ay na shirya, daddy yace to wacece matar,
Affan ya rufe idonshi yana girgiza kai fuskar Afeeyah nata mishi yawo a cikin kwayar idonshi da kwakwalwarshi,
yayi saurin bude ido yace Barbie din jabeer, daddy ya kara sautin dariyarshi yace wacece kuma barbie, Affan yace AFEEYAH, daddy yayi dariya yace Afeeyar da jabeer zai aura,
Affan ya gyada kanshi yana dariya yace eh daddy ay yace zai bani ita ta dawo nan gidan da zama,
daddy yayi dariya yace to naji tashi kaje ka kwanta kaga ruwa na neman tsugewa,
Affan ya mike yana murna yana fadin daddy zai aura min barbie..
dariya alhj basheer yayi ya mike ya wuce dakinshi dan oyizah tayi tafiya tun da safe..
Affan na shiga ďaki ya haye kan gado yanata wakar abu ďaya, tsawar da akayi mai karfi tayi daidai da faďuwar gabanshi, mikewa yayi daga kan gadon ya leka window yana kallon ruwan da ya tsuge kamar da bakin kwarya,
Affan cikin tsoro ya rike kirjinshi dake tsananin bugu ya fita da gudu yayi dakin daddy,
da kyar daddy ya lallabashi suka kwanta tare amma fa bacci ya kaurace a idonshi dan daga ya runtse idonshi to fuskar jabeer zai gani yana kuka mai tsanani..

Hakan ta kasance da Afeeyah, wannan tsawar da akayi ita ta farkar da ita daga baccin da bata san tayi ba mai cike da mafarkai,
agogon wayarta ta duba taga 9:56 ta zauna tana sauraron zubar ruwan sama tana kara duba agogo kirjinta na harbawa da sauri,
10:20 ta kira wayar jabeer taji ta akashe, a hankali ta koma bayan hajja ta kwanta tana duba wayarta ko zata ji kiranshi shuru taji har 11 ta gota,
a hankali ta fara rero kuka tana kiran sunanshi,
kamar a mafarki hajja taji kukan ta farka da sauri tace yanzu ke Afeeya har yanzu baki bar kukan nan ba,
wani irin iskanci ne wannan,
Afeeyah tace hajja sha ďaya fa ta wuce kuma shi ya cemin goma da wani abu zai dawo,
hajja cikin masifa tace shikenan kuma ana wannan ruwan in ya dawo sai yaki zuwa ya huta yazo gurinki saboda gaki yar gwal ko,
Afeeyah ta shige jikin hajja tana kuka sosai tace hajja fa ya kashe wayar shi ne, kuma tun jiya fa ban ganshi ba, dan Allah ki taimaka min wallhy bazan iya bacci ba in ban ganshi ba,
hajja taji tausayinta sosai tace to yi shuru ya isa haka,
kinga yanzu dare yayi babu mamaki wayarshi ta mutu babu charge kuma bayason yazo ya sameki kina bacci kinga kuma ruwa akeyi kina son ya fito cikin ruwan nan ne, Afeeyah ta girgiza kanta,
hajja tace to ki mishi uzuri gobe nasan tun kafin ki tashi daga bacci zaizo kinji, Afeeyah ta gyada kanta tana share hawaye haďe da ajiyar zuciya,
hajja ta kwantar da ita tace yi addu’a kiyi bacci,
Afeeyah ta fara karanto adduoi hawaye na zubo mata ta gefen idonta a zuciyarta tana jin haushin jabeer na kin cika alkawarin da yayi mata, yanzu haka zanyi bacci banganka ba yaya jabeer, atlst ko waya ya kunna naji muryarshi zan dan rage wani zafin abinda ta dinga fadi a zuciyarta kenan, baccin ranar a gurin Afeeya rabi da rabi ne, saboda duk farkawa saita duba wayarta taga ko ya kirata,
( Allah sarki Afee zanso ace kinsan gani da muryar jabeer ma bazaki kara ji ba bare har kiga missd call dinshi,)

Abida ma juyi take tayi idonta na kan agogo, babu irin kiran da batayi ma wayar jabeer ba amma taki shiga,
Alhj bara’u yace Abida ya kamata ki cire duk wasu tunani a ranki kiyi addu’a ki kwanta kiyi bacci in shaa Allahu babu abinda ya sameshi babu mamaki mota ce ta bashi matsala,
Abida tace matsalar mota sai tasa ya kashe wayarshi yasan dole hankalin mu zai tashi alhj,
alhj bara’u da shi kanshi daurewa yakeyi yace kinsan sharrin netwk mu zuba ido zuwa da safe mu gani, Abida dai uhum kawai tace saboda yadda takejin nauyi a kirjinta, rungumeta yayi ta baya yana faďa mata kalamai masu kwantar da hankali dan in ya bari tasan shima hankalinshi a tashe yake to fa zata kara daga hankalinta fiye dashi ma,
Kaka liman ma ya kira har sau uku yaji ko ya iso,
shima hankalinshi a tashe yake saboda jin har lokacin jabeer bai isa gida ba…

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣1⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Washe gari tunda alhj Bara’u ya idar da sallah yake zaune kan dadduma,
hankali tashe ya kalli Abida da ta zuba tagumi tana jan carbi yace Abida har yanzu wayar yaron nan bata shiga ba ko,
Abida ta gyada kanta kawai tana kallonshi,
yace innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Allah dai yasa jabeer lfy yake dan bai taba irin wannan abun ba, ko wayarshi nada matsalar charge ay duk inda yake bazai rasa wayar da zai kiramu ya sanar damu halin da yake ciki ba,
Abida tace uhummm zuciyata tana faďamin duk inda jabeer yake ba lafiya yake ba,
alhj bara’u yace ki daina faďin haka, haka kawai zuciyarki ta dinga kitsa miki mugayen tunani, ya mike tsaye yana duba lokaci yaga 7 har ta wuce ya fita daga dakin yayi hanyar waje,
Abida ta share kwallar data ďan fito daga idonta tace ya Allah ka sassauta min zafin da nake ji a zuciyata ka bani ikon jure duk wani abu da zanji game da jabeer,

Malam Atiku na kwance idonshi a lumshe da radio a gefenshi yanajin labaran karfe 7 kamar yadda ya saba kullum, bayan an gama labarai akan halin da kasarmu take ciki da kuma na kasashen ketare, sai aka sako labaran kwallon kafa, cikin kosawa ya mika hannu zai kashe radion saboda sam labaran kwallon kafa basa gabanshi,
tsayar da hannunshi yayi sakamakon jin sanarwar hatsari da akayi anan hanyar shigowa gari wanda akace an tsinci gawar saurayi mai suna Jabeer Bara’u, wadanda suka cinci gawar sunyi saurin mikashi ga hukumar yansanda, yanzu haka yana can asibitin Aminu kano, ga duk wanda yaji kuma yasan inda yan’uwan baw—– ay malam Atiku bai karasa sauraro ba ya diro daga kan gado yana faďin innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
ko takalmi baisa a kafarshi ba ya fita waje da sauri jikinshi na rawa,
a kofar gida ya samu alhj bara’u zaune kan dakali, da sauri alhj bara’u ya mike yace malam Atiku lafiya na ganka haka ko takalmi babu,
Malam Atiku ya saki ajiyar zuciya yace tunda na ganka zaune lfy lau ay alhamdullh, wallhy wata sanarwa naji yanzu a radio akan wani hatsari da ya faru a daren jiya kuma sai naji an kira sunan jabeer shiyasa hankalina ya tashi,
Alhj Bara’u ya mike yana salati kamar zararre, malam atiku yace alhj lafy,
Alhj bara’u baki na rawa yace jabeer dina ne,
jabeer dina ne wallhy, tun jiya muke neman layinshi bamu samu ba, innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
malam atiku yace lahaulu wala kuwwat illa billah, alhj bara’u ya rike hannun malam atiku ya rasa ta inda zai fara sai janshi yakeyi yana fadin muje asibitin da suka ce, malam Atiku zaiyi magana parking din motar alhj basheer ya dakatar dashi,
da sauri ya fito yace lafy alhj bara’u ,
alhj bara’u ido zuru2 yace jabeer ya tafi,
alhj basheer cikin rudewa yace ina ya tafi,
malam atiku yace karka yanke hukunci alhj muje asibitin tukunna, in shaa Allahu ma bashi bane, alhj basheer yace wani asibiti,
malam atiku ya fada mishi abinda yaji a radio, alhj basheer da sauri yace kuzo mu tafi asibitin,
alhj bara’u da bakinshi bai daina salati ba ya shiga motar jikinshi a sanyaye suka wuce Aminu kano T.H,

Tunda suka shiga gaban alhj bara’u ke faduwa har suka karasa cikin mortuary, suna shiga aka nuna musu D.L din jabeer sannan aka karasa dasu inda yake,
Juyawa alhj bara’u yayi da ya kalli gawar sau ďaya ya fara addua cikin sambatu kamar tababbe,
D.L din kawai yake kallo yana jujjuyashi yanaso ya gasgata shin wannan gawar ďanshi ne da gaske ko mafarki yakeyi,
dafashi alhj basheer yayi yana zubar da hawaye yace alhj muje kayi signn mu amshi gawarshi muje ayi mishi sutura,
alhj bara’u bai kalleshi ba yace kaima mahaifinshi kaje kayi signn din, Allah ya amshi bakuncinshi yana gama faďin haka ya fita,
nurse din dake tsaye a gurin ta fashe da kuka tace alhj kuje kawai no need, Allah ya jikanshi da rahama,
nan aka gunguro gawar jabeer aka sata a ambulance suka wuce gida cikin jimami suna kallon alhj bara’u da ya kurawa d.l din jabeer ido,
kallon motar aka dinga yi a layin wasu suka bita dan ganin inda zata tsaya, motar na tsayawa a kofar gidan, alhj bara’u ya fito da sauri ya shiga ciki,
a parlor ya tarar da Abida Amirah na tsaye a kanta da ruwan tea da magani a hannunta, kallon Amirah yayi kamar babu abinda ya faru yace har yanzu baki shirya kin wuce makaranta ba,
Amirah tace nayi wanka baba yanzu zan gama in—, sallamar su malam Atiku da wadanda suka shigo da gawar jabeer ita ta hana amirah karasawa,
da sauri Abida ta mike tabisu da ido har aka shimfiďe gawar jabeer a kasa,
cikin firgici ta karasa kan gawar zuciyarta na dukan uku uku ta tsuguna ta buďe fuskar da tayi faca2 da jini, runtse idonta tayi da sauri tana fitar da wani irin numfashi tace nasani jabeer, zuciyata ta sanar dani, Alhamdullilah da Allah yasa aka tsinci gawarka akan lokaci, Allah ya rahamceka jabeer, yadda ka faranta mana kayi mana biyayya Allah ya faranta maka a cikin kabarinka dan nan ne gidanka na gaskiya, Allah ya sanya aljanna firdausi ta zama makoma a gareka,
ta shafa fuskarshi a hankali tace na yafe maka,
na yafe maka jabeer,
ta mike da sauri ta wuce daki alhj bara’u ya bita,
Amirah kasa gasgata gawar tayi dan gaba daya ta kasa fahimtar abinda ake nufi, ta kalli su alhj basheer da suke sharar hawaye tace daddy, Abba, me ya samu yaya jabeer, alhj basheer yace Amirah addua zakuyi mishi dan wanda ya fimu sanshi ya karbi abinshi,
Amirah ta saki kofin hannunta ta tsuguna a gabanshi tana kuka mai tsanani tana kiran sunanshi,
da kyar alhj basheer ya rarrasheta yasa Dayyaba dake tsaye tana kuka ta shiga da ita ciki,

Mahmud kanin Afeeyah ya shiga gida da gudu ya ajiye biredin da ya siyo a tsakar gida ya karasa ďakin hajja,
hajja na zaune tana gyaran wake, Afeeya kuma tana kwance jikinta ya ďau zafi sosai saboda zazzabi, fadowa dakin mahmud yayi, hajja tace haba mahmu irin wannan shigowar ba sallama ay sai ka tsoratani, yace hajja motar gawa ta asibiti na gani kofar gidan alhj bara’u kuma naji mutane suna cewa yaya jab– Afeeya ta diro daga kan gado tayi ma mahmud wani irin riko tace me ya sameshi, mahmud cikin jin zafin rikon yace ban sani ba mutane sunce sunga an fito dashi cikin jini…

Mrs tijjani shattima…
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣2⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Wurgi Afeeyah tayi da mahmud ta fita da gudu,
duk irin kiran da hajja take mata baisa ta tsaya ba,
da gudu ta shiga gidan ta tarar dasu baba ado zaune da wasu mutane sunyi tagumi a bakin gate, da sauri ta karasa kusa dashi tace baba ado me ya samu yayana?,
baba ado ya kauda kanshi da sauri yana share hawayen dake zuba a idonshi, Afeeyah ta bar gurin da gudu ta shige cikin gidan,
murďa kofar parlon tayi da karfi kamar zata balleta,
tana shiga ta dinga bin mutanen dake parlon da kallo,
ganin mutum kwance cikin jini a kasa yasa zuciyarta bugawa da karfi,
a hankali ta fara motsa kafarta tana tafiya har ta isa gabanshi,
tsugunawa tayi ta yaye abin da aka rufe mishi fuskarshi da shi, gaba ďaya hanyoyin sadarwa na jikin Afeeyah suka daina aiki sakamakon ganin fuskar jabeer,
kallonshi ta tsaya yi bata ko kiftawa,
alhj basheer ya taso ya karaso gurinta ya ďagota dakyar dan jikinta a sake yake kamar wacce bata da rai,
zaunar da ita yayi akan kujera ya fara mata nasiha, ko kaďan bataji abinda yake cewa ba idonta na kan jabeer da alhj bara’u da mahaifinta ke kokarin ďaukarshi suyi mishi wanka,
alhj basheer ya girgizata yace Afeeyah kina jina,
lumshe idonta tayi lokacin da aka fita da gawar,
alhj basheer zaiyi magana hajja ta shigo da gudu tana faďin innalillahi wa inna ilaihir rajiun, me yasamu jabeer alhj, na shiga uku na lalace, alhj basheer yace dan Allah hajja kiyi shuru kar gidan ya rikice adduarmu jabeer yake bukata ba kuka,
hajja ta zauna tana kuka tana fadin kukan ne babu mai iya hana shi fita alhj,
ta kalli Afeeyah da idonta ke lumshe har lokacin ta riketa sosai ta kira sunanta har sau uku taji shuru,
ta girgizata da karfi tace ki bude idonki Afeeyah, nasan abinda kikeji dan Allah kiyi tawakkali, kar wata cutar ta kama ki,
dan Allah Afeey— Afeeyah tace hajja me kika gani yanzu, kuka nakeyi ko me, ba tawakkalin nayi ba,
me kukeso inyi, ku faďa min me zanyi yanzu hajja,, kome kukace inyi zanyi walhy,
alhj basheer ya fita da sauri saboda kukan da yaci karfinshi yasan sam Afeeyah bata cikin hayyacinta,
hajja cikin kuka tace addu’a zakiyi Afeeyah, addu’a jabeer yake bukata,
Afeeyah ta bude idonta sosai tace hajja a ina zanyi adduar,
hajja ta rungumeta tana sheshshekar kuka tace a bakinki zakiyi ta,
Afeeyah tayi yake tace hajja kunce kar inyi kuka, kuma ku gashi kuna yi dan Allah kiyi shuru bari in shiga gurin ummi,
hajja ta rike hannunta suka shiga gurin Abida inda makota suka kewayeta,
tana ganin Afeeyah ta sunkuyar da kanta kasa sai a lokacin wasu hawaye masu zafi suka fito daga idonta,
Afeeyah tace ummi kuka kikeyi, daddy yace kar muyi kuka,
ta kalli Amirah tace Amirah dan Allah ki faďa min yadda zanyi hawaye su fito a idona, Amirah ta fada jikinta tana kuka sosai, Afeeyah tace dan Allah ku fadamin yadda zanyi, zuciyata zata buga ku taimakeni inyi kuka ko zan samu saukin nauyin da zuciyata tayi,
Alhj bara’u ne ya shigo ďakin shima idonshi jajur yace Abida kuzo kuyi mishi addu’a an gama shiryashi,
Abida kanta a kasa tace kuje kawai rahamar ubangiji ita kadai nake mishi fatan samu a kabarinshi, Afeeya ta mike ta fita da gudu a tsakar gida taga gawar an shiryata cikin likkafani,
da gudu ta karasa bata lura da mutanen da sukayi dafifi a gurin ba ta faďa kan gawar tana shafawa,
a hankali tace yaya jabeer alkawarin da kayi min kenan, meyasa zaka tafi ka barni, saida nace maka mu tafi tare kaki yarda ka tafi kai kadai yanzu ka faďamin yadda za’ayi in cigaba da rayuwa babu kai, meyasa bakayi tunanin abin da mutuwarka zata haifar a cikin zuciyata ba, dan girman Allah yaya jabeer ka tashi karka tafi ka barni, kai kaďai gareni,
malam atiku ya matso kusa da ita ya dafata yace Afeeyah Allah baya barin wani dan wani yaji daďi, Allah ba ruwanshi da duba shakuwarku,
Allah ya kaddara— ta katseshi ta hanyar bige hannunshi tace wace irin kaddarace wannan, meyasa bata daukeshi tun kafin inzo duniya ba, sai yanzu zata zo ta dauke min shi a lokacin da nake bukatarshi,
ta mike tsaye tace abba dan Allah ka fadamin yadda zan iya cigaba da rayuwa, kasan dai bazai yiwu ba,
malam atiku ya rungume yarshi yana kuka sosai, yace Afeeyah nasan yadda kikeji,
ta sakeshi tana girgiza kai tace wallhy abba babu wanda yasan yadda nakeji sai yaya jabeer,
ta kankameshi tace kai kadai kasan yadda nakeji, dan Allah ka tashi,
duk rashin imaninka sai ka zubar ma da Afeeyah hawaye, babu yadda ba’ayi a banbareta jikin gawar ba amma abin ya faskara tana kwance kanshi tana sambatu babu ko ďigon hawaye a idonta,
dago kanta tayi saboda ganin mutum yayi kneel down a gefenta yana shafa tun daga kafar jabeer har kanshi,
kallonta yayi yana kaďa kanshi hawaye na fitowa a idonshi yace barbie yau kwana 9 banga abokina ba, yanzu kuma naga sun rufeshi da fararen kaya ina zasu kaishi,
kice mishi ya buďe idonshi inason muyi magana, I missd him so much,
sai a lokacin Afeeyah ta kara maida kanta kan jabeer ta fara kuka mai tsanani tana fadin maganganun da ita kanta bata san suna fitowa daga bakinta ba,
Affan ma duk da baya cikin hankalinshi yaji a jikinshi wani mummunan abu ya samu abokinshi,
da kyar aka iya banbare Afeeyah jikin gawar jabeer,
ana sashi cikin makara ta kara fashewa da kuka tana faďin dan Allah ku dawo min dashi wallahi zai dawo gareni, dan Allah karku fita dashi, ta dinga fisge2 jikin wadanda suka riketa tana fadin a dawo dashi ko ya mutu a bar mata gawarshi,
suna shashi a mota Afeeyah ta saki wani gigitaccen ihu ta faďi kasa sumammiya….

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣3⃣ By Aysha Ya’u Kurah

A hankali ta fara buďe idonta da yayi mata nauyi sosai,
dishi2 take gani tayi saurin mayar dasu ta runtsesu tana fitar da wani irin wahalallen numfashi,
muryar Anty Asiya ce yasa ta kara bude su ta kalleta,
anty Asiya ta shafa kanta idonta cike da kwalla tace sannu Afeeyah, babu inda yake miki ciwo,
ta lumshe idonta tana girgiza kai hawaye na zuba a gefen idonta, anty Asiya ta fara yi mata nasihar da daga ji itama na karfin hali ne,
saida ta daďe tana mata nasiha sannan ta tashi ta fita,
da sauri safnah ta dawo gefenta ta rike hannunta tana zubar da hawaye tace Afee,
Afeeyah ta kara runtse idonta hawaye na gangarorowa cikinsu kamar an saki ruwan pampo,
Safnah ta kwanta a jikinta cikin muryar kuka tace don’t stop dis tears Afee let it flow nasan yadda kikeji, cry as much as u can,
Afeeyah ta kara fashewa da kuka, suka dinga yi ita da safnah dake jin mutuwar ta ko ina a cikin jikinta,
sun daďe suna kuka kafin safnah tayi shuru ta mike tana kallon Afee,
safnah tace Afee tashi kiyi sallah kinsan fa bakiyi azhar ba gashi har la’asar ta wuce, dakyar Afeeyah ta gyaďa mata kai tace shikenan safnah sun kaishi sun birne min shi ko,
shikenan ni yanzu bani da wani sauran gata a duniya ko, dan Allah safnah ki roka min Allah in mutu in bi shi dan wallhy bazan iya rayuwa ba,
Goggon daura ce ta shigo cikin dakin ta zauna gefensu tace zaki iya rayuwa Afeeyah,
wannan kukan da kikeyi babu wanda zai hanaki yinshi domin shine kadai ne zai rage miki raďađin da kikeji, ki sani jabeer yayi mutuwar da ko wane musulmi zaiso yayita, ya mutu a daren alhamis aka kaishi ranar jumma,a, ya mutu a hanyarshi ta ziyara kuma da kyakykyawar niyya a zuciyarshi,
ko wannan muka tuna ya isa yasa mu ji dadi saboda yayi mutuwar da akeso,
tashi maza kije kiyi sallah ki karfafa zuciyarki kiyi mishi adduar samun rahama wannan ita kaďai ce hanyar da zaki nuna tsantsar soyayyarki gareshi yanzu,
Afeeyah ta gyaďa kanta ta mike dakyar ta shiga bayi..

Karfe biyu saura motar oyizah tayi parking a cikin gida,
tayi mamakin rashin ganin “saunanta” a waje yazo tararta kamar yadda ya saba, ciki ta wuce cikin farin ciki tana kwala kiran sunan Affan,
salma da farida ta tarar a parlor suka yi mata sannu da zuwa, ta amsa haďe da zama tace ina “rakumi na” yau banga yazo yi min oyoyo ba,
salma ta tabe baki tace yana can gidan rasuwa kinsan Abokinshi dan girman kan nan ya wullah,, oyizah cikin tashin hankali ta mike tace how comes ya fita daga gidan nan,
farida tace nayi mamaki nima mummy, Alhj basheer yayi gyaran murya ya fito daga ďaki,
oyizah ta boye tashin hankalinta tace sannu da gida “ya hajj” yace yauwa safiya kin dawo lafiya, tace lfy lau,
ya kalli salma yace kun shiga gidan gaisuwan kuwa,
suka turo baki suka ce yanzu zamu shiga da mummy,
alhj basheer yace ya kamata bari in koma gurin zaman makoki,
oyizah ta matso kusa dashi cikin kissa tace alhj ina ďana yake,
alhj basheer yayi murmushi yace kice dan rigima, yana can wai shi bazai dawo gidannan ba sai an dawo mishi da abokinshi,
oyizah bata san sanda tace to waye ya fitar dashi daga gidannan,
alhj basheer cikin rashin fahimta yace ban gane ba,
tayi dan murmushi tace naga ya ďade bai fita bane bana son ya fita shi kaďai wani abun ya sameshi,
alhj basheer yace Ayya, baba ado mai gadi na fara turowa ya taho dashi saboda yazo yayi sallama da abokinshi duk da ba wani hankali gareshi ba,
sai baba ado ya dawo yace wai yaki zuwa daga sunzo bakin gate sai ya juya a guje,
shine naje da kaina na ďaukoshi dakyar yana ihu ya iya fitowa daga cikin gidannan,
saida muka shiga gidan alhj bara’u sannan ya iya buďe idonshi, kuma kinsan ya gama tsorata da gidannan dan kiran namun daji kawai yakeyi wai gasu nan zasu cinyeshi a bakin gate,
oyizah da gumi ya tsatsafo mata tace ayya my baby ni na faďa mishi in ya fita akwai animals da zasu cinyeshi saboda ina tsoron ya fita yaje wani abu ya sameshi,
alhj basheer yace aiko ya tsorata sosai dan yace shi acan gidan alhj bara’u zai zauna nan gidan akwai lions da sauransu,,
oyizah ta haďiye miyau tace yanzu zanje gidan ay sai mu dawo gida,
alhj basheer ya ďaga kafaďa yace sai kinzo,, sama oyizah ta wuce tana huci, a zuciyarta tace alhj ya fara bata mata aiki, shikenan ya karya wannan kafin da ta daďe da yinshi, wanka tayi sauri tayi ta shirya suka wuce gidan rasuwa…

Tun a kofar gida inda maza sukayi dafifi ana karbar gaisuwa gaban oyizah ya faďi saboda haďa ido da tayi da wani tsoho mai matsanancin kama da jabeer,
saidai shi ya tsufa sosai, maida kanta tayi gurin Affan da ya lafe jikin tsohon yana tsotson hannu idonshi a lumshe,
dakyar ta iya gaisar da mutanen gurin saboda irin kallon da tsohon nan ke mata,
cikin gida suka shige ita da yayanta sai a sannan hankalinta ya kwanta,
bayan tayi gaisuwa sama2 sai suka fito ta tsaya daga ciki ta aika farida ta kira mata Affan,
farida ta wuce ta keta gurin mazan saboda rashin kunya tasa hannu zata fara bubbuga affan,
da sauri tsohon nan ya tare hannunta yace ke lafiyarki,
ta tsaya kerere tace mummy ce tace in kirashi mu tafi gida,
ya kalleta sosai yace kice wai bacci yakeyi,
farida ta turo baki ta juya taje ta faďa ma oyizah sakon wannan tsohon,
hankalin oyizah ya kara tashi tace kuzo muje, suka fito, har ta fara tahowa gurin da suke sai ta canza hanya,
farida tace mummy gasu can fa,
oyizah tace kuzo mu tafi anjima zan sa a kirashi,
sai a lokacin kaka liman ya ganeta, a zuciyarshi yace tabbas bazaki iya hada ido dani ba dan mugu na tsoron kwayar idona, ya shafa kan Affan a zuciyarshi yana kitsa abubuwan da zaiyi ta karkashin kasa ba tare da wani ya sani ba bare ta kara ajalinshi….

Oyizah na shiga gida ta fara safah da marwah tana sake2 a zuciyarta,
fitar Affan daga cikin gidannan ba karamin tashin hankali bane a gareta,
to wani tsoho ne wannan da ya firgita ganinta kamar wani aljani, yanzu shikenan Affan yana can gurin dubban mutane kuma tasan dole wasu zasuyi mishi addu’a,
Noooo bazai yiwu ba ta fadi da karfi haďe da tashi ta kara fita daga gidan….

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:34] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣4⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Tun kafin ta karasa take kiran wayar alhj basheer bai ďauka ba saboda suna addu’a a gurin zaman makoki, tana karasawa taga maza sun kara yawa a gurin ta kalli gurin da tsoho da Affan suke bata gansu ba,
cikin tashin hankali ta wuce cikin gidan kamar zata rusa ihu,
a waje ta tarar da Amirah ta rako yan makarantarsu tace “ke” ina Affan yake,
Amirah ta fara waige2 sannan ta juyo ta cigaba da magana da kawayenta,
oyizah ta hassala tace ba da ke nake magana ba Amirah,
Amirah tace ay bansan dani kike ba naji kamar “ke” kikace, yana ďakin yaya jabeer,
oyizah ta harareta a hankali tace mara kunyar banza, ta wuce dakin jabeer,

Kwance ta sameshi ya kura wa makeken hoton jabeer ido baya ko kiftawa,
cikin fushi tasa hannu ta make kanshi da karfi,
a zabure ya mike yana kallonta,
hararshi tayi tace wuce muje gida, bai ďauke idonshi a kanta ba ya girgiza mata kai alamar baza shi ba,
oyizah hassala matuka tace ni kake ma musu Affan,
ya kara marairaicewa yace ni abokina nake jira,
ta damko hannunshi tace dan ubanka wa ya faďa maka wanda ya mutu yana dawowa, wuce muje kafin in ji maka ciwo,
ya noke wuya yace ni bazan tafi ko ina ba,
ta janyoshi da karfi ta hankaďo shi waje,
wani irin ihu ya saka ya ruga bayan Asiya da ke tahowa gurin,
Asiya ta rikeshi tace me ya sameka Affan, Affan ya shige bayanta yana nuna mummy da ta taho tana huci kamar kumurci, tana karasowa ta kai hannu zata kara rikeshi ya kara sa ihun da ya maido da hankalin mutane da yawa gurinsu,
Asiya tace me yayi miki ne wai,
oyizah ta harareta zata kara rikeshi Asiyah ta rike hannunta tace wai me yake faruwa ne, ki kyaleshi mana ko dole ne,
oyizah ta shaka sosai ta kalli yawan mutanen dake gurin zuciyarta na zafi saboda ganin Affan ya fara mata musu,
ta kalli Affan fuskar nan babu annuri tace ka wuce muje gida, Affan ya noke wuya yace ni babu inda zani,
Abida da rabon da tasa Affan a idonta tun kafin ya fara ciwo ta fito ta riko hannunshi tace zo muje ciki,, kaci abinci ko,?
ya gyada kanshi tace to zo muje anjima abokinka zai dawo sai ya rakaka gida kaji,
ya kara gyaďa kanshi cikin murna suka fara tafiya,
da sauri oyizah tasha gaban Abida tace sakeshi tunda babu abinda kika haďa dashi,
Abida tayi mata kallon banza tabi ta gefenta ta tura Affan gaba suka wuce yana waigen mummy dake mishi wani irin kallo, masifa ta fara yi tana zage2 kamar tababbiya dan gani takeyi zasu bawa Affan maganin da zai maido mishi da hankalinshi ya tona mata asiri, dakyar suwaiba ta rarrasheta suka wuce gida suna kulla munafurcinsu..

Kuka sosai oyizah keyi a gaban alhj basheer akan ita a dawo mata da ďanta,
ta share hawayenta tace shekara uku kenan ina wahala dashi sai yanzu zaka barshi can wani guri kace ya kwana,
wallhy alhj bazan iya yin bacci ba yau in affan bai dawo gida ba,
alhj basheer ya juyo yace haba safiya, na yau dai kaďai sai kace wanda zai zauna a can dindindin,
ta harzuka tace kasan abinda zasu bashi yau ďin,
yace kamar yaya abinda zasu bashi, me zasu bashi kuwa, oyizah ta saita kanta tace ina nufin kasan baya cin komai in ba ni na bashi da kaina ba, ta kara fashewa da kuka tace yanzu Allah kaďai yasan yunwar da yakeji,
alhj basheer cikin jin dadin kulawarta ga danshi yace karki damu safiya Affan na can cikin koshin lafiya kuma yaci abinci sosai dan abin har mamaki ya bani,
kuma kinsan ďan zaman nan da yayi a gurin makoki yau har sallah yayi da kanshi saboda ganin mutane nayi,
oyizah ta mike cikin kidima tace alhj kana yi wa Allah kaje ka dawo min da ďana,
alhj basheer yace wai bakiji abinda nace miki bane, ki bari zuwa gobe mana,
ta girgiza kanta ta wuce ciki tana kuka tana faďin dan kaga na damu dashi ne shiyasa kake nuna min ba ni na haifeshi ba,
alhj basheer yayi murmushi a zuciyarshi yana kara jin son oyizah saboda yadda take nuna kulawarta ga Affan. ..

Oyizah taci kuka a wannan daren dan ta hakikance wasu daga cikin abubuwan da tayi ma Affan sun warware, tunda har Affan ke iya mata musu kuma har yayi sallah,
wani irin ihun takaici tayi da ta kara tuno da Affan na can gidansu jabeer kuma Allah kaďai yasan abinda zasu bashi…..

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣5⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Washe gari tun asuba oyizah taje gurin alhj basheer ido luhu2 saboda kuka da rashin bacci,
gaba ďaya ta rasa abinda zata yi a wannan daren saboda bata san ta inda zata fara ba tunda Affan baya gabanta,
alhj basheer ya ďago ya kalleta cikin bacci yace safiya lafiya, tace alhj naga kai baccinka ma kakeyi baka damu da yaron nan ba, ko bacci banyi ba saboda nasan da kyar in ya iya yin bacci,
alhj basheer yayi mika haďe da salati yace lafiyarshi kalau safiya yau a masallaci ma na samesu tare da kaka mahaifin alhj bara’u, rike ciki oyizah tayi hankali tashe tace a masallacin suka kwana?
Alhj basheer yace a’a sallahr asuba suka je, oyizah ta zauna dabass a kan gadon ta marairaice tace alhj inda zaka san irin missing din Affan da nakeyi da baka barshi ya kwana a wani guri ba, wallhy jiya banyi bacci ba dan daga na rufe ido shi kaďai nake gani,
kasan yadda na shaku dashi kuma nake jin tausayinshi, dan Allah ka tashi kaje ka dawo min dashi,
alhj basheer ya tausaya mata dan yasan tana iya kokarinta akanshi yace to bari in yi wanka zanje in dawo miki dashi,
ta saki wata dariyar murna tace nagode alhj bari in je in shirya mishi favourite break dinshi,
alhj basheer yayi dariya ya koma ya kwanta,

Daki oyizah ta koma cikin murna tace wannan karan mai gaba ďaya zanyi akan yaronnan dan bazai yiwu su dinga daga min hankali ba, gara in kashe shi ya bi abokinshi in huta da zulumi,
wata zuciyar ta haneta da sauri tace in kika kasheshi yanzu tayaya zaki samu dukiyoyin da alhj ya mallaka mishi, sannan in kika kasheshi hankalin mutane zai dawo kanki su zarge ki, gara kibi komai a hankali ki kara tsaurarawa akanshi ki maida shi mara amfani,
da wannan tunanin tayi yan tsaface tsafacenta na gaďo sannan ta wuce kitchen shiryawa Affan break…

Karfe 9 da kwata alhj basheer ya iso gidan rasuwar,
zaune ya samesu a cikin parlor sunyi shuru sai muryar Affan kadai akeji yana ma kaka liman hirar shirme,
dariya kawai kaka liman keyi yana tausayawa halin da Affan ke ciki,
da sallama alhj basheer ya shigo parlon ya tsuguna ya gaida kaka liman sannan suka gaisa da alhj bara’u,
alhj basheer ya kalli Affan yace ka tashi lafy,
Affan ya gyaďa mishi kai yace sosai ma tare da kaka mukayi bacci shi ya tashe ni yasa nayi wanka ya bani abinci ko kaka?,
kaka liman yayi murmushi yace kwarai dan kaka,
alhj basheer yace kace yau kai ďan gata ne, to tashi mu tafi gida mummynka na can tana missing dinka,
Affan ya noke wuya yace ni bazan je gida ba, alhj basheer yayi murmushi yace meyasa? Affan yace saboda har yanzu abokina bai dawo ba,
alhj basheer yace ay yana can gida yana jiranka kuyi wasa, Affan ya waro ido waje yace dagaske daddy, alhj basheer ya gyaďa kanshi yace dagaske nake,
Affan ya kalli kaka liman yace wai haka kaka, kaka liman yayi dariya yace haka ne,
Affan ya tashi da sauri yace muje daddy,
alhj basheer ya mike ya rike hannunshi yayi sallama da su kaka liman suka fito tare da alhj bara’u,
a bakin gate suka haďu da hajja rike da katuwar kular abincin sadaka,
da gudu Affan yaje gurin ta yana kokarin karbar kular hannunta, kauda kular tayi tana dariya tace bazaka iya ba Affan,
su alhj basheer suna dariya suka tsuguna suka gaisheta ta amsa haďe da kara yi musu gaisuwa,
alhj Bara’u yace ina Afeeyah dafatan jikin nata da sauki,
Hajja tace hmm sai dai addu’a tana can tun jiya take abu ďaya yanzu na baro mahaifinta yana mata rubutu,
alhj basheer yace kuka fa dole ne hajja shakuwar zaku duba, kai mutuwa, mutuwa mai yankan kauna,
Affan yace daddy Afeeyah ce ke kuka, alhj basheer ya gyada mishi kai,
Affan ya bata rai kamar zaiyi kuka yace daddy tun jiya fa take kuka kaje ka rarrasheta kace tazo muje gidanmu taga abokina muyi wasa tare,
alhj basheer yace to yanzu dai muje gida anjima zan je in rarrasheta sai in kawo maka ita gidan kaji,
Affan yayi dariya sosai yace gaba daya zata dawo gidan mu ko?, dama jabeer yace zai bani ita in ya aureta kuma kaima kace zaka aura min ita ay ko,?
sukayi dariya dukkansu alhj basheer yace eh zan aura maka ita wuce muje, ya fita yana tsallen murna,
sun kusa karasawa gidan ya rungume daddy yace daddy ka goyani kar inga lions, alhj basheer yace babu abinda zaka gani buďe idonka nasa an cire su, a hankali ya buďe idon yaga babu abubuwan da ya saba gani a kofar gidan, a tsorace ya shiga gidan yana zazzare ido,

jiki na rawa oyizah ta fito ta rungumeshi tana faďin oyoyo Affan ďina, nayi missing dinka ďana,
alhj basheer yayi dariya yace ai da kyar ya yarda ya biyo ni saida na ce mishi jabeer na nan gidan sannan,
oyizah tayi murmurshin mugunta tace muje ciki kaci abinci sai in nuna maka abokin naka, Affan yayi dariya ya bita suka shiga ciki,

Special break ta haďa mishi wanda yaji magunguna,
zaunar dashi tayi ta cika gabanshi da abinci ta diba a cokali zata fara bashi ya kauda kanshi yana rike ciki yace mummy munci abinci sosai tare da kaka har da kosai ma mai dadi, oyizah ta ajiye cokalin ta saci kallon alhj basheer da hankalinshi ke kan TV sannan ta kalli Affan tace haba baby na, baka so kaga abokin naka kenan Affan da sauri yace inaso mummy, tace oya open ur mouth kayi ko 1bs ne,
ya buďe bakinshi ta ďebo zata zuba mishi ya kara kauda kanshi da sauri yace ina zuwa mummy kaka liman yace in zanci abinci in dinga yin bismillah, da karfi yace “bismillah”, oyizah ta buge bakinshi da karfi ba tare da tasan tayi ba,
washhhh Affan ya faďi da karfi yana kallonta idonshi ya fara kawo ruwa yace mummy me na miki,
ta dafe kanta tace Affan wadannan mutanen sun koya maka abubuwan da zai kasheka,
Affan ya fito da ido waje yace “kasheni” mummy?
Ta rage murya tace yess,
kaga wannan bismillahr da yace kayi, to daga ka kuma yinta zaka mutu,
Affan yace to ai jiya munyi sosai harda wani karatu ma duk munyi kuma ban mutu ba,
oyizah ta mike ta riko hannunshi tace zo muje in fada maka wata magana,
ya mike ya bita daki ta zaunar dashi gefen gado ta fara tsoratar dashi sosai akan sallah da wasu abubuwan da kaka liman ya koya mishi sannan tace mishi kasan inda abokinka yake, ya girgiza mata kai cikin tsoro tace to ya mutu kaga irin mutuwar da akeyi a cikin film mutum ya fadi ya daina motsi, Affan yace ehh, tace to shima ya tafi bazai kara dawowa ba saboda halin shi bashi da kyau, mugu ne so yakeyi ya kasheka shiyasa yake yawan zuwa yace kuje kuyi sallah,
Affan yayi narai narai da ido yace mummy ba mugu bane, yana kawo min cwts, baya dukana kuma baya min ihu kamar yadda su anty salma suke min,
oyizah tace muguntar kenan ay saboda yanaso ya kasheka wata rana shiyasa yake maka haka, amma kaga saboda am wit u gashi yanzu ya mutu har an kaishi rami, ka manta dashi kaji Affan din daddy,
Affan ya gyaďa kanshi hawaye suka sauka a kuncinshi wanda shi kanshi baisan yanda akayi suka fito ba, maganganu ta cigaba da yi mishi tana kara tsoratar dashi har saida ta tabbatar ya tsorata sannan ta kaishi ďaki ya kwanta tababbiyar zuciyarshi na karyata maganganunta akan jabeer,,

Daki ta koma tana sauke ajiyar zuciya dan ba karamin yaki tayi gurin sanyawa Affan tsoro a ranshi ba, a zuciyarta tace tabbas sai tayi da gaske dan mutuwar jabeer na neman karya duk wasu alkadarinta…..

Mrs tijjani shattima……
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣6⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Da sassafe alhj basheer ya shigo dakin ya tarar da Affan zaune a lallausan gadonshi yayi tagumi, a hankali ya cire hannun da yayi tagumin dashi yace me ya sameka dan daddy,
Affan ya kwanta kan cinyar daddy yace daddy Afeeyah tana can a gida tana kuka, ya ďago kanshi da ya ciko da kwalla yace daddy abokina ya zo yace in je in rarrasheta,
alhj basheer yayi murmurshi dan ya dauki maganarshi shirme yace in ji wa yace maka tana kuka,
Affan yace jabeer ne ya faďa min,
alhj basheer yace a ina kaga jabeer din,
Affan yace ana ruwan sama na ganshi a window na,
alhj basheer ya shafa kanshi cikin mamakin yadda akayi kwakwalwar Affan ta fara rike mafarki yace tashi kaje kayi wanka zan je in rarrasheta anjima,
Affan yace to daddy yaushe zata dawo nan gidan sai in dinga rarrashinta,
Alhj basheer yayi hanyar waje yace kayi wankan kazo ka karya tukunna,
Affan ya mike yayi hanyar bayi yana kallon window inda yaga jabeer cikin baccinshi amma shi ya kasa gane mafarki yayi dan ya hakikance a zahiri yaga jabeer,
bayi ya shiga yayi wanka ya jika ko ina kamar yadda ya saba har ya bude pampo zaiyi alwala kamar yadda kaka liman ya nuna mishi sai kuma ya fasa saboda tuno kalaman oyizah,
da sauri ya fito daga bayin ya shirya cikin matsatsun kaya…

Alamarin Affan ya fara bawa alhj basheer tsoro saboda kullum sai yayi mishi magana akan ya dawo mishi da Afeeyah gidansu, abinda yake fin bashi tsoro bai wuce yadda yake haddace mafarkan da yakeyi akan jabeer ba, yawan mafarkin da yakeyi ne ma yake hanashi tambayar inda abokinshi yake saboda yana ganin kamar a zahiri yake ganinshi,,, duk wannan mafarkin da Affan yakeyi bai taba faďa ma oyizah ba dan ko yazo zai faďa mata sai ya fasa ya kama harkar, daga shi sai mahaifinshi kadai suka sani…

A ranar da za’ayi sadakar bakwan jabeer kuka sosai Affan ya tsare mahaifinshi dashi akan shi gobe in ba’a kawo mishi Afeeyah gidan nan ba bazai kara cin abinci ba, hankalin alhj basheer ya tashi matuka saboda yadda Affan ke kuka harda majina,
dakyar ya lallabashi yace gobe in shaa Allahu zan dawo maka da ita gidannan kaji, Affan ya share hawayenshi ya rungumeshi cikin jin dadi yace bari inje in faďa ma mummy sai tayi mata abinci mai dadi ko,
alhj basheer ya gyaďa kanshi,
Affan ya tashi ya fita yana ihun murna, binshi alhj basheer yayi da kallo a zuciyarshi yana tunanin yadda zai tinkari alhj bara’u da mahaifin Afeeyah da maganar auran mahaukacin danshi dan in ba aure ba babu abinda zai kawo Afeeyah gidanshi ta zauna,
dakinshi ya wuce yana jiyo ihun Affan a waje yana yi yana tsallen murna….

Da wuri aka idar addu’ar bakwai akayi sadaka sosai mutane suka watse,
alhj basheer zaune a parlon alhj bara’u suna yar hirah jefi2,
alhj Bara’u ya kalli alhj Basheer yace alhj tun a gurin addu’a na lura da yanayinka kamar wani abu na damunka, alhj basheer yayi ajiyar zuciya yace wallhy alamarin yaron nan ne ke matukar bani tsoro, alhj Bara’u cikin damuwa yace alhj Basheer kenan ay cuta kaffara ce,
ka dinga godewa Allah da lalurar da ya ďaura mishi dan shi kadai yasan sirrin dake cikinta, gara kai ma zaka kalleshi a haka kaji dadi,
yayi murmushi mai ciwo yace Allah ya kai rahama kabarin jabeer, alhj basheer yace “ameen” amma ni ba ciwon Affan bane ya dameni,
wani abu yake so inyi wanda a ganina son zuciya ne in har na yarda na biye mishi,
alhj bara’u yace menene shi alhj,
nan alhj basheer ya faďa mishi duk abinda Affan ke faďa mishi game da mafarkinshi, alhj bara’u yayi ajiyar zuciya zaiyi magana kaka liman ya shigo da sallama,
da sauri suka mike suna mishi sannu da zuwa dan ya koma Daura tun ranar uku, zama yayi a gajiye yana amsa musu, bayan sun gaisa Amirah ta kawo mishi abin kari ya zauna kamar ba gidan ďanshi ba dan baida wannan kauyancin akanshi yaci abincinshi son ranshi yana ci suna hirah,
alhj basheer ya kalli alhj bara’u yace bari in tafi anjima ma karasa maganar,
kaka liman yayi maza cikin wasa yace zauna tare za”a karasa maganar dani in dai ba ta gulma bace,
suka kwashe da dariya suka ce bata gulma bace kaka, yace to a cigaba mana, daga ganina sai ku bari,
alhj bara’u yace to Baba bari mu cigaba kaima sai ka bada shawararka,
yayi murmushi yace to inaji,
alhj bara’u ya fada mishi komai kamar yadda alhj basheer ya fada mishi,
kaka liman yayi murmurshin jin daďi a zuciyarshi yace ikon Allah kenan jiyan nan nake tunanin yadda zanyi a karasa burin jabeer sai gashi cikin sauki wacce yakeso ita zata karasa aikin da ya dauko na amininshi, tabbas akwai wani boyeyyen alamari a cikin wannan auren in har ya ďauru,
ya kalli alhj basheer yace to meye abin son zuciya anan, aure fa kace bawai wani abu ba, kuma ay Affan a wannan lokacin yana bukatar mata saboda haukarshi ba wata hauka bace kawai dai yana abubuwan kananan yara ne, yanzu in har Allah ya tabbatar da auren nan kai da kanka zaka sha mamaki saboda yanzu ne zai samu wacce zai zauna da ita dare da rana kuma nutsuwa sosai zata shigeshi har ta iya kaishi ga samun sauki in Allah ya so, dan komai sai ya so ko ba haka ba,? suka ce haka ne kaka, yace to ku barmin komai yanzu zanje in samu malam atikun in faďa mishi in so samune ma ayi auren yau tunda me zamu jira, nayi imanin hankalin jabeer zai kwanta a cikin kabarinshi in har wannan auren ya yiwu saboda masoyanshi ne kuma hakan zaisa ako da yaushe su dinga tunawa dashi, amma in mukayi sakacin barinsu suka auri bare to fa zasu manta dashi cikin adduoinsu ko ba jima ko ba daďe,
alhj basheer yace haka ne kaka, to ubangiji Allah ya tabbatar mana da alkhairin dake cikin auren, Ameen sukace gaba dayansu sannan suka kama wata hirar…

Zaune take a gefen gado kanta na kallon sama hawaye na gangarowa daga gefen idonta,
cikin muryar damuwa Hajja dake zaune a gefenta tace yanzu dan Allah bazaki yi tawakkali ba Afeeyah, ace yau kwana bakwai babu ci babu sha sai aikin kuka, duk kin rame kin lalace, wannan kukan da kikeyi bashi zai dawo da jabeer ba, Allah ya fiki sonshi shiyasa ya ďaukeshi daga wannan rikitaciyyar duniyar, kamata yayi hakuri ki dangana lamarinki ga Allah ki dage wajen yi mishi addu’a wannan shine kadai zai nuna lallai son da kike mishi babu algus a ciki, kinsan yadda jabeer ya tsani yaga zubar hawayenki gashi saboda shi kin kwana bakwai kinayi ba bacci bare cin abinci, gaskiya in har kikace haka zaki cigaba dayi hankalinshi bazai taba kwanciya ba gara ki dawo da walwalarki kamar yadda kika saba duk da nasan da kamar wuya amma hakan zaki daure tunda kinsan ba’a taba mutuwa an dawo ba,,
Afeeyah tunda har manzon Allah S.A.W yabar duniya to ki tabbatar da babu mai shigowa cikinta ya zauna,
muma yau ko gobe zamu bi jabeer inda yaje,,,
Cikin kuka Afeeyah tace Allah yasa yau ďin ne, Hajja kin kasa ganewa ne, nayi duk iya kokarin da zanyi in hana kaina kuka na kasa,
dan Allah ki fada min yadda zanyi in daina kukan mutuwar yaya jabeer, tun ina karama bansan kaina ba fa nasanshi,
ya bani kulawar da babu wanda ya bani ita, ya soni ya kaunace ni, kuma yayi yaki da duk wani abun da zai sani damuwa,
ta kara fashewa da kuka murya na rawa tace ya Allah ka sassauta min wannan jarabawar tayi min zafi da yawa,,,,
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣7⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Zama tayi a gefenshi cikin muryar kuka ta gaisheshi,
sai da ya ďan jima sannan ya kalleta batare da ya amsa ba yace bazan hanaki hawayen nan ba dan bansan dalilin zubar su ba,
ki zubar da su san ranki in kin gama sai ki saurareni,,
Afeeyah ta haďiye kukan hade da goge hawayenta tace nagama kaka,
kaka liman ya kalleta yace kin tabbata,,
ta gyaďa mishi kai tana ajiyar zuciya, yace to Allah ya kara miki hakuri ya kuma kara miki dangana, tace Ameen,

kaka liman yace magana nakeso muyi dake, inaso ki saurareni kuma kiyi wa maganar kyakyawan duba a mizanin hankali, kina jina,?
tace eh inajinka,
yace madallah,
yau jumma’a dai2 kwana bakwai da mutuwar jabeer ko ba haka ba,
tace haka ne kaka,
yace gobe sati, satin da yaso zama ranar tarihi mafi girma a rayuwarku ke da jabeer,
sai kuma Allah mai kowa mai komai bai yarda ba saboda dama ya rubuto ke ba matarshi bace kuma shima Allah ya rubuto bazai taba yin aure a rayuwarshi ba zai koma gareshi,
Shin Allah baya sonku ne yayi muku haka,
ta girgiza kanta da sauri,
yace Allah shi kadai ya barwa kanshi sanin boyayyen alamarin dake tattare da rayuwarki shiyasa ya ďauke jabeer a lokacin da kike bukatarshi domin ki fuskanci wata rayuwar,
ki sani Afeeyah in har a rubuce a allon Allah gobe ne ranar da zakiyi aure to babu makawa sai an ďaurashi, Allah sarki jabeer, bayan iyayenshi da yanuwanshi baiso kowa ba kamar yadda yaso ku ke da Affan, shin a soyayyar da jabeer ya nuna miki zaki iya cika burinshi da ya fara bai karasa ba,
da sauri tace koda kuwa wahalarshi zaiyi sanadiyyar raina kaka,,
alhmdullh kaka yace a zuciyarshi sannan yace bana fatan yayi sanadiyyar ranki jikata, nasan zakiyi duk abinda nace,
jabeer ya dauko aiki mai matukar hatsari kuma Allah bai bashi ikon karasawa ba, yanzu ni da ke zamu karasa shi amma banason ya zama hatsari a gareki,
Afeeyah dole ki fitar da kanki a sahun yara domin ke ba yarinya bace, dole ki zama mai jajircewa a cikin wannan kasadar da zamu sa kanmu,
da siyasa nakeso muci yakin nan domin yakin yafi karfin yinmu amma baifi karfin Allah ba,
Allah yasa zaki daure zuciyarki in kikaji jahadin da zakiyi domin masoyinki,
Afeeyah tace koma menene zanyi kaka in shaa Allahu,, kaka liman yayi murmushi cikin jin dadi yace Afeeyah gobe in Allah ya kaimu zaki bar gidanku ki koma gidan Alhj basheer da zama a matsayin matar ďansa,
mikewa Afeeyah tayi da sauri tana girgiza kanta idonta ya fara kawo ruwa tace kaka” Affan??, innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
kaka liman yace nutsu Afeeyah ki nutsu ki zauna muyi magana domin babu abinda zai hana wannan auren sai Allah, kafin ki shigo dakin nan nayi istahara akan lamarin nan na gano abubuwa da yawa saboda haka ki zauna mu cika ma marigayi burinshi,
Afeeyah ta zauna tana kuka tace kaka har abada bazan taba iya auren wani ba, bazan iya ba,
na daukarwa kaina alkawarin bazan yi aure ba har in koma ga mahaliccina, nasa a raina ni zan zama uwar gidan yaya jabeer a aljanna,
kaka liman yayi dariya yace kuruci dangin hauka, alkawarin ki kenan, kika san alkawarin Allah akanki, bakisan mijinki ba, yawan ya’yanki da kuma adadin rayuwar zakiyi kafin ki koma gareshi,
dan haka ki kauda wannan maganar ki fuskanci rayuwar gaba, jabeer ya riga ya tafi bazai dawo ba dan haka mu ida aikin alkhairin da ya fara domin samar ma ruhinshi salama,
nidai bazan faďa miki komai yanzu ba,
zanso ki zauna a gidan ki fara ganin komai dake faruwa da kanki hankalinki zai baki ki gane abinda nake nufi, zan dinga waiwayoki akai akai dan akwai yan tambayoyi da zan dinga miki domin mu dinga sanin matakin dauka ta kasa2, duk abinda kika gani karki nuna kin gani saboda tsaro kin gane ko,
Afeeyah da kuka yaci karfinta ta kasa magana sai kallonshi kawai takeyi yana mata jawabi kamar tace mishi ta yarda da maganar auren,

Kaka liman ya dade yana sako ma Afeeyah magana cikin magana dan bayaso ta fahimce shi ya jefa rayuwarta cikin hatsari,
yasan tana shiga babu dadewa tausayin Affan zaisa tayi ko me ya sata dan kubutarshi,,,

Da daddare bayan ta idar da isha’i ta hade kai da gwiuwa tana kuka sosai tana hango rayuwar da zatayi a gidan su Affan tare da su mummy masu kirar samudawa,
yaya zatayi ta iya zama da Affan a wannan halin da take ciki, bata tunanin zata iya taimakonshi domin itama neman wanda zai taimaketa ya tausheta takeyi,
babu irin rarrashin da hajja batayi mata ba akan ta dauki auren a matsayin kaddara, ita kanta hajja tsoro abin yake bata domin tasan jikarta zata shiga wata irin rayuwa mai cike da jarabawa,,
saida tayi kukan ta gaji dan kanta ta bingire da baccin wahala a takure gurin,,,

Karfe uku da kwata na dare hajja ta jiyo muryarta cikin bacci tana sambatu hawaye da zufa sun jika fuskarta da wuyanta,
a hankali ta matso kusa da ita ta kama hannunta zata fara mata magana taji ta matse hannun sosai tana faďin
“bazan iya ba yaya jabeer, bazan iya ba,,, dan Allah ka dawo gareni, kasan a irin wahalar da kabar zuciyata, dan Allah karka kara tafiya ka barni, hajja ta fara cire hannunta cikin nata ta kara matsesu da karfi tana faďin “bazan kara barinka ka tafi ka barni ba,””
hajja ta share hawaye ta janyota jikinta tana karanto addu’a tana tofa mata a hankali, cikin ikon Allah tayi lamo jikin hajja tana ajiyar zuciya,,
hajja bata koma bacci ba saida ta tabbatar Afeeyah ta daidaita sannan ta kwantar da ita itama ta kwanta tana kallonta….

Mrs tijjani shattima…
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣8⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Washe gari karfe 10am aka ďaura auren “Afeeyah da Affan” banda Hajja, Abida da Asiyah babu wanda yasan da maganar auren, alhj basheer ba karamin farin ciki yayi ba dan ji yayi kamar ya goya malam Atiku dan murna,
godiya kuwa yayita har yana neman tsugunawa saboda acewarshi wanda zai dauki ya’ kamar Afeeyah ya bawa mahaukaci ay ba karamin jihadi yayi ba,
kaka liman kuwa zan iya cewa yafi su murna dan a ganinshi ya jefi tsuntsu biyu da dutse ďaya, yasan in Affan ya samu sauki Afeeyah zatayi alfahari da kasancewarshi mijinta dan yasan babu yadda za’ayi Affan ya wulakanta Afeeyah tunda yasan muhimmacinta a rayuwar Jabeer,

Bayan an gama daura auren da adduoi suka danyi ciye ciyen da alhj basheer yayo ordr sai kowa ya wuce gida cikin farin ciki,,

A kofar gida alhj basheer ya hadu da masu furnitures din daya kira dan gyara side din Affan da rabonshi da shiga tunda ya fara ciwo,, , karasawa ciki sukayi ya nuna musu inda zasu gyara nan da nan suka fara aune aune da gwaje2,
karan mashin din aikinsu oyizah ta jiyo ta fito da sauri tana fadin karan meye wannan,
tsayawa tayi tana kallonsu tace kaiiii daga ina kuke?
Ganin alhj basheer tayi ya fito daga bayi da mai gyaran bayi suna magana tace alhj gyaran me akeyi haka,? ko Affan zai dawo nan da zama ne,
alhj basheer ya bawa mai gyaran bayin kudi sannan ya kalleta yace eh nan zai dawo, oyizah ta haďe rai tace saboda me, kasan fa bazai iya kwana shi kadai ba shiyasa na bashi daki daya a cikin nawa,
alhj basheer yayi murmushi yace nan din ma bashi kaďai zai dinga kwana ba, oyizah tace kamar yaya,?
Alhj basheer yace surprise nakeso in baki, naso sai an kawota sannan zaki ganta amma tunda kin dan fara dagowa bari in fada miki,
yanzu aka daura ma Affan aure,
oyizah cikinta ya ďuri ruwa tace aure alhj? Yace kwarai aure, zanso kiga farin cikin dake raina game da wannan auren safiya,
oyizah ta share gumin fuskarta tace da wa aka daura mishi auren, wayarshi ta fara ringing yayi saurin ce mata da Afeeyah yar gidan malam Atiku, ina zuwa bari muje mu dawo zanyi miki bayani ya fita da sauri saboda wayar ta sake kara alhj Bara’u ke jiranshi zasuje yi mata siyayya tare da Asiyah, ,,
tsaye yabar oyizah baki sake tana kallon masu aikin gurin,
dakyar ta iya ďaga kafarta ta wuce parlor,
wani irin zama tayi akan kujera har saida kujerar ta amsa,
da sauri farida ta mike a kujerar tace haba mummy wannan ay sai kisa muyi kasa, oyizah da idonta yayi jawur tace mukai kasan mana,
farida ta dawo kusa da ita tace mummy lafiya, oyizah tace hmmm aure aka ďaura a cikin gidannan,
farida cikin kidima tace daddy ne yayi aure,
oyizah tace gara min shi yayi aure dan nasan duk wacce zatazo baza tayi karko ba,
farida tace to waye yayi aure, dai2 lokacin Affan ya wurgo kwallo yana bugawa cikin farin ciki ta kalleshi tace wancan saunan aka daura ma aure,
fareeda ta kwashe da dariya tace ita kuwa wannan wace dakikiyar ce ta yarda ta aureshi,
mummy tayi tsaki tace mune dai dakikan da tuntuni banyi tunanin nemo mace sakarya na haďashi da ita ba,,
Farida tace ban gane ba mummy,
oyizah tace ay kwakwalwarki bazata gane ba amma nasan in na faďa miki amaryar zata gane, Ay kwakwalwarki tasan Afeeyah yar kishiyar suwaiba ko?, farida ta dafe kirji tace farin sani mummy ita ya aura,
tace aka daura mishi dai, ta kalli Affan taga ya kara mata nuri sajenshi ya kwanta luff” yayi matukar kyau kamar yasan yau zai angwance,
da karfi ta kira sunanshi ya taho da gudu ya zauna kusa da ita,
ta kalleshi tace u luk very happy my son,
ya kara gyara zamanshi cikin murna yace am happy mummy yau za’a kawomin Afeeyah,
ta kalleshi sosai tace waye ya faďa maka, yace ni nace daddy ya kawomin ita mu dinga wasa ba jiya nazo zan fada miki ki mata girki mai dadi ba kika koreni,
oyizah tayi saurin dafe kanta da ya sara mata tace tashi ka tafi,
ya mike tsaye har ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya tsuguno saitin kanta yace mummy zakiyi mata girkin,
a hassale ta dago ta daka mishi tsawa tace ubanka zan girka mata, wuce ka bani guri,
Affan ya wuce cikin tsoro yana waigenta kamar zaiyi kuka..
Farida ta dafata a hankali tace mummy meyasa kike damuwa naga Affan is under ur control dole itama in ta shigo ta zama a karkashinki, ni mummy kin bani mamaki wannan small girl din kike damuwa akanta, duka fa bata wuce 17 to 18,
oyizah tacee uhmm kawai ta mike tayi sama tana tunanin yadda zata fara bullo ma wannan alamarin…

A can gidan Malam Atiku kuwa tunda suwaiba ta samu labari take bala’i tana zaginshi, wai akan me za’a boye mata maganar auren saida aka daura za’a fada mata dan anga ba ita ta haifeta ba,
malam Atiku cikin fushi yace sannu uwata, wani abun zaki tsinana min in na fada miki, ko nairah dari bazaki kawo kice a siya mata cokali ba to niko saboda me zan faďa miki, aure ne an daura shi babu wanda ya isa ya warwareshi, nan fa suwaiba ta cigaba da bala’i tana aibata auren harda kuka saboda bakin ciki,
acewarta ita bata bakin ciki da auren musaki amma can cikin zuciyarta takaici ne dankare saboda tasan ko Affan zai dawwama cikin ciwon hauka Afeeyah ta gama warkewa, hangowa ta dinga yi da kausar ce da tuni yanzu alhj basheer ya fara jikata da kuďi,
daki ta koma bayan ta gama sababinta tana kukan rashin sa’arsu ita da diyarta,
malam Atiku ya fita ya barta, hajja kuwa ko dekowa batayi ba tana ďaki tana aikin rarrashi…

Mrs tijjani shattima…
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣9⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Bayan isha’i Alhj basheer da kanshi yazo daukar Afeeyah,
suna zaune da hajja da Asiyah suna rarrashinta suna kuma bata shawara akan ta kula da mijinta duk haukarshi mijinta ne kuma aljannarta na karkashin kafarshi,
Asiyah tace yanzu kin zama kamar uwa a gareshi da taimakonki komai nashi zai fara daidaita,
dole ki jajirce ki manta da ke yarinyace ki rike darajarki da ta mijinki kuma karki yarda wani ya raina shi a gabanki, Nasiha sosai sukayi mata har malam atiku ya shigo shima ya daura ya kuma yi mata tuni da riko da adduoi, sannan ya umurceta ta tashi suje ga alhj basheer can yana jiranta,
mikewa tayi tana kuka Amirah ta miko mata sabon hijab dinta tasa Asiyah ta fesheta da turare ta riko akwatinta suka fito rakata,
dakin suwaiba ta shiga yi mata sallama ko kallonta batayi ba ta cigaba da cin tuwon gabanta tana yan wake wakenta,
tashi sukayi suka fita basu ko kulata ba,
motar alhj basheer suka nufah suka sakata a baya ta rike hannun hajja sosai tana kuka tace saidai hajja ta shigo su tafi, dakyar malam atiku ya lallabata ta saki hajja sannan alhj basheer yayi sallama dasu suka wuce hajja na kuka tana ďaga musu hannu sai kace wacce zata bar unguwar,,

Runtse idonta tayi da suka shigo harabar gidan tana karanto adduoi akan Allah ya taimaketa yayi mata jagora a cikin wannan sabuwar rayuwar da ta tsinci kanta a ciki,
alhj basheer ya fito ya buďe mata kofa yace mun iso diyata, Allah yasanya alkhairi a farkon shigowarki gidannan, ya kuma dawwamar da farin ciki a cikin zaman aurenku har karshen rayuwarku,
a zuciyarta ta amsa sannan ta sako kafarta kasa da bismillah,

Zubur Affan ya mike daga kan kujera ya karaso kofa yana faďin daddy na ya dawo, yana buďe kofar ya hangosu da Afeeyah suna tahowa ya rugo da gudu yana cewa oyoyo barbie, chakk” ya ďagata cikin murna yana jujjuyata ya karaso cikin parlon da ita yana fadin mummy kizo ga barbie nah daddy ya kawo min,
wani irin kuka Afeeyah ta fashe da shi yayi saurin sauketa yana nunama daddy hannunshi yana faďin ba ruwana daddy wallhy bani na sata kuka ba,
alhj basheer yayi dariya yace kai ka sata kuka nima babu ruwana bari ma in tafi kar ace har dani,
Affan ya zaro idonshi zaiyi ma oyizah magana tayi saurin jifanshi da mugun kallon da yasa shi ďauke kanshi ya ďago fuskar Afeeyah kamar zaiyi kuka yace ay bani na saki kuka ba ko,?
Afeeyah tayi banza dashi ta cigaba da kukanta,
alhj basheer yace zo nan diyata ki zauna rabu da shirmenshi,
Afeeyah taja kafarta a hankali ta zauna a kasa kusa da alhj basheer Affan ma ya biyota ya zauna kamar zaiyi kuka,
alhj basheer yace share hawayenki ki bude idonki ki gaisar da mamanki da kuma yayyinki,
oyizah tayi saurin cewa ta mayar da idonta abinda muna tare kullum yanzu,
alhj basheer yayi murmurshi yace haka ne,
ya kalli Afeeyah yayi mata yar nasiha ya kuma roketa da ta kula da Affan ta rikeshi amana sannan yace suje oyizah ta nuna mata ďakinta,
oyizah ta mike tace ma Afeeyah ta tashi suje,
kafin Afeeyah ta mike Affan ya mike yace barbie tashi muje ďakinmu,
Afeeyah ta mike tabi bayan oyizah da ya”yanta zuwa side din Affan,
saida tayi addu’a sannan ta shiga ciki ba tare da ta ďago kanta ba,
oyizah ta kalli Affan da ke binta a baya tace to bita zaizai wuce ka tafi daki,
Affan ya bata fuska yace ay nan ne yanzu ďaki na,
Salma ta daka mishi gigitaciyar tsawar da tasa shi fita da gudu, dariya suka watse dashi suka dawo da kallonsu kan Afeeyah,
oyizah ta ďago kumburarriyar fuskarta tana mata kallon banza tace “so called Amarya,”
farida ta kwashe da dariya tace su amarya man gyaďa,
salma ta hada rai tace kuna dariya ne, ay sai ta samu damar raina mu, mummy ki bata warning din da zaki bata mu wuce dan wallahi na mugun tsanar ganin yarinyar nan,
oyizah tace me kike ci na baka na zuba,
ta kalli Afeeyah tace nasan dalilinki na auren Affan bai wuce saboda dukiya ba, to kin makaro yarinya saboda ke da Affan kunyi ma juna nisa kamar tsakanin gabas da yamma saboda Affan is under my control sai abin da nace mishi,
Sannan kisa a ranki aikatau ne ya kawoki gidannan ba zaman aure ba,
salma tace gud mummy dama tunda “Gaje” mai aikin shegiyar mum din Affan ta tafi bamu kara samun mai aiki mai tsafta ba yanzu tunda mun samu wannan sai muyi manage,
oyizah kwarai kuwa, yanzu zan fara miki lissafin daily works din gidannan,
karfe 5 in kika tashi ba ruwana da sallarki in kinga dama kiyi in kinga dama ki barshi, fareeda tayi saurin cewa mummy wannan small gal din ma ay sallah bai wajabta akanta ba,
salma tace tell her ooo,
oyizah tace oho in taga zata wahalar da kanta tayi to tayi nidai amin aiki, girki shine first,
sai gyaran kitchen, gyaran ďakin yara, sai parlor,
tsakr gida da sauransu akwai maza masu yi,
Farida tace mummy wannan special secret flower bed din naki da nake bashi ruwa plss spare me ki kara mata shi a aikinta,
da sauri oyizah ta kai mata duka hade da yi mata dakuwa, farida ta toshe bakinta tace sorry mummy sannan ta fita da gudu,
oyizah ta gama lissafa wa Afeeyah duk aikin da zatayi a gidan hade da concrete warning na in ta saba aiki ko daya ne she will be in fr it,
Afeeyah dai gyada kanta kawai takeyi hawaye na kwaranya a idonta,
har sun sa kai zasu fita oyizah ta juyo tace lastly babu ruwanki da rayuwar Affan, ban yarda ku kebe tare ba bare har ki yaudareshi da wadannan shanyayun idanuwan naki,
salma tace haba mummy wannan mahaukacin meye zai rude shi,
oyizah ta harareta tace shi dutse ne ba mutum ba, mahaukata ma ay suna da feelings tunda akwai zuciya a kirjinsu, dan haka na horeki da kebewa dashi bare har— ta yi saurin dafe kanta tace bana ma fata dan har abada,,,
salma tace har abada me, oyizah ta jata suka fita tace muje ďaki in faďa miki..

Suna fita Afeeyah ta fashe da kuka tana kiran sunan jabeer, kuka sosai takeyi har saida jiri ya fara dibanta sannan ta zauna bakin gado, saida ta gama tunane tunanenta sannan ta mike a zuciyarta tace Allah yasa yawan aikin da suka bani ya kasheni in huta,
drawer dake dakin ta bude zata sa akwatinta taga kaya masu tarin yawa wadanda ba dinkakku ba harda na bacci, cire hijab dinta tayi ta shiga bayin dake ďakin tayi wanka ta fito tana tsane kanta da towel,
tsawar da aka saki tayi daidai da bude kofar ďakin,
da sauri ta waigo tana kallonshi yana kokawa da mukullin kofar alamun yana saurin rufeta dan kar wani ya ganshi ……

Mrs tijjani shattima…..
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣0⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Kallonshi Afeeyah ta tsaya yi har ya rufe kofar ya waigo yana mata murmushi,
kau da kanta tayi ta janyo hijab dinta tasa ta zauna a gefen gado, karasowa yayi yana kaďa kanshi yana dariya ya tsuguna a gabanta ya daura hannunshi kan nata yace barbie yau kin dawo gidan mu ko,,
ta juyar da kanta gefe, ya taso ya zauna kusa da ita yayi narai2 da ido yace abokina ya faďa min kullum kina kuka da daddare meyasa kike kuka?

Afeeyah da idonta ya ciko da kwalla ta kasa ce mishi komai sai kallonshi da takeyi, hannu yasa ya share hawayen da ya digo a idonta yace ki mayar da hawayen nan dan Allah karkiyi kuka abokina zaice ni nasaki kuka in yazo,
Afeeyah ta kara fashewa da kuka a zuciyarta tana mai tausayawa ranar da Affan zai san jabeer ya bar duniya,
kukan shima ya fara yi kamar karamin yaro yana share mata hawaye,

wata tsawar aka sake saki mai firgitarwa kamar zata rusa gidan saboda kararta,
da sauri Affan ya shige jikinta ya kankameta haďe da runtse idonshi,
wani abu mai wuyar faďuwa yaji ya tsarga mishi a cikin kwakwalwarshi,
wani irin shauki ya dinga ji a can cikin jikinshi,
shi kanshi ya kasa fassara yanayin daya shiga a wannan lokacin,
Turashi Afeeyah ta farayi tana kokarin mikewa tasa kaya,
kara kankameta yayi dan bayason ya daina jin abinda yakeji,

kallon fuskarshi tayi a hankali taga idonshi a lumshe yana fitar da wani irin numfashi, tausayi ya bata sosai saboda yadda ya koma cikakken mutum a haka kafin anjima ya birkice ya koma tababbe,

a hankali ya bude idonshi da ya fara canza kala ya saukesu kan nata,
da sauri ta kauda kanta tace dan Allah ka sakeni in sa kaya bacci nakeji,

sakinta yayi cikin muryar lafiyayyan mutum yace “muje in tayaki sawa” cikin mamaki ta zaro manyan idanuwanta tana kallonshi,
murmushi yayi mata ya mike tsaye ya bude drawer ya dauko mata cotton night gown ya mika mata,
kasa amsa tayi tana mishi kallon mamaki, ajiye rigar yayi a jikinta ya hura iska cikin idonta yace ko ni zan sa miki da kaina,
tayi saurin kauda kanta ta ďauki rigar ta faďa bayi tana tunanin canzawarshi lokaci Guda,

tsaye ta sameshi gaban mudubi yana zana kanshi yana dariya,
ta mudubin ya hangota ya juyo da sauri ya janyota yace zo kigani na iya drawing mutum a mudubi, tsaya anan kigani,
Afeeyah ta girgiza kanta tace bacci nakeji,
ya girgiza kai a shagwabe yace ni sai kin tsaya,
Afeeyah ta haďe rai ta juya ta wuce kan gado ta kwanta,
zama yayi a kujerar dressing mirror yana kumbure2 yana kunkuni shi a dole an mishi laifi,

Ko kallonshi batayi ba tayi kwanciyarta ta shige bargo tana karanto adduoi,

muryarshi taji saitin kunnenta yana faďin
Niko?
Niko?
Ya faďi haka yafi sau goma Afeeyah tayi tsaki ta yaye bargon zata fara masifa hawayen da ta gani kwance a kuncinshi ya hanata, ta kalleshi murya a tausashe tace me nayi maka kake kuka,
ya kwanta kan cinyarta yace bake bace kika ki tsayawa inyi drawing dinki ba kuma kika tafi kika barni baki bani hakuri ba,
sai na fadama abokina ince barbien shi ta daina kirki yanzu,

Afeeyah tasa hannu ta share mishi hawaye tace kayi hakuri gobe zan tsaya yanzu bacci nakeji,
Affan ya ďago kanshi ya kalleta cikin ido yace ni bana jin bacci zaki rarrasheni inyi bacci,

Afeeyah ta dafe kanta kwalla ta cika idonta a zuciyarta tace ni kuma kaddara ta kenan, kwanciya tayi ba tare da ta bashi amsa ba tana hawaye tana hango da yanzu fa tana gidan masoyinta abin kaunarta jabeer,
hawa gadon Affan yayi ya kwantar da kanshi a bayanta, nan ta fashe da wani irin kukan da yasashi saurin kankameta yana rarrashinta,
runtse idonshi yayi yana sake jin abin da yaji dazu,

a hankali kwakwalwarshi ta fara daukar caji ya shiga shinshina jikinta yana lumlumshe ido,
kara matseta yayi lokacin da hannunshi ya sauka kan kirjinta a take ya saki ajiyar zuciya yana wani irin nishi,
cire hannunshi ta fara kokarin yi ta kasa saboda irin rikon da yayi mata, yafi minti biyar a haka yana sauke ajiyar zuciya yana sauraron kukanta da yake jinshi kamar waka a wannan lokacin,

mirginowa yayi ya ďago fuskarta idonta a rufe ya fara share mata hawaye haďe da bata hakuri,
bata bude idonta ba kuma bata tsayar da hawayen ba, kwantowa yayi ya haďa fuskarshi da tata yana gogawa a hankali,
cikin kuka ta bude baki zata fara masifah yayi saurin tura bakinshi cikin nata,
duk yadda taso fitar da bakinshi ta kasa saboda sam ya hanata damar hakan,

wani irin rikitaccan alamari ta dinga gani a tare da wanda tasan bashi da isashshen lafiyar kwakwalwa,
Shi kuwa Affan sam baya cikin hayyacinshi bare ya tantace a tsakanin duniyar mahaukata ko a ta lafiyayyu yake,
babu inda baya rawa a jikinshi, gani yakeyi kamar duk cikin wasa yakeyin abinda yakeyi sam ya kasa tsayawa da wannan wasan saboda ba kananan abubuwa yakeji na shauki a cikin jinin jikinshi ba,
a wannan lokacin duk iya kokarin turashi hade da kukan da Afeeyah takeyi bai sa ya daina ba saima shiga yin wasu abubuwa na daban da yayi dan a yadda yakejin kanshi in har ya daina wasannan da yakeyi to tabbas zai iya rasa ranshi,

wani irin kuka Afeeyah takeyi na takaici da bakar azaba tana kiran sunan jabeer dan abubuwan da Affan yake mata sun zarce tunaninta,

“Ni kaina danake dauko rahoto saida na tsorata nayi fitar da babu shiri harda buge kafa saboda sauri dan Affan ya matukar tsoratani yadda ya dinga sarrafa Afeeyah kamar cikakken mai hankali”

A bakin kofar na tsaya ina jiyo muku kukan Afeeyah wanda takeyinshi kamar ana yankata, sai karar ruwan sama da ake tsugashi kamar da bakin kwarya,,

barin kofar ďakin nayi na juya gurin da nake jiyo magana kasa2,

a hankali na karasa side din mummy wacce ta fito daga dakin alhj basheer,
tsaye na same ta a bakin kofar dakin da ta bawa Affan tana magana ita kadai tana fadin ina yaron nan ya shiga,
kardai yaron nan gurin yarinyar nan ya tafi, cikin bacin rai tayi kwafa ta kama hanyar side din Affan…….

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣1⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Muryar alhj basheer taji da karfi yana faďin ina tea din yake ne safiya,
sai a sannan ta tuno da abinda ya fito da ita daga dakin har taga kofar Affan a bude,
hanyar kitchen ta nufa cikin gaggawa ta hado mishi tea ta koma dakin ta mika mishi, ya dafe kanshi yace ina maganin,
da sauri tace ba kai ka ajiyeshi ba,
yayi tsaki yace na manta inda na ajiyeshi duba min ko cikin drawer ko kan mudubi, cikin bacin rai oyizah ta fara duba maganin da kyar ta ganoshi a drawer gefen gadonshi ta mika mishi da sauri, ya kalleta yace yau ko ballo min maganin baza’ayi ba,
ta amsa ta babbalo mishi ta mika mishi tayi hanyar kofa,
Alhj basheer yace wai ina zaki je ne kiketa sauri haka,
juyowa tayi tace umm na manta ban bawa Affan maganinshi ba, yayi murmushi yace karki damu dazu da kuna gurin Amarya na shiga na bashi,
oyizah tace ka tabbatar dai2 ka bashi,
alhj basheer yace kwarai kuwa dawo kiyi min tausa,
oyizah ta dawo ranta a bace ta fara mishi tausa tana tunanin abinda ya kai Affan dakin da aka kai amarya,
wasu irin tunani ta dinga yi dan tasan illar kebantuwar mace da namiji a guri,
wani irin ihu tayi ta diro a gado tana fadin alhj na daura ruwan zafin tea a gas na manta ban kashe ba, sakkowa yayi jiki na rawa yace innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
bari inje in duba, tace koma ka kwanta alhj ka riga kasha magani, hanyar kofa yayi yace wani irin magani ay gara inje in duba kar kije wani abun ya sameki,
dafe kanta tayi lokacin daya fita tana sake tunanin hanyar da zata bi,
waya ta dauko da sauri ta shiga kiran salma, numbr busy aka dinga sa mata tayi tsaki ta kira farida taji a kashe,
wurgi tayi da wayar tace wadannan tambadaddun kuma wayarsu taki shiga,
yanzu ni ya zanyi, muryar alhj basheer taji akanta yace safiya kin tsoratani wallhy, gas a kashe yake,
ta dafe kanta tace lallai tsufa ya fara zuwa min sai naga kamar ban kashe ba, yayi murmushi ya zauna haďe da rungumeta yace baki ma kunna ba a flask kika dibi ruwan,
tace hakane shaff na manta ne wallhy,
nan alhj basheer ya shiga faranta ranshi a jikin oyizah sakin jikinta tayi suka faranta ran juna duk da bataso hakan ba…

Asubar fari oyizah ta farka a gigice sakamakon mafarkin da tayi,
ko wanka batayi ba ta fita tayi dakin Affan,

buga kofar takeyi kamar zata ballata tana kiran sunanshi, cikin bacci Afeeyah taji bugun kofar ta mike a hankali ta fara ture Affan da ya cikwikwiyeta hawaye kwance a gefen idonshi, kara matse jikinshi yayi da nata yana sheshekar kuka haďe da ajiyar zuciya, ba karamin tausayi ya bata ba duk da itama abar tausayin ce saboda irin azabar da tasha,
bugun da mummy kema kofar ya karu muryarta ta cika cikin gidan tana masifa tana fadin in Affan bazai bude ba dan uwarki da ubanki ke bazaki bude ba,
Afeeyah ta fara kokarin yi mishi dabara ta cire hannunshi ta dan turashi tasa pillow a gurin ta daura hannun kan pillown taja bargo ta rufa mishi,
hijab dinta taja tana tafiya dakyar ta karasa kofar dakin da oyizah ke jijjigawa kamar zata ballata,
murda kofar tayi taja ta tsaya,
da karfi oyizah ta hankado kofar har saida ta sameta,
kallon Afeeyah ta tsaya yi daga sama har kasa tana hararrta, ta janyo hijab dinta da karfi tayi wurgi dashi tabi duk jikinta da kallo,
cikin fushi tace a ina kika kwana,
Afeeyah baki na rawa tace a-a-a- — sambatun Affan ya katseta yana kiran sunanta yana fadin wasu kalmomi na shauki haďe da matse pillow a jikinshi,

oyizah tayi saurin kallon inda yake ta karasa ta cire bargon da Afeeyah ta rufa mishi,
wani irin ihu ta saki hade da mayar da bargon tace na shiga uku, me kikayi mishi naga babu kaya a jikinshi,
Afeeyah ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na tsere cikin idonta,
oyizah cikin hassala ta shakota tace yau sai kin fada min abinda kikayi mishi, yaudarar mahaukacin nan kikayi kika mishi fyade ko me,
Afeeyah ta kara sautin kukanta tace wallhi babu abinda na mishi, oyizah ta tsinka mata mari tace karya kikeyi dan uwarki,
ga shi nan babu wando a jikinshi kema kuma kalli yadda kike kin kasa tsayuwa da kyau,
Afeeyah ta kasa magana sai kuka kawai takeyi,
nan mummy ta cigaba da magana cikin ficewar hayyaci tana dukan Afeeyah,
ihun Afeeyah ne ya tada Affan daga bacci ya mike da sauri ganin oyizah tana dukanta, baibi takan daukar wando ba ya diro daga kan gadon yasa duk iya karfinshi ya turata ta faďi kasa ya dago Afeeyah yace yi hakuri barbie me kikayi mata,
Ta runste idonta da sauri ta dakko wando ta mika mishi ya karba ya fara sawa,
oyizah na huci ta mike ta karaso gurinshi ta daukeshi da mari har sau biyu tace dan ubanka ni zaka ture saboda wannan kodadiyyar matar, Affan ya rike kuncinshi ya kumburo baki yana hawaye yace mummy ni kika mara,
tace zan maka abinda yafi mari indai har kace zaka fara bijire min,
ta kalli Afeeyah tace Affan bai taba min musu ba, bai taba bata min rai ba kullum yana kaffa2 dani amma gashi daga zuwanki Affan har tureni yayi na fađi kasa,
yau sai na miki dukan tashin hankali inga uban da ya tsaya miki,
da sauri Affan ya shiga tsakiya yana kuka yace mummy ni ki dukeni dan Allah ki kyaleta jiya fa naji mata ciwo,
wayyyyyo oyizah ta faďi ta hankaďashi gefe tayi kan Afeeyah dake ja da baya da kyar,
tana cimmata ta daga hannu zata fara dukanta alhj basheer ya shigo da sauri yace lafiya me yake faruwa anan,
Da gudu Affan yayi gurin daddy yana kuka yace mummy ce zata duki barbie na daddy dan Allah ka hana ta bata da lafiya jiya muna wasa naji mata ciwo a—- alhj basheer yayi saurin toshe bakinshi yace ya isa haka,
oyizah ta kirkiri dariya ta sauke hannunta kan Afeeyah tana shafawa tace wa yace maka dukanta zanyi,
alhj yarinyar nan taji ciwo sosai shine nake son in kaita bayi in mata wanka shine fa take kuka shi kuma ya dauka dukanta nakeyi, alhj basheer cikin mamaki yace sannu Afeeyah,
tashi kije bayi dan Allah kiyi hakuri kinga yanayinshi komai baya yinshi a hankali,
Afeeyah ta kara fashewa da kuka tace dan Allah ka kaini gurin hajja,
alhj basheer yace kiyi hakuri zan je in kira miki ita in gari ya waye kinji,
yanzu tashi kije mummynku ta miki wanka,
Afeeyah tayi saurin girgiza kanta tace wallhy zan iya,
alhj basheer yace to safiya zo muje ki hado mata abinci,
ya tura keyar Affan dake kallon Afeeyah shima yana kukan..

Toilet Afeeyah ta shige da sauri tasa key ta sirka ruwan zafi ta shiga ta zauna tana kuka sosai tana kiran hajja da jabeer,
saida tafi minti talatin a bayi sannan ta fito a zuciyarta tana tunanin to yanzu waye zaisa Affan yayi wankan tsarki,
Ďaga kafadarta tayi tasa ma dakin key tayi sallah tayi adduo’i sannan ta hau gado ta kwanta tana tunano alamuran da suka kasance tsakaninta da tababben mijinta..

Alhj basheer kuwa bayan ya je ya dauko hajja ya kaita har dakin Afeeyah da kanshi, ya fito waje yana mamakin alamarin da ya kasance tsakanin mahaukacin danshi da matarshi,,
shin dama mahaukaci wanda ke da matsala a kwakwalwarshi yana iya saduwa da mace ko dai ita Afeeyar ce ta sadu dashi,
tambayoyi marasa amsa ya dinga yi wa kanshi sai daga karshe ya samo mafitar yaje gurin doctr musa ya tambayeshi yadda abin yake,,
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI◆◆ 42 By Aysha Ya’u Kurah

A can gida kuwa Afeeyah na kwance kan cinyar hajja tana kuka sosai tana fada mata abinda ya faru tsakaninta da Affan da su oyizah,
a hankali ta ďago kanta tace hajja ni tsoro Affan dinnan yake bani wallhy, sai yayi magana kamar me hankali kuma sai ya juye mahaukaci,
sannan hajja mahaukaci ma na iya yin abinda yayi min, hajja ta share hawayenta tace zai iya Afeeyah tunda yanada duk wata halittar da muke dashi kwakwalwa ce kadai ta samu matsala,
Afeeya ta koma ta kwanta tace hajja to ya zaiyi yayi wanka yayi sallah,
hajja tace wannan ne kuma bansani ba,
tashi muyi magana kuma ki share wannan hawayen ki saurareni sosai,
Afeeyah ta mike zaune tana share hawayenta tace ina jinki hajja, hajja ta kalleta sosai tace Afeeyah kuka yanzu ba naki bane, daga yadda kika bani labarin abinda safiya tayi muku ke da Affan na ďago wasu abubuwan da ke yarinta ya hanaki dagowa,
tabbas rayuwar yaron nan na cikin haďarin da bashi da mataimaki sai Allah sai kuma ke da Allahn ya bashi a matsayin garkuwa,

“Hajara”
yau na kiraki da ainihin sunanki saboda inason in karfafa miki gwiwa dan naga kin shagwaba kanki da sunan da jabeer ya shagwaba ki dashi, dole ki jajirce kiyi amfani da damar
da Allah ya baki gurin kwatowa wannan yaran yancinshi,
dole kisa shi a hanya ki dinga nuna mishi hanyoyin bi masu kyau da marasa kyau,
dole ko yaya ne ki fara koyawa kanki sonshi dan sonshi bashi zaisa ki manta da jabeer ba,
dole duk inda yasa kafarshi kema kisata saboda kuyi shakuwar da duk abinda kika ce mishi yayi zaiyi ba musu,
sannan Addu’a, dole ki jajirce ki yawaita addu’a domin itace makaminki a yanzu, dole kuma kiyi hakuri da duk abinda za’ayi miki saboda mai hakuri shi keda nasara a ko da yaushe,
kina jina ko,
Afeeya ta gyada kanta tace ina jinki hajja,
kafin hajja ta buďe baki ta sake wata magana sukaji an tokari kofar dakin da kafa,
da sauri Afeeya ta ďago tana gyara dankwallin kanta,
hajja ta kalli oyizah dake musu kallon raini tace ina kwana safiya,
oyizah ta kirne fuska tace bamu haďu dashi a hanya ba,
hajja ta kauda kanta, salma ta karaso tace ma Afeeyah kee, kinsan karfe nawa yanzu,
Afeeyah tace a’a, salma tace dan ubanki jiya me mummy tace miki,
oyizah tace ai ta manta da abinda nace mata tunda ta kauda budurcinta a gurin tababbe,
salma tace hmm lallai, naga alama mummy,
ta kalli Afeeya tace wallhy kafin 11 ki tabbatar kin kammala komai na gidan nan in ba haka ba na rantse da Allah sai jikinki yayi tsami,
oyizah tace ay ni bani da bakin magana ki ji da ita dan in har nace zan sauke fushi na akanta to wallhy dakyar zan barta da rai,
salma tace ay dama mummy bai kamata ki dinga kulata ba mun isheta dan tasan babu sa’anta a gidannan, ko shi garan mijin nata bai isa ya hanamu yin komai akanta ba,

Afeeyah ta mike dakyar tace ma hajja tana zuwa,
hajja tace muje in tayaki,
Afeeyah tace haba hajja zauna yanzu zan gama,
hajja ta maida kwallar idonta tace to Afeeya,
hijab ta ďauka tabi ta gefensu ta wuce ta barsu tsaye sunata habaici suna zaginta,

kitchen ta shiga ta tarar dashi kaca2, nan ta shiga gyarashi ta haďe kayan wanke2 tayi ta gyara ko’ina tayi mopping,
tana gamawa taji muryar farida a bayanta, da sauri ta waiga ta kalleta tace na’am me kikace,
farida ta harareta tace ance ki daura rice nd stew 4 lunch akwai komai na amfani ki duba zaki gani sannan ki haďa min corslw,,
salma kuma tace ki soya mata plantain ki kawo mata yanzu,
Afeeyah ta gyada kanta ta wuce store din da ta hango kayan abinci,
saida ta daura white rice sannan ta bare plantain, ta daura shi a wuta ta soya,
ba karamin wulakanci sukayi mata ba da ta kai ma salma plantain din,
Ko kallansu batayi ba ta juya ta koma kitchen ta cigaba da aikinta,

sai sha biyu saura ta gama komai ta gyare ko’ina sannan ta wuce parlor da niyyar gyarawa,

Zaune ta sameshi a parlon yana buga game yana ihu shi kaďai,
bata kalleshi ba ta fara gyara cikin parlon, buruntu yaji ya waigo ya kura mata ido yana dariya,
sam bata lura ya ganta ba tana can tana kakkabe kujeru,
rungumeta taji yayi ta baya yana faďin yeeeee na ganta,
Afeeyah tace dan Allah sakeni aiki nakeyi,
ya saketa ya zagayo yana kallonta yace har yanzu fushi kikeyi dani,
ta dauki remote ta kaishi mazauninshi ba tare da ta kalleshi ba,
binta yayi a baya yace ki yi hakuri ni bansan zaki ji ciw– dan son annabi ka kyaleni kaje ka cigaba da game dinka haba ta fadi da karfi rai a bace,

hanyar waje yayi kanshi a kasa kamar zaiyi kuka,
Kallo ta bishi dashi har ya fita sannan taja tsaki a hankali ta cigaba da aikinta cikin kwanciyar hankali dan har ta gama bai dawo ba,
ďaki ta koma tana haki saboda yunwar da takeji ta samu hajja a kan dadduma ta idar da sallah,
zubewa tayi a jikinta tana maida numfashi tace hajja yunwa nakeji, dan Allah ki samo min wani abu inci a gida,
hajja ta shafa addua tace ke kuwa duk girkin nan da kikayi bakici ko kadan ba,
Afeeyah tace umm banason abinda za’a kira uwata da ubana a zaga,
hajja tayi murmushi a zuciyarta tace lallai mutuwar jabeer ta kashe zuciyar yarinyar nan,
ta kalleta tace kinyi dai2 kici gaba da hakuri wata rana sai labari,
bari inje in kawo miki abinci a gida,
Afeeyah tace to hajja bari inyi sallah kafin ki dawo,

Ta windon bayi ta hangoshi zaune yayi tagumi yana kallon ramin kifi, da ganinshi kasan baya cikin walwala,
tsaki tayi ta cigaba da alwalarta ta fito tayi sallah,
tunanin maganganun da hajja tayi mata ta dinga yi sannan ta tuno da abinda tayi mishi dazun da kuma bacin ran da ta karanta a fuskarshi,
mikewa tayi ta naďe daddumar ta fito tana neman hanyar da zata sada ta da gurin kiwon kifin,
da kyar ta gano hanyar ta karasa gurin ta zauna, sam baisan tazo gurin ba ta waiga gurin da taga abincinsu ta ďiba ta watsa musu,
da sauri Affan ya waigo suka haďa ido ya kauda kanshi ya juya mata baya, murmushi ta kirkiro tace kayi hakuri,
dazu banaso ka hanani yin aiki ne shiyasa,
ya noke wuyanshi yace naki yin hakurin,
ta kamo hannunshi a hankali tace Niko?
yayi murmushi haďi da fari da ido kamar yana kallonta sannan ya kara haďe rai yace eh ďin,
tace to juyo kaga wani abu,
ya juyo yana turo baki yace meye?
tayi murmushi tace fushin fuskarka zan nuna maka,
ta nuna bakinshi da hannu tace kaga yadda bakinka yayi babba, sannan fuskarka tayi katuwa saboda fushi,
ya kara turo bakin yayi kasa da idonshi yace to bake bace kike min ihu,
tace to ai zan daina nace maka,
yayi murmushi kadan yace yaushe zaki daina, tace yanzun nan, ya wangale baki ya rungumeta yana dariya sosai yace yauwa barbie na, to tashi muje can ki tayani buga kwallo,
tace a’a yanzu dai inaso insan ko kayi wankan tsarki,
yace eh nayi wanka sosai jikina yanata kumfa,
yanata kumfa,
yanata kumfa na koma fari sosai,
tayi dariya tace to sallah fa,
nan ya kirne fuska yace ai ni bana sallah, Afeeyah ta kwalalo ido waje tace la haulu, baka sallah,
saboda me,?
Kafin yayi magana sukaji muryar oyizah a bayansu tana cewa saboda ubanki bai koya mishi ba…..

Mrs tijjani shattima…
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣3⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Afeeyah ta sunkuyar da kanta da sauri kirjinta na dukan uku2,
Affan ya kalli oyizah yace mummy dama saboda babanta bai koyamin ba shiyasa bana yi,
oyizah ta mika mishi cup din hannunta tace amshi maganinka kasha rabu da wannan kinibabbiyar,
Affan ya karbi ruwan asirin da ya saba sha kullum ya fara sha ya miko ma Afeeyah yace kema zaki sha, Afeeyah ta girgiza kanta ta mike zata wuce oyizah ta janyo hijabinta tace dawo nan ban gama dake ba, ta kalli Affan tace tashi ka kai cup din kitchen sai kaje kayi wasanka, Affan ya mike yana yafito Afeeyah da hannu yana cewa zo muje ki tayani buga game,
oyizah tace a’a jeka kayi wasanka zata zo ta sameka,
ya wuce da gudu yana dago ma Afeeyah hannu,

Wani irin kallo oyizah tayi ma Afeeyah sannan tace jiya me nace miki game da Affan,,
Afeeyah ta sunkuyar da kanta kasa tace dan Allah kiyi hakuri,
oyizah taja kunnenta da karfi tace hakurin uban me kike bani, bance miki kar ki shishshige ma Affan ba? bance miki karki shiga rayuwarshi ba, ohhh wato kema zaki fara tursasashi akan sallah kamar yadda ďan iskan saurayinki yayi ko?
Afeeyah ta runtse idonta zuciyarta na zafi saboda kiran jabeer dan iska da oyizah tayi,
Rankwashi mai karfi ta sakar mata akai tace zan miki kashedin karshe,
kashedin da idan kika ďauka kin tseratar da kanki daga fushi na,
anyi na farko anyi na karshe tsakaninki da Affan, kin fahimci abinda nake nufi ko sai na warware miki?
, Afeeyah tayi shuru kirjinta na tsananta bugawa,
oyizah tace to ina nufin kwana ďaki daya ke da shi, anyi ta yanke ta gille tsakaninku,
wallhy kinji na rantse duk ranar da kika kara yarda Affan ya shigo dakinki har kika barshi ya kwana, hmmm faďin hukuncin da zan miki ma bata baki ne kina jina ko?
Afeeyah ta gyaďa kanta tace eh inaji, oyizah ta saki hijab dinta ta kara kai mata duka a kai tace bace min a gaba ko in illata ki, da sauri Afeeyah ta wuce daki tana kuka******

Bayan hajja ta gama rarrashinta ta zuba mata abinci ta karba ta fara turawa da sauri saboda azabar yunwar da takeji,
cikin tausayawa hajja ta fara bata baki cikin hikima da kalamai masu taushi,
sai da ta tabbatar da hankalinta ya kwanta sannan ta tashi tafi gida cike da tausayin yar jikarta da ta fara dandana rayuwar duniya, dan da sam Afeeyah bata san bacin rai ba kullum cikin farin ciki take in ka ganta tana kuka to na shagwaba ne, babu wanda zai taka ta ta barshi bare har ya daura mata bacin rai duk wanda yayi mata take zata mayar mishi ta wuce hankalinta kwance..

Haka rayuwar Afeeyah ta kasance cikin kunci da bauta,
wulakanci kala2 babu wanda bata gani,
sam bata bari Affan ya ganta ko yazo yana bubbuga kofarta bata budewa,
ba karamin tausayi yake bata ba in ya fara buga kofar dan baya bugun hankali yana bugata yana ihu wani lokacin ma harda kukanshi,
abinci kuwa saidai hajja ta kawo mata dan bata nasu,
duk wannan wainar da ake toyawa alhj basheer bai sani ba saboda baya gari,

A ranar da ta cika sati uku a gidan tana tsaye tana mopping dining room,
oyizah da suwaiba suna zaune cikin parlon suna gulmarta,
suwaiba tace lallai yarinyar nan ashe duk iskancin da take mana guri ta samu,
ji yadda take muku bauta kuma duk zagin da kuke mata ta kasa tabuka komai,
oyizah tayi dariya tace ay wargi ma guri ya samu,
ni yaushe kamar wannan yarinyar zata tsaya min a gaba, ai wallhi kema suwaiba harda laifinki,
suwaiba tace ai da dinma daurin gindi ta samu to yanzu mai shagwabatan ya mutu shiyasa shegen bakinta ya mutu,
oyizah tace ai ko shugaban kasa ne ya tsaya mata bata isa ta min ba bare wannan tsinannan yaron mai shegen girman kan tsiya..

Afeeyah ta yar da mop din hannunta ta runtse idonta zuciyarta na tafarfasa,
muryar salma taji a bayanta cikin isa da gadara tace
kee..
je kiyi min pepper soup mai yaji sosai yanzu nan ki kawo min,
Afeeyah bata juyo ta kalleta ba ta tsalleke ruwan da take mopping dashi ta kama hanyar side dinta,
da sauri salma ta bita tana huci taja rigarta ta baya har saida wuyan ya yage tace ke dan uban— Afeeyah ta juyo cikin azama ta dauketa da gigitaccen marin da ya hanata karasawa yasata sakin Afeeyah bata shirya ba….

Mrs tijjani shattima…..
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣4⃣ By Aysha Ya’u Kurah

A firgice oyizah da suwaiba suka yo kan salma dake rike da kunci idonta yayi jajur,
fuskarta oyizah ta ďago tana shafawa ta kalli Afeeyah murya a sarke tace m-ari,
suwaibah ta jinjina kai a munafurce tace tabdijam, lallai yarinyar da tsaurin ido kike, ki kalli girman salma ki dauketa da irin wannan marin,
Afeeyah taja tsaki ta juya zata wuce oyizah ta saki salma ta janyota da karfi tana huci,
ihun da Afeeyah ta saki yayi daidai da shigowar alhj basheer parlon,
da sauri ya karaso yace subhanallahi lafiya safiya, me tayi miki,
oyizah ta saki Afeeyah da sauri ta juyo ta fara hawaye tace alhj ace kamar yarinyar nan ta dubi salma ta tsinka mata mari,
Afeeyah ta durkushe ta fashe da kuka tace dan Allah daddy ka kaini gurin hajja, wallhy kasheni zasuyi, dukana sukeyi kullum, yanzu ma dukana suka gama yi har suka yaga min riga,
dan Allah ka kaini gurin hajja,
kafin alhj basheer yayi magana mahmud dan suwaiba ya shigo rike da kular abinci a hannunshi,
ta gefen ido Afeeyah ta hangoshi cikin muryar kuka tace mamu kai min daki ka dauko kular jiya,

alhj basheer cikin mamaki yace meye a cikin kular nan, Afeeyah tace abincin rana na ne,
alhj basheer cikin tashin hankali yace duk abincin dake gidan nan sai an kawo miki abinci daga gida,
oyizah da ta gama tsurewa tace umm al— Afeeyah ta katseta da sauri tace sunce abincin gidan nan ba na talakawa bane wai ban saba cin irin shi ba saboda haka kar in taba musu,
oyizah ta sankare cikin mamakin sharrin da Afeeyah ta lafto musu,
alhj basheer ya juya ya kalleta cikin tuhuma tayi saurin cewa wallhy karya take min alhj, ya za’ayi in hanata abinci,
alhj basheer ya kalli mahmud yace kai tun yaushe kake kawo ma Afeeyah abinci, mahmud yace kullum nake kawo mata da safe da rana da daddare,
alhj basheer ya saki salati yace kin kasheni safiya,
kin tozarta ni a unguwar nan, yanzu kowa ya gama sanin sirikata daga gidansu ake kawo mata abinci,
oyizah tace wallhy alhj kar—rufe min baki ya fadi cikin daga murya,
ya dago Afeeyah ya kalli wuyan rigarta yace yi shuru ki share hawayenki karki kara cewa zaki je gida sannan yau ďinnan zan siyo miki komai na abinci ki dinga girkawa kina ci a dakinki,
salma cikin kuka tace daddy marin da yarinyar nan tamin taci bulus kenan,
alhj basheer ya juyo yakai mata wani marin a baki yace in mafaďin magana wawa ne ai majiyinta ba wawa bane,
yaya za’ayi Afeeyah ta iya daga hannu ta mare ki,
salma cikin kuka sosai tace na rantse da Allah daddy ta mareni,
ta kalli Afeeyah suka hada ido ta sakar mata gwaloo hade da murmushi salma ta kara tunzura tayo kanta zata duketa alhj basheer yace wallhy tallahi kika taba yarinyar nan sai na lahira ya fiki jin dadi,
oyizah dai tana tsaye kamar gunki mamakin Afeeyah ya hanata cewa komai, haka suwaiba,
Affan ne ya fito da gudu jin muryar mahaifinshi, rungumeshi yayi iya karfinshi yace daddy ka dawo,
alhj basheer yace na dawo Affan kana nan lafiya ko,
Affan ya noke wuyanshi ya haďe rai yace daddy nayi fushi da Afeeyah bazan kara mata magana,
alhj basheer yayi murmushi yace me tayi maka,
Affan yace batason wasa dani kullum sai su anty salma suyita sata aiki ta goge can, ta goge nan, tayi girki da yawa kuma ita bata ci, kuma sai ta rufe kofa ta hanani shiga inyita bugawa taki buďewa,
alhj basheer ya harari salma da oyizah sannan ya kalli Afeeyah yace meyasa bakya bude mishi kofa,
oyizah tayi saurin cewa dan Allah alhj kabar maganar nan muje ka huta anjima sai ayita,
alhj basheer bai kalleta ba yace Afeeyah dake nake magana,
Afeeyah ta dago kanta ta kalli oyizah da zufa ya jikata tace daddy saboda shan maganinshi ne na dare, kafin lokacin yayi nayi bacci bana sanin yana bugawa,
oyizah ta saki ajiyar zuciya a hankali..

alhj basheer yace wannan ba hujja bace daga yau ma duk magungunshi ke zaki dinga bashi,
Affan ya kalli oyizah yace mummy wai ita zata dinga bani magani?
Oyizah ta haďiye miyau tayi murmushi tace eh hakan ma yafi, Affan ya kalli Afeeyah yace zaki dinga bani magani dakyau yadda mummy take bani,
Afeeyah tayi murmushi ta saci kallon oyizah tace sosai ma, kasani ma ko in fita iya baka da kyau,
yayi tsalle ya rungumeta yace to muje mu dauko magungunnan mukai dakin mu ko,
alhj basheer yayi dariya yace banason shirme ka bari mummynka zata kawo maka har ďaki,
ya kamo hannun Afeeyah yace zo muje muyi wasa irin na rannan,
Afeeyah tayi saurin fisge hannunta ta wuce daki cikin jin kunya, ya bita a baya da gudu,

alhj basheer ma daki ya wuce ba tare da ya kalli oyizah ba,,
suwaiba tace kinga abinda nake faďa miki game da yarinyar nan ko,
oyizah tace uhummm kawai ta wuce daki salma ta bita har lokacin kuka takeyi,,, suwaibah taja gyalenta itama tayi waje…

Karfe huďu na yamma alhj basheer ya dawo gida motarshi cike da kayan abinci,
masu aikin gidan maza su suka shiga da kayan lokacin Oyizah na zaune a parlor tana ta tufka da warwara, ko kallonsu batayi ba har suka gama shigewa da kayan suka fita,
shigowar alhj basheer ne yasata mikewa da sauri tana mishi sannu da zuwa, bai amsa mata ba yace kin kai wa Afeeyah magungunan,
oyizah tace yanzu zan kai mata alhj, dan Allah ka fahimceni wallhy–yayi saurin dakatar da ita da hannu yace babu abinda zaki fada min in yarda,
tsakani da Allah safiya a bani amanar yarinya ku hadu ke da yayanki ku dinga kuntata mata,
oyizah ta fashe da kuka tace wallhy alhj sharri tayi mana, kaima kasan abinda zanyi da wanda bazanyi ba,
yace in ke baki mata ay yayanki na mata kuma bakya tsawatar musu,
Oyiza ta kara tsananta kukanta tace dan Allah kayi hakuri wallhy zan dauki kwakwaran mataki akan su,
dakyar alhj basheer ya hakura kuma yasa ta kira su salma yayi musu concrt warning akan Afeeyah…
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣5⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Cikin fushi tace dalla ni sakeni in gaida ubangijin da ya halicceni kuma ya raine ni da ni’imominsa,
Affan ya kwantar da kanshi a kafadarta yace ni kike ma ihu ko?
Tayi tsaki tace ay kai duka ne ma ya kamace ka ba ihu ba,
ya dawo gabanta yayi narai2 da ido yace zaki iya duka na,
tace sosai ma in dai bazaka dinga yin sallah ba,
ta tallabi fuskarshi da hannunta ta rage murya tace kasan falalar dake cikin yin sallah?,
Affan ya girgiza kanshi,
tace ko na fada maka bazaka gane ba,
ka faďa min duk abinda kakeso wanda yake ranka yanzu,
ya rufe idonshi cikin murna yace ammmm inason ganin abokina, ya bata rai kamar zaiyi kuka yace abokina ya gudu ya barni ya daina zuwa guri na nayi fushi dashi,,
idon Afeeyah ya ciko da kwallah tace kar ka damu zaizo ya ganka, amma fa sai ka yarda kayi sallah, yace in nayi zaizo tace sosai ma,
Affan yace to sai kuma ina son kullum ki dinga tayani wasa,
mu buga game tare, mu buga kwallo tare, Afeeyah tayi saurin cewa har abinci ma tare zamu dinga ci mu dinga bacci tare amma fa sai ka yarda kayi sallah,
ya daka tsalle yace yeeee zanyi,
Afeeyah tace sai me kuma,
ya bata rai yace sai kuma su anty salma, banason suna min ihu suna zagina wata rana harda duka na akai, in nayi sallah zasu daina, tace sosai ma, ai in ka yarda kayi sallah ko sun maka ihu zan rama maka,
yayi dariya yace yauwa barbie na to muje muyi sallah,
ta dauko dadduma ta shimfiďa mishi duk da tasan ba daidai zaiyi sallar ba amma gara yayi wit tym zai fara yinta daidai,

Guri ďaya suka tsaya ya maida hankali yana yin duk abinda tayi yana waige,
isha’i sukayi da shafa’i kadai banda wutiri,
saida ta gama lazimi sannan tace mishi ya ďaga hannunshi sama kamar yadda tayi, yayi yadda tace,
tace yauwa to duk abinda nace kace “Ameen” ya sauke hannunshi yace nace “Ameen” tace a’a kar ka sauke hannun ka ďaga hannun, yace “Ameen”
tayi dariya ta kama hannunshi tace haka zaka barshi, ya kuma cewa ameen,
cikin dariya ta fara karanto adduo’i yana cewa Ameen,
inuwar mutane ta gani a kansu ta ďago da sauri ta kallesu,
bata tsayar da addua’r ba saima sake mata salo da tayi ta hanyar faďin
“Auzubillahi minash shaidann rajim”
Affan yace ameen da karfi yana kallon oyizah dake huci fuskar nan babu annuri,
salma ta daka mishi tsawa tace tashi ka fita a dakin nan,
jikin Affan ya fara rawa yana kokarin mikewa Afeeyah ta matse hannunshi ta shafa addua’r da ta idar tace ina zaka je,
Fareeda tace gidan uwarki zaije, tashi ka fita ko in tattaka ka,
Afeeyah tace ikon Allah, to dai nasan Affan baida wani dakin da ya wuce na matarshi,
saboda haka babu inda zashi,
oyizah cikin fushi tace kika ce me?
Afeeya ta kalli salma tace maimata mata inaga kamar tana da matsalar ji,
salma cikin fushi ta kai mata naushi da sauri Afeeyah ta kauce tace toh fah!!, ashe dai rashin aure ba masifa kadai yasa ku harda harkar dabanci, fisabillihi ku ko kunya bakwa ji, ni bansan meyasa kuke bakin ciki dani ba dan nayi aure at dis age of mine, dan Allah ku barmu muci soyayyarmu ni da mijina zan muku addua’ kuma Allah ya kawo mashinshini nan bada dadewa ba dan rik’ar da kukayi a gida ta isa haka, abun ma ni har tausayi yake bani,
babu wanda ya iya cewa komai sai kallon mamaki da suka bita dashi,
cikin karfin hali salma tace ina mijin yake anan da zamuyi bakin ciki,
ke nan har wani miji ne, wannan tababben da baisan kanshi ba ma bare mace,
Afeeyah tayi saurin cewa tabdijam,, ke kike ganin tababbe,
ta rungumoshi tace ni nan namiji nake gani wanda a cikin maza ma sai an tona kafin asamu irinshi,
dan Allah ku fitar mana a ďaki dan naga alamar baku san wannan lokacin na hutawar ma’aurata bane,
fareedah ta harzuka matuka ta ajiye maganin hannunta tayi kan Afeeyah zata duketa oyizah tayi saurin dakatar da ita da hannu, tace barta fareedah wallhy sai tasan ta faďa muku wadannan maganganun,
kuzo mu tafi,
Afeeya tace to sai da safenku Allah ya aurar daku ku huta da kunci, amma fa mummy baki nuna min yadda zan bashi maganin ba,
oyizah kamar ta rusa ihu tasa kai ta fita ba tare da ta bata amsa ba,
Afeeyah ta bisu da li’ilah fi quraish ta datso kofar ta dawo ta kalli Affan da ya gama tsurewa tace matsoraci to sai ka zauna tunda dodonka ta tafi,
Affan ya zauna murya a sarke yace mummy tayi fushi dani ko,
Afeeyah tace batayi fushi ba bari in kawo maka abinci kaci sai kasha magungunanka kayi bacci kaji,
Affan ya gyaďa kanshi,
Da kanta ta bashi abinci yana gama ci yasha ruwa da drink ta dauko magungunan da oyizah ta kawo,
saida ta karance su tsaf ta kalli wani ruwan jarka shi ba ja ba shi ba maroon ba, daga kafadarta tayi tace may be na gargajiya ne,
na asibitin ta fara bashi duk wanda ta kai bakinshi sai tace yayi bismillah sannan zata zuba mishi,
tana bude na jarkar taji wani karni karni, da kyar ta tsiyayya a cup tace wa’iyazubillah wannan irin karni haka, ta mika mishi tace kayi bismillah, yana yin bismillah ya kai bakinshi yaji hannunshi na rawa sosai, da kyar da taimakon Afeeyah ya shanye maganin,
boye magungunan tayi ta gyara gurin ta dawo ta zauna tana mishi hirah yana kyakyata dariyah harda buga kai a pillow,
sun shagala sosai cikin farin ciki Afeeyah taji ana buga musu kofa, mikewa tayi tana mita a zuciyarta,
tana budewa taga oyizah tsaye kamar gunki,
Afeeyah taja baya tace kin dawo ne mummy,
Oyizah ta kalleta tace tambayar da ya kamata kiyi min kenan ni da gidan mijina, Afeeyah tayi dariya tace to ai wannan tambayr tafi da inyi miki shuru in kyaleki, kuma nima nan turakar mijina ce,
oyiza tace wallhy zan babbalaki a gidan nan in bawa karnuka kasusuwanki su cinye,
Afeeyah tace waii ay ko da sunci kashi da wahala dan wallhy kashi na taurin tsiya gareshi,
oyizah tayi shuru dan taga abinda ke neman fin karfinta tace kin bashi magungunan,
Afeeyah tace wannan dole ne tunda inason mijina ya samu sauki, oyizah tace akwai wani a jarka ki tabbatar yasha dama dan in jaddada miki ne yasa na dawo,
Afeeya tace karki damu in ma akwai wani ki karo bazan gajiya ba,
oyizah tayi tsaki ta wuce ranta a bace,
ta riga ta gama kudirawa a ranta a daren nan zata lalata rayuwar yarinyar nan, wallhy yau sai tasan ta tabo ni, dan bazan barta ba abinda ta dinga fadi kenan,,,,,

To oyizah sarkin sa’a muna miki fatan nasara akan Afeeyah… …

Mrs tijjani shattima….

[PM, 05/04/2016] Ummu Nan: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣6⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Tun sha biyun dare Afeeyah ke jin wasu irin sautittika masu ban tsoro ta windon ta,
kallon Affan tayi yana baccinshi hankali kwance,
cikin dabara ta cire hannunshi a jikinta ta gyara mishi kwanciya ta mike a tsorace saboda sautin karuwa yakeyi,
cikin karfin hali da dakewar zuciya ta ďaga labulen windon dakin,
sakin labulen tayi da sauri taja baya tana maimaita “HASBUNALLAHU WA ‘NI’IMAL WAKIL” saboda ganin wasu halittu masu ban tsoro kewaye da windon,,,
wani kara taji an saki nan take taji ďakin da suke ciki yana girgiza ta ko’ina,
runtse idonta tayi tana karanto adduo’in neman tsari,
da dai taga kamar kara girgiza ďakin akeyi sai tayi karfin halin buďe kofarsu cikin sauri tayi hanyar da zata sadata da ďakin oyizah,

Tana zuwa kofar dakin ta kama murfin xata bude taji sautin magana da karfi wanda ya sata sakin kofar bata shirya ba,
sunanta taji sosai ana kira a ďakin ta kuma ji wannan sautin na windon su ya dawo nan inda take tsaye,
a gigice ta leka ta windo don jin mai ambaton sunanta cikin wannan sigar a kuma wannan talatainin daren,
tana lekawa ta hango oyizah cikin jajayen kaya tsugune gaban “chummy,”
sai wani bakin basamude a tsaye a gafensu rike da wani bakin kare,
Afeeyah bata kara firgita ba sai da taga oyizah ta dauki kwaryar jini ta shanye tass sannan ta kara daukan wani ungulu tana kiran sunanta dashi,

fitsari ta saki nan take saboda ganin duhu ta ko’ina bata iya hangen gabanta,
lalube ta fara yi tana addu’a da karfi tana kiran sunan hajja dan ta tsorata matuka da abin da idonta ya gane mata, ga wannan girgizar har lokacin bata bar jinta ba,
a cikin laluben taji hannunta ya taba mutum, nan take ta tsandara ihu haďe da faduwa kasa sumammiya,

A gigice alhj basheer da ya fito dan ganin abinda ya samu wutar gidan ya haskata da torch light,
cikin kidima ya fara kiran sunanta yana fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun, safiya, safiya,
oyizah ta tsorata matuka da jin muryar alhj basheer dan tasan yayi bacci,
cikin azama ta tattara kayan tsafinta ta cire na jikinta ta mayar da night gown din jikinta ta fito tana mutsika ido,
alhj basheer yace safiya zo ki kama min yarinyar nan mu kaita asibiti ko numfashi bata iya yi na rasa me ya fito da ita cikin daren nan,
oyizah ta matso da sauri tace wace yarinya,
alhj basheer yace Afeeyah ce, kamata da sauri dan Allah,
oyizah cikin murna ta kama Afeeyah dan a tunaninta tsafinta ne ya kamata,
suna fitowa wutar gidan ta kawo alhj basheer ya bude motar suka tura Afeeyah ciki, oyizah ta koma ta dauko hijab dinta suka wuce asibiti,

Tunda aka kaita asibiti a wannan daren likitoci ke iya kokarinsu suga ta farfaďo amma abin yaci tura,
oyizah cike da murna ta nemi guri ta zauna a zuciyarta tace yarinya ai tunda kika shiga gona ta sai kinyi noma wallhy,
alhj basheer kuwa hankalinshi ba karamin tashi yayi ba dan baisan meye ya sami yar mutane ba, safa da marwa kadai yakeyi a cikin asibitin,
dakyar doctor musah ya lallabashi akan in shaa Allahu zuwa gobe zata farfado in kuma bata farfado ba sai musan abin yi,
alhj basheer akanta ya kwana ko runtsawa baiyi ba,
ana kiran sallar asuba yaje yayi sallah ya wuce gidan malam atiku,
hajja a firgice ta fito idonta ya ciko da kwallah tana tambayar wane asibiti,
alhj basheer yace ki kwantar da hankalinki hajja, safiya na can zaune da ita ba sai kin je ba,
hajja tace inaaa aiko sai naje wallhy, ai kowane aiki da wakilinshi bazamu daura mata nauyin jinya ba,
malam atiku yace Baba ay tunda yace kar— tayi saurin katseshi tace walhi danbaba babu abinda zai hanani zuwa gurin hajara,
alhj basheer yace to shikenan hajja muje,
tayi saurin sa takalmi jiki na rawa ta bishi,

Suna isa asibitin suka tarar oyizah na bacci Afeeyah kuma bata farfaďo ba har lokacin,
gefenta hajja taje ta zauna tana kuka tana tofa mata addu’a,
alhj basheer yace ki kwantar da hankalinki hajja babu abinda zai sameta bari muje gida a kawo muku abinci, hajja tace to sannu alhj an gode,
alhj basheer yace haba ai yiwa kai ne nima ay yata ce,
ya kalli gurin da oyizah ke bacci ya dan bubbugata tayi firgigit ta farka tace
“an gama komai ko”
alhj basheer yace me aka gama,
oyizah ta fara goga ido tace na dauka doctor ne,
alhj basheer yace bashi bane ki sameni a mota mu wuce gida,
dakyar ta gaida hajja sannan tabi bayan alhj basheer suka wuce gida…

Alhj basheer na shiga parlor ya tarar da Affan zaune a kasa ya haďe kai da gwiwa yana kuka sosai,
da sauri ya karasa kusa dashi ya dagoshi yace meya faru dan gidan daddy,
Affan ya kwanta kan jikinshi yace daddy tun dazu nake neman Afeeyah ban ganta ba na duba ko’ina bata nan naje gurin mai gadi yace kai ka dauketa ka fita da ita, daddy ina kuka kai ta?
Oyizah tayi saurin matsowa kusa dashi tace sorry my baby Afeeyanka taje siyo maka abun dadi zo muje kayi wanka kafin ta dawo kaji,
cikin rashin gamsuwa da kalamanta yace mummy karfe nawa zata dawo,
oyizah tayi murmushi tace 10 zata dawo kaji, Affan ya gyada kanshi, tace yauwa baby muje kayi wanka kasha magani ko,
taja hannunshi suka wuce zuciyarta wasai dan jiya kadai Afeeyah ta kusa daura mata hawan jini yanzu kuwa zata ci karenta babu babbaka tunda ta tafi 4 good….

Goggo ta kalli kaka liman bayan ya gama karyawa tace sai tafiya ko,
ya goge bakinshi yace in shaa Allahu ai yau “ta dabo’ tayi kirah, goggo tace da ka bari sai gobe saboda akwai daddawa da dawo da zaka tafin ma da Abida dashi,
kaka liman yace ai ciwo ko mutuwa ne kadai zai hanani isa ta dabo yau,
Ke bazan ma iya bacci ba in banje ba,
tace to Allah dai ya tsare wannan tafiyr ta gaggawa,
yace ameen ke kike ganinta haka ni kuwa a guri na ba gaggawa bace saboda na dade ina sa rana banje ba, mafarkin da nayi jiya shi ya tabbatar min da wannan lokacin ne lokacin sa’a a garemu, Goggo tace to Allah ya bada sa’ar wannan sirrintaccen aikin da ko ni kaki yarda ka fada min,
kaka liman yayi dariya yace ameen ta liman, aikin ne saida sirri, tace haka ne ai sirri a komai ma yana da kyau Allah ya dawo daku gida lafiya,
ya mike tsaye yana faďin ameen ameen,
har zaure ta rakashi inda drivernshi da alhj bara”u ya ajiye mishi yake jiranshi,
saida suka sha mai a filling station sannan suka dauki hanyar KANO TA DABO TUMBIN GIWA…..

Mrs tijjani shattima…….
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: [7:13PM, 05/04/2016] Ummu Nan: ◆◆ RABO AJALI◆◆ 4⃣7⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Tiryan tiryan abubuwan ke dawo mata cikin kwakwalwarta,
a hankali ta fara motsa jikinta tana girgiza kanta, wadannan halittun ta dinga gani kewaye da ita suna kokarin shigewa jikinta,
wani irin ihu ta saki haďe da faďin hasbunallahu wa ni’imal wakil,
hajja dan Allah kizo ki taimakeni zasu kasheni,
zasu kasheni, wayyyo Allah nah,
Hajja tayi saurin katse sallar da takeyi ta yo kanta da gudu ta riketa, nan fa ta kara fasa wani ihun a firgice tana fisge jikinta,
addu’a hajja ta fara karantowa da karfi tana tofah mata,
a hankali ta bude idonta, ganin hajja ce zaune a gabanta yasa ta faďa jikinta tana kuka tana faďin kasheni zatayi hajja, wallhy kasheni zasuyi, dan Allah ki gudu dani gida,
a firgice hajja tace wacece zata kashe ki,
kafin Afeeyah tayi magana doctor musah ya shigo dakin da sauri nurses na biye dashi a baya,
karasowa kusa da gadonta yayi yace sannu mama, yanxu nurse take fada min taji tana ihu,
hajja tace wallhy farkawa tayi a firgice tana ihu bansan takamaimai abinda ke damunta ba,
doctor musah yayi gwaje gwajen da zaiyi yace dan Allah mama kice mata ta kula sosai ta daina yawan firgita saboda cikinta baiyi kwarin da zai dauki hakan ba dan bai wuce sati uku ba, Allah ma ya kiyaye cikin bai samu matsala ba, saboda haka dan Allah a kiyaye,
Hajja cikin mamaki tace ciki doctor, doctor musah yace kwarai mama,
hajja tayi murmushi tace ikon Allah, To Allah ya inganta mana, yace ameen mama ya bata magani yace in taci abinci a bata tasha, hajja ta amsa ta mike da sauri ta hado mata tea,
saboda murna hajja bata kara bi takan zancen da Afeeyah ke mata ba,,
Tana bata magani ta mike ta kabbara sallah,
kafin ta idar su alhj bara’u suka shigo, Amirah ta ajiye basket din abinci tayi gurin Afeeyah ta zauna tana mata sannu,
Abida ma ta karaso cikin dakin tace ashe ta farfado alhj,
alhj bara’u yace saidai in yanzu ta farfado amma dazu da muka zo da alhj basheer bata farfado ba,
Abida ta karasa kusa da ita tace sannu Afeeyah ya jikin,
a hankali tace da sauki ummi,
Abida ta karasa kusa da hajja da ta idar da sallah ta tsuguna suka gaisa, tace hajja me suka ce yake damun ta,
hajja tace to nidai har yanzu bansan dalilin firgicinta ba amma likita ya tabbatar tana dauke da karamin ciki na sati uku,
Afeeyah tayi saurin runtse idonta saboda takaicin fada musu da hajja tayi,
Allahu akbar alhj bara’u ya fadi yana murmushi,
Abida tace lallai Allah da iko yake, Allah ya fito mana da wannan zazzafan rabon lafiya, Hajja taji tausayin Abida sosai a hankali tace Ameen,
nan suka cigaba da yar hirarsu ta manya duk akan cikin, Afeeyah dai tunda ta runtse idonta bata bude ba har suka tafi,,,

Alhj basheer ma da yazo doctor musah ya faďa mishi ba karamin farin ciki yayi ba,,
bai wani dade a asibitin ba ya wuce gida dan kai ma su safiya albishir,,,

Da murnarshi ya shiga gidan, tun kafin ya karasa cikin parlon yake kwala ma oyizah kirah,
da sauri ta fito tana faďin alhj lafiya,
yayi dariya yace lafiya lau safiya albishirinki, gabanta ya faďi da taga yana dariya dan ta dauka kiran fađin mutuwar Afeeyah yakeyi mata,
a hankali tace goro, yace kin kusa samun miji ko kishiya,
cikin rashin fahimta tace ban gane ba alhj, yayi dariya yace ay dama bazaki gane ba tunda ba bahaushiya bace ke,
to ina nufin kin kusa samun jika,
oyizah ta haďiye miyau dakyar tace kana ta min magana a cukurkuďe a gurin wa zan samu jika,
alhj basheer yace kina da wani dan da ya wuce Affan ne,
oyizah ta saki baki tace ciki matarshi ke dashi,
yace kwarai kuwa, kinga rabo ko,
ranar da aka sa aurenta da jabeer a ranar aka daura auren da Affan kuma a ranar Rabo ya rantse kanshi,
oyizah da zufa ke keto mata ta ko’ina tace umm hakane yanzu ta farfaďo kenan,
alhj basheer yace garau ma tana can na barta a zaune,
oyizah ta mike tace to bari a haďa mata abinci a kai mata ko,
alhj basheer yace ya kamata kam, ki haďa mata duk wani abun da kika san me ciki na bukata in ma babu ayi min magana dan Allah, oyizah ta wuce tace to,
Zama tayi a kasa a dakinta ta zuba uban tagumi tana tunanin yadda akayi ta samu failure a aikin jiya, da kuma yadda akayi har ciki ya shiga jikin yarinyar nan,
inaaa bazai yiwu ba dole cikin nan ya fita, dole ne in kashe yarinyar nan dan wallahi bazan yarda ta sake dawowa gidan nan ba,
mikewa tayi zubur ta wuce kitchen ta shiga shirya abinci daidai cin mutum daya, tana yi tana zancen zuci dan bata taba yin aiki irin haka ta samu failure ba..

Gab da la’asar kaka liman ya bayyana a asibitin,
a zaune ya samesu hajja ta tasa mata abinci a gaba tana ci, fuskar hajja dauke da fara’a ta gaishe shi ya amsa yana kallon Afeeyah,
Afeeyah ta sunkuyar da kanta ta gaishe shi ya amsa yana murmushi yace ya jikin kuma,
Afeeyah tace da sauki, ya zauna a kan kujera yace to Allah ya karo sauki, suka ce ameen ita da hajja,
saida suka dau kusan minti biyu shuru sannan ya kalli hajja yace dan Allah hajja in bazaki damu ba ko zaki dan bamu guri,
Hajja ta mike tace haba babu komai wallhy ta fita daga dakin,

Bayan fitar hajja da kamar minti uku kaka liman ya kalleta yace ya mai gidan naki,
Afeeyah tace yana nan lafiya kaka,
kaka liman yace lafiyar ciki ko ta waje,
Afeeyah ta dago cikin rashin fahimta tace ban gane ba kaka, yace ina nufin wace irin lafy, lafiyar koshin lafiya ko kuma ta duka harda kwakwalwa,
Afeeyah tace lafyr koshi kaka, sannan lafiyar kwakwalwarshi ma ina tantama akanta,
wani lokacin in yayi abu kamar cikakken me lafy baya mintina kuma sai ya koma kamar da,
kaka liman yace to yaya kika fahimci mutanen gidan, ina nufin a tunaninki wane irin zama sukeyi da yaron nan, kina ganin suna kaunarshi tsakan— sammm ta katse kaka liman, tace muguwar tsana sukayi mishi wallhy,
amma a gaban daddy sai su nuna basu da kamarshi, sannan kaka bata barinshi yayi sallah, duk wata ibada bata barinshi yayi, sannan kaka jiya da dadd— yayi saurin katseta yace tambaya daya nayi miki, bari in yi miki cikakkun bayanai akan abubuwan da baki fahimta ba tukunna sai mu shiga wani,

mijinki ba lafiyar koshi kadai gareshi ba harda ta kwakwalwa,
tambayarki zanyi,? tsakaninki da Allah kinajin zaki iya yin duk abinda ya dace domin ki kubutar da mijinki daga wannan halin da yake ciki,?
Afeeyah ta gyada kanta tace zanyi kaka,,, yace yauwa yar albarka,

Ki sani mijinki ya samu saukin tabuwar da kwakwarshi tayi sai dai kuma azababben sihirin da ake mishi shi ke kara dagula kwakwalwar ya rasa fahimtarshi ya dinga yin abu kamar yaro, wani magani ake bashi wanda idan yayi awa shida bai sha ba zai iya dawowa mai lafiya amma ba sosai ba saboda akwai wasu tsibace tsibbacen da aka birne a cikin gidan wanda gano su sai ansha matukar wahala,
duk ranar da aka hako wadannan asiran to wannan ruwan maganin ya daina tasiri a jikinshi domin duk wata tabuwar kwakwalwa zata barshi, karki ce sihirin wasa akayi mishi, wannan na gasken gaske ne wanda yake da matukar wahalar karyewa, kin fahimceni ko, Afeeyah ta gyaďa kanta tace ay kaka duk abinda aka ce min matar nan zatayi bazan musa ba saboda ni ganau ce ba jiyau ba,,,
shigowa dakin sukaji anyi babu sallama,
da sauri suka waigo dan ganin ko waye…….

Mrs tijjani shattima…..
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣8⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Oyizah suka gani tsaye idonta kyarr kan Afeeyah, gefenta kuma salma ce rike da basket din abinci,
gaban Afeeyah sai faduwa yakeyi a zuciyarta tana adduar Allah yasa bata ji tautanawarsu ba,
gyaran murya kaka liman yayi ya kalli oyizah yace an wuni lafiya,
da sauri ta kauda kanta tace lafiya lau ta karaso gaban gadon Afeeyah jikinta a mace tace ya jikin,
da sauki Afeeyah ta fadi ba tare da ta kalleta ba,
salma kuwa ajiye basket din tayi ta koma gefe tana cika tana batsewa,
mikewa kaka liman yayi ya kalli Afeeyah yace bari in koma,
Kiyita “hasbunallahu wa ni’imal wakil” saboda maganin musibun duniya, Allah ya kara sauki ya kuma inganta abin dake cikin ki,
Afeeyah tace ameen kaka nagode yaushe zaka dawo,
yace too zan dai gani amma ay bazan koma ban sake dawowa ganin jikin naki ba, tace to sai ka dawo kaka,
ya kalli oyizah da kanta ke kasa yace to hajiya sai anjima ko, tace to sai anjima,
har ya fita ya kuma lekowa yana kallon kwandon abincin yace
“ki danne kwadayinki, in har ya taso miki to ki tambayi goro a baki domin kwantar dashi kin gane ko”
Afeeyah ta kalli kwandon nan take ta gane manufarshi tace to kaka nagode,

Oyizah da ta tabbatar kaka ya tafi sai ta dago kanta ta zauna ta dafa Afeeyah tace sannu, amma jikin da sauki ko,
umm kawai Afeeyah tace,
oyizah tace kin ci abinci kuwa,
Afeeyah ta yatsina fuska tace bana iya cin abinci amai yake sani, oyizah tayi murmushin mugunta tace shiyasa na dafo miki abincin da nasan masu ciki naso,
salma ďan zubo mata,
Afeeyah tayi saurin cewa a’a ta barshi doctor yace a daina bani abinci saboda aman na wahalar dani, oyizah tace doctors din nan sun cika iyayi manta dasu kici babu aman da zakiyi,
Afeeyah tace saidai ko zuwa anjima dan yanzu bacci nake ji, oyizah zata kara magana cikin bacin rai salma ta katseta tace haba mummy dole ne, ji yadda kike wani pettn dinta tunda tace baza taci ba ba sai ki kyaleta ba, cikinta,,,,
oyizah ta harari salma tace baki san me lalurar ciki sai an matsa mishi yake cin abinci ba,
ko so kikeyi in bari ta wahalar min da jika,
Afeeyah ta kwanta tace uhmm,
oyizah tace rabu da salma kinji bata san lalurar ciki ba shiyasa, salma tayi tsaki ta tashi ta fita daga dakin tana mamakin yadda mummy ke lallaba wannan yar iskar yarinyar,
babu yadda oyizah batayi ba akan Afeeyah taci abincin da ta kawo amma firr taki, har hajja ta shigo tasa baki Afeeyah tace ita sam yunwa ne bataji kuma tana ci zatayi amai,
oyizah ta boye bacin ranta tace to hajja anjima ki tabbatar taci saboda bai kamata mai karamin ciki ta dinga zama da yunwa ba,
hajja tace karki damu in shaa Allahu zata ci, oyizah ta dan kara zama shuru kafin ta tashi tayi musu sallama haďe da jaddada ma hajja akan ta kula da Afeeyah ta dinga cin abinci akai2,

cikin mamaki hajja ta kalli Afeeyah tace kin ga matar nan yadda ta canza kamar ba ita ba, gaskiya naji dadin yadda ta nuna kulawarta gareki ga dukkan alamu ta saduda ta fara sonki,
Afeeyah ta juyar da kanta gefe a zuciyarta tace kwarai kuwa tana matukar son kasheni hajja ai dole ta kula dani kafin hakanta ya cimma ruwa,
buďe kulolin abincin hajja tayi tana fadin masha Allah irin wadannan namomi haka,
Afeeyah tayi saurin mikewa tace hajja dan Allah a ina zan samu agwaluma ko cashew anan gurin,
hajja tace aiko akwai wani mai agwaluma da na gani anan waje bari in duba Allah yasa bai tafi ba,
Afeeyah tace ameen dan Allah hajja ya baki mai tsami sosai, hajja tace to ta fita da sauri,
tana fita Afeeyah ta mike ta kwashi kulolin abincin tayi waje dasu ta zuba a bola tayi saurin komawa daki, ko minti biyar hajja batayi ba ta dawo da agwaluma cikin leda ta mika mata,
kwanciya Afeeyah tayi ta dauki agwaluma daya ta fasa ta fara sha,
salatin hajja ne yasata juyowa da sauri tace lafiya hajja,
hajja tace kulolin ne naga babu komai, Afeeyah tace eh na cinye baki ga dama na mutum daya ta yi ba, hajja tace daga fita ta har kin cinye, Afeeyah tace eh mana to nawa abincin yake,
hajja tace shine dan bakar mugunta ko naman baki ragemin ba,
Afeeyah tayi dariya tace ke kuma nama ne aranki sai kace wata kurah,
hajja tace waya sani ko kurar ce gaskiya kin shiga hakkina,
Afeeyah tace karki damu hajja nah anjima nasan zamu samu wasu naman,
hajja tayi tsaki ta tashi ta fita wanko coolers din…

Bayan isha’i kaka liman ya dawo asibitin, sun dade suna hirah da hajja kafin ta basu guri shi da Afeeyah,

kaka liman ya kalli Afeeyah yace dazu muna magana bamu gama ba na tafi,
yanzu sai muyi sauri dan naji gobe za’a sallameku ko,
Afeeyah tace eh,
kaka liman yace nima goben zan koma,
da fatan duk abubuwan da na fada miki dazu kin fahimcesu ko,
Afeeyah ta gyada kanta,
yace yauwa to yanzu sai ki faďa min abinda kika gani,
nan Afeeyah ta faďa mishi duk abinda ta gani jiya da daddare,
kaka liman ya jinjina kanshi yace wannan shine abinda nakeso Allah ya nuna miki dan nasan da na faďa miki hakan tun farko to tsoro bazai barki ki shiga gidan ba ma bare har tausayin affan ya shigeki ki yarda da taimakon da zakiyi,
wannan abun da kika gani shi jabeer ya gani amma nashi ya banbanta da naki saboda shi yaji suna tsafin ne akan Affan da mahaifiyarshi,
shin tunda kika shiga gidan kinji ko sau ďaya alhj yayi maganar zeenatu,
Afeeyah ta gyada kanta, kaka liman yace to bashi ba ma har yan uwanta da makusantanta basa iya maganarta ko ke kin taba tuna ta tun bacewarta,
cikin mamaki Afeeyah tace a’a kaka,

kaka liman yace mugun asiri akayi mata,
karyewar asirin na farko shine jin da jabeer yayi mata har ya sanar da ni,
a aikin da nayi na gano laya ce aka turata cikin bakin DAMO aka binne ta anan cikin gidan da kuke,
Afeeyah ta zaro idonta tace a cikin gidan? yace kwarai kuwa,
sannan duk wasu asiran da tayi a cikin gidan ta binnesu da yawansu bansan takamaimai inda ta binne ba amma suna cikin gidan,
in har Allah ya taimakemu muka san inda suke har muka ciresu to saukin abun yazo dan mun riga mun gama wasu ni da jabeer karashen ne wannan kuma sune masu wahalar,
Afeeyah ta jinjina kanta tace to kaka ya za’ayi musan inda tayi binne binnen,
kaka liman yace shine yanzu abinda nake tunani,
hannu yasa a aljihu ya ciro wata bakar leda, bude ledar yayi ya fito da wasu layu guda biyu da wani ruwan turare sai garin magani,
layun ya fara mika mata yace rike wadannan layun, dafatan zaki jajirce akan duk abinda zaki gani,
Afeeyah tayi kulu kulu da ido tace kaka banyi yarinya da daukar wannan kasadar ba kuwa,
kaka liman yayi dariya yace Afeeyah kenan sai kiga abinda zakiyi ni bazan iya yinshi ba saboda wani lokacin kwakwalwar yaro tafi ta babba kaifin rike abu,
Afeeyah ta gyada kanta tace to Allah ya bani juriyar iyawa yace ameen abinda ya kamata ki fadi kenan,
wadannan layun a karkashin pillown ki zaki sasu,
in zaki kwanta kiyi alwala kiyi sallah kiyi addu’a sosai akan Allah ya bayyana miki guraren da akayi wadannan binne binne, sannan ki shafa wannan turaren a jikinki ki kwanta kina mai kyautata niyya, in shaa Allah cikin kwana bakwai Allah zai nuna gurin da suke,
duk wani abun tsoron da zaki gani na rokeki ki daure kar wannan tsoron ya sare gwiwarki,
ke kadaice garkuwar bayin Allahn nan, in har kika sare to ki sani babu wani wanda zai iya daurewa yayi wannan aikin,
Afeeyah ta gyaďa kanta tace in shaa Allahu kaka zan daure, nasan ina tare da Allah da kuma kai,
yace masha Allah, sannan wannan maganin ki dinga ba Affan yana sha, kafin kwana bakwan nan zai dinga yin wasu abubuwa wadanda zasu dinga dawo dashi cikin hayyacinshi ya dinga tunanin abubuwan mamakin da suka faru dashi a shuďaďdun lokuta, kin gane bayanin ko,
Afeeyah ta gyada kanta tace eh na gane, to amma kaka yaya zanyi in na gansu,
kaka liman ya mike yace wannan kuma shawararki ce,
in kiga zaki iya ciresu ki taimaki uba da kakar abin dake cikinki to in kuma zaki barsu su dawwama a haka nidai na gama nawa yanzu naki kadai ya rage sai mu barma Allah sauran,
Afeeyah tace to kaka nagode sosai, ya miko mata wayarshi yace samin numberki kiyi flashing in wani abu ya shige miki duhu kya nemeni,
Afeeyah ta amsa tasa mishi numbrta sukayi sallama ta bishi da kallo har ya bace ma ganinta
, ganinshi kadai yana kwantar da hankalinta, badan tsufan shi ba da babu abinda zai hana a kirashi da jabeer dinta….

Mrs tijjani shattima…..
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 4⃣9⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Karfe 9 na safe aka sallameta suka ďunguma zuwa gida a motar alhj basheer,
oyizah na zaune a parlonta tana gyara farce hankalinta sam ba’a kwance yake ba dan
tun jiya take jiran jin mummunan labari game da Afeeyah amma shuru gashi har gari waye,

Shigowar motar alhj basheer ne yasa ta mike ta kwashe kayan gyaran kumban dan taje ta tarboshi ko zataji wani labari a gurinshi,
tana buďe kofar parlon tayi tozali da mai taurin kashi wato Afeeyah,
kallon mamaki ta tsaya yi mata a zuciyarta tace to ko karya hajja take mata yarinyar nan bata ci abincin ba,
Afeeyah ta katse mata zancen zucin da takeyi tace ina kwana,
oyizah ta sauke ajiyar zuciya tace lafiya lau ta juya ciki bata ko bi takan hajja dake rike da kaya ba,

Side dinsu ta wuce tana kallon hanya ko zata ga Affan,
da bismillah ta murďa kofar dakin suka shiga ita da hajja,
bayi ta wuce ta cire kayan jikinta tayi wanka ta dauro alwalar walha, ta windon bayin ta hangoshi
zaune gurin fishpond idonshi kyar a cikin ruwan baya ko kiftawa, murmushi tayi ta fito daga bayin,

sai da tayi sallah ta shirya cikin bakar jallabiya sannan ta fita gurinshi,

A hankali ta karasa gurin tayi saurin rufe mishi ido da hannunta, shafa hannun yayi cikin firgici yasa ihu yana ďaga kafarshi dan kar ya faďa cikin ramin kifin,
da sauri ta toshe mishi baki tana dariya tace nice matsoraci, juyowa yayi ya kalleta nan take ya saki dariyar farin ciki ya rungumeta yace ina kika tafi ki barni,
ta dago fuskarshi tace ina daddy yace maka ya kaini,
ya shagwabe fuska yace mummy tace min bazan kara ganin ki ba, jiya suka dinga min ihu anty salma har da duka na,
Afeeyah tace am sorry gani na dawo daga yanzu babu wanda zai kara maka kallon banza ma bare har ya dukeka tashi muje kaci abinci,
ya mike da sauri yana dariya suka wuce daki…

Da sauri oyizah ta bar gurin dan kar Afeeyah ta ganta,
wani irin bakin ciki ne yake taso mata a cikin zuciyarta,
shin me zata ma wannan yarinyar ta daina ganinta kwata2 a rayuwarta,
a cikin yan kwanakin nan ganin yarinyar nan shine abinda yafi komai bakanta ranta, aiki biyu kenan tayi akanta kuma duk masu karfi amma basu kama ta ba,
tabbas wannan gara inyi mata me kankat, tabbas yau ne numfashinta na karshe a duniya dan barin Afeeyah a duniya barazana ce a gareta dan yarinyar na neman fin karfinta,
a tarihin rayuwar oyizah tun tana karama babu abinda ke tsaya mata a gaba bata kau dashi ba dan haka wannan karan Afeeyah bata isa ta rusa sa’arta ba,
da wadannan tunanin ta karasa ďaki ta zauna neman mafita, wani sashi na zuciyarta ya bata amsar cewar ta bada Afeeyah kawai su “chummy” suyi bandaro da jinin tsinaniyya, in ba hakan tayi ba to kuwa tana zaune kwado zai mata kafa,,
dariya tayi cikin gamsuwar shawarar da zuciyarta ta bata, nan ta mike ta fara shirye2 kafin dare yayi ta sadaukar da jinin ďiyar ma’u da malam Atiku,

To oyizah muje zuwa muga zaki iya da Afeeyah…

Cikin jindadi suka kammala cin abincinsu na dare wanda hajja ta aiko musu,
bayan sun gama ta jiko maganin da kaka ya bata ta bashi yasha dakyar yana sha yana furzarwa,
saida ta nuna mishi bacin ranta sannan ya sha da yawa,
yana gama sha ta gyare gurin ta dawo ta zauna suka fara yar hira,
murďa kofar suka ji anyi suka waiga suna kallonta,
da fara’a ta karaso gurinsu tace amarya da ango, sannunku da hutawa,
Afeeyah ta kau da kanta tace yauwa, oyizah ta zauna gefensu tace Afeeyah ya kamata ki ďan leka gida ki gaishesu dan gani nayi tunda kikazo gidan nan baki shiga ba, daga nan sai ki dan zaga da Affan yaga gari ko ya kikace,
Afeeyah tace hakane mummy amma ay naga affan baya fita ko,
oyizah tace shiyasa nake so ki ďan fara fitar dashi yayi refreshing,
Afeeyah tace to duk yadda kika ce, ta mike ta dauko hijab dinta tace tashi muje,
ya tashi yana kallon oyizah alamun yana so ya tambayeta yaje ko a’a,
gyaďa mishi kai tayi alamar yaje, dariya yayi ya bi bayan Afeeyah suka fita,
dariyar jin dadi oyizah tayi ta rakasu har gate sannan ta juyo da sauri tayi dakinta ta kwaso kayan tsafinta ta nufi side din su Afeeyah,

Tafiya takeyi da sauri saboda manta Turaren da tasa a ranta duk ranar da xata gida zata kaima mahifinta,
tun a parlor ta gane akwai mutum a bed room dinta,
labewa tayi ta leka a hankali,
ba karamin firgici ta shiga ba ganin oyizah tsaye a gefen gadonsu tana shimfiďa farin kyalle a kasan katifarsu,
da sauri ta fita daga dakin lokacin da taga ta dauko zanin gadon su ta mayar ta shimfidashi yadda yake,
a guje ta fita ta samu affan a inda ta barshi murya na rawa tace muje,
ya kalleta yace ina turaren, dakyar ta saita kanta tace muje dai gobe zan kai mishi..

Sai goma saura suka dawo gida,
babu wanda Afeeyah ta faďa ma abin da tagani dan ta riga ta gama kudira abinda zatayi tana komawa gida,
suna shiga ta zaunar da Affan a parlor ta kunna mishi tv tace kar ya tashi bari ta gyara cikin dakin,
tana shiga daki ta yaye zanin gadon da bismillah ta ciro farin kyallen ta naďe zanin gadon ta ajiyeshi gefe sannan ta fito ta kalli affan tace ina zuwa bari in mayar ma da mummy zaninta,
yace to ya cigaba da kallon cartoon dinshi,
tana fita tayi hanyar ďakin mummyn cikin sanďa dan tasan yanzu tana gurin daddy,
a hankali ta murďa kofar ďakin ta shiga da addua a bakinta,
da sauri ta yaye zanin gadon tasa farin kyallen kamar yadda taga oyizah tayi sannan ta maida zanin gadon ta shimfidashi yadda yake tasa kai ta fita daga ďakin da sauri…..

Mrs Tijjani shattima
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣0⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Tana komawa daki ta tarar da Affan na gyangyaďi a kan kujera,
da sauri ta shiga ďaki ta canza zanin gado ta tofe ko’ina da addu’a ta sa layun karkashin pillownta sannan ta shiga bayi ta ďauro alwala ta fito ta wuce parlor ta tarar har ya bingire a gurin yana bacci,
tashin shi tayi a hankali ta kaishi ďaki ta tofeshi da addu’a ta rufeshi da bargo sannan ta shimfiďa dadduma tayi raka’a biyu,
a gurin ta zaune har pss 2 tana addu’a tana tunanin abinda oyizah tasa mata a karkashin gurin kwanciyarta,
a zuciyarta tace koma meye ya kare miki can Allah ya kara tsaremu daga sharrinki,
mikewa tayi tana hamma ta hau gado ta kara shafa addu’a sannan ta kwanta tana kara rokon Allah ya nuna mata guraren da akayi binne binnen nan dan alfarmar annabi da hasken al qur’ani….

Ke dai kinji kunya wallahi,
mutum yayi ta tusa sai kace bodari gaba ďaya kinyi polluting iskar ďaki,,, salma ke magana da karfi hancinta a toshe ta doshi parlor,
fareeda ta biyota tana dariya tace ashe ba dadi kullum kike kumbura min ciki cikin dare,
salma tayi tsaki ta zauna tace wallhy bana irin wannan haba wannan irin tusa haka sai kace ana kwasar kashi,
fareedah ta kwashe da dariya ta koma daki tana faďin oho dai in kinga dama ki dawo ďaki ki kwanta dan 12 ta wuce,
salma tace wallhy bazan kwana a dakin nan ba dan bansan wace iri zaki kuma saki cikin dare ba,
fareeda ta shige ďaki tana dariya,
mikewa salma tayi ta leka dakin da affan yake kwana taganshi kaca2 tayi tsaki ta wuce dakin oyizah,
da murnarta ta shige ďakin ganin mummy bata ciki,
kwanciya tayi akan gadon ta cigaba da chattn din da takeyi, sai gurin biyu na dare bacci yayi gaba da ita…

Tun asuba esther ke kiran wayar oyizah bata ďaga ba saboda wani nannauyan bacci da yayi gaba da ita,
sai gurin bakwai da rabi ta tashi babu sallah bare salati, agogon gefenta tayi saurin kallo taga 7:34 da sauri ta diro daga gado tana mamakin baccin da ya dauketa har ya hanata zuwa shan jinin matsiyaciyar yarinyar nan,
karar shigowar kira wayarta ne yasata saurin dagawa tace morning esther, jiya bacci ya hanani zuwa meeting,
esther tace haba ay ni tunda naga ban ganki nasan kina can kina shegen baccinki, amma oyeee meyasa kikayi haka,
meyasa kika bada jinin yari—- oyizah tayi saurin katseta tana dariya tace badai an gama komai kuma kun riga kun koshi da jinin ba, to ay shikenan,
esther cikin damuwa tace oyizah me tayi miki haka da zafi har kikayi sacrificn dinta 4 no reason,
oyizah tace meye ma bata min ba yarinyar nan,
kedai zamuyi magana bari inje mu fara shirye shiryen jana’izah, esther tace to sai munyi waya,
oyizah ta kashe wayar ta shiga bayi ta wanke fuskarta cikin farin cikin ta yar da kwallon mangwaro ta huta da kuda,
a zuciyarta tace yanzu ne zan kara daure alhj da Affan ta yadda su da dukiyarsu zata dawo karkashin iko na gaba ďaya, bazan kara yarda a auro ma affan mace ba bare ma har ta zame min damuwa,

Tana fitowa ta wuce parlor inda alhj basheer ke kallon news,
saida ta gaisheshi sannan tace bari inje in dubo lafiyar Su Affan sai in kawo maka break ko,
yayi murmushin jin dadi yace ya kamata kam saboda mai larurar ciki,
ta shafi fuskarshi tana dariya tace su alhj ana ji da wannan jikan, yace sosai ma,
Allah dai ya fito min da ita ko shi lafiya,
oyizah ta kaurara dariyarta tace ya Hajjjj kenan sannan ta wuce side din su Affan..

Da izzarta ta buďe kofar tana murmushi, bata samu kowa a parlon ba dan haka ta tura kanta bedroom ďin,
zaro ido tayi cikin firgici saboda ganin Affan kishingiďe da towel a jikinshi Afeeyah na zaune da night gown a gefenshi tana mishi gyaran fuska suna kallon juna suna murmushi,

A-f-e-e-yah oyizah ta faďi bakinta na rawa, Afeeyah ta mike tana gyara gashin kanta tace naaaam ina kwana mummy,
oyizah bata iya amsawa ba sai ma fita da tayi dasauri kamar zararriya,
tana gab da shiga dakin alhj basheer dan daukar wayarta ta kira esther taji ihun farida a ďakinta,
da sauri ta juyo ta karaso ďakin dan ganin abin da take ma ihuu…..

Mrs tijjani shattima…..
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣1⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Cikin ruďewa ta isa gaban gadon tana fadin ke lafiya, ihun me kikeyi,
Fareedah ta kasa magana sai nuna salma takeyi da hannu tana kuka sosai,
a firgice oyizah ta fara girgiza salma tana kiran sunanta,
wani irin ihu ta saki haďe da zama a kasa tana faďin wayyyo salma,
da gudu alhj basheer ya shigo ďakin yana faďin me ya faru, oyixah cikin ihu tace salma, salma— yace salma me, tace salma ta mutu alhj,
karasawa gaban gadon yayi kirjinshi na bugawa da karfi ya ďagota yana dubata,
sakinta yayi da ya tabbatar bata rai ya shiga fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
oyizah ta mike kamar zararriya tace alhj ka tasheta wallhy karka bari ta mutu,
wayyyo na shiga uku na lalace,
alhj basheer ya daka mata tsawa yace wani irin hauka ne wannan, waye ya isa da dawo da matacce,
oyizah ta kara rusa ihu tana faďin wallhy sai ta dawo salma bazata mutu yanxu ba,
tsaki alhj basheer yaja ya tashi ya fita daga ďakin hankali tashe,
ihun suka cigaba dayi ita da farida suna kuka suna jijjiga salma suna faďin ta tashi,

Ihun da sukeyi ne ya janyo hankalin Afeeyah dake zaune suna karyawa ita da Affan,
da sauri ta mike tace ya karasa bari ta duba taga ihun me akeyi,
tana fita tayi hanyar dakin mummy dan nan takejin ihun,

sankarewa tayi da ta shigo dakin ta hango salma kwance inda ta shimfida wannan farin kyallen,
innalillahi kawai take maimaitawa a zuciyarta,
sam ta kasa karasawa gurin saboda tsoro,
a zuciyarta tace yanzu da ni ce zan mutu, meyasa matar nan takeso ta kashe ni,
wani irin kuka ta fashe dashi ta ruga dakinta da gudu a zuciyarta tana dana sanin sa farin kyallen a gurin,
da tasan na mutuwa ne da ta daukeshi ta konashi bata shimfiďa wani ya hau ya mutu ba,
kuka sosai takeyi tana fadin shikenan nayi kisan kai,
da sauri Affan ya matso kusa da ita yana tambayarta abinda ya faru,
bata bashi amsa ba ta shige can cikin daki ta dauki wayarta ta kira kaka liman,
ringing biyu wayar tayi ya dauka,
cikin muryar kuka ta gaisheshi ya amsa yace lafiya me ya faru, ta kara fashewa da kuka tace kaka nayi kisan kai,
wallhy bansan abun mutuwa bane, na dauka wani tsafin tayi dan ta nakasa mu ashe na mutuwa ne, kaka liman yace nutsu ki fada min komai yadda yake dan bana fahimtar abin da kike fadi,
nan ta tsagaita kukanta ta faďa mishi duk abinda ya faru,
kaka liman yayi ajiyar zuciya yace kwantar da hankalinki Allah baya kama mutum da laifin da bai sani ba, lallai Allah na tare dake Afeeyah shiyasa har ya nuna miki wannan mummnan alamarin ya kuma baki basirar ki mayar mata da kaidinta,
wannan aya ce Allah ya saukar gareta in har tana da hankali,
har gurin Allah baki da laifi dan ba ke kika kasheta ba uwarta ce ta kasheta,
ki dage ki cigaba da addu’a saboda yanzu ne zata kara karfin tsafinta in har tasan kaikayi ne ya koma kan mashekiya,
Afeeyah ta share hawayenta tace to nagode kaka dan Allah ka cigaba da yi min addu’a dan wallhy abubuwan tsoro suke bani,
kaka liman yace babu komai jikata addu’a kullum munayi saidai akara bude wuta, Allah ya dauraki bisa kanta,
Afeeyah tace ameen sannan ta kashe wayar ta fita ta wuce gurin gawar salma….

Kafin karfe 10 angama shirya salma cikin suturarta za’a kaita gidanta na gaskiya,
har lokacin oyizah bata bar ihu ba sai sambatu takeyi tana fadin wallhy babu inda za’a kai mata ya, babu wanda ya isa yaje ya binne mata ‘ya a rami,
sosai ta fita hayyacinta tun kukan na fitowa har ya daina fitowa,
dakyar aka fita da gawar salma daga gidan, sai da oyizah ta suma sai uku saboda tashin hankali,
tana farfadowa ta shiga tsine ma mutanen gurin tana fadin ita fa yarta bata mutu ba dan ko ciwon kai batayi ba,
Da mutane suka ga abin nata jahilci ne sai suka watse suka barta da kukan takaici,

Bayan azahar esther ta kara kiran oyizah,
cikin kuka oyizah ta ďauka tana faďin esther salma ta mutu, batayi ciwon komai ba, ko mura ba tayi ba lafiya lau muka rabu jiya da daddare,,
esther tayi dariya tace kin iya acting oyizah halan kina cikin taron mutane ne,
oyizah cikin ihu tace wane irin acting ina fada miki yau da safe mun tashi ba salma shine har kike dariya,
esther tace to ay abin naki ne,
ki bada yarinya da hannunki sannan kizo kina kuka,
oyizah ta zaro ido tace wace yarinya,
esther tace salma mana,
salma kika kawo jiya,
kinsan kuwa saboda hakan da kikayi har mukami aka kara miki saboda kin kawo yarki wacce kika fi so dalilin da yasa na kara kiranki kenan dan inyi miki albishir,
oyizah ta saki wata kara mai rikirtarwa ta mike ta shige ďaki tace esther jinin salma kuka sha,
esther tace wai ko kin haukace ne,
har kiranki fa nayi da safe kikace kina sane kika bayar,
oyizah tace wayyyo na shiga uku,
ni ba salma na bayar ba Afeeyah na bayar, ya za’ayi in bada salma,
esther tace ha’a to ya akayi muka ga salma,
oyizah tayi wurgi da wayar hannunta ta yaye zanin gadonta, nan tayi arba da farin kyalle,
cikin firgici ta fara shafa kyallen tana fadin ya akayi wannan kyallen yazo nan gurin, waye ya kawo wannan kyallen nan,?
waye ya kashe min salmata ta fadi cikin karaji,?
da sauri farida ta shigo dakin ta riketa tana rarrashinta tace mummy dan Allah ki daina wannan ihun kinga mutane suna ta kara yawa,
oyiza ta hankaďa ta tace sun ci kutumar ubansu mutanen,
nan ta fara zage2 tana tsinewa mutanen da suka zo mata gaisuwa cikin ficewar hayyaci,
saida farida ta kirah alhj basheer yazo ya lallabata da kyar sannan tayi shuru tana ajiyar zuciya,
gaba ďaya ta dauki tunaninta kacokan ta maida shi gurin gano yadda akayi abin da ta shimfiďa ma Afeeyah ya dawo dakinta, yanzu su chummy basuyi ma diyarta lamuni ba suka zuke jininta ba tare da sun tambayeta ba,
lallai sun taro match dan wallhy sai tasan yadda akayi wannan kyallen ya dawo dakinta sannan kuma sai ta nuna ma su chummy bacin ranta,,

Tun ranar da salma ta mutu nutsuwa tayi ma oyizah tawaye,
kullum cikin mafarke2 take tana bakin cikin yadda akayi aka bada ďiyarta a cikin kungiyarsu ita kuma shegiyar kungiyar mai lakabin sabo da kaza baya hana a yanka ta, in ba haka ba ay sunsan yadda takeson yayanta kamar yar ranta,
a ranar da akayi uku ne ta fara shirin zuwa gurin meeting dan ta warware musu kuma a binciko mata dalilin da yasa wannan farin kyallen ya koma ďakinta…..

Mrs tijjani shattima…
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣2⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Karfe biyun dare suka hadu a gurin meeting kamar yadda suka saba,
oyizah na zaune gaban chummy bayan ta gama masifarta sai cika takeyi tana batsewa,
Chummy ta dafa kanta tace oyeee naji duk bayanan ki
, kuma na fahimci fushinki, amma kinsan mu nan duk wanda aka kawo baya tafiya ba tare da munsha jinin shi ba ko,
mistake din daga gareki yake tunda ke kika shimfiďa farin kyallen,
oyizah cikin fushi tace ba a dakina na shimfiďa ba my lord a dakin yarinyar da na bada anan na shimfiďa bansan yadda akayi ya dawo ďakina ba,
alhj sambo ya kalleta yace haba oyizah dan kin bada yarki daya shine kike ta wannan fushin,
ni yayana biyu na bayar da kannena biyu da nake matukar so,
a hassale oyizah tace abin da kake nema ne dole sai kayi wannan sacrifice din,
ni ay na riga na bada nawa wannan kyauta na bayar saboda kungiya taji dadi,
esther tace calm down oyee,
chummy tace barta ta cigaba,
ta manta duk abinda kungiya tayi mata ne, ta manta da irin rufin asirin da mukayi mata, ta manta da duk wani wanda zai tona asirinta mun kawar mata dashi saboda tasamu nutsuwa a gidan aurenta,
ta manta yadda muka mallaka mata alhj basheer
, ta manta yadda muka lalata rayuwar dan kishiyarta ita kuma muka mayar da ita matacciya alhali tana raye,
oyizah ta sunkuyar da kanta kasa tace am sorry my lord, ni ba fushi nayi ba,
kawai dai ina son in san wanda yayi min wannan aikin ne,

chummy ta janyo wani kokon tsafi ta fara bincikenta cikin kwarewa dan gano wanda ya canza farin kyallen,
a wannan lokacin kuma Afeeyah na zaune kan dadduma tana kallon gabas tana rokon Allah ya karesu daga dukkan sharrin masu sharri,

Babu irin duban da chummy batayi ba amma sam bata ga komai ba sai duhu da ya mamaye kwaryar, ajiye kwaryar tayi hannunta na rawa tace kaii oyee gaskiya na kasa gane ko waye, kar mu zurfafa bincike ko ma waye zamu gane shi wata rana, kedai kije ki cigaba da mulkinki kamar yadda kika saba tunda babu wanda ke taka miki birki,
cikin damuwa oyizah ta ďago da niyyar faďin damuwarta akan Afeeyah amma ta kasa,
daga ta bude baki zatayi magana sai taji wani abu na mata yawo a makoshinta, sai gab da asubahi suka fara bacewa suna komawa gidajensu,
har lokacin bakin oyizah naso ta furta sunan Afeeyah amma ta kasa,
gurin wata kwalba suka je wacce ke dauke da gunki a cikinta,
d’aga kwalbar chummy tayi tana dariya ta mayar ta ajiye tace haka kishiyarki zata dawwama babu motsi a duk inda take,
fanne da fanna dake cikin wata kwalba sukace saidai in bamu fita anan ba, wallhy muna fitowa zamu fasa kwalban nan,
oyizah ta buga glass din tace to dan ubanku ku fito mu gani,
fanne tayi dariya tace wit tym,
chummy tace rabu dasu oyee tafi gida sa’a na tare dake a ko da yaushe,
ta russuna kamar zata mata sujjada tace thank you my lord…..

Kwanan salma biyar da mutuwa har lokacin oyizah bata walwala, kullum sai tayi kuka saboda yawan mafarkin salma da takeyi,
alhj basheer da farida kaďai ke tausarta se kuwa a gurin meeting dinsu,
sam ta tsani ganin Afeeyah dan gani takeyi sanadiyyar Afeeyah ta rasa yarta, jira kawai takeyi ayi sadakar bakwai tayi wani aikin akanta dan wannan karan da hannunta zata kashe shegiya,
mugun shiri takeyi akan Afeeyah dan so takeyi tayi mutuwar wulakanci,,,,

Afeeyah kuwa hankalinta kwance yake dan kula sosai takeyi da mijinta da take ganin yar nutsuwa a tare dashi kwana biyun nan,
shi kanshi hankalinshi a kwance yake saboda daina ganin salma da yayi kwana biyu,

karfe 5 na yamma ta gama girkinta sukayi wanka suka shirya cikin kyakyawar shiga sai kamshi sukeyi, dakin oyizah suka shiga Afeeyah ta tsuguna ta gaisheta tayi mata ya hakuri,
ko kallonta oyizah batayi ba idonta nakan Affan tana hararar shi, boye fuskarshi yayi a bayan Afeeyah yana leken fuskar mummy da har lokacin bata daina hararar shi ba,
mikewa Afeeyah tayi tace sai anjima mummy,
oyizah ta bita da mugun tsaki tace za kici ubanki ne,

Ta wani corridor taja shi tace yau ta nan zamu bi,
kasan tunda nazo gidan nan ban hau gurin nan ba,
yayi dariya yace to muje amma fa mummy tace akwai su lions a gurin,
Afeeyah tace haba dai babu komai muje may be basa so ka hau ka fado ne,
runtse idonshi yayi yace muje amma bazan bude ido na ba, dariya Afeeyah tayi taja hannunshi suka hau can saman gidan,

sakin hannunshi tayi da sauri tana fadin Wowww amma gurin nan ya hadu,
bude hannunta tayi ta lumshe idonta tana shakar iskar gurin flowers sai kaďawa sukeyi,
da gudu taje bayanshi ta fara mishi cakulkuli tana faďin ka buďe idonka ka gani babu komai a gurin sai flowers masu kamshi, dariya yake ta kyakyatawa sannan ya buďe idonshi a hankali,
wasu shuďaďďun abubuwa ya dinga gani suna mishi yawo a cikin kwakwalarshi da kwayar idonshi,
sosai yake ganin abubuwan da suka taba faruwa a gurin kuma yake ganinsu kamar zanen cartoon,
fuskar zeenatu ce take mishi gizo yanata so ya gano ko wacece saboda dishi2 yake ganinta,
rike kanshi yayi dasauri bakinshi na rawa a hankali ya furta
U-M-M-A,….. ..

Mrs tijjani shattima…
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣3⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Maimaita sunan ya dinga yi yana ja da baya kanshi na juyawa saboda yadda abubuwan ke zuwan mishi cikin kwakwalwarshi,
a firgice Afeeyah ta kamashi tana faďin me ya faru,
girgiza kanshi yayi da karfi ya runtse idonshi yace dan Allah ki sakko dani ki kaini ďaki,
Afeeyah cikin tsoro ta rike hannunshi taja shi tana waigen gurin ko itama zata ga abin da yake gani,
daki ta wuce dashi ta zaunar dashi ta tsuguna a gabanshi har lokacin bai buďe idonshi,
a hankali tace ka buďe idonka,
kara runtse idon yayi yana girgiza kanshi,
Afeeyah tace a daki fa muke ka bude idonka ka gani babu komai anan,
a hankali ya fara bude idonshi har ya bude su gaba ďaya ya saukesu a kan Afeeyah,
Afeeyah tace kaga ni ba komai ko,
ya gyaďa mata kai, tace to me ka gani a can saman,
ya ďaga kanshi sama yace babu komai sai fan,
Afeeyah ta dawo kusa dashi tace ina nufin a sama inda muka je, rufe idonshi yayi shi kanshi yana son tuno abinda ya gani duk da bai gansu clear ba amma yasan ya gane fuskar ďaya a cikinsu,,
bude idonshi yayi dan ya kasa tuno fuskar da ya ambaci sunanta a sama,
kallon Afeeyah yayi yace ni ban ga komai ba,
Afeeyah tace kagani mana, baza dai ka faďa min ba ko,
ya tabe baki yace ni na manta kome na gani,
Afeeyah tace to shikenan, tashi muje muyi sallah magriba tayi,
ba musu ya mike ya bita fuskar da ya gani a sama tana ta mishi gizo amma sam ya kasa tuna ta….

Zaune take a gefen gadonta rike da turaren da kaka liman ya bata a hannunta tana shafa shi tana addu’a kamar yadda ta saba,
tofe jikin Affan tayi da addu’a sannan ta kwanta tana istigfari har bacci yayi gaba da ita,,,,

Mafarki*****

Tafe take a cikin gidan tana bin inda bata taba bi ba tun zuwanta gidan a zuciyarta tana yabawa da kyau da tsarin gidan,,
Kamar giftawar walkiya ta hango wani katon DAMO yana bin wata mata tana gudu tana salati haďe da ihun neman ďauki,
da sauri ta bisu tana addu’a zuciyarta cike da tsoron wannan damon dan bata taba ganin suffa irin tashi ba,
ja da baya tayi saboda yadda ta hango wannan damon ya hankaďa matar cikin wani kewayayyen flower bed ya haye kanta,
tun tana jiyo ihun matar har ta daina jiyowa saboda matar ta nitse ciki sai tashin kura mai karfi kawai take gani,,,
a firgice ta juya jikinta na rawa ta hango wannan damon ya fito daga cikin flower bed din yayi gurin fishpond, yana zuwa gurin ya rikiďa ya koma kifi ya shiga ciki,,
a hankali ta tako ta leka cikin ramin ta hango kifayen sun cure kansu sun zama kifi ďaya,
a gigice ta koma baya tana sauke numfashi tana fadin “innalillahi wa inna ilaihir rajiu’n,” dan ganin yadda kifayen nan suka cure ba karamin daga hankalinta yayi ba,
cikin sassarfa tayi hanyar daki,
anan ne ta haďu da wani tashin hankalin dan ganin wata guntuwar halitta tayi a kofar ďakin oyizah tayi wuf ta shige ta kofa ba tare da ta buďe ba,
nan jikinta ya fara rawa ta leka ta window ta hango wannan halittar ta haye gado ta nutse cikin katifar,
wata dariya taji an saki mai karfi haďe da guguwar da ta fito da wani mugun bakin hayaki daga karkashin gadon,
da sauri ta juya zata koma ďaki taji haushin karnuka a bayanta, tana waigawa taga bakaken karnika sun fi ďari sun doso inda take suna haushi kamar zasu tsaga gidan,
a razane ta fara gudu tana fadin “hasbunallahu wa ni’mal wakil,”
bin ta karnunkan suka fara yi da gudu suna kara yin haushi,
tana zuwa kofar dakinta taji an taďiyeta ta fadi kasa sosai,
ja baya ta farayi tana kara karanto adduoi da karfi tana kuka,
wani irin tsalle wani katon kare yayi zai hau kanta,
a razane ta runtse idonta ta saki ihu mai karfi haďe da tashi daga baccin da takeyi,
Affan ta gani a zaune yayi tagumi yana kallonta,
kauda kanta tayi ta janyo wani zani a gefenta tana share zufar da ta jikata tana fadin
“‘A’oothu bikalimaatil-laahit-taammaati min ghadhabihi wa ‘iqaabihi, wa sharri ‘ibaadihi, wa min hamazaatish-shayaateeni wa ‘an yahdhuroon.””
Singlet ďinshi yasa a gefen kunnenta yana share mata zufar da take gangaro mata daga kanta,
juyowa tayi ta kalleshi tace har ka tashi, karfe hudu fa yanzu,
ya karkatar da kanshi gefe idonshi ya ciko da kwalla saboda mafarkin mahaifiyarshi yayi amma sam ya kasa tina mafarkin,
da sauri tasa hannu tana share mishi kwallar idonshi tace menene,?
A hankali ya kwanta lamo a jikinta yana kara zana fuskar zeenatu a cikin kwakwalwarshi,,
shafa kanshi ta fara yi tana karanto addu’a tana tofa mishi a kanshi har bacci ya ďaukeshi,
haka suka kasance a wannan daren Afeeyah bata koma bacci ba dan tana matukar tsoron ta runtse idonta ta kara yin wani mafarkin….

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣4⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Washe gari sukuku ta gama aikinta,
sai da suka karya sannan ta kirah kaka liman tayi mishi bayanin abubuwan da ta gani a cikin mafarkinta,
cikin mamaki yace na faďa miki mugun tsafine dankare cikin gidan nan,
yanzu gurare uku zakiyi aikin kisa a ranki Allah na tare dake,
ki tabbatar yau kinsa an hake wannan flower duk abinda kika gani a ciki ki cire shi,
sannan ki tabbatar wadannan kifayen yau basu kwana a gidan nan ba,
kisan duk irin dabarar da zakiyi kisa a fitar dasu daga cikin gidan a wanke gurin ya zamana ba komai a ciki,
sannan guri na uku shine mai wuyar, yadda zakiyi ki shiga wannan dakin nata har ki iya bankade karkashin gadonta,
Afeeyah dai ta gama tsorata matuka idonta ya ciko da kwalla tace kaka duka suna da wahala, wallhy har yanzu jikina rawa yakeyi,
yace nasani jikata nasan suna da matukar wahala amma Allah zai mayar maki dasu masu sauki daga kin fara,
dan Allah karki ji tsoro zan tayaki addu’a ina daga nan, Allah zai taimakeki saboda niyyarki mai kyau ce, kisan duk yadda zakiyi ki bankade na karkashin gadon nan dan duk wasu alkadaranta anan suke, in mun gama da wannan zan fassara miki na karnunakan nan,
jiki a sanyaye Afeeyah tace to kaka nagode sai anjima, yace to sai anjima Allah yayi miki albarka tace ameen kaka…

Karfe 11am ta fito daga ďakinta ta fara bin hanyar da tabi cikin mafarkinta,
sannu a hankali take tafiya har saida kafarta ta sada ta da wannan kewayayyen flower bed ďin da farida ke raya shi da ruwa babu dare babu rana,,
karasawa tayi gurin flower ta leka ciki dan tasan duk dabarar da zatayi a hake mata gurin,
ta kai minti uku a gurin ta hango tanimu mai Guga rike da bokiti a hannunshi,
da karfi ta kwala mishi kirah ya taho da sauri ya tsuguna yace hajiya gani,
Afeeyah tace dan dan Allah a ina zaka samo fatanya inason a shiga cikin nan ne ayi min digging dinshi naga kamar ana gyara sauran kullum banda nan,
tanimu ya rike baki yace wallhy hajiya ko katakon gurin nan ba’a yarda mu taba bare ganye bare kuma har mukai ga hakeshi,
Afeeyah tace to saboda me, yace wallahu aalamu, nima ban sani ba,
Afeeyah tayi tsaki tace kira min mati naga shi ke kula da flowers din gidan,
da sauri ya mike yaje ya kira mati suka taho tare,
dakyar da yaudara tace ma mati yazo ya hake mata saboda alhj yace za’ayi shuka ne a gurin,
jin alhj ne yace yasa mati zuwa dauko fatanya ya bude gurin ya fara haka tun karfi,
gefe ta koma tana addu’a tana kallonshi, yana tsakiyar hakan ne ya jiyo taurin wani abu, da sauri ya dago shi da fatanyarshi ya fara girgijeshi kasar na kakkaba,
Afeeyah na hango kafar ta gane ta dabba ce, da sauri tace mati ajiye dan Allah ka samo min ruwa in dauraye hannu na,
dasauri ya ajiye yayi gurin pampo,
cikin azama ta karasa tayi bismillah ta dauko wannan damon tayi cikin dakinta dashi ta naďe shi cikin wani zani ta turashi karkashin gado,
tana komawa gurin ta tarar da farida na balbale mati da masifah,
Afeeyah ta karaso da sauri ta kalli fuskar mati gwanin tausayi tace ya akayi ne mati, mati yace hajiya saida na faďa miki ba’a taba gurin nan kika dage sai na hake shi, gashi yanzu hakan na min barazana da aikina,
Afeeyah ta kalli farida dake harararta sannan ta maida kallonta ga mati tace dama wannan ce ta dauke ka aiki,
ya girgiza kanshi yace a’a, Afeeyah tace to dan me zatayi sanadiyar aikinka,
naga dai wannan aikinka ne, ko alhj yasan baka gyara wannan flower,
mati yace a’a bai sani ba,
Afeeyah tace to maza ka cigaba da aikinka tunda dama dan albashi kakeyi,
farida tace ke kuma asuwa dan uwarki,
Afeeyah tace ni as uwarki dan ita uwar taki,
fareedah ta rike baki cikin mamaki tace mummy kike zagi,
Afeeyah tace uwata ce ita ko kuma kina tunanin uwa tafi uwa ne,
kai mati cigaba da aikinka in ka gama kayi watering din gurin ka rufe ni ina da abin yi,
farida ta hassala ta finciko Afeeyah da karfi tace wallhy yau sai naci ubanki a gidannan,
duka duka yaushe aka haifeki da zaki tsaya kina gaya ma mutane magana,
Afeeyah ta haďe rai sosai tace sakeni kar muyi creating sin a gurin nan,
farida tace baza’a sakeki ba,
Afeeyah ta buge hannunta da karfi tace dallah sakeni,
farida ta daga hannunta cikin fushi zata mareta Afeeyah tayi saurin rike hannunta tace karki fara wannan gangancin dan wallhy bazamu kare faďan nan yau ba,
ki bar ganinki katuwa wallhy babu abinda zaki dauka ajikina dan abun a zuciya yake, kuma sannan da kike cewa yaushe aka haifeni to bari kiji ko jiya aka diga maniyyi na na fito yau na fiki daraja a idon duniya saboda nayi aure kuma nasamu Apple of marriage, ke fa? har yanzu kina gida babu mashinshini bare har yayi yunkurin dauka, tayi wurgi da hannunta taja tsaki ta wuce ta barta tsaye idonta jajur….

Gurin Affan ta wuce yana zaune yana kallon kifayen dake cikin fishpond,
runtse idonta tayi saboda tuno mafarkin da tayi,
da sauri ta mike tayi hanyar ďaki tsigar jikinta sai tashi takeyi,
da sauri ya biyota dakin yana tambayarta me ya faru,
a hankali take maida numfashi tace wallhy na tsani ganin kifayen nan,
dan Allah muje gurin daddy yasa a fitar dasu daga gidan nan,
Affan ya bata rai yace kifin mummy ne fa, bazata bari a fitar dasu ba,
Afeeyah ta fara kakarin amai ta mike ta shiga bayi tana kakarin karya tana kuka kamar zata mutu,
da gudu ya tafi dakin daddy yana fadin daddy kazo Afeeyah zata mutu,
da sauri ya tashi ya fita yace tana ina, Affan yace tana bayi daddy,
da gudu ya shiga dakin ya tarar da ita kofar bayin tana haki kamar da gaske,
karasowa yayi da sauri yace me ya sameki, Affan yace daddy wai kifayen nan ne ke bata tsoro,
Alhj basheer yace wani irin tsoro kuma,
Afeeyah tace wallhy daddy kullum sai nayi mafarkinsu bana iya bacci da daddare,
alhj basheer yace subhanallahi to gaskiya gara a fitar dasu daga gidannan dan kar su shafi lafiyar dan cikin ki,
oyizah da ta shigo dakin dan taci uban Afeeyah akan abinda tayi ma farida tace baka isa ba wallhy, babu wanda zai fitar min da kifi,
ance dole sai kinje gurin ne bare ki gansu,
Afeeyah ta kara narkewa tace amma mummy ay a gidan suke, dan Allah kiyi hakuri a fitar dasu wallahy suna firgitani cikin dare,
oyizah tace to zanga uban da ya isa ya fitar min da kifaye daga cikin gidan nan,
alhj basheer yace haba safiya, ni bansan amfanin kifayen nan ba, ace shekara uku ana kiwon kifaye basa girma saidai su dinga cin abinci kullum, gaskiya yanzu za’a fitar dasu daga gidan nan kije can fili na na Na’ibawa ki cigaba da kiwata su,
oyizah tace haba alhj yanzu saboda yarinyar nan tace bata son abu shin— yayi saurin katseta yace saboda kar mu shiga hakkinta ita da abin da ke cikinta karki fassara maganar dan Allah yasa kai ya fita..,

oyizah ta kalli Afeeyah ranta a bace ji takeyi kamar ta shaketa ta huta,
mikewa Afeeyah tayi tana gyara jikinta tana murmushi tace mummy bakiji daddy na kiranki bane,
oyizah ta harareta sama da kasa tayi kwafa tace billahil lazi sai kin gane ba’a shiga gonata, tasa kai ta fita,
Afeeyah tace gonarki na nawa kuma,
ta karshen ta rage in shiga in saki nometa da hannunki..

Karashe 54

Ba karamin tataburza akasha da oyizah ba gurin fitar da kifayen nan,
saida alhj basheer ya nuna mata matukar bacin ranshi sannan ta yarda aka kwashesu ruwan ciki na yauki da kyar aka gama kwashewa,
ana sakin ruwan wani irin wari ya gauraye gurin kowa a gurin saida ya toshe hancinshi,
da gudu mati ya ruga ciki ya samu oyizah zaune tayi tagumi yace hajiya an gama kwashewa,
wani irin harara ta sakar mishi cikin tsawa tace dazu saboda ka rik’a shine ka hake flowers din dana hanaku tabawa ko,
mati ya marairaice fuska yace alqur’an hajiya sani akayi,
tace ka fada min abinda ka hako a gurin, yace na rantse da—- babu abinda ya hako mummy, Afeeyah ta katseta, tace a gabana ya gama gyarawa akwai abin da kika binne a gurin ne,
oyizah ta dafe kanta ta dago tace kan ubanki na binne,
Afeeyah tayi gaba tana dariya tace kan ubana tauri gareshi,
oyizah ta kalli mati tace bace min da gani banza shashasha,
da sauri ya mike ya fita yana bata hakuri,
wani irin juyawa taji kanta nayi saboda abin da ke shirin faruwa da ita yau,
farin cikinta daya da mati yace bai hako komai ba,
to ya zatayi da wadanan kifayen tsafin nata da alhj yasa a fitar dasu daga cikin gidan,

duuffffffff taji saukar mutane akanta suna maida numfashi,
da sauri ta hankade farida da Afeeyah ta kalli su tanimu tace lafiya kuka shigo min parlour,
a ruďe farida tace mummy kifayen nan sun bace a cikin kwanon da aka sasu…….

Mrs tijjani shattima…..
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣5⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Zaro ido oyizah tayi tace kamar yaya sun bace,
Afeeyah ta kalli alhj basheer da ya fito yana gyara hula tayi saurin cewa wallahi bacewa sukayi mummy,
haba shiyasa suke tsorata ni cikin dare ashe ba kifaye bane,
alhj basheer ya karaso da sauri yace kifayen ne suka bace,
oyizah ta galla ma su Tanimu harara sum sum suka fice ta juyo ta kalli alhj basheer tace iskancin su ne ni nace ma wanda ya kwashe kifin ya dauka na bashi shine dan basu gansu ba suke tunanin sun bace, to ina zasu,
Fareeeda tace wallhy tall— oyizah tayi saurin katseta tace dalla rufe mana baki, shekarun su nawa a gidannan kin taba ganin sun bace, dallah ku wuce ku ba mutane guri,
Afeeyah ta ja hannun Affan da jikinshi ke kyarma suka wuce daki a zuciyarta tace 99days 4 the thief muje zuwa, Allah dai ya kara bani sa’a…

Tun karfe hudu na yamma oyizah ke gurin chummy cikin matsananciyar damuwa tana faďa mata anyi destroying fishpond dinta na tsafi,
dariya chummy tayi sannan ta buga kasa nan take ya tsage ruwa haďe da kifaye suka fara fitowa daga ciki, saida suka gama fitowa tsaff sannan suka haďe kansu guri ďaya,
oyizah tayi murmushin jin dadi tace ashe suna nan,
har hankali na ya kwanta, bacewarsu ba karamin daga hankali na yayi ba dan ba karamin taimako na sukeyi ba,
chummy tayi dariya mai karfi tace fitarsu a gidanki tonan asirinki ne saboda haka kisan duk yadda zakiyi ki mayar dasu gidan nan Affan ya dinga ganinsu kullum,
oyizah tayi tagumi tace ta yaya zan mayar dasu bayan alhj da kanshi yace a fitar dasu,
yanzu ina komawa dasu zai fara zargin wani abu,
chummy tace karki damu, akwai abun da zan baki kisa mishi a abinci daga yaci shikenan ko yagansu hankalinshi bazai kawo su bane,
oyizah tayi dariyar jin daďi tana faďin thank u my lord,,
mikewa oyizah tayi ta shigo da wani yaron da zasu sha jininshi a gurin meeting,
da ganin yaron kasan mugun takadiri ne dan ko gezau baiyi ba idonshi a soye babu alamar hawaye,
dakyar ya tsuguna a gabansu,
chummy ta harareshi sannan ta umurceshi da ya miko mata kafafuwanshi,
tirjewa yayi yaki mikowa, babu yadda batayi ba akan ya miko kafafuwanshi tayi wani aikin dasu yaron nan yaki,
kwala kiran BULADUNA tayi nan suka shigo shida abokin aikinshi,
cikin isa ta umurcesu da su kamo yaron su kawoshi gabanta,
da karfinsu suka fara kokarin kama shi yana tirje musu yana tokarinsu da hannu, sai sun daukeshi sunyi sama dashi sai yasa iya karfinshi ya zille ya fado kasa,
daukar da sukayi mishi na karshe ne yasashi wani irin kukan kura ya hankaďe buladuna yayi baya,
tartsasssssss sukaji dukansu suka duba gurin da sauri,
glass din da fanne da fanna ke ciki ne yayi tarwatse ya bullo tun daga bayan buladuna har cikinshi, nan take ya fadi kasa matacce, da sauri su chummy suka yo kanshi suna kiran sunanshi,
su kuwa su fanne cikin azama suka fito cikin glass suka nufi gurin yaron da aka kamo da niyyar taimaka mishi ya gudu,
cikin tausayawa yace ku meyasa bazaku zo mu tafi tare ba,
fanne cikin sauri tace mu matattune gawar mu ta dade a rami kai kuwa ba’a riga an birne gangar jikinka ba kayi saurin komawa gida,
da sauri yace waye ya kawo ku nan,
fanna tace mahaifin mu ne Alhj sambo ministern Abuja na yanzu,
kafin yaron yayi magana ya hango su chummy sun doso su suna kokarin kama su fanne,
da sauri kurwar yaron tabi ta inda su fanne suka nuna mai ya bace daga gurin,
cikin kunan rai chummy ta ciro sandar tsafinta ta fara nuna su fanne dashi,
zagayen dakin suka farayi har suka kai inda kwalbar gunkin zeenatu take,
da sauri fanne tasa hannu ta dauki kwalbar,
wani irin ihu oyizah tasa tace karki fasa, karki fasa,
zan taimakeku in maida ku gidan ku, fanna tace fanne fasa da sauri saboda mu dama a mace muke gurin wa zata maida mu,
kafin chummy ta cimma fanne har ta fasa wannan kwalbar ta karya gunkin ciki,
zama oyizah tayi a gurin tana girgiza kanta tana fadin shikenan, shikenan my lord,
sai da nace miki mu gama da yaran nan saboda nasan zasu iya zame mana matsala, yanzu nasan duk inda zeenatu take ta farfado,
chummy bata ba oyizah amsa ba saida ta tabbatar ta kwantar da fanne da fanna sannan tace yau dinnan zan gama dasu, ki kwantar da hankakinki dan sun fasa kwalbar a banza dan babu wanda yake tunata bare har yayi mata adduar da zaisa ta gama dawowa hayyacinta,,
yanzun nan zan kara yin aikin da yafi wancan akanta,
oyizah ta saki ajiyar zuciya tace nagode my lord..

Afeeyah na zaune tana lazumi, tunda ta idar da sallar la’asar bata tashi daga kan daddumar ba sai gurin biyar,
shafa addu’ar tayi ta mike ta nade daddumar sannan ta zauna a kasa a gefen gadonta ta tura hannunta karkashin gadon ta zaro zanin da ta kunshe damon nan a ciki,
a hankali ta warwareshi ta nade hannunta da leda cikin dakewar zuciya ta fara kakkabe kasar tana kokarin bude bakin damon,
cikin sa’a ta budeshi sai wari yakeyi ta karkatar da bakin ta girgizah shi, nan wata katuwar laya ta faďo kasa,
da sauri ta ajiye wannan damon ta naďeshi cikin zanin ta dauki layar ta warwareta,
babu abinda ta gane a cikin rubutun sai sunan zeenatu,
nade layar tayi ta mike ta fita da wannan damon ta kulleshi a leda takai main bolar gidan sannan ta dawo ta kona layar ta tattara tokar ta zubata a magudanar ruwa…

★ Magaryah Nijar★

Indo!!! tankaďen ne har yanzu baki gama ba, baki gudun malam ya dawo ya tarar ba’a gama abinci ba,
wane irin shashanci ne wannan,
nda tashi ki ban guri sai shegen Nawar tsiya,
indo ta turo baki ta mike tayi hanyar waje,
Sallamar da akayi ne ya tsayar da ita,
da sauri ta rungumeta tana faďin “Tanti Gaje” sannu da zuwa,
Gaje tayi dariya tace sakan ni yar Magaryah ya na same ku,
indo tace kalau muke sai dai har lau Tanti Ayyu na nan da masifarta,
Gaje tayi dariya ta karasa cikin gidan tanti ayyu ta mike tace maraba da gaje mutan jigawa,
gaje tace ina wuni Ayyu,
ayyu ta amsa tana shimfiďa mata tabarma tace ya jigawar,
ay tun shekaran jiya muke zuba ido shuru,
Gaje tayi murmushi tace mun yi sabga ne a kazaure dan haka baki ganni ba,
ya kokari ya kuma mai jikin an samu cigaba kuwa— kafin Ayyu tayi magana wani razananen ihu ya fito daga ďakin majinyaciyar ya ziyarci kunnuwansu,
kallon kallo suka fara yi sannan suka mike da gudu suka shiga dakin har suna bige juna,
zama sukayi a gefenta gaje ta fara shafa kanta tana faďin sannu hajiya,
wani ihun ta kara saki tana faďin zasu kasheni, zasu kashe Affan, Gaje kije ki dauko min shi, gashi can zasu kashe shi, wayyo Allah nah zasu kashe min ďana,
cikin sauri Ayyu tace indo maza je ki kirah malam kice mishi ya taho maza ta farfado…..

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣6⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Cikin sarkewar murya malam maina yace dagaske kike indo,
jiki na rawa indo tace walllhy kawu da gaske nake,
mikewa yayi ya gyara takalman kafarshi yayi sallama da abokanshi suka wuce gida,
Yana shiga ya tarar har lokacin zeenatu na ihu sosai,
da sauri ya karaso ya zauna ya umurci indo da ta kawo mishi ruwa, nan da nan ta fita ta kawo mishi ruwa ya jika wani ganye ya daďe yana tofa addu’a a cikin ruwan sannan ya mika ma Ayyu da take rike da ita yace ta ta bata tasha,
dakyar suka iya ďagata suka bata tana ihu tana zubarwa, a haka har Allah yasa ya shiga cikinta,
kwantar da ita sukayi suna shafa mata ruwan tayi wani irin kakari haďe da amai mai yauki, tana gama aman suka gyare mata jikinta suka kwantar da ita har lokacin idonta a rufe yake, saida suka tabbatar ta samu nutsuwa sannan suka tashi suka fita a dakin suna tattauna yadda zasu billowa al’amarin….

Tun a hanya kan alhj basheer ke sarawa a zuciyarshi yana tunanin wani abu da yayi ma rayuwarshi gibi kuma yakeson tuno shi,
yana isa gida ya wuce ciki yana kallon ko ina na gidan, a hankali ya fara bin dakin zeenatu da kallo komai na rayuwar da sukayi a baya ya shiga dawo mishi har lokacin da aka nemeta aka rasa, tambayar zuciyarshi ya shiga yi akan ko an ganta, ko ta mutu ne, meyasa kwata2 ta bace a cikin kwakwalwarshi,
da sauri ya karasa kofar ďakin ya murďa yaji ta a rufe,
kitchen ya wuce shi kanshi ya rasa me zaiyi a kitchen din, yana shiga ya tarar da oyizah tsaye tana tsiyaya fresh milk a kofi,
wani irin kallo yayi mata wanda shi kanshi baisan yayi shi ba,
a hankali yace safiya ina zeenatu? har yanzu ba’a ganta ba? ko ta mutu ne,?
saboda tsananin ruďewa saida oyizah ta kusa ajalin glass cup din hannunta tace alhj wace zeenatun,
alhj basheer yace zeenatu nawa kika sani a rayuwarki,
cikin in ina tace to ni ina zan san in— kafin ta karasa magana wayar alhj basheer ta katseta,
da sauri ya dauka yace ina wuni baffa, daga ďaya bangaren ya amsa yace bashiru shin ina labarin zeenatu, dazun nan tunaninta ya fado min bayan dogon lokaci har yanzu babu wani labari game da ita,
alhj basheer cikin damuwa yace tunanin da na gama yi kenan baffa, gaba daya na rasa yadda akayi har tunaninta ya bace min,
Baffa yace na cire rai da ita bashiru, addu’a kawai zanyi mata akan Allah ya kai rahama kabarinta,
shekara uku babu amo babu labari,
alhj basheer yace baffa baza’a cire rai da ita ba in har tana da rai, yanzu addu’a kawai zamuyi akan Allah ya bayyana ta in kuma bata raye Allah ya jikanta,
sun dade suna jimamawa a waya sannan suka kashe alhj basheer ya fita daga gidan da sauri ba tare da ya kalli oyizah ba…
Ajiye kofin tayi da sauri ta wuce daki cikin tashin hankali,
kai kawo ta dinga yi idonta yayi jajur tace tabbas mati ya hake wannan damon,
cikin sauri ta bazama gurin tsafinsu domin neman mafita…

Gidan alhj bara’u ya shiga shi kanshi yayi mamakin tsawon shekarun da suka dauka ba tare da an nemi zeenatu ba, Abida harda kukanta dan kamar yadda ake shafe rubutu a allo haka aka shafe babin zeenatu cikin kwakwalwar mutane,,
a ranar saida suka je gurin malamai hudu duk inda suka je sai anyi bincike ace tana raye amma bata cikin hayyaci da nutsuwarta, , addu’a sosai suka baza makarantar almajirai da gurin malamai,
alhj basheer bai koma gida ba sai can dare gurin 11..

Afeeyah najin shigowarshi ta dauki hijab dinta dama ta shirya duk yadda zatayi yau tasa daddy ya barsu su kwana a dakin oyizah,

wani macijin roba ta dauko ta turashi karkakashin kujerar da Affan ke zaune hankalinshi na kan cartoon,
zama tayi kusa dashi tace manya kallon har yanzu bai isa ba,
yayi dariya yace yanzu za’a gama yau bana jin bacci ina zaki naga kinsa hijab,
tace sallah na idar shine ban cire ba,
a hankali ta daura kafarta kan tashi tana mishi waiwaiyi,
da sauri ya matsar da kafarshi ya kalli gurin dan ganin abunda ke mishi yawo a kafa,
wani irin tsalle ya daka hade da ihu mai karfi ya runtse idonshi yana tsalle yana faďin wayyo daddy maciji,
Afeeyah tayi saurin dauke macijin ta boyeshi taja hannushi a rude suka fito suna ihu tare,
da gudu daddy da oyizah suka fito suna fadin lafiya,
Afeeyah tace daddy maciji ne a dakinmu yana can ya shige karkashin gado,
a ruďe alhj basheer yace maciji,
Affan yace eh daddy har ya hau min kan kafata,
alhj basheer yayi hanyar dakin, Afeeyah tayi saurin cewa daddy karka je ya sare ka, ka bari zuwa gobe in Allah ya kaimu sai a nemo masu wasa da macizai su dubashi,
Alhj basheer yace hakane kuma amma a bar maciji ya kwana a daki, wai ni ta ina ma shigo,
Afeeyah tace nima tunanin da nakeyi kenan,
alhj basheer yace yanzu dai bazaku kwana a dakin ba zo muje bangaren safiya ku kwana daki daya, oyizah tayi saurin cewa alhj dakin da na bawa Affan cike yake da kaya a ina zasu kwana,
alhj basheer yace ba ga dakinki ba tunda ba a ciki kike kwana ba, yau kadai ne fa gobe zasu koma dakin su,
oyizah ta kumbura fuska tace sam baze yiwu ba alhj, akan me daki na privacy na in bar wata ta kwana a ciki,
alhj basheer cikin mamaki yace Afeeyan ce wata,
oyizah ta galla ma Afeeyah harara tace ba nufi na kenan ba alhj, alhj basheer yace na riga na gama magana suje can su kwana, Afeeyah ta kalli oyizah tayi murmushi tace to daddy ko za’a bude mana can dakin umma sai mu gyara mu kwana a ciki,
hankalin oyizah ya kara tashi dan tasan in Affan ya shiga wannan dakin to komai zai iya faruwa,
da sauri tace kuzo muje ku kwanta a nawa dakin,
Afeeyah tace a’a mummy kar mu takura miki da dai munje dakin umma,
oyizah tayi mata kallon zaki sani yau cikin dare, tace muje babu komai,
ciki suka shige alhj basheer ya wuce side dinshi oyizah ta kai su Afeeyah nata zuciyarta cike da mugayen kulle kullen data gama shiryawa akan Afeeyah….

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:37] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣7⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Suna shiga dakin Afeeyah ta cire hijab dinta ta kalli Affan dake tsaye har lokacin a tsorace yake tace zo ka kwanta mana,
ya karaso gurin gadon zai hau tayi saurin tare shi tace karka kwanta kan gadon mummy kaga ita babba ce, muyi kwanciyarmu a kasa ko,
ya gyada mata kai yana murmushi ya kwanta a kasa yana kallo sama,
bayi ta shiga tayi alwala ta kare ma bayin kallo tana gyada kai cikin mamaki dan cike yake da magunguna da sabulan bleaching,
fitowa tayi ta dauki hijab dinta ta kwanto dankwalin kanta ta shimfiďa dan bata ga dadduma a dakin ba,
sallah ta hau yi in ta idar ta kara tayar da wata kabbarar,
tun Affan na kirga sallahr da takeyi har bacci daukeshi bata idar ba,

☆ 2:30am ☆
Lokacin ta idar da sallolin da takeyi ta fara adduo’i tana neman taimakon Allah akan abin da zata aiwatar yanzu,
saida tayi addu’a sosai sannan ta mike ta cire hijab dinta ta rufe Affan dashi ta tofe shi da addu’a,
Saida ta tabbatar ta rufe windows din dakin sosai ta yadda ko kuda bazai iya bi ba bare ido yaga me akeyi a ciki,
da bismillah ta yaye zanin gadon sannan ta daga katifar,
dakyar ta iya cire katakon dake kasan gadon saboda nauyinsu,
a razane ta ja baya saboda hango wani makeken rami a karkashin gadon,
hasbunallahu wa ni’imal wakil kawai take fada saboda ta matukar tsorata da ramin, zuciyarta sai bugawa takeyi saboda tuna ita fa xata sa hannunta cikin ramin,
girgiza kanta tayi ta fara ja baya tana fadin wallhy bazan iya ba,
ji tayi kamar ta daki mutum a bayanta ta juyo a razane taga babu kowa sai muryar kaka liman dake mata yawo cikin kunnuwanta,
“na rokeki karki tsorata ke kadai ce garkuwar bayin Allahn nan,
in kika tsorata babu wanda zai iya,
“in kika gansu Ruwanki ne ki barsu ko ki ciresu ki taimaki mahaifi da kakar abinda ke cikinki””
A hankali ta karaso gurin ramin idonta cike da kwalla tasa hannu ta fara ciro kulle kullen dake ciki,
gumakan dake cikin ramin uku ne, daya an soke kanshi da mashi, biyu kuma an haďe su guri daya an kulle,
saida ta tabbatar ta fitar da komai daga cikin ramin sannan ta maida kayan gadon tana yi tana share zufa,
gaba daya a lokacin ta nemi tsoro ta rasa, kwashesu tayi cikin hijab din da ta rufama Affan ta buďe kofar dakin tayi saurin wucewa dakinta,
kitchen ta wuce cikin dakewar zuciya ta fara warware duk wani kullin garin magani tana zubarwa a cikin zinc tana kwarara mishi ruwa, haka layunma duk tayi musu,
gunkin lakan da aka hade su guri daya ta fara warwarewa ta sa tabarya ta dakeshi ya zama gari sannan ta kwararar dashi cikin zinc,
dauko dayan gunkin tayi wanda akayi shi da roba,
da bismillah ta zare mashin ciki,
tana dauko wuka zata fara yankashi taji wata guguwa mai karfi ta bude windown kitchen din,
hannaye taga an ziro ta cikin windown tayi saurin yar da wukar hannunta ta cilla wannan mashin bayan cabinet,
a hankali taga gangar jikin mutum na shigowa,
da gudu tayi hanyar waje tana addu’a,
tana zuwa kofar taji an datseta da karfi,
ja da baya ta fara yi tana salati tana kiran sunan hajja,
oyizah ta gani muraran ta bullo ta cikin kofar,
zaro ido tayi murya na rawa tace m-u-mm-y,
oyizah ta buga mata wata sanda a bakinta,
rike bakin tayi tana ta nemo addu’a a bakinta ta rasa,
cikin kunan rai oyizah ta fara matsowa fuskar nan babu rahama tace yau sai na kasheki, daga yau kin daina numfashi a doron kasa bare har kiyi yunkurin shiga rayuwata,
da hannuna zan kasheki tunda duk wani abu da nayi akanki bana samun nasara,
ban taba haduwa da abin da ya dameni ba sai a kanki dake da matsyacin saurayinki jabeer,
kamar yadda na kawar da jabeer da mahaifiyar Affan kema haka zan kawar dake kije can ki samesu dan babu wanda ya isa ya shiga gonata ya fita ba tare da yayi noma ba,
tayi wani huci hade da daga wannan sandar zata buga ma Afeeyah, da sauri ta goce ta rike sandar sosai,
nan suka fara dambe sosai har oyizah tayi nasarar kwace sandar,
da karfi ta shiga laftar Afeeyah da ita,
ihu Afeeyah takeyi tana ja da baya saboda azaba,
wani jug ta rarumo a gefenta ta kwaďa ma oyizah akanta,
nan jini ya fara zuba sosai,
da sauri Afeeyah ta bangajeta ta kama kofar kitchen din tana jijjigawa tana ihu sosai kamar zata tsaga gidan,
ganin kofar taki buduwa yasata daukar wuka ta nuna ma oyizah dake tahowa kusa da ita tace wallhy kina matsowa zan kashe ki,
oyizah ta goge jinin gefen idonta tayi wata irin dariya tace wai gawa ce ke maganar kashe me rai,
cikin kuka Afeeyah ta juya tana faďin ya Allah ka taimakeni,
tana jan kofar taji ta buďu tayi saurin fita ta datso oyizah a ciki,
da mamakinta tana bude kofar parlonta ta tarar da oyizah da wata mata mai gebararran halitta,
runtse idonta tayi ta fara fadin hasbunallahu wa ni’imal wakil, la ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalumin,
wukar nan dake hannunta ta ďaga da niyyar buga ma oyizah, nan tayi saurin dukawa ta kamo kafar Afeeyah ta daga ta sama tayi wurgi da ita ta bugu da bango da tiles din dakin,
kara mai karfi ta saki wacce ba alhj basheer kaďai ba har masu gadin gidan saida suka girgiza da jinta,
tun daga wannan karar Afeeyah bata kara sanin inda kanta yake ba,
jin Alhj basheer ya bude kofar dakinshi yasa chummy ta bace,,
da sauri oyizah ta yar da sandar hannunta ta tsuguna tana ihu a gaban Afeeyah,
da gudu Alhj basheer da farida suka karaso gurin, cikin rudewa alhj basheer ya shiga jijjiga ta yana kiran sunanta,
kallon oyizah yayi tana kuka sosai yace safiya me ya sameta, cikin makirci oyizah tace nima fitowa nayi na tarar da ita anan tana dambe da iska, ina matsowa kusa da ita sai naji saukar wannan wukar a goshina,
anya alhj yarinyar nan ba matsafiya bace kuwa,?
alhj basheer ya daka mata tsawa yace kamata mu kaita asibiti muji abin da ke damunta,
oyizah ta share hawayen karya ta kamata a zuciyarta tana murna dan suna zuwa asibiti zata karasa ta acan,

Alhj basheer na tada mota yaji kamar muryar Affan a gefen glass din motar, kallonshi yayi yace Affan ka tashi ne,
Affan ya gyaďa kanshi idonshi jajur yace daddy ina zaku kaita,
alhj basheer yace asibiti zamu kaita yanzu zamu dawo je ka kwanta kaji,
bude motar yayi ya zauna a inda aka kwantar da ita yace muje daddy,
alhj basheer yace kayi hakuri Affan ka je ka kwanta kafin mu dawo, Affan kamar zaiyi kuka yace daddy bazan iya bacci ba,
oyizah cikin fushi tace ka sauka akace ko bakaji abin da aka ce maka bane,
kallonta yayi cikin ido hawaye na sauka cikin nashi yace saidai idan tare da Afeeyah zaku saukemu,
oyizah zata kuma magana alhj basheer ya tada motar yace muje kyaleshi,
oyizah tayi kwafa dan wannan mayen ya rusa mata plan dinta,
har suka kai asibitin idon Affan bai bar zubar da hawaye ba,
janyoshi daddy yayi yana rarrashinshi akan ya daina kuka babu abinda zai sameta,
sun dan dade a tsaye kafin doctor yazo, direct ya wuce dakin da aka kaita,
ya dade yana treatn dinta yiyi dressn ciwukan dake jikinta,,
oyizah ma ta je wata nurse tayi mata dressn sannan ta wuce dakin da Afeeyah take,
zaune ta samu Affan ya kwantar da kanshi akan hannun Afeeyah yana kuka alhj basheer na tsaye a kansu yana rarrashinshi,
tsaki tayi a hankali ta karaso gurin tace alhj ya kamata kuje gida ni sai in kwana anan,
Affan yayi saurin dago kanshi ya noke wuyanshi yace um um nima zan kwana,
oyizah tayi dariya tace ya za’ayi mai jinya yayi jinya, kai da ba wani isashshen lafiya gareka ba ina kai ina jinya,
Affan ya kara fashewa da kuka yace ni babu inda zani,
alhj basheer yace to duk babu inda zamu a nan zamu kwana, oyizah ta ja baya cikin bacin rai ta watsa ma Affan harara a zuciyarta tace shege mayatacce ka kusa daina ganinta kwata2…..

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:38] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣8⃣ By Aysha Ya’u Kurah

A tsaye suka kwana a kanta babu wanda ya runtsa,
oyizah taki runtsawa ne saboda tana jiran su alhj basheer su rufe idonsu ta ida mugun nufinta akan Afeeyah,
alhj basheer kuwa yaki runtsawa ne saboda ganin Affan bai runtsa ba kuka kawai yakeyi wanda babu wanda a cikin su yasan dalilin yinshi har ni da nake dauko muku rahoto,

karfe 6 doctor ya iso, dakin Afeeyah ya shiga suka gaisa da alhj basheer yace bata farfado ba har yanxu,
alhj basheer yace ko motsi bata yi ba doctor da fatan dai ba wata gagarumar matsala bace,
doctor musah ya bude idonta a hankali yace buguwa ce kawai tayi sai wadannan ciwukan,
ya akayi ta samu wadannan raunin haka alhj,
alhj basheer cikin damuwa yace ina ganin gamo tayi cikin dare dan ni ihunta kawai naji na fito na sameta a sume ina fatan dai bai taba lafiyar cikinta ba ko doctor,
doctor musah yace dakyar ne alhj dan buguwar a kai tayi amma anjima zanyi scanning dan tabbatar da lafiyar shi,
alhj basheer yace Allah yasa muji alkhairi, doctor musa yace Ameen alhj sannan ya fita,
oyizah tace alhj ya kamata ku tafi gida kuje kuyi wanka sai ku kawo mana abin kari ko,
alhj basheer ya dafa kan Affan yace tashi muje gida ka dan yi bacci ka huta anjima sai mu dawo,
Affan ya ďago idonshi da ya kumbura ya girgiza kanshi yace kaje daddy,
alhj basheer yace haba Affan baka ganin yadda idonka yayi nasan ka gaji kuma bacci kakeji, kayi hakuri kazo muje kaji,
Affan ya mike yana murza idonshi ya fita ba tare da ya kalle su ba,
saida alhj ya dan dade a ciki sannan ya fito ya samu Affan a mota ya daura kanshi kan murfin kofar,
shiga yayi ya tada motar suka wuce…

Suna fita oyizah rufo kofar ta dawo gurin Afeeyah tana dariyar murna,
pillown kan Afeeyah ta cire tana fadin yau taki ta kare,
yau zan karar da duk wata matsalata in huta da bakin ciki, tana daura pillown kan Afeeyah taji an murďa kofar,
da sauri ta zauna ta zame pillown tana dariya tace doctor ka dawo,
doctor musah ya kalleta sosai yace eh na dawo,
nazo daukarta muje ayi mata scanning daga nan zata wuce resting room,
zaifi kyau ki tafi gida hajiya saboda bama yarda kowa ya shiga dakin hutu in ba likita ko nurse ba,
oyizah tayi mishi wani irin kallo tace kana nufin ita kadai xamu bari a asibitin babu wanda zaiyi jinyarta sai kace marar gata,
doctor musah yace haka ka’idar take hajiya baki ga conditn din da take ciki ba, oyizah ta fara masifah tace wallhy baka isa ba, babu inda zaka kaita haka kawai zaka wani zo kayi min iyayi anan,
to anan zaka barta tunda ko ina ka kaita Allah ne zai bata lafiya ba kai ba,
yayi mata wani irin kallo sannan yasa aka shigo da wani gado yace hajiya aiki na nakeyi tunda ba ke kike biyana ba dan Allah ki barni inyi aiki na,
ya kalli nurses din yace ku daura ta muje, suka kinkimeta suka daurata akan gadon,
rike gadon oyizah tayi tana ta bala’i tana wallhy baza’a tafi da ita ko ina ba,
mutane suka taru a gurin anata bata hakuri amma tace ita sam babu inda za’a tafi da ita,
doctor musah da kanshi ya amshi gadon yasa iya karfinshi ya fara turawa oyizah na binsu tana bala’i kamar zararriya,
dr musa bai tsaya a ko ina ba sai office dinshi, da karfi ya bude kofar ya tura gadon haďe da bangajeta ta fadi kasa yayi saurin shigewa ya datso kofar,,
wani sabon bala’i oyizah ta dasa ta dinga masifa cikin daga murya,
babu wanda ya kalleta a asibitin kowa harkar gabanshi yakeyi saboda su a ganinsu mahaukaciya ce in ba mahaukaci ba waye zaiyi wannan daga cewa za’a kai patient resting room,
ita kuwa oyizah musabbabin tashin hankalinta shine yanzu Afeeyah tasan ita wacece in har tabar Afeeyah ta kara kwana a doron kasa to tabbas asirinta zai tonu dan zata iya farkawa a ko da yaushe,
(oyizah bata san ba tun yau Afeeyah tasan ko wacece ita ba, kuma bata san bayan Afeeyah akwai mutanen da suka san ko wacece ita kuma suna nan tunkarota cikin kankanin lokaci )
sai da ta gaji da masifar dan kanta sannan ta wuce gida cikin kunan rai…

Tana isa gida ta faďa ma alhj karya da gaskiya akan abun da doctor musah yayi mata,
alhj basheer yace safiya mutumin nan fa aikin shi ne ya fiki sanin abinda ya dace, oyizah tace babu abinda ya sani alhj kawai mu canza mata asibiti,
alhj basheer ya girgiza kanshi yace babu inda zan kaita a can zata zauna har Allah ya bata lafiya,
in ma yace kar wanda ya kara zuwa gurinta to na yarda dan nasan zai kula da ita sosai, oyizah ta tsaya tana kallon alhj basheer tana huci kamar bakar zakanya,
mikewa yayi ya fita daga gidan gaba ďaya ya barta tsaye kamar zata kurma ihu…

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:38] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 5⃣9⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Kwanan Afeeyah uku a asibiti bata farfaďo ba, a cewar doctors buguwa tayi sosai kuma suna iyakacin kokarinsu gurin ganin ta farfaďo nan da yan kwanaki,
babu wanda ke zuwa dubata daga gida sai alhj basheer da Affan da har wannan ranar bai bar zubar da hawaye ba,
ba karamin damuwa alhj basheer yakeyi ba akan yawan kukan Affan,
gani yakeyi kamar yin kukan yanada nasaba da ciwonshi,
saida doctor musah ya kwantar mishi da hankali yace babu abinda ke damunshi may be ciwon matarshi ne ke sashi yawan kuka,
alhj yayi dariya da dr musa ya fada mishi haka, yace yanzu wannan da kwakwalwrshi bata da amfani har yake iya yin kuka dan wani nashi baida lafiya, kenan yasan zafin ciwo kuma yasan meye damuwa,,
doctor musah yace me zai hanashi yin kuka, alhj ni fa har yanzu kana bani mamaki akan wasu abubuwa da ka kasa fahimt– wani irin kallo Affan yayi ma doctor musah nan da nan yayi saurin canza magana yace kamar ciwon Affan ka kasa fahimtar kullum yana samun cigaba dan wani lokacin yakanyi abubuwa irin na masu hankali,
alhj basheer yayi murmushi yace hakane doctor, Allah dai ya kara bashi lafiya,
dr musah yace ameen alhj, mikewa alhj basheer yayi yace to mu zamu wuce dan inada inda zani,
dr musah yace to sai anjima alhj, nan suka fita dr musah ya bi Affan da kallon mamaki…

Affan ne zaune a kan kujera a palour ya haďa kai da gwiwa yana kuka sosai harda sheshsheka,
mamakin al’amarin nayi a zuciyata nace shi kuwa wannan tababben ko kukan me yake yawan yi tun ranar da aka kai Afeeyah asibiti oho,,
a hankali naji yana faďin sai na dauki fansar kisarku, bazan kyale duk wanda yakeda hannu a cikin kisan ku ba, wannan yakin ni zan karasa shi cikin kankanin lokaci in shaa Allahu,
sosai yake kuka yana faďin wadannan kalaman,
cikin kidima na kureshi da ido a zuciyata nace anya wannan bai samu sauki ba,
anya ba basaja yakeyi ba kuwa?,

Da sauri na maida computer cikin kwakwalwrta baya zuwa ranar da Afeeyah ta aiwatar da ayukanta na karshe wanda yayi sanadiyyar zuwanta asibiti,
da sauri na ciro yar makallaliyar camerar da ke makale a dakin oyizah na kunna,
cikin mamaki na fara dauko muku rahoton abin da ke ciki,
da naso in boye muku kamar yadda Affan ya boye ma su daddy sai naji wayar “Badiyya Aliyu” tana gargadina akan in rubuta muku komai har coma, da fullstop. kamar yadda “bingel” takeyi,

Da sauri na dauki wayata na shiga typo muku abin da na gani mai ban mamaki,

cikin bacci naga Affan ya rike kanshi yana juyi anan inda yake kwance a kasa,
a hankali bakinshi ke motsi yana faďin umma,
Jabeer,
daddy,
can kuma naga ya matse kanshi da karfi yana faďin wayyo ummana,
sun kasheta,
sun kasheta,
sun kashetaaaaaaaa….
ya faďi da karfi hade da mikewa zaune zufa duk ta jika mishi jikin shi,
waige2 ya fara yi a rude yana fadin ina ne nan, waya kawoni nan,, ya maza ya mike ya buďe kofar dakin a firgice ya farayin hanyar dakin zeenatu,
ihu ya jiyo a side dinshi yayi saurin daukar hanyar gurin, yana zuwa kofar dakin yaji oyizah na faďin “kamar yadda na kawar da zeenatu da jabeer” kema haka zan kawar dake,
lekawa yayi dan ganin ko dawa take,
a gigice ya ja baya saboda ganin Afeeyah da yayi bakinta duk jini,
a ruďe yace yaushe jabeer ya mutu, me Afeeyah takeyi a nan gidan, yanzu ummanshi ta mutu kenan,
tambayoyin da ya dinga ma kanshi kenan idonshi na ambaliyar hawaye,
da sauri yaja baya ya boye ya shiga dawo da abubuwan da suka faru dashi shekaru uku da suka wuce,
babu abinda idonshi ke hangowa sai lokacin da ya tarar da kartin maza su biyu sun bankare mahaifiyarshi suna shirin shaketa da farin kyalle gabansu cike da kayayyakin tsafi mummy kuma tazo da wuka tana kokarin dab’a mata a wuya,, ,
shi dai yasan tun daga lokacin bai kara sanin inda hankalinshi yake ba sai yau da ya farka ya kuma tarar da wani tashin hankalin,
me jabeer yayi mata ta kasheshi,
wani irin kuka ya kufce mishi mai ban tausayi ya mike da niyyar komawa dakinshi ya ceci Afeeyah daga kaidin oyizah,
har yakai kofar ďakin ya hango oyizah da wata a bakin kofar,
da sauri ya juya yayi hanyar dakin da ya farka ya ganshi a ciki ko zai samu makamin da zai iya yakar ta dashi,
yana shiga dakin yaji karar waya, da kamar bazai dauka ba, sai kuma yayi saurin dauka,
ba”a bari yayi magana ba daga daya bangaren, murya yaji ta tsofaffi cikin rudewa tana cewa ina fatan kina nan lafiya Afeeyah,
nayi wani mummunan mafarki akanki,
ki tabbatar kin mike kinyi sallah dan komai na iya faruwa cikin daren nan,
a hankali Affan yace waye ke magana, daga daya bangaren kaka liman yace kai din waye,
Affan yace nine Affan, kai fa,
cikin mamaki kaka liman yace Affan nine, kaka liman ne na daura,
Affan ya fashe da kuka yace kaka kana ina aka kashe min jabeer, me jabeer yayi kuka bari aka kasheshi,
kaka liman yayi kabbara da karfi yace Affan ka dawo cikin hayyacinka,
Allah mai iko,
ka daina kuka wannan maganar ba ta waya bace yanzu ina matarka,
a gigice Affan yace wacece matata kaka,
kaka liman yace Afeeyah itace matarka wacce take dauke da cikinka,!
wacce ta yarda ta aureka cikin larura domin ta kubutar dakai daga cikin masifar da kake ciki,!
wacce ta fara zame ma matsalarka ciwon ido,!
nan ya takaita mishi duk yadda akayi ya auri Afeeyah da kuma irin taimkon da tayi mishi,
zaman dirshan Affan yayi yana kuka sosai yace kaka babu mamaki itama bazata rayu ba don gata can sun ritsata a daki zasu kasheta,
innalilliahi W.I.I.R kadai kaka liman ke iya fada yana sauraren kukan da Affan keyi,

a hankali yace ka kwantar hankalinki Allah zai kareta ko don Rabon dake jikinta,
karar da tayi ne yasa shi saurin kashe wayar ya mike zai fito yaji mahaifinshi ma ya fito, jingina yayi da bango yana zubar da hawaye har suka fita da ita suka sata cikin mota,
kara kira kaka liman yayi Affan ya dauka yace ta kasheta kaka, gashi can sun tafi kaita asibiti da daddy,
da sauri kaka liman yace bata mutu ba,
na fada maka bazata mutu ba sai wannan rabon ya taka duniya, kayi saurin bin su karka sake ka barta ita da wannan matar dan zata iya yi mata illah, kuma karka nuna ma kowa kaji sauki domin yin hakan kamar ka bata goma ne daya bata gyaru ba,
da sauri Affan ya fita, musababbin binsu asibitin kenan,

ajiyar zuciya nayi dana gama tariyowa sai kuma nayi gaba har zuwa inda na tsaya muku wato inda Affan ke kuka yana fadin sai ya dau fansa….
Allah ya baka ikon karasa yakin nan Affan domin wannan kawar Bilki Nabayin Hatsabibiyace…..

Mrs tijjani shattima……
[15/12 09:38] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣0⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Tafe take cikin motarta tana neman tsohon almajirin da zata bashi sadaka ta saceshi ta kaima chummy suyi bandaro da jininshi domin ta samu sa’ar kashe Afeeyah,,
tana karya kwanar Gyaďi2 ta ga wani tsohon almajiri tukuf da kwaryar bara a hannunshi,
parking tayi ta sakko ta dunkule dubu biyu hade da farin kyalle ta bashi,
godiya ya dinga mata sannan ya juya mata baya, nan take ya bace ma ganinta,
cikin murna ta shige mota dan duk tunaninta hakanta ne ya cimma ruwa,
da murnarta ta koma gida ta wuce dakinta ta rage kayan jikinta, muryar Alhj basheer taji yana kwala mata kirah da karfi,
da sauri ta fito dan jin abinda ya faru, kauda kanshi yayi dan a yan kwanakin nan sam baya kaunar ganin fuskarta wani lokaci ma tambayar kanshi yakeyi daliilin da yasa ya aureta,
mutunta ta kawai yakeyi saboda darajar aure da kuma yarshi, badan haka ba da tuni yayi ma kanshi katanga da ita,
kallonshi tayi tace alhj ka kirani kuma kayi shuru,
yace eh baki zanyi daga cameroon zuwa anjima,
ina son ayi musu girki, ta bata rai dan ta tsani wani dan uwan alhj basheer ya rabeshi tace to naji sannan ta wuce daki tace wallhy taliya zan kwaba ma tsinannun..

Har bayan magriba baki ba su zo ba sai da akayi isha’i sannan motarsu tayi parking a kofar gidan Alhaji Basheer Balarabe (BB), su hudu ne suka fara shigowa, mata biyu maza biyu,
a parlon suka zauna alhj basheer ya tsuguna ya gaisar da baffa da dayan bakon cikin girmamawa, sannan ya kalli matan suka gaisa ya kure daya daga cikinsu da ido yace kamar nasanki,
tayi dariya zatayi magana oyizah ta fito tana ya tsina,
dakyar ta gaida baffa shima dakyar ya amsa dan kar ace bai amsa ba,
sannan tabi matan da kallon raini tace sann— muryarta ta sarke saboda ganin Gaje da tayi,
cikin mamaki tace gaje,
gaje ta dago tace na’am,
oyizah tace long time ina kika shiga haka tsawon shekaru uku babu ko zuwa duba mu,
Gaje tace walhy kuwa aure nayi shiyasa, oyizah ta tabe baki tace na miki murna,
bari a kawo muku abinci,
Baffa ya kalli alhj basheer yace labarin zeenatu har yanzu shuru ko?
Alhj basheer yace wallhy kuwa baffa, amma mun baza addu’a ana nan anayi kuma muna sa ran in shaa Allahu zata bayyana,
oyizah tayi murmushi a zuciyarta sannan a fili tace alhj in ta mutu fa,
shekara uku mutum ya bace har yanzu babu labari ay ni ina ganin ta mutu,
Baffa ya galla mata harara yace bashiru ina ganin Allah ya amsa addu’armu dan kuwa na samu labarin inda zeenatu take,
saboda firgici oyizah saida ta kusa karya kujerar da take kai, zaro ido tayi tace kana da labarinta,
Baffa ya kalli cikin idonta yace kwarai kuwa inada labarinta mai karfi ko kuma ince ina tare da ita ma,
alhj basheer ya dafa kafar Baffa cikin rawar murya yace tana ina Baffa,
kafin baffa yayi magana an murďa kofar palourn an shigo, da sauri alhj basheer da oyizah suka daga idonsu ya sauka kan zeenatu da tayi wata irin muguwar rama,
da sauri ya mike yana fadin z-e-e-natu, Abida da yadikko dake rike da ita suka nemi guri suka zauna, gabanta ya karaso ya kamo hannunta saboda ya gasgata ita din ce,
murmushi Abida tayi tace ita ce alhj zeenatun ka ce matarka kuma uwar danka,
Allah yayi zaku kuma ganawa,
alhj basheer ya tsuguna a gabanta idonshi ya ciko da kwalla yace ina kika shiga zeenatu,
idonta ya ciko da kwalla ta kalli gurin da oyizah ta sankare a tsaye tace na shiga cikin ukubar da bawa baya iya fitar da danuwansa bawa saidai Allah ya fitar dashi,
an so kasheni amma da yake shan ruwana bai kare ba sai gashi Allah ya dawo dani bayan mutuwar danayi ta dan lokaci,

mikewa tayi a hankali kamar zata fadi saboda rama, ta karasa kusa da oyizah tace ribar me kikaci a wannan izayar da kikayi mana,
me kika samu mai amfani bayan tafiyarmu,
meyasa zuciyarki ta zabi ta dinga kisan kai akan abun duniya da zaki tafi ki barshi a duniyar,
meye ribarki dan na mutu ni da ďana ke kuma kina rayuwa keda yayanki,
ki sani safiya Allah na kare wanda yaso a lokacin da yaso, kin—- oyizah tayi saurin katseta cikin tsawa tace duk wadannan maganganun na menene,
ina ruwana dake da zan kasheki, me kikayi min,
ta fara kukan munafurci ta matso kusa da alhj basheer tace sharri zatayi min dan kawai ta shiga duniya ta kwaso cutar kanjamau shine zata ce ni nayi niyyar kasheta,
alhj inda zan kasheta da Affan shekararshi nawa ina kula dashi ban kasheshi ba,
ba’ayi min godiyar kula dashi ba sai dai a bini da sakayyar sharri,
kan alhj basheer ya ďaure sosai yace wai meke faruwa ne, zeenatu zata fara magana
“Affan ya fito yace ni zan faďa maka duk abinda ke faruwa daddy”
cikin mamaki suka mai da kallonsu kan Affan,
karasowa yayi ya rungume zeenatu yana faďin baki mutu ba umma,
ta dago fuskarshi tana shafawa tace kaima baka mutu ba, ashe kana nan da ranka Affan,
kuka sosai suka dinga yi na tsawon mintuna,
alhj basheer ya janyo Affan cikin mamaki yana shafa kanshi yace kaji sauki ne Affan,
Affan ya gyaďa kanshi yace na dawo cikin hayyacina daddy,
Allah ya kwatoni daga hannun wannan azzalumar da take kiran kanta matarka,
farida da shigowarta parlon kenan ta karaso da sauri ta buge hannun Affan tace karka kara zagar min mahaifiya,
Affan yayi mata wani irin kallo yace kice kar in kara zagar miki matsafiyya ba mahaifiyya ba,
oyizah ta sa kuka tace alhj kanajin sharrin da danka yake min, ko da yake bazan ga laifinshi ba dan nasan mahaukaci ne shi baya cikin hayyacinshi,

alhj basheer dai kanshi ya ďaure yace dan Allah karku rikirkitani, ku fada min abinda ke faruwa,
Baffa ya kalli Affan yace zauna Affan bari mu fara jin komai daga bakin mahaifiyarka
sai muji naka..

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:38] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣1⃣ By Aysha Ya’u Kurah

A hankali zeenatu ta fara jawabinta kamar haka…

Ranar asabar bayan sallar isha’i ina zaune a daki sai naji kamar ana ihu acan sama gurin shan iska,
da sauri na mike na isa gurin dan duk tunanina Affan ne a gurin shi da jabeer dan mun rabu dashi zaije gurin jabeer,
ina isa gurin naga wasu kartin maza zaune kan wani jan kyalle da wani jan kaya a jikinsu,
juyawa nayi da sauri zan koma daki saboda sun matukar bani tsoro,
ina juyowa naga safiya cikin jajayen kayan itama tana dariya,
da sauri naja baya ina ambaton sunanta sai naji saukar sanda a tsakiyar kaina,
dishi2 na fara gani ina salati ina neman dauki gurin Allah,
cikin karaji naji muryar safiya tana fadin kunji ko addu’a takeyi na faďa muku wannan sai kunyi da gaske saboda nasha yin aiki akanta yana lalacewa,
jin haka yasani sake bude wani shafin na addu’a, sai naji sun ďaga ni, daya ya bankareni yana faďin zo ka shake mata wuya muga ta inda addu’ar zata fito,
da sauri ya matso ya matsemin wuya inata kakari na hango wata katuwar wuka a hannun safiya tana faďin wannan gara kawai mu kasheta sai mu kaita asha jininta, tana kokarin daura wukar a wuyana muka ji ihun Affan,
da sauri ta yar da wukar su kuma suka sakeni na faďa kan wani farin kyalle,
daga nan ban kara sanin inda kaina yake ba saida na ganni gaban wata mata wacce halittarta kaďai ta isa ta tsoratar da mai rai,
ajiyeni tayi a wani daki tana faďin yau dake zamuyi dinner,
tana fita naga wasu yara su biyu sun shigo dasauri suka tanbayeni wa ya kawo ni nan,
cikin rawar murya na ce musu kishiyata ce,
daya daga cikinsu tace nasan oyee ce dan bata da mutunci tunda ta kawo uwarta kowa ma zata kawo,
dayar tace har wani karamin yaro ma ta kawo lokacin da take neman cikin ďa namiji,
cikin sauri suka ce in tashi zasu fitar dani, da sauri na mike ina tambayarsu su bazasu tafi ba,
amsar da suka bani tasani zubar musu da hawaye sukace sunfi shekara ashirin a haka, yanzu gangar jikinsu ya riga ya zama kasa,
wani hanya suka nuna min nayi saurin bi na dawo jikina,
dakyar na iya mikewa ina kallon sanda suka dauki Affan zasu jefoshi daga sama su karasa shi dan kar ya tona musu asiri,
da sauri na fito dan kar su ganni na sakko kasa ina bin bango ina neman wanda zaizo ya taimaki ďana dan karsu kasheshi,
a kofar kitchen na hadu da Gaje ta dawo daukar sakon da safiya ta aiketa dashi,
da sauri ta rikeni tana tambayata,
dakyar na iya takaita mata, na kuma ce dan Allah ta dauko min Aff— ban karasa faďi ba naji karar saukar mutum kasa da karfi, tun daga lokacin ban kara sanin inda kaina yake ba sai kwana biyar da suka wuce,,
ta karasa tana kuka mai tsuma zuciya,,

Ajiyar zuciya Gaje tayi tace kwarai abun da ya faru kenan dan tana faďuwa nayi saurin janta store saboda jin muryar madam da nayi ta sakko nemanta,
munfi minti talatin a store sannan na daukota na fito da ita da sauri dan kar wani ya ganni,
ina fitowa naga wani me keke napep a kofar gidan alhj bara’u, dasauri na karasa nasata nace ya kaini dorayi gidan kawu na,
bai tsaya musun kudi ba saboda ganin halin da muke ciki,
tafiya sosai mukayi har muka iso nace ya jirani,
ďakin matar kawuna na kaita nace dan Allah su kular min da ita kafin gobe da safe,
ba musu tace ba komai saboda sunsan irin alherin da hajiya ke musu,
sai kusan goma na koma gidan,
ranar a tsorace na kwana,, washe gari ina tashi na tattara kaya na nayi ma madam karya nace mata mahaifina bashi da lafiya acan nijar,
kudi ta bani tace Allah ya bashi lafiya tare da jaddada min in dawo da zarar ya samu sauki,
amsata kawai nayi na fita daga gidan na wuce ďorayi,
a ranar muka wuce nijar ni da hajiya dan nasan acan ne zata fi samun kulawa saboda kawuna malamine,
babu irin addu’ar da ba’ayi ba amma sam babu sauki dan ko motsi batayi,
A can na barta na dawo jigawa ina wani aikin, har Allah ya hadani da wani mukayi aure,
yau kwanana biyar da zuwa gida na tarar ta farfado,
shekaran jiya ne ta matsa ita akaita can gidansu a cameroon,
bamu so mu kaita ba har saita kara samun sauki amma malam yace lallai mu kaita saboda ta samu nutsuwa,
a can cameroon da muka je ta labarta ma mahaifinta komai shine yace a shirya a taho nan kano domin a fayyace komai dan kar aja lokaci a kuma kullo wani mugun abun da zai fi na da..

Cikin tashin hankali oyizah tayi kukan kurah ta shako wuyan zeenatu tana fadin ni zakuyi ma sharri wallahy yau sai na kasheki,
da sauri Affan ya taso ya banbare mahaifiyarshi a jikin oyizah ya shiga dukanta yana haki yana fadin duk abubuwan da tayi mishi da kuma wanda tayi ma Afeeyah da kuma kisan da tayi ma jabeer,
shaketa yayi idonshi yayi jawur cikin ďaga murya yace me jabeer yayi miki kika kasheshi,
kakarin wuya oyizah keyi idonta sun firfito waje tana girgiza kanta,
babu wanda yayi yunkurin hana Affan har farida da kuka yaci karfinta saboda jin mugun alkaba’in da mahaifiyarta tayi,
zeenatu ce ta taso da sauri ta fara banbareshi a jikinta saboda kar yayi kisan kai,
dakyar ya rabu da ita yana haki idonshi cike da kwalla,
mikewa oyizah tayi ta ruga dakinta da gudu tana haki kamar zata mutu,
tana shiga ta bankade katifarta da katakon, tana dagawa taga babu komai cikin ramin sai kasa,
da sauri tasa hannu tana tone kasar ciki kamar mahaukaciya tana fadin ina kuke, waye ya kwashe ku,
wayyo Allah na shiga uku na lalace,
buga kofar ďakin taji anayi da karfi kamar za’a ballata,
a hankali ta leka ta windon don ganin ko waye,
yansanda ta gani tsaye su kusan shida da mace daya,
dariya ta saki wacce da gani kasan ta takaici ce ta jawo jakar kayan tsafinta nan da nan ta bace daga ďakin….

Mrs tijjani shattima…
[15/12 09:38] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣2⃣ By Aysha Ya’u kurah

Yan sandan sunfi minti goma a tsaye suna bugawa ba’a buďe ba,
cikin sanyin jiki alhj basheer ya taso ya dauko wani key yasa ya bude,
wayam suka gani ba oyizah ba sawunta sai katon ramin karkashin gadonta ne yayi musu sallama a idanuwansu,
alhj basheer idonshi ya kara ja yace jikina ya bani zata gudu dan shaidancinta bazai kare anan gurin ba,
da kun bar Affan ya kasheta mun huta dan yanzu wallahi bazata kyalemu ba,
malam maina ya taso yace ka kwantar da hankalinka in shaa Allahu babu abinda zai faru,
zamu toshe duk wata kafar da zata samu shigowa rayuwarku da addu’a,
alhj basheer ya sharce gumin goshinshi yace to Allah yasa, Ameen duk mutanen gurin suka ce,
Alhj basheer ya kalli Affan ya dawo kusa dashi yace Affan dama duk abinda kakeyi kana sane,
Affan ya girgiza kanshi yace ranar da mummy tayi niyyar kashe Afeeyah ranar na dawo hayyacina da taimakon Allah da taimakon Afeeyah,
nan ya kwashe duk labarin da kaka liman ya bashi na irin kokarin da Afeeyah tayi akansu ya fada musu sannan ya kuma faďa musu dalilin da yasa mummy ta kashe jabeer,,
ya share hawayen fuskarshi yace daddy dalilin da yasa kaga naki tafiya in bar Afeeyah a asibiti kenan saboda nasan muna barin gurin zata karasa ta,
doctr musah ma yasan na samu sauki saboda washe gari da mummy ta matsa sai mun tafi naje na sameshi na fada mishi komai nace ya taimakeni ya dauketa yace su zasu dinga jinyarta,
da kyar ya yarda dan a tunaninshi ban samu sauki ba shirme nake mishi,
muna tafiya yace min yaje dakin dan ya gasgata maganata sai ya tarar ta cire pillow tana kokarin kashe ta,
hankalinshi ya tashi a lokacin sai ya tabbatar naji sauki shine ya shirya plan din za’a kaita dakin hutu,
alhj basheer ya jinjina kanshi hawaye na fita a idonshi yana faďin ku yafe min, duk ni na jawo muku da na shigo da safiyya cikin iyalina,
gashi bata tsaya kai na ba har saida ta taba ya’yan makota na, dan Allah kuyi min afuwa ku dau duk wani hukuncin da ya dace a kaina,
zeenatu tace ka daina kuka alhj ba laifinka bane RABO ne ya shigo da ita rayuwarka, Rabon salma da Farida zai iya AJALIN duk wanda ya hana wannan auren a lokacin,
cikin kuka alhj basheer yace tabbas ya ko yi ajalin mahaifiyarta dan taki amincewa da zancen,
ashe safiyar ce ma ta kasheta da hannunta,
Affan yace har Anty salma itace silar mutuwarta dan jiya da mukayi waya da kaka duk ya faďa min hatsaririkan da Afeeyah ta tsallake a gidan nan,
mamakin alamarin kowa ya dinga yi haďe da ganin jarumta da jajurcewar Afeeyah,
Abida dai banda kuka babu abinda takeyi dan mutuwar jabeer ta dawo mata sabuwa fill a yau,
tabbas da an barta ita da hannunta zata kasheta ta huce takaicin rabata da nagartaccen ďanta mai cike da Haiba da tayi..,

Cikin kuka fareeda ta matso kusa da Affan tace dan Allah Affan ka yafe min abin da nayi maka wallahy sharrin shaidan ne da kuma ganin mummy nayi,
Affan ya janye kafarshi ya galla mata harara,
cikin tsawa alhj basheer yace tashi ki bamu guri yau dinnan zaki bi uwarki dan ban sani ba ko ke din ma ta tsafin ce,
fareeda ta rushe da kuka tana bashi hakuri, a hankali zeenatu tace alhj laifin wani baya shafar wani,
duk wanda yaga farida yaga jininka dan haka hannunka bazai rube ba ka yanke ka yar ba,
alhj basheer yayi saurin cewa saidai kuwa in bai isheni da wari ba,
yanzu ke kina so in zauna da jinsin matsafa a gida,
Baffa yace bashiru hakuri zakayi ya’ dai taka ce dan haka dole ka riketa ku koya mata tarbiyar da addini ya koyar kuma ku aurar da ita,
nan suka cigaba tattauna maganar cikin tsananin al’ajabi….

Cikin tashin hankali oyizah ta bayyana a gurin tsafinsu,
kuka sosai takeyi a gaban chummy tana faďa mata duk yadda akayi har dawowar zeenatu da samun saukin Affan,
chummy ta kalli oyizah cikin mamaki tace ya akayi haka ta faru,
oyizah tace nima ban sani ba, komai na kayan aikina an kwasheshi a karkashin gado babu komai a gurin sai kasa,
sai kuma kwalbar nan da yan iskan yarannan suka fasa nasan shiyasa zeenatu ta farfaďo,
chummy tace na sakeyin wacce tafi tada karfi kin ganta can,
oyizah cikin mamaki tace to ya akayi haka,
chummy tace ni nafi mamakin na dakinki da wanda kika birne a bakin damo,
oyizah tayi saurin ďago kanta tace nasan wanda zaiyi min wannan aikin,
wannan yar iskar yarinyar ce zatayi min, wallahi I will not spare her,
yanzun nan zanje asibitin da take in kasheta,
chummy tayi murmushi tace daďina dake garaje,
bakya tunani kafin kiyi abu,
waye ya faďa miki suma yanzu zasu zauna,
, ai sun riga sun san sirrinmu so sai munyi da gaske ta karkashin kasa musa ki koma gidanki sai ki aiwatar da ayyukanki cikin kwanciyar hankali,
oyizah ta gyada kanta tace wallhi wannan karan mai zafin zanyi duk saina kashesu in mallake alhj da dukiyarshi muyi zaman mu tare har karshen rayuwarmu,,,
chummy tace yauwa ashe kin gane,
yau da daddare zamu fara aikin, kinsan akwai ďan tsoho da kika kawo to dashi za’ayi miki aikin, yanzu tashi muje gurin Dodo BELAH mu dawo kafin lokacin meeting yayi,
oyizah ta mike zuciyarta wasai dan a tunaninta komai nata zai koma normal tunda CHUMMY tayi assuring dinta,,,
oyizah sarkin sa’a……..

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:38] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣3⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Kwance take kan kirjinshi ta cukwikwiyeshi tana kuka mai ban tausayi tana faďin
“meyasa ka tafi ka barni na tsawon lokaci, meyasa baka daukeni mun tafi tare ba ka barni cikin wannan wahalalliyar duniyar mai cike da azzalumai marasa tsoron Allah,
ta tsunguna a kasa kukanta ya tsananta tace dan Allah yaya jabeer karka sake tafiya ka barni,
ba karamin wahala nake sha ba saboda rashinka,
I grew up in your arms plss led me die in it, plsssss,
ďagota yayi suna kallon cikin idon juna taga wani haske mai matukar kyau a cikin kwayar idonshi,
a hankali taji yana faďin tafiyata bazata taba zama wahala agareki ba,
naso kasancewa tare dake amma Allahn da ya hallicemu bai halicceki dan ni ba shiyasa ya ďaukeni domin ki kusanta da wanda yake makusanci na hakika a gareki,
dama ni ba mazauni bane zuwa nayi in nuna kamannina in koma ga ubangijin talikai,
tabbas nasan lokacin da nake da rai baki da wata matsalar rayuwa, yanzu kuwa nasan ko baki gama sanin meye rayuwa ba kinsan kadan daga ciki,
mu’imuni ako da yaushe Allah na jarabtarshi ta kowane bangare, duk wanda ya kansance cikin farin ciki a kullum to tabbas ya binciki kanshi domin duniya kurkukun mu’imuni ce sannan aljannar kafiri,
kafiri marar tsoron Allah, ko wanda ke sabawa Allah shi kaďai ne ke samun farin ciki marar yankewa a duniya,
akwai lokacin da zamu shiga farin ciki amma cikin lokaci kalilan sai bakin ciki ya maye gurbin wannan farin cikin,
to ki sani duk musulmin dake yawan shiga cikin jarabawar Allah lallai ba karamar soyayya bace tsakanin wannan bawan da Allahn shi, domin shiga kunci ga musulmi kankarar zunubi ne,
wasu kuma zaki ga basu da wata damuwa komin zunuban da sukeyi ba shi zai hana Allah ya barsu cikin farin ciki ba, sannan kome suka nema suna samunshi kamar su suka tsara rayuwarsu, to wadannan Allah ya barsu da kansu ne har sai sun tuba,
kullum mu’imunin kwarai yana cikin jarabawar ubangiji masu tsananin rabo su ke cinye jarabawar dari bisa ďari,
ya share mata hawayen idonta yace zanso Afeeyata ta zama daga cikin masu cinye jarabawar ubangiji a koda yaushe,
zanso ki daina yawan zubar min da hawaye domin hawayen basu kara komai sai wahalarwa ga kyakyawan idanuwanki,
zanso ki manta batun soyayyata a matsayin wanda zai aureki ki sanya soyayyar yaya a zuciyarki domin samun tsaftattaciyar addu’a daga gareki,
ki kular min da Affan kamar yadda zaki kula dani domin ni da shi bamu da wata maraba kuma nasan zai kula dake kuma ya kaunace fiye da yadda ni nayi, ki yawaita istigfari domin istigfari yana kusanta bawa da ubangijinshi kuma mai yawan yinshi zai kasance kullum cikin nutsuwa da walwala,

cikin sheshshekar kuka Afeeyah ta buďe baki zatayi magana jabeer ya sa hannu ya rufe bakin yace karki ce min komai ga Affan can yana jiranki zaku tafi gida, nagode sosai da ziyara,
cikin kuka ta cire hannunshi a bakinta tace dan Allah yaya jabeer ka tsaya kaji abinda zan faďa maka,
girgiza kanshi yayi yana mata murmushi hasken hakoranshi suka rufe idonta ta durkushe a gurin tana kallonshi cikin hasken tana kuka sosai tana kiran sunanshi,
wata sassanyar iska ta shiga kaďawa a gurin har hasken jabeer ya bace ma ganinta,
runtse idonta tayi tana kuka sosai tana faďin dan Allah karka tafi ka barni,

Hannu taji cikin nata ana murzawa a hankali sannan taji saukar ruwa a kan hannun,
a hankali ta fara buďe idonta da yayi mata nauyi sosai ta saukesu kan Affan dake zaune kusa da ita kanshi a kan hannunta yana zubar da hawaye,
lumshe idonta tayi hawaye na zuba ta gefensu ta fara tuno mafarkin da tayi akan jabeer,
meyasa ya tafi bai tsaya yaji abinda zance mishi ba, meyasa be bari nasan abinda zan faďa mishi ba,
shikenan bazan kara ganinshi ba har in koma ga Allah,
to ni yaushe zan mutu, wayyo Ya Allah ka dauk—- Affan yayi saurin toshe mata baki da hannunshi yasa hannu yana share mata hawayen dake gangarowa daga cikin idonta,
buďe idonta tayi ta kalleshi tasa hannu ta ďan ture hannunshi cikin muryar kuka tace kukan me kakeyi,
da mamakinta sai taji ya kwanto jikinta yace kukan abin da kikeyi,
a hankali tace ai bakasan kukan da nakeyi ba,
ya ďago jajayen idanuwanshi yace nasan har duniya ta naďe bazaki taba yin kukan komai ba in ba na rashin jabeer ba,
cikin mamaki ta kureshi da ido hawaye ya kara zirarowa a cikinsu cikin rawar murya tace kasa— ya fashe da kuka yace nasani Afeeyah, nasani,
nasan jabeer ya tafi ya barni,
nasan bazan sake ganin fuskarshi mai dauke da murmushi a kullum ba,,
nasan bazamu sake haďuwa mu rungume juna mu faďa ma juna damuwarmu ba,
bansan me yasa mutuwa ta zabi jabeer ta barni, bansani ba Afeeyah,
ya karasa fadi yana kuka kamar karamin yaro,,
kuka suka dinga yi babu mai rarrashin wani a cikinsu,
saida sukayi mai isarsu sannan Affan ya ďago ya kalleta murya a dashe yace nagode, nagode da abin da kikayi min,
kau da kanta tayi tace ka gode ma Allah da kaka liman,
ya juyo da fuskarta yana kallon rinannun idanuwanta yace kullum cikin gode musu nake,
godiyarki ta daban ce Afeeyah, babu wanda zai dauki kasadar da kika ďauka a duniyar mu ta yanzu,
kinyi mana abin da ko dan uwa na jini bazai iya yi mana shi ba, bamu da wata kalmar da zamuyi amfani da ita gurin gode miki, Afeeyah tace karka gode min na cika kudirin jabeer ne, wannan shine burinshi na karshe, saboda wannan kudirin aka kashe min shi,,,
Affan yace nasan komai Afeeyah kuma in shaa Allahu wacce ta kasheshi ba anan duniya ba ma har a lahirah bazata taba samun kwanciyar hankali ba,
Afeeyah tace tun a duniya nakeson Allah ya wulakanta min ita, wallhi da nasan ita ce silar mutuwarshi na rantse da bazan kyaleta ba da nayi mata abun da zata gwammaci mutuwa da rayuwa,

Affan ya share mata hawaye yace ki kwantar da hankalinki nasan yanzu duk inda take a cikin bala’i take,
Afeeyah ta girgiza kanta tace da hannuna nakeson in kasheta kuma yau dinnan,
Affan yace hmm nima naso hakan tun ranar da na dawo cikin hayyacina,
nan ya bata labarin komai harda dawowar umma da bacewar oyizah,,,,,
cikin mamaki Afeeyah tace zatayi abinda yafi haka muguwa azzaluma, Allah ya isa tsakanina da ita,
in shaa Allahu sai tayi mutuwar kask—Affan ya katseta da sauri yace wannan adduar bata kamace ki ba, Allah yasan yadda zai tafiyar da irinsu ki zuba ido ki jira lokaci,
Afeeyah tayi shuru tana kallonshi kamar ba shi bane tababben bawan da baya taba maganar da zaka iya fahimta a da,
Allah mai iko……

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:38] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣4⃣ By Aysha Ya’u Kurah

Daren ranar suna zaune gurin meeting bayan sun dawo daga gurin dodon tsafinsu,
gaba dayansu suna sanye da jajayen kayansu da suke amfani dashi,
bayan sun gama tsaface tsafacensu sai chummy ta mike taje ta shigo da ďan tsoho,
a tsakiya suka sashi kamar yadda suka saba,
kewayeshi ta farayi tana yan sirkullenta a kanshi sannan ta zauna,
ďaya bayan ďaya tsohon yake bin mutanen gurin da kallo,
yana zuwa kan oyizah ya tsayar da idonshi kyarr a kanta baya ko kiftawa,
kureshi itama tayi da ido cikin rashin tsoro ta daka mishi tsawa tace daina kallona, idon wannan tsohon ko rawa baya yi ya fara motsa bakinshi da babu hakori ko ďaya a ciki,
oyizah ta kalli chummy tace my lord plss mu gama da tsohon nan mu cigaba da abinda ke gaban mu,
chummy bata kalli oyizah ba ta cigaba da haďe haďenta na tsafi cikin wani katon koko,
mikewa tayi ta iso gaban tsohon ta ja hannunshi da karfi har yana bigewa ta jona mishi wani abu mai tsini kamar kibiya a jijiyar hannunshi tana kallon cikin kokon,
a firgice ta juyo tana kallonshi ta kuma maida idonta cikin kokon dan gasgata abin da ta gani a ciki,
da sauri ta saki karfen taja baya saboda yadda ya dauki zafi kamar tana rike da garwashi,
wata irin dariya tsohon nan ya saki yace jinin nawa ya isheki haka, in kina bukatar kari kizo ki diba san ranki dan ko zaki dibi cikin tanki bazai kare ba,
su oyizah duk suka marmatso suka leka cikin kokon,
a gigice suka ja baya saboda ganin wani bakin ruwa mai kaurin gaske a ciki,
oyizah murya na rawa tace my lord kiyi wani abu plss wannan kamar ba mutum bane,
cikin su esther da alhj sambo ya ďuri ruwa suka ce kwarai wannan ba mutum bane,
cikin dakewa chummy tace ko ma waye shi tunda yazo nan bazai taba fita ba,
ta dauko wata sanda mai mugun kyalli ta nufi wannan tsohon dashi,
tana karasowa gaban shi ta ďaga wannan sandar ta saita cikin idonshi ta turata ciki, ga mamakinta sai ganin sandar tayi ta rabe gida biyu, daya a cikin idonshi ďaya a hannunta,
sa hannunshi yayi ya zaro sandar yana dariya ya mika mata yace haďata guri ďaya,
a harzuke ta yar da sandar hannunta ta koma ta shirya kanta sosai tace yau ko waye tsohon nan sai na gama dashi,
ta bayanshi ta bullo ta sa farcen hannunta ta shako wuyanshi ta baya, da azama ya juyo ya sanya nashi faratan a makogoranta,
wani irin kakari ta farayi tasa kafarta ta haureshi yayi baya, nan suka fara b’ace b’ace suna faďa sosai,
ba karamin wahala chummy take sha ba amma saboda tsabar ta dahu da tsafi kuma bata so mabiyanta suga gazawarta haka ta jajirce suka cigaba,
wani lungu ta shiga a cikin ďakin ta fito rike da wani magani ta bace tana kokarin watsa ma wannan tsohon,
sam bata san yana kallonta ba ta ďaga wannan maganin zata zirara mishi yayi saurin juyar da hannunta ya zuba wannan ruwan a tsakiyar kanta,
wani irin ihu ta saki ta faďi kasa tana ta shure shure nan take kanta ya fara zagwanyewa, tun tana ihu mai karfi har ta koma yi a hankali gaba ďaya mummunar halittarta ta canza kama,,
a gigice su oyizah suka fara ja baya hankalinsu a tashe babu wanda a cikinsu yayi kokarin zuwa gurin wacce suke kira mai taimakonsu, itama yau gashi ta kasa taimakon kanta,
mikewa wannan tsohon yayi yana kallon su oyizah,
mai da hankalinshi yayi gurin alhj sambo yace alhj sambo Bana, minister mai fuska biyu,
a fili fuskar kamala a zuci ta zalunci,
ina son kayi ma kanka hisabi ka zabi hukunci cikin jerin abinda zan lissafo,
na farko ko in kasheka anan in kaika gida da kayan jikinka, ko kuma in barka ka koma gida ka fito media ka faďi ko me kakeyi sannan ka fadi adadin mutanen da ka bayar akasha jininsu,
alhj sambo cikin rudewa yace kayi min rai dan Allah,
dan tsoho yace Allah shi ke da rai bani ba,
alhj sambo yace ka rufamin asiri wallhy na tuba,
har abada bazan kara aikata irin wannan aikin ba,
dan tsoho yayi dariya yace zunubin da kayi baya kuma fa,
kayi kisan kai, shirka, da sauransu duk dan ka samu mulki,
haka nake so kaje gidan talabijin ka sanar musu da halinka,
alhj sambo ya girgiza kanshi yace mutunci na zai zube,
dan tsoho yace ai gara ya zube a duniya, alhj sambo yace dan Allah ka kasheni anan kawai gara suga gawata,
dan tsoho ya girgiza kanshi yace a’a bazan yi kisa ba gara a hukunta ka kafin kaje ka tarar da na ubangiji,
kuka sosai alhj sambo yakeyi yana mishi magiya akan ya kasheshi ya huta amma tsoho yayi kememe yaki,
alhj sambo da yaga babu sarki sai Allah sai ya amince da abinda tsoho yace mishi ya kimtsa ya bace yayi gida hankalinshi a tashe,

kallon sauran yan gurin tsoho yayi ya dinga neman wacce tayi silar zuwanshi gurin bai ganta ba, girgiza kanshi yayi yace in kere na yawo,,,
sannan ya kalli su esther da suka tsure yace kuje Allah yasan yadda zaiyi daku itama waccan ogar taku banyi niyyar yi mata komai ba saida tazo cutar dani,
yana kaiwa nan ya bace,,
da sauri su esther sukayo kan chummy da ake iya hangen komai na tsakiyar kanta,
dagota sukayi suka ga komai na kanta na zuba a kasa,
a firgice suka saketa suka fara tattara kayansu,

wata a cikinsu mai suna HADASIYYA ta kalli kujerar tsafin chummy, muguwar zuciyarta ta sak’a mata ya kamata ta gaji kujerar itama ta zama 1 daga cikin matsafan da ake ji dasu ta samu mabiya tayi mulkinta san ranta,
murmushi tayi ta ajiye kayan hannunta tayi gurin kujerar,
tun kafin ta karasa karnikan gurin da eagles suka dinga kuka irin nasu na dabbobi,
tana taka step din gurin esther tasa ihu tace Hadiscos karki zauna,
nan hankalin sauran yakai kanta suka haďa baki suka dinga rokonta akan kar ta zauna taxo su gudu,
inaa wanda yayi nisa baya jin kira domin dai hadasiyya gani take bakin ciki suke mata dan karta fisu matsayi,
tana daura mazauninta akayi sama da ita,
wani irin girgiza ďakin ya farayi yana cilli da duk wanda yake cikinshi,
saida ya gama cillar dasu sannan ginin ya ruso gaba dayanshi kan ragowar chummy, “hmmm duniyar chummy ta kare”
saura oyizah ko ina ta shiga….

Sauki sosai ya samu a gurin Afeeyah har an sallameta ta dawo gida,
tana matukar samun kula gurin zeenatu da Affan duk da ba wani sabo sosai tayi dashi ba,
gyara sosai alhj basheer yasa ayi a gidan da saukar alqurani saboda shi har a lokacin a tsorace yake dan yasan indai safiya na raye to bazata taba barinsu ba,
farida ma ta nutsu sosai dan islamiyya ta koma ta zama saliha gwanin ban sha’awa, tsakaninta da zeenatu ba raini sai matukar girmamawa,
haka suna girmama junansu ita da Afeeyah….

3mnts later

Alhj Bara’u ne tsaye a ďakin jabeer yana duba wasu takardun Asiyah da jabeer din ya amso mata ana sauran sati biyu ya rasu,
cikin drawer ya bude ya gama bincikosu ya gansu can kasan kayanshi,
har zai rufe drawer sai yaga wasu takaddu a tsaftace cikin file dinsu,
dariya yayi yace jabeer kenan sarkin ajiyar takardu,
daukosu yayi ya rufe drawer ya budesu yana binsu da kallo,
cikin mamaki yace wannan ai takardun kadororin alhj basheer ne,
fitowa yayi daga dakin ya rufo kofar ya kaima Abida takardun Asiyah sannan ya wuce gidan Alhj basheer….

Mrs tijjani shattima…….
[15/12 09:38] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 65 By Aysha Ya’u Kurah

A parlor suka zauna sai da suka gama gaisawa sannan Alhj bara’u yace wasu takardu na gani a dakin marigayi kuma da sunanka a jiki,
alhj basheer yace takardu kuma,
alhj bara’u ya mika mishi yace kwarai kuwa,
alhj basheer ya amsa ya duba su cikin mamaki yace ikon Allah,
wadannan takardun sune silar shigan iyalina cikin tashin hankalin nan alhj bara’u,
nan ya bashi labarin kyautar da yayi ma Affan, ya daura da cewa ashe jabeer ya bawa ajiyarsu,
tabbas nasan safiya tayi neman takardunnan bata gansu ba,
kai gaskiya nagode alhj ubangiji Allah ya jikan jabeer ya kai rahama kabarinshi,
alhj bara’u yace Ameen,
nan suka cigaba da hirarsu hankali kwance,,,,,

Fitowa tayi daga inda take makale kullum a cikin gidan bayan ta gama jin hirar alhj basheer da alhj bara’u,, tunda ta gudu daga gurin tsafin su kullum a gidan take yini a makale bacci ne kadai ke mayar da ita wani kurgugun daji inda take hada kulle kullenta,
dariya tayi sannan ta shiga parlourn ta dauki takardun tayi kissing dinsu tace me ya rage min tunda na samu wannan,
bari kawai in tafi inje in fantama hankali kwance,
a hankali ta fito daga parlorn ta make jikin window tana jiran alhj ya shigo ta fita,
tana tsaye a gurin ta hango Afeeyah da cikinta dan wata hudu da kwanaki har ya fito sosai kamar dan wata bakwai, Affan na tsaye kusa da ita ya daura hannunshi kan cikin yana mata magana kasa2 suna dariya,
wani bakin ciki ne ya turnuke oyizah saboda tuno cewar Afeeyah ce silar fitarta daga gidannan,
itace silar rushewar komai na farin cikinta,
kwafa tayi cikin bacin rai tace wallhy bazan bar yarinyar nan ta dawwama cikin farin ciki ba,
dole in dawo da shirina gobe in tarwatsa rayuwarta kafin in bar kasar nan gaba daya….

Washe gari tun takwas na safe ta gama shirinta na zuwa gidan alhj basheer ta gama da Afeeyah ta huta, takardun da ta ajiye can kasan katifarta ta daga cikin izza zata dauka taga wayam,
hankali tashe ta bankade katifar tanata dubawa ko idonta ne amma sam bata gansu ba,
cikin tashin hankali ta karaďe arear da take zaune ko zata ganshi nan ma babu labari,
a gigice ta sa takalminta ta nufi cikin gari rike da kwalbar acid da ta tsaya ta siya jiya da daddare kafin ta dawo makwancinta,
bacewa tayi kamar yadda ta saba ta shiga gidan, dakin alhj basheer ta shiga yana kwance yana bacci hankali kwance gidan sai kamshin girki yakeyi,
tana kallon side drawer dinshi ta hango takardun da ta tabbatar ta kwana dasu a dakinta,
a rude ta daukesu tace ya akayi suka dawo nan,
rungumesu tayi tace koma wani tsinannan ne ya dawo dasu to sun dawo hannuna kuma bazasu kuma fita ba,
saurin bacewa tayi saboda jin motsin kofa tayi dakin su Afeeyah,

Kwance ta sameta tana bacci cikin bargo shi kuma Affan yana zaune a gefenta yana duba wasu takaddu, murmushi tayi ta makale jikin bango ta buďe kwalbar hannunta ta ďaga zata zirara a kyakykyawar fuskar Afeeyah,
juyi Afeeyah tayi hade da mika tana faďin
“la’ila ha illallahu muhammad rasoolullah sallalahu alaihi wasallam”
Alhamdu lillaahil-lathee ‘ahyaanaa ba’da maa ‘amaatanaa wa’ilayhin-nushoor.,,
nan kwalbar hannun oyizah ta fara girgiďi nan take tayi taka juye a fuska da jikinta,
a gigice ta saki takardun hannunta tasa razanannan ihun da saida ya girgiza gidan saboda kararshi,
a firgice Affan yaja Afeeyah yana kallon oyizah da ta sauya kamanni,
mikewa yayi da sauri yana fadin “Allaahumma ‘innaa naj’aluka fee nuhoorihim wa na’oothu bika min shuroorihim.”
Da gudu su alhj basheer suka shigo dakin suna fadin lafiya, ganin oyizah sukayi a kwance tana birgima ta yage duka kayan jikinta tana ciccisge gashin gabanta dan tsananin azaba,
da kafarta alhj basheer ya ganeta yace safiya!!! Innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
ya waiga ya kalli zeenatu yace kin gani ko na fada miki safiya bazata kyalemu ba,
“Tabbas bata kyaleku ba dan tana bibbiyarku kullum a cikin gidannan, tare kuke yini da ita,”
sukaji wata murya ta ratso kunnensu mutumin ya bayyana a gabansu,
gaba dayansu suka ja baya a tsorace,
da sauri tsohon yace kar kuji tsorona, ni ba mugu bane, asalima na zama kariya a gareku tun lokacin da take bibiyarku,
a jiya ne ta samu damarta da take ganin ta gama samun komai saboda kwashe wadancan takardun da tayi,
a daren na maido da takardun shine yau ta dawo ta kwashesu kuma tazo da niyyar kashe Afeeyah ta hanyar zuba mata ruwan batir,
cikin ikon Allah sai ta farka da addu’a nan take mai kowa mai komai ya tsareta ya mayar mata da kaidinta,

mamaki suka dinga yi suna Allah wadai da oyizah dake ta faman ihu tana fisge fisgen gashin gabanta,
godiya suka dinga yi ma tsohon har ya bace ma ganinsu sannan suka dawo akayi waje da oyizah dake zabura babu komai a jikinta,
gudu ta dingayi tana ihu kamar mahaukaciya ta fada gidan Malam Atiku,
suwaiba na zaune tana cin kosai tana hararar hajja taji an fado kanta ana ihu,
da sauri suwaiba ta mike tana ihu ta fada daki ta datso tana leke tana haki,
cikin kuka oyizah tace suwaiba nice, nice safiya, suwaiba tace safiya, safiyar alhj basheer,
oyizah tace eh ita, ki bude min kofa,
suwaiba tace Allah ya kyauta in bude ma matsafiya kofa,
safiya ta kara sa ihu tace suwaiba na daina, wallhy na daina, nayi dana sani, ki yafe min, ni na kashe abulbait, ni na bashi sweet yasha ya mutu muka sha jininshi,
suwaiba ta saki salati tayi saurin bude kofar tace ke kika kashe abulbait,
oyizah tace nice ki yafe m— ay bata karasa ba taji saukar tabarya a bakinta,
wani ihun ta saki ga azabar konewar fuska gata jibgar tabarya,
bugunta suwaiba takeyi baji ba gani tana kuka tana fadin kin cuceni,
dakyar hajja ta hankada oyizah waje ta dawo bawa suwaiba hakuri,
cikin kuka tace hajja ki yafemin na cuci kaina, dan ALLAH ki yafemin,
hajja tace babu komai ai dama duk wanda ya hau motar kwadayi to babu a inda zata saukeshi sai tashar wulakanci,
wannan ya zama darasi ga masu hali irin naki,
daki suwaiba ta shige cikin nadama tana kukan mutuwar danta….

Kwanan oyizah huďu tana yawo akan titi babu wanda yake kulata bare yayi yunkurin taimaka mata,
gaba daya ta gama cisge gashin gabanta da hannunta,
ga ciwon jikinta da fuskarta yana mata radadi kamar zai tarwatsa kwakwalwarta,
gurin wata kwata take zama ta dinga ďiban ruwan gefe tana watsawa a jikinta ko zata samu sassaucin azaba,

a ranar kwana na biyar din ne tana zaune tana ihu tana fadin irin mugayen abubuwan da tayi taji an tsuguna a gefenta,
da ido ďaya ta kalli gurin taga Afeeyah ce ta daga kanta taga fareeda tsaye tana kuka,
mikewa tayi tana kokarin rungume farida tayi saurin ja baya tace karki tabani mummy,
zuwa kawai nayi in ganki saboda an fada min hakkinki a kaina,
Afeeyah tace a’a fareeda uwa uwa ce, kome tayi mahaifiyarki ce,
oyizah tayi tsaki cikin azaba tace kece ma kike fada mata abinda zata min,
ta kalli farida tace wannan ce take saki a hanya,
zata kara magana ciwon jikinta ya mintsileta ta zaburah ta fara tsalle tana kokarin sosa jikinta, Afeeyah ta kalli farida tace kije ki kamota farida mu suturc— bata karasa magana ba sukaji karar bugun abu,
da sauri suka kalli gurin wata katuwar trailr ce tayi ciki da oyizah ta murje kanta,
da gudu suka isa gurin mutane har sun taru ana kallon oyizah amma babu wanda yayi yunkurin taba ta, wasu daga sun kalleta suke barin gurin,
sunfi karfin awa daya a gurin babu wanda ya taimakesu dakyar drivernsu ya dauketa aka nadeta cikin boot suka tafi da ita gida,

saida zeenatu tasa baki sannan alhj basheer ya kira akayi mata wanka aka suturce ta,
daga alhj bara’u sai alhj basheer sai malam atiku da masu aikin gidan kadai suka tafi kai oyizah gidan ta na gaskiya,
gidan da kafa bata fitowa,
gidan da ibadarka sune abokan hirarka,
gidan da kudi ko mulki bazasu hanaka kwanciya kan kasa ba,
gidan da babu fanka bare a.c babu iskar shaka sai in kayi aikin alkhairi,

Allah kasa mu cika da kyau da imani……
Ameen

Tunatarwa–
Ya yan uwana mata masu son mallakar namiji ta kowane hanya,
shin in mun mallakeshi muna tunanin in mun mutu wannan mallakar bazata hana namiji ya manta damu yaje ya nemi wata ya aura ba,
mallakar namiji itace biyayyarki in kikayi ma namiji biyayya tsakani da Allah wallahy kin gama mallakeshi duniya da lahira dan bazai taba mantawa dake ba,
akwai matan da suke wanke najasar gabansu su sawa namiji a abin ci ko sha,
wallhy,
wallhy,
duk macen da take wannan aikin in tazo mutuwa sai ta cisge gashin gabanta gaba daya da hannunta, shan najasa haramun ne,
cutarwa ne ga dan uwa musulmi,
in mallaka muke so to muyi koyi da matan manzon Allah s.a.w, akwai ayoyin saka soyayya a zuciya ko ita muka rike mun gama mallakar mazajenmu ba cuta ba cutarwa,
saboda saida soyayya mallaka ke tafiya,
Allah ya ganar da dukkan yan uwa musulmi baki daya, su kuma mazajenmu masu sa mu kauce hanya ta hanyar wulakanta mu Allah ka ganar dasu ka basu ikon kulawa da hakkokinmu Ameen thumma Ameen…

In shaa Allah gobe zan gama muku gaba daya,
kuyi mini afuwa na rashin posting da wuri

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:38] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣6⃣ By Aysha Ya’u kurah

Rayuwa mai cike da so, kauna, nishaďi, farin ciki, da annashuwa shi akeyi a gidan alhj basheer, rayuwar mai cike da koyarwar addinin islama,
Ni’imtacciyar rayuwa sukeyi wacce duk a da suka cire rai da samunta,
Alhj basheer yana matukar kula da kowa a cikin gidan, duk wasu hidimdimu nasu yana kokari wajen daukeshi ba tare da sun kai ga bukata ba,,
haka zeenatu kulawa sosai takeyi ma kowa har masu aikinta, bata bari kowa ya koka saboda matukar sanin darajar biladama,
Fareedah ma rayuwa takeyi me dadi wacce take ganin ashe da can baya ba rayuwa takeyi ba saboda tana zaune cikin duhun kai ga rashin samun nutsuwar zuci saboda rashin ibada da batayi, yanzu kuwa wani nishaďi take ciki musamman in ta idar da sallah sai ta dinga jin kamar iskar wannan lokacin daban take saboda yadda take ratsa ko ina na jikinta…

( tabbas iskar wannan lokacin kam daban take ga wanda ya hankalta,
duk wani musulmi da zaran ya idar da sallah to nasan a wannan lokacin zaiji kamar an sauke mishi wani nauyi akanshi kuma zai dinga jin yalwatacciyar iska mai dadin gaske,
kaii musulnci yayi, Allah ka sa duk ibadun mu karbabbu ne, Alhamdulillah ala ni’imatul islam)….

Soyayya da shakuwa su suka shiga tsakanin ma’auratan biyu, soyayya sosai suke gwadawa junansu haďe da mutuntawa, basa taba yarda su bata ran juna,
komai nasu suna yinshi cikin so da kulawa gwanin ban sha’awa,
Affan sam baya kaunar ganinta ita kaďai tana damuwa dan yasan damuwar akan jabeer ne,
wani lokacin ma in ya sameta tana kuka in ya bata hakuri sam bata yin shuru har sai ya dangana da zeenatu sannan dakyar zasu hadu su rarrasheta tayi shuru,
shima kuma duk ranar jumma’a sai ya kai ziyara kabarin amininshi bayan yasa an sauke qur’ani yayi sadaka sannan ya zauna a gurin ya dade yana mishi addu’a,
haka cikin dare in sun idar da sallah addu’a ta musamman suke mishi da sauran yanuwa musulmai wadanda suka rigamu gidan gaskiya…

Cikin ikon Allah cikin Afeeyah ya isa haihuwa yayi girma sosai dan ko mikewa bata iya yi in kuwa ta mike to sai tafi minti ďaya kafin ta iya daga kafarta,
rubutu da magunguna sosai take shansu dan kaka liman musamman yake mata jarkar rubutu tun cikinta na wata,
a wannan lokacin ne wani dare ta farka da nakuda mai zafin gaske,
cikin gaggawa suka kaita asibiti, likitoci sun fi karfin awa biyu akanta ana abu ďaya,
Affan kuka ya fita waje yakeyi saboda jin irin kukan azabar da takeyi,
ganin har lokacin ba improvement doctor ya yanke shawarar yi mata c.s saboda service dinta bai buďe ba,,
alhj basheer da kanshi yasa hannu saboda yadda yaga ta galabaita,
a gaggauce suka shiga da ita dakin theater suka fara aikinsu cikin kwarewa,

cikin farin ciki doctr ya fito musu da jarirai mata manya manya guda biyu,
da sauri zeenatu ta mike ta karbi ďaya alhj basheer ya karbi daya sunata ma doctor godiya,
Affan kuwa bai bi takansu ba dakin da aka kai Afeeyah ya shiga ya zauna gefenta yana shafa kanta yana mata addu’a yana jin sonta na kara ratsa ko ina jikinshi…

Kwananta hudu a asibiti aka sallameta suka koma gida aka cigaba da kula da ita da yaran dan jikinta har lokacin baiyi kwari ba,,
Ranar suna yara suka Amsa sunan Asma’u (Nuwairah) da Zeenatu (Nawwarah),
anyi shagalin suna cikin kwanciyar hankali dangi kowa ya halarci sunan harda su suwaiba da akayi nadamar gaske…

Mrs tijjani shattima….
[15/12 09:38] Anty aisha ya’u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣7⃣ By Aysha Ya’u Kurah

★ 7yrs ltr ★

Tsaye take a kofar islamiyya tana jiran fitowar yara su tafi gida,
tana tsaye jikin motarta da ďan cikinta na wata hudu tana siyan tsamiyar biri,
ihun fitowar yara ne yasa tayi saurin mika ma mutumin kuďi ta bare daya tasa a bakinta ta fara hangen yara,
can ta hango rabon faďa cikin taron yara malaman na rabawa yaron na kara tusa kanshi yana kuka yana fadin shi sai ya rama,
da sauri Afeeyah ta jefa ledar hannunta cikin mota tayi gurin yaron tana faďin Oh my Word JABEER again,
ta kamo hannunshi da karfi tace wuce mu tafi, ya tsala ihu yana magana cikin kuka ta make bakin tace rufe min baki masifaffe kawai,
ta kalli Nawwara dake kwaso mishi takalmi tace kuna tsaye ku bazaku iya kamo hannunshi ku fito ba kun tsaya kuna kallonshi yana fada,
Nuwaira tace wallhy mummy mun hanashi yaki har haurin Nawwara yayi,
tsaki tayi ta bude motar ta wurgashi baya su Nuwaira suka shiga ta ja motar ta wuce tana masifa shi ko sai tsala ihu yakeyi,
shop rite ta wuce dasu tayi siyayyarta ta sai musu ice cream suka fito suka wuce gurin mota,
tana buďe motarta taji ihun wani yaro cikin motar kusa dasu,
da sauri ta rufe kofar ta nufi gurin taga jabeer tsaye yana huci, cikin bacin rai tace me yayi maka ka dukeshi, jabeer ya turo baki cikin maganarshi ta yara yace tun da muka shigo yake kallona,
Afeeyah ta dauke keyarshi da mari tace uban me zai kalla a jikinka,
dan kaga bana dukanka shiyasa kake iskanci san ranka ko,
ta ja hannunshi yana ihu ta turashi cikin mota ta koma ta rarrashi yaron taja mota suka wuce gida,
a bakin gate suka tarar da Affan,
tun kafin a bude gate din jabeer ya balle motar ya fito ya ruga gurin shi yana kuka ice cream din hannunshi duk ya zube a kasa,
kwace robar yayi ya wurgar ya dagashi sama yace waye ya taba min kai,
jabeer yace ba mummy bace tun a islamiyya take dukana har mukaje chopurite tana dukana tana zagina suna ta min dariya,
Affan ya hade rai kamar gaske yace tun a islamiyya take dukanka har a chopurite,
jabeer ya gyada kanshi,
Affan yayi kwafa yace muje gidan yau sai ran kowa ya baci,
suna shiga ya tarar da ita a kitchen tare da Amirah ya kalleta yace me babyna yayi miki kika dukeshi,
Afeeyah tayi tsaki tace nidai dan Allah gobe ka siyo min rago wallhy canjin suna za’ayi wannan ba jabeer bane,
jarabar tayi yawa, kullum sai yaro yayi dambe a islamiyya,
sai shegen tsaurin ido ko kallonshi akayi sai ya daki yaro in yafi karfinshi,
Amirah tayi dariya ta dungure kanshi tace gaskiya yaya Affan ka siyo mana ragon suna wannan bai amsa sunanshi ba,
jabeer ya kai ma Amirah duka yana kuka Affan yace har da ke ko Amirah,
to zanga mai canza mishi suna,
ya kalli Afeeyah yace ke meye bakiyi ba, tace naji nayi amma bankai wannan mai katon kan ba,
kuma canza suna ya zama dole in na haifi salihi sai insa mishi jabeer amma wannan JAZULI zan sa mishi,
Amirah dasu Nawwara suka fita suna dariya sosai,
Affan ya share ma jabeer hawaye yace rabu dasu yanzun nan zamu fita yawo ko mutum daya bazai bimu ba,
jabeer ya shanye kukanshi yana ma Afeeyah gwalo, tsaki tayi ta cigaba da abinda takeyi tana mita….

Washe gari da safe suna zaune suna shan tea,
kowanne jikinshi da skool uniform gwanin ban sha’awa,
jabeer na zaune yana shan tean shi yana daukar bread baya ko kallon su Nuwaira,
kallonshi sukeyi suna dariya dan yaci slize bread fin shida kuma ya cinye kwan gabanshi,
yana jin dariyar da sukeyi kasa2 bai tanka musu ba,
yana gamawa ya mike yana mika ya zagayo gefen da suke ya ďauki kofin tean Nawwara ya kwara musu a jiki ya dauke kwan plate dinta ya ruga cikin daki da gudu yana dariya,
mikewa sukayi baki bude ga zafin tea ga haushin yasa sai sun canza kaya,
Nuwaira da idonta ya ciko da kwalla tace wallhy sai na ma yaron nan dukan tsiya, Nawwara tace ki kyaleshi sai munje skool,
Nuwaira tace wallhy a gida zai daku ji yadda ya bata min jiki,
cikin fushi tayi hanyar dakin ta murďa kofar, wayar av din jikin game ta cire ta fara tsuga mishi,
nan ya dinga ihu yana shigewa jikinta Nawwara ta fincikoshi tana dukanshi da hannu yana ihu yana ramawa,
a gigice Afeeyah ta diro a gado ta fito tana kiran me aikinta taji ko lafiya,
kafin ta kai ga shiga dakin Affan dake parlor yana jiransu har ya shige yana ta ma su Nuwaira masifa,
cikin fushi Afeeyah ta kwace wayar hannunta tace dukanshi kukayi har da waya,
Nuwaira ta fara kuka tace mummy ruwan zafin tea fa ya watsa mana a jikinmu kalli kayanmu,
Affan yace me kuka mishi ya watsa muku nasan haka kawai bazai watsa muku ba, Nawwara tace wallhy babu abinda muka mishi,
jabeer yayi saurin cewa karya takeyi dariya suke ta min,
Afeeyah ta kalleshi a hassale tasa hannu zata janyoshi ya sa ihu ya shige bayan Affan yana fadin wayyo mummy kiyi hakuri, Afeeyah ta rike kanta tace wallahy yaron nan zai iya haukatar da mutum,
na kusa daukar ka in mayar dakai bolar da na tsinto ka kaje can cikin yanuwanka spiders, coacroach da sauransu,
jabeer ya leko yace wai haka daddy,
Affan ya daukeshi suka fita yace eh mana tunda baka jin magana,
Afeeyah ta kalli su Nuwaira tace tsayuwar me kuma kukeyi,
ko inzo in shiryaku ne, sukayi saurin fita daga dakin suka je suka canza kaya suka wuce skool…

Bayan yan kwanaki, Afeeyah na zaune ta mike kafarta tana tsinkar ayayo, yara kuma na gefenta suna wasa,
jabeer kuwa yana zaune yana shan cornflakes yana kallon cartoon,
Amirah ce ta shigo gidan tana ma jabeer wakar tsokana, hararrta yayi ya cigaba da kallonshi,
kanshi ta taba tace su jazuli ba tayi,
ya buge hannunta ya turo baki yace kece jazuli,
Amirah tayi dariya ta zauna kusa da Afeeyah ta dauki sandar ayayo daya tace har yanzu su umma basu dawo ba,
Afeeyah tace kedai bari ina missing dinsu wallhy ko dan wancan dargozon,
Amirah tayi dariya tace ummi ce ta aikoni tace ki tambayi yaya Affan gobe zanje kaduna wai su Nawwara su shirya mu tafi tare,
Afeeyah tace to ba matsala amma banda jabeer ko,
Amirah tace wake gaba in ba shi ba, kin san anty asiya in bamuje dashi ba sai munsha query, Afeeyah tace wallhy masifarshi ce bana so, gashi in sun hadu da irfan dinta suyi ta fada kamar jakai,
Amirah tace ay duk daya suke mugun rashin jin tsiya,
Afeeyah tace ay inaga ke zamu hadawa kuje can ku karata ke da angon ki,
Amirah ta rike baki tace akai singa market, ta ina zan fara dasu,
Afeeyah tayi dariya tace hanyoyi da dama, Amirah ta mike takai ayayo kitchen tace bada ni ba sa lallen hen,
Afeeyah tayi dariya ta mike ta bita kitchen…

Karfe 12 na rana driver ya kwashesu suka tafi kaduna,
dawowa ciki Afeeyah tayi tace yau zan huta da fitina,
dakinta ta wuce ta kwanta tayi bacci,
karfe biyu da kwata ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta fara gyare gyaren gidan kafin mai gidan ya dawo,

Karfe 6 suka gama komai ita da mai aikinta,
ta wuce tayi wanka tayi sallah ta shirya cikin free gown mai shegen kyau,
parlor ta dawo ta zauna ta canza tashar zee world ana sacred ties, nan tayi paying attention saboda tana matukar son film din,

a hankali ya shigo gidan bata san ya shigo ba,
ta baya ya tsaya ya ziro macijin roba ta saitin kafarta yana mata waiwayi,
a gigice ta kalli kasa, wani irin tsalle ta daka hade da ihu tana fadin na shiga uku na lallace wayyo hajja, wayyo kuzo ku taimakeni, rungumeta yayi ta baya yana dariya sosai yace matsoraciya kawai,
ďanewa tayi kan jikinshi ta kankameshi tana faďin maciji, wallhy maciji na gani,
dariya sosai yakeyi ya sa macijin a saitin kunnenta,
wani ihun ta kara sawa tayi saurin turashi baya cikin masifa tace wannan ay mugunta ne,
kasan inada larura kuma kake tsorata ni, yanzu fisabillilahi da karamin ciki ne na haka zakayi min,
wurgo mata macijin yayi ta goce ta dauko shi ta fara buga mishi tana masifa,
chakk ya ďauketa yana dariya yace am sorry sweety,
tasa baki a kunnenshi ta cijeshi da karfi yayi saurin direta yana ihu,
daki ta gudu tana dariya sosai tace gobe ma ka kara,
bin ta yayi yana dariya yace wallhy sai na rama yau sai jikinki ya faďa mishi,
zaki san kin cijeni,
da sauri tasa ma kofar key tana dariya tana faďin sai dai ka rame a nan,
yayi dariya yace zaki ga rama zaki fito ki sameni ya wuce ďakinshi…
Haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya cikin farin ciki,
Afeeyah ta kara haihuwar ďa namiji wanda yaci sunan Basheer, abba suke ce mishi,
yanxu haka tana final year ďinta a “international relationship” dan tana matukar kaunar course ďin..

To ALHAMDULILLAH, Nan zan tsaya da wannan kagaggen labarin nawa,
Godiya ta musamman ga Allah s.w.t da ya bani ikon farawa kuma na gamashi ba tare da na gaza ba,
alkhairin da muka fada ciki Allah ka bamu ladanshi, sharrin dake ciki ya Allah ka yafe mana..

Allah ya kara muku tsawon kwana mahaifana waďanda sukayi sanadiyyar zuwana duniya, Allah yayi muku sakamako da gidan aljanna firdausi,,,

Allah ya barmu tare mijina, ya kauda duk wata fitinar dake cikin auren mu, Allah ya raya mana zuri’armu kan tafarkin Addinin musulunci,,,

Jinjina ga kungiya mai albarka.
HANNU DA YAWA WRITERS,
Allah ya kara haďa kanmu ya kauda fitina a tsakaninmu…

Godiyah ta musamman gareku yan fcbk nagode sosai da soyayyarku gareni, …
Aysha kurah novels…
Khaleesat haydar novels…
deeja abdul novels….
Mu sha karatu….
Dama sauransu….

Banda kamarku… kawata ta da da yanzu 😀 Badiyya Aliyu umar,
Namcy Dangusau, $
Aneesah Abdulsalam….

Godiya ta musamman gareku yan uwana masoyana yan “world of Hausa novels 1 nd 2,” bansan wanda zan tsame in kira sunanshi a ciki ba MAXXY, NI’MA NAKOWA, NABAYI, BIEBEE, SADEE, NAMSY MISAU, HASKE, ASMEE YA’U, SOFTIE, DEEBOX ku fito ku tayani lissafo sunansu,,, thanks for ur support dearies Allah ya barmu tare…

jinjina gareku yan uwana yan group ďin Ruffy na classic ladies novels nd ROF novels, Allah ya barmu tare ameen,

Godiya gareku..

Yan group din kawalli ummu abdool, Taskiraa.. ku ma Allah ya barmu tare,

Hausa novel group na sheedat..
Hausa novel group na Raff…
Zauren karatu…
Feenat jaafar novels…
Excellent writers…
Wisdom writers…
Perfect writers…
M jabo novels…
Only hausa novels….
Fasahar marubuta….
Matan kwarai….
Hausa novels na Pherty….
Hausa Novels na chuchu Ammani….
Zarah bb novels….
Meesha love novels….
Fillin takarddun hausa….
Khadija candy novels…..
Taskar ya’ya mata….
Sahaf’s novel …
Best hausa writers….
Kamshi novels…..
Haima fans….
Autar hajiya novels….

Da duk sauran groups ďin da ban anbata ba kuna raina Allah ya bar mu tare cikin Aminci da kaunar juna..

Ga masu bukatar littafai na, kuyi searching blog ďina ayshakurah.mywapblog.com ko kuma facbuk group dina Aysha kurah novels

Mrs tijjani shattima kema dukkan masoyanta fatan alkhairi Allah ka hada fuskokinmu a cikin aljanna firdausi…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button