Gyaran Jiki

YADDA AKE HADA HUMRA FARA, BAKA, TURAREN WUTA , NA KAYA, DANA TSUGUNNO

♜ YADDA AKE HADA HUMRA FARA, BAKA, TURAREN WUTA , NA KAYA, DANA TSUGUNNO ♜

✎yar’uwana Mata inayi muku tuni da Ku rike turare da kyau, don turare maganadisu ne na Jan hankali, amfanin da turare a jikinki, sutturar ki, gidanki yana sa maigida ya Fara samun natsuwa zama dake, ya Saki jiki dake, kuma ko yaushe zai dinga son kasancewa dake…

 

         ⁍ BAKAR HUMRA

⇢mahala.
⇢hawi.
⇢farce.
⇢turaren marakana.
⇢turaren sandol na ruwa Dan awo.
� turaren amarya.
⇢madarar turare aba rai dadi.
⇢madarar turare Sudan.
⇢turare me sanyi ruwa kalar da kike so Mara maiko.

✎yadda Zaki dake mahala dinki, bayan kin soya sama-sama sai ki dake ta tayi taushi, shima hawi ki dake ki tankade, ki jika farceki a ruwan omo ko clean, idan yayi kamar awa biyu da jikawa, sai ki Dora farce da kika jika da ruwan clean yayi ta dahuwa, har sai yayi kamar awa biyu ko uku ruwan na tafasa da farceki a ciki, sannan ki sauke ya huce, sai ki samu reza ko brush din goge baki ki dinga kankare farce da rezar daya bayan daya, wanna nama-naman da ya taso na jikin farcen sai ya fita gaba daya, idan kin gama kankarewa sai ki shanya farcen ya huce, sannan ki zuba farcen a kasko ki yi ta juyawa a kan wuta har sai farcen ya kone yayi baki, sannan ki dake yayi laushi sosai.

 

Yadda Zaki hadashi shine ki zuba ruwan turarenki na marakana kwaiba daya ta awon man kuli, sannan ki zuba turare sandol na ruwa gwangwanin madara ruwa guda daya, turare amarya, ma gwangwanin daya, turare me sanyi ruwa Mara maiko kalar da kike so gwangwanin daya, kisa madara turare aba rai dadi cikin kwalbar fiya-fiya, ki sa garin mahala cokali biyu na abinci garin hawi cokali biyu, garin farcen ma cokali biyu, ki juya sosai , bayan ki gama hadawa sai ki rufe humrar ki barta ta tsumu a gun Mai zafi ko ki Dora Kaya a kanta Inda ba zata sha iska ba har zuwa sati daya ko biyu ko sama Inda ta tsumu sosai tayi kamshi.

 

Zaki iya yin humra da ruwan turare amarya wato ya fi yawa turare marakana kuwa sai ki sa gwangwanin daya yadda dai kike so, wannan dakakken su farcen Zaki ga in kin zuba kwalba suna yin kasa,Amma zai saka humra ta dinga Kara tsumu wa tana Kara kamshi.

♜ GIDAN KAMSHI SIRRIN ZAMA DA MIJINKI ♜

 

⁌⁍ FARAN HUMRA ⁌⁍

▻ ruwan turare amarya.
▻jawul fari.
▻hawi.
▻ambur.
▻madarar turare jadun.
▻madara turare Jamila.
▻madara turaren aba rai dadi.
▻madara turare sabon yayi.
▻madara turare kafin kafi.
▻madara turare matan arewa.

ki samu turare amarya roba daya, ki daka Ambur fari da ja guda uku-uku ki zuba a ciki ki daka hawi ki zuba cokali biyu a ciki, ki narka misk guda hudu ki zuba a ciki, ki daka jawul kisa cokali daya, ki zuba garin dakakken misk dinki cokali biyu, ki zuba madara turare ciki kwalbar fiya-fiya dai-dai ki barshi ya tsumu kwana goma zuwa sati biyu shima wanna garin su misk din ne zai dinga Kara masa kamshi.

❖ TURAREN WUTA NA DAKI

 

⇝farce.
⇝sukari.
⇝lemon tsami.
⇝jawur fari.
⇝misik.
⇝garin sandol.
⇝madara turare Jamila.
⇝” “wanis.
⇝” ” sabon yayi.
⇝” ” Binta Sudan.
⇝” ” kamfani.
⇝” ” naludu.
⇝” ” Dan duwala.
⇝ ” ” kafin kafi.
⇝” ” aba rai dadi.
⇝turaren ruwa Mai maiko.

” ” ma’ana madara turare

Yadda Zaki yi ki samu itacen al’ud dinki kilo daya, ko biyu, sai ki jika shi a madara turare Jamila da madarar turare wanis,da madara turare sabon yayi , sannan ki sa turarenki mai maiko na ruwa irin Wanda ake aunawa, a dogwayen kwalabe sai ki jika da wadannan turaruka ki rufe ki barshi ya jiku har yayi kwana bakwal, bayan sati daya sai ki bude itacen al’ud din da kika jika da turare, idan al’ud din kilo biyu ne sai ki sa gwangwanin daya, idan kuma kilo daya ne sai ki sa gwangwanin daya, idan sukarin gwangwanin biyu ne sai ki sa gwangwanin daya, idan sukarin gwangwanin biyu ne sai ki zuba ruwa cikin karamin roba, ki matsa lemon tsami, hudu a Kai, ruwan sukari sugar, idan kuma gwangwanin daya ne sai ki zuba ruwa Rabin karamin Kofi, ki matsa lemon tsami biyu a Kai, sannan ki saka garin jawur cokali daya, da ruwan lemon tsami, sukarin kisa miski kwaya uku a ciki, sannan ki Debi garin farce, da kika barza ki zuba, kadan a Kai, Amma shima farcen Zaki gyara shi kamar irin gyaran da akace za’ayi masa a hadin humra, Sai dai shi banyan an soye barje shi ake ba daka shi akeyi ba, idan kin zuba sai ki barshi yayi ta dahuwa har sai ruwan sukarin ya Fara ja, sannan ki zuba garin sandol dinki, a Kai da garin dakakken miski , da garin dakakken jawul, da barzajjen farcen duk ki zuba a Kai, ki juya sosai, sannan ki zuba madara turare Binta Sudan, da madara turare Dan duwala, da madara turare kafin kafi, da madara turare sandol, da madara turare aba rai dadi, ki zuba a kan turare al’ud din da kika baza a faranti, madara Zaki Iya yadda kike so sannan ki juya sosai, sai ki zuba a kwalabe a kwaiba ma Zaki kuma zuzzuba madara turare a Kai.

TURAREN JIKI NA KAYA

itacen hawi da inik.

yar’sirara ne kamar saiwa, Amma wasu suna da kauri, dukkan kayan hadin turare al’ud da shi Zaki yi amfani kamar yadda aka yi turare wuta na al’ud haka Zaki yi , sai dai Zaki Iya canja kalolin madarorin turare da kike so Zaki dinga turara jikinki da shi da kayan sawarki.

[email protected]
[email protected]
✣+2348037538596

 TURAREN GAF-GAF NA TSUGUNNO 

↦itacen gaf-gaf.
↦sukari.
↦jawur.
↦lemon tsami.
↦misik.
↦farce.
↦hawi.
↦garin sandol.
↦madara turare zuzan.
↦madarar turare sondol rose.
↦madara turare Binta Sudan.
↦madara turare sondol
↦garin sondol.
↦madara turaren mena.

Kamar yadda Zaki yi turare al’ud irin Wanda na koya yanzu zakiyi, sai dai shi farcen bayan kin gyara kin kona daka shi Zaki yayi laushi. Shi kuma itacen gaf-gaf din idan kika siyo Zaki ganshi kamar kashi, sai ki jika kin wanke, sannan ki baza ya bushe,sannan ki farfasa a turmi, sannan kiyi kamar yin turare al’ud Zaki dinga turare gabanki, dashi Ana turare jiki Amma gollon da hawi shika dakawa Zaki yayi gari, ki zuba wani a gun soya ruwan sukarin ki juya wani banyan kin gama kamar dai al’ud…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button