Gyaran Jiki

Matakai 3 Domin Magance Ciwon Sanyi Maza da Mata Har’abada

MATAKAI GUDA UKU DOMIN MAGANIN CIWON SANYI INFECTION GA MATA DA MAZA

 

Ganin yadda cutar take da wahalar Magani Yasa Na Ce barin Baku hanyar da zaku bi Ku rabu da Ita gabadaya inshaa Allahu.

 

1. A nemi wadannan abubuwa kamar haka:

1-Khurunjal

2-Dammul-akhawaan

3-Qudnuful

4-Zanjabil

5-Ful-ful

6-ikhlilul-jabal

7-Daqiqul-Thawm

8-Habbatussaudah

9-Habbaturrashad

10-Hulbah

11-Na’ah-Na’a

12-Asalin furen Albabunaj

13-Asalin itacen sazabu

14-Asalin Ganyen zaytun

15-“Ya”Yan majamfari sai a soya Su a dake Su Su zama gari.

 

Wadannan abubuwa da Na lissafo ana son a dake Su gabadaya Su zama gari sosai sai a dinga diban tea spoon ana zubawa a Ruwa karamin cup Daya sai a dafa in ya tafasa sai a sauke a Sa Zuma daidai gwargwadon yadda zakin Zai fito yadda za a Ji dadin sha kaman shayisafe da yamma, in kuma yayi Tsanani a jikin mutum toh ya dinga sha sau Uku a kowacce rana, ana son a kai tsawon sati Biyu a Jere ne ana sha, inshaaAllahu Zai kashe Na cikin yadda ya kamata.

 

MATAKI NA BIYU DON MAGANCE CIWON SANYI (INFECTION) WANDA YA ADDABI CIKIN FARJI GA MATA

 

A nemi wadannan abubuwa kamar haka:

 

Ganyen lalle Wanda bai zama gari sosai Ba

Yayan hulbah

Kwallayen tafarnuwa

Kaninfari

Ganyen magarya

Ganyen zaytun Na Asalin

Sai a hadasu GU Daya a dinga diba cikin Babban chokalin cin shinkafa biyu, Ruwa liter Biyu sai a dafa ya tafasa sai a juye a baho, in ya Dan huce yadda bazai cutar da ke Ba sai ki nemi ruwan khal tiffa, ba kowanne irin khal ake so ba, asalin khal tuffah me hoton Appke shi xaki nema, sai ki zuba chokali takwas a cikin ruwan, sannan sai ki cire wando ki shiga Ciki ki zauna tsawon mintuna 10 kina Ciki kuma ki wanke yatsanki ki dinga wanko ciki da ruwan maganin,

amma in ke budurwa ce kar ki sa yatsa, kuma ki tabbatar kin aske Gashin Gaba Sbd ruwan Maganin ya samu damar ratsa pussy Ciki da waje sosai, Bayan kin fito sai ki nemi muski me Kyau da man zaytun me Kyau ki dangwala da auduga sai ki Yi matsi da shi, Bayan kaman awa Uku sai ki cire audugar, sannan Bayan awa Biyu da cire Audugar kina iya kara dafa wannan Maganin ki kara shiga ki kuma yin matsin again, son samu ki dinga yin wannan sit-birth din sau Uku ko Biyu a kowacce rana, inshaaAllahu dukkan matsalolin da infection ya Sa miki a farji misali kaman tsagewar farji ko kuraje, ko wari, ko zubar Farin Ruwa inshaaAllahu duk Zaki rabu da Su cikin ikon Allah, kuma Zaki Ji gun yayi Dadi kuma ya zama daidai Ba Matsalar komi.

 

In kuma Namiji ne shi Ba sit-birth Zai dinga Yi Ba, shi kawai ana son ya Hada Na sha din kuma Yana Yawan tsarki da ruwan Zafi sau Biyu a rana.

MATAKAN DA YA KAMATA A DAUKA DON KIYAYEWA KAR A KAMUWA DA CUTAR

 

1. Idan Ku ma’aurata ne ana son Ku dakata da yin jima’i har sai kun gama Maganin tsawon sati Biyu a jere.

2. Idan kina da Miji to dole tare zaku sha Maganin

3. In kina da Kishiyoyi Dole Ku sha Magani tare

4. Gyara bandaki da barbada Gishiri a cikinsa lokacin da za a wanke shi.

 

5. Ki wanke pant Dinki da ruwan Gishiri Bayan kin wanke da omo ko sabulu sai ki jika ruwan Gishiri da ruwan Zafi ki tsoma duka pant Dinki a ciki su kai mintuna goma sai ki cire ki shanya su a rana, in da hali kuma kawai ki Sayi sabbi ki watsar da wadanchan.

6.kiyaye shiga toilet din da kowa da kowa ke Iya shiga ya Biya bukatarsa musamman a Gidan biki ko Kasuwa (Public toilet).

7. Yawan tsarki da ruwan Zafi akai-akai.

InshaaAllahu idai am Yi amfani da wannan hanyoyi za a rabu da Ciwon Sanyi infection kwata-kwata da yardar Allah

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button