Gyaran Jiki

Maganin Karfin Maza na Gargajiya

MAGUNGUNA KARFIN GABA DAGA ITATUWA MUNA GIDA

 

Kamar yadda mu ka ambata tun da farko duk mai fama da daya ko wasu daga matsalolin can da mu ka zana a sama magance su shine warakarsa da ikon Allah. Duk da haka Hausawa kan ce, idan kana da kyau ka kara da wanka bayan magance kalubalen lafiya da ake fama da ita/su za a iya amfani da wadannan hade-hade da zamu zana a kasa.

 

 

Hakanan, ko da mutum ba ya fama da daya daga cikin wadancan matsaloli, masana na ba da shwarar yawaita motsa jiki da kuma lura da nau’in abincin da ake ci. Domin samun cikakken bayani karanta makalarmu mai kanun “Nau’ikan Abinci Ma Su Karawa Namiji Sha’awa Da Kuzari Yayin Jima’i” Da kuma “Nau’ikan Abinci Ma Su ragewa Ma’aurata Sha’awa Yayin Jima’i” za su taimaka ma ka kwarai gaya.

 

 

Hakika Allah Madaukakin sarki Y halicci gangar jikinmu daban-daban, sakamakon haka ya sa, maganin karin kuzarin namiji da sauran magunguna, su kan bambanta ne daga wani mutumin zuwa wani. Ba lallai ne maganin da wani ya sha ya yi ma sa aiki, kuma wani mutum ya sha ya dace ba. Wannan dalilin ya sa mu ka ga dacewar kawo nau’i daban-daban, idan ka gwada ba ka dace ba, za ka iya dacewa a wani.

 

 

1. Dabino; Yadda ake amfani da shi, shine, ka samu dabinonka mai kyau guda 13 ko 15 sai ka wanke, ka zuba a mazubi mai tsafta sai ka zuba ruwa ya sha kansa, ka bar shi tsawon awa uku sannan ka cinye. Idan da hali ayi safe da yamma, amma idan ba hali sai aci da yamma kadai.

Sai dai ba a son aci wannan hadi da zarar an kammala cin abinci, idan son samu ne ana son aci lokacin da ake jin yunwa, sai a jira mintuna 20 zuwa 30 kafin aci wani abinci.

 

2. Kwai; Za a samu kwan kaza guda 2, babban cokali 1 na garin habbatus sauda, sai a cakuda su sosai sannan a soya sama-sama kar ya kone, sannan a cinye.

 

 

3. KANKANA ; Kankana na kunshe da wasu sinadarai dake aiki kwatankwacin maganin karfin maza na zamani da ake kira ‘Viagra’ a turance. Don haka tana kara karfin maza sosai.

Don a samu amfaninta sosai za a sha mintuna 30 kafin fara jima’i.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button