Hausa Novels

Bintu Diyar Bayi Ce Hausa Novel

Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 1

WAIWAYE
Daga cikin Masallaci aka fara abinda ya had’a jama’a a
wannan masarauta, wato d’aurin aure, in da aka umarci
waliyin Ango da Amarya su matso kusa. Waziri ne ya fito daga
6angaran Sa’ayrasa, Fabarusa kuma Sarki Abdulrahaman ne
ya nuna kan sa a matsayin waliyi.
Daga waje Khalil ne ke ta yiwa Yarima Barde hira, amma shi
ina hankalinsa na ga Gimbiya K’amariyya, Allah Allah ya ke a
shafa fatiha ya tafi garera don jin soyayyar ta ya ke har ransa,
bare kuma yau gabar da ke tsakanin Masarautasu za ta kau, za
su yi soyayyarsu a zahirance ba tare da wani shakku ba. Jin an
shafa fatiha Yarima Barde ya tashi ya na mai fad’in.
‘’Alhamdulillah tunda an amra sai ku tashi mu tafi ko?’’
Har Khalil da Jafar sun tashi, tuni su ka tsaya cak jin marok’a
na fad’in
‘’An d’aura auren *Yarima Abubakar BARDE* tare da *Gimbiya
Fatima* akan sadaki (50000 CFA)”
Yarima Barde da sam bai lura da abinda su ka ji ba tsabagen
hankalinsa ba ya wajan, a hasale ya kai kallonsa ga
abokannasa ya na mai fad’in
‘’Me ku ke jira ne? Mu tafi, Allah Allah na ke na gana da
Gimbiyata.’’
Su kuwa marok’a ba su fasa shela ba. Khalil ne yayi k’arfin hali

Related Articles

 

ya ce
‘’Da ma kai ne Barde?’’
Cikin rashin fahimta Barde ya ce
‘’Ni ne wa?’’
‘’Angon da aka amrawa amren.’’
Jafar ya bashi amsa a tak’aice. Kai Yarima Barde ya girgiza
cike da murmushin irin ban son rainin hankali fa. Khalil ya ce
‘’Saurara ka ji Barde’’
Nan kuwa muryar wani marok’i da ya zo giftawa ta dafda su ya
doki kunnan Barde, fad’i ya ke
‘’An amra auren Yarima Abubakar Barde da Gimbiya Fatima….’’
Nan ya ya tsaya cak tamkar wanda aka zarewa rai, su kansu
abokannasa sun girgiza kwaran gaske.
Daga cikin masallaci, ana gama d’aurin auren, inda kowa ya ke
mamakin sauyin al’amura da aka samu, musammam jama’ar
Sa’ayrasa, shi kuwa Aisar tunanin hanyar fita daga cikin jama’a
yake, domin zuwa neman Bintu ba tare da Junaidu ya ankare
ba. Bayin Sa’ayrasa ne d’auke da farantin goro da alawa, su ke
bin kusirwa kusirwa in da suke mik’a farin tin jama’a na d’iba
san ran su.
Bawan da ya zo kusurwar da su Aisar su ke, Aisar ya fara
mik’awa, in da ya girgiza masa kai alamar ba ya buk’ata, har
bawan zai wuce, nan idanun Aisar su ka sauka bisa yatsun
bawan, me zai gani? Zobensa da ya bawa Bintu ne cikin
yatsun na shi, bai ankara ba sai ji yayi Aisar ya damk’o
hannunshi, a tsorace bawa ya saki farantin hannun sa dan ko
shakka babu ya san tawagar shugaban k’asa ne
gabansa.Hakan ya dawo da hankalinsu Junaidu da sauran ‘yan
tawagar garesu.

 

Aisar na mai duban idanun bawan ya furta
‘’Ina ka sami wagga zo6en? Menene dangantakarka da mai
zo6en? Ina Bintu d’iyar bayi?’’
Babban gida kuwa 6angaran Jakadiya, Bintu na zaune tare da
su Jakadiya sai ga Gimbiya K’amariyya ta shigo, ta yi kyau
kwarai cikin jajayen kaya, ta d’aura alkyabba ruwan zuma bisa
kayan, ga bayi nan biye da ita. Ta zo kar6ar mabudin wajan aje
baki na musammam domin kar6ar Yarima Barde.
Ta na zaune ta na jiran Jakadiya ta shiga ciki dan d’auko mata
mabud’in, su ka ji an shigo 6angaren Jakadiya an gud’a. Tuni
hanjin cikin Bintu ya kad’a don kuwa ta san ta faru ta k’are an
yiwa mai dami d’aya sata, aure dai an aura. Tuni ta fashe da
kukan da dama ya tsaya k’asan mak’ogaran ta.
Jakadiya ta fito d’auke da mabud’i, yayinda Ladiyo ta shigo jiki
na rawa, sai tafa hannu ta ke cikin salati da sallallami.
Jakadiya ce ta tambaya ko lafiya, yayin da hankalin kowa ya
koma gareta.
Cike da ladabi Ladiyo ta durk’usa gaban Jakadiya ta na mai
fad’in
‘’Yau na ga lafiyar Allah Maigari gauro talaka da mata hud’u.’’
Cikin k’aguwa Gimbiya K’amariyya ta ce
‘’Me ya faru ne Ladiyo?’’
‘’Wato Allah shi taimaki Gimbiya, ji da gani dai ba ya k’arewa
sai randa kurman bebe ya makance, Sarki Abdulraman na
Fabarusa cike ya ke da abin mamaki, wani lamari sai shi…..’’

 

‘’Yo to wani abin mamaki? Ya ce ya fasa ne?’’
Jakadiya ta tambaya cikin rashin fahimta. Kana Ladiyo ta ce
‘’Eh to ya fa fasa be kuma fasa ba, da ya tashi yin bazata, sai
ya amrawa d’ansa Barde Bintu…..’’
Hakan yayi daidai da ihun da Gimbiya K’amariyya ta kurma ta
na mai zubewa k’asa sumammiya. Nan da nan aka yi kanta.
Bintu kuwa yanda maganar ya doki kunnenta ta tabbatar ta
zama kurma, don kuwa ba ta jin hayaniyar da ake gabanta
‘’Ya amra ma d’an sa Barde Bintu….’’
Maganar da ke ihu jikin kunnenta kenan.
1⃣
Tuni waje ya kaure da salati da salallamin bayi, Jakadiya ce ta
sa aka yi maza aka shigar da K’amariyya daga cikin d’aki
gudun gulman da ta san tabbas sai ta yad’u daga bakin bayin
da ke wajan. Bintu kuwa ta ma kasa gane komai, kukan ta
kawai ta ke, aure dai an d’aura mata, ko ta na so ko ba ta so
tafiya ne dole a tafi da ita. Gashi a rasa wanda za a d’aura
mata sai saurayin Gimbiya K’amariyya, Yerima Barde na
Fabarusa! Hannu biyu Bintu ta d’aura bisa kan ta ta na mai
fad’in
‘’Wayyo ni Bintu alk’iyama ta ta zo’’
Daga cik’in uwar d’aka, bayan an kori duka bayin da ke
b’angaran Jakadiya, Hajja Kilishi da Inna Salti wanda Jakadiya
ta aika Ladiyo da Kyallu su sheda ma su abun da ke faruwa ne
su ka shigo d’aya na bin bayan d’aya, biye da su Gimbiya Binta
ce, wacce ita ma labari tuni ya je mata.
Jakadiya ta umarci bayin da su ka taka mata baya su yi jiran
ta waje. Bayan an watsa ma Gimbiya K’amariyya ruwa, da
rokan Allah ta farfad’o ta na mai bin su da kallo kamar lokacin
ta fara ganin fuskokinsu. Kanta bisa kan cinyar Inna Salti,
Jakadiya zaune gaban ta sai kuma Gimbiya Binta wacce ta
dad’e da gigicewa da jin lamarin da ya faru, in ban da kuka
babu abinda ta ke don gani ta ke duk laifin Bintu ne ko shakka
babu ita da uwarta ne su ka sa musu hannu wannan balk’in ya
fad’a kan ‘yar uwarta.
Ko da idanun Gimbiya K’amariyya ya sauka kan Gimbiya Binta,
ita ma d’in ta fashe da kuka don sai a sannan ne ta dawo cikin
hayyacinta sosai. Cike da damuwa Hajja Kilishi ke tambayar
‘’Menene ne? Gide menene ke faruwa? Tun dazu fa nake
tambayar ki Binta amma amsa ta gagara daga gareki, yanzu
kuma mun samu ta farfad’o maimakon a sami sauki ina, kun
maishe da gida kamar wajan makoki! Shin ba kwa gudun
abinda zai je ya dawo? Kun fa san gidan ga cike yake da baki
da kyar na sami hitowa daga cikin jama’a, ko rufa mana asiri
ku sheda mana abun da ke faruwa.’’
Cikin kuka muryarta dak’yar ya ke fita, Gimbiya K’amariyya ta
amsawa Hajja Kilishi, ta na mai fad’in
‘’Na shiga uku Hajja, Inna Salti na shiga uku, na d’au wuk’a na
dab’a ma kaina, Allah Ya nuna min ikonSa, Barde…..Yarima
Barde na Fabarusa……’’
Kuka ya ci k’arfinta, ta kasa k’arasawa sai shasshek’a ta ke.
Cikin rashin fahimta Inna Salti ta ce
‘’Barde? Me ya faru da Barde na Fabarusa?’’
‘’Ni kam ta dad’a sa kai na cikin duhu, jakadiya wagga yarinya
ba gamo ta yi ba kuwa?’’
Cewar Hajja Kilishi cike da damuwa.
‘’Yarima Barde da Didi masoya ne, shi ne dalilin ta na k’in
amincewa ta auri sarkin Fabarusa wanda yake mahaifi a
gareshi.’’
Gimbiya Binta ce ta amsa ma su.
‘’Kayya! Kai wagga lamari da me yayi kama! Kun ga irin ta ko?
Gashi dai an cuci d’iyar mutane kin kuma cuci kanki
K’amariyya, anyi gudun gara an tadda zago! Jakadiya dai ga
irinta nan dai kin gani don kuwa wagga kulli ke da wagga d’iya
ku ka kulla.’’
Fad’in Inna Salti ta na mai nuna matuk’ar b’acin rai.
Jakadiya da tunda aka fara maganar ta sha jinin jikin ta, jikinta
ya yi sanyi kamar wacca aka tsunduma cikin ruwan sanyi
cewa ta yi
‘’Uhum Allah shi ja da ran ki, yo to ni me zance? Ni ina naga ta
ce wa? ‘’
Cikin kuka don kuwa idanunta sun rufe K’amariyya ta furta
‘’Don Allah ku taimaka a warware wanga lamari, don Mai
Sama, kwarankwatsa zan iya rasa rayuwata, dan Allah ayi
maza a shedawa takawa kafin na rasa raina, Ammu ki taimaka
min…..’’
Kai Hajja Kilishi ta jinjina kafin ta ce
‘’Gide Takawa zai saurari wanga azzance kuwa Jakadiya?
Yanzun ga ya na can wajan liyafar d’aurin amren nan……’’
Kafin Jakadiya ta amsa Gimbiya Binta ta yi saurin taran
numfashin ta ta hanyar fad’in
‘’Ku taimaka tun kafin a makara, dan kuwa ba Sidi ba ko ni ma
ina tara muddin ba a warware wanga
amre ba, ya d’iyar bayi za ta amri mutum kamar Barde, dan
Allah Jakadiya ki sama mana mafita tun kan na had’iyi zuciya
na mutu dan kuwa ciwon da na ke ji ya ma fi na Didi’’
‘’Makara kam an riga an makara, saidai fa a jira bayan komai
ya lafa a yiwa Takawa magana watakil shi bai zai rasa dabara
ba.’’
Cewar Hajja Kilishi yayin da tashi tsaye jiki sanyaye, tak’ara da
fadin.
‘’Kunsan mu na da baki, duk abinda za ku yi kada ku manta da
martabar Takawa, ku kula ku kame kanku kada ku jawo mana
abun da zai halaka yankin ga gaba d’aya’’
Ta na gama Magana ta juya abun ta ta fice, ta bar Inna Salti
tare da Jakadiya cikin al’ajabi. Gimbiya Kamariyya gani ta ke
sam Hajja Kilishi ba ta damu ba saboda ita dama ba ta ta6a
haihuwa ba shi ya sa sam ba ta damu da lamarinsu ba. Ita
kuwa Gimbiya Binta abinda ya tsaya mata a rai bai wuce na ta
na murnar raba Bintu da masoyin a Aisar, sai gashi ta zama
matar wanda har ta gama rayuwar ta a doran k’asa ba za ta
sami kamar shi ba, abun takaici ta yiwa yar uwarta asarar
masoyi, duk akan wanda sam be ma san ta nayi ba.

Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 2&3
Admin 001 Sayyadi Sadiq
@Whatsapp 08146934644
2⃣
Daga cikin masallacin Sa’ayrasa, ko da bawa ya tsinci kansa
gaban Aisar, hannunsa damke cikin na sa yayinda yake jero
masa tambayar da shi kansa bai ta6a jin ko da makamancin
sunan ba a matsayinsa na bawan barga da kwananan ya dawo
cikin sawun bayin da ke kula da lambu. Zufa ne ya shiga keto
masa, cikin kame-kame da in’ina ya ce
‘’Eye? Na’am lillahi warasulihi wanga zoben tsintarsa na ka yi,
idan kuwa na yi karya aratta kashe ni….’’
Maimaikon Aisar ya saki bawa sai dad’a damke hannu bawa
yayi. Cikin neman d’auki bawa ya kai dubansa ga sauran yan
tawagar na shugaban k’asa ya na mai neman d’oki. Hakan
yasa Junaidu tausaya ma bawan duk da ko shakka babu ya
san zoben hannun bawa mallakin d’an uwansa ne. Kana ya na
mai shiga tsakanin bawa da Aisar ta hanyar ciro hannun Aisar
daga cikin na bawa yayinda yayiwa bawa nuni da ya ciro
zoben, nan da nan bawa ya ciro zoben, ya mik’awa Junaidu kai
durkushe ya na mai fad’in
‘’Tuba na ke, aradun Allah tsinta na kai, ku min rai……’’
Nan bawa ya fashe da kuka, wanda hakan ba k’aramin dad’a
kular da Aisar ya yi ba, ji yake kamar ya shek’eshi har sai ya
matso gaskiya daga bakin bawan.
‘’Ka ga ba kuka za ka yi ba, babu abun da zai ma muddin ka
fad’a masa gaskiya, shin in aka sami wanga zoben?’’
Cewar Junaidu ya na mai kok’arin saka idanunsa cikin na
Bawa don gano inda bawa ya dosa. Shi kuwa bawa ya gama
rikicewa sai rantse rantse kawai yake, fad’i yake
‘’Tsinta na ka yi, kwankwasi tsinta na ka yi a lambu, aradu
tsinta na ka yi.’’
Jin an furta
‘’Ko shakka babu gaskiya ya ka fad’i, don na shedi wanga
bawa mai gaskiya ne.’’
Gaba d’aya hankalinsu ya koma ga mai maganar. Sanye ya
yake cikin bakar jamfa wanda aka masa ado da bakin zare,
idan ka d’auke rawaninsa da yake fari komai na jikinsa bak’i ya
sanya, kai kace wani taron bakin ciki ya halarta, ko da shike a
nasa 6angaran hakan ta ke. Kallo d’aya Aisar ya masa ya
d’auke kai ya na fad’in
‘’A matsayinka na wa za mu k’ar6i shedanka?’’
‘’A matsayinsa na Yarima Nuhun Sa’ayrsa ranka shi dad’e.’’
Fad’in bawan da ke tafe da Yarima Nuhu kenan, ganin idan ba
a yi dagaske ba yanda ran Yarima Nuhu ya ke a dak’ule komai
mai afkuwa ne. Jin haka Junaidu ya bawa Yarima Nuhu hannu
suka gaisa haka sauran yan tawagar amma ban da Aisar
wanda idan ransa yayi dubu ya 6aci, don haka a kusa ya ke.
Sanin hakan ne ya sa Junaidu yin saurin yiwa Yarima Nuhu
bayani, ya na mai nuna ma sa zoben. Ganin zoben da kuma jin
wanda Aisar ya ke tambaya Yerima Nuhu ya san ko shakka
babu Bintunsa ta arziki a ke nema, zoben nan shine zoben da
ya kar6a daga hannunta ya wulgar. Wato wannan shi ne Aisar
d’in da yake soyayya da Bintunsa….
Bawan nan dai da ke tafe da Yarima Nuhu ne cike da ladabi ya
furta
‘’A hakik’anin gaskiya wanga bawa ada bawan barga ne, be
dad’e da dawowa sahun bayinmu masu kula da lambu ba,
saboda haka ina mai tabbatar maka ba zai san wagga d’iyar
bayi da ku ke magana akai ba, dan yanda alama ya nuna ko
shakka babu ta na daga cikin bayin cikin babban gida tun da
har aka iya tsintar zoben hannunta cikin lambu, haka nima da
na ke bawan kofar gabas, ba mai yiyuwa ba ne na santa,
domin kuwa ba mu da wata alak’a da zai had’amu da bayin
cikin babban gida’’
‘’Shin ina za mu sami wagga d’iya?’’
Aisar ya tambaya ya na mai fatan samin mafita daga bakin
bawa. Nan take bawa ya masa alk’awarin tayashi cigiyar Bintu
nan ba da dad’ewa ba, sannan su ka sallami wannan bawa da
zoben Bintu ke gareshi. Yarima Nuhu ya shaida mu su abinda
ya kawo shi gare su, wato sheda ma su ana buk’atar su d’akin
taro. Ya na gama shaida mu su yayi gaba dan kuwa yanzun da
ya gane Aisar shi an samrayin da ya kwace zuciyar Bintu ya fi
ma sa d’aci akan auren da aka d’aurawa Bintu a yau, dan
wannan ya san ba mai d’orewa ba ne musammam idan aka yi
la’akari da wanda aka d’aura mata.
Dakyar Junaidu ya lalla6i Aisar, sai da ya masa tuni da ba fa
su kad’ai ba ne, akwai manya cikinsu, sun zo d’aurin aure ne
bisa wakilcin shugaban k’asa ba wai hakan nan bak’akatan su
ka zo ba, sannan ya samu ya d’an shawo kansa, ta hanyar
masa alk’awarin bayan komai ya lafa Junaidu da kansa zai
tsaya har sai sun samo Bintu kafin su juya gida, ko da kuwa
hakan ya na nufin raba tafiya da tawagar ta su. Da wannan su
ka yi tattaki zuwa d’akin taro ba tare da sun bari manya daga
cikinsu sun fahimci abinda ke faruwa ba.
Yarima Barde kuwa da dabara Yarima Jafar da Khalil su ka ja
shi mota, gaba d’aya ya zame mu su tamkar mutum mutumi,
ya d’auke mu su wuta. Cikin mota sai da su ka d’au kusan
rabin awa babu wanda ya iya furta komai.
Dogarin Masarautar Fabarusa ya zo ya buga musu kofa, nan
ya zube ya na mai sheda mu su umarnin Sarki Abdulrahman
na a ma su iso gareshi.
‘’Su na cikin masallacin ne?’’
Yarima Jafar ya tambaya, in da Dogari ya ba shi amsa da
‘’A’a, sun wuce ga d’akin taron masarauta tunda jimawa,
Yarima kad’ai ake tsimayi ranka shi dad’e.’’
‘’Mu na nan tafe.’’
Cewar Khalil, yayinda Dogari ya tashi da sauri ya na fad’in
‘’A iso lafiya.’’
Yarima Jafar na duban Yarima Barde ya ce
‘’Ka bawa zuciyarka hakuri mu amsa kiran Mai Martaba’’
Ko kallonsa be yi ba bare ma ya nuna alamar ya san da shi
ake, kamar an aje dutse. Ganin haka Khali ya ce da Yarima
Jafar.
‘’Ka san halin Barde a sama ya ke, ina zaifi mu lalla6a mu je a
dai ga fuskarshi, in ya so sai mu nemi izinin tafiya ta hanyar
ba da uzirinmu ga Mai Martaba.’’
Da wannan shawara su ka fito daga motar, amma Yarima
Barde fitowa ta ma sa wuya, sai da Yarima Jafar ya ma sa tuni
akan wanda ya sa a yi kiransa sannan ya fito cike da k’asaita,
dama shi idan ransa ya 6aci nan fa sarautar ta sa ke bunk’asa.
Ko da dogarawan da ke tsimayinsu su ka ga fitowarsa tuni su
ka rufa musu baya, zuwa d’akin taro, kai kace Sarki
Abdulrahman na Fabarusa ne da kansa ke tafe.
3⃣
Dakin taron ya cika fal da jama’a, tawagar Aisar da shigowar
su ke nan, na su 6angaran na shugaban k’asa su ka zauna.
Haka ma hakiman Sa’ayra da Fabarusa, Agadez, Diffa da
sauran Hakiman yanki da sassa na jamhuriyar Nijar wajan su
na musammam su ka zauna. Haka kuma yankin Sarakuna
wanda Sarkin Sa’ayrasa mai gayya mai taro ya hakimce, kusa
da shi kuma Sarkin Fabarusa ne zaune cikin aminci. Hakan ba
k’aramin farantawa jama’a rai yayi ba, wai ashe dai akwai
ranar k’arshen gaba tsakanin Sa’ayrasa da Fabarusa? Shin
dama akwai rana irin ta yau da za a ga Sarakunan wanga yanki
zaune cikin aminci?
Busa na alkgaita ke tashi daga waje, jama’ar Sa’ayrasa kwan
su da kwarkwatar su sun yi dandazo cikin d’akin taro, murna
gun su ba a cewa komai domin kuwa a yau yunwa zai kau a
k’asar su. Ganin shigowar su Yarima Barde tuni dogarai su ka
hau yiwa ango kirari. Shi kuwa Yarima Barde sam ba cikin
hayyacin sa ya ke ba, amma in aka d’auke Yarima Jafar da
Khalil wanda dama sun san halin da abokin na su ya ke ciki
babu wanda zai kalle shi ya ce ya na cikin wani hali, sai dai ma
ayi tsammanin tsabar sarauta da miskilanci ne yake d’ibar sa.
Sai kuma Mai martaba Sarki Abdulmalik na Fabarusa, wanda
kallo d’aya ya yiwa d’an na sa Yarima Barde bayan ya kai
gaisuwar sa ga Mai martaba Sarki Sule na Sa’ayrasa, ya gane
halin da ya ke ciki, kasancewar wajan mahaifin na shi ya yo
gadan kafiya, cijewa da kuma yin burus kamar be san abun da
ke faruwa da shi ba, amma in aka tona cikin zuciyar su, Allah
kad’ai ya san tafasar da ta ke. Murmushi Mahaifin na sa yayi,
cikin ran sa kuwa yacewa ya yi
“d’an mu Abubakar, alkhairi ne mu ka kulla ma ka ba sharri
ba, nan gaba za ka gode ma na kwaran gwaske’’
Ganin Yarima Barde durk’ushe gaban Sarki Sule, haka ma
abokan na sa biyu, hannun su na dama dunkule suna mai
jinjina ga Sarki Sule, fadawan Sa’ayrasa su ka amsa ma su da
“Jinjine dama lafiya alher, gaishe ka Yarima Badde, an gaishe
ku samari”
Sarkin Sa’ayrasa kuwa cikin nuna ya amsa gaisuwar ta su shi
ma ya dan daga na shi hannun daman a dunk’ule. Yarima
Barde ya shiga ran sa saboda kamala da kwarji na sa, ji ya ke
ina ma ina ma, ina sirikin na sa ne na gaske, da ya san haka
Sarkin Fabarusa zai aikata, da ya bayar da d’iyar sa ko da
kuwa ba a san ran ta ba ne.
Ko da Yarima Barde ya had’a ido da Mahaifin na sa, sai ya yi
saurin saukar da na sa idanun. Duk wannan abun da ke faruwa
a kan idanun yayan Barde, wato Yarima Sadauki na Fabarusa
wanda tun da ya ji abun da mahaifin na su ya aikata bisa ga
auran da ya d’aura ya k’ara jin tsanar Barde ya dad’u a kirjin
sa. Domin kuwa shi ya kamata Sarki ya d’aurawa aure shi da
ya ke babban d’an sa ba k’anin sa, hakan da yayi shi ya nuna
k’arara Sarki Abdulraman ya fi kaunar Barde, ya kuma fi fifita
shi akan Sadauki. Hakan ne kuma Yarima Sadauki ba zai
lamun ta, dan ya san ba k’aramin girma aka zubar ma sa ba a
idanun jama’a, dole kuma ya d’au Mataki. Idanun sa kan
Barde, cike da tsana ya ke duban sa yayin da aka yiwa su
Barde nuni ga na su wajan zaman, wato kusa da Yarima
Sadauki da abokan sa su ka zauna.
Tun shigowar su Yarima Barde idanun Yarima Nuhu ke kan sa,
ji yake kamar ya je ya sheda ma sa wacece Bintu in ya so
kowa ma ya rasa. Haka ma Aisar wanda ya san burin Bintu na
ganin Yarima Barde ko da sau d’aya ne a rayuwar ta, wai ta
rasa wanda za ta kira mai kyawun duniya sai wanga buzu!
Cewar Aisar cikin ran sa yayinda wani bakin kishi ya ta so ya
mamaye ran sa, shi dai fatan sa Allah ya sa ya sami damar
ganin Bintu tin ka a tafi da ita cikin bayin da za su raka gimbiya
Binta Fabarusa, ko dan Yarima Barde dole ya d’auke ta, sam
jinin su be had’u ba, dan haka Bintun shi ba za ta yiwa matar
Barde bauta ba, ko da kuwa duka dukiyar sa za a buk’ata
domin mallaka ma sa Bintu, a shirye ya ke ya rasa komai.
Bayan an sami nutsuwa ne aka bud’e taro da addua’a, sannan
aka shiga abun da ya tara su a wajan. Su Yarima Jafar sun so
su nemi izinin tafiya, amma hakan be samu ba, sai hakura su
ka yi su ka zauna kamar gumaka, ba um ba um um, ga abokan
Yarima Sadauki da shi kan shi Yarima Sadauki sai harbin iska
su ke. Barde kam duk be san ana yi ba.
Sarkin fabarusa ne ya fara jawabi, ya mai nuna farin cikin sa na
kulla aminta da auratayya wacce ta kawo k’arshen gaba
tsakanin Masarautar ta su biyu. Bayan haka ya gabatar da
takardar shedar sun bayar da bashin da masarautar Sa’ayrasa
su ka buk’ata, ya kuma ce tun da an zama d’aya, sa iya biya a
tsanake sannu a hankali ba tare da tashin hankali ba.
Nan waje ya kaure da ihu da sowa na jama’a, kowa na nuna
jin dad’in sa da kuma alfahari da halin girma irin na sarkin
Fabarusa. Dogarawan Fabarusa su ka shiga jera kirari ga
Sarkin Su, fad’i su ke
“Lafiya Sarkin yakin Sarkin musulmi
Lafiya maida garin wani kango
Lafiya Barden mahadi
Lafiya Sukukun bakaka
Lafiya Darzaza amalen sarakuna
Lafiya ba hau da wani ba sauke wani
Lafiya hana kangara
Lafiya Sakaka babban bako
Lafiya Bango madafar bayi
Lafiya hadarin kasa maganin mai kabido
Lafiya kwankwason jimina mai wuyar shafawa. Lafiya adali,
lafiya salamun, salamun salamun”
Jikin sarkin Sa’ayrasa ba k’aramin sanyi yayi ba. Sai da waje
ya lafa sannan Sarki Abdulraman ya k’are jawabin na sa da
adduar zaman lafiya tsakanin Masarautar da kuma fatan Allah
ya bawa shugaban k’asa lafiya.
Sai da sarkin Sa’ayrasa ya sa hannu a takardar ta hanyar
amfani da hatimin masarautar ta sa, yayi na sa jawabin na
nuna farin ciki da godiya ga masarautar Fabarusa, sannan
kuma ya yaba da halin dattako na Sarki Abdulrahman dan har
ga Allah ya bashi mamaki matuk’a. ya k’are jawabin na sa tare
da fatan alkhairi tsakanin Masarautar biyu. Cikin ran sa ya na
alhinin aurar da d’iyar bayin da yayi maimakon d’iyar sa,
maimakon ya kawo k’arshen gaba, gudunmawar dad’a k’arfafa
gaba yayi muddin sarkin Fabarusa ya fahimci yanda ya haince
shi saboda san zuciya.
Daga tawagar shugaban k’asa Kwaminishinan da yayi jawabi
ne ya mik’a gaisuwar shugaban k’asa tare da gudunmawar sa
na buhuhunan hatsi, shinkafa da dabino ga masarautar ta
Sa’ayrsa, wanda sam kyautar ta shi ba burge su ta yi ba, a
fad’ar su sai da yunwa ta ci ta cinye su har su ka kai ga neman
taimako gun abokan gaba sannan zai wani kawo musu
gudunmawar sa na bogi. Kafin kwaminishna ya k’are jawabin
sa, wayar Junaidu ta d’au k’ara, ko da ya amsa kiran tuni
fuskar sa ta canza, cikin dabara ba tare da ya bari an san halin
da ake ciki ba ya ja Aisar su ka yi waje.
A cikin mota ya ke sheda masa ai jikin Shugaban kasa ya
dad’a tashi kiran da aka masa kenan, su za su fara yin gaba in
ya so sauran tawagar za biyo su a baya gudun kada a d’aga
hankalin jama’a. Aisar ya na ji ya na gani haka su ka bar
yankin Sa’ayrasa, ya na mai kudirin dawowa da sun sami kan
Shugaban k’asa.
Daga d’akin taro kuwa tawagar shugaban k’asa sai neman su
Aisar su ka yi su ka rasa, bayan sun kira su ne su ke sheda mu
su ai sun yi gaba saboda wani uziri da ya taso, duk da dai ba
du sheda mu su ainihin abun da ke faruwa ba, sai da jikin su
yayi sanyi matuk’a.
An kamala taro yayinda aka ci aka sha, dan kuwa yau take
salla a masarautar Sa’ayrasa. Yarima Jafar ne ya nemi a kai
su ga masaukin su da ke su dama nan Sa’ayrasa za su kwana
su da tawagar Yarima Sadauki. Amma bakin ciki da kuma
Allah Allah da ya ke ya bud’e ido ya gan sa a Fabarusa domin
shedawa Mahaifiyar sa cin fuskar da aka masa ya sa Yarima
Sadauki fasa kwana, nan ta ke ya juya shi da tawagar sa ba
tare da sun jira Sarki ba. Su Yarima Barde kuwa da wasu
dogarawa aka had’a su domin kai su masaukin su.

Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 4&5
Admin 001 SAYYADI SADIQ
@Whatsapp 08146934644

4⃣
Bayan sarkin Fabarusa ya yiwa Sarkin S’ayrasa bankwana, ya
d’au hanya tare da tawagar sa. Haka d’aya bayan d’aya taro ya
shiga watsewa. Tawagar shugaban k’asa ma tuni su ka d’auki
hanya dan tadda su Aisar.
Sarkin Sa’ayrasa na komawa turakar sa Jakadiya ta zo ma sa
da buk’atar iyalan sa na ganawa da shi. Ganin magariba ta
gabato ya ce su maza su iso gare shi kada ya rasa sallah.
Hajja Kilishi, Inna Salti, Gimbiya Binta da kuma Gimbiya
K’amariyya ne zaune gaban sarki, sai kuma Jakadiya da Bintu
can gefe nesa da su. Jikin Bintu har karkarwa yake, fatan ta
Allah ya sa Sarki ya duba lamarin ta hanya warware auren
masifar da aka d’aura mata.
Ya na mai kallan Gimbiya K’amariyya ya ce
‘’ke mu ke sauraro’’
Maimakon ta bashi amsa sai ta kai kallan ta ga Inna Salti, cikin
idanun ta ta na mata magiyar ta taimaka ta shedawa sarki.
Inna Salti da ta gane halin da K’amariyyar ke ciki ta ce
‘’Allah shi ja da ran Takawa, batun amren da aka d’aura ne,
wanda aka d’aura amren da shi, shi ke neman amren
Kamariyya’’
‘’dama akwai wanda ya zo ya same mu da batun amren d’iyar
mu? Ba mu san da wanga Magana ba’’
Fad’in Sarki Sule. Inna Salti na mai kame kame ta ce
‘’eh dama ba su zo din ba, kasancewar da akwai rashin jituwa
tsakanin Masarautar ta Fabarusa da ta mu, hakan shi ya kawo
jinkiri Allah ya taimaki Takawa’’
Sarki Sule na mai gyad’a kai cikin nuna 6acin rai ya ce
‘’ki nufin d’iyar mu ta na sauraran wani ba tare da sanin mu
ba?’’
‘’ta yi kuskure, ayi mata afuwa’’
Cewar Hajja Kilishi, da ita kad’ai ke iya bawa Sarki hakuri idan
ya na cikin yanayin 6acin rai. Shiru ne ya biyo baya, kafin daga
bisani Sarki Sule ya ce
‘’a shedawa wanda d’iyar mu ta ke saurara a bayan idon mu,
ya zo nan da kwana biyu dal mu na so mu gana da shi’’
‘’shi ne Yarimar da aka d’aurawa amre da d’iyar bayi Allah ya
huci zuciyar babban bijimi’’
Cewar Inna Salti a hankali kamar wacce ke tsoran maganar.
Sarki na duban Gimbiya K’amariyya ya dad’a tambayar
‘’ku na nufin Badde na Fabarusa?’’
‘’Badde kuwa Allah ya k’ara ma ka lafiya’’
Ga mamakin su sai gani su ka yi Sarki ya murmusa, kafin ya
k’ara da
“shin kin san ita d’iyar bayi a matsayinwa aka d’aura mata
Badde?’’
Inna Salti wacce ta fara dana sanin furta maganar ta ce
” a matsayin Binta, Allah ja da ran ka’’
‘’wacece Binta?’’
Tambayar Sarkin Sule da ya sa kowani mahalukin da ke wajan
sai da ya sha jinin jikin shi. Da kyar Inna Salti ta yi k’arfin halin
furta
‘’d’iyar babban bijimi ce’’
Cike da 6acin rai ya ce
‘’ita Kamariyya da aka amrer da d’iyar bayi a matsayin kaunar
ta, kuma ta zo mana da zancen alakarta da wanda aka d’aura
din, ya ta ke so mu yi ma ta?’’
Shiru babu wanda ya iya furta komai. Idanun sa bisa silin yace
‘’an bar mu muna jira, ke mu ke sauraro K’amariyya!’’
Murya na rawa ta ce
‘’dama tin da haka abin ya kasance, na ke so a warware
matsalar ta hanyar raba amren …….’’
‘’yashasheshshen zance!’’
Sarki Sule ya katse ta ta hanyar daka mata tsawa, tuni jikin
K’amariyya da Binta ya hau k’yarma tsabagen firgici, kowa sai
da ya sha jinin jikin sa, Jakadiya ta durkusa ta na fad’in
‘’tuba mu ke ran Babban biji ya dad’a, Allah huci zuciyar
Babban Biji, lafiya salamun’’
Sarki kuwa be gushe b ya cigaba
‘’mun biye mu ku mun bi san zuciya mun aikata ha’inci,
hakik’a Sarki Abdulrahman ya kasanse mai zurfin tunani, mu
kuma mun kasance daga cikin ma’abota san zuciya, fatan mu
shi ne gyara wanga kuskure da mu ka aikata bisa san zuciya
ba tare da 6ata dangantakar arziki da mu ka kulla a wanga
rana ta yau ba’’
Kallan sa ya mayar ga Bintu, kana ya ce
‘’ina Kilishi?’’
‘’ran Takawa ya jima, gani kusa gaban ka’’
Cewar Hajja Kilishi.
‘’wagga d’iya ta arziki (yayi nuni ga Bintu) ta ma na abun da
jinin mu basu ma na ba, sanadiyar ta yunwa ta kau a
masarautar mu, idan ba mu maishe ta d’iya ba, ko shakka
babu mu na daga cikin wanada ake kira butulu, wagga d’iya
d’iyar mu ce, ni Sule na kira wagga d’iya da d’iya a gare mu,
maza a shirya d’iyar arziki, idan an wayi gari ta bi tawagar
masarautar Fabarusa dan kuwa jinkirin makwannin biyun ka
iya zama barazana a gare mu, da zafi zafi akan bugi karfe…
mun gama Magana’’
Ya na dasa aya ya tashi cike da Sarauta yayi shigewar shi daga
ciki, ya na jiyo koken Gimbiya K’amariyya da Gimbiya Binta
amma ya mu su kunne uwar shegu duk da kuwa har ran sa ya
ke jin abun.
Ita kan ta Bintu jin gobe gobe za a wuce da ita hankalin ta ya
dad’a tashi, ta ma kasa motsawa daga in da ta ke, ta nemi
kuka ta rasa.
Gimbiya K’amariyya kuwa wacce har shid’ewa ta ke tsabagen
kuka da ya ci karfin ta, tuni ta sake fad’uwa sumammiya a
karo na biyu. Nan waje ya sake kaurewa da salatin su Hajja
Kilishi da Jakadiya. Dan kok’ari har da Bintu cikin kawo d’oki
ta hanyar ciro mayafin ta, ta shiga yiwa Gimbiya K’amariyya
fifita, yayin da Inna Salti ke yayyafa mata ruwa.
Wani k’akk’arfar ajiyar zuciya ta saki, alamar ta farfad’o,
amma idanun ta lumshe ta kasa bud’e su, hawaye ke gudana
bisa kuncin ta. Sai fa a sannan Gimbiya Binta ta ankare da
Bintu da ke sunkuye bisa kan Didin na ta, sai fifita ta ke ma ta,
ai kuwa ta daddage ji kake tas! Ta sauke yatsun ta biyar bisa
kuncin Bintu sai da ta ga wuta a idanun ta. Hannun ta biyu bisa
kuncin ta ta ke duban Gimbiya Binta, hakan ne ya dad’a k’ular
da ita, ta sake d’aga hannu da niyar kai mata wani marin caraf
Inna Salti ta ruke hannun ta, ta na mai fad’in
‘’kul kar ki kuskura ki sake! Kin san kuwa matar Yeriman
Fabarusa ki ka d’aga hannu ki mara? Ina hankalin ki ya tafi?’’
Jin haka Gimbiya Binta kamar ta yi hauka, fad’i ta ke
‘’d’iyar bayi na mara, d’iyar bayi wacce na saba takawa ita na
mara, babu wata matar Yariman Fabarusa da ta wuce Didi, duk
makirci da munahunci wanga wulak’antacciyar Baiwa arudu ya
k’are bisa kan ta! Ku ma mu zuba ni da ke ina mai tabbatar mi
ki alkiyamar ki ta zo dan kuwa da ki tafi zuwa Fabarusa a
gurbin Didi gwamma ki je ki kashe kan ki, dan kuwa masifa da
balak’I ya na nan an tanadar mi ki, kuma shi za ki riska, sai dai
uwar ki ta haifi wani…..’’
Ta juya fuuuu ta fice gudun kar Bintu ta ga hawayen ta, dan
kuwa su ke sauka d’aya bayan d’aya tsabagen bakin ciki da
takaici. Hajja Kilishi shi ce ta ja Bintu zuwa turakar ta dan
neman yanda za a yi idanun Bintu da ya kumbura da shatin
yatsun Gimbiya Binta ya baje, bayan Inna Salti ta bata baki bisa
ga lamarin Gimbiya Binta da kuma mata alk’awarin irin haka
ba mai sake faruwa ba ne. Nan su ka bar Inna Salti ta na
rarrashin Gimbiya K’amariyya, domin kuwa bakin alk’alami ya
bushe tuni.

5⃣
Da daddare bayan an idda sallar isha’i, Yarima Jafar da Yarima
Barde zaune a falo sun yi jigum kamar wanda aka yiwa
mutuwa, Khalil na daga d’aka ya na waya da matar sa.
Babban falo ne mai d’auke da k’ayataccun kujeru na sarauta,
masauki ne da dama a ka tanada na musammam domin
saukar bak’i na alfarma irin su Barde.
Tun da su ka isa ga masauki Barde ke zaune nan falon, sallah
kad’ai ke iya sawa ya motsa. Shigar sa na d’aurin aure ke jikin
sa, sai dai ya cire babbar riga da rawani, sumar kan sa kwance
lub lub bisa kan sa.
‘Daya daga cikin dogarawa da ke ciran kofa ne ya shigo ya
zube gaban Yerima Barde, kana ya ce
‘’ran Yarima ya dad’e, Gimbiya K’amariyar d’iyar Mai martaba
Sarki Sule na S’ayrasa ce me neman iso gare ka’’
Jin sunan K’amariyya tuni kafad’a Barde ta tasa, yayinda
jijiyoyin wuyar sa su ka bayyana. Amma ya kasa furta komai.
Yarima Jafar ne ya ce
‘’ka iso da ita gare shi’’
Dogari na mai fad’in
‘’an gama ran Yarima Ja’afar ya dad’e’’
Ya tashi da sauri ya fice. Yarima Ja’afar ma tashi yayi, ya d’an
dafa kafad’ar Yarima Barde sa’annan ya shige ciki. Shigar sa
ke da wuya Dogari ya shigo biye da shi Gimbiya K’amariyya ce.
Sai da ya kawo ta gaban Yarima Barde sannan ya juya ya koma
waje in da bayan Gimbiya K’amariyya ke tsumayin ta.
Tin shigowar ta ya kafa mata ido, har ta iso gare shi sanye
cikin atamfa koriya wanda ta rufe da farar alkyabba ta alfarma.
Duk tashin hankalin da ta ke ciki da kuma wanda Yarima Barde
ke ciki be hana shi ganin kyauwun Gimbiya K’amariyya ba. Ga
wani k’amshi mai saka kwanciyar hankali da ya kasa gane kan
sa ke tashi daga jikin ta sa’in da ta zaune gaban shi. Yayi
kok’ak’arin sanya kwayan idanun sa cikin na ta, amma hakan
ya gagara kasancewar ta yi k’asa da na ta idanun.
‘’K’mariyya…..’’
Ta ji murya mai d’auke da tarin kwarjini ta daki kunnan ta,
wanda tun da aka d’aura masa aure da Bintu, kwakkwarar
kalma d’aya be fito daga bakin sa ba sai a yanzu da ya ga
K’amariyya zaune gaban sa.
‘’K’amariyya’’
Ya sake kiran sunan ta a karo na biyu, maimakon ta amsa,
kawai sai ta sa ma sa kuka, ya rasa yanda zai yi da ita dan
kuwa Barde sam be iya rarrashi ba. Ta d’au lokaci mai tsayi ta
na rera kuka gaban sa, tin ya na iya ba ta baki, har ya mata
shiru dan kuwa shi dama Magana wahala ta ke masa. Sai da
ta yi shiru dan kan ta, sannan ya dube ta, kana ya ce
‘’ban san kud’irin mahaifina ba, sai bayan da bakin alk’alami ya
bushe, sai da aka d’aura min amre da kauna gun ki Fatima….’’
Jin haka Gimbiya K’amariyya ta kai duban ta gare shi, ta ga ya
k’ara ma ta kyau da kwarjini na kwaran gaske, wai kuma an
d’aura ma sa Bintu! Bintu dai d’iyar bayi! Ji ta yi kamar ta
bud’e baki ta fad’a masa gaskiya komai ta fanjama fanjam,
tunawa da ta yi da na ta Mahaifin ya sa ta a dole ta na ji ta na
gani ta yi shiru, babu mamaki shi ya na da wani shiri ne na
daban. Murya na rawa ta ce
‘’ina cikin damuwa Yarima, ina mafita?’’
Kallan ta yake na wasu dak’ikai, kafin daga bisani ya saki
ajiyar zuciya mai karfi gami da sauke kafad’a, kana ya ce
‘’Allah shi ne mafita, shi za mu kai kukan mu gare shi, hallo
bana yiwa Mahaifina musu, ban ta6a ba K’amariyya shi ya sa
ma ki gaya aiwatar da wanga lamari ba tare da ya tuntu6e
niba, yanzu ban da tsumi hallo ba dabara, amma ina so ki sani
ina son ki, kwaran gaske’’
Cikin hawaye K’amariyya ta ce
“me zai hana ka sanar da Mahaifin ka gaskiya kamar yanda na
sanar da nawa Mahaifin?’’
‘’ban da wannan ikon K’amariyya, da ina da shi da tuni na
aiwatar da hakan’’
Cewar Yarima Barde ya na amai girgiza kai. Nan Gimbiya
K’amariyya ta fusata, ta tashi da sauri za ta fita. Yarima Barde
ma tashin ya yi, ya dakatar da ita ta hanyar fad’in
‘’kar ki yi fushi K’amariyya, kunar za ta min yawa, badan
wacce aka d’aura min jinin ki ba ce kuma kauna gun ki da na
ce duk duniya babu wacce na tsana face ita, sam ba za ta
sami kulawa bare wani abu wai soyayya daga gare ni ba
saboda soyayyar ki, hallo babu yanda zan yi dole haka zan
zauna da ita har Allah ya kawo karshen zaman, dan darajar
Mahaifan mu da Masarautun mu’’
Kallan sa ta ke yayinda hawaye ke gudana daga idanun ta, a
hankali ta furta
‘’ina ma ka fatan alkhairi Yarima Badde’’
Sannan ta juya a hankali ta na ficewa. Tsayawa yayi ya na
kallan ta yayinda ta ke ficewa daga rayuwar sa, idanun sa sun
yi jajur, ji yayi k’afafun sa sun kasa d’aukar gangan jikin sa, a
hankali ya zauna zuciyar sa cike da tunanin yanda rayuwar sa
ta sauya a wuni d’aya. Shi ba mutum ba ne mai san mata,
mata ne ma ke san sa da bibiyan sa. Tin da Allah ya had’a shi
da Gimbiya K’amariyya, ita ce mace ta fari da ya ji ya na kauna
zai kuma iya aura. Amma yau gashi an ma sa Katanga da ita
ta hanyar aura ma sa kanwar ta. Yatsun sa ya tusa cikin sumar
kan sa sanadiyar sarawa da ya ji kan sa na yi, ya na fad’in
‘’lahaula walakuwata illa billah!’’

Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 6
Admin 001 Sayyadi Sadiq
@Whatsapp 08146934644
Khadija Sidi..✍🏼
6⃣
Ko da Gimbiya K’amariyya ta koma d’akin ta, sai ta sallami
bayin ta gaba d’aya sannan ta kulle d’akin ta haye tsakiyar
gado ta na rusa kuka. Bintu kuwa d’akin Hajja Kilishi bayi ke
jera kaya da aka d’inka ma ta na alfarma, yayinda Hajja Kilishi
ta sa ta gaba sai bayani iri-iri ta ke mata akan kayan da kuma
yanda za ta na amfani da su, da yanda ake son zaman na ta
ya kasance a fadar Fabarusa kasancewar Sarki ya janye
makwanin biyun da ya kamata a kai Bintu ga Masarautar
Fabarusa.
Bintu da ba cikin hayyacin ta ta ke ba, babu abun da ta gane
kawai dai amsa ma ta ‘’um’’ ta ke. Da wuri Hajja Kilishi ta
bawa Bintu umarnin kwanciya saboda sammakon da za su yi a
washagari. Yanda ta ga rana haka ta ga dare, haka ta kwana
cikin zulumi sai da asuba wani bacci mai nauyi ya sace ta.
Ba ta jima ta na bacci ba, Hajja Kilishi ta aiko d’aya daga cikin
Bayin da aka bawa Bintu, wato Ladiyo ta tada ita gudun kada
su makara. Nan ta ke tseguntawa Bintu cewar Gimbiya Binta
har ta wuce Nigeria makaranta bisa ga umarnin Takawa. Kuka
Bintu ta saka ta na mai fad’in
‘’Na shiga uku ni Bintu, wallahi ni Bintu na ke ba Binta ba,
d’iyar bayi na ke ba d’iyar Sarki ba, ashe dai ba zan kammala
makaranta ta ba, wayyo Inna ki zo ki taimake ni na shiga uku
na lalace!’’
Da ladiyo ta ga haka, kawai sai ta fice, jim kad’an sai ga ta
dawo biye da ita Hajja Kilishi ce rai 6ace. Tuni ta hau Bintu da
fad’a, ta na fad’in
‘’Wai ashe ba ki da tawassali Fatima? Ba ki yarda da k’addara
ba? Idan ba ki fasa kuka ba ba ba ki nuna mana ba a isa da ke
ba’’
Jin wanna kalame na Hajja Kilishi tuni Bintu ta shiga taitayin
ta, sai ajiyar zuciya ta ke kawai. Hajja Kilishi ba ta gushe ba ta
cigaba da maganar ta kamar haka
‘’Ki d’au kaddara ki yi fata Allah ya sa hakan shi an alhairi gare
ki, yoto ai alkhairin ne ma. Ina ke ladiyo ?’’
Ladiyo ta matso kusa tare da fad’in
‘’Ran ki shi dad’e’’
‘’Maza ku shiga bayan gida ku had’o mata ruwan wankan
amare’’
Cewar Hajja Kilishi.
‘’An gama ran ki shi dad’e’’
‘’Ke kuma Hansai maza shirya kayan Gimbiyar ta ku, Ina
Maman Cangwai ne? maza ku sheda mata ta ta kawo maganin
d’ar nan da lalle domin yiwa amarya wankan lalle’’
Hansai na mai duk’ar da kai ta ce
‘’Ranki shi dad’e ai tuni Maman Cangwai na can rariya, fitowar
Bintu kawai ake jira……’’
‘’Bintu ki ka ce!!’’
Hajja Kilishi ta daka ma sa tsawa. Hansai ta zube k’asa jiki na
6ari ta ke fad’in
‘’Tuba na ke ranki shi dad’e, na tuba ran ki shi dad’e ki min rai
aradu na tuba’’
‘’Kwarankwatsi ki na rasa ran ki muddi ki ka kuskure asirin
Masarautar ga tonu sanadiyar kuskure irin wang, shasha
kawai, me an sunan Gimbiyar ga?’’
Hajja Kilishi na magana ne a hasala kamar mai shirin bugun
Hansai. Ita kuwa Hansai idanun ta ke kawo ruwa.
‘’Gimbiya Bintu…..’’
‘’Gimbiya Fatima, ban yarda kin kira ta Bintu ko Binta ba!’’
‘’An gama ran ki shi dad’e, godiya na ke’’
Cewar Hansai. Allah Allah ta ke Hajja Kilishi ta sallame ta ko ta
sami sarari. Jin Hajja Kilishi ta ce ta yi maza ta idda umarnin
da aka ba ta, Hansai ta tashi da sauri ta fice. Kan ace me?
Tuni aka shiga hidimar shirya Bintu, sai ga ta ta fito tsaf da ita
cikin fararan tufa tun daga sama har k’asa. Hajja Kilishi ce ta
d’auko wani dank’areriyar sark’a na gwal tare da yari da
warwaro ta ce a sanyawa Bintu na ta gudunmawar kenan.
Haka ma Inna Salti ta turowa Bintu goma ta arziki, ciki har da
farrar god’iya. Sauran matan Sarkin ma suma ba a bar su baya
ma, sai da su ka yi tattaki domin
nuna bacintar su dan kuwa abu na kishiyoyi sai da ya so ya
zama gasa.
Rana ba ta k’arya, sai ga shi ana fitar da kayan Bintu zuwa
motocin da ke jere domin kai amarya ga Masarautar Fabarusa,
yayinda dattijiwar da ta zo amsar amarya, me suna Uwalanze
ke zaune ta na jira. Wasu dattijai mata guda biyu, wanda su ke
tamkar kakanni wajan su Gimbiya K’amariyya ne bisa ga al’ada
su ka zo raka Bintu wajan Sarki domin su yi sallama a
matsayin Mahaifin ta, sannan su damk’a ta ga mutan
Fabarusa.
Bintu na ji ta na gani su ka sa ta tsakiya, gud’a ke tashi su
kuwa tsofi fad’i su ke
‘’Allah Ya ba da sa’ar tafiya Gimbiya Binta, Allah ya sa a dace
d’iyar arziki’’
Ba su zame ko ina ba sai turakar Sarki, in da su ka tadda
Jakadiya tsaye bakin k’ofa ta na jira. Da isar su ta mu su iso
zuwa gaban Sarki da ke daman abun da ta ke jira kenan.
Gaban Sarki su ka aje Bintu dan idan aka d’auke dattijiya mai
suna Gwaggo Munari cikin su, duk a na su zatan Gimbiya Binta
ce. Sai da su ka kai gaisuwar su ga Sarki sannan su ka juya su
ka bawa Sarki waje domin su gana da d’iyar sa.
Murya na rawa Bintu ta furta
‘’Barka da safiya ran ka shi dad’e’’
Shiru be iya amsawa ba, tsabagen tausayin Bintu da ya ji ya
lullu6e shi, gami da nadamar hukuncin da ya aikata bisa ga
san zuciya. Daga bisani ya nisa tare da fad’in
‘’Da wata murya za mu amsa mi ki Fatima? Da wata murya za
mu amsa mi ki d’iyar arziki? Da wani baki za mu amsa mi ki
wanga d’iya da ke gaban mu? Yau mun yi kad’an mu amsa
gaisuwar wagga d’iya, wacca jama’a su ka ku6uta da ga
yunwa saboda ita. Sanadiyyar wagga d’iya, mutan Sa’ayrasa
na godiya gare mu, mu kuma godiyar mu gare ki ya ke, Allah
ya saka mi ki da alkhairi sa’’
Shiru ya yi na d’an wani lokaci sannan ya cigaba
‘’Mungode kwarai hak’ik’a mun yi dana sanin abin da ya
wakana a Masarautar mu, hallo mu na fatan hakan ya zama
alkhairi a gare ki. Ki tsaya tsayin daka domin tabbatar da rufin
asirin mu, shakka babu kin mana abin da ‘ya’yan mu ba su ma
na ba. Tashi ki tafi d’iyar arziki, mu na addu’a albarkar Allah
ya bi ki duk in da za ki kasance’’
Jiki na rawa, amma Bintu ta kasa tashi ta kuma kasa magana.
Jakadiya ce ta lek’o, ganin yanayin da Bintu ta ke ya sa ta yiwa
Dattijan nan magana su shigo su tafi da Bintu Sarki ya gama
ganawa da ita.
A 6angaran Hajja Kilishi su ka tadda Dattijiwar Fabarusa wato
Uwalanze. Nan aka damk’a hannun Bintu gare ta bisa alada da
amana. Bintu fuska k’udundune cikin alkyabba kuka har da
majina, Uwalanze ta ja hannun ta, biye da su d’aya daga cikin
wannan dattijan ne da su ka kai ta ga Sarki, dama kuma ita
d’in ce cikin su ta san gaskiyar lamarin wato Gwaggo Munari.
Kai tsaye motocin Fabarusa su ka numfa.
Motoci ne na gani na fad’a wanda ke tashe wannan k’arnin.
Mota ta farki cike fal da dogaran Fabarusa, sai ta biyu wacce
ke rufe ruf da bakin gilashi, ita ce motar da su Yarima Barde ke
ciki. A ta ukun Bintu ke zaune tsakiyar Uwalanze da Gwaggo
Munari. Sai ta hud’in kuma bayin da aka bawa Bintu ne, wanda
idan ka d’auke Maman Cangwi ko wacce daga cikin su tafe ta
ke da na ta kullalliyar akan Bintu. Mota ta biyar ma dogaran
Fabarusa ne ciki. Nan su ka d’auki hanyar Fabarusa.
A hankali Bintu ta ji ana ta6a kafad’ar ta, maimakon ta tashi
sai ma dad’a lumshe idanu ta yi ta na mai murmushi,
kasancewar mafarkin da ta ke mai dad’i, wai ga ta a
makarantar su, tare da Aisar su na zantawa ya sa ta ji sam ba
ta so ta farka. Gwaggo Munari ce ta katse mata jin dad’i ta
hanyar jijjaga kafad’ar ta, wannan karan da d’an karfi domin
kuwa sun jima da isa Masarautar Fabarusa, yanzun haka kofar
fada su ke, Uwalanze har ta fice daga motar amma Bintu na
nan ta na baccin asara.
A firgice Bintu ta tashi jin jijjigar ta wuce hankali, ga busar
algaita da ke tashi, har da hayaniya da wak’e dake tashi daga
bakin mutan Fabarusa da su ka cika kofar fada domin ganin
isowar amaryar Yerima Barde.
Ganin alamar Bintu ta tashi, Gwaggo Munari ta shiga gyara ma
ta alkyabba yanda fuskar ta zai rufu da kyau, ta na fad’in
“Ko ke fa Gimbiya d’iyar Sarki mai dole, ai ke kuwa bacci be
same ki ba”
Kalmar nan ta Gimbiya da jama’a ke kiran Bintu da shi sam ba
ya mata dad’i, gani ta ke tamkar ana raina mata iyayen ta, ya
ga wanda su ka haife ta amma fin k’arfi zai sa a raba ta da su?
In dai haka zama Gimbiya ya ke Allah wadar da irin na
Sa’ayrasa.
Ta na kan wannan tunani ne gilashin motar ya sauka, yayinda
Jakadiyar Fabarusa ta bayyana a gare su, kana ta ce
“Gide mutan Fabarusa, na cikin gari hallo da na fada, kwan mu
da kwarkwatar mu, mun hito domin tarbar amaryar zaki,
Yariman mu abin alfaharin mu. Mu na neman alfarmar
bayyanar wagga Gimbiya ta Sa’ayarasa, da ta kasance
Gimbiyar Fabarusa da ga ranar jiya har illa MashaAllahu”
Gwaggo Munari na mai murmushi ta amsa mata da
“Gimbiyar ta mu, wacce ta kasance fure a gare mu, wacce
babu shakka za ta wadata ku da kyawu gami da kamshi da ke
tattare da ita, Gimbiya Fatima ta Sa’ayrasa ta amsa kiran
mutan Fabarusa”
Jakadiya ta rangwad’a gud’a, tuni waje ya kaure da
hayaniya,yayinda mata da yara su ka hau wak’a su na tafi, fad’i
su ke
“Mun nema! An ba mu! Mun k’aru!
Mun nema! An ba mu! Mun k’aru!”

Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 7
Admin 001 Sayyadi Sadiq
@Whatsapp 08146934644

7⃣
Sidiya ce…✍🏼
Jakadiya ta bud’e kofar motar ta in da Bintu ta ke. Bayi mata
guda goma shabiyu, wanda su ka kasu gida biyu sahu su ma
jere kan sa sunkuye gaban motar su na jiran fitowar Bintu
domin taka mata baya. Idan Bintu ta motsa toh dutse ma ya
motsa, sai da Gwaggo Munri ta fito sannan ta zagayo gare ta,
hannun Bintu ta lalabu cikin alkyabba, sannu a hankali, cikin
azanci kai ka ce Gimbiyar ce da gaske ta fito da Bintu. Tuni
bayin nan su ka zube gwiwowin su biyu a k’asa cike da
girmamawa. Mata da yara masu waka ba su fasa ba. Cewa su
ke
‘’Mun nema! An ba mu! Mun k’aru!
Mun nema! An ba mu! Mun k’aru!!’’
Jakadiya kuwa ba ta fasa gud’a ba. Tuni hayaniya da sowar
jama’a ya rud’a Bintu, har sai da Gwaggo Munari ta fahimta
ganin yanda ta cize waje d’aya ta kasa tafiya. Cikin rad’a
Gwaggo Munari ta ce da Bintu
‘’yo to ki ka cize nan Gimbiya kya iya wad’uwa ba ki sani ba,
gide rufa mana asiri mu tai, ke kawai ki ta salati, hallo ka da ki
kuskura ki kai kallan ki ga jama’a, hakan ka iya rud’a ki, maza
soma ambaton Allah’’
Nan da nan Bintu ta tsinci kan ta ta na mai ambaton Ubangiji.
Tsakiyar Uwanlenze da Gwaggo Munari, Jakadiya daga baya,
biye da ita bayi goma shabiyu ne, su ka kutsa ta hanyar da aka
tanada na musammam domin wucewar Gimbiya. Ba su zame
koina ba sai cikin fadar Fabarusa.
Kansencewar Masarautar Fabarusa ta yi biyun ta Sa’ayrasa a
girma da tsari, ba su Ladiyo ba, hatta Gwaggo Munari sai da ta
yi da gaske wajan 6oye shawa’an ta ga Masarautar domin
kuwa lokacin da su saka k’afar su a katafariyar fadar Fabarusa,
sun ga abin mamakin gaske, wato bayan girman fadar na da
ban al’ajabi, kuma yadda aka fasalta ko tsara ginin ta shi ma
abin mamaki ne. A tak’aice sai da su ka zamo tankamar
k’auyawan da su ka shigo birni. Gini ne irin na gargajiya wanda
aka kafa harsashin ginin da manyan duwatsu ma su tsada,
wad’an su kamu takwas wasu goma. Tsakanin kowace
katanga akwai duwatsu masu tsada wad’anda aka yanka su
bisa ga ma’auni san’annan aka dasa itacen al’ul daga gefan
su. Tsuntsayen fada iri iri ke shawagi, musammam d’awisu da
jin su ne su ka fi yawa.
Sai da su kusta sauro gomasha biyu kan su kai ga shiga cikin
gidan Sarki, kowanne da na sa irin adon da kayan k’awa,
wanda idan su ka shiga wannan su ka shiga na gaban sa sai su
ka ashe na baya ba komai ba ne idan aka had’a sa da na
gaban sa. ‘Bangarn uwar gidan Sarki Abdulrahman, wacce ake
kira Goggon nan aka sauke su. In da aka zaunar da Bintu bisa
shimfid’a na musammam da aka ta na dar mata daga tsakiyar
falo, yayinda su Ladiyo, Hansai, Lanta da Maman Cangwai su
ka yi zaune daga gefe matsayin su na bayin Gimbiya.
Tuni Barori da Bayi su ka shiga kai kawo da hidima domin
tarbar baki cikin aminci ta hanyar tabbatar da ba su bawa
Masarautar su kunya ba. Kayan marmari na daga ‘ya’yan itace
ne, nama na k’arama da babban dabba kai har da ma na
d’awisu, su dubulan ne, caccabe, alkaki da nakiya komai bajau
sai wanda jama’ar Sa’ayrasa su ka za6a. Gwaggo Munari na
mai jinjina kai cikin ran ta take fad’in
‘’ma su abu da abun sa, gaskiya dukiya cikin wanga masarauta
ba a cewa komai! D’iyar bayi ke kuwa Allah ya yankewa kakar
saka, amre cikin wanga Masarauta shi an baiwa’’
Ciki su ka bud’e su ka ci su ka yi nak. Amma ita ko Bintu ruwa
ma kasa sha ta yi bare ta kai ga cin abinci duk da kuwa
azababban yunwa ne ya addabi cikin ta. Bayan an tabbatar su
huta ne wata baiwa ta zo ta ce da su idan sun shirya za ta kai
su ga masauk’in su domin Gimbiya Fatima ta shirya ta sami
fitowa zuwa taron wankan amarya wanda za a yi nan ba da
jimawa ba.
🐫🐪🐫🐪🐫🐫

Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 8
Admin 001SAYYADI SADIQ
@Whatsapp 08146934644

8⃣
Sidiya ce…..✍🏼
Shiryayyan d’aki mai had’e da 6and’aki aka aje su Ladiyo, su
Bintu kuwa d’aya daga cikin d’akunan Goggon nan a matsayin
ta na uwar gida aka sauke su kan a gama wankan amarya a
mik’a ta ga na ta 6angaran.
Su na shiga masaukin na su ba da jimawa ba, wata baiwa ta
sake dawowa d’auke da kaya, gaban Bintu wacce ke zaune
bisa gado har lokacin ba ta bud’e fuskarta ba baiwa ta zu6e,
ta na mai aje kayan gaban ta, ta ce
‘’ an gaida Gimbiya Fatima, wagga kaya tsaraba ne da ga
Goggo nan, ta ce a shedawa Gimbiya Fatima ta sanya su
yayinda za ta hito wajan wankan amarya nan ba da jimawa ba’’
‘’Gimbiya Fatima ta amsa, ta na godiya’’
Cewar Gwaggo Munari. Bayan fitar baiwar Gwaggo Munari ta
yaye alkyabbar Bintu, sai ga ta ta yi wuri wuri da ido.
‘’Gimbiya yanzun ga ba lokacin tuntuntuni ba ne, kin dai san
dalilin da ya sa ki wanga Masarauta da kuma a gurbin wacce
ki ka zo, gwara dai ki sake shawara ki nutsu in har ba so ki ke
ki rasa ran ki sa’annan ki haddasa yaki da gaba wanda ka iya
halaka ta mu Masarauta gaba d’aya’’
Fad’in Gwaggo Munari cikin gazawa da halayyar Bintu dan
kuwa idan ba ta yi da gaske ba ko shakka babu asirin su mai
tonuwa ne. A sanyaye Bintu ta ce
‘’ina tuba….’’
‘’ba tuban ki mu ke buk’ata ba!’’
Gwaggo Munari ta katse Bintu, kana ta k’ara da
‘’ Aikin ki mu ke buk’ata Gimbiya! Wanda za ki fara yanzu ta
hanyar zama Gimbiya ba d’iyar bayi ba. Allah ya mi ki zubi irin
na jinin mulki, kowa ya gan ki ya san hakan nan Allah ya yo ki,
ba ki gada ba amma Allah ya baki su a halittar ki, Dan haka
tak’ama da isa shi na ke so daga gare ki, ki saka a ran ki
wannan dama ne da Allah ya baki dan jin dad’in rayuwa da
kuma taimako ga Masarautar mu, idan asirin mu ya tonu gaba
d’aya farin cik’in masarautar mu ne zai koma ga zubar jini, ina
fatan kin fahimce ni?’’
Bintu ta gyad’a kai. Kana Gwaggo Munari ta dafa kafad’ar
Bintu ta ce
‘’madallah da d’iya ta gari. Sai ki yi shiri yanzu su Ladiyo za su
zo su had’a mi ki ruwan wanka. Hakuri za ki yi na san kin saba
yiwa kan ki komai amma daga yau komai yi mi ki za ake yi, ki
jure Bintu wata rana sai alkhairi’’
Bintu ta dad’a jinjina kai. Ana hakan kuwa su ka ji an sake turo
kofa an shigo. Maimakon Ladiyo da Gwaggo Munari ta ce,
Lantana ce baiwar da Yarima Nuhu ya za6a ta musammam
domin kular masa da al’amran Bintu ta shigo ta zube gaban
su. Gwaggo Munari na mai duban ta tace
‘’Lantana gide ke ce mai shirya ruwan wankan ne? yo to ina
sauran? Kar dai sun tsaya kallan kauye mu ka biya ku fa sai
mu makara!’’
Lantana waccen ita dama da ka gan ta ka ga zubin munafunci,
dan ko magana ka ke da ita haka za ka ga ta na sinsin da
idanu sam ba ta bari a ga kwayar idanun ta. Ta kada baki ta ce
‘’ai ga su nan tafe, sauri na yo dama na shirya ruwan wankan
kada a makara’’
Jin haka Gwaggo Munari na mai mata nuni da bayan gidan da
ke cikin d’akin ta ce
‘’yauwa madalla da ke, maza je ki ga bayan gidan can shirya
mata gide’’
Sim sim ta shige bayan gida. Sai da ta fara taran ruwa sannan
ta shiga had’a ruwan da turaruka iri iri kamar yanda su ka saba
had’a ruwan wankan Gimbiyoyi. Ko da ta zo kan turaren
karshe, sai ta faki idanun Gwaggo Munari ta tabbatar hankalin
ta na kan su Ladiyo da shigowar su ke nan, ta na mu su
bayanin yanda ta ke so su kasance wajan taro. Sannan ta jawo
kofar bayi ta rufe. Gefan zanin ta ta kwance, ta dauko wani
kullin magani, cikin sauri da azanci ta bud’e maganin ta na
mai zazzage shi cikin ruwan wankan Bintu. Tuni wani irin bakin
hayaki mai wari ya taso daga ruwan yayi sama, ita kan ta
Lantana sai da ja baya ta na mai toshe hancin ta cikin tsoran
kada fa su Bintu su ji duk da dai Yarima Nuhu ya tabbatar
mata babu wanda zai ji warin bayan ita da ta zuba. Sai da
ruwan ya dena kumfa da hayaki sannan ta mayar da sauran
kullin maganin cikin zanin ta ta kulle, ta fito hankali kwance
kamar ba ta aikata komai ba.
🐫🐪🐫🐪🐫🐪

Bintu Diyar bayi…..book 2 chapter 9 to 11
sSayyadi Sadiq ……08146934644
+234 808 323 2323: 9⃣
Sidiya ce……✍🏼
Fitowar ta ba da dad’ewa ba Gwaggo Munari ta sanya Bintu
wankan dole dan kuwa ba da san ran ta ba. Da taimakon su
ladiyo da Hansai Bintu ta fito fes cikin doguwar riga ruwan
d’orawa, rigar da Goggon nan ta aiko mata. Material ne mai
tsada ke, sai kuma mayafi kore mai turawa da ratsin ruwan
d’orawa. Gwaggo Munari ruke da hannun ta domin kuwa ita ta
ke gane mata hanya su ka fito, Su Ladiyo biye da su yayinda
aka mu su iso zuwa babban zaure in da mata da iyalan Sarki
ke jiran isowar su.
Babban zaure ne wanda ya fi k’arfin a k’ira sa da zure sai dai
ko d’akin taro, tsawon sa kamu d’ari, fad’in sa kamu hamsin.
Haka kuma ko wacce kusurwa na zauren an masa ado da
itacen al’ul a bisa ginshishik’an sa. Bayan ga dadduma mai
kulliyar jikin damisa da ke shimfid’e tun daga fari har zuwa
k’arshen zauren da kuma tintin masu adon jikin damisa da ke
baje bisa daddumar, akwai duwatsu wanda aka auna sa’an
nan aka yanka su da zarto ciki da baya daidai da juna, aka jera
su zagaye cikin zauren tamakar kujerun zama irin na zamani.
Haka kuma bangon zauren zane ya ke da tambarin Masarautar
Fabarusa.
Cikin zauren su ka tadda dukkanin iyalan Sarki Abdulrahman
tare da y’anuwa da abokan arziki wanda su ka zo domin ta ya
su murna. Matan Sarki Abdulrahman uku wanda su ka had’a
da Goggon nan (uwar fada), sai ta biyu wacce su ke kira da
Goggo ta dole(uwar dole) sai ta ukun wacce ake kira Uwar
Soro, wacce itace mai k’arancin shekaru cikin matan sarki.
Kowacce hakimce, k’ishingid’e bisa tuntin. Gaban su kuma
wani tulu ne wanda aka masa ado da azurfa cike da ruwa mai
d’auke da turare da garin lallel.
Haka kuma ‘ya’ya da jikokin sarki da na su wajen daga gefe
wanda d’irga su ba k’aramin aiki ba ne kasancewar ‘yay’an sa
mata ma su aure da ‘ya’ya sun kai su goma sha takwas, kuma
dukkanin su ba su yi k’asa a gwaiwa ba haka su ka zo da
sassa da yankunan Jamhuriyar Nijar domin tarbar amaryar
d’an uwan na su. Duk da dai ciki akwai mu su bakin cikin
lamarin kasancewar ciki d’aya su ke da Yaremi Sadauki.
Musammam Yaya Mai Soron Baki, babbar d’iyar Sarki
Abdurahman da mai bin mata wato Yaya Jidda wanda su
‘ya’yan Goggon nan.
Wajan da aka tanadarwa Bintu gaban su Goggon nan aka
zunar da ita. Tun da ta yi wanka da ruwan nan na Lantana
hankalin ta ya ke a tashe, gashi gaban ta sai fad’uwa ya ke, ta
na son fad’awa Gwaggo Munari amma ta tsoran za ta yi zatan
fad’an da aka mata ne be shige ta ba, dan haka a dole ta
hakura da ikon Allah. Maimakon Gwaggo Munari ta zauna
gaban ta, sai gani ta yi ta ja gefe daga wajan su Gwaggon nan.
Cikin girmamawa ta mik’a gaisuwar ta tare da damk’a amanar
Bintu gare su bisa ga al’ada. Goggon nan wacce a ran ta ta yi
farin cikin fasa auren d’iyar Sarkin Sa’ayrasa da Sarki
Abdulraman yayi, ta kuma yi bakin cikin aurar da aka aurawa
Barde a maimakon d’an ta Sadauki, ta fara kar6ar amana ta
hanyar saka hannu ta bud’e mayafin Bintu da ke gaban su, tuni
Bintu ta yi k’asa da idanun ta cikin fad’uwar gaba. Sai da ta
kalli fuskar Bintu na d’an wani lokaci ta na mai yamutsa fuska
ta saki mayafin ba tare da ta rufe fuskar gaba d’aya ba. Kana
ta ce
‘’ni Munzaratu jikar Sarki Abdulrahman na difa, d’iyar Sarki
Abdulmuminu iii na Agadez, matar Sarki Abdulraman ii na
Fabarusa, na bud’e fuskar amaryar dan mu, d’iyar Sarkin
S’ayrasa, Sarki Sule Inuwa Magaji da zannuwa hamsin, kallabi
hansin tare da bayi guda uku’’
Jakadiya ta rangwad’a gud’a, yayinda waje ya d’au sowa. Ita
Bintu ta yi k’asa da idanun ta, ji ta ke kamar ta dan ta k’arasa
rufe fuskar ta gaba d’aya. Amma me za ta ji? Goggo ta dole ce
ta sa hannu ta k’ara yin baya da mayafin Bintu yanda za ta ga
fuskar Bintu da kyau, kafin ita ma ta jero sunan ta da
nasabobin iyayen ta, ta bud’e fuskar Bintu da silallan gwal. Ita
kuwa Uwar Soro da tashi na ta bajintar da dawakai tare da
rak’uma ta bud’e fuskar Bintu. Tuni Bintu ta zama mai arziki
da kadarori, su Ladiyo cikin ran su sai mamakin baiwa da Allah
yayiwa Bintu, su na jin ina ma dai su ne.
Bayan da matan Sarki suka gama budar ka, sai kuma sauran
‘yan uwa da abokan arziki, yayye da k’Annan Barde su ma su
ka nuna ta su bajimtar.
Bayan an gama ne Jakadiya ta mik’a wa matan Sarki tulu.
Matan sarki su ukun nan su ka tsaya bisa kan Bintu su na mai
tsiyayo mata ruwan cikin tulun kad’an kad’an bisa kan ta,
yayinda Jakadiya ke bada wak’a jama’ar wajan na amsa mata
“Ayyare daure jure
ayyaraye daure jure!
zaman gidan wani tilas ne!
ba kan ki ne aka fara
ba da kan ki ne aka fara ne
da kin ci kuka kin k’oshi
ke yar tsohuwa mai ‘yar tulu
Allah ya kar ki watan gobe
Mu ci gumba’’
[10/08, 11:59 AM] +234 808 323 2323: Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 10&11
Admin 001 Mukhtar Adam Nation
Tareda Naja’atu Lawal Rijau
@Whatsapp 08083232323 09060202323

1⃣0⃣
Sidiya ce….✍🏼
Ana gama wankan amarya Bintu ta ja jik’akken mayafin ta ta
rufe fuskar ta tana mai shar6ar kuka. Ba tare da 6ata lokaci ba
d’aya bayan d’aya sauran iyalan Sarki su ka dinga zuwa
Jakadiya na gabatar da su, har su ka k’are sannan aka rufe
taro da addu’a. Da aka gama maimakon a kai Bintu d’akin
auren ta, 6angare ne na musammam cikin gidan Sarki, sai
wani 6angare aka sake kai ta na daban daga cikin 6angaran
Goggon nan wanda ya kunshi d’aki biyu kowanne da bayi sai
kuma falo. Nan za ta zauna har sai sanda ta kai budurcin ta
d’akin mijin ta. Za6in bawai d’aya daga cikin bayin ta wanda za
su na kwana 6angaran ta aka bata. Gwaggo Munari ce ta za6a
mata Ladiyo dan kuwa ta fi yabawa da hankalin ta, sauran
kuma wuni za su na yi, idan lokacin bacci yayi ko kuwa Bintu
ta sallame su sai su koma 6angaran da aka tanadarwa bayi.
Yarima Barde kuwa duk wannan bikin da ake masa ya na daga
na sa 6angaran. Su Yarima Jafar da Khalil tun suna iya jure
shirun da ya mu su har su ma su ka gaji su ka yi na su gurin.
Da ya gaji da zaman ne ya watsa ruwa yayinda ya sanya
jallabiya, kai tsaye in da ya saba zuwa duk sanda ran sa ya ke
6ace ya nufa, wato lumbun da yake k’yatare da 6angaran
matan Sarki. Nan bisa dutse ya kusa raba dare, sai da ya ji
idanun sa sun masa nauyi sosai sannan ya tashi a hankali ya
nufi 6angaran sa. Ko da ya zo giftawa ta 6angaran da ya san
babu shakka nan aka sauki amaryar da aka aura ma sa, sai ya
tsinci kan sa ya na mai mummunar fad’uwar gaba. Hakan ya
sa shi wucewa da sauri ya na mai ambaton ubangiji. Bakin
kofar sa ya tadda dogarai da bayin sa sun yi jugum jugum
kasancewar ya mu su hani da biyo shi, ganin sa su ka fara
masa kiran lafiya su na mai fad’in
‘’takawa sannu Yarima Barde, lafiyarka dama da hauni, dama
da hauni lafiya, salamun salamun’’
Ganin ya zo daf da shiga kofar da za ta sada shi da 6angaran
sa, su ka taka masa baya, har ila yau fad’i su ke
‘’gicciye dama Yarima, gicciye salamun’’
Tsayawa Yarima Barde ya yi, ya d’aga mu su hannun alamar
baya buk’ata su biyo shi kafin ya sa kai ya shige ciki. Ya bar su
waje su na kallan kallo, dan kuwa sun san lamarin auren
Yarima Barde kan su zai k’are duk da dai ba su suka kar
zuman ba, rataya aka ba su.
Washagari da sassafe jama’ar Fabarusa, Samari da ‘Yan mata
har da tsuffin cikin adon su na burgewa su ka yi dandazo kofar
fada domin kallan hawan angonci bisa al’ada. Amma Yarima
Barde ya yi k’yememe ya ki fitowa ko da kuwa kofar 6angaran
sa ne bare a sa ran zai hau. Ko da su Khalil su ka je da numin
bashi baki, a bakin k’ofa dogarawa ma su tsaran kofar Yarima
Barde su ka fad’a mu su buk’atar Barde na kada a bawa kowa
damar isa gare shi. Dan haka sai hakura su ka yi, Magatakarda
ne yayi shela ga jama’a cewar Yarima Barde be shirya yin
hawan angoncin shi a ranar ba, su yi hakuri sai zuwa ran da ya
shirya za a sheda mu su. Da kyar kamar ba su hakura ba su ka
watse, dan ba k’aramin cin burin hawan angoncin Yarima
Barde su ka yi ba, kasancewa akwai k’auna tsakanin sa da
Talakawa, musammam ‘yan mata da samari, Yarima Barde na
su.
“Bayan hayaniyar kofar fada ta lafa, jama’a sun watse su
Gwaggo Munari da sauran tawagar Sa’ayrasa su ka yiwa iyalan
Sarkin Fabarusa sallama, an had’a mu su koma ta arziki
sannan su ka d’auki hanyar komawar su gida S’ayrasa, in da su
ka bar Bintu tare da bayin ta, wato Ladiyo, Hansai, lantana da
Maman Cangwai a sabon Masarauta. Gwaggo Munari ce ta
shedawa Iyalan Sarkin Sa’ayrasa irin tarbar da aka mu su da
tarin dukiyar da Bintu ta samu. Gimbiya K’amariyya kuwa sai
da ta had’a da kwanciyar asibiti. D’aya daga cikin bayin da su
ka juyo ne ta isar da sak’on Lantana ga Yarima Nuhu. Sakon na
cewa ta aikata komai yanda ya umarce ta, kuma komai ya tafi
daidai. Tsabagen dad’in sak’on na ta har kyautar zani da
kallabi ya bawa baiwar domin kuwa in har maganar hakan ta
ke babu shakka hakin sa ya cimma ruwa.
Kwanci tashi. Bintu ta cika sati guda Masarautar Fabarusa,
amma ko da wasa Yarima Barde be ta6a takowa in da ta ke
ba bare ma ta san kalar fuskar sa. Gata kuwa ta na sha gurin
matan Sarki, musammam Goggon dole da Uwarsoro ,domin
kuwannan su burin su ace amaryar Barde daga ta ta ce,
Maman Cangwai ce ke saka Bintu a hanya kasancewar ita ta
gane manufar su ba lalle alk’airi ba ne. Ita dai ta bi kowa
sannu a hankali. Goggon nan kuwa mulki da jin kan ta kad’ai
ya fi k’arfin ta, shi Yarima Barde ba gaban ta ya ke ba, bare
uwa uba matar sa.
1⃣1⃣
Sidiya ce…..✍🏼
Da hantsi Sarki Abdulrahman zaune bisa kujerar mulkin sa,
ana zaman fadanci sai ga Yarima Barde. Ganin sa Sarki be san
sanda ya murmusa ba, dan kuwa ya lura wasan 6uya Yarima
Barde ya ke da shi, idan har ba zaman fadanci ba ba ya ta6a
yarda su had’u da Sarki duk dan gudun duk wate magana da
ya shafi Bintu wanda tun da aka d’aura auren ba su sami
kye6ewa da Sarki ba bare su tattauna batun.
Sanye ya ke cikin fararan kaya an masa d’inkin hannu irin na
sarauta. Ya sha rawani irin na buzaye kai da ka gan shi ka ce
daga sahara ya ke. da shigowar sa dogarai su shiga yiwa Sarki
kiran lafiya su na mai sanar ma sa da isowar Barde
‘’ kimtsi gyara daidai alher, gyara kimtsi ga kyau’’
Gaban Sarki Yarima ya zube, hannun sa na dama dunk’ule ya
kai jinjina ga Sarki, dogarai fad’i su ke
‘’jinjine dama lafiya alher, an gaishe ka Yarima Barde’’
Da ga gefe kusa da Yarima Sadauki ya ja ya zauna. Nan fa aka
ci gaba da fadanci ana tattaunawa akan abin da ya shafi
cigaban al’umma da ma kuma matsalolin al’umma da yanda
za a magance su. Har aka yi aka k’are idanun Sarki na kan
Yarima Barde. Ko da Sarki zai tashi sai cewa yayi da Barde su
na san ya riske su a turakan su. Yayinda Sarki zai tashi dogarai
su ka rufe sarki ta hanyar baza babban rigunan su yanda ba
wanda zai iya ganin motsin sa bare tashin sa. Fad’i su ke
‘’ rangwame Tafsawa, sannu rangwame alher, lafiya Adali,
lafiya Mataimakin Musulunci, gyara kyamtsi ga kyau’’
Haka su na masa kiran lafiya har ya kai ga ficewa daga fada.
Bayan fitar sa ne Yarima ya kai gaisuwar sa ga sauran
Hakiman, ciki har da wanda ke masa Allah ya sanya alkhairi.
Ya zo fita kenan Yarima Sadauki ya shagaban sa, ganin sa
Yarima Barde ya Murmusa ya na mai dunkule hannun sa na
dama ya jinjinawa Sadauki sa’annan ya furta
‘’Sadauki ne kai’’
Cike da tak’ama, shi lalle Yarima mai jiran gado, Sadauki ya
maida masa da martani yanda ya saba ta hanyar fad’in
‘’kai ma Barde ne, musammam sa’in da na hau kujerar mulki’’
Barde be fasa murmushin da ya ke ga d’an uwan na sa ba duk
da kuwa ya san magana ya ke fad’a ma sa. Kana ya ce
‘’barka da hantsi, da fatan mu na lahiya’’
‘’lahiya lumi fa, ya kwanan amaryar dole? Ko da shike har yau
ba mu ji labarin budurcin ta ba bare mu ce ango ya sha
k’amshi, d’iyar abokan gaba ce duk da kuwa abun ba dambe
ba ne ba, kada Barde ya ba mu kunya!’’
Ya na gama fad’in haka ya yi gaba. D’if Yarima Barde ya
d’auke wuta, Khalil da ke tsaye daga bayan su, ya kuma ji
dukkannin maganan da Sadauki ya fad’a ne yayi saurin ta6a
kafad’ar Yarima Barde, kana ya ce
‘’ba kai an babba ba, amma babba gare ka Barden mahadi
maida garin wani kongo’’
Jin haka ya san hakuri Khalil ya ke ba shi. Ya ko yi na’am da
Khalil ta hanyar murmusawa ya na mai fad’in
‘’ina da muradin zuwa wucan gadi mutumi na, ko za mu sami
dama tafiya kafin na sami saduwa da Sukuku Bakaka(Sarki)’’
Cikin jin dad’i Yarima Barde ya fara sakewa Khalil ya nemo
Yarima Jafar domin su tafi wucan gadi.
Da yamma likis bayan Yarima Barde ya dawo daga wucan gadi
ya isa ga Sarki. Turakar Sarki su ka d’an ta6a hira sama sama,
kafin Sarki ya kawo batun Bintu ta hanyar tambayar
‘’ya amanar da mu ka ba ka? Shin an duba kuwa?’’
Barde na mai durk’usar da kai k’asa ya kasa magana. Ganin
haka Sarki ya fahimci in da ya dosa, kana ya ce
‘’kar ka damu d’an mu, ka bi sannu a hankali ba laifi ba ne,
amma dai mu na ruk’on ka da kar da mu zamo daga cikin
azzalumai ta hanyar d’auka lokaci mai tsayi, wannan gona ta
ka ce, kada ka manta akwai idanu dayawa bisa kan ta, da
fatan za ka kula a wadata ta, san samu ma a ziyarce ta ko da
kuwa daga yau zuwa kwana uku ne’’
Maganar Sarki ba k’aramin nauyi ta yiwa Barde ba, dan kuwa ji
ya ke ina ma zai iya masa musu ko da kuwa na sakan d’aya
ne, amma ina tsaintar kan sa yayi ya na mai fad’in
‘’an gama Sarkin yakin musulmi, bango madafan bayi’’
Sarki kuwa ba k’aramin jin dad’in yanda Barde ke masa
biyayya ya ke ba, cikin ran sa ya na mai jin ina ma shi ne
babban d’an sa ba Sadauki ba. Sai bayan da su ka idda salar
isha’i sannan Barde ya baro wajan Sarki. Kai tsaye lambun nan
da ya saba zama duk dare ya nufa, zuciyar sa na sak’a masa
yanda zai yi ya gujewa had’uwa da amaryar da aka d’aura
masa, wato kanwar budurwar sa.
🐫🐪🐫🐪🐫

Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 12
Admin 001 Sayyadi Sasiq
@Whatsapp 08146934644
1⃣2⃣
Sidiya ce…..✍🏼
6angarn Bintu kuwa kamar yanda ta saba, yau ma ta sallami
dukkanin bayin ta, ya rage daga ita sai Ladiyo, wacce ita dama
d’aki d’aya su ke kwana idan ta tabbatar kowa ya d’auke k’afa,
tsabagen tsoro da rashin sabon kwana ita kadai. Bintu na
kwance bisa gadon ta, tunanin Innar ta ta take da rayuwar ta
na da wanda shi ya fi mata dad’i akan wannan daula da ta
tsinci kan ta a ciki. Ladiyo da ke tsaye bisa taga idanun ta kan
hanyar lambun da ke kyetare da 6angaran Bintu, sai ajiyar
zuciya ta ke ba tare da ta san ta na yi ba saboda tsabagen
muradin sake zuwa lambum da ya addabi zuciyar ta, ba dan
komai ba ko dan ta ga wannan buzun da ta gani ciki mai irin
sifar aljanu tsabagen kyauwu.
Gashi ran da ta fara shiga lambun satar hanya ta yi bayan Bintu
ta yi bacci ta ga wucewar sa, kasancewar shi kad’ai ne ya sa
ta yi tunanin kila talakan Sarki ne, wanda su ke da daurin gindi
wajan fadawan Sarki ko kuwa d’aya daga cikin ‘ya’yan
hakiman masarautar nan. Nan ta gan shi zaune bisa kan dutse
ya na sakar zuci, har ta k’are masa kallo be san ta na yi ba
tajuya tana tasbihi ga Allah bisa tsarin halitta da yayiwa bawan
Allah nan.
A hankali ta kai kallan ta ga Bintu, kana ta ce
‘’gide Gimbiya ba ki da muradin ganin farin wata ne? aradu
zaman cikin kurya ya ishe ni’’
Jin haka Bintu ta yi farat ta tashi zaune ta na fad’in
‘’yo to Ladiyo mu tai mana, ba tun yau na ke da muradin mik’e
k’afa, kwankwatsi ni ma na gaji da zaman nan, hallo ki na ga
babu matsala aka gan ni a rariya?’’
Abun da Ladiyo ke so ta samu duk da kuwa ba ta yi
tsammanin haka daga wajan Bintu, ko da shike dama ai d’iyar
bayi ce Ladiyo din ce ke sha’afa. Ta yi saurin dawowa gaban
Bintu jiki na rawa ta ce da ita
‘’gide ai da yawa ba su san fuskar ki ba, ba na jin za su waye
ki, kai in ki na son badda kama ma zai fi na ara mi ki d’aya
daga cikin kaya na na bayi……idan fa Gimbiya za ta iya
sanyawa’’
Ta k’arasa ne cikin d’ard’ar kada Bintu ta ce ta raina ta, duk
dai ita kan ta ta san babu laifi Bintu ba ta canza mata ba, in
har ba wai akwai mutane gun ba yanda ta saba mata tun tana
baiwar ta hakan ta ke ma ta. Ga mamakin Ladiyo sai gani ta yi
Bintu ta tashi cikin hanzari ta na mai fad’in
‘’kayya ku ji mu da Ladiyo da yasasshen zance, tuwo ne towo
ba a sake masa suna, maza d’auko mu tai ko ba komai na
sha iska’’
Cike da farin ciki Ladiyo ta da’aukowa Bintu d’aya daga cikin
kayan ta na bayi, kan kace me sai ga Bintu ta koma gidan ta
na da, wato shigar kayan bayin Sa’ayrasa, Ladiyo har ta na
mata tsiyan ya ta ga kayan sun kar6e ta sun zauna jikin ta
sosai, ko da shike daga jikin ne.
Bintu na duban kan ta cikin madubi, idanun ta cike da kwalla
ta ce
‘’Allah Sarki wata rana, aradu Ladiyo na fi san rayuwa ta a da
akan wagga sabuwar rayuwar’’
‘’yo to Bintu ina ga cigaba ki ka samu, wani sa’ilin sai na ji
dama ni ce ke aradu da kin ga yanda ake tsiya da mulki. Mu
tai dan Allah kar wani abun ya zo ya sa mu fasa hita’’
Bintu na me goge kwalla ta bi bayan Ladiyo. Daga waje su ka
tadda bayi mata wanda Goggon nan ta bawa Bintu zaune.
Ganin su sai da Bintu ta ja da baya gudun kar da su waye ta.
Ladiyo ce ta yi maza ta ja hannun ta tana mai fad’in
‘’barkan ku da dare’’
‘’barka dai Ladiyo, an fito shan iska ne?’’
Su ka amsa mata amma idanun su na kan Bintu. Ladiyo ta ce
‘’eh Gimbiya na da muradin a bar ta ita kadai’’
Kai su ka jinjina su na mai musu fatan dawowa lafiya. Har sun
yi gaba su tsaida su ta hanyar fad’in
‘’ba ku ji ba’’
Cak su ka tsaya, Bintu na mai rawan jiki, cikin ran ta fad’i ta ke
‘’shikenan sun gane ni’’
Ita kanta Ladiyo mutawar tsaye ta yi ta na jiran tsammani.
D’aya daga cikin bayin ce ta matso gare su kana ta ce
‘’Ladiyo wagga baiwar ban waye ta, shin ko ita ce Lantana?’’
Ta na magana ne yayinda ta ke k’ok’arin ganin fuskar Bintu
wacce ta 6uya cikin duhu. Ladiyo na mai sosa k’yeya ta ce
‘’ah ah wagga Batula sunan ta’’
‘’Batula?’’
Baiwa ta sake maimaitawa, Ladiyo ta jinjina kai kafin ta ja
hannun Bintu su ka yi gaba ta na fad’in
‘’bari dai mu je mu dawo….’’
Ko da su ka k’urewa ganin bayin sannan su ka karya kwanar da
za ta sada su ga lambu, har lokacin gaban Bintu be dena
fad’uwa ba, haka kuma Ladiyo ba ta fasa mitar gulma irin na
bayin Fabarusa ba.
Hankalin Bintu be kyauta ba sai da ta tsinci kan ta cikin lambu.
Lambu ne mai ban sha’awa wanda ya sha ado da bishoyin
kayin marmari iri daban daban. Hasken wata da yayi fari kal a
tare da hasken lantarkin da ke daga cikin kowacce kusurwa na
cikin lambun ba k’aramin k’ayata shi yayi ba. In ban da koken
tsuntsaye da na kwari babu abun da ke tashi cikin lambun.
Tuni Ladiyo ta shiga raba ido ko Allah ya sa ta ga wannan
mutumin, ita kuwa Bintu wani dutse ta samu ta yi zaman ta kai
ta na fad’in
‘’kai Ladiyo wagga lambu ba dai ni’ima ba, ni dai na yi wajan
zama daga nan’’
Ladiyo na mai raba idanu ta ce da Bintu ita dai za ta d’an taka
to, yanzu za ta dawo. Nan bisa dutse ta bar Bintu yayinda ta
kutsa cikin lambu domin neman wannan mutumin.
Barde kuwa da daman shi Ladiyo ke nema zaman Lambun ne
ya ishe shi, gaba d’aya ya kasa samin nutsuwa. A hankali ya ke
shawagi cikin lambu, wani irin wari ya ji yana bak’untar hancin
sa sannu a hankali, tun ya na iya jurewa har ya kasa ya yanke
hukuncin ficewa daga Lambun gaba d’aya dan kuwa warin ya
fi k’arfin na mataccen dabba. Ko da ya d’auki hanyar fita daga
Lambun nan ya ji wari na k’ara gabato shi. Nan bisa dutse yayi
kaci6us da ita kishingide, idanun ta runtse tamakar mai bacci,
hakan nan wani irin wari da tun da yazo duniya be ta6a jin irin
sa ba ya daki hancin sa har sai da ya ja baya da sauri wanda
k’aran sautin motsin na sa ya sa Bintu bud’e idanun ta yayinda
ta kai kallan ta ga kyakkawan buzun da ke tsaye gaban ta,
hannayen sa biyu bisa hancin sa da alama yana k’ok’arin kare
hancin daga jin wari ne.
🐫🐪🐫🐪🐫🐪

Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 14
Admin 00 Sayyadi Sadiq
@Whatsapp 08146934644

1⃣4⃣
Sidiya ce…✍🏼
Barde kuwa a nasa 6angaran komawar sa turakar sa har da
amai. Hankanlin sa be kwanta ba sai da ya amayar da
dukkanin abun da ke cikin sa. Abun da ya ke bashi mamaki be
wuce yanda yaji dan adam ya na wari kamar na mushe ko
kuwa ja6a ba, daga ganin shigar ta ya san baiwa ce sai dai ba
irin kalar shigar bayin Fabarusa ba ne, ko koma baiwar wata
masarauta ce dole ya sa a nemo masa ita a sallame ta daga
cikin fada ta je ta nemi magani gyambon da ke jikin ta idan dai
ba so ake kar shi har lahira ba. Da wannan ya sami mafakar
rashin zuwa ya ga amaryar sa, yayi kwanciyar sa abun sa.
Washagari da sassafe Jakadiya ta je masa da karin kumallo
na musammam bisa ga umarnin Sarki Abdulrahman. Wanda
Yarima Barde ya san ba komai ba ne illa tambayar
‘’shin ka je wa matar ka?’’
Saboda haka ko da Jakadiya ta tashi tafiya sai Yarima Barde
ya bata sak’o zuwa ga Gimbiya Fatima, ya na mai fad’in
‘’a shedawa Gimbiya Fatima, bayan gaisuwa da fatan ta na
lafiya, ta saurari zuwan mu bayan fad’uwar rana, kada ta
tsawaita buri ba ma buk’atar komai daga gare ta’’
Kalaman da Barde ya k’arasa da su be hana Jakadiya
rangwad’a gud’a ba, dan kuwa ta san tabbas idan aka juri kai
zuga gabas wata ran ta zo da ruwa. Ai kuwa ko da sak’on
ziyarar Barde ya riski su Bintu, nan fa Bintu ta ga ta kan ta dan
kuwa tun da safiyar Manman Cangwai ta shiga gyara ta da su
turarukan wuta, tsimi ne da cukwid’i kai har da wanda ma ba
a sa ta ba, domin fa Maman Cangwai ita ta na da nata
manufar na musammam cikin ran ta na game da Bintu, sai dai
sa6anin sauran ita kad’ai ke san Bintu da alkhairi.
In dan ban da fad’uwar gaba babu abin da Bintu ta ke, bini bini
ta ke duba lokaci ta na mai fargabar fad’uwar rana da abun da
za ta zo mata da shi na daga ziyarar Yariman Fabarusa. Haka
kuma kaman nin wannan da ta gani cikin lambu be dena mata
gizo ba, da za ta sami dama ko shakka babu ta na komawa
cikin lambu ko Allah ya sa ya k’ara bayyana a gare ta.
Yarima Barde ma cikin zulumin had’u da k’anwar Gimbiya
K’amariyya a matsayin matar shi ya wuni. Rana na fad’uwa ya
shirya cikin shigar sa na saraki, biye da shi amintaccan bawan
sa ne wanda ake kira Bakar namba, su ka nufi 6angaran su
Bintu.
Lifaya fara kyal Bintu ta d’aura bayan ta sha turaruka na hayaki
da humra. Ta na daga zaune bisa gado gaban ta na fad’uwa
tsabagen fargaba ji ta ke kamar ta zura a guje. Maman
Cangwai ce ta sa ta a gaba ta na ta jera mata bayanai tare da
kashedi, fad’i ta ke
‘’kin san dai ke d’iyar Sarki ce ba d’iyar bayi ba, ki kasance
mai rowar muryar ki a gare shi, ban da yawan surutu in dai ba
ya zama dole ba, ki kasance gwanar iya kalamai duk san da
zaki bud’i baki ki yi furuci, ki tabbatar kin tauna kin juya kan ta
hito daga leban ki………’’
Daga waje tun isowar Yarima 6angaran na Bintu warin nan da
ya ji a lambu ya fara bakuntar hancin sa, hankalin sa ne ya fara
tashi yayinda ya ji bugun zuciyar sa na dad’a k’aruwa. Cikin
wannan hali ya yi tsaye bakin k’ofar falon Bintu, yayinda bak’ar
namba ya shiga kwad’a sallama.
Ladiyo na mai amsa sallamar ta fito, ganin wanda ke gaban ta
tsaye ta yi ta na duban sa. Sanye ya ke cikin fara Jabba wanda
aka mata ado da koran zare, bisa babban rigar sa ce na
dokakkiyar shadda fara kyal sai d’aukan ido ya ke. Haka
rawanin da ke bisa kan sa irin na buzaye zuwa huffin da ke
sanye cikin k’afafun sa farare ne kyal kai ka ce shirya shi aka
yi.
Ganin ta saki la66a da su ga66a ta na duban Barde, ba ta da
niyar motsawa bare ta kai gaisuwar ta gare shi, ya sanya Bakar
numba fad’in
‘’hattara d’iyar talakawa! Yarima Barden Mahadi shi an gaban
ki’’
Tuni Ladiyo ta zu6e k’asa jin buzun nan dai ba kowa ba ne illa
mijin Bintu, fad’i ta ke
‘’tuba na ke Yarima, Allah ya huci ran Yarima, babban Barde
babban bako’’
Shi kuwa Barde ganin tufar jikin ta ne ya dad’a d’aga masa
hankali ba wai yanda ta masa ba, dan kuwa tabbasa wannan
baiwar mai wari da yayi arba da ita cikin lambu a daran jiya
irin shigar ta kenan. Idan kuwa haka ne to lalle d’aya daga
cikin bayin matar da aka aura masa ne ke wannan mugun
warin da ke neman halaka shi.
Bakar numba ne ya amsa da
‘’an gaishe ki d’iyar talakawa, ki shedawa Gimbiya Fatima
Yarima Barde na neman iso gare ta’’
Da sauri Ladiyo ta tashi har tana hard’ewa, yayinda ta ke fad’in
‘’an gama ran Yarima ya dad’e’’
Ciki ta shige jiki na rawa, ta tadda bayin da ke hidima cikin
falo wanda k’atuwar muryar Bakar numba ya sanar mu su da
isowar Barde, kowannan su ya nutsu jere cikin sahu,
musammam bayin Fabarusa wanda dama sun fi na Sa’ayrsa
sanin darajar Barde. Kai tsaye cikin d’akin Bintu Ladiyo ta
shige ta na mai zubewa k’asa gaban Bintu dan kuwa ganin
Barde ya sa ta tsorata da sa’a tare da nasarar da ke tattare da
d’iyar bayi
‘’ran Gimbiya ya dad’e, Yarima Barde ya iso ya na mai neman
iso gare ki Gimbiya’’
🐫🐪🐫🐪🐫🐪

Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 15
Admin 001 Sayyadi Sadiq
@Whatsapp 08146934644

GARGA’DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA
YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI ‘DAUKE TAMBARIN
SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA
NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN
ALLAH MU KIYAYE.
1⃣5⃣
Sidiya ce…✍🏼
Jin haka hankalin Bintu ya tashi, cike da fargaba ta kai duban
ta ga Maman Cangwai, wacce ta gane halin da Bintu ta ke ciki
kana ta ce
‘’ki nuna masa hanya ya iso gare ta, ni da sauran bayi za mu
tsaya daga wancan d’aki, ke kuma Ladiyo da ke ku tsaya
daga wajen kofa kafin Gimbiya ta sallame ki’’
Cikin rawan jiki Ladiyo ta tashi ta na mai fad’in
‘’an gama ran gimbiya shi dad’e’’
Ko da ta koma gun su Yarima Barde, Maman Cangwai ce ta
fito da kan ta ta sallami sauran bayi zuwa ga d’ayan d’akin,
duk da kuwa bayin Sa’ayrasa ba haka su ka so ba, su ma dai
so suke su ga Yarima Barden nan da jama’a ke yawan
ambaton sa wajan kyawu. Ladiyo a gaba, biye da Ita Yarima
Barde ne in da shi kuma Bakar numb ya tsaya daga waje, su
ka shigo falon Bintu.
Warin nan da ke d’aga masa hankali shi ya ke bunk’asa ya na
dad’a bakuntar hancin shi duk sanda ya d’aga k’afa ya sauke a
falon. Isar su tsakiyar falon Yarima Barde ya tsaya cak, ga
mamakin Ladiyo ji ta ya furta
‘’gide bayi masu shiga irin ta ki nawa ne cikin wanga turaka?’’
Ladiyo na mai susa k’yeya yayinda ta shiga kame kame ta
cikin fargabar kar dai ya gane ita ce mai bin bayan sa cikin
lambu ta yi saurin fad’in
‘’iye na’am? Mu na da d’an dama ran Yarima Barde ya dad’e,
wagga shiga ita an shigar bayin Sa’ayrasa, dukkanin mu wagga
shiga mu ka yi Allah shi da ran Yarima’’
Yarima Barde na mai duban ta ya ke d’an tuntuntuni, dan kuwa
ko shakka babu ya san wagga baiwa ta gaban sa ba ita ce mai
warin da ya gani a lambu jiya ba, duk da dai be ga fuskar
waccan da kyau ba amma ya san a jiki waccan tafi domin
kuwa Ladiyo irin k’ananan matan nan ne. Shi kuma a yanzu be
da buri da ya wuce ya gano baiwar nan da ke wari ko ya sami
lafiya domin kuwa muddun ta na nan ba zai iya zama ko da na
minti hud’u a turakar amaryar ta sa ba, abun mamaki shi ne ta
yaya bayin Gimbiya kamar Fatima za su na zama da wari har
haka ba tare da ta d’auki mataki ba? Hakan ke tabbatar masa
da k’azantar da ke tattare da ita.
Juyawa yayi ba tare da ya sake tankawa Ladiyo ba, wacce ta yi
kasake ta na duban sa ta rasa yanda za ta yi da ran ta, ganin
dai da gaske ficewar ya ke ta bi bayan sa da sauri, amma ina
kan ta cima su tuni ya d’au hanya, Bakar numba biye da shi.
Da gudun ta ta dawo d’akin Bintu in da ta zu6e k’asa ta na
kuka fad’i ta ke
‘’ki min rai Gimbiya, kwankwatsi ban san shi an Yarima Barde
ba, aradu da na san shi na da ban bi bayan shi ba, in k’arya na
ka yi aratta kashe ni’’
Cike da mamaki Bintu ta yane lifaya da ta rufe fuskar ta,
tambaya ta ke
‘’gide lafiya? Yo to minana? Mi Yariman yay mi ki da har ya
sanya ki kuka Ladiyo? Ina Yariman ya ke?’’
Ladiyo wacce duk a zatan ta Yarima Barde ya gano ta ne ran
sa ya 6aci har ya juya ya fasa ganin Bintu ta ce
‘’ Yarima Barde ya juya ya koma, ki min rai kar ya sa a tsire ni,
ina ni ina lek’en surrun Yarima Barde, ki taimaka ki min rai,
wayyo ni Ladiyo sai kuma yanda aka yi da ni d’an daudu a
kabari’’
Ganin dai Ladiyo ba ta da niyar bata cikakkiyar amsa ya sanya
Bintu tashi ta fita da kan ta, ita ma Ladiyo bayan ta ta biyo
wanda kukan ta ya sa sauran bayi fitowa. Maman Cangwai na
mai tambayar ko lafiya? Ina Yariman ya ke? shin me ya fito da
Bintu daga uwar d’aka ita kuma Ladiyo kukan me ta ke?
Kasa amsa mu su Ladiyo ta yi har sai da Maman Cangwai ta
daka mata tsawa sannan ta iya labarta mu su yanda ta bi
bayan Yarima Barde zuwa Lambu ba tare da ta fad’i jan Bintu
zuwa lambu da ta yi ba, yanzu haka ya gano ita ta ke lek’en
asirin sa.
Cikin jimami kowa ya ke duban Ladiyo wacce ta had’a zufa,
hawaye da majina. Ita kuwa Bintu waje ta samu ta zauna cikin
neman mafita, dan kuwa muddin abun da Ladiyo ta fad’a
gaskiya ne, ko shakka babu dole sai an hukun ta ta, lek’en
asirin Yarima ba k’aramin laifi ba ne, za a iya amfani da
wannan ace so ta ke ta idda wani mugun nufi kan sa ko kuwa
dai ta ha’d’a baki da abokan gaba ta na san halaka shi.
Yarima Barde kuwa da fitar sa kai tsaye gun Jakadiya ya nufa.
Ya tadda ta bisa sallaya tana lazumi kan ta zo ta shiryawa
sarki sauwar dare. Ganin Barde ta san da matsala wanda shi
ma be 6oye mata ba ya sheda mata cikin azanci ba tare da ya
fayyace mata komai ba.
‘’ya Jakadiya, a had’a fanteka na turaruka, na jiki zuwa na
kaya, a aika ga Gimbiyar Sa’ayrasa, a kuma sheda mata
Yarima Barde ma’abocin k’amshi da tsafta ne, ta gaggauta
sauya gimshikin kusurwar ta’’
Cewar Yarima Barde, wanda ya juya ya tafi ba tare da ya tsaya
amsa tambayoyin da Jakadiya ke shirin jera masa ba. Abun da
kuwa ya fi d’aure mata kai shi ne fantekar turaren da za a kai,
ga kuma batun na Barde na Bintu ta gaggauta sauya gimshikin
kusuwar ta, ko shakka babu Barde ya ji wari daga wani
6angare na Bintu ko kuwa bayin da ke tattare da ita.
Ba tare da 6ata lokaci ba Jakadiya ta aikata yanda Barde ya
ce. Cikin baitul mali ta shiga, daga cikin daular iyalan Sarki
Abdulrahman ta jido turarurruka fanteka guda, cikin bayi ta
za6i wacce ta fi tsana sannan ta d’aura mata fanteka ta tere
da bata sakon Barde zuwa ga Bintu. Jin sak’on da aka bata sai
ga baiwa a k’asa ta na yiwa Jakadiya magiya da kada ta tura ta
da wannan mugun aike, amma ina sai ma tafiyar ta yi ta barta
ta na share hawaye dan kuwa dai ta ta ce ta same ta kishiya
tara rana d’aya.
🐫🐪🐫🐪🐫🐪

Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 16
Admin 001 Sayyadi Sadiq
Whasssp. 08146934644

1⃣6⃣
Sidiya ce…✍🏼
Ta na tafe ta na hawaye haka ta isa 6angaran Bintu in da ta
tadda Ladiyo zaune gaban Bintu ta sha kuka ta k’oshi, daga
gefan Bintu kuwa Maman Cangwai ce zaune a k’asa, d’ayan
6angaran Hansai da lantana ne zaune. Bintu ta sallami
dukkanin bayin Fabarusa domin samarwa Ladiyo masalaha.
A gaban Bintu baiwa ta aje fanteka ta na mai rawan jiki, tun
gaisuwar da ta kai ga Bintu, bakin ta na motsi amma tsoro da
kwarjinin Bintu ya sa ta kasa furta komai. Maman Cangwai na
me duban ta ta furta
‘’ke mu ke sauraro ya ke d’iyar Fabarusa….’’
Maimakon Baiwa ta fad’i dalilin zuwan ta da kuma sak’on
Barde, sai gani su ka yi ta fashe da kuka ta na mai fad’in
‘’tuba na ke ran Gimbiya ya dad’e, ki min rai na tuba ki rufa
min asiri, tuba na ke’’
Nan fa su Ladiyo da lantana su ka shiga kallan kallo cike da
mamaki. Bintu ma mamaki ya ne ya lullu6e ta, cikin ba da
umarni ta ce da Maman Cangwai ta bud’e fantekar ta ga abun
da baiwar ke tafe da shi. Ko da Maman Cangwai ta bud’e
fanteka sai da gaban ta ya fad’i ganin turaruka iri daban daban
masu yawa ciki. A hankali ta kai kallan ta ga Bintu wacce ita
ma ta hango me ke cikin fantekar kafin ta maida kallan ta ga
baiwar, kana ta furta
‘’wannan kuma daga ina?’’
Baiwa ba ta fasa hawaye ba ta furta
‘’gide sak’o ne daga Yarima Barde zuwa ga Gimbiya Fatima,
hallo ya na mai sheda mata cewar Yarima Barde ma’abocin
k’amshi da tsafta ne, ta gaggauta sauya gimshikin kusurwar
ta…….’’
Ta k’arasa furucin na ta ne cikin rawan murya. Shiru kake ji
babu mahalukin da ya furta komai tsabagen bazata da kalamin
baiwar ya mu su, babu shakka Barde na me shedawa Bintu
wani abu daga 6angaran ta ya na wari duk da dai be fayyace
mata ko menene ba, wanda turo fantekar turaren da yayi ba
k’aramin cin fuska a gare ta ba ne, ba dan ma an riga an
d’aura mu su aure ba da hakan daidai ya ke da ya ce ya fasa
auren ta saboda wari da ya ji na daga wani 6angare da ya
shafe ta.
Sai a sannan Maman Cangwai ta gane kukan da baiwa ta ke,
dan kuwa a k’aida ya zama dole Bintu ta hukunta ta bisa ga
sak’on cin fuska da ta iya duban tsabar idanun Bintu ta sheda
mata, in kuwa ta yi sake ta rabu da ita salin alin, toh tabbas ta
siyawa kan ta raini daga kan jama’ar fada har izuwa sauran
bayin na fada babu wanda za ta k’ara yiwa kwarjini bare a ji
shakkar ta.
Jin Bintu ba ta furta komai ba Maman Cangwai ta dawo daga
gefan ta, in da ta zauna kamar me jiran umarni daga Bintu, a
kaikaice yanda baiwar ba za ta fahimta ba ta ce da Bintu
‘’hattara Gimbiya, wanga batu ba na sassauci ba ne, dan haka
zan ari bakin ki in ci albasa, ina mai neman alfarma rashin
maganar ki bisa hukumcin da zan aiwatar kan wagga baiwa ta
fabarusa’’
Ba tare da ta jira amsar Bintu ba ta mayar da kallan ta ga
baiwa, sannan ta ce
‘’bisa ga umarnin Gimbiya, ta yaba da kyautar Yarima a gare ta,
sa’annan wagga baiwa da ta kawo sak’o gare ta, zaki amshi
bulala hamsin na daga tsimagiyan Gimbiya Fatima’’
Da sauri Bintu ta kai kallan ta ga Maman Cangwai cike da
6acin ran jin furucin na ta ta yi k’ok’arin dakatar da ita, wanda
hakan ya sa Maman Cangwai saurin fad’in
‘’na yi kuskure Gimbiya, bulala sittin Gimbiya ta ke nufi, maza
Lanta tashi ku fitar da ita zuwa d’akin horo, ki kuma sheda ma
su umarnin Gimbiya kowa ya ji ya gani ya kuma sheda!’’
Baiwa na kuka ta na fad’in
‘’tuba na ke ran Gimbiya ya dad’e’’
yayinda Lantana ta tasa ta gaba, ta na mai fad’in
‘’godiya ta ke Allah shi taimaki Gimbiya’’
Su na fita hawayen da ya ciki idanun Bintu tuni ya gangaro
bisa kuncin ta tsabagen tausayin baiwa da ba ta san hawa ba
ba ta san sauka ba an k’ak’aba mata horo tsabagen rashin
adalci. Cike da 6acin ran da ita kan ta Maman Cangwai ba ta
san Bintu na da irin wannan fushin ba, ta furta
‘’akan wani dalili za a yiwa baiwa horo? Gide ita na ta ba sak’o
ba ne? idan adalci ne na lalle sai kin nuna an min ba daidai ba
ki hukunta shi Barde wanda ya aiko ta mana? Saboda ita baiwa
ce? Su bayi ba su ‘yanci? Bayi su an bola?’’
Jiki a sanyaye Maman Cangwau ta furta
‘’hakan da na yi kad’ai zai nuna matsayin ki na d’iyar sarki,
dan kuwa babu d’iyar sarakin da za a yiwa wanga cin fuska ta
kasa aikata yanda na aikata, in ba dai so ki ke asiri ya tonu ba.
Na san yanda ki ke ji, amma fa kada ki manta ko nima baiwar
ce, ina fatan za ki fahimce ni…..’’
A fusace Bintu ta tashi tsaye, ta na mai girgiza kai ta ce da
Maman Cangwai
‘’ba zan ta6a fahimtar ki ba in dai bisa zalinci ne, ba da
yawuna ki ka aiwatar da hukuncin ga ba, umarni na anan shi
ne ki gaggauta dagatar da shi!’’
A fusace ta wuce d’akin ta, wanda kan ta kai ga shiga
sallamar wata baiwa ya tsaida ita. Ta na ji baiwar na gaishe ta
amma 6acin ya sa ta kasa amsawa ta d’aga k’afa za ta shige
kenan amma jin furucin na baiwar ne ya tsada ta. Jin ta na
fad’in
‘’Yarima Sadauki ya na da murad’in ganin dukkanin bayin
Sa’ayrasa!’’
A hankali Bintu ta juyo, wato 6acin ran da take ciki ya sanya ta
rikidewa hatta Maman Cangwai, bare kuma su Ladiyo, tashi
guda ta tashi daga Bintun da su ka sani ta zame mu su wata
daban mai wuyan fasaltuwa. Ta na mai duban baiwar ta furta
‘’wa an Sadauki? A matsayin sa nawa ya ke da muradin ganin
bayin Sa’ayrasa gide? Akan wani dalili?
Baiwa ta yi jim dan kuwa ta tsorata da yanayin da ta ga fuskar
Bintu, cike da 6acin rai da kwarjini ga kuma tambayoyi na
gadara da ta mata akan Yarima Sadauki. Nisawa ta yi kafin ta
amsa mata da
‘’Allah huci zuciyar Gimbiya, Yarima Sadauki shi an Yaya ga
Yarima Barde wanda ya ke maigida a gare ki, dalilin sa na
murad’in ganin bayin Sa’ayrasa shi kad’ai ya barwa kan sa
sani’’
Bintu na mai jinjina kai ta ce da baiwa
‘’ki koma ki shedawa Sadauki ni Fatima na ce bayin Sa’ayrasa
ba za su isa gare shi ba muddin be zo mana da
gamshashshiyar dalilin sa na murad’in hakan ba!’’
🐫🐪🐫🐪🐫

Bintu ɗiyar bayi ce (book 2) Chapter 17
Admin 001 Sayyed Sadiq
@Whatsapp 08146934644

1⃣7⃣
Sidiya ce…✍🏼
Bintu na k’arasa magana ta shige uwar d’aka. Baiwa kuwa
tashi ta yi cikin jinjina maganar ta na mai gyad’a kai ta fice ta
bar Manman Cangwai da su Ladiyo cikie da mamakin sauyin
Bintu lokaci guda duk akan kishin bayi. Minti kad’an sai ga ta
ta fito sanye da lifayar nan da ta cire kafafun ta sanye da cikin
farin takalmin fata ta ce da Ladiyo
‘’wuce mu tai d’akin horo’’
Da sauri Ladiyo ta yi gaba Bintu na biye da ita, ita kuwa
Maman Cangwai bin Bintu ta yi da ido, cikin ran ta kuwa fad’i
ta ke lalle dole ta aika da sak’on neman taimako Sa’ayrasa
domin kuwa alamu ya nuna Bintu mai yin gaban kan ta ce.
Cikin sak’ar zuci Sadauki wanda ke zaune bisa daddumar da
ke shimfid’e a lambu ya ke duban baiwar da ta zo masa da
amsar Bintu gare shi. D’aya da ka cikin bayin sa ne ya furta
‘’gide Gimbiya d’iyar Sa’ayrasa ba ta da masaniya akan girman
Yarima Sadauki, ko shakka babu za ta tuba Allah shi taimaki
Yarima’’
Baiwa na mai gyad’a kai cikin amincewa da maganar na
bawan ta ce
‘’kwaran gaske, tuba ta ke ran Yarima ya dad’e’’
Murmushin mugunta Yarima Sadauki ya saki, cikin ran sa ya
na mai jaddada dana sanin da Bintu za ta yi bisa ga kuskuran
da ta yi a gare shi, tabbas ta tari aradu da ka dama dai ta bar
abin ya tsaya ga mijin ta da ya fi mata sauk’i, zai kuwa nuna
mata bakin rijiya ba wajan wasan makaho ba ne. Mik’ewa yayi
tsaye yayinda bawan sa yayi saurin matso da takalman sa
gaban sa. Cike da tak’ama ya sanya bayi na masu ram masa
baya su ka d’au hanyar fita.
‘Dakin Horo kuwa Lantana ce ta idda sak’on Maman Cangwai,
nan da nan kuwa Dogarin horo ya shiga gyara tsumagiyar sa
domin aiwatar da umarnin Gimbiya Fatima. Sauran bayi fada
kuwa tuni labari ya zaga, sun yi tattaki zuwa d’akin haro
domin ganin yanda baiwa za ta fuskanci hukunci. Kujerar horo
aka sanya baiwa ta zauna yayinda aka zuba mata ruwa bisa
cinyar ta har zuwa k’asan k’afafun ta yanda ko da zafin
tsumagiya zai sa fitsari ku6uce mata ba zai nuna ba. Waje yayi
tsit kuka baiwa kad’ai ke tashi yayinda Dogarin horo ya d’aga
tsumagiyar sa ya na shirin sauke ta bisa cinyar baiwa muryar
Ladiyo ya dakatar da shi ta hanyar fad’in
‘’dakata Dogarin horo, Gimbiya Fatima ce tafe!’’
Tsayawa yayi cak yayinda Bintu ta taho, bayi na bud’a mata
hanya haka kuma ba su fasa kai gaisuwa gare ta ba har ta iso
gaban dogarin horo. Cikin bayin kuwa har da Bakar number
wato babban bawan Barde wanda jin an ambato sunan Bintu
ya shiga baza ido domin ganin matar uban gidan sa.
Ganin Bintu gaban sa Dogarin horo ya saki tsumagiya k’asa ya
na mai kai gaisuwar sa ga Bintu ta hanyar nuna ladabi da
mik’a kai a gare ta cikin aminci. Bintu na duban baiwar da ta
had’a hawaye da majina, a hankali ta k’asara gare ta, hannu ta
sanya ta tada ita tsaye kana ta ce
‘’gide bar kukan ga haka, wagga hukunci baya bisa kan ki,
maza tai abun ki, idan uwar gijiya ba ta zama mai tausayawa
ga bayin ta ba shin ana tunanin za mu sami tausaya daga mai
duka wanda mu an bayi gare shi?’’
Jin haka bayi su ka hau sowa, shewa da tafi, daga masu fad’in
‘’Allah shi ta ya mi ki, Allahu y ja da ran gimbiya, Allah ya sa ki
dad’e ki na yi’’
Sai masu fad’in
‘’madallah da Gimbiyar Sa’ayrasa, mun biki, mu na madallah
da ke’’
Ita kuwa baiwa ba ta san sa’in da ta zube k’asa hannayen ta
rungume da k’afafun Bintu tsabagen farin ciki ma kasa
magana ta yi. Bintu na mai murmushi a gare ta tare da duk
kanin sauran bayi da ke wajan ta zame k’afafunta, bayi na mai
darewa domin su bata hanya cike da nuna k’aunar su gare ta
haka ta d’auki hanyar komawa turakar ta.
Babban bawan Barde da tun kan Bintu ta bar wajan ya ruga
domin komawa ga Barde, tuni ya labarta masa yanda ta
kasance tsakanin Bintu da bayi, ya k’are da
‘’lillahi warasulihi Gimbiya Fatima ta isa d’iya adala wacce ta
san darajar bayi ko shakka babu halayyar ta ya yi
kamanceceniya da na ka ran ka shi dad’e, aradu ma kuwa.
Bayin Fabarusa za su zama su na alfahari da ita tun daga rana
ita yau’’
Barde na mai duban Bakar number, duk maganar nan da ya ke
hankalin sa ba gun sa ya ke ba, tunanin K’amariyya ne ya
addabi ran sa ya na mai takaicin ina ma dai ita aka d’aura
masa ba k’anwar ta ba, shin da wani ido ake so ya dube ta a
matsayin mata har ya kai ga kusantar ta?
****
Sadauki da tashi tawagar kuma a nasu 6angaran fitowar shi
daga lambu bayan ya gama d’an shawagin sa ya na mai
tunanin matakin da zai d’auka bisa matar Barde ya hangi Bintu
da Ladiyo a kan hanyar su na komawa turaka. Tsayawa yayi
cak idanun sa bisa Bintu ba komai ya ja hankalin sa ba sai
yanayin zubi da tafiyar Bintu da ya gani iri d’aya sak da na
baiwar nan ta Sa’ayrasa da ya gani a daren jiya har ya kai ga
aikawa Gimbiya Fatima muradin sa na ganin bayin Sa’ayrasa.
Idanun sa kan Bintu ya furta
‘’gide wagga d’iya ba ita an baiwar Sa’ayrasa da na gani a
daren jiya ba?’’
Bawan sa na mai duban Bintu da Ladiyo ya furta
‘’kwaran gaske, waccar mai tafe bayan Gimbiya Fatima na
d’aya daga cikin bayin Allah shi taimaki Sadauki’’
Sadauki na mai girgiza kai cikin nuna rashin yarda da maganar
bawa ya ce
‘’bayan Gimbiya Fatima? Wacce Gimbiya Fatima? Matar Barde
gide? Yoto ai ni bayi biyu na ka gani, waccar mai tahiya irin na
d’awisu, ma’ana mai sanye da lifayar can, ko shakka babu ita
na gani sanye cikin kayan bayi a daren jiya, ba na mance abu
mai kyau, ba zan manta da wagga tahiya irin ta ta ba, duk
duniya ita d’ai ta na gani da wagga baiwa na iya taka k’asa
kamar d’iyar Saraki’’
Bawa na tsoran kada ya yiwa Yarima Sadauki musu ya
fuskanci hukunci, dan haka wannan baiwar da ta kawo sak’on
Bintu ya yiwa nuni da hannu ya na mai tambayar
‘’ya ki nan, gide shin ko waccar mai tahiya tare da baiwar
Sa’ayrasa baiwa ce?’’
Ko da baiwa ta ware ido ta hangi Bintu tuni ta shiga girgiza kai
kana ta ce
‘’ina mai tuba, wagga Gimbiya Fatima d’iyar Sarki Inuwa na
Sa’ayrasa ce ran Yarima ya dad’e’’
Jin haka Sadauki ya shiga shafa gashin bakin sa, har ila yau
be d’auke idanu daga kan Bintu ba, dan ya tabbata ita d’in ya
gani cikin shigar bayi, abun da ya kasa ganewa shi ne
‘’me zai sa Gimbiya, d’iyar Sarki kuma matar Barde shigar
bayi? Shin menen dangantaka ko alak’a da ta ke da Shi mai
k’arfi haka tsakanin ta da bayi da har za ta aiko masa da
bak’ar magana dan kawai ya nemi ya gana da bayin
Sa’ayrasa? Ko dan ta san ya gan ta daren jiya ne? Shin akwai
wani lamarin 6oye dangane da ita?’’
Tambayoyin da ya ke ainawa cikin ran sa kenan yayinda tunani
kala kala ke ratsa zuciyar sa. Ya na mai duban bawan sa ya ce
‘’ban yarda da wanga lamari ba, ina so a yi min bincike akan
lamarin wagga Gimbiya, a gaggauta yi ba tare da sanin kowa
ba, in kuwa na ji magana ta fita rariya sai da uwar mutum ta
haifi wani!’’
🐫🐪🐫🐪🐫

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button