Kwarata Return Hausa Novel Complete
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN…*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa…
*JAMILA MUSA…*
*SAI NA AURI D ‘ K*
🅿 —— 1
Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai….
Dakel aka fiddoshi daga wurin , dan bashi da hankali akan ɓarar da kuɗi. Idan zai kwana a haka baya gajiya kuma ba zai daina ba , zaiyi ta zubawa ne baya gajiyawa , haka kuma idan zai bayar yake kyauta maisa ɗimuwa.
Wace ce ita……………???
Wata irin dariya yakeyi bayan an fito dashi yana tsaye gaban Momy data bishi da kallon takaici , hahahaha yaci gaba da dariya yana kallonta , nima binshi nayi da kallo ina murmushi saboda ba ƙaramin kyau yakeyi ba idan yana dariya….
Momy tace idan ka gama haukar ka ɗauki matarka ku tafi gida , daina dariyar yayi tare da taɓe fuska , a yatsine yace ai ba tare nazo da ita ba. Murmushi mai cin rai nayi , ba tare dana sake kallon inda yake ba. Kafin inyi magana akaja Momy wai anayin faɗa , binta Rabiya tayi da sauri ni kuma na kalli Dikko ƙasa da sama a yatsine nima nace , tir tittir nabi tsoho ya ɓatamin wanka , nine tsohon ? Ya tambayeni yana nuna kanshi.
Yadda ya ɓata ranshi yasa nayi shiru ina kallon ƙasa , jinjina kanshi yayi cikin ɓacin rai sannan yace Allah ya maida mu gida lafiya , banyi magana ba kuma banyi gigin sake ɗagowa na kalleshi ba , nine dai tsoho ko ? Ya sake tambayata da yanayin ranshi ya mishi babu daɗi , hmmm tsoho , ƙara jinjina kanshi yayi cikin ɓacin rai , mtswww , ya wuce daga wurin yana magana ƙasa².
Da sauri na ɗago ina kallonshi dan harya tafi ya sake dawowa , nine dai tsoho ko ? Dan ina tausayinki kenan yasa kika raina ni ? Har nine zaki kalli tsabar idona kicemin tsoho tsabar kin ɗaukeni sallau , duk shekarar nan ni banma samu wanda ya ɗaukeni sakarai ba kamar ki , ajiye kai yayi da ɓacin rai , zaki ci gidanku Allah ya maida mu gidan lafiya zaki faɗamin nine tsohon idan na riƙeki , yana faɗin haka ya wuce , a firgice na juya bayana da sauri , Rabiya ce ta dafoni ta baya , nayi tunanin shine ya sake² dawowa.
Ana fita da Dikko itama ta sulale ta fice daga cikin holl in da farin cikinta , ta wani ɓace abunta ba tare da anga fitarta ba , jikin motar ta , ta tsaya ta saka hijabi da niƙaf , bayan ta gama ta wani shige tayi layar ɓata abunta , wannan shine ɗabi’arta , hijabi da niƙaf , bata rabuwa dashi ita musulma , idan kuma zata tafi bariki bata fita da motarta dan gyaran tako…..
Wai ke me zakiyi mata ne kike neman ta ? Barni na ganta sai in ɗauki mataki a gabanku , tou wai yaushe suka saba haka har ya saki jiki yana mata ɓarin kuɗi a gaban bainan nasi….? Waye ma zai iya sani ? Tsoki ƙawarta tayi cewa wai kema Jiddah bazaki bar wannan banzan Dikkon ba ? Sai kace Dikkon diamond ? Murmushi Jiddah tayi tare da kallon Mardiyya cewa faɗa mata waye Yaya D ‘ K.
Cike da tsantsar soyayyar Dikko Mardiyya ta fara rattafo mata , hmmm ai ya wuce duk inda hankali baya tunani , saima kin ganshi , gashi mai kyau , ɗan gayun bala’e uwa uba ga kuɗi ga mulki , idan yana magana sai ya baki sha’awa , gashi sakatacce wani irin kallo yakeyi mai burgewa , Dikko matashi ne mai wayewar kai , buɗewar ido da gogewar rayuwa amma bashi da mutunci ko kaɗan , damen ɗan iska ne , kuma shiɗin ƙyalƙyal na lariya ne , tantirin kwallon ɗan iska ne yanzu mutum anjima bai sanki ba , yana da baƙon hali , haƙurin zama dashi sai ɗiyar ɗan caca , dan itama “yar tasha ce. Kinsan auren tasha baya ƙarewa saida aci uban juna yanzu , anjima kuma a zama masoya , duk da biyu Mardiyya tayi wannan maganar , sanin manufarta na faɗar haka sai ita da kanta.
Ƙawar Jiddah tace tou ni me yasa baku kirani na ganshi ba lokacin daya shigo ? Murmushi Jiddah ta sakeyi tare da cewa har hanzu baki makara ba , Mardiyya bata hotonshi ta gani , a duniyance Mardiyya tace waye yaba Mardiyya hatimin nasara ita ba jikar matsafi ba , ai hoton Dikko sai wurin matarshi , gaba ɗaya suka ɗingumo suka yo wurina !
Sultana Momy tace muje in ajiyeki gida , tou na faɗa tare da kallon agogon wayata 11:22am gaba nayi ba tare dana sake magana ba , ta baya Jiddah ta riƙomin riga , da sauri na juyo dukana dan ganin waye ya rainamin wayau haka ? Cikina ta kalla sannan kuma ta kalleni amma yanayin fuskarta ya nuna taji babu daɗi , amma dake “yar duniya ce , saita wayance da murmushi cewa ina ta magana shiru nace ai nasan bakiji ba , banyi mata magana ba na tsareta da ido , dafe kafaɗa ta tayi kamar ƙawarta tana cewa Aunty Rabiya ai muma a gidan Yayan zamu kwana.
Rabiya bata kalleta ba tace ai kina da numbershi ki kirashi ki faɗa mishi , ai basai na kirashi ba kuje gidan muma muna zuwa bayanku , Rabiya bata sake magana ba ta wuce , sauke hannun Jiddah nayi daga jikina nima na wuce muka tafi , har muka zo gida Rabiya batayi magana ba nima banyi ba , a waje ta ajiyeni ta wuce. Ni bansan abinda ya haɗasu ita da ɗan uwanta ba , ni na shiga da kaina ciki raina a jagule , a get na biyu na haɗu da Ashiru , yana gani na ya tsaya yana cewa ranki ya daɗe mai gida yace naje na taho dake , ko inda yake ban kalla ba kuma banyi masa magana ba na wuce , shi kuma ɗayan marar kunyar a get na ukku na haɗu dashi shima fita zaiyi , wato bai gaji da iskancin ba zai sake komawa , kenan dawowa yayi gida ya sake sabon wanka , yanzu garin nashi ya waye , ko wane bawan Allah idan dare yayi yana gidanshi yana bacci , koba a gida ba duk inda kake idan dare yayi zaka samu natsuwa , idan bakayi bacci ba , tou kana kusa da ubangiji kana bauta masa a dai² irin wannan lokacin , amma banda Dikko daya maida dare lokacin huɗɗoɗinshi.
Shima magana yayi min wai daga ina nake ? Kuji fa ? Wai ma daga ina nake ? Kamar ma baisan ina ya baroni ba , shima ko inda yake ban kalla ba na wuce , An mata bakyaji ina miki magana ne ? Ban dawo ba kuma ban tsaya ba na wuce , da ribos ya biyoni saida yazo inda nake yace ke Yarinya bakiji ina magana ne ? Canja hanya nayi naci gaba da tafiya , An mata dake nake fa ? Ganin Sultana tabi hanyar da zata shigar da ita ciki batayi mishi magana ba , yasa yayi parking ya fice da sauri yabi bayanta.
A palo na zauna ina cire takalmi na , idona cike da hawaye , ai dama Inna ta faɗamin Dikko ƙyalƙyal na lariya ne , bana iyawa da duniyancin shi , tace Dikko ba mijin aure bane ba , amma na kafe kai nace ni ina sansa a haka , yau naga kaɗan daga iskancin shi. Goge hawayen da suka gangaromin a fuska nayi tare dayin shashshekar kuka , shine saida aka tara taron dubu da dubu ya fito yana ma wata liƙi dan ya nuna ma duniya ni ban kai mace ba , ni ban kai sahun irin matan da yake aura ba , ya nuna ma duniya ni ba’a bakin komai nake ba a wurinshi , Momy tace masa ya taho dani gida yace shi bashi ne yazo dani ba , ashe kuma gidan zai taho dan ya sake nunamin ban kai macen dashi zai saka a gaban mota ba ko wayewa yasa ya taho ya baroni , hakan bai mishi ba zai tura Ashiru ya ɗaukoni dan ita budurwar tashi taga shi bashi ne ya taho dani ba , ta gani saida shi ya koma gida sannan ya turo driver ya ɗaukoni , dole Ashiru ya ɗaukoni mana tunda dare yayi yanzu ne yasan amfani na , maganar Inna ta sake duwomin da tace , haka zaiyi ta ɗura miki ciki kina haifar mishi “ya “ya nan ne kaɗai matsayinki.
Da sallama ya shigo palon , takalmana na ɗauka nayi gaba , ban ansa sallamar ba haka kuma ban kalleshi ba , An mata baki lafiya ne ? Yayi maganar yana biyo bayana , ban mishi magana ba har ɗakina , ina shiga na fara tattara kayana , miye haka kikeyi ne ? Haba An mata wai duk miye na fushi ? Kiyi haƙuri akan abinda ya faru dan Allah , goge hawaye na sakeyi naci gaba da tattara komai nawa , kusa dani ya matso yace An mata Dikko zaki ma yaji ? Haba jarumar mata ban sanki da irin wannan halin ba , kiyi haƙuri ya ƙarasa maganar yana riƙeni jikinshi , kalleni , saida na sake goge hawaye na kalli Dikko , nine ? Yayi maganar kamar zaiyi kuka , banyi magana ba ina kallonshi shima ni yake kallo , a kasalance yace kinyi haƙuri ko ? Ya ƙarasa maganar yana warware fuskarshi da yanayin burgewa , har yayi surutunshi ya gama bance masa kaci kanka ba , saida ya gama rattofo yaudararrin kalamanshi yai tafiyarshi ya barni.
Tun daga ranar Dikko ya sake ɗaukewa , ma’ana ban sake ganinshi ba , nima ban sake komawa gidansu ba , Jiddah kuma a ranar waje ya ganta masu gadi sun hanata shiga , saida yayi mata rashin mutunci mara ɗaura zani ya ƙara da cewa dama yana cike da ita akan abinda tayi ma Papi , akwai lokacin daya iba mata zai sameta har gaban uwarta anan zai nuna mata tsabar rashin mutuncin shi , duk su basu san halinshi ba labarin iskancin shi sukeji. Tou zaizo har Kadunar , shiru yayi yana kallon wayarshi , bayan wani lokaci yaci gaba da cewa tou a ranar zataji shi yadda yake , kuma idan take sake shiga sabgar iyalinshi kota kuskura ya sake ganinta a goruba koba gidanshi tazo ba , ya jinjina kanshi tare da cin taya ya barɓaɗeta da ƙura , ta gane abinda yake nufi , kawai zaibi ta kanta ne kamar yadda yaci ƙasa ya wuce abunshi….
Ko a makaranta , haka nake kasancewa suku². Banayin wata walwalla , ina ɗauke da damuwar da tafi ƙarfin shekaru na , cikin kwanakin da basu wuce biyu zuwa ukku ba nayi duhu na rame , kuma ba rashin ci ba nasha , babu abinda na nema na rasa , ina tunanin Dikko ne kawai dakemin wahalar gani , dan yanzu ankai gafen dako text na tura mishi baida lokacin bani ansa , idan na dameshi sai yacemin wai bansan yadda abubuwa suka sha mishi kai ba , saiya rufeni da faɗa ta waya , idan kuma nace na taga barinshi Inna bama zata anshe ni ba , haka nan kawai na fashe da kuka a class , kuma gaba ɗaya ajin yayi shiru saboda malamin dake ciki , duk wanda ke cikin kilas in maza da mata kowa ya juyo yana kallona , miƙewa nayi na fara tafiya ina ƙara yawan kuka na , har nayi nisa. Na dawo na ɗauki sch bg ina da makullin mota naci gaba da kuka ina fita daga cikin ajin ko malamin baimin magana ba.
Daga makaranta kai tsaye gida na nufa har naje kuka nakeyi , dakel nayi parking na fita ko gabana bana gani na shiga ciki , a palo na sameshi zaune , hankalinshi kwance yana cin abinci baida wata damuwa , kenan idan ina makaranta yake dawowa gidan yayi duk abinda zaiyi ya tafi kafin in dawo tunda yasan lokacin dawowana , sannu da zuwa ya faɗa tare da bina da kallo , cike da ɓacin rai na nufi kicin na ɗauko wuƙa ina cewa saina kashe ka , da sauri ya tashi yana innalillahi wa’inna ilaihir raji’un , An mata kinyi hauka ne ? Yake tambayata yana nuna saman ƙoƙon kanshi , ey hauka nakeyi , na faɗa ina matsawa kusa dashi , da sauri ya koma can saman inda ake jingina na kujera idan an zauna ya zauna ƙafafuwanshi a saman wurin zaman , yace waye yace miki ana wasa da wuƙa ? Ba wasa nake ba kashe ka zanyi kowa ya huta na gaji da baƙin halinka ko kuma ka sakeni in kama gabana , ta baya ya sauka yana dariya. Lallai An mata amma ban taɓa sanin mahaukaciya bace ke sai yau. Ai dole zakacemin mahaukaciya tunda ka samu mai hankali , riƙe wuƙar nayi dai² yadda zatamin sauƙi wurin burma mishi nace ka sakeni kafin in tuno maka asiri , dafa kujera yayi yana kallona ,
Zagayawa nayi inda yake har yanzu ban daina kuka ba , dariya yakeyi sosai , cikin dariya yake cewa ni idan wasa kikeyi nawa na gaske ne , ina nan yadda kika sanni ban canja ba. Dan kinga kwana biyu na ƙyaleki kike duk iskancin da kikaga dama , cike da tsantsar ɓacin rai yazo kusa dani yace cakamin wuƙar , cikin hayaniya yace caka׳ , shiru nayi nasa wuƙar ta kalli ƙasa , ƙaryar rashin kunya dakin sake nunamin ita dasai na burma miki ita kin mutu kuma na kashe banza , bari jin Mama tace ke taurin kai gareki , ke kuma kina iƙirari idan kika sa kanki abu babu wanda ya isa yasa ki bari ni nafiki taurin kai da rashin kunya , zanje in zauna ko motsi mai ƙarfi kika sakemin sai kinga yadda zanyi dake , yayi maganar yana komawa inda yake yaci gaba da cin abincinshi.
Kuma koba yau ba saina kashe ka , ke idan wasa kike ni zan kasheki da gaske ne , a tsorace na wuce ban sake magana ba , shi kuma yace zoki ki zauna muyi magana , ƙara fashewa nayi da kuka nace bazan zo ban , ki daina ganin ina lallashin ki , duk ranar da kika cika ni idan kika bari na riƙeki jikinki zai baki labari yayi maganar yana nunamin belt in dake ɗaure ƙugunshi , a wurin da nake wucewa na yadar da wuƙar na wuce ciki ina gunguni , kuma saina ɗauki number duk wata mace a wayarshi , anan zan gano wace ce zai aura saina cicci ubanta…..
Satina ɗaya rabona da zuwa makaranta , kuma Nabeela da kanta ta tabbatar min cewa Yaya zaiyi aure , zai auri ɗiyar ƙanwar Dady da suke Baba ɗaya , { idan baku manta ba shi Dady a ɗakinsu shi ɗaya ya rage , “yan uwanshi kaf sun rasu sakamakon gobara data cinyesu , su kuma sauran matan bayan an basu kuɗi ko wace ta kama gabanta ita da “ya “yanta , dalilin auren ne yasa yake aikin gidanshi na G R A , kuma itace yarinyar da yayi ma liƙi , Dady ne yakejin farin ciki Dikko zai auri ɗiyar “yar uwarshi kuma shine yayi mishi tayin auren dan ƙara ƙarfafa zumincinsu a matsayin shi na babba , wanda shima Dadyn Mamar yarinyar ce ta nuna masa alfanun hakan , tunda tayi tayin Dady ya karɓa dan cika farin cikin mahaifinsu da yace yasan ko baya raye Umar zai zama jigo ga “yan uwanshi , wanda shima Dadyn yake fatan Dikko a zama bango ga “yan uwanshi mata idan baya nan , shi yasa ya miƙe tsaye saida ya tabbatar Dikko ya daskaru hankalinshi ya kwanta tare da binshi da addu’a , Momy ce bata san auren dan ta raina ahalin Dady yadda mai tunani baya zato , wannan dalilin ne yasa duk suke fushi da Dikko , da Momy ta fara wani tirje² Dady yace ta bari kar rabo ya kashe ta , ai itama an auri nata “yan uwan amma ba’a dace ba , dan haka a bari a taga gaba ko a dace dan auren zuminci abu ne mai kyau , wannan kenan. }
A makaranta kuwa an kira Dikko cewa na daina zuwa makaranta , su kuma ƙawayena har gida suka zo , suka tambayeni abinda yasa nayi kuka a waccan rana , da abinda yasa na daina zuwa makaranta , na faɗa musu mijina ne zaiyi aure , kuma auren ma na zuminci dan dai kawai su haɗemin kai da “yar uwarshi ni a juyamin baya , na kuma basu labarin liƙin da yayi mata , wanda ni bansan dalilin da yasa yayi shi ba , juyamin baya da rashin san kasancewa dani a inuwa ɗaya , rashin dawowa gida da wuri sai nayi bacci , fita tun safe kafin in tashi , da dai wasu halayya dani bansan yana dasu ba sai yanzu da zai ƙara aure , shine Farisa tacemin ai mazan yanzu idan ana raga musu iskanci suke na wuce shari’a , kar in wani damu kuma na daina ajiye damuwa idan ba haka ba hawan jini zai kamani na mutu a banza in bar yarana , shi kuma zaiyi jimamin rashina na kwana 3 daga nan yayi aurenshi ya buɗe sabuwar rayuwa ya manta da labarina , “ya “yana kuma ayi ta gana musu azaba , su tashi babu wani galihu ko “yanci kamar almajirai , itace ta bani shawara ƙauracewa ɗakin miji , daina bashi abinci , rashin kunya kuma saina cire shakkun Dikko dan matsoraci baya zama gwani ko waye , ta ƙara da cewa na fita sabgar kaf ahalin miji dan dasu ake haɗa duk munafurcin , wannan duk ɗabi’ar mahaifiyarta ne , idan suka samu matsala da Dadynsu bata zuwa ɗakinshi kuma batayin yaji saida tanayin gayu mai ɗaga hankalin namiji , tace idan anyi yaji babu ta inda za’aga miji bare a samu damar gasa masa aya a hannu , a gida za’ayi duk masifar ayi a gama , tou kundai ji matan aure , shine fa tun daga wannan rana na birkice na zama fitsararriya , abun bai tsaya a iya Dikko ba ya shafi kowa da kowa.
Wani irin gigitaccen mari na yankawa Papi tare da ce masa dan ubanka waye yace ka zubarmin lemu a kafet……? Tashi Papi yayi ya tafi wurin Dikko…….! Da fatan mai karatu ya gane………..???
Ci gaba nayi da cewa ni banajin tsoron wani zare²n idon banzar mutum , idan taƙamar mutum yace zai dakeni saina bari ya kwanta bacci in mishi wanka da ruwan zafi ko in dafa mai in toye mishi fuska , ko inda nake Dikko bai kalla ba yaci gaba da rirriga Papi da yaƙi ya daina kuka , ni har an nunamin iya zare ido ? Ko rashin kunyar kafi ni iyawa ne ? Nima nan na iya ai shiru² ba tsoro bane ba , kace tuf ka gani , saboda nasan nayi masa nisa , dan tunda na mari Papi na koma matakal bene na zauna daga wurin nake yanko magana , { idan kun tuna benen g r a ya sauke lokacin dana faɗo , na goruba kuma na hau nace zan faɗo ? Yace shine zai jefani na faɗa na mutu , wanda bayan na gudu da yake bani labari yace shi ya ɗaure kanshi da wayar wuta ya faɗo daga sama , wanda ya tafi doguwar jinya…. } fita yayi yaje ya bada Papi ya dawo , har lokacin ban daina zage² ba , shine yajani yakaini ɗakinshi ya rufe bakin rashin kunya.
An mata wai meke damunki ne ? Gaba ɗaya kin zama mahaukaciya , cike da ɓacin rai nace kaine mahaukaci…….. , duk girman kwanakin da kake saukewa ai ba’a kaina kakeyi ba , wannan matsalarki ce , tunani da neman mafita ya rage naki ƙaramar yarinya……! Riƙe yatsana yayi a bakinshi……. ` saida ya gama duk abinda zaiyi ya shirya ya fice abunshi…..
Wasu irin zafafan mata ne zagaye dashi ,,,,,,,,,,,,, duk girman daren nan batajin shi bata kuma ganin shi.““, tsaye take a jikin madubi , fitowarta daga wanka kenan , da wayarta ta saita kanta bayan ta danna video , cire towel in dake jikinta tayi taci gaba da ɗaukar kanta tana iskanci ………. Madaidaicin gida ne a cikin anguwar kwaɗo duk yara²n mata ne suke ta gulmar mazajensu , wayarta ta kanga a jikin ƙugunta tayi wasa da jigidar dake ɗaure a ƙugunta , Jiddah bata da burin daya wuce Yazeed yayi auren kishin wuta da ita , *KWARATA RETURN…* fatan mai karatu ya fahimta ko….?
Ƙwas׳ ƙarar takalmin ta kakeji a saman tayils , duk lokacin data motsa dan takawa sai jigidar dake ɗaure jikin ƙugunta ta wani ce cas׳ , idan tayi girgiza kuma sai ta wani ce kacau׳ , gyara zaman ɗaurin kallabinta tayi tana ci gaba da tafiya , harta bayyana a cikin palon , sai yanzu ta samu damar fesa turare bayan ta tsaya a gaban wani mutum wanda shekarunshi zasu kai kimanin 50 , Alaji barka da safiya , ta faɗa a shagwaɓe tana kwarkwasa , ɗagowa yayi da niyar ansa gaisuwar , ita kuma ta ɓalle botiran gabar rigarta dake sanye a jikinta , after dress ce a jikinta. Tana buɗewa ƙanan kayan data saka daga ciki suka samu damar bayyana , a aljihun wando ta tura kwalbar turaren data gama shafawa dakel tare da gyara kitson atach ta watsoshi ta gaba da bayanta , miƙa tayi sosai tana cewa yi haƙuri Alaji na rashin fitowa ta da wuri take maganar tana wani mimmiƙewa kamar macijiyar data samu wurin sanyi a lokacin zafi , cikin ɓacin rai mutumin yace ke me yasa baki da ɗa’a ne ? Kuma ni bake nake nema ba mijinki nake kira ,
Cire after dress in tayi ta wurgar a ƙasa ta ƙara matsawa sosai kusa da Alhaji tana cewa taya zanyi ɗa’a , mai siyar da kayan ƙara kuzarin maza me ya haɗata da ɗa’a tarbiyya ko kunya ? Kaje anguwarmu kayi binciken Sa’adatu mai gilashi kaji me zasu ce maka ? A wannan duniyar idan akwai wani sirri daya kamata al’umma ta sani akan mu’amalar aure tou bai wuce na mata da miji ba , dalili kuwa shine sirrin da ba’a koyar dashi a makarantu ko a gidaje , shi kaɗai ne sirrin da sai wani da wani ke saninsa , to amma kasancewar hanyoyin isar da saƙon sun yawaita nake ganin ta wannan hanyar ya kamata kasan wani daga cikin irin nawa sirrin , matar malam bahaushe ce kan gaba wajen shiga matsalolin aure , kamar yanda zakaji matan na faɗa babu soyayya tsakanina da mijina , shi yasa nake fuskantar matsaloli a gidan aure na , ni gaba ɗaya wannan matsalar duk na tattarata na jibgata akan mata , ɗan yatsina fuska tayi tare da ci gaba da cewa nima dai hakan take daga gareni tunda banyi auren soyayya ba , tsoki tayi sannan taci gaba da cewa , kawai ƙusani akayi wanda ni ba haka naso ba , wannan auren baya hanani neman mazan waje kamar dai yadda nake nemanka. Ci gaban da aka samu na sanin sirrin rayuwar da nayi maka magana shine , hanyar kula da mazaje ta yawaita , wayewar kai da buɗewar ido , zamani ya kawosu sun kuma yawaita ta haryar gidajen karuwa da kuma ganin wannan sirrin ta kafofin yaɗa labarai a nahiyar yana giza gizo a maimakon da can zamanin iyaye da kakanni da wannan sirrin yake ɓoye , an samu ci gaba sosai wanda har takai yanzu idan za’ayi ma yarinya aure basai an faɗa mata cewa idan mijinki yazo yaja zariyar wando karki gudu , ko kuma idan yayi haka , ta zage zif in wandonta , cikin yanayin jin kunya Alhaji ya kauda kanshi gefe guda , wata “yar munafikar dariya tayi tare dayin wasa da yatsun hannunta taci gaba da cewa , suma ƙawaye dake zuwa gidajen ƙawayensu idan sunyi aure danjin labarin sirrin auratayyar yadda yake sun daina zuwa saboda zamani ya kawo manashi sauƙaƙe , ni da kuma kai kowa yasan abinda yake faruwa tsakanin namiji da mace idan suka keɓance , amma ci gaban zamani yasa yanzu su kansu iyaye sun daina wannan huɗubar wa “ya “yansu saida kaji ana cewa yi nayi bari na bari , me zakiyin me kuma zaki barin ne……?
Murmushi Alhaji yayi tare da kallon Sa’adatu , ɗan girgiza ƙirjinta tayi cewa tou ya kaga nan , da kuma nan tayi maganar tana nuna gabanta da kuma bayanta , bayan ta tabbatar ya kalla ta fara bada step tana tafiya cikin salon mai ɗaukar hankali , saida ta ɗanyi tafiya kaɗan ta juyo tare da ɗan zira yatsunta a aljihun wandonta , gaɓar hannunta riƙe da ƙugunta taci gaba da karkaɗo ƙugunta tana tahowa wa da girgiza , girjinta yaci gaba motsawa , dariya tayi a dai² lokacin data dawo gaban Alhaji ta riƙo kanshi ta ɗora fuskarshi a saman ƙirjinta cewa ya kagani ne ? Shiru Alhaji yayi , ita kuma tace karka damu ina da sirri , sakin kanshi tayi tare da ɗaukar rigarta bayan ta ajiye mishi number wayarta a rubuce jikin takarda tace idan kana da buƙata ka kirani , tana faɗin haka ta rataya rigarta a ƙafaɗar ta fice ba tare data maida rigar ba……. Kamar wani gelele haka yabi bayan Sa’adatu da kallo. 👇🏻
Cikakken sunan nata shine Sa’adatu Ibrahim , iyayenta talakawa ne na bada misali , babu arabi ba boko haka ta taso a sake kamar ɓatattar dabba , bata nan bata can , bata da aiki sai tallace² , cikin tasha kasuwa da sauran madakatar “yan iska , idan kuma dare yayi sai a kasa mata tallar kayan mata take bin gidajen karuwai , a gidan karuwai ta fara sha’awar shiga sabgar karuwanci dan tana ganin yadda karuwai keyin sabgoginsu , da kuma yadda suke wasa magungunanta da faɗar irin matsayinsu da aikinsu idan sunyi amfani dasu , ita abinda yafi bata mamaki shine , yadda karuwa ke cika ƙatuwar roba irin ta wankan jego da ruwa , mintuna kaɗan namiji yana jiga ɗaki zai fito ya bada maƙudan kuɗaɗe , idan namiji ya fita sai ita karuwar ta shiga cikin robar ta wanke ƙasanta da wannan ruwan , ashe lemun tsami ne ake matsawa a ciki shine ke hana namiji daɗewa idan ya kwanta da mace , yana zuwa akan mace batsal² zai sauka ba tare da ya biya buƙatarshi ba yadda yaso ,
A gidan karuwai ta fara laɓe jikin window idan mace da namiji sun keɓe , nan ta fara sanin muhinmancin kanta da kuma taƙama da ƙatuwar ƙaddarar da gareta , jin manyan maganganun da suka girmi tunaninta yasa itama ta farajin shauƙin buƙatuwa da abun , wannan dalili yasa ta fara kokowa da maza a tasha , da namiji yayi mata abu saita kamashi da kokowa , shine ta samu wani damen ɗan iska ya fara ɗora mata hannu akan alƙalaminshi , daga nan abun ya zame mata abun tunani da san ganin alƙalamin rubutun maza yadda yake a bayyane , tun daga wannan ranar taci gaba da binshi da kokowa , shi kuma duk lokacin data kamashi saiya ɗora mata hannunta , a hankali ta fara warwarewa ta kwace gaba ɗaya , ta daina bari saiya taɓa mata , daya zo sai kawai ta cafko wurin , shi kuma idan ta taɓo sai yake ƙara gudun numfashin alƙalamin , a hankali dai ya samu ya maida ita “yar hannu ,
Itama lokaci guda ta faso ta zama riƙaƙƙar “yar iska , tafi ƙarfin iyaye ta daina ɗaukar talla , kafin wani lokaci ta zama Sa’adatu mai gilashi , bayan wani lokaci kuma ta koma mai gilashi kawai , ganin tana ta ansar wuta a harkar bariki yasa iyayenta suka kwantar da ita da aure , tsaye take har yanzu , tunda akayi aurenta taga ita bata dace da zaman BQ ba , Alhajin ne ya kamata ya aureta ko kuma kawai taci gaba da saƙashi a ɗaki tana ci mishi uwa a gado , tunda tazo gidan ta fuskanci yadda Alhaji ke zama da iyalinshi shi yasa take ta mishi tayin kanta , amma ya cika kafiya har yanzu bai amshi tayi ba , ita kuma ta duƙufa akan saita farautoshi ya zama nata ita ɗaya , ta bashi yaƙi ansa , shine wata rana taje ta bashi number wayarta , yadda ya fara kiranta har aka ƙulle duk zamuji….
Riƙe take , ta wanku iya wankuwa , tana sanye cikin wasu irin sheɗanun kaya masu nuna shatin bireziya da fant , a haka ta tunkari Dikko tana tafiya irin ta riƙaƙƙin “yan bariki , ƙafa ɗaya ake fara shigar da ita ta gaba sai wata ta biyo bayan waccan ta fita , ba bazar² ake tafiyar ba a nutse akeyin tafiyar kuma takon bada tazara ake miƙashi ba , sai tafiyar taɗan riƙayi kamar mutum yana harɗewa kai baƙon abun sai kaga kamar mutum zai faɗi , ba kuma kamar yayi tuntuɓe ba , sudai “yan duniyar sune suka san dalilin yasa sukeyin irin tafiyar a gaban maza , ita kuma tafiyar idan anyita zata ba jiki damar motsawa , kafin ta ida isowa ya gama kalleta tsaf daga ciki , tunda munafikin gilashi ne motarshi , wato na ciki ke ganin na waje , shi kuma na wajen baya iya ganin ka dan duhun gilashin motar , ɗan taɓe baki yayi tare da ɗage girarenshi ya gyara gemunshi sannan ya saka cingom a bakinshi. Saida tazo jikin motar ta kama da niyar buɗewa taji ta a rufe ,
Ɗan fara kwanƙwasawa tayi , bata san ya ganta ba kuma yaga zuwanta iskanci ne kawai yasa ya basar da ita saiya gama kallonta zai fito , idan ya fito kenan bazai kalleta ba bare ta gane tayi ko batayi ba , har ta gaji da tsayuwa taɗan fara canja wuri Dikko bai fito ba kuma bai buɗe ba haka kuma bai daina kallonta ba , Sultana ya kawo ya jera kusa da Yusra , girgiza kanshi yayi tare da cewa kai An mata fa ƙarshe ce , murmushi yayi tare da kallon hotonta a waya yace rashin kunya kenan , Dikko ׳ suna na kenan a bakinki ƙaramar yarinya , dariya yayi tare da ƙara zuƙo hoton yace wai nine zaki dafa mai ki ƙonamin fuska ke mahaukaciya , in Allah ya yadda saina samu lokaci na zaneki An mata dan naga iskancin naki kullum gaba yakeyi , ya ƙarasa maganar yana sumbatar hoton yace ina sanki ƙawar faɗa ta. Ƙara kallo Yusra yayi sannan ya sake kallon hoton Sultana , yace An mata babu inda Allah ya rage ki amma da wannan yajuju wa majujun aka tsere miki , me na rage miki ne ? Fita goma idan zanyi saina shigo miki da duk abinda nasan zaki ƙara sama dashi a zuciyata so goma , ragamata gaba ɗaya na miƙa miki amma kin kasa riƙewa , babu abinda kika aje sai rawar kai kafiya da rashin kunya nan kaɗai kikafi auki.
Mafiya yawan maza da irin wancan ƙarshen duniya mata ke fizgar imaninsu su cusasu harkar bariki ko basu shirya shiga ba, wasu kuma mazajen laifinsu ne , misali , banbancin matar aure da karuwa , rashin adalci da wasu mazajen sukeyi shine , su kansu kaɗai suka sani kuma rayuwarsu kawai suke ginawa ta hanyar ba kansu cima mai gina jiki da kuma sutura mai martabasu , ka auri matarka ka kawota gida ka jibge , sabulun wanka da turare man wanke baki da kuɗin kitso da ƙunshi ka gagara tsare mata su , amma kai duk sabon yadi ko shadda takalmi da agogo sabuwar fitowa ko wata hula ka siya kai kanka kawai matarka kuma ko oho , kamar Babansu Sultana kenan , ka gagara ciyar da iyalinka da abinci mai kyau ka haɗata da ƙanzo ko garin kwaki , kwaɗon tuwo taliya da manja , kai ko kullum kana can biye da santa lungu da saƙo kana gano sabbin gidajen dahuwar abinci da aka buɗe , kabar matarka da koko kai kuma kaje ka raya kanka da lafiyayen shayi da biredi saboda rashin adalci , abin nufi anan shine ita matar aure ga Allah ta dogara gareka ta dogara , kaine duniyarta kuma kaine take jira ka bata komai na rayuwa , tou bakayi mata ba kuma baka bata ba , ba tada wata wadata ga kuma rashin kwanciyar hankali lokaci guda saita buge gaba ɗaya ta tashi aiki , ga masifar ka na yawan buƙatuwarta gareka , bata da wani ishashen ƙoshi bare ta samu ƙarfi da kuzarin anshe jarabarka kafin a ankara mace ta tashi aiki.
Shikenan kai kuma ka gama da ita , baka da aiki sai zaginta idan ka zauna majalisa , matarka ƙazamiya ce , bata kitso ba wanka ba ƙunshi gaba ɗaya ta tsofe , tare mukayi aure da wane ko wane ya rigani aure amma har yanzun matarshi kamar yanzu ya aurota , bata tsufa kullum “yar yarinya take komawa kaza׳ bayan kaine mugun , kuma kaine ka tsofar da ita , ka kuma ƙazantar da ita ta hanyar rashin bata duk irin kular daya kamata , shi kuma wanen da kake magana yana kula da matar tashi , yana tsaye akanta wurin ganin ya ciyar da ita ta yadda ya kamata , duk sabuwar atamfar data fito ko wani less janbaki sabon yayi saiya siyo ya kawoma matarshi , sai kuma akaci sa’a mai gayun ce da ansar wanka ba dole zata zama yarinyar ba ?
Ana haka sai kaga wata “yar budurwar tana wucewa da ƙyallinta , iyayenta suna tsaye kanta suna ta siyen fauda jagira da sutura basa gajiyawa , data wuce ku majalisa saita bar muku ƙamshinta , daga nan sai kace saika aurota , kaje kayita ɓarin kuɗi ka samota dakel itama ka kawota gidanka , kamar ta farkon itama haka zata bige saboda rashin kula kafin ka ankara ka tara mata kuma duk ka kasa riƙesu , babu sauran wurin dan haka saika fara harin na waje. Tunda su sun iya shafa fouda,
Bayan duk “yan shafe²n da sukeyi da ƙwalisar suna ɗaukar ido duk a aljihunanku suke tatsar kuɗaɗen , baka raya gida ba amma ka raya waje , baka siyawa matanka kayan shafa da sutura ba ka siyawa matan bariki wanda bakai kaɗai ne kake morarta ba , wasu kuma matan laifin nasu ne , a siyo a kawo musu amma basa dai gyarawar , matsalolin dai daban² ne , wasu rashin kula da mazajen nasu ta hanyar gagara fita haƙƙinsu da kuma rashin iya kula dasu a makwancin , ɓangaren sabta rashin iya kalami mai laushi da kuma rashin girmama miji kesa suna fita daga zukatan mazajensu , mtswww nima dai gani nan…. Fita dai haƙƙin iyali kawai shine mafita.
Ɗaure fuska yayi ya fito da fuskar rashin mutunci , baima Yusura magana ba ya wuce tabi bayanshi tana mishi sannu da zuwa , bai tsaya ba bai kuma ansa ba itama bata daina binshi ba , motarta ta koma ta ɗauko wayarta da wata “yar ƙaramar food flarks wai tayo mishi danbun nama….
Da Abbakar suka gaisa shima ba magana sukayi ba hannu sukayi kawai ya wuce , Abbakar shima bayanshi yabi kamar dai yadda Yusra kebin bayan shi , haka yaita gaisawa da mutane sune rufa mishi baya , duk taron mazan nan Yusra ce kaɗai mace da shiga irinta kafirawan da basa zuwa coci , har wurin da Dikko yake zama , daga nan yace kowa yaje kenan zai gana da Yusra , bayan sun fita ne ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa ya gda ? Lafiya qalau ranka ya daɗe ta faɗa tana miƙa mishi kular data zubo mishi danbun , ansa yayi a mutunce tare da kallonta kamar na minti ɗaya , sauke kanta tayi ƙasa tanajin kunyarshi , ɗan tauna cingom yayi sannan yace zauna yayi maganar yana harɗe ƙafa ɗaya saman ɗaya.
Bata zauna saman kujera ba ta zauna ƙasa dan bashi girma , ta fahimci shi mutum ne mai san a girmamashi , su masu kuɗi duk ƙanƙantarsu suna so a basu girma na musamman saboda kuɗi , kuɗin ne kesa musu girman kai , izzar kuɗi kesa suke ganinsu su wasu manyan shegu ne na daban , tou bare Dikko daya raina mutane , gashi da rainin hankali dan idan ya raina maka ƙura babu daɗi , bare su dama Mom insu bata nuna musu sanin darajar mutane ba wanda yin haka ba kyau ba , kawai dai iskanci da rashin kunya a cikin jininsu take.
Buɗe kular yayi tare da cewa ya akayi ne ? Ya maida ya rufe , ba komai ranka ya daɗe kawai dai naji anyi maganar dambun nama ne shekaran jiya da kuna fira sai nace bara inzo maka dashi , ba tare daya sake kallonta ba yace da kyau , bayan wani lokaci yaci gaba da cewa zaki iya tafiya , ba haka taso ba , dole ta tashi ganin shima ya miƙe ya fice , kallon kular tayi sannan tabi bayanshi da kallo tuni ya fice , a waje ta sameshi yana magana da mutane , saida safe tayi musu ta wuce , su Abbakar suka cinye dambun nama , shi kuma mota ya koma yana tunanin girman rashin kunya da raini irin wanda Sultana tayi mishi har 12 tayi , lokacin nayi ya buɗe wayarshi ya fara ansa kira daga mutane daban² , waya biyu kawai ya ansa duk da tarin yawan kiraye²n dake shigowa ya leƙa yanar gizo , a whatsapp saƙo biyu kawai yayi reply , ɗaya na ɗiyar ƙanwar Dady , data turo mishi fatan alkairi da addu’ar samu nasara a rayuwarshi , ya tura mata ngode. Saina wani abokinshi daya ya samu ƙaruwa , yace Allah ya raya , saƙon Yusra kuwa kasa kalla yayi , yana ƙorarin gogewa text in Sultana ya shigo a ɗayar wayarshi.
Dubawa yayi , bayan ya gama karantawa ya kirata , An mata ki kiyayi ɓacin raina tara ki nakeyi karki bari in riƙeki , magana tayi cikin kuka , yanzu me zan miki ne ? Magana ta sakeyi , to wai me zan miki a gidan ne ? Bayan tayi magana , yace da Allah bazan dawo ba , wallahi bazan zo ba karki ɗaukeni ƙaramin yaro mana , ba yanzu kika gama zagina ba ? Ey bazan dawon ba sai 3 na dare , yana faɗin haka ya ajiye waya.
Yauma bai dawo gida ba sai 3 na dare , kuma idona biyu , inajin lokacin daya shigo ya kwantar da Papi ya kashe fitila ya fita , yana fita na kunna hasken , saida na tabbatar ya isa ya shiga wanka na nufi ɗakinshi , wayarshi na ɗauka nabi jerin kira babu kiran mace ko ɗaya kuma shima bai kira ba , danshi dama ba ma’aboci waya bane ba , inbox na koma ban samu ba dan haka na tafi whatsapp na fara dubawa , har cht in da bai buɗe ba saida na buɗe ,
Wayata na ciro daga jikina na fara ibar numbobi , bayan na gama naci gaba bin cht ina dubawa , wata irin zufa ta ketomin ganin hoton mace tsirara aihuwar uwarta a wayar Dikko , kyarma jikina ya fara , da sauri na fara ƙoƙarin turawa a wayata , jikina yana kyarma , bansan lokacin daya fito ba kuma har yanzu jikina bai daina kyarma ba , saida na gama na ajiye wayar , zan fita na ganshi jikin ƙofa tsaye ya rumgume hannayeshi yana kallona.
Baimin magana ba ya taro hannunshi in bashi wayata , ba gardama na miƙa mishi , goge videon yayi ya maidomin wayar tare da bani hanya ya nunamin da hannunshi in fice , ƙin fita nayi ina kallonshi , ya akayi ne ? Ya tambaye ni , cikin kuka nace kadai ji kunya , da yanayin ko a jikinshi yace you sai me ? Ni banji kunya ba kece dai kikaji kunya da kika kasa ɗaukemin idona akan su , yayi maganar yana nunani da ɗan yatsa , to kinga ke kin ɓoye naki , ga na wata nan a wayata , kyauta ta bani ko sisi ban biya ba duk saboda inyi farin ciki , kuma banyi “yar murya ba cewa a taimaka min na gani , bina takeyi na taimaketa na bata abinda ke nake haɗaki da Allah in baki bakya so , to ita ni take haɗawa da Allah in bata ya ƙarasa maganar yana riƙe ƙugunshi yana ci gaba da cewa shin na bata ne ko kuwa kina so ? Tirrrr na faɗa tare da fashewa da kuka , hanya ya sake bani a karo na biyu yana nunamin da hannunshi cewa ai baki fara kuka ba sai amarya tazo tunda ke daƙiƙiya ce , zoki fitar min daga ɗaki.
Fita nayi ban mishi magana ba na nufi ɗakina ina kuka , ɗan gajeren tsoki yayi bayan fitar Sultana sannan yace kyaji dashi , kashe haske yayi yai kwanciyarshi , tunda ya kwanta zuciyarshi ke cewa ya kira Sultana kartaje taita kuka , gyara kwanciyarshi yayi a bayyane yace da Allah ƙyaleta tunda bata da wayau.
Bayan sati 2.
Har yanzu banje makaranta ba , Dikko yayi faɗa harya gaji ya ƙyaleni , dan yanzu ko zai kasheni bana magana , bana tura mishi saƙo , idan dai yacemin inyi mishi kaza , zanje inyi ne , amma bana masa magana kuma bana masa dariya , idan ina palo ya shigo kawai zan tashi ne , ko ina naje idan ya biyoni zan bar mishi wurin idan yayi magana ba amsa saidai in aikata kawai a aikace. Na zamar mishi kurma a magana.
Ita kuma Inna naje wurinta kuma na faɗa mata Dikko zai ƙara aure , tace ni na jiyo kuma damuwar nice wannan bai shafeta ba , a ranar gidan na yini dani da Papi sai 9:37pm na koma gida , yace ina wuta ya sakani ina naje nayi wannan zaman ? Yafa gaji da iskanci na in ajiye mishi ɗanshi in koma daga inda na fito , keda ke gidanki idan kinji shi tou naji abinda yace , cike da masifa yazo gabana ya ɗallarmin bakina da yatsunshi , da sauri na zabura tare da rufe idona saboda azabar ɗallin da naji a bakina, bakyaji ina miki magana ne ? Ban kalleshi ba kuma banyi magana ba , shigowar Papi ɗakin ne yasashi fita yana magana ƙasa² wai zai dawo dana rainashi yanamin magana nake mishi shiru.
Har safe bai dawo ɗakina ba , ni kuma yau na shirya dan zuwa makaranta……..
*JAMILA MUSA…*
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN…*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa…
*JAMILA MUSA…*
*SAI NA AURI D ‘ K*
*ASMA’U ZAYYAN* {{ Asmeenat Xeyyan }}
🅿 —— 2
Palon ƙasa cike yake da duk wani ma’aikaci dake gidan mace ko namiji gaba ɗayansu hallare suke zaune a ƙasa amma shi mai gidan baya wurin. Duk yadda akayi zaibar ƙasar ne , duk lokacin da akayi irin wannan zaman zaiyi tafiya ne , idan zaije Abuja ko ina ne ba’a haɗuwa sai zai tafi yabar nigeria. Ina ganin haka banma yadda na sauko ba na nufi ɗakinshi.
Da sallama na shiga ya amsa yana gyara ma Papi riga , kusa dashi naje na tsaya ba tare da na sake magana ba , shima baimin magana ba yaci gaba da abinda yakeyi , bayan ya gama yace ma Papi yaje ya jirashi wurin Ashiru yana zuwa , saida ya taɓoni yana murmushi yace kayyalni nayi cau….? Murmushi nayi nima tare da cewa kayi kyau , na ƙarasa maganar ina kallon Dikko dake ta wani haɗe rai , Papi yana fita na ƙara matsawa kusa dashi nace ina kuma zakaje ne ? Rai a riƙe kuma bai kalleni ba yace inda kika aikeni…..
A ɗan tsorace na taɓashi da hannuna na dama ina kallon fuskarshi , da yanayin tsoro nace yanzu kuma meya faru kake fushi ? Ba komai ya faɗa a taƙaice yana matsawa daga kusa dani , ƙara matsawa nayi inda ya matsa jikin madubi yana tattara wasu takaddu , baimin magana ba saida ya ajiye makullin ɗaki a gabana , girgiza kai nayi alamar a , a , to minene ? Cikin rawar murya nace zanji babu daɗi ne idan ka tafi , da gaske ? Ey , kin tabbata ? Na tabbatar da haka , ai bazan daɗe ba ya ƙarasa maganar yana ɗaukar takkadun ya matsa gaban gado ya ajiye sannan ya nufi wurin weldrop , ƙara binshi nayi na fara kuka , har yanzu yaƙi ya kalleni , amma a tausashe yace kinsan ni bana san wannan kuka²n ko ? Yayi maganar yana miƙomin hannunshi. Riƙe hannun nashi nayi shi kuma ya riƙe tare da shigar dani jikinshi. A kasalance yace yi shiru An matana.
Cikin kuka nace to me yasa zaka tafi ne ? Yi haƙuri ai zan dawo in Allah ya yadda , kwantar da kaina nayi saman ƙirjinshi naci gaba da kuka , bai sake magana ba kuma bai ɗagani daga jikinshi ba , yadai cire hannunshi daga kaina ne tun lokacin daya shigo dani jikinshi. Kenan bai rumgumeta ba , saidai a ranshi yaji babu daɗi tanayin kuka , a zahirance kuwa ya nuna ko oho da yanayin ma idan tai mishi ɗanyen kai zai zaneta ba abinda ya dameshi , Allah ya sani yana san An mata kuma yana tausayinta amma ta rainashi iya raini dan ko gaban waye idan ta tashi mishi rashin kunya sai taje inda take so hankalinta zai kwanta , kuma ita rayuwa ba’ayinta haka wannan dalilin yasa shi yaja mata layi ya kuma tsare gida yanzu yasan tsoronshi ya fara hawa zuciyarta. Gashi yanzun ma taji tsoronshi shi yasa ta firgita dashi take mishi magana a tsorace , naso na tambayeshi abinda yasa zaiyi tafi bai faɗamin ba , kuma ince mishi kenan da banga ma’aikata a palo ba saidai inji labari baya nan , tou ya wani haɗe rai cikin rashin mutunci , sauka nayi daga jikinshi bayan nasha kukana harna gode Allah duk na ɓata mishi rigar jikinshi da hawaye , ina sauka ya cire kayan ya canja wasu.
Bayan ya gama ya ɗauki abinda zai ɗauka da wayoyinshi danshi bayayin tafiya da kayan sakawa shi kaɗai ɗinshi yake tafiya saidai ɗan abinda ba’a rasa ba , da ya tashi fita yayi bankwana dani kamar yadda ya saba , ya sumbaceni tare da shafa gefen fuskanta , ya riƙe haɓata yana ɗagota dan mu kalli juna , na kalli cikin idonshi yayi murmushi mai tattare da tsantsar so sannan ya ƙara shafa fuskata ya kama kumatuna da yatsu biyu kamar anayi ma yaro wasa yanamin wani irin kallo , ajiyar zuciya nayi tare da sauke idona wani wuri daban na daina kallonshi , wasa yayi da tafin hannunshi a gefen fuskata { kumatuna }sannan ya fita daga ɗakin ba tare da yayi magana ba. Yana fita na fashe da wani irin kuka mai kama zuciya , yana jin kukan Sultana har a ranshi amma ya daskare yai tafiyarshi…….
Wani irin ihu nayi tare da buga wayata da bango ta watse lokacin da naga kuɗi sun shigo a cikin asusun bankina , kuɗin banza kuɗin wofi ko an faɗa mishi kuɗi nake so ne wai….? Nayi kuka׳ , bana san Dikko yanamin nisa nafi so ya zauna gida muyi ta faɗa…. Duk taron mutanen dake palo suka ɗinguma dan rakiya bayan Dikko ya bulalesu da manyan kuɗi , su Ashiru kaf dasu aka tafi hada Papi.
Sai azahar nabar ɗakin Dikko bayan nayi sallah kuma banje makarantar ba , a ɗakina na haɗa wayata data fashe na kira Mai gilashi , babu wani ɓayata lokaci ta ɗauka , bayan gaisuwa nace ko kirana bakya iyayi kinga kwana biyu bana zuwa makaranta , ai kyace ita wannan lafiya….? Daga haka nayi shiru danjin amsar da zata bani , wata irin dariya nayi sosai dan wata irin ƙatotuwar batsa data sako , jin ina dariya yasa tace bana san iskanci fa sai anjima , ah jira Mai gilashi zaki zo gidana ? Keni fa na faɗa miki bana iya zuwa gidanki , babu munafurci tsakanin ni da kuma ke , D ‘ K ka haɗa hanya dashi ya maka rashin mutunci ina kuma kazo gidanshi….? Gaskiya ni bana iya zuwa gidan D ‘ K , baya nan fa , kizo dan Allah , kashe waya Mai gilashi tayi tare da ƙurawa wuri ɗaya ido…..
A bayyane tace gidan D ‘ K , hmmm….
Kyakkyawan murmushi ta hasko yayin da aka gurfanar da ita a gabanshi , da wannan kallon rainin wayan nashi da yake ma mutane ya kalli Mai gilashi , cike da duniyanci ya ke wani murza bakinshi yana cin cingom cikin salonshi mai ɗaukar hankali , kuma shi bawai dan ya burge wani ko wata ba yakeyi , a , a ra’ayinshi ne yake ci , sai yakeyin abun cikin yanayi mai motsa ma mata hankali , dan ita mace abu ƙalilan yake ɗaukar mata hankali tare da tayar mata dashi , yana da kyakkyawan baki ne , ga gemun daya ajiye kamu ɗaya. Kuma gemun yayi matuƙar martaba mishi kyakkyawar fuskarshi gashin gemun ɗan gazar² kuma gazar ɗin mai ladabi da sheƙi dan ko bai gyarashi ba baya wani duƙunƙune wa ɗin nan yayi kalar ƙazanta ko rashi kyau. Yana da kyakkyawan gashin gemu mai burgewa , sai kuma kyau ya haɗu da gyara , kuma shi gemun nan fa ba dan wata ya ajiye ba. Shima kwalliya yayi ma matarshi An mata dan ya riƙa burgeta tunda yaga gemun yana burgeta dan tana yawanyin wasa dashi idan suna tare. Shi yasa yabar mata dan tayi farin ciki. Ita kuma taunar cingom inshi baiwai taunar hauka yake mishi ba , baya buɗe bakin motsawa yakeyi cikin natsuwa sai salon ya bada wani irin sirrintaccen sirri mai ɗaukar hankalin mace da sa mace taji ya burgeta kuma ta kasa daina kallonshi , kawai dai zataji sha’awar yadda yakeyi , cikin sakata irin tasu ta rigimamin yara yace kece kike san gani na ido² ko ? Ya ƙarasa maganar yana murmushin mugunta , yadda yayi maganar ne yasa ya bata sha’awa dan haka itama mai gilashi tayi murmushi tare da sauke kanta ƙasa tayi shiru.
Murmushi Dikko ya sakeyi a karo na biyu ya ɗauka robar ruwan dake gefenshi yasha , turo leɓonshi na ƙasa yayi kaɗan tare da riƙe shi da leɓonshi na sama yana mata wani irin ƙazantacen kallo , saida taji cikinta ya juya lokaci guda jikinta ya nuna taji tsoro. Ɗan karkace kanshi yayi shima kaɗan da alamar kowa ya fita , da sauri ta fara juye² tabi mutane da kallo har suka gama fita , ya akayi ne…? Ya tambayi Mai gilashi , cikin rawar murya tace yi haƙuri ranka ya daɗe , a , a , kuka ta farayi tana ci gaba da cewa kayi haƙuri dan girman Allah , gyara zamanshi yayi cike da mugunta yana cewa har kin gama gani na ne ? Ya ƙarasa maganar yana mata kallon ɗage , shiru tayi shi kuma yace tou kin fasa ɗaukar hoton dani ne…? Tuba nake ranka ya daɗe , zo nan ? Yayi maganar yana nunawa da hannunshi ta matso gabanshi , matsawa Sa’adatu tayi tana ci gaba da kuka , tashshi { yaji } ya ɗauko cikin wata “yar ƙaramar roba ya watsa mata a ido….
A firgice Mai gilashi ta goge zubar data tsatstsafo mata a fuska ta goge idonta dake ɗigar da zufar hawayen azaba dan tuno azabar da Dikko ya gana mata kamar yanzu ne yake zuba mata yajin , wanda ba kowa ne yaja mata ba sai Sharifa , kuma itace wacce Dikko yayi ma liƙi , kuma Sharifa karuwa ce ta gaban mota amma musulmin karuwanci takeyi , murmushi ɓacin rai Mai gilashi tayi tare da ɗaukar wayarta ta fara kiran Sultana….
Ina kallon kiranta yana shigowa yana fita nima nayi fushi. Murmushi Mai gilashi tayi tare da turama Sultana text , Allah ya huci zuciyarki uwar gidan D ‘ K kuma Amarya , daga kanki idan dai kuɗin da D ‘ K zai biya da sunan sadaki ne dan ya auri wata mace , tou ina miki albishir daya ƙare. Kina ciki muna waje , a gida kika san Dikko a waje mune zamu baki labarin ko waye D ‘ K , kizo makaranta idan Allah ya kaimu gobe akwai labari.
Maƙiyi zai iya mutuwa amma har abadan duniya gaba baza’a daina ba , kamar yadda na faɗa muku karuwanci shine abinda mai gilashi ta zaɓa , to shine cinikinta kuma karuwanci shine sana’arta , Sharifa ƙawar mai gilashi ce ta hannun dama kuma ƙawancen an haɗashi a bariki ne. Sharifa tana alfahari da Dikko da kuma gwamna , ko taɓota mutum yayi sai ta fara burga a waya Yaya D ‘ K kaza² alhalin kuma ko number wayar Dikko bata dashi a wancan lokacin. Gwamna Yayan Mom inta ne , munyi waya da Yaya D ‘ K yana saudiyya ko yanzu yabar Madina ya tafi Makka , yaje London ko yana America kullum shine ƙaryar Sharifa idan aka zauna a mutane. Kiran sunan Dikko da takeyi yasa ake santa dan su a ganinsu zata jasu suje wurin Dikko yayi danbe dasu ya basu manyan kuɗaɗe , dan da harkar mata Dikko ya nufa da tunin duniya ya lalace dan zina ƙarshen rashin kunya ce. Kuma ba ƙaramin ɓarar da mutunci daraja da kuma martaɓar ɗan adam take ba , sun ɗauka Dikkon ɗan tsakiyar fili ne ashe ɗan bayan fage ne basu sani ba , suna mishi kallo go ashe back ne basu sani ba , yadda suka fassarashi kuma suka kalleshi haka yake amma iskanci shi da duniyanci da duk wata tasharshi shidai An matarshi kawai yake mawa , kafin ita Sa’adatu tasan Dikko sunanshi ta faraji da rashin kunyarshi.
Sharifa tayi alƙawari wa su Sa’adatu idan Dikko ya dawo nigeria zasuje wurinshi , ita kuma Sharifa ganin Sa’adatu tana san ƙureta yasa ta fara neman faɗa da ita , amma Sa’adatu ta liƙe taƙi zuciya tana dai manne bayan kuma ita Sa’adatun tayi bincike ance mata Dikko yana nan baije ko ina ba , ana haka ne akayi rasuwa can ahalin Maman su Dady , ƙanwar Kakar Dikko ta wurin uwa data aifi Dady , dake ba’a abu dan Allah ƙwai da kwarkwata ƙannen Dady da “ya “yansu suka je ranar addu’ar 3 , anje kara wa Dady , shi kuma Dikko dama baya shiga hurumin kowa tunda ko family meeting da sukeyi shi baya zuwa ba abinda ya dameshi da sabgar kowa daga doki sai mota sai kuma bugun zuciyarshi An mata da tazo daga baya ta hana ma zuciyarshi hutawa da soyayyar ta , a wurin ta’aziyar ne Sharifa ta ratso dubun mutane ta isa wurin Dikko tace mishi dan Allah ya tsaya suyi solfie , idan sunce shi ɗan uwansu ne sai ace ƙarya sukeyi , yadda tayi sakin layin ne sai abun yasashi yayi murmushi Sharifa ta ɗauki solfie kenan yana cikin yanayin farin ciki , wannan hoto fa shine ta maƙale mishi take ta yaɗawa a kafafen sadarwa na yanar gizo. Face buk , Instagram , whatsapp d p inta shine kullum , wannan hoto shine status inta ba dare ba rana , da ƙawaye suka fara mata gori mai hoto ɗaya , sai ta shiga familynsu ta samo hotunan Dikko irin wanda “yan uwanshi ke sassakawa masu numbobinsu suke samu , nan fa tazo taci gaba da kafawa , kuma itace tasa Mom inta ta sama mata number Dikko a wurin Aunty Bilki abiyar zaman Momy kenan , Maman Sharifa kuwa ta faɗa ma Aunty Bilki tana san Sharifa ta auri Dikko bata ɓoye mata komai ba saboda su biyun nan aminan juna ne kuma aminci ake na ƙuryar ɗaki. Gashi kuma Momy bata shiri dasu saboda ta rainasu rainin har na wuce misali , dake taga kishiyarta zata shiga damuwa yasa ta miƙe itama sai anyi auren nan dan Momy ta ƙuntata tunda tasan bata sansu , tana so ayi auren kodan Momy ta gune , da kuma buƙatar ta na daban tunda ba Al ‘ Ameen , tana so Sharifa ta shigo. Ta nan ne ma kaɗai zata rufe littafin rayuwar Dikko , tayi waje da Momy ta fasa gidan dan Dikko shine ƙaryar Momy da ma duk wanda uwarshi bata gdan.
Itace ta miƙe da gaske tasa Dady yasa Dikko ya auri Sharifa dan tasan Dikko baya tsallake maganarshi , su kuma maza basa gane makircin mata da irin “yar nehun nan , sai akayi ma Dady nehu haɗe da bariki shi kuma ya fahimci hakan abune mai kyau da kuma ƙara martabar zumincin su , shine fa Dady ya tura Dikko yaje wasan ya kuma ƙara da cewa ya riƙa zuwa zance akan lokaci dan su samu fahimtar juna , banda fushi ɗaure fuska kar yayi duka ya zama mai haƙuri da sakin rai idan yaje , Momy kuwa tace masa bata so , amma sai yace ta kwantar da hankali shi bazai riƙa zuwa zance ba , tace ita ba ma zancen ba auren nan ne gaba ɗaya bata sanshi kuma baya yinshi , dan jakanci fa shine ita kuma Sharifar take zuwa wurin Dikko , ko zai kai ƙarfe nawa bai tafi gida ba zata zauna dashi tana mishi fira , da lafazin su dai irin na “yan bariki har akayi mata liƙi , wanda kuma duk karatun Aunty Bilki ne dan itama sai jawo Dikko jikinta take danma shi Allah yasa mishi wani irin hali haka na kamar dai yanajin tsoron mutune , kuma baida sakin jiki dasu , kana iya zama dashi yau kuyi fira yafa sanka amma idan ya ganka gobe ya nuna shi baima taɓa saninka ba kwata² a rayuwa , kai ta mishi bayanin ka yace shifa bai wani gane ka ba , kuma zaiyi wahala ka bashi abu yaci ko yasha ko kuma ya saki baki kamar sakarai yaita maka surutu ko yawan murmushi , wallahi Allah akan Sultana kawai Dikko ya faracin abunda ya fito daga hannun mace a waje kuma daga kanta ya daina , shi kanshi ya natsu yayi nazari tunda yake bai taɓa ganin macen data bashi wahala kamar An mata ba , kuma shima babu macen da tasha wahalarshi a duniya sai An mata , yana santa soyayyar da tunda yake bai taɓa ma kowa irinta ba sai ita , akan An mata ya fara mafarkin mace , kuma itace farkon macen daya bi ya wuce , itace mace ta farko data mareshi ta zageshi taja mishi gemu yayi murmushi bayan ta gama , itace macen data kashe mishi dokin daya fi ƙauna wanda har yanzu idan ya tunoshi sai yaji babu daɗi saboda san da yake ma dokin , itace macen data maida rungumarshi ba,a bakin komai ba , yana san Sultana fiye da yadda tunanin mai tunani baya iya hasasowa amma bata kunya ko kaɗan haka kuma ta rainashi sai babban iskancin data koya yanzu na raba shinfiɗa dashi , ya ƙyaleta ya kuma zuba mata ido bawai dan baya san su kasance taren ba a , a saboda cikin da take dashi ya ƙyaleta dan idan ya riƙeta da fushi tou fa lallai za’ayi ɓarna. Yana addu’a ta sauka lafiya zataci ƙaniyarta idan ya riƙeta a ɗaki…..
Sa’adatu kuwa wani abokin barikinta ne ya haɗata da Yazeed , Yazeed shine ya kaita wurin Dikko bayan ya biye allonta shima { danbe }, daya faɗa mata ranar da zusu wurin Dikko shine take faɗa zatayi hoto da Dikko idan suka haɗu. Kuma tayi mishi shirin hana bacci , yau duk wasu musu ƙaryar suna tare da Dikko suma zasu je wurinshi kuma zatayo hoto dashi , Sharifa ce ta bawa Dikko labarin zuwan Sa’adatu wai akwai wata karuwa tana faɗa a gari zata zo tayi mishi fyaɗe , abun ya bashi dariya amma baiyi ba a gaban Sharifa saida ta tafi , yaso yaba Sultana labari amma daya koma gidan tai² mishi ɗanyar ƙwalwa , shi yana so ko abu ya faru dashi , ko ya gani , ko yaji yana so ya riƙa faɗa mata suyi farin ciki tare amma ita kwalwarta tana kallon ƙasa , ita kuwa mai gilashi tayi alƙawarin miƙewa tsaye da ƙarfinta da barikinta da tasharta sai ta rama abinda Sharifa tayi mata dan raba tarayyarta da Dikko kamar yadda ita Sharifa ta zuge wani mai san ita Sa’adatu ya fasa aurenta tou itama ta lashi bala’en hana aurenta da Dikko ko da kuwa hakan zai zamar mata silar barinta duniya , wannan kenan.
Kamar wasu mayu haka suke ta yayam² suna cin shawarmar da Yazeed yasa aka basu , Jiddah ma data zo yanzu an bata nata kasafin itama ɗayar mayyar ta lashe. Bayan ta gama ci ne tace ma Yazeed wurinshi tazo fa , babu wani damuwa yace ina saurarenki yayi maganar yana bata umarni da hannunshi tayi magana , kasan dai komai yana buƙatar sirri ba , cikin matan ne wata tayi katsalandi cewa ba buƙatar sirri a wurin nan malama faɗi abinda ya kawoki basai kun wani tashi ba , ke bake a maganar nan dan haka tsamewa mutane baki , Jiddah ta faɗa. Idan naƙi kuma ? Sai jikinki yayi tsami , umarni karuwar ta bayar cewa jikin Jiddah ya tsamama yanzun nan. Dakatar dasu Yazeed yayi ta hanyar miƙewa yacewa Jiddah suje , a motar Jiddah sukayi masauki dukansu.
A hankali ya turo ƙofar ɗakin kamar ɓaron tsakar dare a barikin sojoji , ƙiyyyyy ƙofar tayi ƙarar buɗeta a yayin daya fara tura ƙofar dan shiga cikin ɗakin. A tunanin shi tayi bacci amma da mamakinshi sai ya ganta zaune gefen katifa tana ta shafa wayarta mai tambarin apple a bayanta. Cike da ladabi ya takure daga bayan ƙyaure ya durƙusa cikin biyayya sannan ya matsa gaba kaɗan ya ajiye mata ledar daya shigo da ita da kuɗi cewa ranki ya daɗe gashi. Hankalinta yana saman wayarta tace masa nawa ne ? Cikin rawar jiki yace dubu biyar ne… ! Bakaji me nace maka ba ? Kiyi haƙuri dan girman Allah wallahi har rance na nema a daren nan ban samu ba , shiru tayi ta manta ma da yana cikin ɗakin taci gaba da sabgar gabanta a waya……
Yazeed barka da dare , barka dai matar mai gida , kanta taji yayi mata wani irin gingime cikin izza da nuna ita wata shegiya ce tace , am Ya Yazeed meya haɗaka da Ya D ‘ K , shiru yayi na wani lokaci sannan hawaye ya gangaro mishi daga idonshi yace , hmmm dare ake bi a samu suna , inko ba’sha dare ba asha rana , idan kikayi duba mutum biyun nan basa sabgoginsu da rana ko safiya , daren nan dai shine suke bi su nema kuma sun biɗa sun samu , kiyi tunani duk ɓarowa sai dare yayi yake fita dan haura katangu , masu nema wurin ubangiji idan dare yayi su lokacin garinsu ya waye , zasu kasance ne a saman abinda sallah suna Allah ka yafe mana ka bamu׳ , shin ko kinsan dalilin yasa D ‘ K yake huɗɗonshi cikin dare ne…..?
Kai kunnamin hasken can kaji , jikinshi yana ƙyarma ya tashi duk ya haɗa uwar zufa kamar manomin da ruwan damina ya ɗauke a lokacin da gero ya fara bininiy , duhu yabi ya lalubo makunnin fitila dan tunin duniya ta ajiye wayarta haka ne yaba duhu damar gauraye kaf ilahirin girman ɗakin , a kiɗime ya kalli Sa’adatu bayan haske yazo , cike da tasha tasu irin ta “yan tasha ta buɗe jikinta gaba ɗaya , idonta na dama ta kashe mishi cikin salon jan hankali , ha… Ya sauke ajiyar zuciya. Wasu wurare ta nuna masa a jikinta tare da bashi damar zuwa kusa da ita , tafiya yayi kusa da ita ya durƙusa ƙasa ƙiƙi² ya hunce ita kuma ta bashi damar tattaɓa jikinta itama tana tayashi da shashshafa mishi wasu mahimman wurare a jikinshi dan tabbatar mishi da martar cewa shima namiji ne. Kaɗan ta ɗan lulashi saman network saida ya tafi ya kusa cinma nasara tace dubu biyar ya ƙare , dan haka ta saukeshi daga saman katifarta ta mayar da kayanta sai ya kawo cikon dubu biyar zai shiga gabatar da wasan danbe…… Wani irin gurnani yayi tare sake nufa inda Sa’adatu take yana wani irin huci kamar an jiƙa mahaukaci a lokacin sanyi , dakatar dashi tayi ta hanyar cewa idan ka haumin katifa saina yaga mutuncin ka , ni nafika ƙaryar rashin kunya iskanci tasha da kuma lalacewa , tattara gashin kanta tayi cewa bani kazar inci…… Ta ƙarasa maganar tana ɗaga mishi gira. Kamar wani gele haka ya miƙo mata , yagar kazar ta farayi saida ta cika bakinta da ita sannan tace tou yi sauri kaje ka samo cikon kuɗin ka kawo ni kuma na ɗoraka a saman lambar girma tayi maganar tana murmushi tare dakai hannunta ta nuna mishi tsakiyar filin wasan danbe…… Bashi da yadda zaiyi dole ya maida kayanshi ya fita daga ɗakin dan yasan tashar Ade mai gilashi ta girmin tunaninshi.
Gyara zama Jiddah tayi ta kalli Yazeed sosai sannan ta tambayeshi kamar yadda ya tambayeta itama tace me kuwa yasa yake huɗɗonshi cikin dare……. ? Yazeed yace shine abinda nake so na sani tun farko kenan dan duk yadda akayi nasarar rayuwarshi a cikin dare take , kinga D ‘ K baya waya da rana saida daddare idan kika cire wasu ƙalilin mutane wanda su wayarsu ma daban ya fitar musu , uwa uba matarshi sai Ashiru danni tunda Ashiru ya wulaƙanta ni ya korani daga company ya kawo Abbakar bana samun layin da nake kiranshi dashi da rana ko safe duk dai lokacin dana so nayi magana dashi. Jiddah tace nima yanzu ko na kira saima acemin number ma babu ita a duniya saida na sameshi a layin da kowa yake samunshi , idan kuma na saka number a wani waya shima dai baya tafiya wai meya ɗauki mutane ne…. ? Jiddah tace koma meya ɗaukemu zamuji mu kuma gani idan na koma gidanshi.
Wani irin kallon raini Yazeed yayi mata mai nuni da tama samu warwarewar tunani , ita kuma tana ci gaba da cewa manta da wannan damuwar kaji abinda ya kawoni wurinka , inajin ki ya faɗa bai sake kallonta ba , hoton Sharifa ta nuna mishi tana ce masa kasanta ne ? Kallon hoton yayi sosai sannan ya miƙawa Jiddah yace ya akayi ne ? Yaya D ‘ K yayi mata liƙi kuma aurenta zaiyi , kai tsaye Yazeed yace wallahi D ‘ K bazai aureta ba , ke kina wasa da Dikko ko ? Tou D ‘ K mashaune shi ɓadda musulmi , shi kanshi tsoron kanshi yakeyi kuma bai yadda da kanshi ba , ita wannan yarinya da kike magana yanzu haka tana wurinshi Abuja taje mishi rakiya zaiyi tafiya. Jiddah tace zai aureta , Yazeed yace bazai aureta ba , haka sukayi ta maimaitawa kusan sau goma , shi Yazeed yace Dikko bazai auri Sharifa ba , Jiddah tace zai aureta , daga ƙarshe dai suka rabu a haka kowa yana cewa zaka gani , shima yace mata zaki gani…..
A wahalce ta ajiye kwalbar cikin maye tace wallahi saina auri D ‘ K , wata irin dariya Amisty tayi tare da cewa Dikkon ne zai auri “yar shaye² ? Cikin maye tayi magana cewa tsaya kisha kallo…… Dariya Amisty ta sakeyi tare da cewa me kuwa zan kalla saidai inga yadda zakici ubaki , murya a lalace da maye Hafsa ta nuna Amisty da ɗan yatsa tana rufe ido da yanayin buguwa murmushi ɗauke a fuskarta tace kema kina layin “yan hassada ko……? Tayi dariya. Tou dama malam ya faɗamin “yan hassada zasu fito ɗaya bayan ɗaya ngode ma Malam daya nunamin ke Kaka , ashe haka kike hassadata ban sani ba ? Gaki nan Malam ya zaƙulomin , buɗe tafin hannunta tayi tare da nuna ma Amisty tace me kika gani ne ? Wata irin ƙatuwar ƙuna ce a tafin hannunta , bayan ta tabbatar Amisty ta kalla ta naɗe hannun da tsumma kamar yadda yake farko cewa malam yace wannan ƙunar sai a gidan D ‘ K zai warke , ta ƙarasa maganar tana dariya irin ta mashaya……
Da massara ya isa Abuja shi yasa tunda ya shiga ciki bai fito ba yana kwance a gado jikinshi har ƙyarma yakeyi , saida yayi sallah isha’e yasha magani ya koma bargo. Ba tare daya juya bayanshi ba yace Papi tashi ka kawomin wayata ana kirana , sauka yayi ya ɗauko wayar ya kawo mishi , samin a kunne na yayi maganar yana kallon Papi , yadda yaga anayi idan za’a ɗauki wayar yayi tare da ɗorawa a saman kunnen Dikko shi kuma ya fara magana , bayan gaisuwa yace wallahi banajin daɗi ne Momy , magana tayi sannan yace a , a , shiru ya sakeyi bayan wani lokaci yace gaskiya ban sani ba. Ey Papi Momy zatayi magana dakai , cire wayar yayi daga wurin Dikko ya kara a kunenshi yana magana da tsantsamar muryarshi , kusa da Dikko ya ajiye wayar bayan ya gama ya koma ya kwanta gabanshi , yana mishi sannu , cikin yanayin damuwa yace Papi kaga Momy bata kirani ba ko ? Ta kiyaka Yaya , a , a Momyn goruba , ɗaukar wayar yayi yana cewa bari a kirawota Yaya ,
Tsareshi da ido Dikko yayi , saida ya yagaji da shirmenshi ya ajiye wayar ya fara bacci tunda bai iya kira ba , saida ya tabbatar Papi yayi bacci yayi mishi addu’a tare da gyara mishi kwanciyarshi shi kuma ya fara kiran Sultana , amma tsabar iskanci taƙi ta ɗauki wayar , ya kira harya gaji ya haƙura wanda bai ɗauki waya ba taya zaiyi lokacin duba wani saƙon banza can….
Tunani daban² a ranshi na sabon iskancin da An mata ta koyo , amma yayi alƙawari bazai sake kiranta ba taje can ta ƙari rashin wayanta. Yau sai 12:23am ya cire wayarshi daga jirgi , yana buɗewa kiran Yusra yana shigowa da bazai ɗauka ba amma sai yaji tausayinta har wane tsawon lokaci ta ɗauka tana ta kiranshi sai yanzu ta samu kuma bata gaji ta daina kiranshi ba haka batayi bacci ba. Yasan dan dai kawai tayi mishi sannu da hanya ne wacce ma baa matarshi ba ta damu dashi da san sanin halin da yake ciki , shidai bai faɗa mata ba amma yasan kila taje g r a ance mata yayi tafiya ne , ɗauka yayi tare da kara wayar a kunnenshi yayi sallama.
Ajiyar zuciya Yusra ta sauke cikin kissa sannan ta amsa sallammar da mairainiyar murya , ya gda ? Ya tambayeta , bata ansashi ba taci gaba da watso kalamai na matan waje cikin rashin kunya tana kambamashi da zugashi tare da turashi wata madakatar da bai isa zuwa ba , murmushi yayi kaɗan kuma mara sauti ya kalli Papi dake bacci ya riƙe mishi wuya da hannu ɗaya , shiru yayi yaƙi magana ita kuma taci gaba tunda ai tasan yana jinta , duk kiran dake shigowa bai ɗauka ba kuma bai tsinke kiran Yusra ba haka kuma baiyi magana ba yana dai kallon Papi , itace ta gaji ta sauka a layi.
Kiran Hafsa shima ya ansa saidai ita bata doguwar tafiya dan bata da irin kalaman da yake so , duk da yanajin haushin Jiddah yana ɗaukar kiranta , itama Mardiyya tayi nata kuma duk sun hura mishi kanshi yanajin yakai wani baban shege , Sharifa kuwa ai suna tare amma ba’a ɗaki ɗaya ba. Yau ko namiji ɗaya baiyi magana dashi a waya ba saidai a cht , tunda ya buɗa wani saƙo ya haɗe leɓunanshi tare da riƙe na ƙasan ta ciki da haƙori ya kura ma hoton wata kyakkyawar yarinya ido , ɗayar wayarshi ya ɗauka ya kawo hoton Sultana a bayyane yace akwai tazara har yanzu….. Ajiye waccan wayar yayi yaci gaba da kallon hotunan Sultana yana murmushi wani kuma yayi dariya yace An mata rigima Allah ya saukeki lafiya jarumata…….
A dajin data gama tsibbunta a wurin ta kira Dikko tayi magana dashi kamar yadda mushiriki ya faɗa cewa idan ta gama ta kirashi kuma zai ɗauka idan harya ɗauka a lokacin ruwa da iska baya hana Dikko ya aureta sai sunyi aure ,
Ɗan madaidaicin gidane a nan cikin anguwar kwaɗo duk yara²n mata ne suka taru suna ta gulmar mazajensu………. Har 12:39am gidan cike yake wai ana fira , wasu mazajen su matafiya ne basa nan , wasu kuma suna da abokan zama mazansu suna gidan abokiyar zamansu , ita kuma mamallakiyar gidan mijinta yana can majalisa.
Jakar mace da ita , duk sauran mata sun gyaro gidansu sun gogo ɗakunansu sun saka turaren wuta sunsha wankansu sun taho gidan ballagazar mace fira , ita kuma daƙiƙiyar ta kora mijinta waje ƙawaye sunfi miji dai. Bursunai² da ita sai wari takeyi ba wanka bare wanke ido , wacce batayi haka ba wace fikra gareta na sanin rayuwar duniya….? Tou hausawa dai sunce wanda maciji ya sara idan yaga igiya guduwa yakeyi , masu iya magana kuwa cewa sukayi wanda aka mara yayi hankali yafi wanda aka haifa dashi. Ɗaki daya ne tsal a gidan , nan kicin yake bedroom da toilet , palon nan da kujerunta sunyi daƙa² kalar tashin zuciya , kwanukan da sukaci abinci da wanda aka zuzzubar duk ba’a ɗauke ba , tunda sun ɓata palon kuma wai sai suka koma ƙuryar ɗaki ana fira ,
1 saura mijinta ya shigo gida , a palo ya ajiye ledar biredi daya shigo da ita da ɗan naman daya riƙo musu ya fara tattara kwanukan dake palon , jin buruntu a palo yasa ita mai gidan tace Hadiza leƙa kiga waye , ita Hadiza data tashi fita sai ta cire hijabi ta gyara ɗaurin kallabi tayi palo…..
A palo , da sauri ta isa wurin mijin Halimatu tana riƙe tsintsiyar dake hannunshi cike da makirci irin namu na mata tace haba “yar laɓai ai wannan aikin ba naka bane ba , a gafarcemu tayi maganar tana murmushi mai tattare da ɗaukar hankali , shima riƙe tsintsinyar yayi yana cewa ta bari kawai zai share ya faɗa yana murmushi , suma na bedroom sunaji amma Halima bata fito ba sai kuma Zainab ta fito aka baro Fadila da Halimatu matar gidan kenan a bedroom. Ita kuma Hadiza tana riƙe da tsintsiyar suna jayayya da mijin Halimatu akan bazai saki ba zai share…
Itama Zainab tana isowa ta riƙe tsintsiya haba ranka ya daɗe ina za’ayi wannan abun kunya ka rufa mana asiri mu share , daga cikin bedroom kuma Halimatu tayi dariya tana cema Fadila ai dake bashi da matsala shine zai share bazai basu ba , a palo kuma Hadiza sai cewa takeyi ya bada tsintsiya , ganin dai sun dameshi yasa ya haƙura ya bata tsintsiyar kuma idan sun gama shine ai rakasu gida ,…….
Idan namiji bashi da matsala kece kike koya mishi ya zama mai matsala , idan namiji bai iya yawon majalisa ba kece kike koya mishi , Halimatu da mijinta auren soyayya sukayi , mijinta bashi da kuɗi amma yana da rufin asiri kasancewarshi ƙaramin ma’aikacin gwamnati , sauran matan nan dana lissafo su 3 , ɗayan su huɗu ne a wurin mijinta , bata yini gidanta kuma batacin abincin gidanta kuɗin cefanenta da komai nata take aikashi wa iyayenta tunda ta samu na mijin ballagar mace iyayenta suna buƙata tunda ta wadata saita wadatasu da kasonta na gidan miji. Kullum da ita ake majalisa amma idan mijinta yazo gidanta zata zauna ta kula dashi ta bashi duk irin kulawar da yake buƙata asha soyayya sai ya tafi taci gaba da zuwa kuma shi baisan tana wannan iskancin rashin zama gida ba.
Ita kuma ɗaya mijinta driver ne , idan ya tafi sai yayi wata biyu bashi nan , itama a gidan jakar mace take ci tana sha tayi wanka da wanki itama kuɗin da mijinta yake bata idan zai tafi sai ta shiga adashe tunda an samu na mijin daƙiƙiyar mace , ɗayar kuma mijinta gadi yakeyi a asibiti shi dama baya bayar da wani kuɗi saida idan an samu albashi ya ɗan sissiyo abinda ya sawwaƙa daga ita har mijinta a gidan mijin wawiyar mace suke ci suke sha , itace Hadiza , Halimatu kuwa matar gida ba , mijinta yana aiki a C B N ubangidanshi ya cusashi da satifiket ƙaramin ma’aikaci ne amma dogon buri yasashi yakeyin digiri karatun asabar da lahadi , { part – time } ya kusa gamawa ubangidan nashi yake san ganin ya tashi daga ƙaramin ma’aikaci ya zama babba.
Sai 4 saura na sauka a abin sallah , kuma sai a lokacin naje inda wayata take , bayan na ɗauketa ne naga miss calls inshi 7 , data na buɗe nasan yana online , baya online ya daɗe ma da sauka amma ya turo min hotonshi shida Papi suna kwance a saman gado , wai suna gaisheni kuma in sa Allah a raina in daina fushi. Su basuda zuciya kamar yadda nake mishi gori suna gaisheni. Murmushi nayi tare dabin hoton da kallon , ko ina zaije da Papi ? Oho……! Bakuyi kyau ba shine abinda na tura mishi nima na sauka.
Yau na samu damar zuwa makaranta , kuma Mai gilashi ta bani labarin Sharifa ta tsoratani sosai akanta ta firgitani , na gigice na tsorata , ta ƙara da cewa idan ina maido hankalina jikina tou in tashi daga wannan asararren baccin da nakeyi , ta nunamin hotunan Sharifa ita da Dikko wanda koni da nake aurenshi ban taɓayin irinsu ba , bawai riƙeta yakeyi ba ko taɓata ba dan shi baya da ɗabi’ar taɓe²n mata kawai dai anyi hotunan cikin takon so. Hotunanshi shida Yusra , abindai yamin babu daɗi , raina ya ɓaci matuƙa , amma dake ina da ɗanyen kai kamar yadda Dikko yace sai nayi ma abun bahaguwar fahimta akan yadda ita Sa’adatu ta fahimtar dani , maimakon nabi abun a sannu naji yadda sirrin abun yake saina fara kiran wayar Dikko , wayar a kashe take ma wacce baya rufemana ita kwata² duk lokacin da mune muka kirashi zamuji shi…. Haka na haukace cikin aji naci gaba da turawa Dikko saƙon zagi na kirashi da mayaudari munafuki ɗan iska , Farisa taci gaba da zugani ina ta ɓarke²n zagi kamar mahaukaciya tana cewa ai wannan ma nuna miki yakeyi tsaron gida ya barki , ya barki gadi matar tana waje ya tafi da ita ke kuma an barki tsaron gida , haka taita tunomin lokacin da yayi mata liƙi na ida ƙwacewa gaba ɗaya na warware kamar falfela , duk yadda Sa’adatu taso ta fahimtar dani naƙi saurarenta saida na gaji dan kaina na tsaya , bayan wani lokaci kuma na tura masa cewa tunda dai kai ka lalace ka zama karuwa saina fitar da cikin nan. Duk haka bai isa ba na farakiran wayar Ashiru , shima nashi a kashe yake , shima na tura mishi saƙo cewa Allah ya isa tsakanina dakai har kaga ana cin amana bazaka faɗamin ba , munafukai “yan partyn amarya…..
Umar na kira shima na zage tatas kuma nace masa munafuki da kilbibin faɗi ba’a tambayeka bane ka iya faɗa , dake shi Dikkon tsoronshi kakeji shine baka faɗamin ba yana tare da “yan mata , shima dai na tata mishi ɗan ƙaramin haukata na kashe waya. Wannan duk ya zama zargi da wani tunani daban irin namu na mata , duk lokacin da akace miki mijinki yana can yana kaza ko yayi kaza ko kaza yake aikatawa karki kuskura ki yanke hukunci akan abinda baki da tabbaci akanshi , zargi baida kyau haka kuma yanke hukunci cikin fushi yake haifar da ɗa mara ido , domin ita zuciya kamar iska haka take halbawa hawa take da sauka , ƙoƙari ake ana danneta ba’a biye mata haka kuma ba’a bata abinda take so domin za’ayi nadama da dana sani idan ta kwanta…..
Har aka tashi makaranta ban sake magana ba , haka na koma gida jikina suku² duk abin duniya ya dameni na rasa ina zansa raina , sai yanzu na fara tunanin hukuncin da zai biyo , dariyar shi na tuno da yake cemin ki daina ganin kwana biyu na zuba miki ido ina nan yadda kika sanni ban canja ba halina yana nan yadda kika sanshi. Me zai faru idan Dikko yaga texses in nan ? Me zaice ? Ya zaiyi ? Ni kuma ya zaimin ? Me zai faru………….??? Zuciyata tace duk abinda ya faru sai me ?
Jikin madubi na matsa na kalli kyakkyar fuskata da idanuwa na masu burgewa zararan giraren idona da suka ƙara fitomin da kyan idanuwa na , girata yadda tayi wata kyakkyawar ziririyar saƙa su biyun suka haɗe suka ɗanyo ƙasa , dogon hancina na kalla da kyakkyawan bakina , murmushi nayi tare da maida idona saman goshina. Lallausan gashi ya kwanta luf abun gwanin burgewa , ida cire kallabin kaina nayi nabi gashin kaina mai cikar kyau da ɗaukar ido irin na cikakkin fulanin asali da kallo , dirina na kalla ga haskakakkar fatata komai yaji ga hutu ya tabbata a gareni , zuciya tace kallarki Sultana ɗanyar yarinya dake kin cika ta ko ina komai ya zauna kalar burgewa , shekarunki ma yanzu suke tafiya dan zuwa 20 , me zakiyi da Dikko wanda yaƙi yadda ma ya faɗa miki shekarunshi saboda yawansu , gashi nan ma harya fara squeezing , Allah ma yasa yayi fushin kiga yadda zakici wuta a garin nan , ga kuɗinki a account ga mota ga tsadaddun suruta masu yawan gaske. Sarka “yan kunne zobe ɗan hannu duk na zinari kala² , idan kika fita zaki ci gaba An mata da hannuna na nuna da bakina yadda jirgi ke tashi sama , dariya nayi tare dayin rawa a jikin madubi dan mafitar dana samu , kai zanci uwar² uwayen masu wuta , ashe ma hauka yasa nayi aure a Katsina ? Ai ban taɓa lura da haka naɗu ba sai yau , ana ta faɗamin ban ɗauki abin serious sai yanzu na ƙarasa ina wasa da kyawawan idanuwana………
Rawa naci gaba dayi ashe dai na haɗu da yawa shi yasa shima kanshi Dikkon yake cemin An mata , gani da tsawo dai² kuma ni ba ƙatuwa ba. Kai gaskiya inada siga da kuma launin burgewa gani kuma yarinya , Sultana yanzu lokacinki ya fara……..
*JAMILA MUSA…*
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN…*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa…
*JAMILA MUSA…*
*SAI NA AURI D ‘ K*
Naki ne “yar uwata 👇🏻
*ASMA’U ZAYYANA*
{{ Asmeenat Xeyyan }} alfaharina bugun zuciyar *JAMILA MUSA…*
🅿 —— 3
Bani kaɗai ba , mafiya yawan mata haka muke. Duk lokacin da muka shiga cikin wata ni’ima ta daban sai kanmu ya fara rawa mu riƙa yin wani hange na daban , wasu matan basa fara gilu² da kansu sai sun ƙoshi nan zasu ɓalle ƙofar iskanci da rashin kunya. Kamar dai ni yadda na kasance. Gani na tsaya a jikin madubi ina ta kallon kaina yayin da wani sashe na zuciyata ke nunamin in kalli kyauna ! Ashe haka na haɗu ? Haka nake kyakkyawa ? Aiko yadda nake mai kyan nan baima kamata ace ni ina aure a katsina ba , kamata yayi ace ina irin su Abujar nan idan ba Abuja ba ina can wasu ƙasashen duniya mijina ya ɗaukeni yabar nigeria dani , abun ba haka yake ba kuma ba’a kyau take ba. Jin daɗi da arziƙi duk kyanki da iya haɗuwarki sai Allah yaso zakiji. Ba’a kyau , asali ko nagarta yake ba. Arziƙi da hutuwa baiwa ce daga Allah idan yaso sai ya baka ya kuma sa kaji , ni’imar aure daban ce. Allah ya darata ta haka kuma ya martaba ma’aurata. Idan kina ƙarƙashin inuwar aure kinfi ƙima daraja da kuma martaba duk kuwa irin talaucin da mijinki yake fama dashi , kiyi haƙuri kiyi zamanki a gidan aurenki arziƙi na Allahna , kuma wannan ɗin dai shine hatimin tsirarki. Yayin da kika kalli kanki a madubi kika ga ke kin kai ƙarshe wurin haɗuwa ko kyau tou albarkacin martabar aure kika ci , daga zaran inda kikayi yarinta irin tawa kika zuge auren nan kin tashi aiki.
Saboda kiyi duba da wani abu. Gidanku da gidan miji akwai ƙaton banbance² , karki kalli gidanku ana kashe kaji goma duk rana , ana yanka rago duk sati , kina da ɗakin sama ƙaton gado da a c ba’a ɗauke wuta ga wata ɓarkekiyar talabijin ta cinye rabin bango. Kuna cin shagali shayi da biredi duk safiya a haɗa da wani lafiyayen kayan cikin rago , dankali doya kwai da rana a samu wani lafiyayen abinci aci ku kulle na dare da wasu kayan marmari , idan zaki fita a baki driver ko ke ki tuƙa kanki , idan buƙatar shiga bayan gida yazo zaki sauko ne kawai daga saman gado ki shiga toilet hmmmm. Gidan miji kuma koko , tou wallahi wannan kokon ya fiye miki mutunci da kuma kwanciyar hankali , idan kuma kina ganin kin haɗu bara ki kashe auren kiyi gaba , tou budurwar bana tafi ta bara , duk haɗuwarki duk nasabarki duk mutunci duk yadda kike jin kina da nagarta siga ko kyau duk haɗuwarki duk kuɗin gidanku duk iyakar gogewarki da haɗuwarki idan wasu matan na wure tou wallahi ke mayino ce , da kika kalli madubi kika ganki ke kyakkyawa ce ko kin haɗu tou darajar aure ne yasa kika zama haɗaɗɗar idan har tsautsayi ya kaiki kika cire auren nan kina tunanin zaki auri sarki tou fa lallai ko dogari ba naki bane ba danma karki ji ƙamshin masarauta. Ku kiyayi rashin kunya wa mazajenku , kar kuyi irin nawa kuga zagin miji ko rashin kunya ƙauracewa shinfiɗarshi ko rashin mishi sannu da zuwa hanashi abinci da rashin yi mishi magana shine mafita , a , a , wannan babban zunibi ne ga kuma ke mai aikatawa kina kashe kanki ne , kuma kina rage ma kanki mutunci , duk duniya babu abinda yafi mutunci haƙuri da kuma biyayya , zaman lafiya yafi komai karki kuskura ki zama mai tashin fitina a gidan aurenki , ki zaɓi zaman lafiya yafi komai ki kuma kiyayi kanki da haƙƙi……. Karki ce irin halina ya burgeki uhum a , a kar kiyi….
Har dare haka na samu aiki jikin madubi. Saidai inyi sallah in dawo inci gaba da kallon kaina , saida aka kira isha’e nabar jikin madubi naje nayi wanka tare da ɗauro alwallah dan gabatar da sallah , ina gama sallah na fito dancin abinci. Zama na kenan ban fara cin abincin ba akace min wai Umar yana jirana a palon ƙasa ,
Cewa nayi aje ace masa banda lokacinshi , tunda dai na gano makircinshi nasan yadda zan zauna dashi. Ai ni lokacin nida Dikko zai aureni shine yaje ya faɗawa Jiddah , amma ni za’amin bazai faɗa ba , shima Dikkon zai dawo ya sameni sai ya sakeni tunda ba tare aka haifeni dashi ba….
Momy kuwa idan hankalinta yayi dubu ya tashi ɗaya bayan ɗaya , Aunty Bilki baƙar muguwar munafuka ne ta bugawa a jikin mujalla , Umar yazo ya faɗawa Momy Mai gida fa yayi tafiya da Sharifa , wai duk girman Dikko ita Momy bata daina fargaba akanshi ba , ga kuma Papi data matsa mishi tace dole sai yaje dashi tunda hada su Ashiru zai tafi. Saida aka kai ruwa rana ya yadda yayi tafiya da Papi.
Dikko kuma koda yaga saƙonni Sultana baima da lokacinta bare kuma yasa ran zaiyi tunanin bata amsa , mafiya yawan mata suna da cusashshiyar ƙwalwa , ƙalilin ɗinsu ne zasuji zancen ƙarin aure suyi abu na hankali da tunani , ita An mata bai ɗauketa mai hankali ba. Amma insha Allah idan yaga wanda zai auri mai ƙaramar shekaru irin An mata saiya bashi shawara kar ya aura yaje ya auri macen da tasan abinda takeyi , shidai yau gashi har An mata tace mishi karuwa wai shi…. Shine karuwa kamar An mata ta zauna ta rubuto mishi zagi na rashin mutunci , haka Jiddah itama tayi lokacin da zai auri An mata tayita hauka tana zaginshi. Jinjina kanshi yayi cikin ɓacin rai yace aure ba fashi sai nayi idan kin gune ki gyara hali. Kallon Papi yayi dake kwance jikinshi yana bacci duk ya rirriƙeshi saboda gajiya , a bayyane yace idan An mata batayi hankali yanzu ba yaushe zatayi hankali ? Shi kuma yana ganinshi babba duk ya wuce irin wa’anan shirmen , da kuma anyi rashin sa’a suna wuri ɗaya tayi wannan maganganun zai ɗauki zafi shima ya yaɓa mata magana mai zafi ita kuma ta kasa riƙewa ta tattaro nata ɓacin ran da yarinta ta kwaɓa mishi rashin wayau.
Daga nan sai duka , ita kuma a kunne take sai fuuu ta tafi gida tayi yaji. Yadda Mamarta bata sanshi bata ko ƙaunar ganinshi itama sai ta tafasashe ta fara turo doguwar wasiƙa a saki “yarta , ƙalilin matsala ta fito amma ƙaliliyar magana bata iya kashe wutar dake ƙoƙarin ruruwa. Yana ta ƙoƙari wurin ganin ya farka da ita daga baccin rashin wayan data tafi amma baida lokaci kuma shi a ganinshi abinda yasa An mata ta rainashi girmanshi tun farko daya buɗe a gabanta. Yana gani shekarunshi yakai na ita ta girmamashi tasan matsayinshi da ƙimarshi ta kuma riƙa kiyaye wasu kalaman akanshi bata gani kuma bata dainawa.
Shidai da shine mace mijinshi ya tashi ƙara aure ba zagin mijin zaiyi ba , zagin miji , rashin kunya , ƙauracewa shinfiɗarshi da zance yaji ko tambayar sakin aure bashi ne mafita ba. Haka kuma bazai daina dafawa miji abinci ba , sannu da zuwa da Allah ya kiyaye hanya duk sai yayi , da farko dai abinda zaiyi shine , zai duba wace ce mijin nashi zai aura , shi kuma ɗin waye shi , ita wacce za’a auron ya take ? Shima ɗin ya yake ne ? Me yafi ta me tafishi ? Me gareta wanda shi bai kai ba ? Duk namijin da zai ƙara aure dole yana da wani dalili nashi na daban tunda kowa da ra’ayinshi kuma ba a bayyane yake ba a ɓoye yake. Gyara dai kawai shi yafi a gareki , bawai sai auren yazo ba kullum ki kasance a gyara da kiyayewa tsafta biyayya iya lafazi da girmama shi. Kuma duk hakan bazai hanashi ƙara auren ba idan Allah ya rubuto da wani rabon. Kije kiyi duk abinda kikaji kina iyawa danni banda lokacin da zan zauna na koyar dake zaman takewar rayuwa na yau da kullum ƙaramar yarinya dake.
Duk kyan mace idan ba gyara zero. Duk nagartarki da sigarki idan babu biyayyar aure zero. Duk kuɗin gidanku idan kinajin ke wata shegiya ce idan baki bi mijinki kuka zauna lafiya ba baki haɗu ba. Duk kuma yadda namiji yake sanki a zuciyarshi rashin kunya da rashin mutuntashi ke ƙaton zero ce mai ido da kunnuwa a wurinshi dan rashin biyayya wa namiji ba ƙarami rage miki martaba yake ba. Amma duk rashin kyanki idan dai kina da ɗa’a da biyayya haƙuri tsafta iya girki kauda kai akan duk girman abu bawai dan ba’a ɓata miki ba , a , a haƙuri dai kikayi kika bashi baya tou kinyi a haka idan kika haɗa da iya gyara tsakiyar filin wasa. Misali duk kyau ko haɗuwar abinci. Yaji manya tsokokin nama yasha mai idan dai babu kayan masarufi da aka sarrafashi dasu duk wannan manya namomin idan kaci sai ka tofar saboda ba’a ƙawatashi da abinda zaisa ya ciwu ba , wasu zasu nemi magi yaji da ɗan gishiri su gyarashi dan su samu damar ci a sauƙaƙe amma bazaiyi daɗi ba a hakan ma tunda ba’a dafo dasu a tare ba , ɗan ɗanon dai zai bada wani iri daban kawai dai babu daɗi , tou haka kyakkyawar mace take idan babu abinda na lissafa a sama ko an zauna da ita sai an tofar. Ku gyara domin zamani ya canja akala fa……
Daga Abuja Sharifa tayi sallama da Dikko ta juyo bayan ya ajiye mata manyan kuɗi a account ya kuma bata wasu a zahirance , danshi mutum ne mai bala’en san yaga kana girmamashi ka kuma yi mishi ladabi. Haka kuma Dikko yake san godiya idan yayi maka abu kuma wannan halin shine tuni yake ƙoƙarin ganin ya koyawa Sultana , tunda ko dukanta yayi zaice ta gode masa.
Tunda Sharifa ta dawo katsina taci gaba da halba hotunan da ta ɗauko ita da Dikko , da yake ta iya kwanciyar aska har Papi ta jawoshi jikinta yana kwakwarta. Dan da zata tafi shine Papi yaita kuka yana cewa Yaya mu tafi da ita , shine abun ya bawa Dikko mamaki tunda Papi yake bai taɓa kuka idan An mata bata nan ba , ko idan zata fita. Sai yaga zama ɗaya duk rashin yadda na Papi yana kuka dan Sharifa zata tafi. Wannan abu ya ɗaga hankalin Dikko anya An mata tasan abinda take ….?Tsakaninta da Papi duka ne idan kuma yayi mata magana sai tace ai shima haka yake dukanta kamar wata jaka saboda haka wurin ɗanshi zata rama duk dukan da yasan yayi mata a duniya.
Mai gilashi kuwa tana ganin status in Sharifa kuma tabi duk ta yaɗa a kafafen sada zumunta na nahiyar yanar gizo. Hankinta fa ya tashi , kuma tayi alƙawari da rayuwarta ko zata mutu yadda Sharifa ta lalata mata aurenta wallahi babu gudu ba ja da baya itama sai ta lalata nata da Dikko. Addu’arta ɗaya shine Sultana ta bata haɗin kai a dai² lokacin da Sultana ta ɗauki waya. Mai gilashi barka da dare. Yawwa matar D ‘ K ya gda ? Lafiya qalau ya Papi ? Wallahi baya nan yayi tafiya da Babanshi. Zuwa ina haka ? Kinga ni wallahi bansan ina suka tafi ba , kai ƙawata ƙaddarorinki har biyu basa nan kuma baki san ina ne suka je ba ? Ey bai faɗamin ba nima ban damu da sanin can inda zaije ba , kai Sultana ? Tou me yasa haka ? Ke kindai san halina sabgar gabata ma ta isheni…… Lallai sai wata “yar iskar banza da bata aurar miki miji ba tasan ina zaije. Gaskiya ke Sultana jakace , nice jaka Mai gilashi ? Cikin kwantar da murya Mai gilashi ta fashe da kuka tace Sultana kiyi haƙuri idan ranki ya ɓaci matsala ce na hango miki ina ta ƙoƙarin gyara miki amma kin gagara fahimta ta , wata maƙiyata mijinki zai aura , idan har kika kuskura ya aureta wallahi׳ ƙaryarki ta ƙare……..!!! Tana faɗin haka ta tsinke wayarta.
Mai gislashi na fita a wayar Sultana kiran Momy yana shigowa , irin zagin da take ma “ya “yanta irinshi tayi min , kuma tayi min rantsuwa da Allah idan har ban raba Dikko da Sharifa ba idan tazo gidan abin bazai min kyau ba , kuji wani irin ɗanyen hukunci. Momy wace Sharifa ce ? Kamar dai yadda Nabeela ta faɗamin haka Momy itama taimin bayani. Sannan ita ma ta kulle da cewa , idan har kika kuskura Dikko ya auro Sharifa wallahi׳ kashinki ya bushe , Dikko tsabar tantirin kwallon ɗan iska ne shi. Duk yadda baki zato ko tunani ya wuce. Idan kika bari ta shigo tou tabbas kece a waje………. Tana faɗin haka ta kashe wayarta. Abin duba anan shine , da Dikko manemin mata ne idan har Sharifa ta dafeshi sai ta Allah saboda sabon halin da nazo mishi dashi , kunga dai nice da kaina na ƙirƙiri matsala a gidana saboda ɗaukar shawara marar makama , idan kuma an samu namiji mai surutu daya je wurin mace zai kwace ɗimi kamar ya lashi wuta matarshi kaza². Tou macen bariki bata bashi haƙuri saidai tace rabu da banza taje can ta ƙunshe har yayi wari , duk lokacin da kaji kana buƙata kazo in baka. Kinga daga nan kin zama ruwan kwance , haka take faruwa ne yanzu. Kina zaune da mijinki lami lafiya hankalinku kwance baki nemi komai a wurinshi kin rasa ba , haka kawai sai kiga ya tsiro miki da wasu sabbin ɗabi’u yana cin ubanki babu gyara babu dalili. Duk yabi ya ƙuntata miki ki rasa abinda kikayi mishi ya fito da wasu manyan miyagun halaye wanda kuma ke ada sam baki sanshi dasu ba , hmmm bance mijinki ba kila ya samu wata mace can ta riƙe mishi wuya an barki da ciwon damuwa. Haka suke matan bariki su ba aure suke ba mazajen wawayen mata suke mayar wa jarinsu , sune zasuyi ta karta suna ƙwalƙwale musu aljihu. Su riƙesu da bariki suyi ta gabatar da wasan danbe kina gida kwance kamar asara kinci kinsha sai neman fitina da hana ma miji zaman lafiya , ɗari biyar tayi miki wahalar gani dubu ɗarin shi tana wurin mata. Wanda kuma ya faɗa miki gaskiya ya zama abokin gabarki rai ba haƙuri sai a tattara kaya ayi gaba…. Kudaiyi nazari sai ku gano inda damuwar take mune ko su ?……
Bayan Momy ta kashe waya taci gaba da faɗa , waime ma Sharifa take dashi baƙar banza , me Dikko ya gani a jikinta ? Ga matarshi kamar balarabiya ta fara haifo mishi kyakkyawan ɗa dan Papi yana da kyau sosai masha Allah , ita ko Momy tana ma mamakin yadda Dikko lokaci guda ya zama mara kunya , saboda a da ta mishi maganar Sharifa da farko kenan dai yace mata ta kwantar da hankali komai zaizo a sauƙaƙe , jiya kuma da zaiyi tafiya tai mishi maganar Sharifa ce mata yayi ci gaba ake san samu. Dogon nazari Momy tayi tou wane ci gaba zai sama wanda matarshi bata bashi ba ?Tayi maganar a bayyane tare da rufe idanuwanta tana wasa da wayarta a saman goshi.
Babban gidan daya sha ado da ciyayi , sai mamallakin gidan ya fara samun matsala. Misali , tsakar dare sai yaji ana dukanshi sai ya tashi dan ganin mai dukan nashi , amma saiya duba ya duba baiga kowa ba. Ya sake komawa ya kwanta a tsorace ya kasa bacci sai yaji haniniyar doki da ƙarar takonshi yana tun karo shi. A firgice sai ka tashi , kana tashi saika sake ganin ba kowa. Amma sai aka gaggaɓe maka da dariya , me zaka fahimta ? Da farko dai idan zamanka ne na farko a gidan zakace iska ne , idan kuma ka daɗe a gidan baka taɓa jin irin haka ba zakace jifa ce { asiri } daga nan sai ka samu ayi maka addu’a dan kawar da wannan matsalar. Amma sai abun yaci gaba maimakon a samu sauƙi sai damuwar taci uwar ta farko , bayan wani lokaci sai kaji ana cewa idan baka tashi ba a gidan nan zamu kashe ka , ko zamu nakasa ka , sai kaƙiji baka tashi ba. Bayan wani lokaci sai a nakasa maka ɗa ɗaya ko kai. daga haka kai mai gidan zaka fara nazarin canja muhalli ƙarshe kana iya samun ƙaramin gida wanda baikai ƙwatar wanda kake ciki ba. Ba shakka ci gaban da Dikko yake nema matsalar tana nan ta tare a wurin Sultana. Wata zuciyar tace a , a matsalar tana wurin Dikko , wani sashe na zuciyarta kuma yace wallahi Sultana ce mai matsalar amma abinda za’ayi ki fara zama da ita ki gano ina damuwar take , idan ta gyara zakiji zance aure ya mutu , idan kuma Dikko yayi aure tabbas matsalar tana nan wurinshi……
Duk da bazai yuwu mace ta hana mijinta aure ba idan Allah ya rubutu hakan. Wayonki ko dabararki hikima da iya tattalin miji duk kissarki duk kwarkwasarki duk feleƙenki da iya duniyancinki idan Allah ya rubutu da rabon wata a cikinshi sai tazo , idan kuma kika taso da hauka sai ajalin rabo yazo yayi gaba dake. Ita bawai ta hana Dikko yayi aure bane ba a , a iskancin ita Sharifa ya girmi tunanin duk inda mai tunani baya tunani , musulmin karuwanci takeyi gata da kisan mummuƙe kuma haka ta kware wurin iya kwanciyar kwantar ɓauna. Ba Sultana ba har ita idan har Dikko yayi gigin aurar Sharifa tou fa lallai itama kanta Dikko ba nata bane ba.
Wata irin dariya suka gaggaɓe da ita gaba ɗaya duk karuwar dake wurin , ƙarar kiɗa ta karaɗe kaf ilahirin girman gidan karuwan dake can wurin Sitirolin , sanye ta shigo cikin wata irin zureriyar hijabi tasha niƙaf da safa , tana shigowo aka canja sabuwar waƙa ta matan bariki , da rawa Sharifa ta shiga tana shiga tsakiyar wurin da ake gabatar da shagalin ta cire hijabinta daga ita sai fant da bra , *KWARATA* n ta kuwa sukace gasu nan , a tsakiyar fili suka fara ɓarin kuɗi….
Mai gilashi kuwa tana gama waya da Sultana ta fara kiran wani kwartonta , babu wani daɗewa da ɓata lokaci ya ɗauka , ba ko gaisuwa tace kana ta ina ne haka ? Ina gidan “yanci ya faɗa a taƙaice , na wace anguwa ? Ya faɗa mata ko wane yake , kaga Sharifa ne ? Bana tare da ita tana can babban gida. Lafiya ne dai a wurin ? Ey tanayin shagali ne , wanda zata aura yaje egypt daga can zai wuce yayi umara yana dawowa za’ayi musu baiko…. Waye zata aura ne ? D ‘ K mana. Shima ya zama ɗan hannu kenan ? A , a , to me yasa zai aureta ? Nima dai ban sani ba , shiru Mai gilashi tayi tana nazari bayan wani lokaci tace sai anjima ta kashe wayarta….
Bayan sati 3…
Haka dai rayuwar take ta doka ƙaraurawa tsakanin rayuwarmu gaba ɗayanmu. Kwaɗo , ni su Amisty , Mai gilashi , Sharifa , mardiyya , Yusra Yazeed Jiddah Aunty Suwaiba Momy Aunty Bilki & Dikko…..
Har yanzu Dikko bai nemeni ba nima na manta dashi , ina nan ina fama da girman kai , kuma kullum saina ganshi online. Bayamin magana nima bana mishi , dani dashi kowa yana huɗɗar gabanshi kawai , ko hotunan daya turomin nace masa basuyi kyau ba. Daya gani bai bani amsa ba ,
Dikko kuma bawai yayi fushi bane ba , a , a ya dai zubawa Sultana ido yaga iya gudun ruwanta da hankalinta. Shin zata nemeshi ko kuwa ? Shima kullum yana ganinta online , idan ya ganta saidai yayi murmushi yace An mata kina ɗauwaniyar da yarinta , wai ni ? Nine kike ma haka ko ? Hmmm ai ya miki kyau….
Kullum sai Momy ta kirani tace nayi waya da Dikko ? Sai ince mata nayi. Shine ya faɗa mata bana kiranshi koma dai miye nikam ban sani ba. Nabeela ma ta kirani tace matar Yaya kinyi waya dasu Papi ? Itama nace mata nayi Rabiya ma haka……
Gaba ɗayanmu zaune muke a palo. Duk mu 6 ɗin babu wanda yake magana , palon yayi shiru irin yadda yara kecewa mutuwa ta ratsa da ba’ayi shiru ba data ɗauka. Mai gilashi kuwa ta tsareni da kallon takaici nima na ƙura mata ido naƙi na daina kallonta. Kowa yana kallon kowa bayan ta faɗamin cewa ta gaji da rashin zuwata makaranta kullum² da banayi kuma bana ɗaukar wayarta sai naga dama to tashawo ta dubu tazo. Murmushin takaici tayi tare da kauda kanta gefe tana girgiza kanta cikin yanayin damuwa……..
Gabatar min da ƙawayenta tayi. Hadiza Fadeela Halimatu Zainab sai ita duk dani mun zama shidda kenan. Ƙawayena ne su dukansu kuma duk matan aurene. Wacce ta kira da Hadiza ta nunamin tana ci gaba da cewa kinga wannan ƙawata ce sosai Hadiza kenan , amma mu a cikin ƙawayenmu muna kiranta da ashana. Kallonta nayi sosai bayan wani lokaci nace ƙona gidan kowa na faɗa ina jinjina kaina.
Ita kuma mai gilashi taci gaba da cewa , su duk maƙota ne kansu a haɗe yake kowa bata ɓoye sirrin kowa. Nuna su tayi duka , tana nunasu tana tafiya da maganarta cewa kuma mu dukanmu a gidan wannan muke zaman majalisa ta nuna wacce ta nunamin a matsayin Halimatu. Idan kin yadda zaki shiga cikinmu kema kije majalisa ko azo gidanki ayi. Inji Hadiza kenan ta anshi maganar daga hannun Mai gilashi. Nace a , a , me yasa ne ? Saboda nan ɗin ba gidana bane ba. Tace ya raina ki kenan shi yasa kika ce haka ? Ummm gaskiya kam ko bai rainani ba ni har yanzu banfi ƙarfinshi ba saidai , zan bar gidanshi na faɗi barin gidan a zuciyata. Ita kuma Halimatu tace nikam nafi ƙarfin nawa domin ina amfani da kayan mata masu kyau shine yake bina bani nake binshi ba dan yana tsoron yayi min laifi dare yayi in juya mishi baya….
Wata irin haramtacciyar batsa Mai gilashi ta liliyo ta watso , gaba ɗayanmu dariya mukayi na tsere Mai gilashi da ido danni dai Allah ya sani ɗan tasha yana burgeni sosai. Har kowa ya gama dariya ni ban daina ba , wayata na ɗauka na rubuta batsar ina dariya. Ban gama dariya ba ta fara bada labari dan kawar da zance ni na shiga madakatarsu ita tafi so tayi zama daga ita sai Sultana dan ganin Dikko bai auri Sharifa ba…
Ita kuma idan ta faɗi zancen iskanci bata dariya sai ta ɗaure fuska taci gaba da bada wani labarin , kai da ake bawa labarin kaine abun zai daɗe yana zungurar zuciyarka kana dariya. Kuma ita bata munafurci akan iskancin da takeyi duk namijin data nema sai ta faɗa. Ci gaba tayi da cewa , wata rana naje asibiti banda lafiya dani da Hadiza mukaje , ta nunata , murmushi Hadizar tayi tana kallon Mai gilashi. Ita kuma bata kalli Hadiza ba taci gaba da cewa , ciwo ya isheni kamar zan mutu , sannan ban daɗe da aure ba. Kuma ban fara tararayya da Alhajin da muke gidanshi ba. Nadai ɗana masa tarko yana ta wani zuƙewa , ni kuma jin labarin zamu zauna a BQ in gidan wani attajiri yasa nasha uban gyara , ashe abun ba sauƙi ne dashi ba , wasu mazan tayi ɗaya kake musu su amsa wasu kuma sai ankai ruwa rana sai ka nuno musu maitarka fili , jin zanzo zama a BQ n gidan kuɗi yasa na ɗirki kayan mata kamar ba gobe. Mara ciwo ciki ciwo kamar zan mutu , shi kuma ango ya saki baki yana jiran a kawomishi Sa’aden banza yashani basilla. Auren da akayi da ganganɗe² sai kawai inzo in zauna ya sussukeni kamar ƙasar kasuwa yaita bi yana wuce babu wani gata. To banzo gidan ba saida naje aka sakamin allurar tazarar iyali na shekara biyar implant , abinda yasa nayi har na shekaru biyar shine.
Na farko dai zan fita daga gidan wanda nake aure a yanzu zanje in samu matashi mai ƙarfi da wadatacciyar lafiyar gabatar min da wasan danbe ko ba abinci dan ina tara manyan kuɗi a asusun banki na , saboda idan nayi sabon aure ba maganar zina zan tuba ga Allah ne na nemi lahirar da gaske tunda dai mun samu mun ajiye tarihi a katsinar…. Duk gidan karuwan dake garin nan idan kikaje hotuna ne na farko a jikin album insu saboda nice karuwar data fara lalata namijin da bai taɓa karuwanci ba. Nice karuwar dana fara karuwanci da “yan samarin yara wanda suke makarantar gaba da primary , wato secondery sch. Makarantar masu kuɗi nake bi ina zaliƙo “ya “yan wanda Babansu yafi kuɗi , nice nake ɓatasu in kuma sa suyomin satar kuɗi a gidajen iyayensu su kawomin ni kuma na ɗorasu a network sune sukaji yadda abun yake sai suke farautomin abokansu ina basu suna bani kuɗi. Tarihi ya nuna ni nice karuwar danayi iskanci da wani tsohon malami wanda yake wa’anzatarwa da tunatar da karuwai muji tsoron Allah mu daina zina , to nice naje na rufe bakin wa’azi dan shima malam ya zama kwarto , nice karuwa ta farko da tayi ma namiji fyaɗe kuma Baban ƙawata ne har a cikin ƙuryar ɗakinshi kuma a cikin gidanshi.
Nice karuwar dai da karuwancin yasa na fita ƙasashen ƙetare , { wai kunsan ina take nufi ? Wasu states in fa take magana } na kafa manyan tarihi sosai nice karuwar da ƙasa ya kamata tayi alfahari dani amma har yanzu gwamnati bata nemeni ba duk yadda na jajirce wurin yima jahata hidima. Na bautata ma jahar katsina sosai wurin ganin na ciwo mata babbar lamba a cikin sahun manya karuwai duk a cikin shekaru 2 nayi wannan ɓarnar ina da shekaru 28 a duniya. Amma har yanzu ba’a haskoni a cikin talabijin ba , saidai dana kamo tasha dan ganin ko za’a hasko ni sai inga ana cewa wannan ce taje gasar karatu a wata ƙasa , sune sukaje fareti gaban gwamna , manyan “yan kwallo sune suka ceci wane daga kaza , an kamo manyan ɓarayin da sukayi sata a wuri kaza suka samu damar nasarar guduwa tou an kamosu , ko sune sukaje wurin musabaƙa , ɗan sanda kaza ya kamo “yan ƙwaya da dai² sauransu wannan itace ta zama kaza² amma an kifewa karuwai ciki duk babu su a cikin tv. Haba ai nayi ƙoƙari sosai shi yasa ko kinje gidan karuwan dake garin nan sai an baki hotuna na kin gani tare da bada ɗan taƙaitaccen tarihin rayuwata cewa kiyi koyi dani. Tarihi kuma dai har yanzu ya sake nunawa nice karuwa ta farko da nayi aure na koma makarantar boko. Kuma nice karuwan dana faɗi bayan na haɗu da abin harin nawa { haɗuwarta da Dikko kenan } , zan tuba amma sai nan bayan shekaru biyar. Idan kika mutu kafin lokacin fa ? Na tambayeta , kallabin kanta ta cire tana duƙomin da kanta daya yasha kitso da ƙarin gashin doki , furfura nawa kika gani a kaina ne ? Ba ko ɗaya na bata amsa , rufe kan tayi tana cewa sam mutuwa bama zata fara zuwa wurina ba a yanzu. Ke kina da matsala ana maganar arziƙi kizo ma mutane da wata maganar da bata dace ba. Ta ƙarasa maganar tana tsoki tare da gyara zaman gilashin dake manne a saman fuskarta cewa tunda ma kika kira mutuwa na fasa baki labarin. A haka dai ta tsaya bataci gaba ba ta tattara zugar ƙawayenta suka tafi tana cemin inyi ƙoƙari inzo makaranta…
Duk mutanen dake cikin gidan sun kasa bacci a daren nan saboda wani irin kuka da Hafsa takeyi mai tada hankali. Sai burgima takeyi tana riƙe hannunta dake zubar da wani irin ruwa marasa kyan gani , da anzo warware hannun sai tace karku buɗemin hannu ku tafi ku barni , fita kowa yayi daga ɗakin aka barta ita da Amisty , tagumi Amisty tayi tana tunanin yadda sukayi da malamin. Tayi masa bayani kaf akan labarin rayuwar Hafsa da kuma yadda take san Dikko kamar ta kashe kanta , tace zata rako Hafsa idan tazo karya nuna yasanta suna zuwa yaja zare ya karanto mata komai kuma yace zai iya aikin yasa kuɗi masu yawa , ita zata ma Hafsa wayau ta saido gidajen Dady a kawo kuɗin sai ita da Malam su raba kuɗin , ya yadda ? Yace ya yadda da hakan…..
Cike da yaudara Amisty ta fashe da kuka ta rumgume Hafsa sukaci gaba da kuka tare , saida suka sha kuka har suka gode Allah sannan Amisty tayi ma Hafsa labarin ta gano inda malamin Sultana yake ta kuma ƙara da cewa shine yayi ma Sultana aiki ta auri Dikko dan haka zasuje wurinshi idan Allah ya kaimu , Hafsa taji daɗi kuma tayi na’am da haka ta ƙara riƙe Amisty sosai a jikinta tana godiya.
Ya Yazeed idan baraka damu ba ina so muyi auren sati ɗaya , sarai fa ya gane amma sai yace ya auren sati ɗaya yake ne ? Zaka aureni ne bayan sati ɗaya saika sakeni ina so zan koma ɗakina ne , kallon rainin wayau Yazeed yayi mata cewa gaskiya banayi , dan Allah Ya Yazeed , cike da duniyanci yace tou faɗi farashi ɗaya mai tsoka naji , wane irin farashi ne ? Jiddah ta tambaya , Yazeed yace kije ki fara tambayo yadda abun yake , yana faɗin haka ya wuce wurin motarshi ya shige yaja ya kama gabanshi cikin farin ciki. A ranshi kuma yanajin yakai wani babban ƙwaro shi zai auri matar da D ‘ K ya saki , farashin da yake magana kuma shine ita Jiddah nawa zata biya shi ya aureta , idan kuma ya aureta zataci ubanta sauran ƙudirin nashi kuma shine da zuciyarshi yabar ma ranshi……
*JAMILA MUSA…*
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN…*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa…
*JAMILA MUSA…*
*SAI NA AURI D ‘ K*
🅿 —— 4
Saida Yazeed ya ɓace ɓat Jiddah ta kalli agogo. 10:29pm , tou ? Wannan wane irin farashi ne haka ? Kuma farashin wai mai tsoka….! Haka kidahumar ta gaji da tunani amma tsabar doɗewar basira ta gagara gane irin farashin da Yazeed yake nufi. Haka ta haƙura itama ta koma motar ta taja ta nufi gidansu Dikko da ɓacewar tunani…
Zaune suke a gaban bokan Al ‘ Ameen. Saida bokan yasha kuka sosai dan rashin Al ‘ Ameen a cikin wannan duniya. Yana faɗin Allah ne kaɗai yasan tsakaninshi da Al ‘ Ameen da irin girman amanar dake tsakaninsu , bayan yayi shiru ne ya warware wani bakin ƙyalle yayi tsafe²nshi ya wurgashi sama , cikin ƙanƙanin lokaci ya dawo ƙasa fari fat dashi. Ɗauka yayi ya miƙawa Mardiya yace taje ta cire kayanta ayi mata wankan gawa , idan ta gama ta fito ga mankara can ya nuna mata yana ci gaba da cewa a cikinta zaki shiga a sallaceki bayan an gama za’a kaiki maƙabarta ki kwana. Zaki dawo nan wurina alfijir yana ketowa , idan kika yi wannan idan har Dikko bai aureki ba , ni ba ɗan sunna bane ba….
A gigice Mardiyya ta kalli Aunty Suwaiba cikin kuka tace tsoro nakeji Aunty , Aunty Suwaiba tace duka² miye wani abun tsoro a wurin ? Da Allah malama tashi , Mardiyya tace ita dai tsoro takeji , boka yace ai magana ya ƙare wannan shine abinda rauhanai suka aiko dashi , ko taje gida ta kwanta zata tashi ta ganta a maƙabarta ne. Kuma wallahi iskokai zasu shanye mata jini ta mutu , wankan da sallah shine zaisa basa iya mata komai , shawara ya rage nata. Ihu Mardiyya tai tayi , ta bani ta lalace , amma Aunty Suwaiba ta riƙa ƙarfafa mata guiwarta dan na yau kaɗai ? Tou meye a ciki ? Taje tayi kawai.
Aunty Suwaiba itace ta raka Mardiyya inda boka ya nuna musu wurin wankan gawa , gurguwar banza itace ta zauna kamar gunkin baƙin kafurawa , Mardiyya ta kwanta irin yadda matacci sukeyi akayi mata wanka , bayan an gama aka saka likafani , sallah a makara tafiya zuwa kaita maƙabarta….
Tunda Mai gilashi tabar gidan Sultana bata koma gidanta ba har 11 ta dare tana ta yawo a gari tana neman Sharifa amma bata ganta ba. Ganin bata samu ganinta ba yasa ta tafi anguwarsu , tayi bincikenta kamar haka…. Sharifa tana bin malamai ne ? A , a , amma mahaifiyarta muguwar mai neman asiri ce kamar rainon maguzawa. Ƙarfe nawa take komawa gida ? Aka faɗa mata , Dikko yana zuwa gidansu ? Baya zuwa ! Ya yanayin ibadarta ? Bata damu da sallah ba gaskiya danko azumin ramadan batayi , idan an mata magana sai tace tana ulcer , mutanen da mahaifiyar Sharifa ke mu’amula dasu a cikin anguwa ta nema tayi musu wasu “yan tambayoyi , tana gamawa ta wuce babban gida , a wurin ne takejin wai ta tafi kano wurin taro Dikko.
Idan hankalin Mai gilashi yayi dubu ya tashi ɗaya bayan ɗaya. Kiran wayar Sultana ta farayi amma ba’a ɗauka , ta kira so adadin da ita bata iya ganewa amma sam Sultana bataji ba dan wayar baya tare da ita. Kai tsaye gidan Sultana ta dawo , amma fur aka hanata shiga , number Sultana ta nuna da duk wani abu da zaisa a yadda tasanta , amma aka hanata shiga idan dai Sultana ta ɗauka waya zata sanar dasu ne su kuma sai su yadda taje , tou bata ɗauka ba. Har 11:38am Mai gilashi bata tafi ba , Sultana bata ɗauka waya ba kuma bata kira ba haka basu barta ta shiga ba. 11:40am ta daki get in gidan cikin tsananin ɓacin rai da takaici tabar ƙofar gidan….
Saida tayi tazara mai nisa ta fara kiran wayar Sharifa , ita kuma saida ta mula tasha iska ta ɗauka cikin yauƙi da rainin wayau tana wani cakal² da cingom irin na riƙaƙƙin “yan bariki , hmmm Mai gilashi tayi tare da cewa suna na Sa’adatu Mai gilashi…… Saida Sharifa ta sake cakal׳ tace ai na sani. Kina ina ne haka ? Mai gilashi ta tambayeta. Kin aikeni ne ? Murmushi Mai gilashi tayi tare da cewa , dani dake babu wanda ya aiki kowa ko yasa nake tambaya , inda kike kawai nake so ki faɗamin….. Zaki zo ne ? Dariya mai Mai gilashi tayi cewa ai hannun haggu ba baƙon inda kike amfani dashi bane ba. Yanzu dai ba wannan ba , naji ance zakiyi aure ?
Cike da ƙwarin guiwa tace eh , waye zaki aura ne ? D ‘ K , ba naki bane ba. Sharifa tace nawa ne , Mai gilashi tace ƙarya kike ba naki bane ba… Sharifa tace wallahi saina auri D ‘ K , kamar ya kikejin shi ne ? Shine duniyata , zaki iya faɗamin ko adadin mutane nawa suka bar duniya ne duk soyayyar da suke mata ne ? Suna santa kuma sunajin daɗin ta , amma dole sun tafi sun barta suna can ƙasa sun kwanta badan ransu yaso ba dalilin yasa kikaji nace ba naki bane ba yana da dubunki , amma kuma tunda kika kirashi da duniyarki tou ba naki bane ba. Me yasa kika ce haka ne ? Mai gilashi tace yawwa, bara na baki misali. Hafsa Jiddah Mardiyya Yusra ga kuma Sharifa matarshi na gida , ita ta gidan ƙaddara kawai bata a lissafi tunda an aureta. Nawa zai aura a cikinku nawa zai bari bai aura ba ? Su waye su ? Sanin su waye su da matsayinsu a wurinshi ansar tambayarki tana wurin D ‘ K ki tambayeshi abinda yace miki ki kirani ni zan buɗe miki yadda abun yake , tana faɗin haka ta tsinke wayarta…..
Mai gilashi da damuwa ta koma gida. Addu’arta ɗaya Allah yasa Sultana taje makaranta idan Allah ya kaimu gobe , yanzu dai tasan gidan Dikko bazai zuwu wurinta ba tunda ya dawo , itafa bawai tana gudun kar ayi ma Sultana abiyar zama bane ba , a , a , ita abinda Sharifa tayi mata kawai zata rama , kuma itama yadda ta sata ta kashe kuɗaɗenta wurin bin malamai dan ganin wancan daya fasa aurenta ta sameshi amma Sharifa tayi mata zagon ƙasa tou itama sai tayi gwale² da Sharifa da duk kuɗin data tara a bariki. Dariya tayi cikin farin ciki cewa an kunna. Yarinya da *MAI GILASHI* kike wasan , muje zuwa……….
Saida na farka kamar yadda na saba a ko wane dare. Bayan nayo alwallah na fito na ɗauki wayata , missed calls na gani babu iyaka. Sai text in Dikko daya cemin inzo ɗakinshi yana kirana… Cike da fushi na fita na nufi ɗakinshi , da sallama na shiga ! Palo na sameshi kwance saman kujera yana cht , gitsi² nace gani. Ba tare daya kalleni ba ko ya daina abinda yakeyi a waya yace zo nan , wurinshi naje na tsaya ina fushi. Ɗago idonshi yayi ya kalleni cikin sigar zaman lafiya yace bacci kikeyi ne ? Ey na faɗa ina turo baki a tsiwace , to ? Sai yanzu kika ga text ina ? Ey , yayi kyau kije kawai. Bazar² na juyo , bayanta yabi da kallo saida ta fita ya maida hankalinshi a wayarshi yaci gaba da abinda yakeyi…
Ina dawowa ɗaki na fara kiran wayar Mai gilashi , kuma a lokacin 2 saura. Bata ɗauka ba , saidai ta turomin text cewa tana ɗakin Alhaji waya bazai yiwu ba , amma in sani Dikko yana zuwa katsina , kuma yana tare da Sharifa , abinda take so ta sani shine. Bawai tana zargin shi bane ba , abu ɗaya take so inyi a daren nan in baibaita rayuwa kawai nayi mata ƙoƙari na kyautata a daren nan cht inshi da Sharifa takeso na cire kaf na turo mata dan Allah ! Kar in kirata kuma kar in maido mata reply kar ince a , a , tamin alƙawari zata bani labarin da bata faɗamin ba , idan ban turo ba kuma wallahi bazata faɗa ba. Kiyi ɗamara….. Ki tuɓe , kuma ki kife gidadanci , ai kin gane abinda nake nufi , kiyi tunani , ki tuna. Tuna׳… Ki tashi ƙura kuma kiyi ƙoƙori a yada dogon zango in jini…
Shiru nayi bayan na gama karatanta saƙon Mai gilashi , wato nine zata latsa ? Tou wai meye ma matsalar ta da Sharifa ? Bata zargin Dikko kamar ya kuma ? Shi Alhajin ina iyalin tashi take ne a wannan dogon daren ne ? Ita Sharifar kuma wai me yasa ne kowa yakejin tsoronta ? Nima lallai ina san sanin abinda kowa yake tsoron ma Dikko Sharifa , ina san gani kuma nima ina san sani. Ajiye wayar nayi tare da ɗaukar ɗamara kamar yadda Mai gilashi tace , cire hijabi na nayi na ƙara mammatsa turare naɗan kakkaɓe dai bayan na tabbatar nayi na nufi ɗakin Dikko…..
Da sallama na shiga , yana kwance a inda na barshi , amma yanzu ya juya baya yayi takurarriyar kwanciya mai nuni da gajiya. Itama sallamar a gajiye ya ansa ta. Saman hannun kujera na zauna tare da cewa sannu da zuwa. Ba tare da wani damuwa ko rashin jin daɗin da farko ban masa ba yace yawwa , shiru ya ziyarci palon har na tsawon mintuna 3. Nice na katse shirun da cewa ina Papi da Sharifa ? Shiru yayi baiyi magana ba , dakai nake. Juyo da kwanciyarshi yayi yana kallona amma baiyi magana ba , ɗan kauda kaina nayi gefe haka nan naji gabana yana faɗuwa. Ban sake magana ba na miƙe , riƙoni yayi tare da jawoni a hankali zuwa saman jikinshi yakai hannunshi yana shafo cikina.
Kwantar da kaina nayi haka ta tsaye ba ta gefen fuska ba ina kalloshi cikin damuwa. Murmushi yayi kaɗan ya tsareni da ido , gyara kwanciyar fuskar tawa nayi zuwa gefe fuskata na fara wasa da gemunshi. Zame hannuna yayi daga wurin , sake maidawa nayi ya sake zameshi duk munyi haka yakai sau biyar , zuciya nayi na tashi da niyar fita , karki fita zo kiji , shiru nayi fuuu na wuce , An mata dake nake fa kizo nace , haka nan naji zuciyata tanamin tuƙuiƙi. Da ɓacin rai naje ɗakina , ina zuwa toilet na wuce na wanke hannuna ina cewa kuma bazan sake taɓa gemunka ka ba har abadan duniya , dan kaga ina taɓawa shine zaka ciremin hannu tou bazan sake taɓa maka ba tunda baka so Dikko…
Cike da damuwa yabi bayan Sultana. Ita kuma a dai² lokacin data fito daga toilet. Rufe ɗakin yayi sannan ya matsa jikin bedsite ya ajiye tarkacen wayoyinshi bai mata magana ba ya wuce toilet shima. Gefen gado na zauna naci gaba da haɗe rai kamar an sace uwata , shima ranshi a haɗe ya fito kamar an kaiko mishi saƙon mutuwar uwa uba a lokaci ɗaya….
Bedsite in kusa dani ya zauna tare da bani umarnin ni in matso kusa dashi , ƙin matsawa nayi na ɗauki wayata ina latse². Ki matso nan nace kuma ki ajiye wannan wayar tun kafin raina ya ɓaci , basar dashi nayi naci gaba da latsan waya cikin taurin kai da ƙaddarawa ma bashi a wurin. Miƙewa yayi ya ɗauki wayoyinshi ya tunkari hanyar fita , me yaji me ya gani ? Oho ya dawo , saida ya zauna ya ajiye wayoyinshi ya ɗan riƙoni jikinshi da soyayya , hannuna ɗaya ya riƙe tare da ɗorawa a saman fuskarshi yana shafawa a hankali harya gangaro saman gemunshi yana shafawa kuma ya tsareni da ido da kallonshi mai burgewa yanayin wasa da iskar bakinshi cikin salo mai yanke damuwa.
A ɗan damuwance nace ai tunda baka so ina taɓa maka na daina , ina so yayi maganar yana rage girman idanuwanshi. Ai nayi fushi , na bari , ya faɗa yana min kallon rainin wayau. Ey dama dole zakace ka bari tunda ga Sultanar banza yanzu ne kasan amfani ta rashin kunya kawai. Da yanayin tsinkuwa ya kalleni yace wai me ke damun kanki ne ? Haba An mata ni banajin daɗin abinda kikemin haka ! Ey dama ai dole zakace bakajin daɗi tunda ka ɗaukeni Sultanar bayan fage.
Tou waye ta bayyanannen fage An mata ? Kasan inda ka barta , ya za’ayi in sani tou ? Jakar da ta rakaka tafiya , taje ta rakoka Katsina tunda baka san hanya ba , ni danma ka ɗaukeni bansan abinda nakeyi ba ai baka faɗamin zakayi tafiyar ba saidai na tashi na gani zaka tafi , ko inda zakaje baka faɗamin ba sai wasu “yan iska karuwan banza , kuma bana sanka dama jira nake ka dawo Allah bazan sake zama dakai ba na ƙarasa maganar ina fara kuka , cikin kuka naci gaba da cewa da wata “yar iskar karuwa mai turo maka hoton tsiranci tunda dai yanzu ka daina so na kawai ka sallameni nayi gaba abuna , dan dana fita daga nan wallahi wani babban Alhaji zai kwasheni ya tafi dani can ya gina min sabuwar rayuwa mai inganci. Wacce babu firgici ko tashin hankali a cikinta. Ni ɗawisuwa ce kuma ai kasan babu yadda za’ayi abar ɗawisu sake yana yawo. Martabashi ake , ɗawisu baka rayuwa gidan matsiyata sai gidan kuɗi. Idan ba gidan kuɗi ba sai gidan sarauta , da rubibi za’a kamani kuma duk sai masu kamanin sunsha wahala duk sai sun bugu da wahala sannan mai rabo zai sameni dakel , a dakel inma sai mai tsanantaccen rabo gidan kuɗi nawa ka leƙa amma babu ɗawisu ? Kuma kaji kunya an girma ba’a san an girma ba mai gemun yaudara. Taƙaitaccen murmushi yayi ba tare da yace wani abu ba ya tsare Sultana da ido.
Ci gaba nayi da feƙa rashin mutunci , Dikko ya tsareni da ido cike da mamaki shi al’ajabi ma ya hanashi yayi magana yadai bita da kallo , kuma gidanka banza kaje ka ajiye duk jakar macen da zaka ajiye ni bana zama da kishiya , ai da daka dawo sai kaje can inda kake zama sai 3 na dare ka dawo gidan , a gajiye ya jawoni jikinshi ya rufe idonuwanshi cikin ɓacin rai yace ƙaramar yarinya. Daga haka bai sake magana ba ya fitar dani daga jikinshi yanayin fushi. Nayi kwanciyata naci gaba da bacci….
Bayan Sultana tayi bacci Dikko ya tsareta ido yana sake² a zuciyarshi. A daren yau baiyi bacci ba , kuma ɓacin rai bai barshi yayi cht in dare ba , gyara mata kwanciya yayi tare da jan bargo dan lulluɓeta sai kuma ya tsaya yana kallon cikinta. Na tsawon wasu mintuna sannan ya tafi da bargon a hankali ya lulluɓeta cike da soyayyarta a zuciyarshi. Wayoyinshi ya ɗauka ya fita bayan ya kashe hasken ɗakin.
Ya so a daren nan yaɗan rage nauhi amma An mata ta ɓata mishi , a gaban idonshi take cewa wani babban Alhaji zai kwasheta ! Ashe idan ya mutu An mata mantawa datayi dashi ? Bara tayi mishi addu’a ba ? Papi da wani babyn zata zubar dasu taje tayi sabgar gabanta ? Tunani barkatai a ranshi. Ya saƙa ya warware baisan iyaka ba , ƙaramar yarinya ta zauna tai ta faɗo mishi maganganu na yarinta , mtsww wannan damuwa tasa kafin safiya ta waye Dikko ya kwanta rashin lafiya….. Fatarshi ya wuce kawai kar yaga wannan baƙar ranar wallahi…..
Ni bansan Dikko bashi da lafiya ba , gari yana wayewa na shirya nai tafiyata makaranta banje ta ɗakinshi ba. Papi kuma yana can wurin Momy dan Nabeela ta dawo da suka fara zuwa tacan shine ya liƙe wurinta……
A makaranta. Yau ajin ba daɗi dan Mai gilashi bata zo ba , dana kirata na tambayeta abinda yasa bata zo ba , cemin tayi ina cht in da tace na turo mata ne ? Sai anjima zan turo miki , tou ya akayi kikaje makaranta bayan kuma ance D ‘ K baida lafiya ? Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji , meya samu Dikko na tambayi kaina……? Meke damunshi har abun ya fita waje yabi duniya ni banda labari ? Tsinke kiran Mai gilashi nayi na fara kiran wayar Dikko , bai ɗauka ba , Ashiru na kira shima bai ɗauka ba , Umar na kira , tana shiga yana ɗauka , Umar kana ina ne ? Qerau , wai me yake faruwa a goruba ne ? Ba komai , kowa lafiyanshi qalau ? Lafiyan kowa qalau ya bani amsa… Kashe wayar nayi na sake kiran Mai gilashi. Tana shiga ta ɗauka , Mai gilashi waye yace miki Dikko bashi da lafiya ne…? Sharifa , ki duba a whatsapp na ajiye miki saƙo kiga cht inta da mijinki , gaskiya Sultana baki da wayo , duk kina ina wannan iskancin ke faruwa ne ? Waton shi mai wayau idan yayi magana sai ya goge maganarshi , na turo miki dai ki gani abinda na fahimta ni zanji da sauran aiki , saboda yaƙin yafi ƙarfinki nima nace na Dikko An mata , tana faɗin haka ta tsinke wayarta….
Haka nan naji gabana yana halbawa ɗil׳ sai tashin hankali da nakeji gaba ɗaya wani ruɗu yazo min na kasa zama. Wurin Farisa nabar jakata na nufi gida cikin tashin hankali , a ƙofar shiga palon ƙasa nayi parking kuma gidan yana nan cike da mutane maza da mata kamar yadda yake kasancewa a ko wane rana. Kowa yana hidimar gabanshi da gudu na shiga ciki kai tsaye ɗakin Dikko na wuce ko takalmi na ban cire ba danni bana shiga ɗakinshi da takalmi komai sabuwarsu dana shiga palo zan tuɓesu……
Zaune na sameshi gefen gado ya jingina bayanshi da kan gado ƙafafuwanshi miƙe ɗaya saman ɗaya ya rungume hannayenshi kanshi yana kallon ƙasa. A tsorace na isa wurin ina cewa Dikko me ya sameka ? Bai ɗago ba kuma baimin magana ba , kusa dashi na zauna na ɗago fuskarshi , kallona yayi. Kuka ? Na tambayeshi ? Gyara bakinshi yayi yana ci gaba da kallona , rumgemeshi nayi nima na fashe da kuka , cikin kuka nace me ya sameka kakeyin kuka ? Zuciyata , shine amsar daya bani , amma me yasa baka faɗamin baka da lafiya ? Na ƙarasa tambayar ina riƙe fuskarshi da duka hannayena biyu. Ba kinsan na kwana gidan ba ? Idan har ina da mutunci da daraja zaki tafi makaranta baki zo kika ce wannan banzan ka tashi lafiya ?
Kefa yarinya ce , ni kuma na tsufa inji ki fuskata ta fara squeezing. Kamar ƙaramin yaro yake cemin nima fa ɗan saurayi ne , duka²na a nawa nake hararata yayi cike da soyayya sannan yace , ni a haka nayi miki tsufa dai ko ? Idan dai ni tsoho ne kema tsohuwarce tunda daga ni harke kowa ɗanshi ɗaya da zaki wani kalli tsabar idona kicemin wani Alhaji zai kwasheki. An mata wannan mutunci ne ? Ke da , da ne lokacin ina Dikkona har kin isa ki faɗamin wannan iskanci ban kashe ki ba ? Kika mutu murus , babu wanda yaji ba kuma wanda yasan anyi saidai a nemeki a duniyar nan a rasaki. Ko yanzu ni ba iya dukanki ne banayi ba wallahi tausayinki nakeji saboda kina da ciki. Duk wannan iskarcin da kikeyi ba tsoro yasa na zuba miki ido ba , ko zan mutu idan bana tare dake ni banajin kaina ke nakeji. Duk a wahalce yake magana cikin shashsheka a sanyaye cikin laushin murya maisa natsuwa….
Ki kalleni tsaf daga samata har ƙasa na kinsan ni ba sakaran namiji bane ba , kuma kinma san na tsufar kikace kina so na ? Tou ni ba tsoho bane ba , duka² shekaruna nawa ma ? Tsoki yaja sosai , tare da nunani yana cewa a gabanki ma zan zauna ina kwancewa har nake da lokaci maida miki magana , tsohon ne yayi maganar yana min wasa da harshenshi cikin salo mai ɗaga hankali ya raka wasan da kallonshi maisa mutum yaji cikinshi na halbawa , a kasalace na matsa da fuskata kusa da nashi na ɗora bakina a bakinshi. Maida harshenshi yayi yana murmushin jin daɗi tare da lumshe idanuwanshi a hankali cike da shauƙi , yana nuna yanayin zaƙuwa kuma har yanzu idanuwanshi a rufe , baya nayo da fuskata ina kallon kyakkyawar fuskarshi , bai buɗe idonshi ba yana a rufe kenan yana jiran tsammani , jina shiru yasa ya laliboni tare da riƙo kaina da hannunshi jikinshi yana kyarma ya haɗe cikin soyayya , bayan wani lokaci ya cire “yar guntuwar hijabita ya kwantar dani gefenshi ya kwanto shima har yanzu idonshi a rufe cikin yanayin farin ciki. Battery low……
Mai gilashi kuwa saida ta gama tuɓe kaf sirrin Sharifa sannan take tambayarta shin ko Dikko yana da wani logo ne ? Sharifa tace bashi da. Shi miskili ne kuma yana da wahalar sabo baya maganar data wuce biyu , baya dariya kuma baya murmushi idan kuma surutunki yayi mishi yawa zai tsareki da ido ne. Kinga taya kuwa za’a iya gano logon shi ? Amma da me kike da ibar mishi fili ? { abinda takeyi tana ɗaukar hankalinshi kenan } Sharifa ta faɗa mata , Mai gilashi tace tou ko ya taɓa faɗa miki aibun matarshi ne ? Da dalilin yasa zai aureki ne ? Sharifa tace gaskiya a , a , yadai cemin shi yana san matarshi sosai kuma yana tausayinta bai haɗata da kowa ba kuma yarinya ce ni na girmeta. Duk kuma wanda ya taɓota tou ba itace ba shine aka taɓo. Idan An mata tayi kuka shine idan tayi farin ciki shine. Wanda yaso mata farin ciki shine yaso , kuma duk yadda yake san mutum idan ya aibata ko munana mata tabbas zaija layi tsakanin shi da koma waye , shine kaɗai ya isa ya ɓata mata kuma shine farin cikinta duk duniya bata san kowa ba saishi , haka bata gane kowa saishi. Shi kuma itace rayuwarshi , lumfashi , bugun zuciyarshi , itace komanshi dan haka in kiyaye. Kuma shi abinda yasa zai aureni shi bawai ra’ayin shi bace ni , ba irin tsarinshi bace ba. Umarnin Dad inshi ne , Mai gilashi tace tou me ya kawo akayi maganar ne ? Ko haka kawai ya faɗa ? Sharifa tace nice dai naɗanyi maganarta , duk dalilin maganar nan kuwa matar Babanshi ce tayi wani aiki akan shi bansan ko na miye ba shine tace idan naje wurinshi naɗan aibata ita matar tashi kome yace nazo na faɗa mata ta nan zasu gane idan nasara ta samu karɓuwa…… Bayan ta gama jin duk abinda take so taji. Ta turawa Sultana saƙo duk abinda takeyi ranar yau tayi ƙoƙari tazo gidanta , bayan ta ajiye mata adireshi gidan….
Hafsa da Amisty gurfane a gaban sabon malamin da ta samawa Hafsa kamar yadda ta faɗawa ita Hafsat in. Saida ya zana ƙasa ya goge , ya sake zanawa , ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama zane²n ƙasarshi sannan ya fara rattafo mata bayani kamar yana karantawa a rubuce. Ya kuma ɗora da cewa ta gode Allah da tazo wurinshi daga yau kuma damuwa ya ƙare. Aurenta da Dikko anyi an gama kuma a ƙarshen watan nan ne , yaci gaba da labarta mata rayuwarta ita kanta , Hafsa tayi na’am da wannan bayani sosai dan haka akayi ciniki bugun farko miliyan biyu ba tayi idan aka taya ko anyi aikin baya ci , za’a siya jajayen raƙuma da jajayen sanaye jajayen tumaki tattabaru jajaye da kaji suma ja kuma duk ko wane za’a siyo mata da mijinta guda biyu² , shanaye maza biyu mata biyu kenan huɗu² mace da namiji a cikin ko wace dabbar daya faɗo….
Zatayi magana Amisty ta rufe mata baki tana cewa malam yi haƙuri zamuyi magana , jibi idan Allah ya kaimu za’a kawo kuɗin , tana faɗin haka taja Hafsa suka tafi. Bayan sunje gida ne Hafsa take cewa ita ina zata wani samo 2million ne ? Tada ma sigari wuta Amisty tayi saida ta ibi hayaƙi tace riba zaki ci ne , duk gidan da kika ga anyi zazafen abinci tou karki bincika ma’ajiyar abinci dalilin haka da sanin gaskiyar sirrin yana wurin mutanen gidan. Ki zuba kuɗi gona yarinya ko kin samu albarkatun gona , wannan malami da kika gani malamin “yan siyasa ne shi yasa kikaji aikin nashi da kuɗi sosai , ga tsada fa amma akwai biyan buƙata , gwamna kanshi wurinshi yake zuwa shine ya ɗaurewa gwamna ƙugu ya koma mulki , ai ya miki sauƙi ma ne saboda ni. Ai da banje ba aikin nan kila sai ya kai miliyan huɗu , ba nace miki shine yayi ma Sultana aiki ba? Kinga tana can ta shige abunta. Hafsa tace miliyan biyu fa Kaka ? Amisty tace miliyan biyun , miliyan har kuɗi ce da zaki tsaya kina wani jinjinata ? Hafsa tace ai inda zan samosu shine damuwata….
Kashe sigari Amisty tayi sannan tace ke kuwa kike da miliyan biyu da wurin samunta. Idan baki dashi ai Babanki yana da. Kije kawai ki tattaro takaddar wani ƙaton gida ki siyar , idan aka ɗaura aure ƙarshen wata D ‘ K zai biya. Kinga basai mu siya ma Dady sabon gida ba a manyan anguwanni dake cikin garin nan ba ? Murmushi Amisty tayi tare da nuna Hafsa da ɗan yatsa manuni tana cewa anya ma mu D ‘ K zai barmu muje gidanshi……? Dariya Hafsa tayi cikin jin daɗi cewa sai kunje mana tunda yana aurena ai dole ma ne yaso duk abinda nake so. Amisty tace yawwa “yar gari yarinya ta gano hanya mai takaba ta buƙaci kwarto…
Hafsa kuwa dariya tayi tare da warware hannunta taci gaba da cokalar ciwon tsakiyar hannunta , ihu take dan azaba amma cikin yanayin kafurci take ƙara faɗaɗa wurin dan bata so ya warke tunda malaminta yace idan hannun ya warke bata babu auren Dikko har abadan duniya , shi yasa ta hanama hannun nan zaman lafiya kullum sai ta kwareshi , sai rami hannun yake yana tafi , wani irin wari yake mara daɗi har ya kusa ɓulewa ta baya , dan dai karya warke ta rasa Muhammadu Dikko. Ba magani kuma ba’a buɗeshi yana shan iska kullum sai caɓewa yakeyi abunda zot takaici……
Mardiya tsakiyar dare ta firgice. Bayan an kaita maƙabarta a daren , ganin gari yana tafiya , shiru yana ƙara dosowa. Maƙabarta tana daɗa ɗinkewa duhu yana ƙara bayyana ta gigice , hmmm hausawa dai sunce komin hasken farin wata dare abun tsoro ne , ga dare ga matacci kwance a cikin ƙasa , wadda su duniyar da komai sun tattara sun ajiye badan sunso ba suka tafi suka kwanta. Duk kashedin da Aunty Suwaiba tayi mata bataji ba , saida dare ya kusa rabawa biyu taji sukuwa saman bedinan dake zagaye da inda aka ajiye ta a cikin mankara kukan tsuntsaye da duk wasu ƙwarina dake cikin maƙabarta ya ƙara yawa kasancewar duniyar tayi shiru. Dan haka ta yada likafanin da aka lulloɓota dashi ta tsallake katanga ta ibi hanya tsirara , hauka sabon kamu……
Boka da Aunty Suwaiba basu san ba Mardiyya ba. Saida alfijir ya fito , bayan anyi da Mardiyya zata dawo alfijir yana ketowa , har 6 saura ba Mardiyya ba labarinta dan haka suka tunkari maƙabartar ba labarinta sadai mankarar da likafinin data yada ina ta tafi…………???
Kwance take cikin kujera , ba kwanciya irinta ta yadda ake kwanciya ba , zaune take tayi irin kwanciyar nan ta “yan gayu kujerar ta riƙeta dai² burgewa , wani fitsararren ɗinki ne jikinta , halittar jikinta tayo waje ta kashe ɗauri dai² da zamani , hoto tayi tare da turawa daga ƙasa ta ajiye mishi barka da dare… Tun kafin daren yayi har anyi an ajiye. Yusra… Bayan ta gama hotonta kuma ta fara tallar surar jikinta tana video , duk saida ta safke kayan jikinta tayi ma Dikko video ta nuna mishi muhimman wurare a jikinta tare da faɗa masa ta sadaukar mishi. Tana video tana faɗa mishi nashi ne fa duka ya gani ya daina kawaici , kuma me yasa baka kallona idan nazo wurinka ? Baka cewa nayi kyau ? Videon ma har yanzu baka cewa ka gode ? Ƙafarta ta ɗaga ta ɗora saman madubi tana ci gaba da ɗauka tanayi tana dai maganganu irin nasu na gogaggin karuwan da suka san hannunsu , saida ta gama tasharta da iskanci iri² ta yadda duk musulincin namiji da tsoron Allahn shi idan ya gani saiya ƙara kallo sannan ya fara istigifira ya goge , idan kuma sheɗan yayi galaba ya tafi ruwa , maida kayanta tayi sannan aka yi ma Dikko vye² aka wani ajiye mishi a whatsapp…..
Murmushi yayi a wahalce. Cikin jan hali da jarumta bawai dan yanajin daɗin yinshi ba , shi kaɗai yasan bala’en dake zungurar mishi zuciya , danben ma dakel ya maida naushi saboda baiyi shi cikin natsuwa ba , wallahi baida lafiya zuciyarshi tun jiya take zugewa. Dakel ya kalli Sultana dake kwance gefenshi tayi ruf da ciki tana kuka , a wahalce yace An mata ki rufamin asiri ki dawo nan ya nuna bayanshi yana cewa kuma ki gyara kwanciyarki. Bazan koma ba , da damuwa yace to² ba komai haka ma yayi , daga haka bai sake magana ba ya dafe ƙirjinshi yana yin bayyanan nen numfashi , jin bai sake magana ba kuma na gaji yasa na tashi na koma inda yace in koma in kwanta tun farko ina mita cewa kuma a saman cikin zan kwanta , shiru yayi yaƙi magana yana kallo bango da yanayin tunani. Jin zan mutu yasa na ɗauki wayata na nufi ɗakina…
Saida nayi wanka na gyara jikina sannan na ɗauki wayata na buɗe data nake duba saƙon da Mai gilashi tace ta ajiyemin , ganin cht in da yawa yasa na kasa binshi na tattara na ajiye , amma na duba saƙonta da tace ni duk yadda za’ayi inzo gidanta , kuma zanje , saida nayi azahar na shirya dan zuwa gidan Mai gilashi , komawa da nayi ɗakinshi ɗaukar makullin mota yasa yasan fita zanyi , duk da baida lafiya ya balbaleni da masifa waini wace irin mahaukaciya ce ? Baya faɗamin baida lafiya ba shine zan fita ? Tou inje in fitar idan na dawo zan samu ya mutu sai in zuba ruwa ƙasa insha. Wuri na samu na zauna ina kallon ƙasa , yaci gaba da cewa zaki ga kamar ina takura miki ne duk girman duniyar nan wanda kike ganin yafi ni ko yafini sanki yaudararki yakeyi , niɗin dai da kika raina nine zan faɗa miki ko zai miki zafi , ai baka san abinda zanyo ba. Koma me zakiyo bazaki fita ba , kuma na rantse da girman Allah idan dai kika fita yau wallahi idan kika dawo saina zaneki ki fitar wawiya dake. Ƙasa² nace dole kacemin wawiya tunda ka samu abinda kake so har ka samu bakin magana , tsaf ya jini yace kije duk inda kike so , in Allah ya yadda zan zuba miki ido kuma saina ƙara aure ke kije kiyi yawo tunda shi kike so , yadda kika san katsina ko ni kaina bansan garin nan ba , lungu da saƙo sai ance Dikko naga matarka kullum kina bisa titi ke da kikafi ƙarfin mijinki. Idan na ƙara auren ta zauna ta kula dani , ta dafamin abinci ta bani inci da soyayya bata bari yunwa ta kamata , abinci akan lokaci kalami masu daɗin sauraro bata barin kunne na yaji magana mara daɗi saboda soyayya bare taimin gori na kwanta da ita , kullum ma nema na zatayi ko bana so sai ta bani tana ƙaramin cikin san kasancewa da tsari. Taimin wanka ko ɗakina an gyaramin , idan banda lafiya ta riƙa bani magani insha tanamin sannu. Ta faɗa da launin so. Kije can kita haukarki ta kwaceni miki ni sai gani na yayi miki wahala. Ina can inda ake riritani kamar yaron goyo , da nace uhum za’ace ina ne ….? Ya faɗa a shagawaɓe yana wasa da idanuwanshi. Kallonshi nayi ina kuka , yace ey aure ba fashi tunda ke kinajin yarinya ce kije kita rashin wayonki , duk kyan ɗawisu idan baida ado ai komai kuɗi yai maka banza bara ka siya ba , magana ce ya faɗa mata a kaikaice ta zancen da tayi mishi a daren jiya…
A tsiwace nace zan gyara maka ɗakin , bana so zan gyara abuna. Yi haƙuri , ki naɗa gammo ki ɗauka keda za’ayi ma abiyar zama , ƙara kallonshi nayi yace daina kallona kar in cake miki ido ya ƙarasa maganar yana fiddo duk girman idanuwanshi , ƙara fashewa nayi kuka na tashi na fara gyara ɗakin ina kuka. Murmushi Dikko yayi tare da bin Sultana da kallo cike da tsantsar so , yanzu ya gano ciwonta , a ranshi yace kaji yarinya da baƙin ciki zata hanani zaman lafiya ta firgice ta tafi Mama tace ta gama aurena , da gaskiyarta fa , wallahi An mata babbar ƙaddara ce sai mai rabo zai sameta , tabbas idan ta tafin a tsautsayi labari zaisha ban² , ki rufemin baki bana san kuka kin sani ko ? Bazanyi shirun ba , tou kiyi zanzo in kamaki. Amma ai kasan mai ciki batayin aikin wahala kace inyi , ni nace kiyi aiki ne ? Amarya nace ko kece amarya ? Allah yana kallon ka na faɗa a dai² lokacin dana zo ina goge gado kuma har yanzu banyi shiru ba…
Da amaryar da zan auro ce idan tazo kusa dani sai ta sumbaceni a nan ya nuna yana min kallon ƙasan ido , cikin fushi na sumbaci inda ya nunamin , riƙeni yayi yana wannan kukan yaudarar nashi da bana so , a gajiye na kwanta saman jikinshi. Murmushi yayi sannan yayi magana da yaudararriyyar muryarshi ya faɗa a wahalce An mata daina kuka yayi maganar yana hawo dani saman gadon , kalli , kallonshi nayi ina fushi , kwantar da idonshi yayi yanamin kallon rainin wayau , yi haƙuri ya bada haƙurin yana rufeni a bargo….
Kwaɗo…
A gajiye ya shigo gidanshi ya ɗibo gajiyar makaranta , yunwace yake dan ya fita baiyi kalaci ba haka ko wanka baiyi ba , saboda da ya dawo masallaci tuni Hadiza tazo gidan har ta shiga toilet in tanayin wanka , haka nan ya fita waje ya ɗan wanke jikinshi ya goge bakinshi da omon wanke baki ya fice daga gidan. Yanzu ya dawo palon kuma cike yake da mutane , hada Mai gilashi data gangaro kwaɗo itama dan rage rana take zaman jiran kiran Sultana amma shiru kakeji , ita kuma tana tsoro ta kirata ace Dikko yana nan… Mijin Halima yana shigowa Mai gilashi ta gaishe ta fice da damuwar rashin kiran wayar Sultana….
Gaishe shi kowa yayi tare da mishi sannu , ansawa yayi da yanayin anshi karka rasa ya wuce ciki. Shiru² Halimatu ta shigo amma taƙi ta shigo , ga yunwa yanaji kuma a matse yake yana san ya fita yaje toilet amma yana jin nauhin ratsasu suna zaune a palo ya shiga ya kuma ratsotso ya fito yanajin kunya gaskiya…
Matarshi ya fara kira a waya , amma sai bata ɗauka ba daga palon tace ya akayi ne kake kirana ? Bayan kasan ina gidan , baiyi magana ba ya tura mata text tazo yana kiranta , duk saida ta nunawa ƙawayenta wai kiranta yakeyi , shewa akayi gaba ɗaya aka dunƙule kawuna wuri ɗaya ana zance maganin data sha shine haɗarin , ashe ba dare kaɗai yake aiki ba harda rana , saida ta ballabaɗashi tayi bedroom..
Halimatu dan Allah kuɗan koma daga tsakar gida zan shiga toilet , cike da rashin kunya tace mu koma waje duk iska da ƙura ta barbaɗemu muyi datti ? Da yanayin san zaman lafiya yace duka mintuna nawa zanyi in fito in bar muku gidan , gaskiya bazamu fita kaje kayi abinda zakayi ai su basa kallonka , haba Halimatu sai in ratsa matan aure da gajeren wando in tafi toilet tsabar ɗan iska ne ni ? Tou meya damesu da kai ? Kaje kayi huɗɗoɗin ka , Halimatu wai me yasa haka ne ? Tou taramin mutane kai mai gida , dama tun jiya naga kakejin masifa , kace buhun shinkafa bai kai maka yadda kake so , maganar jiya ya wuce kiyi haƙuri…..
*Jinin Katsinawa ce….* 👇🏻
*JAMILA MUSA….*
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN…*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa…
*JAMILA MUSA…*
*SAI NA AURI D ‘ K*
🅿 —— 5
Ai ba maganar inyi haƙuri bane ba. Idan dai na fahimce ka kawai dai kana mana kora da hali ne. Ah² yi haƙuri ba haka nake nufi ba , yayi maganar yana nunawa da hannunshi da yanayin ladabi. Inda ya ajiye rigarshi daya cire ya matsa ya ɗauka yana cewa ai duk abun bai kai haka ba , nayi wankan ma da daddare idan sun tafi , da ka rufawa kanka asiri. Ɗan shafa gefen fuskarta yayi yana murmushi tare da cewa idan akwai sauran abincin ki bani sai in tafi can shagon Salihu inci….
A tsiwace tace na ajiye maka sai naga bai ishemu ba. Kawai dai mun cinye nasan ka siya can waje idan ka fita. Da kinɗan silalamin ko taliya tunda akwai miya wallahi yunwa nakeji sosai , abincin sayen nan ina ci zuciyata tanamin ba daɗi , tsoki tayi ta fice tana gunguni har palo ba tare data bashi amsa ba. Tana isa wurinsu Hadiza taci gaba da cewa wallahi babu wanda zaisani tsira wata girki yanzu danni ba jakace ba , gidajen abinci nawa a garin nan ? Dan dai kawai kar ya fita ya isa. A shi a dole sai yazo gida yaci shi mai mata….!
Hadiza tace ya akayi ne ? Shi mana , shi waye ? Abdul mana , meya faru ? A dai² lokacin daya fito dan fita ita kuma tana cewa wai in dafa mishi abinci. Ko tausayi na ba’ayi a gidan nan , tun safe nake hidima da mutane a ya kamata na riƙa hutawa. Cike da ladabin ɗan ƙunama Hadiza tace haba dan ɗan wannan ? Ai komu kika ce a cikin mu wani yayi zamuyi , ba komai ki huta bara a dafa maka tayi maganar tana miƙewa , Halimatu tace ai da kin barshi tunda fita zaiyi ai yace zai siya a waje. Hadiza tace ah yi haƙuri Oga a girka babu jimawa , tayi maganar tana shiga kicin… Salam² ya koma bedroom.
Ita kuma Halimatu ta zauna a palo cikin ƙawayenta akaci gaba da maida yadda akai ana shewa…. {{ Kina aikin me “yar uwata…? Ƙawar banza ƙawar wofi…? Wace ce ita ? Me kike nema a wurinta da har zaki fi²ta ta akan miji ? Wacce yau tana iya canja ki , shifa miji ? Ko kun rabu idan da zuri’a an zama “yan uwa. Hmmm ki kiyayi kanki da duniya kinji ko….??? Murmushi , kuma bawai nace kici ƙaniyar ƙawarki ba , a , a adai riƙa abun da lissafi… Karki canja ma ƙawarki fuska tace ƙawata lafiya ? Kice Jamila Musa tace a sakeku a riƙe miji , ba haka nake nufi ba , kudai fahimci inda na dosa. }} cikin ƙan²nin lokaci ta gama dafo abincin ta kawo mata , da farko tace Hadizar ta miƙa mishi , Zainab tace a , a ki kai mishi mana… Wai ita a dole nan tayi fushi wai wallahi bara takai mishi ba tunda jiya yace ana cinye abinci da wuri , {{ ba dole yayi miki faɗa ba ? Kin san wahalar daya sha ya samo ? Wace ce ke da baraya yi miki magana ba ? Ke kaɗai ya ɗauki alƙawari zai ciyar , yasharwa , tufatarwa , ilimantar magani idan baki lafiya wurin zama da kuma kyautatawa a gaban magabatanki haka ya ɗauko alƙawari , baice dake da ƙawayenki ba , ke kaɗai ya biya sadaki aka bashi kuma yayi alƙawari ya ɗauko ki. Duk abinda yayi ko ya bari kikayi da dukiyarshi ko abincinshi da komai nashi tou wannan shine kyautatarwa. Idan kuma bai fita haƙƙin naki ba zai haɗu da sakayya. Akan me zaisa ya samo abunshi ki wulaƙanta mishi ne ? Ko kece kike nemo mishi kuɗin ? Ba kuma nace ki riƙa yiwa mutane rowa ba , idan kinji maƙota ki noƙe risho. Ba rowa zakiyi ba , abinda ka bada shine naka. Kar kuma kina cin abinci idan wasu suna zuwa ki ɓoye kiƙi basu. Ko ki daina fita haƙƙin masu haƙƙin ku basu ba , kar abun duniya ya rufe miki ido. Ki bada , wanda kika bashi zaiji daɗi. Kuma zaiyi godiya da addu’a wa mijinki Allah ya ƙara buɗi da rufin asiri. Bana nufin kiyi rowa wa mutane a , a , ba haka ba , ina nufi dai abun komai kiyi shi dakai… Bawai duka “yan anguwar ku zaki ciyar ba , sai ki duba dai² ƙarfin mijin naki , wani yana da ikon ciyar da jaha ɗaya ma , amma mugun marowaci ne , tou karki almubazzarar masa amma a hankali ki riƙa nuna masa matsayin kyauta da kuma kyautata ma wanda baya da ƙarfi sai kiga a hankali yau da gobe ya rage , wani kuma yana san ya ciyar amma baida ƙarfi , kawai dai duk abinda za’ayi a riƙa sa nazari tunani da kuma lissafi… }} shine take fushi dan yace abinci yana saurin ƙarewa. Shin tasan dalilinshi nayi magana ne ? Ga nauhi yayi mishi yawa , gidansu shine yake riƙe dashi , ga Allah suka dogara shine sukayi ma zuru , itama gidansu Halimar ana aika musu da kasafi duk watan duniya , tou ke zaki nuna masa yadda zai kyautata a rayuwa ? Wace ce ke ? Daga “yar karo baki kau ba fa….. Sai wani kumburin banza take tana cika fuska tunda taga gareta ya miƙa wuyanshi. Mai abun hana miji idan ya buƙata , waye yace miki hana miji haƙƙi shine zai siya miki mutunci ? Tou idan dai wannan shine mafita a gareki zero…….
Dakel Zainab tasa Halimatu takai ma mijinta abinci , tana zuwa ta dungura mishi tayo waje. Shi kuma yaso taɗan zauna yana ci ana ɗan tattaunawa irin nasu na ma’aurata , amma ita ba ruwanta tunda dai ta samu ya ɗaure mata ƙugu zataci tasha tayi gulma tou an biyata , sai idan an kawo kayan mata ta loda ta riƙa mishi ƙarya yana bata kuɗi , ita kuma taita loda ma cikinta kamar akuyar mahaukaciya…..
Yau babu abinda na girka dan tunda na kwanta bacci sai bayan la’asar na farka , bai kuma wani tasheni ba saida na gaji na tashi dan kaina. Babu inda ya fita yaje saboda bayajin daɗi kuma ma ai dama shi ba ma’abocin fitar rana ba ne. Ganin na kasa tashi ne yasa aka kawo mishi abinci daga gidansu , na nashin dandai ina da cikin amman da ko ba abinda zanyi mishi saiya tasheni dan dai ya ɓatamin rai. Ba abinda naci tun kalacin safe sai bayan sallah isha’e na jiƙa garin rogo { garin kwaki } kuma Dikkon nasa da kanshi a siyomin , dan bana ra’ayin abincin da aka kawo. Shine yasa aka kawo buhu ɗaya. Bayan yayi faɗa wai salan inje inba babynshi wahala zanci wani gari bana daijin magana , nace baby ne zaici garin ai bani ba , wai babu wani ya faɗa yana hararata nace da gaske shine yasa aka kawo.
Bedroom na sameshi zaune saman gado da irin zaman ɗazu yana kallon ƙwallo. Kusa dashi na zauna , ina zama ya gyara min zamana tare da matsowa ya kwanta ya ɗora kanshi a jikina ya riƙe ƙuguna da duka hannayenshi yana kallona , nima kallonshi nayi tare da cewa tashi muci , ɗauke idonshi yayi daga kallona yana kallon tv yace me ye ? Gari , murmushi yayi me sauti yana cewa Allah ya sawaƙe , garin ne Allah ya sawaƙe ? Ah ni bana iya cin garin gaskiya sai kace inyamuri….? Aini inyamurar ce shi yasa zanci , shiru yayi bai sake magana ba , ya ɗauki wayarshi yana duba dokuna…. Shikenan tunda bara kaci ba bari in tafi nayi maganar ina ƙoƙarin tashi , riƙeni yayi sosai yaci gaba da abinda yakeyi a waya….
Ni tafiya zanyi , ba tare daya kalleni ba yace kinyi fushi ? Ey , tou ina ci kawo min cokali , ai bada cokali akeci ba , da me akeci ne ? Da hannu , tou bani ya ƙarasa maganar yana buɗe bakinshi ba tare daya kalleni ba… Ai haka kayimin haggunce , ya zanyi ? Ka tashi…. Tashi yayi zaune amma har yanzu hankalinshi yana kan wayarshi saidai bakinshi a buɗe yake , bashi nayi , riƙeshi yayi a bakinshi tare da ɓata fuska ya taɓe baki yana juyashi , ƙara ibowa nayi. Da garin a bakinshi yayi magana cewa dan Allah An mata ki kyaleni kinga banda lafiya….. Dan Allah kaci , kallona yayi a sakace yace baya tafiya , jeka dashi kawai ka kora da ruwa….. Idan banci ba zakiyi kuka ? Dariya nayi dan yadda yayi maganar kamar ƙaramin yaro wallahi. Shagwaɓa tana mishi bala’en kyau kuma yana burgewa idan yayi , hada hawaye. Na faɗa ina kallonshi da irin kallon da yakemin. Ɗan kauda kanshi yayi gefe tare da shafa kanshi yaci dakel , yace ngode. Hahahaha bawan Allah , yau da Jiddah tana nan da nace mata Dikkon ma da kowa da kowa yake taƙa dashi ni nasa ma yaci garin kwaki dan ubanta….
Aimu dama mun saba , kuma ni ban manta ba har yanzu nasan martabar gari , duk irin matsayin da nake a yanzu baisa na manta da rayuwar baya ba. Ai gari yayi mana kuma mu bama wulaƙanta shi duk matsayin da mukaje muna tare da gari gaskiya , kuma ina ƙara godiya da Allah yasa nake a wannan matsayin , haka nan naji ina sha’awar garin. Na ɗan haɗo rayuwar baya da yanzu ! Nayi tunanin nima bazan iya ci ba , ashe dai zan iya ? Allah ya ƙara yalwata arziƙin Dikko amin…. Da gefen ido yake kallona har na gama ci. Saida na gama ya kalleni ta gaba yace sannu , yawwa na faɗa tare da tashi dan fitar da filet in , idan kin jiye kizo , ni bazan dawo ba , ki dawo nace miki , ban sake magana ba na nayi gaba , tana fita ya tashi dakel yaje ya ɗauki cingom yabi bayanta…..
Ɗakina na sameshi kwance yana waya , ɓata rai nayi tare da samun can gefe na zauna na ɗauki wayata , text in Mai gilashi ne kaɗai , ban zo ba , me yasa ? Idan naga D ‘ K baya nan in kirata dan Allah , yau D ‘ K bai fito ba lafiya ? Ko har yanzu baida lafiya ne ? Inyi ƙoƙari in riƙeshi gida na kwana 3 kar in barshi ya fito in rufa mata asiri don girman Allah za tayi wani aiki , kuma inzo makaranta duk yadda za’ayi idan Allah ya kaimu inzo makaranta dan Allah…..
Taya zan riƙe Dikko a gida in hanashi fita ? Abinda ma baya yuwuwa ne gaskiya. Wane aiki ne zatayi ? Koma dai miye Dikko bai zama , yanzu ma jira yake dare yayi ya lallaɓa ya fece abunshi , zuciyata kuwa cewa tayi ai saidai ki jashi kuyi faɗa kawai tunda dai yace bazai dakeki ba tunda kina da ciki. Ci gaba nayi da cika fuska ina ɓata rai , bayan ya gama waya yace An matana miye ? Dikko wai mema yasa kaje kayi ma karuwa liƙi ? Da yanayin rashin jin daɗi yace ba karuwa bace ba , Mamanta fa ƙanwar Dady ne. Ni bana san sanin wani dangantaka ko alaƙa , amma me yasa baya bakimin magana ba sai yanzu ? A lokacin abun bai shafeni kamar yanzu ba , yanzu kinajin fitina kenan ko ? Ey fitinar nakeji , tou ai ba ƙyaleki zanyi ba , zaneki zanyi. Fashewa nayi da kuka sai abun yaci gaba da zungurar min zuciya kamar yanzu ne akeyin abun wani irin azababen kishi yaci gaba da ƙwal²rmin zuciya. Da videon da Yusra ta turo mishi gaba ɗaya na ƙwace na fara ɗuɗɗurma ma Sharifa da Yusra zagi , da sauri ya taso yazo kusa dani yace haba An mata meye haka ? Cikin kuka nace dama ai dole zakace zaka dakeni tunda na taɓo karuwowin ka , kiyi a hankali kinsan bamu kaɗai ba a gida , so kike ace kin rainani ne An mata ? Ace na rainanka kaima ai raini yasa kaje kayi mata liƙin a gabana , da Jiddah ce ka isa ? Saini duk wani shararka da komai akan An mata. Saina faɗar da ƙarfin dandai kar asirinka ya tonu asan kana da karuwowi , salati Dikko yayi tare da cewa idan dai kika kasheni hankalinki ya kwanta… Nine ma nake da karuwowin ko ? Ni An mata ? Ya ƙarasa maganar yana riƙoni jikinshi , fizgewa nayi na miƙe naci gaba da kuka ina zagin su Sharifa.
Riƙeni yayi da ƙarfi. Ya rumgumeni jikinshi , bayan wani lokaci ya sassauta riƙon zuwa riƙo da tako mai kyau ya fara maida lumfashi da salon da yasan zaisa na ɗauke wuta da wuri , ƙasa² na farayi da murya cikin shashshekar kuka ina cewa amma ai kasan baka kyauta ba , yi haƙuri yarinya na yake faɗa yana ƙara sautin. Kasala ta fara zuwa. Dakel na sake furta kuma na ɓata dakai , ai bamu ɓatawa An mata yayi maganar yana fara kukan kissarshi , wani ɗan iskan kuka yakeyi cikin kurman sauti maisai jiki ya mutu da sauri , sai ya riƙayin wani jaririyar ƙara “yar ƙararrama yana numfashi , shidai yasan yadda yake abunshi amma dole dai idan kikaji sautin sai tsikar jikinki ya tashi , kasala da san kasancewa dashi ya tattaru ya lulluɓeki a lokaci guda dan da shagawaɓe yake fitar da sautin sai kuma ya ƙadaddabe ki da raunanannen riƙo , hmmm Dikko ? Bayajin magana kona misali. Saida ya gama sinsineni ya fara lasar bakina , muƙus nayi shiru , a gajiye yaja ni ya ɗora saman tsakiyar gado dakel. Yana maida numfashin wahala da yanayin rashin lafiya cewa bakijin magana kuma tunda kika ɓatamin rai naushin mai ƙarfi zanyi , riƙeshi nayi ina kuka , kallona yayi a shagwaɓe yace me ye kuma ? Yayi tambayar yana ɗaure fuska , na bari , a , a ya faɗa badai bakijin magana ba ? Yi haƙuri. A wahalce ya gyara kwanciyarshi yana cewa tou zoki bani haƙuri ya ƙarasa maganar yana min dogon kallo ranshi a haɗe…….. Matsawa nayi kusa dashi nace yi haƙuri , kallona yakeyi har yanzu , bayan kamar mintuna biyu yayi murmushi tare da ɗan tattauna cingom da salon jan rai sannan ya huroshi irin abun nan kwai ya kuma riƙe kwan. Da kanshi ya nunamin in sauka muje , sauka nayi. Shima ya sauka ya biyo bayana har ɗakinshi , inda aka ajiye kayan da ya dawo dasu daga tafiya yace in buɗe inyi ta sakawa yana gani. Ya ƙarasa maganar yana kwanciya saman gado,
Wasu irin riguna ne masu kyau da tsada , bawai baƙaƙe bane ba dukansu kaloli ne masu kyau launin “yan gayu , takalma masu kyau haɗaɗi suma , sai sarƙa da “yan kunne “yan hannu da zobe kala biyar kuma duk na zinari ne masu masifar tsada. Manya² bawai “yan kucilaye ba kamar na wasan yara. Jakunkuna turaruka masu ƙamshin gaske da dai duk abinda yasan zai haɗani ya siyo , haka naita gwadawa ina saka takalmi ina bada step yana daga kwance yana kallona , idan bai burgeshi ba sai ya gyaramin , idan na burge shi da yawa yana daga inda yake zaice inzo , idan naje saiya sumbace ni yace An mata mai kyau. Ko kuma yace bara in miki hoto Yarinya….
Mai gilashi yau ta kasa fita zuwa wurin Alhaji. Sai zagaye takeyi tsakanin ɗakinta da ɗan madaidaicin tsakar filin BQ insu , meke faruwa ne ? Sultana ba reply kuma ba fita ba kira ? Kardai zuwa tayi taje ta nunawa Dikko cht in ? Kila ana can ma ana faɗa , ta shiga 3nta , ɗaki ta koma ta ɗauki wayarta ta fara kiran Sharifa…..
Babu wani daɗewa ta ɗauka , ko gaisuwa babu Mai gilashi tace alherin Allah dai ya kaimu wannan rana amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida , ni Mai gilashi ? Oh , naga Nana Ade a gidan amarya , ashe ina da rabon ganin wannan rana……….? Hmmmm , ׳ Sharifa tayi dariya cike da izza ita amaryar Dikko , Mai gilashi taci gaba da cewa ni ina nan na duƙa addu’a Allah dai yasa karya haɗaki da matarshi. A yatsine Sharifa tace ni wannan ai ban ɗauketa a mace ba. Kinsan da haɗemu zaiyi sai nayi wani nazari nace masa bana so kowa ya raba mata gidan ta , yanzu ke ina ne zai ajiyeki ? Cike da kwarin guiwa tace G R A , wannan gidan duk ke ɗaya Sharifa ? Cass ni ɗaya abuna daga ni sai bataliyata ga kuma Dikko nawa abuna , kai zanfa zuba tasha danni wannan banzar matar tashi banajinta wallahi. Dan bata da ban²nci ita da kashin da nayi a toilet ruwa kawai zan sheƙa tabi 5v abunta…. A hankali dai Mai gilashi taci gaba da zungurar mata ciki , daga ƙarshe tace ko tayi magana da Dikko ne ? Tace ai zasu haɗu 1:00am a G R A , Mai gilashi tace idan sauran kishiyoyin naki sun bar miki shi ya samu zuwa wurinki ko ? Sharifa tace waye su ? Bana ce komai ba , amma ni na faɗa miki yau gobe da kuma jibi Dikko ba naki bane ba , na waye……? Murmushi Mai gilashi tayi tare da cewa na wata gogaggar ce , tana can ta ɗaukeshi sai sun dawo………. Tana faɗin haka ta tsinke kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya….
Ya Yazeed ni wallahi na kasa gane wannan farashi da kake magana. Jiddah da Yazeed zaune a mota kuma a gidan Rabiya ake zancen , dan jiya da Dikko ya dawo daga tafiya da Papi ya maƙale yace shi zai zauna wurin Nabeela sai Momy tace ita Jiddah ta tafi can gidan Rabiya ta zauna , kora ce da hali akayi mata amma ta kasa ganewa jakar. Shiru Yazeed yayi yana kallon sitiyari , Jiddah tace Ya Yazeed kayi shiru baka ce komai ba…..!!!
Cike dajin haushi yace tunda bakya ganewa a daina maganar ko dole sai anyi auren ne wai…? Haƙuri ta bashi tare da cewa bara in kira Nabeela. Tayi maganar tana danna wayarta dan neman lambar Nabeela , anshe wayar Yazeed yayi daga hannunta yana cewa kema kanki zawara baki fahimta ba taya ita Nabeela zata sani ? Shiru tayi tana saurarenshi , Yazeed yace waye zai saci kayan wani tou inba ɓarawo ba ? Jiddah tace gaskiya , shi kuma yaci gaba da cewa ni sakarai sai in biya sadaki lefe wurin zama abincin da zakici har na tsawon sati biyu da kuɗin hidima sai su tashi a banza bayan kwana biyu in sakoki alhalin ban gama gurje kuɗin ba….? Tou ya akeyin abun ne ? Yadda akeyin abun tsarin da komai kawai ki bada miliyan 5 zanji da komai , Ya Yazeed yanzu banda kuɗi duka² fa a account ina baifi miliyan ɗaya ba ,
Kallon rainin wayau yayi mata yana cewa karki ɗauki Yazeed sakarai mana ? Wallahi kuwa Yaya ta faɗa kamar zatayi kuka , kina nufin duk zaman da kikayi da D ‘ K haka nan kika fito fayau ba wasu manyan kuɗi a account ? Yaranshi ma sunyi kuɗi bare kuma ke matarshi ? D ‘ K da macen zai bari kiyi talauci ? Nafa san D ‘ K fiye da yadda ke kika sanshi. Halinshi da komai na rayuwarshi ni ina iya rubuta littafi Jiddah , ai bana tunanin nan da shekaru biyar miliyan biyar za tayi miki wahala wurin bayar da ita a matsayin kyauta. Bare kuma wannan ba kyauta zaki bayar ba kece za’ayi ma hidimar dasu , ina gwala²i ? Ina kuɗi Jiddah……? Wallahi duk na siyar na ba malamai , sakaran kallo yayi mata , taci gaba da farfaɗo mishi irin manyan malaman data bi amma har yanzu shiru kuma kullum idan ma Ya D ‘ K ya ganta kamar zaici ƙaniyarta ne. Yazeed yace tunda kinbi malamai ba’a dace ba ki zubo hannun jari a asusun banki na , zaki sha mamaki , Yaya banda kuɗi wallahi , Yazeed yace idan ba kuɗi ba aure karta sake kiranshi idan bata samu ba , daga haka fira ya tsaya. Yazeed ya tafi ita kuma ta koma ciki da tashin hankali , ita dake so suyi aure ya sakota ta koma gidan Dikko ? Ya kuma Yazeed zai rusa mata bajet haka ? Dole ma a samu kuɗin a daren nan…
Tunda ta shiga take tunanin inda zata samu kuɗi. Ta juya ta zaga ta rasa yadda zatayi , tayi waya wa ƙawayenta ko zata samu duk kowa yace babu , Ashiru ta kira yace shi baima san yadda miliyan take ba bare kuma miliyan 5 , tambayarshi tayi idan ta tambayi Dikko zai bata ne ? Ashiru yace tou shidai bai sani ba amma ta jaraba kila ta dace tunda su ɗin “yan uwane. Bayan Ashiru ya gama waya da Jiddah ya kira Dikko yake faɗa mishi. Tun kafin Jiddah ta kira Dikko ya tura mata miliyan goma , shi a ganinshi idan ta nema bata samu ba zataje tayi iskanci ne , shi kuma dudduniya abinda ya tsana yaga mace tana barbaɗewa….. Shi kuma Ashiru wallahi da yasan Dikko zai bata kuɗin da bazai faɗa mishi ba , dan koshi yana iya bata kuɗin amma haushinta yakeji kamar ya babbakata da wuta tunda taba Papi fiyaya². Dan yasan bata iya tunkararshi da zancen ya bata wani abu saboda abinda tayi ma ɗanshi. Shi kuma Dikko ba haka yake ba , idan dai ta haɗoku zaiyi hayaniyar shi yayi bobbotanshi tare da rufe idanuwanshi ya zazzaga ma mutum rashin mutunci dai² iyawarshi , kuma wani dalilinshi bazai hana shi ya kyautata maka ba , haka ta faru dashi da Yazeed ai. Lokacin da yake tarayya da Sultana akace ya korashi daga company yace su ƙyaleshi , yanzun ma bashi ne ya koreshi ba. Ashiru ne kuma ya kawo Abbakar ya ɗora , da Dikkon yayi magana yace Mai gida haka za’ayi , kuma shikena ya wuce wurin……
Wani irin ihun farin ciki Jiddah ta kwarara , lokacin da taga kuɗin da ya shigo account inta kuma daga Dikko ne , tayi murna sosai ta fara kiran wayarshi , a kashe yake , ita kuma a tunaninta na neman biko ne , dan haka ta zauna ta tsara yaudararrin kalamai ta aika dasu ta whatsapp tasan komai dare zai hau kuma zai gani , kila yana jin kishi ne Yazeed zai aureta shi yasa ya fara neman shiri , ita kuma batayi tunanin Ashiru ya faɗa mishi ba a ganinta kai tsaye ya bata dan kyautatawa , ai tasan wannan sharar fage ne idan manyan suka taho account inta baya ɗauka. Kai Yaya D ‘ K mahaukaci ne , aiko bayan kwana biyu zatace ya bata 20 tasan zai bada 40 ne kaɗan ne daka aikinshi , kai ai dole ma ta koma a ci duniyar nan da ita , tayi murna har ta rasa irin wacce zatayi , gaskiya Dikko baisan darajar kuɗi ba haka nan yake nemansu mutane na cinyewa , a nata tunanin kenan………..
Bakajin komai sai ƙarar ragonshi dake fita { munshari kenan } kwar , kwar , kir² kwar² , da sanɗo ta shiga ɗakin bayan ta tabbatar da babu mai ganinta har jikin wadrof, a hankali ta buɗe wadrof ƙiyyyy , ƙarar buɗewa , a ɗan tsorace ta cije haƙoranta tare da yaƙewa cikin yanayin tsorata ta kallo inda Dady yake kwance yana jan rago. Maida hankalinta tayi wurin neman takaddun gidajenshi , saida ta sabko kayan tass sannan ta taka tayi sama bayan wani lokaci ta sauko da wani fayil , a ƙasa ta ajiye ta dudduba tsadajjin gidaje da Dady yake taƙama dasu a cikin anguwannin “yan gayu da akeji dasu ta ɗauko har 3 ta ajiye ƙasa sannan ta maida sauran ta mayar da kayan yadda suke , ta rufe weldrop in ta fice yana nan kwance kamar asarar safe yana bacci….
Itama a wurin Sultana haka ta kasance , tana kwance gefen mijinta kamar asarar itama shi kuma yana cht. Murmushi yayi kaɗan tare da juyawa ya ɗauko bluetooth wurin dawowa ne ya bugeta , da sauri ya ajiye wayarshi yana rirrigata irin yadda akeyi ma yaro idan ya farka , riƙeshi tayi taci gaba da bacci , ajiyar zuciya ya sauke. Cikin jin daɗi ya lumshe idanuwanshi a gajiye yana numfashi kaɗan. Saida ya tabbatar ta koma bacci ya cireta daga jikinshi ya gyara mata kwanciya ya lulluɓeta , a hankali ya sauka daga saman gadon ya ɗauki wayarshi ya koma palo….. { kunga bai iya gani ba , amma yau da gobe tasa zaije ya kalla , tou a hankali suke raka mana mazaje suna dawowa , idan abun ya ɗaure haka tun tana mishi tayin kanta yana a , a , a hankali zata labbaceshi ta nuna mishi ai ba wani abu bane ba. Da kaɗan take ɗorawa idan kuma tafiya tayi nisa haka zata rufta miki miji , daga nan sai ta Allah , karuwa ba…. }}
Kashe fitila yayi bayan ya shiga palo , ƙasa ya kwanta saman kafet ya sargafa bluetooth a kunnenshi sannan ya buɗe cht in da Yusra ta turo mishi. Hotunan ya fara kallo da yanayin mayata , bayan ya gani ya kunno voice note ya saurara a kasallance ya furta mata yana ci gaba da kallon hoton Yusra , a voice note kuwa lallausar magana ce da manyan kalaman irin na “yan tasha wanda yaji sunyi mishi dai² da sauron kunnuwanshi , daya kai ƙarshe sai ya sake kunnuwo , taɓe bakinshi yayi tare da fara kallon video , da sauri ya rufe idanuwanshi yana murmushi , amma yanajin maganar da takeyi lokacin tana video , buɗe idonshi yayi ya sake kallo yana murmushi , bayan wani lokaci ya sake rufewa yana dariya….. Gyara kwanciyarshi yayi yana miƙa alamun saƙo ya fara shiga jikinshi. Dariya ya sakeyi mara sauti sannan yagoge ya kifa kanshi saman pilown da yake kwance yanajin wani baƙon yanayi yana shigarshi. Bayan wani lokaci ya ɗago yaci gaba da dubawa bai bawa Yusra amsa ba , ya duba saƙon Sharifa itama baice mata umm² ba ya wuce wurin na Jiddah , kallon hotonta yayi data turo tayi kyau sosai wai ga Jiddah tana godiya Yaya , itama bai bata amsa ba , ya duba saƙon da wata number ke turo mishi hotuna , gani yayi ya wuce yana duba na abokanshi , zuciyarshi kuwa sai san ƙara jin labarin Yusra takeyi , komawa yayi ya gogeshi da hotunan yasan idan An mata ta gani kuka zatayi…. Ɗayar wayarshi ya ɗauka ya fara kallon hotunan da yayi mata ɗazu , da wanda itace tayi musu tare , bayan ya gama gani yace An matan Dikko……
Yauma shirye na fito cikin kayan makaranta amma Dikko ya rufe ido wai babu inda zanje , ai da kwata² na daina zuwa makaratar. Dan naga ya dawo daga tafiya yana huta gaji shine zance makaranta , kuka na farayi tunda yanzu na lura kukan shine ƙarfina a wurinshi , shikenan muje in kaiki ya faɗa yana cewa jirani ,
_kiyi ƙoƙari ki riƙeshi gida na kwana3 karki barshi ya fito…._ maganar Mai gilashi ta dawomin da turomin a saƙo jiya , binshi nayi ciki ina ƙara yawan kukana nidai bazanje dakai ba , idan dai ba tare dani ba saidai ki fasa zuwa , zama nayi gefen gado nace tou naji na fasa ina cire takalmina. Kallona yayi cikin ɓacin rai yace wato ni ban isa in jera dake mu fita tare ba ko ? Ko kuma karki tafi dani ace kinzo da tsoho ? Tou sai kinje makarantar wallahi , kuma nine da kaina zan kai daga yau ma idan ina nan nine zan riƙa kaiki ko ina tunda na lura so kike ki ɗaukeni wani bansan abinda nake ba , nine ma tsohon ? Yayi maganar yana shafa gefenmu , to idan dai dan wannan na zama tsoho yau saina kwasheshi , da sauri nayi wurin nace yi haƙuri dan Allah , rufe idanuwanshi yayi da yanayin haukarshi yace ke…….. Saina cireshi duka wai shekarata nawa ne ? Ke baki da lissafi ne ? Ko dan kinji ina ce miki yarinya ne ? Tou nima bara in dawo yaron tunda kin rainani dani dake duk mu haɗu muyi yarintar , ya ƙarasa maganar yana nufa hanyar toilet , da gudu nasha gabanshi cikin kuka na haɗa hannayena ina cewa na roƙeka da girman Allah kar kayi min haka , daka min tsawa yayi tare da cewa matsa ki bani wuri ya janyeni ya shiga toilet in , binshi nayi ina ƙara yawan kukana dan Allah Dikko kar kayi , so kake idan na fita naga masu gemu in riƙa kallonsu ? Nayi maganar cikin sanyi , tou me yasa kikemin abinda bana so ne ? Bazan ƙara ba , nunani yayi da ɗan yatsa yana cewa daga yau ko me kikayimin zan cireshi kuma banajin yi haƙuri , goge hawaye na nayi tare da jinjina kai nace na yadda , maimatawa yayi a karo na biyu cewa ko me kikayimin. Zan , ya nuna da hannunshi yana fitar da sauti mai kamar fito , kenan zai cireshi. Nace na yadda , tou wuce muje yayi maganar yana murmushi , fitowa mukayi saida ya tsaya gaban madubi ya sake gyarashi kalar fizgar hankali sannan yace muje yayi gaba…..
Binshi nayi ina sauke ajiyar zuciya. Gaskiya yana da kyau maza ku san abinda yake ɗaukar hankalin matayenku daga gareku , kuma ku ɗan riƙa cancaɗewa kuna yin kalar burgewa a gaban matayenku , ita fa mace abu kaɗan ke ɗaukar mata hankali , idan dai bakayi ma matar ka gayu ba tou gaskiya baka haɗu ba , wallahi wasu mazan ko ɗaki ɗaya baka iya haɗawa dasu , ba wanka bare kuma kasa ran samun ƙamshi a jikinsu , yadda yaje kasuwa ya dawo haka zai dawo ba wanka ba wanke baki duk ƙurar kasuwa ta gama barbaɗeka , ita kuma matarka tasha wanka taɗauki fili da gayu kamar zataje gasar wanka , ta haɗu tana ta zuba ƙamshi kamar matar sarki sai kace a haka zaka zo ka wani rungumeta , tsakanin ka da Allah kayi mata adalci kenan ? Gaskiya duk mu haɗu mu gyara gaba ɗaya sai a zauna lafiya. Idan kuwa ba haka ba ta sauke ka daga saman gadonta har sai ka koyo wanka wanke baki da kuma shafa turare…. {{ ba cewa nayi ki saukeshi ƙasa ba , ah kidai ɗan gyara mishi dan kema zakiji daɗin tafiyar idan da ƙamshi , ai kindai gane ba , kinsan wasa bai tafiya idan ba abokin wasa haka kuma baya daɗi idan babu abun wasar , kenan wancan hikimar da nake magana tafi daɗi idan da gyaran fili }} haba kuma kuyi koyi da Dikko mana. Ku zama “yan gayen mazaje shalelen matayenku.
Da sauri Ashiru ya fito yana cewa Mai gida bari in kaita , bai mishi magana ba ya wuce wurin mota ina bin bayanshi , da kanshi ya buɗemin na shiga ya rufe , wurinsu Ashiru ya koma suna gaisawa , duk banajin me suke cewa bayan ya gama ya dawo yana ɓata rai , juyar da kaina nayi nima ina fushi har muka fita daga gidan…..
Har mukaje makaranta baimin magana ba , nima banyi mishi ba. Tuƙinshi ya jawo hankalin mutanen dake kusa dan baya tuƙi da natsuwa kwata² , fita. Yace bayan yayi parking , matsawa nayi na shafa fuskarshi nace amana nayi maganar idona cike da hawaye , naji jeki , saida na sumbaci gemunshi sannan nace ina sanka na faɗa ina kallon idonshi , murmushi jin daɗi yayi yace Allah yasa da gaske kike , da gaske nake Dikko , riƙeni yayi tare da cewa zanzo in ɗaukeki idan kun tashi , kuma ki daina ɓatamin rai An mata kinga banajin daɗin abinda kikemin , wallahi maganar da kikamin shekaran jiya bakiji yadda naji ba har yanzu zuciyata ciwo takemin , ki daina haka babu kyau , to , ngode ya faɗa yana ɗan gyarawa. Nima godiya nayi mishi tare da fita , addu’ar Allah ya tsare yaimin nima nayi masa Allah ya tsare hanya , saida ya tafi na wuce……
A aji kuwa Mai gilashi ta tambayeni yadda aka ƙare jiya , kai tsaye nace mata janshi nayi mukayi faɗa duk dai abinda ya faru na faɗa mata. Cewa nayi kuyi faɗa ? Ta tambayeni ? Waike baki iya irin ɗan karuwancin nan ba ? Waye yace miki da faɗa ake hukunta namiji ne ? Ai namiji bakiyi mishi hauka , da sannu kike latsashi , kuma da kinja kika ga yaja sakar mishi ki kuma bishi da swry My President. Shiru nayi bayan wani lokaci nace nima yadda kika ganki a da haka nake , wani abokin Babana ne yayi min asiri naɗan firgice bayan kuma an samu nasara lalatawa na zama sai a hankali , tunda kinga abinda nakeyi dama bani ce nakeyi da kaina ba , tsoki Mai gilashi tayi. A hankali ta ɗan fara labarta min halin Sharifa tare da cewa kuma idan ta faɗamin na daina zuciya ina aikawa Dikko da saƙon zagi , in kwantar da hankali in bata haɗin kai yauma inyi ƙoƙarin riƙe Dikko karya fita domin tana shirya ma Sharifa gadar zare ne , so take ta rifto cikin rami ita kuma sai ta bita da ƙasa ta rufe , tana min maganar taga wani malami ya wuce , miƙewa tayi tare da cewa bari inje wurin wancan mai zanzaron inji me yasa zai ɗauro mana ƙugu yana tayar mana da hankali , tana faɗin haka ta fice daga ajin.
Har aka tashi makaranta Mai gilashi bata dawo ba , Dikko ne yazo ya tafi dani gida , ina ta tunanin yadda zanyi in hanashi fita a daren yau , dan nayi imani yadda ya samu sauƙin nan tou fa lallai babu abinda zai hanashi fita………
*JAMILA MUSA….* ce.
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN…*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa…
*JAMILA MUSA…*
*SAI NA AURI D ‘ K*
🅿 —— 6
Gareku 👇🏻
UMMIEE ZARIA
UMMU FATIMA
&
ZAINAB MUSTAPHA MUSA { Mmn Sadig }
Wata irin zufa ce ta ratato ma Dady. Da sauri ya cire hular saman kanshi ya fara firfita da ita , itama wayar tashi ya sauke daga saman kunnenshi. Miƙewa tsaye yayi bayan ya ajiye wayar da hular a saman tebirin gabanshi ya cire babbar rigarshi ya ajiye cikin tashin hankali , kamar wani zararre ya dafa tebirin yana furzar da hayaƙin ɓacin rai , ganin banza bata kai zomo kasuwa yasa ya ɗauki makullin mota da waya ya fita…. Da irin tuƙin Mai gida Dikko ya fita kuma dashi ne yaje har gidanshi……
Ba kowa gidan. Dan haka kai tsaye ɗakinshi ya wuce. Inda yake ajiye takaddar ko wane ƙaddara nashi ya nufi wurin ya fara ɓaro kaya harya sauko da kaf kayan ya ɗauko fiyel in. Salati ya farayi jikinshi yana kyarma , a hankali yake ɗagawa yana salati harya gama dubawa amma babu takaddun gidajen da akace masa anga Hafsa tana takai dillah² , da gaske kenan ? Wata irin luƙeƙiyar ashariya ya atura yana fizge² ya ɗauki wayarshi…..
Matarshi ya fara kira , amma harya ƙari kiranta ya gama bata ɗauka ba dan bata da lokacinshi. Hafsa ya fara kira itama tanaji tana kallo ta watsar da kiran nashi wanda Amisty ce ta hanata ɗaukar kiran , fita yayi da sauri yabar sauran takardun watse a tsakar ɗaki , har ya fita me ya tuno ? Oho ya dawo ya tattara su ya ƙanƙame a jikinshi kana kuka kamar gawar jaririn mahaukaciya……
Hello……… Ta faɗa cikin irin yanayin da mata keyi idan zasuci banzar samari. Tsoki Yazeed yayi cikin gunguni yace ummm , Ya Yazeed ya naji sai wani riƙe fili kakeyi ko baccin rana kakeyi ne ? Ummm ya faɗa da yanayin rashin san yayi wayar , kuɗi fa sunzo ta faɗa cikin farin ciki da zaƙuwa , yaji daɗi sosai amma bai nuna ba , yace wasu kuɗi kuma ? Yayi maganar yana ɗan sakin muryarshi kaɗan. Cikin warwarewar lissafi tace Yaya D’ K ya turomin da 10miliyan na biko , da sauri Yazeed ya miƙe tsaye yace kina ina ne yanzu ? Ina inda ka sameni jiya , yanzu D ‘ K yana sanki kenan ko ? Ummm itama ta bashi amsa cikin yanayin jin daɗi da kuma kunya haka kaɗan , ba damuwa gani nan zuwa muyi magana , sai……ka…..zo muah. Ta bashi kiss tare da tsinke kiran.
Yazeed yace wawiya wane ɗan tashar bokan ne yace miki D ‘ K yana bikonki ne ? Halan yayi haka ne dan ya ruftaki , tunani yayi sosai bayan wani lokaci yace kai ai ba haka yake fitar da zakka ba , jakunnan banzaye kuso Yazeed ko ba kuɗi yarinya ta hau network mai service , ai dake da Sharifa da ma duk wata ƙazarma mace na rantse da girman Allah baku gabanshi , da dai yana ɗan biya allon mata { danbe } da sai ince zai wanke ku ne yayi gaba abunshi. Bara dai in tafi da wuri kafin wani malamin tsubbun ya rigani ƙwacesu.
Da wata irin rashin lafiya mijin Halima ya tashi yau , ko idonshi baya iya ɗagawa , yayi amai tun cikin dare baisan iyaka ba , yayi na safe yayi na rana har a marecen nan sai yunƙuri yakeyi , waƙƙƙ , yaci uwashi yaci ubanshi har yai laushi. Duk ƙawayen matarshi zagaye dashi sai jera mishi sannu sukeyi kamar sakin kurwar mayu. Halimatu kuma na gefe tana ta duba sabbin kayan matar da ƙawarta ta aiko mata dasu tana karantawa da kuma irin matsayinsu da wutar da suke bayarwa idan an shiga tsakiyar filin wasan danbe. Saidai ayi murmushi idan aka karanto “yan bala’e , ita a gefe ƙawaye a gaban gado…..
Da gudu na fito daga toilet jin wayata na ƙara , nayi tunanin kila ma ko Mai gilashi ce ? Dikko na gani tsaye gaban wayar zai ya ɗauka , aikinshi kenan idan yana nan aka kirani , An mata waye ya kiraki ? An mata me akace ? Kawo in gani ? Shi gani yakeyi ta waya ake zuge mishi ni. Da Allah nace ka daina taɓamin waya , kai ake nema ko ni ne wai eye ? Haƙuri ya bani tare da miƙomin yana cewa na ɗauka fa Mama ce ta kira. Idan Innar ce kai take kira ne ? Nifa gaskiya bana san abinda kakemin ko kai zuwa nakeyi ina tsareka idan kanayin cht da karuwowinka ne ? Sa ido kamar maƙocin mai kura. Ansar wayar nayi daga hannunshi , baƙuwar number ne kuma kiran ma ya tsinke. Kayan dana cire na ɗauka na wuce ɗakina ba tare dana gama wankan ba , ina zuwa na rufe ƙofa na zubar da kayan ƙasa na wuce toilet.
Gefen gado Dikko ya zauna cikin ɓacin rai…. Yana ƙoƙarin riƙe ɓacin rai amma An mata bata gani dai ko ? Tou wallahi idan dai ta kuskura ya riƙeta na lahira sai yafita jin daɗin , wai karuwowinshi ? Jinjina kai yayi cikin tsananin ɓacin rai a hankali ya furta saina kashe ki…. Ya faɗa yana riƙe wuyanshi… Rufe idanuwanshi yayi yana hasko lokacin data fito da gudu daga toilet , banda ma hauka da yarinta ji yadda ta wani fito da gudu ? Da taje ta faɗi ta kashe mishi babynshi , taci albarkacin ko ma waye kwance a cikin cikinta , amma akwai ranar ƙin dillanci , wato ranar da wandon mai gari ya ɓace…….
Tunda na shiga wanka kiran yake ta sake shigowa har na gama wanka ba’a daina kira ba , ni nayi tunanin Mai gilashi ce dan haka na ɗauka , suna na *SHARIFA…* , wai Allahna na rantse da girman Allah na kaɗu gabana ya yanke ya faɗi kawai dai naji tsoro , dakel nace to ya akayi ne ? Kiranki nayi in faɗa miki nice wacce Dikko yake so. Kuma ni kaɗai yake ma soyayyar da bata da farko ballantana ƙarshe , ya gina min soyayya mai girma tsakanin saman sararin filin zuciyarshi zuwa tawa. Ni kuma na gina mishi tawa soyayyar bulo da bulo tsauni da tsauni tafiya da tafiya kalma da kalma tsakanin dare da rana na gina a cikin zuciyarshi….. Nice yake ma soyayyar da bayayi miki irinta , iska ce ni idan na kaɗo saina ɓaro da “ya “yan kanya daga jikin uwarsu iska ta tana ƙarfi. Ki tsaya ki gani haka zan kakkaɓeki tsaf inyi waje dake…….
Murmushi nayi mai sauti tare da cewa aikin banza an tura agwagwa ruwa. Duk lokacin da kikabi kika gina ko ya gina wannan ba matsala ta bace ba. Nidai abinda na sani na kuma fahimta ke daƙiƙiya Dikko ya ɗaukeki , idan kuma kina ganin shi zai aureki tou ƙarya yayi miki dan har yanzu zuciyata ta ƙaryata aurenshi. Bata faɗamin ƙarya akanshi wallahi duk abinda ta faɗamin ko ta ansa akan shi tou wallahi zai faru , liƙi a idon bainan nasi bashine yake tabbatar da soyayyarki a zuciyarshi ba , idan ke iska ce to Dikko guguwa ne. Gittawarshi tashin hankali ne domin idan ya taho kowa saiya gudu ya ɓoye saboda girman hatsarinshi , sahun keke ne shi mai gasawa mata azaba a tafin hannu , naji ke iskace. Kanyar kaɗai kike iya ɓarowa banda ɗan kuka , zubdo ɗan kuka saida babban makami badai iska ba ko jifar ƙananun yara , Dikko kuwa iccen kuka ce shi koda karfinka saida rabonka ko ka jira bushewarshi , to shi ɗanye ne yini ɗaya zur kana jefa amma baya faɗowa sai kayi jan ido , idan kuma kika ce ki hau tou lallai sai kin sauko gurguwa. Icce kuka hawanshi sai an shirya , idan ba’asha dare ba asha rana. Dan haka ni soyayyar da yake miki bai shafeni ba , nawa na tabbatar tunda ya kawoni gidanshi ya adanani a matsayin matarshi , ku ya ɗauka mahaukata abon firarshi idan ya fita , jakuna banza da baya zuwa firar zance wurinku a gidan iyayenku saidai ku baro gidajen iyayenku ku biyoshi , ni ban ɗaukeki a bakin komai ba. Saboda duk abinda zaki faɗa masa ko ya faɗa miki a kaina ya fara faɗa , kuma daga gareni ni kalamanshi kaf suka ƙare banza sharar bisa titi mai kauyawan kalamai Dikko baya auren karuwa…….
Zagina tayi sosai tare da cemin *SAI NA AURI D ‘ K* nace ƙarya takeyi , ta sake maimaitawa , nima na maimaita ƙarya takeyi Dikko ba ƙaddarar mallakin ballagazun mata bane ba , haka mukai ta caccakar juna kowa yana yanka kalamai masu ciwo tare da yima abokin faɗar tashi gori , ita ta gaji da kanta ta kashe wayar ta bayan ta tabbatarmin da sai na fita a gidan Dikko. Tsoki nayi bayan ta kashe nace shirmen banza shirmen wofi.
Haka yaita garari tsakanin Qerau da duk inda yasan akwai wata madakata ta “yan iska har dare amma baiga Hafsa ba kuma babu Amisty , Qerau ya koma ya kafe motarshi ya fito ya daki gaban motarshi ya halbi tayar da ƙafarshi yace wallahi idan Amisty da Hafsa basu fito ba saiya cinna wuta ga duk wani gida dake cikin Qerau kuma haka duk wata karuwa daga yau kasuwarta ta mutu dan duk wata karuwa dake anguwar nan sai ta koma gidan ubanta , “yan iska kowa tabar jaharta da iyayenta sunzo sun zamar musu annoba a cikin garin Katsina. “Yan iska zuwen banza da wofi , tou yanzu zanyi waya a kawo min tankar man fetur duk saina babba gidajen dake cikin anguwar nan , haka yaita ɓuɓɓurma zagi kamar sabon hauka lokacin da sarara.
Babu wanda yayi ma Dady magana. Haka ya kashe santa yaci gaba da ƙaryar rashin kunya iskanci kuma sanka² , karuwan dake zaune a ƙofar gida saman dakali suna lido ko kallo bai ishesu ba , ganin zasu ɗaukeshi mahaukaci da hankalinshi yasa ya samu wani yaro yace yaje maza bakin titi ya kira mishi duk wani ɗan bunburutu kuma su taho da jarkar fetiri. Yaro ya ƙwalƙwala da gudu ya tafi dan tattaro duk wani mai siyar da fetir. Wata tsohuwar karuwa ce da ta gaji da karuwanci har ta gagara tuba ga Allah ta tsufa iya tsufa , breziya ne a jikinta sai zani ɗaurin ƙugu da kallabinta tayi mishi ɗauri irin na tsofaffin “yan iska , kai da ka kalleta kasan ba Allah a lamarinta domin har yanzu duniyar gaba suka bata ba baya ba , tsaye take a ƙofar gidan Amisty fitowarta kenan daga cikin gida tana shan sigari , riƙe tabar tayi da bakinta ta dafa hannayenta a ƙofar. Saida ta gama kalle waje tass sannan ta fito da rangwaɗa….
Wuri ta samu ta zauna ƙafa ɗaya saman ɗaya tana ci gaba da kora hayaƙi tana wani hankaɗe kai sama cikin iskanci da sanin hannunta wurin kwarema iya jan sigari. Kallonta Dady yayi yace ke tsuhuwar karuwa ko kinga Hafsatu ne ? Banza tayi dashi taci gaba da jan hayaƙi tana aikashi sama , wurinsu ya matsa yana cewa zaku fiddosu ko saina tona muku asiri ne ? Sai yanzu tsohuwar tayi magana cewa , karuwan yanzu kamar man kitse ne a saman wuta , yayin da suka ga hasken rana sai su gudu su koma ciki gudun karsu narke , zamaninmu mu kuma , ta nuna kanta tana tafiya da maganar ta cewa mu wutar muke nema ido rufe amma da ta hangomu sai ta suƙe kafin mu iso , ni da lokacin da nake Adda ta ce da saina rabaka gida biyu bayan na ɗaukeka na saka cikin ɗakina shegen nan dasai nayi maka fyaɗe , karuwan yanzu matsorata ne. Su ke gudun mazan ba mazan ke gudunsu ba , zamani na ni kuma da nayi iskanci maza idan suka ganni ɓoyewa sukeyi saboda wutace ta doso wuri , kallon taron yara²n karuwan dake zaune tayi tare da cewa mataye……. Gareku tayi maganar tana nuna Dady. Sannan ta haɗe kai dasu tayi musu ƙus² a dai² lokacin da yaron ya dawo da “yan bunburutu layi ɗaya kowa ɗauke jarkar fetir…..
Gaba ɗaya karuwan suka haɗa baki cewa. Dan Allah Dady kayi haƙuri , 🙏🏻idan ka ƙone mana gida ina zamu zauna ? Wannan gidan da kake gani ba namu bane ba , amma tunda munga da gaske kakeyi bara mu faɗa maka gaskiya , har yanzu tare suke magana kuma a tare kowa ta nuna da ɗan yatsanta manuni suna cewa ai Hafsa da Amisty suna hango motarka suka shige can gidan suka ɓoye suka nuna gidan da Dikko ke kiwon dawakan shi , tare sukeyin magana babu wanda yake wuce wani kamar suna biya karatu , amma kayi haƙuri karka ƙona gidan idan ka ƙonashi wannan gidan za’a siyar a biya masu gidan can kuɗin fenti da abinda ya ƙone , idan kuma aka siyar kaga shikenan kasuwarmu zata mutu kamar yadda kace kayi haƙuri don Allah , suka ƙarasa maganar suna haɗa hannayensu wuri ɗaya na neman gafara…..
Dady ganin sun tsorata shima ya haɗa kanshi da masu bunburutu yace tou kuyi da wasa ku yayyafa fetir ɗin nasan zasuyi musu waya su fito , masu fetir zasuyi magana Dady ya toshesu da kuɗi yana cewa idan dai dan wannan ga kuɗinku , su kuma suna so su faɗa mishi gidan Dikko ne ya duba yaga wace karuwa ta isa ta mallaki gida layi ɗaya tun daga farko da kuma ƙarshen santa , amma sai Dady yace ai bafa ashana za’a ƙyarta ba , ya ƙara musu kuɗi , aje ma Dady fetir sukayi ya ɗauka yaci gaba da watsi dashi yana cewa saina ƙone shi , su kuma karuwai sukaci gaba da cewa Dady dan Allah ka rufa mana asiri karka toya gidan nan. Idan ka ƙoneshi asirinmu zai tonu komai da muka mallaka zamu rasashi wurin gyaran gidan nan , Dady yace saina tona muku asiri , a tare sukaci gaba da cewa ka rufa mana asiri karka tona asirinmu , ci gaba yayi da mita yana saiya tona musu asiri , saida ya gama zazzaga fetir ya ɗauko layter ya kunna yana cewa zan cinna fa…. A dai² lokacin da Umar ya fito shi kuma warin fetir in ya fiddoshi , idanuwa ya zaro tare da cewa kai׳ kashe mu zakayi ne ?
Dariya Dady yayi tare da cewa halan ka tsora ko ? Umar yace ba dole inji tsoro ba zaka kashe mu ? Matsowa Dady yayi da wutar yana cewa to koma ka fiddomin Hafsa da Amisty ance sun sayar min da gidaje 3 da suke duk a cikin lay-out masu haya a gidan ne suka kirani akan ban musu adalci ba na siyar da gida babu notice , su fito su kaini wurin wanda suka siyi gidan ni a bani gidajena , kasan ko miliyoyi nawa na siya ? Tou kaf kuɗin gadon “yan ɗakinmu ne na lashe yayi maganar yana nuna lashewa da harshenshi. Murya ƙasa² tare da matsawa kusa da Umar yana cewa dukiya…… Akan kuɗi babu abinda bazanyi ba , da hannun haggunshi ya murza “yan yatsu biyu sukayi ƙara cewa koma ka fitomin dasu kafin in toye wannan gidan…..
Karuwai kuma cewa sukeyi mun tuba Dady kayi haƙuri karka toye , shi kuma Umar cikin rashin fahimta yake kallon Dady , dariya Dady yayi tare da nuno bayanshi yana cewa ya kaji suna cewa….? In rufa musu asiri fa , saina toye , shin na toye ko kuwa ? Zaɓa mutuwa ko kuɗin gidajena ne ? Umar ya fara takawa baya Dady yana binshi yana cewa me kace ne ? Hannu Umar yakai da niyar ɗora hannunshi akan layter amma sai Dady ya fizge , wurin fizagewar ne ta faɗi wuta kuwa taci gaba da ci…. Karuwai sukace yawwa tou kane asirin ka zai tonu gidan Dikko ne……. Suna dariya , aimu babu wani da ya isa ya kashe mana kasuwar karuwanci ko ya tona mana asiri saidai mu , mu tona asirin mutum , ana baka haƙuri kana rashin kunya , kaga sai kaje ka saido sauran gidajenka kayi mishi gara da ramuwar dokunanshi , tsohuwar tace dokin da aka kawo shekaran jiya na miliyan talatin da biyar ne , shin ka ajeta….? Kwaiwayon maganar Dady sukaci gaba dayi , yayin da Umar yayi gaba yana akawo ɗauki Dady kuma ya fara kiran “yan kwana² asara goma da ashirin…..
Amisty da Hafsa kwance a wata lafiyayyar hotel dake cikin garin Abuja , banƙararren rago ne aka gaso musu , sai kaji da aka kaso musu sunkai ashirin , manyan lemuna na kwali masu tsadar gaske da kwaleyen sigari an jera su da kwalaben giya , ɗakin cike yake da manyan karuwai da suka gode ma zamani da zuwan wannan rana , ita kuma Hafsa daga kwance ta kwance hannunta ta ƙara ƙwalƙwaleshi tasha kukanta sannan ta maidai abunta ta rufe….. Daga kwance Amisty ta fara gabatar da bayani kamar haka…….
Barkanmu da kasancewa a wannan lokaci manya karuwa maza da mata , na baya , gaba , haggu da dama duk muna muku barka da zuwa , {{ wato masu maɗigo da “yan luwaɗi sai kuma mazinata…. }} kamar dai yadda kuka sani muɗin masu sa’ar rayuwa ne kullum nasara muke samu babu faɗuwa , mune manyan jajirtaccin karuwai da muka kafa manya² tarihi a cikin jahar birnin garin Katsina , kuma mune zamani na farko da muka kawo wasan danbe a duniya , kullum nasara muke samu dan haka ya kamata a jinjina ma bariki don Allah , shewa sukayi gaba ɗaya tare da ɗaukar kwalaben giya kowa ya ɗaga…..
Saida kowa yasha yayi gyatsa alamar ta sauka ciki Amisty taci gaba da cewa. Bariki tayimin komai , ta biyani kuma ta raineni fiye da yadda nayi tunanin samu daga gareta , bariki ta itace uwata kuma itace ubata a cikinta na rayu tun bansan wace ce ita ba. Mutane na cewa bariki bata da tabbas , tou ni kuma na ƙaryata masu wannan maganar , bariki kuwa itace mai tabbas ga amana haɗin kai da kuma ƙaunar juna , a taƙaice dai ni bariki tamin tabbas….
A gurguje dai muyi abinda ya taramu a wurin nan , manyan gidaje dake can cikin lay – out na Dadyn su Hafsa mun siyar dasu akan farashi mai tsoka saboda kunsan komai shi ke siyar da kanshi , dalilinmu na siyarwa kuwa sirri ne tsakanin rayuwarmu mu biyun duk dai bama ɓoye ma juna sirrin juna tare ake ci kuma idan an samu , ku nawa ne duk taron ku ? Irga kansu sukayi sannan aka faɗawa Amisty ko su nawa ne , Amisty tace mutum goma ? Tou za’a bawa kowannen ku a ciki zunzurutun kuɗi har naira miliyan ɗaya a cikin kuɗin. Jibi kuma dani da Hafsa zamu wuce india mu wanko zumibi mu dawo….. Idan kuma aka sake samun wata sa’ar sai a tura wasu a cikinku su tafi , tou ya kuka ga tsarin ne ? Kowa yace haka yayi Kaka……
Shagali…… Suka faɗa gaba ɗaya , dan haka aka rufawa kwalaben giya da sigari , suma kaji da naman rago aka ciccinye aka kora da ruwan lemu , bayan sunci iya cinsu aka tattara sauran aka fitar…….
Mutumin da Amisty ta kai Hafsa a matsayin malamin tsibbu shine ya kira Amisty akan shima ta fiddashi , cikin maye tace ai babu kasonka a cikin , haɗata ya farayi da girman Allah amma fur Amisty tace ai ko Hafsa bata kashi da gaurayen kuɗin nan , kuɗi duka suna wurinta sun kuma zama nata. Mallakinta bata rage musu ko sisi kuma da asuba zata fece abunta ta tafi can ƙasar waje ta buɗe sabuwar da’irarta , karuwan suma da tace za’a basu one² miliyan ƙarya takeyi , ai ita ba daƙiƙiya bace ba tasan hannunta , ta siya sabuwar mota ta miliyan 5 dan haka daga nan zata canja akalar tafiyarta zuwa Mambila , idan taje ta huta daga can zata wuce gaba abunta ta wani ɓace cikin duniya kamar yadda jirgi yake lumewa a cikin giza²i dake saman sararin samani , dariya tayi sosai cewa kusha zamanku a Katsina Amisty ta tafi yawon buɗe ido sai mun haɗu a lahira. Hahahahaha tayi dariye cike da iskanci kamar zatayi kuka , Allah sarki zanyi ƙewarku Katsinawa…… Dariya ta sakeyi bayan ta kashe wayar tace Amisty tayi gaba kuma babu dawowa……..
Wata irin ashar ya fesa bayan Amisty ta kashe wayarta. Cikin ɓacin rai ya sake daddana ashar kamar rainon mutane gafiya , yarinya idan kinsan wata baki san wata ba , shima dake kwallon gigiye ne wurin iskanci da taurin kai , cikin garin ya famtsama a daren saida ya gano har hotel in da Amisty take a Abuja , mutanensu na can Kaduna da kuma “yan iskan dake saƙe a sansanin yanki Abuja manyan “yan ta’adda ya buga ya rattaɓa musu komai ya kuma ƙara da cewa su hari Amisty. Su ƙwace kaf kuɗaɗen har motar karsu bar mata……. Shima yana zuwa Abuja a daren nan , suma bayan sun gama waya dashi suka sanar da mutanensu na Katsina suka kuma tura hotonshi da adireshin cewa su ɓarar dashi suna da kaso biyu a cikin kashi goma na kuɗin , shiri suka farayi ta yadda zasu riƙe Amisty da kuɗin cikin sauƙi……
Kirari yake ta goga mata kamar tsohon maroƙin da yayi shekara baici ba , su Jiddah saidai a juyar da kai ayi dariya kan׳ dariya irinta jakkan mata , haka Yazeed yaita ɗorata tana hawa shi kuma ya rungume banzar yaita lalubarta. Daƙiƙiyar ta saki baki taci gaba da dariya kamar kwarto yaga wa²n zama. Haka yaita suɗeta yana bazo mata manyan kalaman batsa , a cikin motar dai ya labbaceta ya buga round ɗaya na danbe , yau yanajin shi wani babban shege ne yabi hanyar da D ‘ K ya taka ya wuce….. Bayan ya karance tayi mishi transfer na 5miliyan. Sannan tace a tsaida ranar aure tunda an samu kuɗi , kai tsaye yace sati mai zuwa…. Da farin ciki Jiddah ta fice Yazeed kuwa ya wuce wurin harkar danbenshi tunda ya samu kuɗi.
A ɗakinta dake gidan Rabiya ta kwanta ruf da ciki a saman gado tana tunanin Dikko , jinjinoshi tayi sosai sannan ta jinjino haɗuwarta da Yazeed kai zanen ba ɗaya bane ba kuma karatun yasha ban². Dikko fa daban ne yayi zarra + zarra , gaskiya da gaskiya ce , jarumta ta zahiri duka da duka , salo bisa salo ƙwarewa da iya gugar zanar sanin abinda ake kira da danbe yana nan wurin Dikko , wannan shi ake kira jarumin namiji ba lusari ba , kana ta ina ne haka ? Me kakeyi yanzu ? Kana tunani na ? Koma dai miye ina nan dawowa gareka ka ƙara haƙuri ɗan uwana.
Sun nemeta har sun kaji , bokansu ya bugi ƙasa ya zana , ya goge amma ya kasa ganin inda Mardiyya ta shige , haka nan Suwaiba ta haƙura ta dawo Katsina. Kuma bata wuce Daura ba tana nan ta saƙe a cikin Katsina !
Bayan anyi nasarar kashe wutar dake ci a wajen gidan Umar ya riƙe Dady tare da cewa saiya kaishi wurin Mai gidansu. Haƙuri Dady ya bawa Umar cewa shi baisan haka abun yake ba , iyakar dai wutar waje , babu abinda taci sai fulawowin da sukasha fetir dan haka suka babbake bangon wurin yai duhu. Umar ganin tashin hankalin da Dady ya shiga bai faɗawa Dikko abinda ya faru ba , saidai zaiyi sabon zubi na filawowin da sukaci wuta , sai fenti da yace gaba ɗaya kaf gidan daga ciki har waje zaiyi fenti dan idan akayi a wajen gidan kaɗai Dikko zai gane , idan kuma ya gane zaiyi tambaya shi kuma zai faɗa masa kai tsaye baya munafirci , sai shi kuma a bashi na toshiyar baki.
Wannan tsohuwar karuwa ba haka taso matsalar ta tsaya ba , taso a toye kaf gidan dan Dady yaci uwarshi wurin yaron nan , ita sau ɗaya ta taɓa ganin Dikko shima abinda yasa yadda taji Hafsa tana zuzutashi , ita tasharshi da aka bata labarin abinda yayi ma Sultana ya burgeta yadda taga Dikko tana so taga Sultana itama , to shine fa ta matse lamba taga ɗan iskan yaron nan , da taga hotonshi ta matsa sai ta ganshi da idonta , matashi ne kyakkyawan yaro amma kai da ka kalli Dikko kasan baida mutunci ko kaɗan ɗan iska ne bugu ɗaya , kuma wasu irin firgitaccin idanuwa gareshi tsaitsaye na rashin kunya , ita a yadda ta auna shekarunshi zasu fara daga 35 har zuwa 38 ita dai a yadda ta ajiyeshi fa , dan yana da suffa mai ɓoye shekaru yana da cikar zati da ƙwarjini saidai daga ganinshi kasan sangartacce ne , yana da tsayi dai² kyau , yana da murzajjen jiki na zubin jaruman maza ba ƙaton jiki ba dan baida ƙiba kuma ba siriri bane ba yana dai da jiki mai kyau sai hutu ya zauna. Gaskiya Dikko yayi mata kyau , kuma kyakkyawar fatarshi ta dace da gemun daya ajiye mata , zuwa ɗaya idan kayi mishi dogon kallo yana da ɗabi’un mutanen kirki amma gogaggen ɗan iska ne kuma bashi da kunya yadda ta fahimce shi , tou taso ace gidan ya ƙone taga yadda zaizo yayi ranfar da akace yanayi wallahi yau taso aci ƙaniyar Dady a murje bakin tambayar kuɗin gidaje har sai Kaka ta dawo suma ta basu kasafinsu…. Itama dai Dikko ya burgeta gaskiya addu’arta ɗaya Allah yasa da rabon Hafsa a cikinshi.
Misalin ƙarfe 11 da wasu “yan mintuna na dare na ɗaure Dikko dake kwance yana bacci saman gado da igiya. Buɗe idonshi yayi ya kalleni cikin ɓacin rai , cike da rashin kunya na murguɗa baki tare da zazzaro ido nace yau na ɗaure ƙafar yawo wallahi , sai naga ta inda zaka bi ka fita , da chat in dare da fita yau gaba ɗaya An mata ta hana nayi maganar ina watsa hannunawa alamar babu , fiffizgewa ya farayi yana cewa idan na kwance sai na zaneki An mata , zama nayi gefen gado tare da faɗa cikin rainin wayau cewa ai bama zaka iya kwuncewa ba , taimako ɗaya zanyi maka. Bara in kunna maka kwallo ka kalla , nayi maganar ina ɗauka rimot kusa dashi na kunna tv. Tsoki yayi a gajiye ya koma ya kwantar da kanshi yana bina da kallon takaici….
Ka daina kallona ka kalli talabijin na nuna mishi tv , ajiyar zuciya ya sauke tare rufe idanuwanshi. Tashi nayi daga inda nake zaune na koma cikin kujera na zauna inacin gurguruna { pop corn } ina cin abuna ina kallon kwallo , buɗe idonshi yayi ya kalli Sultana sannan yace An mata kizo ki kunce ni kafin raina ya ɓaci , naji shi sarai amma sai na ƙure volume ina cewa ka rufe min baki bana san surutu ina kallon kwallo ka kalla nace , nayi maganar ina watsa gurguru baki. Ke……… Zoki kunce ni nace , cikin faɗa nace anƙi a kuncen kan kuma ka rufemin baki bana san surutu idan ina kallon nace maka , An mata……… Ban barshi yayi magana ba na zaro ido tare da haɗa masa da shittttt 🤫 nayi masa ina ɗora ɗan yatsa na a saman baki.
Kallona ya ƙarayi. Bayan wani lokaci yayi ɗan taƙaitaccen murmushi kaɗan ya kauda idonshi gefe yana nazari……….
*JAMILA MUSA…*
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN…*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa…
*JAMILA MUSA…*
*SAI NA AURI D ‘ K*
🅿 —— 7
Ƙasa² nake magana ina cin gurguru cewa. Ƙaryar rashin kunya. Ai sai an bar zomo yake zama guza. Kowa ai ɗan iskan kanshi ne , ni har an nunamin hanyar hukunci , a dai² lokacin daya sake kalloni da dogon kallo , murmushi nayi kaɗan tare da ibar gurgurun kamar zan bashi bayan kuma muna da tazara. Ya² ne ? Zakaci ? Na faɗa ina murmushin nasara. Girgizamin kai yayi alamar a , a , ya bani amsa. Ban sake magana ba na ci a bakina ina cewa saina….. Na nuna da hannun hagguta yankawa alamar zan yanka mishi wuya kenan. Idan bai daina kallona ba kalli can nace ma na ƙara nuna mishi tv…
Gyara bakinshi yayi ya kalli talabijin. Ni kuma naci gaba da cewa wato da ka kwanta kayi bacci , misalin 12 saura ka tashi. Daga saman gado zaka wuce bayi ka watsa ruwa , zaka fito ɗaure da rigar wanka. Kana fitowa sai ka tsaya jikin madubi , zaka goge jiki da towel , da hannuwa na na nuna yadda ake shafa mai ina shafawa a fuskata , daga fuska naci gaba da nuna duk inda ake shafa mai a jiki. Bayan ka gama saika fara goge fuska , ummm na nuna yadda yake sharce gemu da kuma yadda yake shafa turare dariya nayi sosai tare da komawa da baya na kwanta cikin kujera , bayan ka saka kaya sai ka wani fece abunka. Cikin dariya naci gaba da cewa tou yau Jarumarka ta ɗaure kafafuwan yawo , no cin cingom & no cht na nuna yadda yake riƙe waya da wayata , da hannun dama na sake nuna babu. Ina cewa kaji….??? Na riƙe kunne na dan ya tabbatar min yaji.
Baiyi magana ba kuma bai kalleni ba yaci gaba da kallon tv kamar yadda na sashi. Banda tuƙuƙi babu abinda zuciyarshi ke mishi , yana ta ƙoƙarin riƙewa da kuma dannewa ya gagara , cikin wata irin murya yace ke kunceni nace miki. Ya faɗa yana rufe idanuwanshi. Da hannu na nuna karka dameni da baki kuma nace ka fita idona in ba haka ba mizanete kana daga kwancen nan. Kai…………. Nine zaki dakar ? Tou saina kunce kuma saina kashe ki , da sauri na tashi ganin yana fiffizgewa da ƙarfi , saina kashe ki…….. Da gudu na fita a bakin ƙofar fita daga ɗakinshi na zame , shi kuma ihunshi ya ƙara yawa , ninen ma zaki daka ? Yau idan basai na ma kasheki ba tabbas saina kashe kaina…… Da sauri na tashi nayi ɗakina ina kuka ashe har yanzu Dikko bai warke ba. Rufe ƙofa nayi har nayi fitsari saboda tsoro. Har yanzu ina jiyo ihunshi yana faɗin saina kashe ki………..² ƙyarma jikina ya farayi kodai in fita in gudu ? Nine zaki daka ma………. ? To zo ki dakenin , kai………….. Saina kashe ki…………. Kowa da kowa ma saina kashe shi……. Ah² ba lafiya ? Na faɗa ina ƙara fashewa da kuka. Babu wani ruwana da ciki har babyn shima sai na kashe shi…………….. Kai……… Wai nine ma mace zata zane , a sauƙaƙar murya yace aiko dana zama lusarin namiji. Daga haka ya ɗauke. Tunda ai kunga yana kwance ne , dan dama idan ciwon ya taso mishi kwantar dashi ƙasa akeyi , idan dai aka kaishi ƙasa anci galabarshi. Sai a bashi magani dan idan ya tashi dawowa ya dawo da tunani.
A firgice na juya inda na yada wayata tana ƙara , ummm na faɗa tare da goge zufar dake bin fuskata. Rairafawa nayi inda take na ɗauka , Ashiru ne yake kirani , ɗauka nayi cikin kuka nace Dikko ne baida lafiya , ke kina ina ne ? Na kulle a ɗakina. Waye ya ɗaureshi ne ? Cikin kuka nace ai kaine ka siyo igiyar , Ashiru yace ba wanda ya siyo igiyar ba wanda ya ɗaure shi nake magana , nice na ɗaureshi , meya haɗaku ? Shiru nayi banda abin cewa , Ashiru yace kizo ɗakinshi. Cikin kuka nace ni gaskiya bazan zo ba , ranki ya daɗe kizo mu duk muna ɗakin , tou na faɗa tare da ajiye waya. Toilet na shiga na wanke jikina sannan na fito na gyara inda na ɓata da fitsari , kaya na canza bayan na gama na kira Ashiru yana nan ? Ya tabbatar min suna nan , hijabina na saka na buɗe ɗaki na nufi ɗakin Dikko.
Gaba ɗaya su Ashiru suna wurin , Dikko yana kwance a ƙasa ya dafe kanshi da hannun damarshi cikin yanayin jigata , ya fiffizge igiyar , wurin saukowa daga saman gadon ƙafarshi ta riƙe shi yasa ya faɗi kenan ? Kallona Ashiru yayi cikin ɓacin rai yace amma me kika faɗamin maganar siyo miki igiya ? Shiru nayi ina ta karkasa ido kamar an kama ɓarawon “ya “ya ina kallon Dikko sai kuma in kalli Ashiru. Gaskiya baki kyautawa abinda kikeyi. Mai gida dai kike ma haka ? Ya faɗa yana jinjina kanshi , kausasa murya yayi da fushin zuciya yace tabbas ke yarinya ce. Amma komin yarintarki ya kamata ki riƙayin abu da lissafi , tunani da kuma hasko abinda kaje ya dawo. Wannan ɗin dai da kika raina shine bangon rayuwarki idan har kika ɓata mishi ko wulaƙantashi kanki , idan kuma ya mutu tabbas ke zaki shiga3nki. Shawara da neman mafita ya rage naki. Ya ƙarasa maganar yana gyara mishi kwanciyarshi.
Durƙusawa yayi gaban Dikko yana kuka kamar ranshi zai fita , bayan wani lokaci yayi magana cikin hayaniya cewa ke bake kaɗai ba. Bango ne kuma jegone ga duk wani da kika ganshi yana tsaye a wurin nan yayi maganar yana nunasu hada kanshi , ƙasa² yayi da murya cewa duk yawancinmu nan da kika ganmu kusan mu goma sha wani abu rabin mu duk mu marayu ne , rabi daga cikinmu duk basu da uwa uba ko ahali , haka akaje aka kwaso mu aka kawo mu domin kula dashi , an ɗaukomu ne kamar karnukan shi muyi haushi yayin da wani yake tunkaroshi , babu wanda yasan darajarmu ko tausayin mu rayuwar da zamu shiga. Mu rayu ko mu mutu ba damuwar su bane ba shiɗin dai ake so mu ba rayuwarshi kariya , muyi haushi wan² yayin da wani yake zuwa dan taɓashi , mu kula dashi bayan ƙarshen wata biyu abamu naira dubu hamsin.
Cikin ɗaga murya yace amma shi bai mai damu karnuka ba……….. Shine ya jawo mu jikinshi ya ɗauke mu kamar “yan uwanshi , ya soke wata banzar dubu hamsin da Mai gidansu yake bamu {{ wato Dady }} bayan ya nuna mana kowa yaje yayi rayuwarshi , haka mukai ta kuka ya rufa mana asiri ya barmu mu zauna dashi koda an daina biyanmu albashin zamu zauna dashi saboda dubu hamsin ɗin dashi bai ɗauketa kuɗi ba , ganin yadda muka shiga tashin hankali yasa shi da kanshi yace zai riƙa biyanmu , shin kinsan farashin da yake biyan ko wane ɗaya a cikinmu ? Me mukeyi masa ne ? Bamayi masa wanka bama dafa mishi abinci bama masa wanki bama shara komai bamuyi mishi , zaiyi fita goma bai fita damu ba. Muci musha kowa dake wurin nan mazaunin shi yana a cikin gidan da yake rayuwa. Duk inda yake muna da gidanmu muma a can ƙarshen gida , palo bedroom toilet yadda yake da A C a ɗakinshi muma namu dashi. Yaga munyi kuka shi yasa yake san ya rayu damu domin muma muyi farin ciki kamar shi. Masu kuɗi nawa sukeyin haka ? Wanda sun ɗauki duk wani ɗan aikinsu kamar wani jakinsu. Shi yasa suka kira talaka da suna bawa………. Cikin kuka yace wai talaka shine bawa , wai bawa ? Kuma alere dangin jaki wai ya mutu gobe a sake sabo. Tou shi bai banbanta ba saboda soyayya , abincin da mukeci shi kanshi abun duba ne , idan ciwo ya kama ɗayanmu shine magani kuma ba’a cikin wanda zai bamu ba , albashin kowa a cikinmu da yake biyanmu idan kikaji sai kanki ya kwance , kafin albashi kuma ya bamu׳ , ya ƙara mana² , kullum cikin bamu yake , da marainiyar murya yace wai dandai muyi farin ciki , shi bai ɗauki duniyar a bakin komai ba dan ba itace gabanshi ba , tsaye yake ba dare ba rana , ya hana idonshi bacci zuciyarshi da kwalwarshi sunƙi samun natsuwa , bawai dan ya rasa yake nema ba. Ba kuma dan zai rasa yake tarawa ba , akwai su… Kullum zuwa suke da yawa….. An tarasu tun ba’asan amfanin kuɗi ba , tashi yayi ya ganshi cikin arziƙi tunda ya buɗe idonshi duniya kuɗi ya fara gani ba labarinsu yaji ba. Tunda Mai gidanmu ya girma suma kuɗin san ganinshi sukeyi , da kansu suke zuwa domin suma kansu sun san shine zai yaɗasu domin suje inda ba’a da labarinsu. Yana nema ne domin al ‘umma kuma nemanshi yanayin shi ne domin ya gina rayuwar duk wanda yake da rabo a ciki. Akan Mai gida gaba ɗayanmu zamu iya sadaukar da rayuwarmu dan nema masa farin ciki. Ya ƙarasa maganar yana dukan ƙirjinshi bisa gaskiyar shi. Mu bazamu yadda ba , haka kuma bazamu lamunta ba , idan ke baki san darajarshi ba mu mun sani , idan bashi da amfani a wurinki mu yana dashi a wurinmu , idan kin gaji mu bamu gaji ba. Ya ƙarasa maganar suna maida Dikko saman gado. Duk ma wani mai cewa Mai gidanmu bashida mutunci ko ɗan duniya ne ko ya raina mutane koma dai miye mu yana da kyakkyawan hali a wurinmu. Mune muka sanshi muka zauna dashi muka kuma san ɗabi’unshi dan haka mune zamu faɗi ko waye shi…… Yayi maganar yana kaima bango naushi da hannunshi. {{ yadda yayi maganar hasashe na ya bani da Inna yake… }}
Duƙawa yayi tare da dafa gefen allon gaban Dikko yana ci gaba da cewa. Me kike so ? Idan soyayyar ce an baki , kuɗi ne damuwarki ? Suma an baki. Sultana me kike nema ne wai …..? Ko har yanzu kuɗirin fansa bai goge ba ? Rungume Dikko yayi ya ƙara yawan kukanshi yana cewa bawan Allah da wannan dalilin ya ƙwammaci ƙare rayuwarshi ba aure. Yana sanki amma yarinta da rashin tunani ya hana ki fahimta. Iya ruwa iya fidda kai……… Ko wae’…iya allonshi ya wanke. Gaki ga Mai gida tunani da samun mafita yana wurinki , dabara da sanin sirrin rami ya rage ga mai shiga rijiya. Daga haka bai sake magana ba ya riƙe hannun Dikko cikin soyayya yana mishi kallo mai nuni da tausayi , janshi aka suka bar ɗakin Ashiru yana ci gaba da kuka.
Kamar wata jaka haka nabi bayansu da kallo har suka gama fita daga cikin ɗakin. Goge hawayen daya taru a fuskata nayi. Na maida kallona inda Dikko yake kwance yana bacci. Tou ya haka ? Meya faru Dikko ya sake warwarewa ? Ko wayau yayi min daya bani labari cewa ya warke ? Ko yayi tunanin ni bazan iya ci gaba da zama dashi ba idan bai warke ba ? Labarin daya bani G R A a ɗakinshi ya tunomin da yacemin…..
_Naso naga Al ‘ Ameen dan naso zanyi magana dashi amma hakan bai yuwu ba. Shi Mustaphan yayi ma Ashiru jagoranci zuwa inda suka binne tsafe²nsu , komai Ashiru yayi saida suka gama komai lunfashi na ya dawo , tunda nake ban taɓajin irin wannan tashin hankali ba wai an shanyemin numfashi kiji wani masifa ? Hmmm Yazeed kuwa Ashiru yaci ubanshi kuma shine ya maido Abbakar company duk bansan anyi ba._
Dogon nazari nayi , na hasko duk maganganunshi na baya. Tabbas a maganar Dikko akwai lauje cikin naɗi. Wato ni zaima ƙarya ? Dani da ku masu karatu idan baku manta ba , ni yacemin wai yaje yayi jinya har na tsawon shekarun da nayi ina zaune a gidan Inna , ku kuma tuno. Tou ya akayi ya saki Jiddah bayan shi baisan inda kanshi yake ba tun daga ranar da ni nabar gidanshi naje gidan Inna ? Ya akayi takebinshi har Abuja ? Me yasa yayi min ƙarya cewa dawowarshi kenan yazo ya tafi dani a ranar daya aiko Abbakar ya kawomin waya ? Bayan tafiyar Abbakar kuma Ummar yazo da Umar ya tafi kuma shi Dikkon yazo da kanshi ! To me gaskiya ? Ni miye matsayi na a wurin shi ? Meya ɗaukeni ne ? Me yake nufi dani ? Tabbas duk yadda akayi maganar Inna itace gaskiya Dikko baya so na……… Mai gemun yaudara na faɗa cikin hayaniya ina cewa yau saina bar maka gidanka kaje ka samu daƙiƙiyar da zata zauna dakai , ka raina mutane ni nafi ƙarfin kai ka rainani…… Wai ni zaka faɗawa ka ɗaure kanka da wayar wuta ni zaka ba labarin “yan sfires {{ Express }}….? Fuuuu na fice daga ɗakin na koma ɗakina. Wayata kawai na ɗauka da makullin mota na fice…..
Da gudu na fito waje ina kuka har wurin mota ta , ina shiga mota Ashiru ya iso wurin yace ina zakije ne ? Cikin ɓacin rai na nunashi da makulli cewa zanje gidan Babana. Ai kasan nima Babana da Mamana suka haifeni ko ? Yadda iyayen Dikko sukeji dashi kuma suke ƙaunarshi nima Babana haka yake so na , yadda yakeji shima ɗa ne a gidansu nima ɗiyace na nuna kaina , yadda aka haifeshi nima haifata akayi ba ta sama na faɗo ba , har yanzu hannu na yana kan ƙirjina ina nuna kaina. Goge hawaye nayi da hannun haggu na ina ci gaba da cewa duka׳ kullum Dikko saiya dakeni doke²n shine soyayyar da kake iƙirarin yana nunamin wacce har kake min gori akan ta ? An baki soyayya da kuɗi. Cikin marainiyar murya nace shin baka tambayeni me nake nema ba ? Saki nake buƙata daga wurin Mai gidanku. Bana san ɗaya ko biyu a rubutoshi duka a aiko dashi a gidanmu na ƙarasa maganar ina karta makullin motar a jikin sitiyari , zana makullin nayi a goshina ina ci gaba da cewa Sultana bata ɗaukar fansa kuma ba ƙudirin wata fansa zamana da Dikko , kafin insan Dikko inayin rayuwa dan mun rabu yanzu kuma bazai sa in mutu ba , nayi maganar nima ina dukan sitiyari cikin ɓacin rai. Nuna Ashiru nayi da makulli sannan na cije leɓina na ƙasa na tashi mota ina kallonshi….. Riƙe murfin motar yayi yana cewa idan dai kinga kin fita a gidan nan sai idan bana numfashi…..
Ko kayi rayuwa ko ka mutu bai shafeni ba , nasan dai ni na gama magana kuma tunda na yanke hunkunci magana ya ƙare. Ba tare daya kalleni ba yace can baya na taɓa faɗa miki kiyi haƙuri idan baki manta ba , yauma shine nake daɗa baki Hajiya , bayanshi banda abinda zan iya baki a duniyar nan , tunda kike a duniya kin taɓajin wanda yace rashin haƙuri ya sa yacimma nasara ne ? Saidai kiji ance haƙurinta yasa ta cimma nasara , ba wanda zaiyi haƙuri yaji nadamar yinshi saidai nadama takan zo yayin daka gagara haƙuri.
Ban faɗa miki maganganun nan ba dan kiyi zuciya ba , raina ne yaimin babu daɗi. Baki gaji fushi da gudu daga gidan aure ba dan wani ƙalilin abu. Tarbiyya kika gada , Babanki idan yana nan bazai so yaga kinyi yaji ko kina cewa a sakeki ko faɗa da miji. Kuma da yana raye ko kin tafi zai dawo dake bayan yayi miki faɗa da ƙara nuna miki matsayi da kuma martabar miji , dika² ma miye abun fushi ? Ya tambayeni yana murmushin ƙarfin hali , yaci gaba da cewa ai anyi wanda yafi wannan kuma anyi haƙuri sai ɗan wannan Hajiya…..? Wanda bai dakeki ba bai zageki ba ? Ki ƙara haƙuri tunda an hau tudu ai gangarewar baya wahala , kalli ya nunomin hoton Papi a wayarshi , ji yanayin farin ciki kin ajiye ɗan digu²n Papi ina zakije ki barshi ne ? So kike yayi kukan rashin uwa bayan kina raye ? Rayuwar aure da kika ganta gaba ɗayanta haƙuri ne a cikinta , idan akayi haƙuri sai a samu mafita , kiyi haƙuri sai Allah ya baki ladar haƙurin , kibi mijin ki zauna lafiya kiyi masa biyayya saiki samu albarkar rayuwa. Ki nemi gafararsa sai ubangiji ya gafarta miki , fito ki koma dan Allah ki kwantar da hankalin mijinki kema sai naki hankalin ya kwanta. Ya ƙarasa maganar da yanayin tausayi….. Yana ci gaba da cewa ba’asan maci tuwo ba sai miya ya ƙare , masha ruwa magirbi karki biye fushin zuciya kiyi abinda zai jawo miki damuwa. Da yaji da tambayar sakin aure sai “yan gidan da basu da tarbiya , ke ko kina da tarbiya da ɗa’a kiyi haƙuri ki koma idan har kika tafi zaki naƙasa matsayinki da kuma mutuncinki. Kiba Mai gida haƙuri zai haƙura kuma bazaiyi fushi ba danshi mutum ne mai mantawa da damuwa , a inda akayi mishi yayi faɗa ya gama da wurin. Yana da zuciya amma yana da ba abun duniya baya….. Fita ki nuna masa ke ɗin “yar Babanki ce….. Ki basa haƙuri domin ya ƙara tabbatarwa keɗin mai tarbiyace , ki nemi gafararshi sai yayi alfahari da iyayenki domin sune suka koya miki tarbiyar bawa miji haƙuri.
Ko ba komai naji daɗi daya kira iyayena da masu tarbiya duk dai nasan za’ace niɗin eyar ɗan caca ne , ci gaba yayi da magiya yana bani haƙuri , kashe motar nayi tare da zare makullin na wuce banyi magana ba , ɗakina na koma na zauna gefen gado. Yayin da wani sashe na zuciyata yake cemin inyi haƙuri kamar yadda Ashiru yace , kuma in bawa Dikko haƙuri , ba ruwana da wani ciwonshi idan yayi aljannunshi idan ya gaji zai sauka , ya warke ko bai warke ba , ba damuwarki bane ba Sultana , abinda ya hanashi zuwa ya dawo dake tuni shima bai dameki ba , lokacin da ya saki Jiddah da binshi da takeyi dashi da ita da kowa ma can su ta matsemawa , kiyi tunani ki rufawa kanki asiri ki dawo daga rakiyar shaiɗan tun kafin duniya tai gwanjonki.
Tunda ta gama waya da Sultana take ta ɓaɓɓarka zagi , wayar Mai gilashi ta kira amma kafirawan company suka ce mata a kashe yake. Dan haka ta bugi mota tayi gidanta , ba yabo ba fallasa Mai gilashi ta tarbi Sharifa kuma bata , bata izinin shiga ɗaki ba. Haka kuma babu maraba bare kuma sannu da zuwa. Da yanayin tsinkuwa Sharifa tace Mai gilas an fa samu matsala , dakel ta kalli Sharifa tare da tambayarta meke faruwa ne ? Mu shiga daga ciki cewar ita Sharifa , Mai gilashi tace ba buƙatar sirri a ƙuryar ɗaki , magana dake a fili da ɓoye duk iri ɗaya ne. Da mutum yayi maganar sirri dake gara yaje B B C ya faɗa kila idan anci sa’a a ranar wani bai kamo tashar ba. Faɗi abinda ke tafe dake ko na iya baki shawara. Mai gilashi ni a gwadamin iskanci ne ? A , a , waye ya isa ya nunawa na rigingine hasken farin wata ? Cewar Mai gilashi. Sharifa tace to ni matar D ‘ K ta zaga , ta faɗamin magana , tayimin gori ta wulaƙantani ta muzantani ta tozartani sannan kuma ta tonamin asiri…….
Cikin ko in kula tace duk me yayi zafi haka ne ? Zama kusa da ita Sharifa tayi cewa kwana biyu kenan bama waya bama cht kuma bana ganinshi , Mai gilashi tace kila a tunaninta yana wurinki ne ko ? Cikin rashin fahimta Sharifa tace kamar ya ? Riƙe bakinta tayi da sauri tare da cewa rufama kanki asiri kar aji mutuwar sarki bakinki Ade…. Inji Mai gilas.
Sharifa tace kamar ya haka kuma ? Me zaki ɓoyemin ne bayan kinsan duk karatun iri ɗaya. Mai gilashi tace aini kin daina shawara dani faɗin gaskiya kuma zamanin nan yayi wuya , ina iya faɗa miki kije kiyi ta tallar terere dani , dan girman Allah Mai gilas faɗamin , Mai gilas tace gaskiya Sharifa ni inajin tsoro , dafa Mai gilashi Sharifa tayi tare da cewa idan dai baki faɗamin ba duk yadda tarenmu take tou lallai ƙullu yaci amanar koko , ɗan motsa kanta tayi alamar ta sanar da ita tare da cewa na baki dama kuma nayi miki alƙwari babu wanda zaiji ba wanda zai san anyi.
Mai gilashi tace:• shin bana faɗa miki kina da kishiyoyi ba ? Wanda suke ta harar Dikko a waje ba ? Sharifa tace kin faɗa , shin tunda kike ke Dikko ya taɓa² koda hannunki ne ? Ai bama ya kallo na , tou lallai cikin hijabi kike je mishi zance , Sharifa tace ey wallahi , kina zama kusa dashi ko a , a ? Shiru Sharifa tayi , Mai gilashi tace tou lallai nesa kukeyi da juna ta faɗa tana dariya tare da nuna Sharifa da ɗan yatsa , kallonta Sharifa tayi cewa ai babu ma ta yadda za’ayi ni na zauna kusa dashi , Mai gilashi tace da irin wannan baƙauyar soyayyar zaku cinma nasara har a kai ga matakin aure ? Miƙewa Mai gilashi tayi ta kalli Sharifa sosai sannan tace duk dabbar da tayi kuka tana da dalilin da yasa ta koka , yayin da wasu kan koka lokacin da suke buƙatar abinci , wasu kuma sukanyi kuka yayin da suka ƙoshi ne , kare yakanyi haushi yayin da rigimarshi ta motsa , duk wanda kika gani kwance kila yana rashin lafiya ne ko kuma yana da ƙatotuwar damuwa , haka take ga duk namiji daya tirki ƙarin aure…..
Dalili kuwa shine :• duk gero sunanshi gero. Yayin da aka sarrafashi zai tashi daga sunan gero ya koma wani suna na daban , misali , za’a sarrafashi zai zama fura , kunun kanwa , kunun tsamiya , wainar gero , tuwon gero , gumba , farin kunu , kunun zaƙi ke har danbun gero na gani kuma naci shi a bakina…. Amma duk miye silar zamar da duk wannan abubuwan dana lissafo ? Gero ne ! Shine duk aka sarrafa yayi duk abubuwan nan dana faɗa , tou haka take ga duk namijin daya baro gidanshi. Wasu mazajen zasu fito ne cikin soyayya da rashin jin daɗin sunyi nisa da ilayinsu , me yasa sukejin haka ? Kula , soyayya kissa kisisina kwarkwasa iya fira mai daɗi uwa uba kuma kindai gane ba……..? Matansu zasu ɗauke musu tunani su kasance sunayin kewarsu da wa’ancan abubuwan dana lissafo har suje su dawo zuciyarsu da ƙwalwarsu baya barinsu su kalli wasu matan , ko kuma suyi tunanin kowa sai nasu , yana kasuwa ko office amma lissafinshi yana gida , burinshi ya tashi daga kasuwa ya koma dan kasancewa da shi wannan farin cikin dai. Dan haka zasu koma gida cikin farin ciki a taresu da soyayya kuma…….. Kinga namiji ne ba , amma hikimar mace ta juyashi yasa ya zama wani daban..
Wasu mazan kuma zasu fito gidansu da ɓacin rai. Su fito kasuwa ko wata ma’aikata , idan ogane a wurin aikin abu ƙalilan zakayi ya ɗaga murya , ɓacin ran gida ya shafeka wanda kai bakaji baka kuma gani ba , idan ɗan sanda ko alƙali kila ma idan makuyi sa’a ba yace ku duk ɗin ayi gidan yari daku , tou a fara faɗo mishi karatun da shi kanshi baida lokacin da zai tsaya sauraronku ko yayi lokacin fitar da haƙƙin mai gaskiya dan haka zaice da mai ƙarar da wanda ake ƙarar duk a haɗaku a kaiku magarƙama. Shima mace ce ta juya mishi lissafi da kuma tunani , mazan haka suke sukan canja ne daga horon da matayensu suka basu , mai tunani ya zama lurasi , lusarin kuma ya zama jarumi. Ya danganta dai da horon da aka bashi daga gida , Sharifa anshe goruba a hannun kuturu ba abu mai wuya bane , tunda har ya ƙetaro iyakar matarshi ya fito sai ki bari matan waje su duma mishi wa² ? Shikenan ke kin haƙuri ? Ki bar musu ? Ke bakya da buƙata ? Sharifa tace ina da… Tou Yusra Jiddah da wata banzar yarinya dana manta sunanta duk kiyi ƙoƙari ki rabasu da Dikko , {{ banzar yarinya da ita Mai gilashi ke nufi itace Sharifa , }} taci gaba da cewa idan kin shirya kin kuma shirya ɗaukar huɗubata bisimillah , tashi sharifa tayi ta matsa kusa da Mai gilas kunneta ta kama tayi mata raɗa bayan sunyi alƙawari da kuma yarjejeniyar amana. Sharifa ta yadda ta kuma ansa , ta yadda da huɗubar *MAI GLASS…* abinda ta faɗa mata zamuji shi idan taje wurin Dikko ne. Dariya Mai gilashi tayi tana kallon Sharifa aka wani tafa , Mai gilas tace haka suke ai mazan iri ɗaya ne , kije ki jaraba. Wannan farashin da zakiyi tukuici sai buƙata ya biya…..
Bugu:• bugun bala’e sukayi ma Amisty bayan sunyi nasarar cafke banza. Kuma dukan bawai irin na yara ba ko na susar jiki ba. Basu bigeta da wasa ba duka na tashin hankali sukayi mata , dukan da idan dai akayi ma mutum irinshi to sai mutuwa. Tafiya babu dawowa. Tunda sukaji zancen kuɗi sukaje wurin suka kafa tarko , duk wani da zai shiga ko fita a gaban idonsu. In banda wawanci da rashin lissafi kuɗin nan wai suna cikin motar Amisty idan taje wai inda zataje sai ta canja da kuɗin ƙasar tayi hidimominta. Haka sukayi mata duka kamar wanda ya tun kari fadar shugaban ƙasa rungume da bindiga…. Ita kuma bayan ta tabbatar kowa yaje ya kwanta ta sulale dan ta gudu saboda bata yadda kowa ya kwana ɗaki ɗaya da wani ba. Ƙarya tayi musu wai zatayi baƙo shine taga dare yayi zata wani ɓace abunta. Tafa ci ƙaniyarta yadda tunani baya zato. Suka ɗauke motar da kuɗin suka barta nan zube kamar asarar tsakar dare.
Har gari ya waye ban samu nayi wani baccin kirki ba , haka kuma na kasa zuwa ɗakinshi , tsoro da fargaba kawai ke damu na , sai zantukan Ashiru dake tayimin luguden san zaman lafiya a zuciyata. Wannan dalili shine ya hanani san zuwa makaranta naji ni kamar wata mara lafiya. Ganin har 1 saura yasa na tafi ɗakinshi a tsorace , da sallama na shiga yana fitowa daga toilet ran nan nashi a haƙe fuskar nan tayi kalar ban tsoro dasa mutum ya shiga cikin yanayin firgicewa , ɗan rakuɓewa nayi cikin rawar murya nace barka da safiya , baimin magana ba bai kuma kalleni ba ya ɗauki wayoyinshi ya nufoni dan fita daga ɗakin….. Cike da tsoro na sake cewa Dikko ina kwana , ke…….. Ya faɗa tare da yankamin wani irin firgitaccen mari saida na juya naje jikin bango dakel na haɗiye yawu lokaci guda zufa ya tsatstsafomin a fuska cikina ya juya yayi wani irin zakuɗa a tsorace na kalleshi , da ɓacin rai ya tambayeni wannan marin meya bayyana miki……?
Cikin kuka da marainiyar murya nace har yanzu jikinka da ƙwari , yace to ina nan a yadda nake , ban sauya ba ban kuma tashi a yadda kika sanni ba , dama idan baki manta ba na faɗa miki. Tou yauma na sake maimaitawa idan zaki kiyayi fushina tou ki kiyaye sai ki zauna lafiya , na warke ko ban samu sauƙi ba wannan bai shafeki ba saboda daga matar gida baki kau ba , ya nuna da hannunshi. Rayuwa da ƙaddara abokan juna ne , komai yana da ranar tashi daga aiki kama daga kifin gwangwani har zuwa mu “yan adam , kin gane ba ? Jeki…….. Ya nunamin , tafi ya nunamin hanyar fita , ƙara yawan kukana nayi na taho daga inda nake na shige jikinshi ina cewa na bari Dikko na faɗa maganar ina ɗagowa dan kallon idonshi , sassauta murya yayi yana cewa bakijin magana , iskancin ki kullum gaba yakeyi , wai nine kike faɗa zaki zane ? Haba An mata….? Kayi haƙuri bazan ƙara ba , tou me nayi miki kika ɗaureni bayan ni ba mahaukaci ba. Ko abokin wasanki ne ni ? Ya tambayeni yana ɗagoni daga jikinshi , saida nayi shashshekar kuka nace bana so kana yawon dare ne , sai kuma ki ɗaureni ? Wannan wane irin hukuncin hauka ne ? Ai bana so kana fita na ƙarasa maganar ina komawa jikinshi. Murmushi yayi kaɗan a sakace yace An mata……… Ya ƙarasa maganar yana rumgumeni sosai. Cikin dariya yace wai wane mai bahaggon tunanin ne ya baki wannan shawarar ne ? Ɗagoni yayi kowa yana kallon idon kowa yace sai kawai tace miki idan kika ɗaureni zan daina fita ne ehem. Yayi maganar yana shan idanuwanshi. Suna shanyewa a hankali tare da murza su da salon duniyanci. A kasalance na koma na sake kwanciya , dariya yayi da murya mai kama zuciya ya ɗaukeni yaje ya kwantar dani saman gado , saida ya lulluɓeni ya sumbaceni yace jirani ina dawowa yanxu. Yayi maganar yana fita daga ɗakin……..
Bayan sati 1.
Mijin Halimatu dai har yanzu baida lafiya. Jinya har ta kaisu asibiti zugar ƙawayenta kuma babu wanda ya bita sai Hadiza. Da ita ake yini akeyin komai sai dare suke dawowa gida ƙannen shi Abdul in maza suke kwana dashi. Da Halimatu ta tambayi sauran ƙawayenta me yasa basa zuwa cewa sukayi mazajensu basu yadda ba…..
Har sati ya cinye Yazeed bai zo ba kuma bayayin waya da Jiddah. Shiru kuma har yanzu baiyi maganar turo magabatanshi ba tunda ya tafi waccan ranar sai yau yazo , duk an ɗaɗɗaure mishi jiki da tsumma an sagale hannunshi da igiya an sargafa igiyar a wuyanshi , wai Jiddah ta bashi mamaki shine dan ta tura mishi wata banzar 5million zata turo mishi ɓarayi suzo su kashe shi su ansar mata kuɗinta. Ai ba dole² yasa ta bashi ba , basai ta turo a kasheshi ba , tou ya basu kuɗin ta daina kiranshi kar yayi mata rashin mutunci , shi da ta ganshi duk cikar garin katsina babu ɗan iska kamarshi. Kuka Jidda ta farayi ita wallahi bata tura kowa ba , Yazeed yace ƙarya zaiyi mata ne ? Bafa a wata banzar miliyan biyar inta ya fara riƙe kuɗi ba. Me yasa a lokacin can da bai santa ba ba’aje an dakeshi ba ? Sai akan ita data bashi ne ? Tou ya fasa auren taje tayi da wani.
Jiddah ta fara wallahi². Yazeed yace shi tama wani daina mishi kukan makirci yasan sharri irin na mata , haka taita bawa Yazeed haƙuri dakel ta shawo kanshi a yadda ya nuna kenan , saida ya sake buɗe fili akayi danbe Jiddah ta tura mishi miliyan biyu tace ta ba malamin ta anayin aiki , dakel Yazeed ya yadda ya anshi biyu , kuma ya tabbatar mata da kuɗin danbe ne ta biya , shi baya wani ra’ayi yana mata yayyafi ne dai dan ta rayu karta mutu. Tayi ma Dikko waya ya ƙaro wasu kuɗin……
Dady kuwa ya bugu iya bugu a yadda yayi fentin gida da sabbin filawowi , Umar ɗan iska ne kuma baƙin mugu , da Dady yasa aka sauke fentina yace ya bada kuɗin ma’aikata zaiji da komai , ya anshi kuɗi masu yawan gaske a wurin Dady hada na toshiyar baki , Umar kuwa wajen gida kawai yasa aka gyara sauran fenti yaci kasuwa…
Duk satin nan Mai madubi bataje makaranta ba , naso zuwa gidanta Mai gida D ‘ K ya hanani , makaranta ma shine yake kaini yake kuma ɗaukoni , ga wayar ta idan an kira ba’a samu , sai na haƙura kawai.
Har yanzu Dikko bai cire wayarshi a jirgi ba , kuma satin nan ya bigeshi bai fita , ko gidansu rabon da yaje tun ranar daya kwantar dani a gado yaje. Kuma ya taho da Papi saboda Nabeela ta tare gidanta. Banje ba , abinda yasa kuma saboda ciki shi yasa ya hanani zuwa.
Sharifa da Aunty Bilki ganin ana neman a buga musu game over yasa ta samu Dady akan yayi ma Dikko magana yaje wurin Sharifa , ya kama waya ya rufe sati 1 kenan da kusan kwana 2 basa waya kuma basa haɗuwa. Tadaiyi “yar barikinta a gaban mijinta irin tamu ta mata , Dady kuma ya kira Dikko yace duk abinda yake yau yaje ya haɗu da Sharifa. Shi Dady gani yakeyi ita Aunty Bilki tafi Momy mutunci tunda tana san “yan uwanshi har take tunatar dashi akansu.
Wani irin ihu Dady yayi tare da zubewa ƙasa somamme. Yayyen Hafsa suka rufa mata da duka wanda sune sukayi tsaye wurin nemota. Can abuja suka kamo “yar iska a wata asibiti wai tana jinyar Amisty tana so ta dawo taji ina kuɗi suke ? Shine suka tattaro su dukansu da Amisty da ita Hafsa….. Shine fa kawai ya wani some dan Hafsaf fa kawai ta tabbatar mishi da ɓarayi sun kwashe kuɗi , daga an faɗa mishi shine kawai zai wani zama mataccen bakin maƙabarta………????
*JAMILA MUSA…*
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN…*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa…
*JAMILA MUSA…*
*SAI NA AURI D ‘ K*
🅿 —— 8
Saida sukayi mata lullusar fitar hayyaci sannan suka shafawa Dady ruwa ya dawo. Kamar ƙaramin yaro haka ya riƙa gumza , muuuuu , tutu² sai kace sabuwar mota ta haɗu da tsohon inji. Dady kayi haƙuri ka daina kuka , saida ya gama kallonsu sannan ya kalli Hafsa yace shin an kamo ɓarayin ne ? Suka ce a , a , luuuu Dady ya sake komawa suma. Haka sukayi ta dawo dashi daya dawo sai yace an kamosu ne ? Amma da ance masa a , a , sai ya sake somewa. A na ƙarshen ne ya wani babbanƙare ya riƙe yaƙi lanƙwasuwa baya gaba kuma yaƙi yayi baya kamar aljannun mata sun taso. Bayan ya tabbatar musu da cewa kada wanda ya sake dawo dashi idan har ba’a kamo ɓarayin nan ba. Babban ɗanshi yace Dady idan ba’a gansu ba fa ? A hankali ya maida kanshi ƙasa ya lumshe idanuwanshi cikin tashin hankali sannan yace ku barni kawai in mutu…..
Cike da farin ciki Yazeed ya isa majalisarsu. A mota ya warware tsumman daya ɗaɗɗaure jikinshi yana dariyar ƙeta. Lallai Jiddah muguwar daƙiƙiya ce. Wato ita har ga Allah ma ta yadda anje anyi mishi dukan ? Ballagar mace uwarki tayi asarar aihuwa. Fita yayi daga cikin motar haka ya shiga cikin da’irar abokansu yaci gaba da fallasa Jiddah , wai wasu zawarun ballagazu ne. A kyauta yake shan iska babu wani damuwa. itama kanta a kame take kamar barden goyon daya yini baisha nono ba , da yaji gari yayi mishi zafi can yake tafiya yawon honey time. A can dai yake zubda ƙura ya dawo gida , ga kuma kuɗi kwance a account , ya nuna kwanciya da hannun shi yana ci gaba da cewa lallai Yazeedu babbar ƙaddarar mata ne ni. Ɗan yatsina fuska yayi sannan yaci gaba da cewa bafa laifi tana barbaɗa wuta a filin wasa D ‘ K ya kowa mata doguwar tafiya. D ‘ K…? Hmmm Dikko duniya sai Allah , ya faɗa yana riƙe haɓarshi da yanayin mamaki ya ƙurawa wuri ɗaya ido alamar tunani.
Tambayarshi akayi ina ya samo zawara a arha haka ? Dariya yayi sosai tare da jinjina kanshi yace matar D ‘ K da suka rabu. Cikin dariya yaci gaba da cewa wai dan uwar biko shi D ‘ Kn yake bikonta dan ta ɗauki kanta alalan gero. Hmmm lallai iska tana wahalar da mai kayan kara , idan dai D ‘ K ne cikin ruwan sanyi zai kasheta bata san iskancinshi ba aradu labarinshi takeji. Tou kai meya haɗa ka da ita ne ? Waye ma ya sanar ma angulu a masai…… Ya ƙarasa yana ƙara gaggaɓewa da dariyar fita addini.
Bayan wani lokaci ya nuna kanshi yace wai ni ? Nine zan aureta , in banda haukar mata da rashin tunani ni ? Wai ni Yazeedu nine zan aureta ? Gaskiya bata da lissafin rayuwa. In banda abunta bata duba can²nta ne ? Idan na aureta uwar me zan bata ? Filawa ai tafi kyau da gidan masu kuɗi , shanyar dusa kuma da kauɗar bushashen tuwo wannan kuma ai sai gidan talaka. Zanyi ta zuwa dai ina karantawa inyi gaba , wata irin azzalimar dariya ya sakeyi yana cewa bata san itama ta gidan neman hanyar tsira takeyi amma bata samu sa’a ba , hahahahaha kai yarinya bakiyi ma cikinki da gangar jikinki adalci ba , zo zo² zoki mana idan dai nine ni naci uwar ɗan tasha , dan bana tunanin duk cikar faɗin birnin jahar katsina kawai irina , banda mutunci kuma na tabbatar da cewa tantiri iri na a duk faɗin yankin katsina bafa za’a taɓa samu ba. Dan babu tantirin ɗan iska kamata , idan dai kinajin wasa ki tambayi Dikko ya baki labarina.
Fat , Fat , ² haka lumfashin Amisty ke halbawa tsakanin rayuwa da mutuwa. Yau duk abokan tashar nata babu wanda yake ɗakin da sunan jinyarta. Uwa ko uba nata kuma ? Basu da labarin halin da take ciki. Tunda ko tana da lafiyarta basa ganinta basa kuma jin labarinta , a gari ɗaya ake amma kowa yana nashi matsugunin. Wani bushashen ɗan sanda aka aje wanda koke mace idan baki da yunwa kina iya bashi kashin bala’e. Wai shine aka ajiye dan ya kula da Amisty. Idan ta dawo hayyacin ta , ta nemo musu inda takai musu kuɗin Baba. Likita ne ya shigo tare da malaman jinya bayan yayi ɗan abinda zaiyi aka taimaka ma tafiyar numfashin nata da iskar bature. {{ Oxygen }}.
Kallon agogon dake ɗaure jikin tsintsiyar hannuna nayi sannan na kalli inda yake tsaye jikin madubi yana murza hula , ta cikin madubin ya kalleni so ɗaya sannan yaci gaba da abinda ya shafeshi. Bakin ƙofa na koma na tsaya ina cewa gaskiya ba inda zakaje na ƙarasa maganar kamar zanyi kuka. Juyowa yayi tare da jingina da jikin madubi ya dafa hannunshi ta baya cewa. Nace miki bazan daɗe ba , tou kuma tunda kasan baka daɗewa ai ba buƙatar fitar ko…? A hankali ya fara tahowa yana cewa tou ki hanani fita da ƙafafuwa na in gani mana. Kwanciya nayi ƙasa a bakin ƙofa kaina na kallon sama na miƙe ƙafafuwana da hannuwana nayi irin kwanciyar gawa. Cikin kuka nace shikenan ka tsallake kabarina Dikko ka wuce. Da sauri ya maida ƙafarshi baya daya ɗago da niyar tsalleki ne ya wuce. Cike da shagwaɓaɓɓiyar muryarshi yace haba An mata wai miye kike haka dan Allah ? Ban tashi ba kuma ban daina kallonshi ba nace ba kace sai ka fita ba ? Kai da ƙafafuwan ka ? Tou gani nan kwance ka tsalle gawata kawai kaje abunka na ƙarasa maganar ina zarge hannayena a ƙirjina na rufe idanuwana. {{ hmm taf aradu idan wani namijin ne ba kabarinki ba ko makomarki ya gani sai yayi abinda yasa kanshi can ke ta matse mawa . }}
Cire cingom in bakinshi yayi yana wasa dashi a hannun shi , bayan wani lokaci kuma yayi ɗan latse² a waya ya kara a kunnenshi. Saida na cikin wayar yayi magana Dikko yace Abbakar kuje , ya ƙarasa maganar yana ɗan shan idanuwan shi da suka canja launi. Ey ya faɗa yana komawa ciki. A , a kawai dai na fasa fita ne , kaina yanamin ciwo ya faɗa a dai² lokacin da yake zama gefen gado yana nuna kan nashi da yanayin damuwa. Ey , yayi bacci tun ɗazu. Babu damuwa saida safe. Ya faɗa yana ajiye wayar , ɗayan wayarshi ya ɗauka ya cireta a jirgi , data ya buɗe tare da antaya duniyar yanar gizo.
Saida saƙonni suka fara shigowa ya ajiye wayar ya tashi yana rage kayan jikinshi. Tasowa nayi daga inda nake kwance na matsa inda yake nace yi haƙuri. Ba tare daya kalleni ba yace kawai ya wuce yayi maganar yana komawa inda ya ajiye wayoyinshi ya ɗauka ya koma palo , ƙasa² nayi dariya bayan ya fita a zuciyata nace shegiya ni , na ƙarasa maganar ina kwanciya a gado na ɗauki wayata na fara kiran Hajiya Mai gilashi. Wayarta a kashe har yanzu lallai duk yadda za,ayi in Allah ya yadda sai naje gidanta idan Allah ya kaimu. Allah dai yasa ya barni inje , wani sashi na zuciyata yace kawai cewa zakiyi ya kaiki , wannan shine gaskiyar magana , saukowa nayi daga saman gadon na fita palo inda yake.
Ya toshe ɗayan kunnenshi da abun sauraron magana , ya ƙurawa waya ido yana murmushi. Duk maganar da nayi kwata² ma bayajina sam² , zagawa nayi ta baya da niyar in ɗan riƙeshin nan irin idan mata suka tashi labbatar namiji idan suna san wani abu daga gareshi. Amma kafin in riƙeshi sai me…? Wani irin ruɗaɗɗen ihu nayi tare da faɗar da wayar daga hannunshi. A firgice ya juyo ya kalleni sannan ya tashi da sauri zai ɗauki wayarshi a lokacin har na zagoyo na rigashi ɗauka , bani wayata yayi maganar ranshi a matuƙar ɓace , kyarma jikina ya farayi saboda na tsorata da irin kallon da yakemin. Dakewa nayi tare da cewa idan fa naƙi bayarwa ? Sai in kashe ki………… Ya faɗa yana nuna shaƙewa da hannunshi saman wuyanshi , cike da tsantsar ɓacin rai nace ai yau nice zan kashe ka. Nayi maganar idona yana kallon ƙasa. Wani irin wulaƙantaccen kallo yayi min tare da nuna kanshi nine zaki kashen ? Kafin inyi magana Papy ya shigo yana kuka , ihun da nayi ne ya tasoshi daga koma ina yake yana bacci , cike da ɓacin rai Dikko ya jinjina kanshi ya matsa yaja hannunshi suka fita.
Wuri na samu na zauna na shiga binciken waya. A raina kuma addu’a nakeyi Allah yasa Papy yaita kuka ya hanashi dawowa da wuri , dan abinda na fahimta baya so yanayin wani abu wanda bai kamata ba idan ɗan shi yana gidan. Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un , wata irin yamutsa kaina yayi da sauri na rufe idanuwana dan irin ƙazantar dana gani , tunda nake da Dikko duniya bai taɓa abinda naji na tsaneshi ba sai yau , wayyo Allahna ? Mayun mata wai ina ruwanku da mijina ne ? Kunzo kun daddaɓeshi sai kace ƙuda ya samu ruɓaɓɓen nama. Ga kira waya sai shigowa yake ba ƙaƙƙautawa , saƙonni sai kokawa sukeyi wurin shigowa , jikina na kyarma idona cike da hawaye na fara neman number Sharifa , dakel na gano ta ɗan iska wai “yar uwarshi ya rubuta a jikin numberta , kam bala’e wai duk ina , ina wannan iskanci ya faru ? Da wata ɓeranyar yarinya shegiya zata girmeni baifi da shekaru biyu zuwa 3 ba , ta ciko mishi saƙon nata itama da ɗanyayen kalamai daɗaɗa , sanyaya , Sharifa kuma ta rubuto mishi cewa ni na kirata na zageta , nayi mata gori wai ni injini ni Sultana wai nice nace wa Sharifa ita karuwan Dikkon ne , a taƙaice dai ita Yusra kaf a cikin kwaratan itace ta saman iska , kaf babu feƙaƙen ɗan tasha na sama a wayar nan sama da ita , guguwar “yar iska ce , dan kalamanta data faɗa tana tattaɓa wasu sansa na jikinta nida kunya ta haifa na rantse da girman Allah ba a baki ba a rubuce duniya ni bana iya rubutawa bare kuma azo fagen in furta. Karuwai…..?׳ hmmm karuwai na sha’aninsu idan suka samu mazajen ballagazanzun mata , a hayaƙe ya dawo saida ya wanwanka min mari ya anshi wayarshi. Cike da rashin tsoro nace kadaiji kunya kuma kayi asara daka kallar da idonka tsiranci haram , naji kunyar kuma naje na kalla haram ɗin naki ne ko nata ? Banyi magana ba na nufi hanyar fita , har na fita zuciyata ta hayaƙoni na dawo ,
Nima dai a daren nan nayi ɗan ƙaramin hauka , haka na rufe idona naci gaba da zage² ba shi nake zagi ba su Yusra nake ta ɓaɓɓarkawa zagi , keda ke gidanki idan kinsan halin da nake ciki Dikko yasan ina nan ko yanajin abinda nake cewa ya basar dani yaci gaba da cht inshi hankalinshi kwance , inda yake saman kujera naje na kamo ƙafarshi na jawo da ƙarfi ina cewa saina faɗar dakai na ƙarya maka kashin baya , da ɗayar ƙafarshi yayi min wani irin kyakkyawan harbi a fuska saida hancina ya fashe. Shi kuma yaci gaba da latse² a wayarshi da yanayin shauƙi , baya nayi inajin juwa ɗakin na gani yana juyamin duniyar tayi shiru banajin motsin komai watan saurarena ya ɗan ɗauke shima numfashin an riƙeshi. Ina dawowa jin sauti na sake tafiya inda yake ina faɗar saina kashe ka , janye wayarshi yayi daga fuskarshi yana kallona da wani irin jarabben kallo , a kasalance yace wai nine zaki kashe….? Ya nuna kanshi , ey , An mata dukana ? Ey , har wannan shima zaki ? Ya nuna daddatsewa da hannunshi , gemunshi kenan , dai² lokacin dana iso kusa dashi , riƙeni yayi da yanayin mayata yace muje saman gado mu kashe kanmu nima saina kashe ki…… Ni ka sakeni , anƙi a sakekin ya ƙarasa maganar yana rufe ƙofofin hancina da “yan yatsunshi biyu , da hayaniya nace wai ba nace ka ƙyaleni ba ne iye ? Shima da irin magana na yace wai bana ce bazan ƙyale ba iye ? Ya faɗa a gajiye yana sauke numfashin jaraba yana min wani irin kallo.
Kwacewa nayi , ya riƙoni da sauri yace ai ƙarya kikeyi yarinya , ina ne zakije ? Sai kin kashe ni….. Ya ƙarasa yana lumshe idanuwanshi tare fitar da numfashi cike da kissa , ƙiƙi² muka fara rigel². Ni ina so in ƙwace , shi kuma yana so ya riƙoni har ya sauko daga saman kujerar , saina tafi , bana sanka׳ na ƙarasa ina ƙara yawan kukana. Ai basai kinsha wahalar faɗa ba nasan wannan shekaru 3 zuwa huɗu da suka wuce. Jana ya farayi hanyar bedroom wai muje in kasheshi. Da Allah ka ƙyaleni kaji , ah ni bazan ƙyaleki ba aradu sai kin kasheni yayi maganar yana murmushi tare da kafe ni da mayataccen kallonshi.
Nanfa abun yaci tura naci gaba da ɓarin maganganu , tun yana kallona har ya fara rufe ido ya sake hannuna. Nan gori ya tashi tunda na lura yana da buƙatuwa dani , haka na warware kamar farfera na ci gaba da zazzaga ranshi mutunci ni matar da za’a sauke buƙata a kaina , ƙarshen film in nace tafiya zanyi , cike da ɓacin rai yace ina ne zaki iya zuwa ? Bayan baki da gidan da yafi wannan ya nuna ƙasa da ɗan yatsanshi na hannu dama , yana ci gaba da cewa kije mana ? Idan kin tafi zan mutu ne ? Ya nuna kanshi cikin tsatsanin fushi mai sa kaji cikinka ya juya na kasa kallonshi , dan kinga ina lallaɓaki ? Idan kinyi haƙuri baki je ba kin zama banza , ki tafi ya nuna hanyar fita , rage murya yayi da cewa ina da dubunki a waje sai me ? Ko an faɗa miki wai bana iya rabuwa dake ne ? Kullum² zakije sai na tafi gidanmu kaza² tou kije ko wani ne ya baki haƙuri ? Hmmm ke baki san iskanci na ba , nafi ki ƙaryar rashin kunya wallahi , inda duk kike zato na tuni na wuce wuri nayi gaba…. Idan kina nan wata zan kawo idan ma kin tafi haka dai zan sake kawo wata.
Kina iskanci ana baki haƙuri tou an daina cewa kiyi haƙuri ki tafi duk gidan da zakije , ba burin daya fi duk macen da bata da lissafi tanayin faɗa da miji tace gidanmu zanje , fuuuu tayi yaji ya nuna da hannu , tou idan baki sani ba babu babban kuskure da yafi wannan jakancin , ko shi mijin dake aurenki bai san kuna da gida ba ? Ai yasan ba a sama kika faɗo ba , ya nuna yana ci gaba da cewa ai ina ganin idan yaso zaice kije gidanku. Mahaukaciya ma dake da Allah , fitarmin daga ɗaki yanayin fushi ya fara hawa kaina kafin inji miki ciwo , kuma na rantse da girman Allah idan kika fita gidan nan ko ina kikaje har can zan biki saina lalata miki fata , kaca² zan miki. Fita nace…………………… Ya faɗa yana nuna hanyar fita tare da rufe idanuwanshi cike rashin mutunci. Fashewa nayi da kuka nace yi haƙuri don Allah , zo nan , ya kirani da hannunshi , tafiya nayi ina kuka ina kallonshi. Riƙeni yayi a jikinshi yana sauke ajiyar zuciya bakiji An mata , wai ni miye matsalar ne ? Kullum sai kin ɓatamin rai wai me nayi ne ? Haba An matana ya ƙarasa mganar yanamin kyakkyawan riƙo , cikin shashshekar kuka nace kaine , nine kuma ? Tou wai meye nayi da zafi haka ? Ka daina so na ai , haba Yarinya ke ko wani ne ya faɗa miki ai zaki ce a , a , duk duniyar nan wai waye yake dani idan bake ba ? Haba ƙaramar yarinya…. Duk kin burkeni na zama wani lusari sai anfani kike da soyayarki kina murzamin zuciya san ranki ya ƙarasa yana min kyakkyawan murmushi , shiru nayi ban mishi magana ba , kefa yarinya ce ? Kalli Dikko fa ? Akwai tazarar tsayi shekaru da kuma tunani , cikin dariya yace wallahi kin maidani kamar wani zararre ke ko tsoron Allah ma bakyaji ? Haba An mata , ɗagoni yayi daga jikinshi yace ai nasan ma kin yafemin ko ? Ey tou zo muje. Yana riƙe dani har toilet da kanshi ya wankemin fuska yana cewa dan Allah An mata ki daina ɓatamin rai gaskiya banajin daɗin abinda kikemin.
Wai ke baki san ba’a ɗagawa miji harshe ba ? Baki san idan mijin yanayin zuciya yadda ake saukeshi ba ? Ba’a hawo namiji yayin da yakejin tuƙuikin ɓacin rai , komai yana iya faru a dai² lokacin da yakeyin fushi , Juyowa nayi na riƙeshi ina ci gaba da kuka , a wahalce yayi gajeriyar dariya cewa ai nasan baki iya tafiya ki barni wasa kike , ƙaramar yarinya. Wai miye ke damun kanki ne ? Meye nake miki wanda baya miki daɗi….? Ni kifaɗamin , faɗamin matsalata dake sai nima in faɗa miki matsalolinki kowa ya daina ɓatawa kowa sai a daina faɗan tunda kin gaji. Kinga ko a rigima kin fahimci ni nafi sangarta bana gajiya haka zakiyi ta hawoni ina baki kashi kullum kina fama da jinyar fata , kuma kinsan banayi zuciya in zaneki kuma in maƙalƙaleki anjima inyi ta warwarewa ya riƙeni yana nuna yadda yakeyi idan yana kwance dani , dariya nayi ina kallonshi. Shima dariyar yayi tare da ɗagamin gira yace wallahi kuwa , tou ni ina ruwana ? Gani ga “yar yarinta ina fa morewa , niɗin mai sa’ar rayuwa ne , duk da dai kince wai niɗin tsoho ne , amma a haka dai ai ina bada wuta a tsakiyar filin wasa ko ? Ya ƙarasa maganar yana ɗan taɓe bakishi tare dayin wasa da girarshi.
Murmushi nayi ba magana amma har yanzu ina kwance a jikinshi , ɗan wayancewa yayi dai yaci gaba da yabona wanda nidai nasan a zuciyarshi ba haka bane ba , yana dai yabo na ne dan inyi farin ciki ya kuma sauke buƙatuwarshi yayi bacci da natsuwa. Koma dai bada gaske yakeyi ba ni naji daɗi , yana da kyau maza su riƙa farfaɗawa matayensu kalaman da zasuyi farin ciki su girmama musu kansu sai suji su suma ashe dai wasu manyan shegu ne , ta hakan ne zaka riƙa zaliƙo mata matsalolinta a hankali idan mai hikima ce saita riƙa gyarawa , irin dai kana yabonta kana cewa ai idan kikayi kaza kinga yadda kike bada haske ? Ko kike ruɗani ? Ko bana tare dake sai inyi ta tunaninki , kaza². Nan zaka ga ta warware tace you ai kaza da kaza ma da nakeyi kaza. Ni nayi farin ciki da yacemin duk nafi su Yusra kyau , gani “yar gayu kuma ni “yar yarinya su duk sun tsufa ma , ai haɗuwa ta ta wuce duk inda bana zato , shi a ganinshi ma yafi ko wane namiji sa’ar aure , bayan ni nasan Dikko ƙarya yakeyi , kuma wai da nace masa ba wani cewa yayi in kalli kaina a madubi fa , An mata kalli idanuwanki , ji lallausar bakinki ya nunamin saman lips ina , kalli nan ji can uwa uba kuma saikin dafe uztaz D ‘ K a gado. Kalamanki suna da daɗin sauraro bayan ni nasan duk lokacin da zai kwanta dani sai ankai ruwa rana , yanzu nan ya gama min faɗa ina ɗaga mishi murya , amma da yayi dai nayi farin ciki ,
Wai ni ina da kyakkyawar fata idan kuma nayi mata ado da lalle zan ƙara haɗuwa wai kuma lallen na hausa amma a zuba turare a cikin lalle dan ya kashe ƙaurin lallen , warware kaina yayi yana shafa gashin kaina wai na iya gyaran gashi ya mishi kyau a haka. Shiko banyi kitso ba yafi ibar mishi lissafi , haka na saki baki naita dariya kamar sakara ina cewa ai idanma nayi kitson warwarewa yakeyi , ey ai dama nima bansan kitso , saidai ina san wannan kitson kin tunashi ? Wani mai kyau ? Kai yayi miki kyau An mata , nifa nasan bana kitso harma gara kalaba , amma da nace masa ni banyi kitson nan ba , cewa yayi na manta yana ta nunamin yadda kitson yake. Yadda yake nunamin irinshi ni nasan ban taɓayin irinshi ba a tarihin rayuwata. Amma Dikko ya kafe kai wai nayi shi in tuno mana , saida na natsu sosai na gane irin kitson dake kan Yusra ne , dakel dai nayi yaƙe mai ciwo , shima zanen lallen a wurinta ya gani ai na gani itama lallen hausa ne akayi mata wani irin ado mai ɗaukar hankali.
Wato duk duniya ita mace baka da abinda takeso sama da a yaba mata , suma mazan haka suke , haka kuke mana “yan rainin hankali , kuma so kuke a yaba ku kan nan naku yana muku wani girma kunajin ku wasu manyan “yan duniya , kuna wani ciccika fuska ku masu gida ana zugaku kuna wani karkace baki kuna dariyar ƙasaita kan׳ dariyar cikin izza da nuna isa. Yana da kyau mazaje ku riƙa gyarawa matayenku da irin yajuju wama jujun da ku kuke gani a waje. Kuma a hikimance , ba zagi ba duka ba gori wance ta fiki ko wane matar shi kaza² a , a , ba haka akeyi ba a hankali zakayi mata dan kune kaɗai kuka san a inda kuke shiga kuna gano irin wannan duniyanci. Bawai nace kuɗin “yan duniya ne , ina nufin irin matan da kuke huɗɗoɗi dasu. Ba kuma ina nufin tasha ko sakarci ba , kamar a kasuwa ko a ofisoshinku da dai sauran wuraren da kuke mu’amula dasu , tunda suna ɗauko wanka da gayu kamar zasu tashi duniya dan haɗuwa , su barbaɗo muku turare a ciko ido da kwalli ana firfira muku idanuwa. Ku saki baki ba aji kuyita gaggaɓa dariya irin wacce ko matanku bakuyi ma irinta. Tou karta burgeka kuma karta ruɗa maka lissafi da tunani , ka riƙe karka bari tayi wasa da tunaninka nata ƙarya ne zahirin tana gida , idan tayi nata sai yafi baka sha’awa akan na sharar bakin titi , wai su kun gane matsalarsu…..? Matsallar auren su ba a gabansu yake ba. Haka zasu shaƙe miki wuyan miji suyi ta ranfa dashi , idan kuma ta gaji da cin aljihunshi taci shi har babunshi saita tura wata itama taci gaba da gayar miki miji babu tausayi , itama idan ta gaji tayi gwanjonshi shi kuma zuwa wannan lokacin ya zama ɗan gari. Ma’ana ya gane hanyar yadda take , kafin ki ankara an firgita miki miji , wata macen ma su biyu ne a wurin miji amma dai lusaranci da hauka yasa sunyi sake sun barwa karnukan bisa titi suna ta mishi haushi , baki jin haushin ta waje wai ta gidan itace ta tsone miki idon tsabar hassada , kullum kika tashi da ita a zuciyarki baki da buri da kwanciyar hankali yadda zakiyi waje da ita , tou idan ta tafi ance miki shikenan bazai sake aurar wata ba ? Ba matan gida ya kamata kuyi hassada dasu ba yaƙi zakuyi da matayen dake matse mazanku a waje , ku kuma maza gaskiya kuma kuji tsoron ku tausayawa matayenku , ku kyautata musu , kuyi musu magana da sanyi² ku lallaɓa su , ku tarairayesu , ku ririta su ku jawo su jikinku da farin ciki. Kuyi kwanciyar aure dasu cike da soyayya da kuma nuna musu finsu buƙaturwa hakan , ku gode musu ku yaba ƙoƙarinsu ku basu ƙwarin guiwa ku jinjina musu ko bakuji daɗi ba , a hikimance zaku riƙa nuna musu yadda abun yake har su ƙware su anshewa ɗan tama doki. Wasu matayen sunfi wasu mazan gogewa ta wannan harkar da kuma gogewar rayuwa ta zamantakewar rayuwarmu tayau da kullum. Wasu kuma mazan sunfi matan , idanuwansu a tsaye yake tsakiyar kai , tou koma dai waye tafi gogewa ta gogar da abokin rayuwarta sai kuyi rayuwarku gidan aurenku da natsuwa.
Kuma bawai ina nufin kuna biyewa matan waje ko ku fahimci magana ta da wani yanayi. Ku fahimce ni da kyakkyawar fahimta amma aradu ku ƙyale gaibu ku kama zahiri , idan kuma ka nuna mata taƙi gyarawa kayi mata…… Ba cewa nayi ka ƙaro aure ba , nufi na a ƙaro miki kayan ado a ci gaba da baki kula ana ta kwantanci nuniya da gyara har ki gane ki gyara , dan kunsan mu mata ba kishi mukeyi ba hassada muka iya. Sanin sirrin kishi zahiri babu munafurci da yadda akeyin shi kanshi kishin aradu yana nan wurin maza. To kuyi kishi yayin da akafi matayenku ku tsaya tsaye da gaskiyarku kuyi gyara.
Tou lallai fa idan taƙi gyarawa ka lallaɓa kayi mata ƙarin…… Haske , dan inda kuke shiga mu bama shiga wurin , irin matayen da kuke gani mu bama ganinsu , kuke ganinsu kune kuma kuka san inda kuke ganosu har sukeyin abinda kuke ganin mu bamayi muku irinshi , wata matar daga gidan aurenta maƙotanta sai familynka da nata ahalin su kaɗai ta shiga kuma ta sani , sai abokan arziƙi , kuma kila su basu da wayayyun idanuwa bare ta waye da wayewarsu. Sanin da daka santa dashi tun tana budurwa kafin kuyi aure shine dai har yanzu babu wani ci gaba , wata macen kuma da wayewar ido take zuwa gidan auren amma sai ta zama wata aljihun gefen riga ta daƙiƙance ta zama wata sai addu’a kawai. Tou kai da kake shiga kana fita kana zuwa inda ita bata zuwa kuna ganosu suna labbatarku da irin abubuwan da suke jan hankaliku ka sanar da ita mana , ka koyar da ita , idan ka faɗa mata raguwa kayi ne ? Kaɗan faɗaɗa mata kwalwarta ka buɗar mata da idonta dai² irin yadda ka gano suka ɗauki hankalinka. Ka wadata matarka da sutura dai² ƙarfinka ka wadata ta da kayan ƙamshi mayuka masu kyau hoda sabulun wanka ka ciyar da ita karka riƙa maƙalewa wurin mai indomie ko mai tsire da wasu lafiyayen kaji kabar matarka taita kokowa da tuwo , wallahi kuji tsoron Allah kuci irin abinda kuke ba iyalinku irin abun nan da kukeyi kuci daɗi ku barsu da marmarin irin abinda ku ya gundireku dan nacin cinsa da kukeyi wallahi zalinci ne. Cuta ce , ku kuma matan kuma muji tsoron Allah masu siyar da shinkafar miji kuna zubin adashe Allah yana kallonku tom…..
Idan an gyara miki kema ki riƙa gyarawa mana , kar yace kije kiyi kisto two step , ki karkace baki ah ni wallahi bana san wannan kitson kaza² , to wane iri kike so ? “Yar rainin hankali. Ke harma sai ya faɗa miki kiyi irin style kaza ? Ashe ma baki san abinda kike ba. Idan akwai abinda yafi two step kiyi mishi mana , ke meye naki a ciki ? Ba shine yake so ba ? Tou ayi mishi mana a zauna lafiya ? Ko yace miki wallahi kaza na gani ya burgeni , kiyi irinshi , ke uwar tsiwa maimakon kice tou sai kice ah sai kaje can idon daya gano a wurinsu kaje kayi ta gani. Ƙalu balenki da bawa namiji wannan ansar idan ya fara gani tou fa lallai ƙaryaki ya ƙare , kenan kinma yadda yaje ya gano na wajen ko ? Shin wai mema kika tsaya yi har namiji yafi ki hikimar rayuwa ? Ke bakya kishin kanki ne eye ? Haba Hajiyata da Allah karki bani kunya mana. Ko ke baki so tou kiyi mishi idan dai shi zaiyi farin ciki mana , sai sunje sun kallo na wajen a ɗauke miki hankalin miji ayi yamma dashi a barki da ciwon tunani , idan shima ɗan rainin hankali ne kuna gari ɗaya fa da kinyi waya zaice yana abuja ko kaduna ina nan airport zan hau jirgi in tafi lagos , ke ya maida jirgin tana can ta ɗaukeshi an barki gadin gida , kar kuma mijinki yayi tafiya ki tuno cewa kila yana miki ƙarya ne baije ko ina ba , kulli inki ahir inji tsofi , ƙalubalen ki da zargi. Damuwa ta dameki daga nan sai neman shawarar abokai , idan kinyi sa’a da ƙawar kirki ta baki shawara ta gari , idan baki dace ba ta haska ki da malam tsibbu suma daga nan kasuwa ta buɗe , idan kuma kika hau layin maijin taushinki tasa ki , ki kakkaɓo auren , dama tana can tana ta yawon zawarci ita ɗaya ta rasa ƙawar cin titi tou ta samu abokiyar yawo , idan kuma ta ƙwarewa cin amana ta auren miji a barki da wallahi² , ke baki gane illar abun sai kin shiga makarantar , baza ki fahimci wuyar karatun ba sai an shiga second semester ku kula dai……
Gadai Dikko yana faɗawa Sultana , wanda ita a ranta tasan ba haka bane ba. Amma taji daɗin yadda ya yabeta tare da nuna mata tasha gaban mata da yawa. Tou kai idan ka tashi faɗar naka kalaman ka faɗa mata su da gaskiya cikin soyayya. Ku daina haɗe fuskoki wa matayenku haka babu kyau , wani namijin idan kika ganshi a majalisa yafi kowa harshe dariyarshi tafi ta kowa , duk mai tallar da tazo sai yajata da surutu , sai matarka zaka rainawa wayau idan ka tashi shigowa gida ka haɗe fuska kayi ta wani gadarar banza wai kar ta raina ? You bayan ka manta kun haɗu a tsakiyar filin wasa ? Allah wani namiji idan ya shigo gidanshi kamar “yan fashi sunyo samamen dare. Ba “ya “ya ba iyayen suma kansu gabansu harbawa yake kamar an ɗorawa mutum wuƙa a maƙoshi…..
Cike da soyayya mukayi wanka muka baro toilet in cike da tsantsar muradin san kasancewa da junanmu. Kuma har muka fito bai daina zugani ba sai dariya nakeyi ina watse baki kamar lefen wacce babu uwarta a gidan babanta , ina ta sakin layi , zuwa wannan lokaci gaba ɗaya na manta da wasu banzayen hotunan da na gani a wayarshi na fuskanci rayuwa mai daɗi da gusar da damuwa a wurinshi……..
Bayan kwana huɗu.
Ni na rasa inda mai gilashi ta sake a cikin jahar katsina , na nemeta na rasa inda take , kuma har gidanta naje bata nan kuma Dikko da kanshi ya kaini. Wayarta ma a kashe. Daga gidanta gidan Inna mukaje kamar dai kullum yauma haka taita habaice² tana zagin Dikko wai bazai zauna mata a kujera ba , ƙiri² Inna ta koma wata zararra , shiko murmushi yayi kaɗan ya samu wuri a saman kafet ya zauna , nima kusa dashi na zauna. Haka taita zaliƙe²n da ita kanta bata san dalilin yinshi ba , taita zaginshi tana aibatashi saida ta gama kaf tace idan yaji fushi ya sakar mata “ya , shafa kanshi yayi ƙasa² yace ban gaji ba ya faɗa yana suɓaro baki a sakace , saida ta gama dashi ta juyo kaina tace kema ɗayar mara zuciyar kaza² nima taci gaba da sheƙeni har ta gaji tayi shiru , saida ta sauka ta gama da kanta ta rufe bakinta mukayi mata godiya mai gida Dikko ya sauke mata manya kuɗi muka wuce gidansu.
Ajiyeni yayi ya tafi huɗɗoɗin shi , Momy kuwa sai ɗan zungurar min ciki takeyi tanasan ta gano wani abu ne daga gareni akan Sharifa. Shiru nayi nidai idan ta matsa min da tambaya saidai ince mata Momy ban sani ba wallahi , wai har yanzu munayin faɗa da Dikko ? Tambaya ɗaya takemin ni kuma ansa biyu nake bata , ah umm. Gajiya dai tayi ta ƙyaleni , har ɗaya saura na dare bai dawo ba saidai ya turo Ashiru ya maidani gida , wato yau ya samu hanyar tafiya wurin “yan iskan matanshi ko ? Ita kuma Momy harma ta yadda da ƙaryar da yayi mata wai ya fita da Dady. Dan da Ashiru yazo tafiya dani sai ta kirashi wai shi yazo da kanshi ya tafi dani mana , shine yace mata yana tare da Babanshi kenan dan karta dameshi. Tun a mota nake kiranshi , shine ya turamin da saƙo wai yana meeting , danma ya ɗaukeni kidahuma. Ci gaba nayi da kiranshi ƙarshe kashe wayarshi yayi. Ashiru ka kaini wurin Dikko , lafiya ? Ya tambayeni ? Lafiya qalau shine yace ka kaini. Mai gidan ranki ya daɗe ? Tou meye a wurin da bazanje ba ? Ai banma san inda yaje ba , daga haka bai sake magana ba , nice naci gaba da cewa amma ai a wannan motar yake a ina ka samoshi ka ɗauko motar ne ? Shiru yayi ya ƙyaleni , fita nayi daga motar ba tare dana sake cewa komai ba na nufi ciki , Papi yana kwance a palon ƙasa yana bacci saman kujera. Ɗaukarshi nayi ina taɓashi ya buɗe idonshi yana shashshekar kuka , ɓata fuska yayi a hankali ya rufe idonshi yana cewa Yaya…. Kila ya dakeshi ne. Me yayi maka ? Saida ya sake sauke ajiyar zuciya da yanayin bacci ya sake cewa Yaya…..
Majalisar ɗinkin “yan matan tashi. Muji , yau da Jiddah ya fara zama sai kuka take masa wai Ya Yazeed yace zai aureta kuma tayi hidima dashi mai girma amma yana ta wani zamewa baya ɗaukar wayarta kaza׳ , shi Dikko ma daga farko bai gane wane Yazeed take magana ba saida tayi mishi bayani , tou shi Yazeed harma ya zama Yaya baida labari ? Hidimar da ta ita Jiddahr tayi ma shi Yazeed ya tambayeta , cikin inda² tace kawai dai kayi mishi magana muyi aure. Cikin rashin fahimta yace waike kece zaki auri Yazeed ? Ey , jinjina kai yayi tare da ɗan karkace kanshi ya tafi duniyar tunanin rayuwa irin ta gidan Yazeed…..
Ƙaton gidane ginin zamani , ya tsaru gidan iya tsaruwa kuma anyi mishi ado da ciyayi masu kyau. Ɗakin mai gadi da ɗakin janareto , a gefe kuma ga wasu irin zabga²n motoci masu masifar kyau da tsada an jera wanda shi mamallakin gidan ne ya ciyosu a harkar wasan danbe. Ajiyar zuciya Dikko ya sauke a wahalce yana jinjina kanshi , duk duniya shidai baya so yaga mace tana wahalar rayuwa. Baya so yaga rayuwar mace tana tangal² , kallon Jiddah yayi sannan ya gyara zamanshi ya miƙe ƙafafuwanshi yana daga saman kujera ƙafa ɗaya saman ɗaya. Wannan inji haka ake cika shi da mai safe rana da dare har gari ya waye a cikin awanni 24 haka yake aiki ba’a kashe shi saida idan za’a zuba mishi mai ko idan ya lalace , duk fitulun gidan a kunne suke suma cikin awowi 24 da wasa ba’a kashe su dare ko rana addau² haka suke amma ɗakin matar gida ko kwan fitila bata dashi , babu wata cima a gidan ita kanta matar gidan duk haɗuwar gidan da tsaruwarshi wankau takeyi tana ciyar da kanta.
Ga hausawa da wani irin hali wai sai kaje zuminchie wa ɗan uwanka amma ka tattara burinki baka kallon rayuwar gidan sai girman gidan , idan ka ɗora mata buƙatarka tace bata dashi sai zagi da gulma munafuka ta tattare komai ta hanamu , daga ita sai “yan uwanta sai iyayenta , ta shanyeshi ta hana ya bamu ko ya bata ta bamu ta hanamu , shin tana samu tana dashi ko bata da ? Kudai , a baku………׳ kamar mutuwa. Shi Yazeed inuwar giginya ne shi , yana dashi da ya bawa matarshi gara yaje ya zuba harajin wasan danbe , gashi cikakken ɗan iska wata rana ma a gidanshi yake kai mata matan bariki , azzalimin namiji ne dan shi matarshi ta gida ma bai ɗauketa a bakin komai ba , “ya “ya ne ta kwarkwartsa mishi bi da bi a tunanin ta idan ta aihu da yawa ko zai gyara halinshi amma abun sai ci gaba yakeyi kamar ana daka mishi tsawar bakin iyaye. Ni a tunanina duk mai shi zai bada ne , kyauta dai bata kawo talauci. Haka kuma rowa bata kawo arziƙi , duk mai bayarwa baya rasawa , idan kuma ka samu kaci kai ɗaya dan kar ka bayar ka rasa ? Tou wata rana ma gaba ɗaya barin duniyar zakayi da kuɗin da duk tattalin da kakeyi karsu ƙare ko kuma ka tara da duk wani tsari naka na rayuwa , tou fa lallai duk zaka barsu ka tafi kai ɗayanka kaje wata rayuwa ta daban. Gara dai idan kun samu kuɗan taimakawa masu buƙatar taimako sai kuma Allah ya ƙara taimaka muku.
Caf Yazeed cikakken ɗan tasha ne. Baida mutunci ko kaɗan , dan ko A C ɗakin matarshi da yasa daga farko daga baya ƙwaƙwulewa yayi taci gasar danbe. Amma saboda riya yabar iyalinshi da wahalar rayuwa , ko tace baya bata abinci tana cikin wahala , sai ace bata godiyar Allah , abinci buhunna² gasu na ajiye a store taci ɗin ma ta ci ƙaniyarta dan tasan ba nata bane ba kwalliyar gidane saboda mutane su gani suce yana da kirki , bayan wani lokaci kuma ya jera mutane layi ya rarraba musu shi sadaka.
A anguwar sai zaginta akeyi ita marowaciya ne tabar “ya “yanta da yunwa sai azabar neman kuɗi kamar zataje dasu lahira. Wani faɗa da sukayi har iyaye suka shiga ciki tace har a c ya cire a ɗakinta da palo tace yasa musu fanka ya ƙiya , shine yace tana wurin gyara , ganin iyaye yasa yaje ya samo hoton a c n yazo ya maƙala mata , shima tayi magana yace ya gyaro itace ta lalace shi bata da tattali kaza² , aka haɗu aka bata rashin gaskiya , shi kuma ganin ya samu sa’a yasa yaketa gurje mata mutunci da wahala. Duk wanda ya kalli gidan Yazeed akace ansan sunan wani abu waishi wanki ko wankau ? Sai su “yan cikin anguwa sunce ƙarya ce , ita kuma tunda anguwar masu kuɗi ne take sa ana tattaro mata kaya tana wankewa ta goge tunda dama kayan “yan gayu ba wani datti yakeyi ba , haka azzaliman maza sukeyi dan rashin imani. Shine Jiddah zata shiga ? Allah ya basu zaman lafiya….. Allah ya rufawa An matarshi asiri da tana can tancin ƙaniyarta gata yarinya , wani hali nata ya tuno dan haka yayi taƙaitacciyar dariya , da tace wai ya tsalleke kabbarinta ya wuce , cikin dariya yace niɗin banza An mata , saida yasha dariyarshi Jiddah tana daga gefe tana kallon ikon Allah , shi yama fita daga wannan sabgar ya tafi kallon hotunan matarshi.
Duk hoton daya kalla zaiyi murmushi a ranshi yace An mata rigima , wai Dikko ka tsalleke kabarina kaje kawai , haba An mata kar Allah ya nunamin ranar da zaki tafi ki barni a duniyar nan , bana fatan naga ranar da ni zaki shige cikin ƙasa ki barni , ina so in rayu dake har ƙarshen rayuwata in tafi in barki ki rayu rayuwa mai cike da farin ciki , gaki ga Papi da “yar ƙanwarshi ko ɗan kaninshi , burina yanzu a duniya bai wuce in mutu a hannunki ba , ina sanki׳ ki jarumata….. Hayaniyar dake tashi ne ya dawo dashi daga duniyar kallon hotunan da yakeyi….
Salati yayi tare da fiddo duk girman idanuwan shi ganin Sharifa da wata irin bahaguwar shiga ta jahannama ga fasinja. Rankatakaf su Ashiru suna wurin , shi wallahi kunya ma abun ya bashi , gata ta shigo full battery wato cake take. {{ tana cikin maye }} tasha wasu irin zaƙo²n akaifu ansha girar ido atach har tsakiyar baya , wasu irin “yan kunne girman round insu yakai girman ɗan hannu sai ibar hayaƙi take tana barbaɗashi sama yana bin iska. Jiddah na riƙe da ita sai zazzabga mata mari takeyi wai ranar da Ya D ‘ K yai mata liƙi ita Sharifar wai tanayi ma ita Jiddah gwalo wai an saketa , tun ranar nake nemanki shegiya ƙazama , shine fa aka cakume rigima. Dikko kuwa lallaɓawa yayi yai layar ɓata bai yadda kowa yaga fitarshi ba. Har baya ganin gabanshi ya shiga mota dakel. Shi gaskiya bawai zaice yana san Sharifa ba , ah tunda dai zai aureta ya kamata ta kasance mai tarbiyar da kamun kai. An mata har hannunshi ta zauna kafin suyi aure amma kullum tana cikin hijabi , gaskiya yana san matarshi ta kasance mai sirrinta jiki yayin da wasu mazan da ba muharramanta ba suke a wuri. Baifa isa yace baya auren Sharifa Dady zaiyi damuwa.
Taya za’ayi shi matar da zai aura ta kasance haka ? Irin wannan dressing ai ba nan akeyi ba , ko a gidanka kayi irin shigar ai zaka saka hijabi idan mutane suna zuwa , tirr mtsww… Gaskiya zai faɗa mata ta daina yin haka shi baya so. Haka ya iso gida da tunani barkatai a zuciyarshi , bayan yayi parking yake ƙara hasko yadda ya ganta zuciyarshi na daɗa soyuwa da ɓacin rai , kai a , a gaskiya a , a , haka ya shiga ciki ranshi a matuƙar ɓace kawai dai yaji babu daɗi yana tayin damuwa har zuwa safe.
Dady kuwa an kaishi asibiti. Bayan likitoci sunyi bincike²nsu suka tabbatar wa da iyalinshi cewa ya samu shanyewar ɓarin jiki , ai uwar Hafsa cewa tayi ita bada ita sa lallen kaza ba , dan ba zata wani iya zaman jinya ba. Da sauranta zata taga gaba tayi aurenta ta gurji sauran shekarun da suka rage mata , wallahi bata zama tayi ta kwasar ƙazanta , Dady ya karkace baki yadda masu irin lalurar suke magana yace baya sakinta , tace bara ta kira inda za’a ansar mata tikitinta na saki a hannunshi tunda ba tare aka haifesu ba , wayarta ta ɗauka tana cewa zaka ga yadda za,a ansar min idan kazo musu da rainin hankali ƙarfin shari’a ba wani ruwanshi da shanyewar jiki zasu tafi dakai su calika ka. A taƙaice dai sun rabu kuma dan rashi inami ta tattara duk ɗan sauran abinda ya rage na ƙaddororinshi tayi gaba dashi wai karya cinye tattalin arziƙin kuɗi “ya “yanta su tashi a hoto , yadda ya nannaɗen nan idan ta zuba mishi ido sai ya cinye kaf kuɗin a wurin jinya…..
Haka taje asibitin da Amisty take ko tausayin Amisty bataji ba , ta ɓanɓare abun ƙarin lumfashin , Amisty ta fara rawar kyarawa , Momy tace kuɗina suna ina ? Faɗamin gidan uwar da kika kaimin kuɗina ko ki tafi lahira tsaye……. Ha׳ Amisty keyi , dariya Momy tayi cikin rashin imani tace rayuwa ko mutuwa…..? Amisty ta nuna rayuwa watom ta mayar mata da abun , mayarwa tayi tare da jaddadawa Amisty kwana biyar ta bata ta haɗo mata kan dukiyarta idan ba haka ba zataje gidan yari , akwai wani sabon d p o da aka kawo acan sabon gari police station inyamuri ne zata haɗata dashi , zatace idan ya anshi kuɗin ya ɗauki one miliyon haba kundai san inyamurin mutum da kuɗi…..
Halima mijinta da sauƙi sosai anma sallomoshi ya dawo gida , yana dawowa kuma da zancen ƙarin aure yazo , fitina ya tashi da rashin kunya nan fa ta tattara ƙawaye ana neman mafita. Kowa da irin shawarar da yake kawowa gashi lokaci ya ƙure ita tanayin mamaki a inama ya haɗu da matar da har zasuyi aure…….? Ɗaurin aure ranar juma’a yau saura kwana 4 , wace ce zai aura…….? Wace ce…..׳ ita……….??? A iya sanin da tayi mishi bashida budurwa dan kullum saita zindire wayarshi tayi bincike amma ba wani alamar soyayya , ashe suma maza sun iya munafurci….? Hmmm maji dai.
Hafsa abun yaci tura alhamdu ta kakarewa malam. Itama tana can sun jagalgaleta sun kaita asibiti saboda ciwon hannunta. Sai masifa takeyi itafa lafiyanta qalau duk wanda ya taɓa mata magani zatayi ma mutum uwar watsi….. Gata nan dai suka watsar a asibiti kamar asarar noma , muje gaba daga baya maji me likita yace……….?
Jiddah data ishi Yazeed da kira cewa abokanshi yayi ya tafi hutun honey time , ƙaraurawar nasararshi ta doka zaije ya buga lamba tara ya dawo…….
Shi kuma mai gida Dikko da yayiwa Sharifa faɗa dan toshewar basira sai taje ta faɗawa uwarta Mai gilashi , raɗa ta ƙara yiwa Sharifa tunda ita daƙiƙiya ce. Mai gilashi tace ta dage karta sa shakku fatan nasara.
A tsagina kuwa , yau tunda na tashi jikina yayi min wani irin sanyi , gani nan dai ni ba mara lafiya ba kuma ba lafiyayya ba , yau komai ya kasa shiga cikina saidai in bi wannan kujera inbi gado. Gajiya nayi nacewa Papi yaje yace Yaya banda lafiya. Babu wani ɓata lokaci shi yazo , Pa-Pi kuma bai dawo ba.
Gabana ya tsuguna ya riƙe cikina da duka hannayenshi cike da tausayi yace meye ne ? Yayi tambayar yana kallona. Fashewa nayi da kuka tare da ɗora fuskata a saman kanshi nace nidai banajin daɗi inajin wani abu yanamin babu daɗi kamar zan rasa wani abu a rayuwata , murmushin ƙarfin hali yayi sannan ya da dawo kusa dani ya zauna. A hankali ya jawoni jikinshi yace babu wani abu da zai faru sai alkairi , ummm ? Ki daina biyewa tunanin zuciya zataje tasa ki shiga ruɗun rayuwa , ba gani ba ? Ya nuna kanshi Kalli kuma ina tare dake , meye zai faru ne ? Munayin zaman lafiya kuma ni nakine ke kaɗai. Tou tayama kike tunanin zaki rasa wani abu mai muhimmanci bayan ni ina tare dake , ai kinsan bazan taɓa rabuwa dake ba har abadan duniya , ki kwantar da hankali ki daina wahalar saƙa tabarmar kabar da bata dace da zamanki ba gimbiya Sultana. Idan kinayin kuka hankalina tashi yake tsikar jikina duk ta mimmiƙe , hawaye basayin kyau a wannan kyakkyawar fuskar. Kuka bai dace da rayuwarki ba. Ke kiyi shiru bara ni in miki kukan tunda kina so kiga hawaye a fuska yana zuba. Ah ai sai inyi ke ki huta , baki san ba’asan mai ciki tanayin damuwa ba ? Ko so kikeyi ki haihu ne ? Yayi maganar cikin sigar zaula. Nace ey , hmmm kima ƙara dagewa kina da sauran kwanki zai kai 90 da Allah kiyi shiru ya ƙarasa yanamin hararar so, tou naji kawomin wayata , tashi yayi ya ɗaukomin wayar , bayan ya bani ya zauna ya sake riƙeni. Kowa dai daga ni harshi muna saƙa wani abu a zuciyoyinmu. Wayar Inna na kira babu daɗewa ta ɗauka , bayan gaisuwa mukayi fira da ita lafiya lau babu wani zage²n nan , kuma na haɗata da Dikko shima suka gaisa cikin mutunci , tace ina Pa-pi ? Yace ya fita yanzu. Wai jiya ba’azo dashi ba.
Me yasa shi ba’asan kawoshi ne wai ? Dikko yace insha Allah Ashiru zai kawoshi bayan la’asar , har sai wannan lokacin ? Kubar shi bana so tunda ba zaizo min yini ba. Ashirun ne baya nan idan ya dawo zasu zo insha Allah , har suka gama wayar babu wani alamu na rashin mutunci kowa ya ajiye waya da farin ciki.
Ni kuma kuka naci gaba dayi , yace bari fa ganin ina baki haƙuri ni kinsan abu kaɗan yake ɓatamin rai kodai kiyi shiru ko in tafi ko kuma ke kibar ɗakin nan sai ki zaɓa , nidai gaskiya bazan yi shiru ba , kasan yadda nakeji ne wai ? Sannu yaimin tare da tashi ya fita nima na miƙe nabi bayanshi har ɗakinshi……
*ZAINAB ABBAKAR MATAWALLE. Ina godiya sosai da saƙo uwar gidan KWARATA…*
06/02/2019
*JAMILA MUSA…*
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN…*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa…
*JAMILA MUSA…*
*SAI NA AURI D ‘ K*
🅿 —— 9
A palo na sameshi zaune saman kujera. Ci gaba nayi da kuka na nufeshi. Hankalinshi yana saman wayanshi yace so kike dai in zaneki ko ? Kusa dashi na zauna nace baka san ya nakeji ba. Riƙoni yayi da hannun da wayar take riƙe cikin tausasassar murya yace baki so in zaneki ne ? Yayi tambayar yana kwantar da firgitaccin idanuwanshi masu saukar da kasala. Kaɗan na kalleshi a kasalance na ɗaga mishi kaina alamar ey. Yace to shikenan jeki ciki ki kwanta ina zuwa. Miƙewa nayi na riƙo hannunshi ina janshi , ba tare daya kalleni ba yace ya wai meye kuma ? Ban bashi amsa ba naci gaba da jan hannunshi , taƙaitaccen kallo yayi min sannan ya tashi muka shiga ciki tare.
Cike da farin ciki Yazeed ya isa gidan Rabiya. Yau ciki aka shiga kasancewar ita matar gida bata nan. Yazeed kuwa tun a waje ya ɓalle botiran gaban rigarshi yana nuna yanayin haɗama. Kai tsaye ɗakin da aka bawa ita Jiddah a ɗakin ta wuce da Yazeed , suna shiga ya rumgumeta suuuu suka sulale saman gado gaba ɗayansu sunayin farin ciki tare da nunawa junansu kowa yayi maraicin kowa.
A gaggauce dai aka shiga gabatar da wasa. Ya nemi yaddar gado da kuma sa’ar makoma sai addu’a na gaba ya samu nasara mai girma. Danshi a tunanin shi a filin wasa ake. Wasan yau yafi ko wane wasa martaba da mutumci a wurin Jiddah , kasancewar an samu wadatuwar fili da tsaftatuwar muhallin da akeyin wasan. Yazeedu kuwa ya ɓata manyan awowi kuma ko wace awa minti da seconds ya bada lafiyayyen naushi mai zama a zuciya har abada. Jiddah ma ta mayar da martani domin ita dama tuni Yayanta ya gogar da ita kuma ta ɗauki karatu.
Rabiya kuwa tunda Yazeed da Jiddah suka shiga ita ta iso gidan , biyosu tayi tana lafiya ? Ina ne zataje da namiji ? Duk babu wanda yaji bare kuma yasan tana magana , suna shiga suka turo ƙofa garam har aka bige ma “yar sa idon banza goshi. Ai bawai Jiddah taji kunya ba ita Rabiya itace taji kunya dan haka ta koma ɗakinta tana neman mafita.
Taya zata iya furtawa Momy wannan zance ? Shedar zina wahala gareshi. Shin wai waye ma yace mata suna aikata saɓo ? Kuma ita bata kamasu sunayi ba , tou dan kawai sun shiga ɗaki ? Ta yuwu wani abu ya faru , sai saƙawa takeyi tana warwarewa lokaci² kuma tana kallon agogo kamar mara aikin yi har Yazeed ya fito , sai yanzu ta gane Yazeed. Shi ɗaya ya fito Jiddah bata biyoshi ba , tou meya faru ? Me sukeyi a ɗaki tsawon awowi 2 har zuwa 3… Ta shiga 3 zafa a samu matsala…..
Saida Yazeed ya wuce itama ta fito ta nufi ɗakin Jiddah. Kwance ta sameta riƙe da wayarta tana ta latse². Da hannunta ta nuna da yanayin karta shiga haƙƙinta cikin warwarewar haruffa tace am Ji-dd- , ah Jiddah am dama nace lafiya naga Yazeed ya fita ? Ba tare da Jiddah ta kalli Rabiya ba tace lafiya qalau kawai kaina ne yake min ciwo ta ƙarasa maganar tana nuna kanta. Ɗan yatsina fuska tayi tare da ajiye wayar ta taci gaba da cewa gashi gida ba kowa kawai sai nayi ma Yaya D ‘ K waya ina buƙatar magani , shine fa ya aiko abokinshi ta ƙarasa maganar tana watsa hannunta….
A ɗan tsorace Rabiya tace Dikkkkkkkkkko ? Ta kira sunanshi da mamaki cikin jan kalmomi wurin faɗar sunan tare da warware kaf ilahirin gininta. Ummm Jiddah ta faɗa tana jinjina kanta alamar gasgatawa. Rabiya tace taf Dikkon ? Jiddah tace shifa. Fuuu Rabiya ta fita , murmushi Jiddah tayi tare da cewa ai nasan idan na shigo dashi a tafiyar dole zai fito yayi masifa ya tilassa ayi auren , ba jiya naje muyi magana ba shine ya basar dani yana waani dariyar banza , An mata rigima , rigimo. Dariya ta sakeyi kaɗan tare da nunawa da “yan yatsunta sati biyu cif zanyi nayo waje. Wata 3 idda a cikin wata na huɗu zamu tare a sabon gida. {{ G R A }} a wata na biyar kuwa Caca zata kama gabanta , Pa-Pi zai zama nawa , wama ya sani ko jinina ne aka kai can…..? Da yanayin tunani tace babu shakka Pa-Pi nine uwarshi shine yake ƙwaƙwata , oho dai hakan ma bazai hana in kasheshi ba…….
A tsagin Rabiya kuwa tunani takeyi , meye tsakanin Dikko da Jiddah ? Wane irin magani ne ya bada a kawo ma Jiddah ? Ciwon kan ƙaniyarta ? Karfa su maida ita wata gwanjon bisa titi , tana can tana huɗɗoɗinta suyi ta wucewa ba tare da tasan so adadin da ake wucewa ba. Anya Dikko yana da gaskiya ? Kardai zagayewa yakeyi idan bata nan…..? Har zata kira Momy ta fasa kawai ta kira Dikko. Babu daɗewa ya ɗauka ko gaisuwa babu tace yazo yanzu²n nan tana nemanshi. Magana yayi sannan ta bashi amsa da cewa kawai kazo nace idan kuma ni inzo tou… Magana ya sakeyi ita kuma tace shikenan kayi sauri ina jiranka.
Dan Allah kaje tare dani. Cikin faɗa yace wai ina ne zanje dake ? Saida nayi kalar ban tausayi da marainiyan murya nace dan Allah. Baimin magana ba ya ɗauki wayoyinshi , shikenan tunda bara ka fita dani ba Allah yasa ka dawo ban….. Bakiyi me ba ? Gyara bakina nayi ina kallon ƙasa , bai sake kallona ba yace zo muje. Da sauri na wuceshi na tafi ɗakina , hijabi kaɗai na ɗauka ko wayana ban tafi da , nayi waje. Pa-Pi shima biyoni yayi yana kuka jaije…. Kafe kai yayi shi bazaije da Pa-Pi ba , shi kuma Pa-Pi riƙeni yayi idan ba’a zuwa dashi nima babu inda zanje. Dikko yace ka sakarmin mata kaji ? Yayi maganar yana zaro mishi ido. Da ita zanje kaine bazan tafi dakai ba. Riƙeni yayi Momy karci tafi ci barni. Dikko yace kai so nawa ka tafi ka barta ɗan rainin hankali sakarta nace maka. Kamar an matsi bakinshi yace kaicuwa jakuje….? Ya faɗa da yanayin tsoro ! Yaci gaba da cewa kuma fa’a cuwa da Pa-Pi ya ƙarasa maganar yana ma Dikko wani irin kallo haɗe da murmushi. Kete Momy ce cinyi kuka , jinjina kanshi yayi sannan yace cima Yaya ce yayi kuka ya ƙarasa yana dariya. Nuna kanshi yayi sannan na nunamu yace ni kuma can muku dayiya wayyayi.
Yadda yayi abun ne yaba Dikko dariya , yace ni kuma wallahi in zaneka. Dariya Pa-Pi yayi cewa kowa ce yayi kuka wayyayi. Yana ƙara yawan dariyar wai zaiga Yaya yanayin kuka. Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji lokaci guda wata irin zufa ta ketomin , murya a sanyaye nace ma Dikko nidai na fasa zuwa. Dariya Pa-Pi yayi tare da cewa wayyayi Momy taji tsoyo. Dikko yace keda Allah manta dashi taho muje yayi maganar yana jan hannu na , kinga sai kirana takeyi zo muje kinji….? Ƙwacewa nayi nidai kawai kai kaje , cikin rarrashi yace ke An mata haukan Pa-Pi zai tsorataki ? Da Allah zo muje yana ci gaba da jana. Fizgewa nayi nidai na fasa , cikin ɗaga murya yace kada Allah yasa kije kuma tunda har kika ce zaki kika fasa , idan na fita sai 2n dare zan dawo.
Jiki a sanyaye na kalleshi. Ɗagamin gira yayi tare da kwantar da idonshi na haggu , a hankali ya fidda sautin sumba cikin natsuwa da salo mai tada hankali yana ƙara riƙe ganin idanuwanshi , duk iya masifar sa idonka bara ka gane abinda yayi ba , wannan karatun daga ni saishi kaɗai muka fahimci yaren juna. Ajiyar zuciya nayi kaɗan cikin ƙarfin hali , shi kuma ya ɗagamin hannu ya wuce. Tunda na fasa zuwa ya tafi da Ashiru….
Dariya Pa-Pi yaci gaba dayi yana riƙe da hannuna har muka shiga ciki. Saida muka zauna na tambayeshi wai waye yace mishi zamuyi kuka ? Zama yayi kusa dani yace wai a cikin wayar Yaya ya gani , cike da ɓacin rai nace dan ubanka a wayar aka ce zamuyi kuka ? Kallona yayi ya ɗaure fuska shima da yanayin fushi yana hararata wai saiya faɗawa Yaya nayi zagi ya zaneni , shima ai jiya Yaya ya dakeshi da yayi zagi wa kare…. Tsoki nayi sannan nace ya tashi ya bani wuri. Ƙin sauka yayi saidai ya juyamin baya wai yama fata dani. Kaje ka ɓatan. Ba’a ciyyawa dake…. A palo na barshi na koma ciki , kasancewar zufar da naji inayi dole tasa naje nayi wanka. Ina fitowa kuma masassara tace gata nan zuwa , dakel na iya shafa mai kaɗan sannan naɗan kashe masƙin man da fauda , kayana na saka na kwanta.
Dikko jin kiran waya yayi yawa , ya fara faɗa wai ita Rabiya bata da haƙuri gashi yana tafiya zuwa wurinta amma ta dameshi da kira. Wannan ɗan abun harya hasalar dashi danshi baida wahalar fushi amma yana saurin sauka. Cike da ɓacin rai ya ɗauki wayar a inda take ajiye amma sai yaga Inna ce take kiranshi. Ɗauka yayi da sallama ba Inna ce ta ansa sallamar ba mijinta ne ya ansa dakel yace kana ina ne ? Saida Dikko ya kalli hanya sannan ya faɗa masa ta inda yake. Tou wai kazo gidan Kaka dakai da Sultana. Lafiya Dikko ya tambaya ? Umm ai na tura maka saƙo ka duba , a , a , wai meye ne….? Baiyi magana ba ya ajiye waya.
Wai Allahna , Inna ta tafi itama….. Lahaula walaƙuwat illabillah shine abinda ya furta. Dakel ya nunawa Ashiru ya koma gida , taya Ashiru yaci suka dawo gida , dawowarsu ne shi Dikko ya shigo ya samu Sultana tana wanka , ɗakinshi ya koma yana tunanin ta wace hanya shi zai iya furtawa Sultana wannan saƙo….? Ita ya zata kalleshi ? Saƙon mutuwa baƙin saƙo ne , har abadan duniya baraka manta da wanda yazo maka da wannan aike ba. Ya juya ya rasa yadda zaiyi , ko Ashiru bai faɗawa ba. Wane hali An mata zata shiga ? Zatayi kuka kamar zata cinye ranta ya sani , shima kuma za shiga tashin hankali , duk duniya a wannan rayuwa idan akwai abinda ke tada mishi hankali yake firgita mishi tunani yake sashi ɗimuwar rayuwa da manta shi ɗin ko waye wallahi bai wuce tashin hankalin Sultana ba. Shi kaɗai ya isa yayi mata amma idan wani ya taɓota bayan shi ? Tou fa lallai zaici gari da yaƙi…..
Kira ne yake ta shigowa a wayata babu ƙaƙƙautawa. A wahalce na miƙa hannu na dakel dan ɗauko wayar dake saman bedsite. Kafin in ɗaukota a hannuna tuni ta tsinke har wani kiran ya sake shigowa ya fita. Saƙo ne ya shigo dan haka ban fara duba rashin kiran dana samu ba na fara da saƙon.
_Ke Sultana an faɗa miki uwarki ta mutu baki tahowa ? Tou ta mutu can wurin siya ma ɗanki abun wasa , mota tayi ƙoli² ta dakota da ƙasa sannan tabi ta kanta ta wuce. Ba wata tsiya nake kiranki ki bani ba bare kijamin aji ke surukar gwamna…_
Yayar Inna ce surukar Sultan wanda zan aura da farko tasa aka fasa auren ya auri “yar ta. Duk me ya kawo wannan dogon bayani tou ? Salati nayi na sanar da mahalicci na daya isa da rayuwata. Dakel na iya gano number Dikko a wayata na fara kiranshi komai bana iya gani kasancewar inaji na a cikin wata irin baƙuwar rayuwa. Shikenan na zama marainiya gaba da baya , babu uwa ba uba , Allahu Akbar , tabbas ubangiji shine mai iko akan komai da kowa.
_Kema ɗayar mara zuciyar_
Itace kalmar data fara dawomin a cikin kaina , ina hango Inna palonta a daren jiya……
_Me yasa shi ba’asan kawoshi ne wai ? Har sai wannan lokacin ? Kubar shi bana so tunda ba zaizomin yini ba._
Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un , wani irin ihu na kurma , na fara magangu na sakin layi , kai… Wai Allahna , innalillahi wa’inna ilaihir raji’un , nayi kuka sau adadin yadda naji ciwon mutuwar Inna a zuciyata , haba Inna sai kuma kema ki tafi ki barni ? Shikenan ? Tou wai mema yasa kika je siyen wani abun wasa ? Waye ya aikeki ? Haba Innata meya sa²….. ? Kema shine dai kika tafi kika barni ? Gaskiya nadai zauce nayi maganganu marasa daɗin rubutawa. Dikko yayi maganar shi banama jinsa dan gaskiya bana iya gane abinda yake cewa. Kukan da nakeyi ne shine ya tayar mishi da hankali shima yaita kuka kamar ƙaramin yaro wai zai mutu. Shi baya so yaga inayin damuwa , in rufa mishi asiri nasan bashi da lafiya , shima yaji ɓarin maganganu kamar aradu ta faɗo.
Ko a gidan rasuwa haka naita bori ina ihu mai tayar da hankali duk wani imani , babu wanda ya damu dani bare yace ke daƙiƙiya ki gyara kalamanki ko kiyi ma mutane shiru , Kaka ce kaɗai take rarrashi na , sai Pa-Pi daya riƙeni yana ta ihu wai waye ya dakeni. Yayar Inna ni bansan abinda yasa bata ƙaunana ba , bansan me nayi mata ba ta tsaneni da zafi haka. Ko waye ya rasa yayi kuka , nidai a duniyar rayuwata banga abinda yafi rashin iyaye raɗaɗi da ciwo ba. Inajin yadda aketa faɗar yadda mutuwar Inna ta kasance. Wai bayan tayi waya dani a yadda shi mijinta ya basu labari.
Baiwar Allah ashe abinda tayi mana jiya ya dameta. Ta faɗawa mijinta cewa gaskiya Dikko jajirtaccen namiji ne , kaifi ɗaya ne ita a yadda ta fahimta , tsaye yake babu munafurci a lamarinshi. Idan zaiyi kawai zaiyi idan bayayi ko za’a mutu zai tsaya a wurin. Wai tace masa idan yaji fushi ya sakar mata “ya , shine yace bai gaji ba , wai me yake nufi ? Ta ɗauki biro da takadda tayi rubutu akai , bayan ta gama sukazo gidan Kaka dashi da ita. Yace shi baisan abinda ya kawota ba , haka kuma baiji firarsu ba. Yau kuma tace a kawo mata Pa-Pi , wai shine taje ta sissiyo mishi abun wasa wai tasan Dikko zaiyi farin ciki dan ta goge damuwar data saka mishi a daren jiya. To shine fa ta gama sissiye²n tana zuwa wurin motar ta mota yabi ta kanta ya wuce…..
Ni ɗaya a wurin Inna , banda Ya banda ƙani haka nake ni ziƙau ina , ba uwa ba uba ba Yaya ba ƙani. Ga “yan uwan Inna ni basa so na , ahalin Babana kuma gasu dai ga yadda suke , “yan uwan Dikko sune suketa bani haƙuri , bawan Allah shi kuma ya kasa zaune ya kasa tsaye sai turowa Rabiya saƙo yakeyi wai An mata tayi haƙuri ta daina kuka , bayan wani lokaci kuma ya rubuto cewa wai shi yana nan bazai tafi ya barni ba insha Allah , hmmm haka dai yaita rubuce² har akaje aka rufo Inna aka dawo.
Duk ahalin Dikko sun tayani zaman makoki har Momy. Mai gilashi da zugar ƙawayenta “yan tasha amma banda Halima tayomin gayyarsu zuga guda. Akayi ta gulma na wai ni na tara karuwai a wurin rasuwar Mamana , Nabeela ma tazo kuma tayi kuka kamar yadda taga inayi itama , ta tausayamin sosai , tamin sannu da rashi. Sati ɗaya nayi a gidan Kaka nan nake kwana , Dikko kuma idan yazo sai dare sosai yake tafiya dashi da Pa-Pi.
“Yan uwan Inna kuwa bawai ta mutuwarta suke ba , abinda ta bari kawai suke ta lissafi. Babu kunya bare tsoron Allah suke farfaɗo suturunta kowa yana cewa ya kamasu , ita surukar Sultan itace take maganar kayan ɗaki wai dama wallahi ita kafinta yayi mata ha’inci kullum tana fama da “yan ƙwanƙwashe² gado ba kirki , kujerun ma duk sun rubza kaza². Shin aisai ta kwashe ita da zata tsaya tsaron duniya.
Ranar da akayi addu’ar 7 a ranar na bar gidan saboda wulaƙancin da sukemin. Da zan tafi ne Kaka ta bani wata takkada cewa Maryam gashi mahaifiyarki tace a baki. Meye a ciki ? Nima bansan ko ta miye ba , tadai cemin zata turoki ki ansa , amma itama kanta gaskiya batayi tunanin zaki anshi takardar bata a raye ba. Ansa nayi nabar palon. Dikko da kanshi ya ɗaukeni muka koma gida.
Nidai babu wanda a cikinsu yayi min magana game da duk wani abu daya shafi Inna. Basa gabana dan ni basu ne damuwata rashinta shine ƙaton ciwon dake damuna. Suke san abun duniya wanda har ya gusar da imani daga zukatansu , ana kukan mutuwa suna lissafin abinda zasu gada. Tun a mota Dikko kemin nasiha har muka je gida. Da kanshi yayi ma Pa-Pi wanka ya kwantar dashi. Duk inda na juya Pa-Pi sai yayi ta kallona sai kuma ya kalli Dikko.
Har bacci ya fara fizgarshi ya buɗe idonshi yace cinci abinci ? Murmushi nayi kaɗan tare da nuna mishi da kaina alamar eh. Shima murmushi yayi ba tare daya sake magana ba ya rufe idanuwanshi yaci gaba da bacci. Nima saida nayi wanka sannan naɗan taɓa fura. Saman gado na koma na warware takaddar da Inna ta bayar a bani , Dikko kuma yana tacan gefen Pa-Pi yana latse² a wayarshi…… Ga abinda Inna ta rubuta a takadarta.
_Aminci Allah , yaddar Allah wadatar zuci zaman lafiya da kwanciyar hankali su ƙara tabbata a gareki ɗiyata…._
_Sultana ki gafarceni a rayuwa. Nasan bakyajin daɗin abinda nake miki… ? Ni wallahi duk abubuwan da nakeyi ma Dikko dake banyi da nufi ba. Saidai ina hasko miki rayuwar gaba. Ke ɗaya na haifa a duniya baki da Baba haka kuma baki da “yan uwa da kika fita ciki ɗaya dasu. “Yan uwana kuma bakya gabansu , daga ni saike muka rage a duniyarmu , ina neman yafiyarki dan Allah , ki yafemin kuma insha Allah bazan sake ba…_
_Amma ki san wani abu a rayuwa. Nifa ba san Dikko ne banayi ba , a , a ni iskancin shi ne gaskiya bana so. Idonshi ya waye da yawa. Ni gaskiya a tsarin rayuwata bana sha’awa ko muradin namiji mai buɗewar ido da gogewar rayuwar irin na Dikko , amma ya za’ayi tunda haka Allah ya rubuto ? Nidai ina neman yafiyarki karki ɗaukeni a matsayin uwar data fi san kanta akan “yarta. Ban hanaki zaman aure ba haka kuma ban tilasta ki kashe ba. Saboda aure dai sunna ne mai ƙarfi daga cikin sunnonin Manza Allah S. A. W , kamar yadda ayoyi da dama suka nuna mana:•_
_Allah {{ S W T }} yana faɗa a suratul rum cikin alqur’ani mai girma. “Kuma daga ayarSa ne ya halitta daga garemu mataye domin mu samu natsuwa daga garesu. Kuma ya sanya tsakaninmu ƙauna da tausayi , haƙiƙa wannan aya ce ga ma’abota hankali. “Wannan aya ta tattara duk wani ma’ana na aure a cikinta. Saura namu farfasawa mu auna mugani , shin ma’anar aure da abinda yake cikinsa kuwa kamar yadda Allah ya nuna mana hakan mukeyi. Da farko Allah ya ambaci ma’aurata da ababen samun natsuwa duk anan ya kawo jinsin mata ne. To amma ai mun sani idan har macen bata samu natsuwa ba ? Shi kanshi namijin natsuwarshi ragaggiya ne. Tambaya anan ta ina ma’aurata zasu sami kwanciyar hankali…….?_
Hah. Ci.. Nayi tare da yin murmushi mai ciwo na goge hawayen dake bin idona. Ina ci gaba da kuka. Naci gaba da karatun takardar Inna…..
_Na farko:• a samun natsuwar aure shine hadafin yinsa. Bai taɓa yiwuwa aure ya kasance an ginashi kan wani hadafi sannan ya zamo ɗorarre. Wannan shi yasa Annabi {{ S A W }} bayan ya zayyano kaso na matan da ake aure. Ƙarshe yace “na hore ku da ma’abociyar addini. To haƙiƙa abun nufi anan shine ba wni hadafin da zai haifar maka da cikakkiyar kwanciyar hankalin aure sai hadafin tarayya domin Allah…_
_A cikin aure mai kawo natsuwa kenan. Haƙiƙa a yau munyi sake tare da watsi da haƙƙin junanmu ta yanda takei har wasu abubuwan ma an shafesu daga rayuwar auren sai wajen mutane jefi² mun barwa turawa wanda kuma mu addininmu ne ya koyar damu su. Ina horonki da ki zama mai biyayya , ki zama mai kunya da juyawa abin duniya baya. Kiyi kara ki zama mai haƙuri. Rayuwar gaba ɗayanta haƙuri ce , ki guji yaɗa sirrin mijinki wa kowa da koma waye. Kar kiyi abinda bakiyi shawara da mijinki ba , ki kiyaye fushin shi ki guji ɓata masa rai da gudun duk abinda baya so idan har bai tsaɓawa Allah ba. Haƙuri׳ ki zama mai haƙuri da biyayyar aure kinji uwar masu gida. ?_
_Ki kiyaye munanan kalamai. Karki kuskura ki jiyar da kunnuwan mijinki ɓatattar magana daga gareki. Magana mara daɗi ko muni kiyi ƙoƙarin kare kunnuwan mijinki dasu. Kar kiyi masa:• ƙarya. Ki kula dashi , ki zama mai tsafta , kar kici amanar shi , banda zargi ki guji abokai , karki raina masa iyaye. Ki kiyaye kuma kisan yadda zakiyu ma’amula da “yan uwansa._
_Kinga wa’anan abubuwan da zan lissafo su ? To ki kiyayesu domin sune ke taka rawa wurin rusa aure matsawar ba’a kiyayesu ba._
_Rashin ilimin zamantakewar aure , al’adu , rashin binken halin miji , rashin binciken halin mace , matsalar iyayen miji , rashin tsafta , matsalar dangin miji , rashin iya magana , rashin iya ciyarwa , rashin iya kwanciyar aure , rashin adalci , auren kisan wuta , cin amanar aure , ƙawaye , zafin kishi , sata , gulma , wayar miji {{ phone }} , rashin lafiyar miji wajen gamsar da iyali da itama rashin lafiyar macen wajen gamsar miji , sharrin boka. Ke kina tunanin ni bana sanki ? Taya ma zaki yadda ki fara wannan tunanin ? Tunda kike a duniya kin taɓa ganin uwar data haifa “yarta tace bata santa ne….? Ni ina so ne ki goge da rayuwa ke ɗaya , ki kuma iya haɗiyar baƙin ciki da magance damuwa dan ki zamar da kanki garkuwar rayuwarki. Domin idan yau ina nan gobe bana nan , yadda kike ke ɗayan nan babu abokin shawara ko na bar duniya barakiji wahalar rayuwa da kowa ba. Ina so ne kawai in auno iya girman soyayyarki a zuciyar mijinki. Na gani kuma ni nasan yana sanki dan nayi masa wani abu a abuja. Wallahi nayi tunanin yadda ake faɗar rashin mutunci zaizo ne kawai ya sakeki. Sai baiyi ba kuma nima baimin rashin kunya ko kallon banza ba kamar yadda nayi tunani… Wallahi inajin kunyarki ne , abun nan da nayi muku banyi da nufi ba , yayi ta damu nane banji daɗi ba , shi yasa na fara rubutun neman yafiya kafin mu haɗu dan mashala.Tou dake dashi duk ina san ganinku domin na nemi gafararku , sai kuma kema zamuyi zama na musamman…… sai mun haɗu kafin inyi tafiya_
_Fatima Salis Abbakar {{ Inna }}_
Wata irin ƙara nayi tare da cewa da yaushe ne zamu haɗu ? A ina me zaki ce man ne iye ? Cike da tashin hali ya kallo inda nake yace haba An mata wai meye kike haka ne ? Cikin muryar kuka na raunana murya tare da cewa ƙarshena yazo. Wannan kalma dana furta shine yasa Dikko kakkafawa , wani irin birkitaccen ihu na ƙarayi tare da matsawa inda yake , sautin ihun yasashi ɗaukewa gaba ɗayanshi. Da gudu na fita na gayyato Ashiru , cikin tashin hankali muka dawo tare dashi , shi ɗakin Dikko ya wuce sannan yazo ɗakina , haka yaita mishi shaƙe² harya dawo. Ɗan gajeren tsoki yayi tare da cewa insha Allahu saina mutu tunda dai baki bari in zauna lafiya. Fita Ashiru yayi ni kuma na matsa kusa dashi ina kuka , a gajiye ya jawoni jikinshi idonshi cike da hawaye yace wallahi bana san kina ihu , ki ƙyaleni in huta dan Allah. Kwanciya nayi a jikinshi nace na bari. Gefenshi ya nuna min in sauka daga jikinshi in kwanta , sauka nayi na kwanta ina kallonshi dakel ya lumshe idanuwanshi cikin yanayin jigatuwa kiyi bacci , rufe idanuwana nayi hannuna a saman gemunshi.
Bayan wani lokaci mai nisa ya sauke ajiyar zuciya tare da sauke hannun Sultana daga jikinshi. Wayoyinshi ya ɗauka ya fita a ɗakin. A gefen gado ya ajiye wayoyinshi bayan yaje ɗakinshi sannan ya wuce toilet kai tsaye. Wanka yayo ya fito ɗaure da rigar wanka yana tunane² , shi kaɗai yasan yadda yakejin rayuwarshi da kuma yadda yakeyinta a daddafe. Taƙaitaccen tsoki yayi tare da zuwa wurin wayoyinshi dan ganin mai kiranshi , Sharifa ce. Ɗauka yayi ba tare daya bari tayi magana ba yace yana zuwa….
Ajiye wayar yayi ya matsa wurin madubi. Kamar mace yaita ƙwasƙwarima , yana gamawa yabi kayan da zai saka ya bulbulesu da tulare shi zaije zance. Kallon kanshi yayi sosai a madubi shi kanshi yasan haɗaɗɗe ne shi ɗin. Murmushi yayi kaɗan tare da ɗan shafa gemunshi da bayan hannunshi na haggu sannan yayi kallonshi na gefen ido mai tabbatar da shi ɗin cikakken ɗan duniya ne.
Taf yauma Sharifa ɗif take ta ibi wuta sosai. Har bata iya tafiya sai layi takeyi , ga wasu irin kaya data saka kuma ko breziya bata da , kaf halittar surar ƙirjinta babu wanda baka gani kawai kamar buɗe yake. Full light yayi a dai² lokacin da yayi parking. Dogon kallo yayi mata daga cikin mota inda sukayi zasu haɗu dan yau ba g r a aka haɗe ba. Wasa yayi da fitilar mota ta nufoshi tana rangwaɗa , tana isowa ta wani kama murfin mota ta inda yake ta buɗe , rufe ta da faɗa yayi wai ita wata irin jaka ce ? Haka ta ratso duniya ta taho kowa yana kallonta ? Irin barinkinta zata yi mishi wai Dikko zata runguma , ƙara ƙufulewa yayi dan duk duniya ya tsani ana taɓashi , turata yayi baya da ƙafarshi cike da ɓacin rai yace Dikkon zaki kaiwa hannu eye ? Cikin hayaniya yace kai…… Lallai kin isa yayi maganar yana buɗo duk girman idanuwanshi. Ƙara nufoshi tayi da sauri ta ƙara ƙaddabeshi , ta ɗauka shiru zaiyi ya fara aiko numfashi kamar yadda Mai gilashi ta faɗa , sai taji karatu yasha ban². Da tsiya² ya fitar da ita jikinshi dakel. Kafin ya fito mota ta ƙara komawa ta cakumeshi , kai……….. Da Allah ki daina riƙemin jiki , riƙo fuskarshi tayi tana matsar da nata kusa da nashi. Tureta ya ƙarayi da ƙarfi tayi baya. Da sauri yasa hannunshi aljihu ya ciro cingom kasancewar warin sigari da sauran wasu kayan mayen da yaji warinsu daga bakinta zuciyarshi ta tashi.
Tsalle tayi ta anshe cingom in tasa a bakinta wai yaci daga bakinta , kakarin amai Dikko ya farayi yana matsawa gefe tare da riƙe bakinshi. Caɓoshi tayi ta baya , aiko kamar jira yakeyi ya kakkaɓota ya fara kwallo da ita , saida ya bata kashin bala’e ya shige motarshi yai tafiyarshi ya barta kwance a hanya tana kuka.
Tsoki yayi tare da ɗaukar wayarshi dake wata ƙara zutt². Yusra ce , reject ya latsa yana gunguni. Cike da ɓacin rai ya koma gida duk saima yaci uwar matan nan dan ubansu , kawai ma dan ana magana dasu zasu ɗaukeshi wani daƙiƙi ? Bari har itama mai turo kanta tsirara zaici uwar ubanta ta sake zuba mishi banzayen hotunanta a waya saiya kasheta….. Ya faɗa yana kaiwa gado harbi da ƙafarshi. Dama su mata ma basu da wayau jira suke ayi musu magana su fara rainawa mutane wayau. Kamar shi ? Sai kace wani sa’ar wasansu ? Shi waccan jakar yarinyar ma zata wani daƙune ? Jinjina kanshi yayi da damuwa yace sai kace wani jaririn da yazo inda aka daɗe ana addu’ar samun shi , kai wallahi ya raina kanshi da har shi wata daƙiƙiya zata runguma. Tuno yadda Sharifa ta kasance a jikinshi da yadda harma ta samu damar tallabar mishi fuska , duk yana ina ? Aikin me yakeyi ina zamarshi ? Aiko wallahi da bai daketa ba har abadan duniya da baida kwanciyar hankali , tsoki yayi tare da cewa duk dai haka ta moremin wallahi…… Balgazar mace. Haka yaita masifa shi ɗaya a ɗaki dama tusa hali bare anci wake. Fushin mutum ɗaya ke sa idan yana fushi yake haɗawa kowa da kowa , wanda yasan anayi da wanda baiji bai gani ba , ai kuma kunsan laifin wani yake hucewa akan kowa. Yau duk wata macen dake cikin wayarshi Sharifa taja musu anyi blocking insu , anyi adding nasu zuwa blacklist. Wato shi harkarshi ba baƙin ciki bajin haushi sabgar Katsinawa.
Dikko shine ya shiga yai ruwa yai tsaki aka ɗaura auren Jiddah da Yazeed. Rabiya ta labarta mishi komai tsakaninta da Yazeed iyakar abinda ta gani , hankalin Dikko kuwa ya ɗagu domin shi yasan waye Yazeed. Sadaki da lefe har kayan ɗaki shine yayi dan Yazeed yace bashi da kuɗi , Jiddah ta faɗawa Dikko ita ta bada kuɗin aure. Shine Yazeed yace ɓarayi suka sace kuɗin. Andai ɗaura aure amarya ta tare a gidan angonta…… Ita kuma tana lissafin kwanakin fitowarta da ko nawa ga wata zata koma gidan Dikko.
Hafsa. Duk maganin da akayi ma Hafsa a asibiti hannu yaƙi ɗauka bare asa ran samun sauƙi har zuwa matakin warkewa. Bayan dogon bincike likita ya tabbatar Hafsa tana da ciwon shiga. Cire hannun shine maslaha inji malamin asibiti dan idan ba’a cire shi ba matsalar zatafi haka injisu. An cire mata hannu dai² gaɓa.
Amisty kuwa kafin ta gama warwarewa Momyn Hafsa tasa aka cafketa. Bayan tasha shegen duka aka tambayeta kuɗi tace babu , a yadda su “yan sanda suka fahimta Amisty tana da damuwa a ƙwaƙwalwarta. Haka suka gogawa Momy bayani dole tasa suka saketa dan Amisty ta samu ɗimuwar tunani. Amma duk wannan bai ishi Momy ishara ba saida ta siyar da gidan iyayenta da gidan Amisty na Qerau. Amisty dai ga hauka ga kuma yawon haya…. Bariki kuma ta kama gabanta , sheɗan ya fita a kanta ya sake sheƙa. Duniyar yanzu ba Amisty take buƙata ba zamanin wasu ne. Haka takeyin juyin ɗan mangwaro ita duniya dawowa take daga rakiyarka da zaran ta raka ka sai ta dawo ta sake raka wani halakakken wanda sheɗan yayi ma tusa a zuciya.
Halima dai ba kowa bace wannan amarya sai ƙanwar Hadiza. Wata garɗamemiyar budurwa ce takai shekaru 27. An tura anyi ciniki amma bata samu shigewa ba , anyi addu’a an bada sadakar ƙuli da alawa amma abu ya gagara dan haka ta shiga ta fita har gidan uwayen mijin Halima ta basu labari irin uƙubar da take ba ɗansu. Nan fa dangin miji suka fara cacai² , akai ta faɗo baƙin halinta , raina dangin miji uwar miji raina miji da baƙar rowarta. Itama dai Hadiza ta kawo nata sharrin ta raɓa da “yar ta² barikin dai ta samu aka siyi kanwarta. Shima Abdul haka aka ɗaurashi kunsan maza basa wuce tayin mace kamar almajiri ne da sauran abinci… Cikin ikon Allah yaga yarinya kuma tayi mishi. Gata “yar kyakkyawa kamar Rabi’atu Aminu Maman Dee. Mai kunya da laushin magana kamar Asmeenat Zeeyan. Mai kyawun kallo da iya murmushi kamar Aunty Musa Qerau. Ga iya wanka mai ɗaukar hankali kamar Hauwa Musa Qerau. Ta iya adon lalle mai burge kamar Zainab Abbakar Matawalle haka ta iya gyaran kai kamar Fati M Ga magana da salon ɗaukar hankali bakinta kamar Ruƙayya Sharif Maulaya hassan. Kai tafa haɗu haɗuwar haɗewa , idan zatayi kallo tanayinshi ne da salon bugun zuciya kamar Rabi Musa Qerau. Bari dai in daina zugata haka nan karta kamo Halimatu Musa {{ Uwa }} haɗuwa.
Abdul da yaga yarinya tayi mishi sosai dan haka suka antaya a duniyar munafukar soyayya. Ita kuma Hadiza kullum tana liƙe da gidan Halima tana ƙara kakkaɓowa “yar uwarta sirrin gida. Har daren ɗaurin aure duk suna tare da Halima sunajin hukuncin da zatayi wa amarya. Da taji saita dokawa “yar uwarta waya suyi shawara su san hanyar da zasu hudowa lamarin. Ina wanda ya raba faɗa bai kallo ba , sun haɗu sun haɗa ƙarfi da hikima duka ɗaya zasuyi su zare Halima a gidan miji idan tayi wasa saboda sunyi mata ƙofar raggo , ita bata sansu ba , su kuma suna tare da ita suna shirya mata gadar zare.
A kusa da gidan Halima Abdul ya kama haya ya ajiye amaryarshi Amina. Tunda bai shirya aure ba hawoshi yayi kai tsaye. Anan fa akayi uwar watsi , Halima ta fara bori da wallahi² data tabbatar amarya ƙanwar aminyartar ce. Nanfa fitina ya ɓalle suka kashe santa aikata ruwan bala’e babu ƙaƙƙautawa , Hadiza ta biya kuɗi ta ibo hayar “yan daba tace duk matar data sake cewa tuf ko ta leƙo daga gidanta idan dai ba Allah sa alkairi ta fito ba aradu su yagewa koma waye baki. Dan su sunaso suyi hidimar biki cikin natsuwa , a gefe kuma ga masu DJ sunata wulakanci da waƙoƙi na habaici umarni daga Hadiza , c b n gidan kuɗi. Can naga sabbin kuɗi suna wali bisa iska. Shagali wanda ko a bikin Halima basuyi irinshi ba. Hadiza kuwa a yanzu zasuci na ƙurya da bakin gado. Ballagazar mace ga ƙarsheki.
Tunda Mardiyya ta haura katangar maƙabarta ta ibi santa. Mota tahau ? Da ƙafa taje ? Oho , candai Yola ta yadda zango , hauka tuburan marar gane matsayin ido da ciki. A gidan mahaukata aka ajeta shine suka shiga neman “yan uwanta , bayan an samosu aka danƙata wa iyayenta , sai suyi ta magani har a dace , wa gari ya waya ? Ruwa ya ƙarewa ɗan kada bai gama wanka ba.
Amarya Jiddah kuwa an wani saki baki aci kazar amarci. Ai a ranar ango bai kwana gida ba. Tou dama me zai tsaya yi ne ? Abinda za’a tsaya danshi ayi murna da ɗoki ai ansanshi tun a gida. Saboda shi dama za’aci kazar tou yabi ya wuce , anyi karatu an tusa feji , allonta kawai take wankewa gwargwadon yadda ta biya karatun. Sati ɗaya da “yan kwanaki ta fara zance tafiya , Yazeedu yace ina ? Ai yadda baya tare da D ‘ K a yanzu gara ma yayi ƙoƙarin riƙe auren “yar uwarshi yasan ya mishi sauƙin gani. Haya² ta taso da rashin kunya ya nannagawa banza duka na fitar misali. Wannan shine horonta duk idan ta sake zance saki….
Duk wannan sa’a da Sharifa ta gwada na shawarar da mai gilashi ta bada taga ta faɗi ? Bata daddara ba. Dan haka ta faɗawa Mai gilashi Dikko ya rufeta a waya. Mai gilashi tace mafita na ƙarshe kizo makarantarmu ajinmu ɗaya da matarshi kashin bala’e zaki bata , daga nan idan kika daki matar zai nemeki danjin dalili , sai ki faɗamin ni kuma zan baki shawara na ƙarshe. Idan kika daketa zataje ta faɗawa mijinta , tana faɗa mishi shi kuma zai nemeki danjin ba’asi. Yana kiranki ke kuma ba ɗauka zakiyi ba sai ki kira ita Aunty Bilki ki farfaɗa mata maganar da zan faɗa miki idan kinyi dukan. Daga nan zatace kizo gidan gwamnati. Idan kikaje government house sai ki kira Dikko ki faɗa masa cewa kinga kiranshi bakya kusa ne sai yanzu. Zai ce me matata tayi miki kika daketa ne ? Sai kice ai ina nan gidanku ma. Fuuuu zai tako mota yazo , ai kinsan dai dama bawai wani can² yake santa ba suma nashi familyn basa santa. Ai nanfa za’a haɗu a bata rashin gaskiya duk idan kinyi dukan zan faɗa miki abinda zaki ce ya haɗaki da ita Sultanar.
Sharifa tace amma kina ganin wannan ba matsala ? Mai gilashi tace haba Sharifa idan da matsala harna faɗa miki kiyi ? Matsalata ai taki ce. Dole mu haɗu muyi maganin matsala kodan ci gabanmu. Sharifa tace idan aka faɗi fa ? Mai gilashi tace shikenan sai ki sake ƙawar shawara. Sharifa tace tou shikenan. Batayi tunanin matsalar da hakan zai haifar ba……
Hmmm su kuma zugar gidanmu duk abun nan wai sai yau suka zomin gaisuwa. Ƙwansu da ƙwarƙwata babba da yaro babu wanda aka rago har iyaye , jimillarsu dai su sattin da wani abu. Kacaniya kenan , gaskiya nayi farin cikin ganinsu sosai har farin ciki na yaƙi ɓoyuwa. Haka suka shigo wurjanjan kamar an ɓalle garken shanu. Kowa da irin siffarshi. Kai gaskiya Baba ɗan bala’e ne , wannan kwanyaman “ya “ya inama amfaninsu ba ɗaya na zaɓe. Haka suka shigo palo sukaita hayaniya , har bakajin maganar wani. Abinci nasa aka kawo musu. Ɗiff kowa ya ɗauke wuta suka fara caccaka. Gayam². Gurum² taunar nama. Abinci kuma nakai karo suka ci gaba da surutu……
Da hada “yan gidan Baba ƙarami zamu zo sukace basu zuwa. Cacai² gardama ta buɗe , bafa haka sukace ba ku faɗi gaskiya ni nafi san abinda mutum ya faɗa ana faɗinshi. Daga maida magana sai faɗa , har ana neman bugawa. Haƙuri na basu dakel dai suka haƙura , duk lemunan da aka kawo musu kowa cikin jakarta tasa abunta wacce bata da jaka ta matse abunta a hannu. Tashi sukayi wai zasuje su zagaya gida dan kar suje wata rana anayin labari su kasa ƙarda komai. Kamar wata geliya haka nabisu babu inda basu shiga ba a gidan sai ɗakin mai gidan ne kaɗai basu shiga ba. A store kuwa buhun garin kwakin nan suka jawo , kalluba suka cire ba tare da izinina ba suka hau rabo , wai wannan ai kiran tsiya ne wai meya kawo fir’auna aljanna ga gidan wuta. Haka dai sukai ta zambaɗa iskanci suna maganganun irin nasu na “yan cikin lungu. Duk abinda suka gani yayi musu a store sukayi gaba dashi. A ɗakina kuwa cewa sukayi in basu zazzagar kayan sawa. Fa’iza kuwa cewa tayi saidai wasu a basu kaya wasu takalmi wasu jikkuna , kuma wai waye ma nake bawa kwance gasu ? Duk zasu sakamin numbobinsu idan zamu koma sabon gida a basu kayan tsohon gida , weldrop na buɗe na fiddo musu kaya sukai ta zaɓe. Ciki kuwa hada rigunan da Dikko ya kawomin tsaraba suka ɗauka. Nan dai suka yini sai dare suka tafi nayi musu hasafin kuɗi masu nauhi suka kama gabansu….
Kwanan “yan gidan biyu da zuwa Dikko yana kallon hutana na a waya ya karkatomin waya wai insa mishi wannan rigar yau. So ɗaya na kalleta nace na bada ta. Sake zuƙo hoton yayi yace wannan kalli. Ba tare dana kalleshi ba nace wannan ɗin. Haba yarinya wasa kikeyi , wallahi da gaske na bayar da ita , cike da ɓacin rai yace waye yace kika bayarmin kayata………..?
Kar kuji Dikko yana da kuɗi kuce ya tsaya akan wani banzar riga yana surutunshi. Duk iya kuɗin namiji ke mace yafa kamata da Allah ki riƙa abu da lissafi. Tunatarwa ne. Duk irin kuɗin mijinki baifa kamata haka ba gaskiya , ta yuwu kila a jikin wata ya gani tayi mishi kyau ya siyo shima kiyi mishi gayu. Bawai nace ba’ayin kyauta ko karki bayar a , a abunda dai ina nufi a ɗan riƙayinshi haka dai da lissafi.
Domin shidai Dikko a saudiya yaga riga jikin wata “yar budurwar balarabiya. Shine ya hasko idan tashi matar ta shiga a irin rigar itama zata bada irin abinda waccan ta bayar , ina fatan dai kun ɗan fahimceni. Shine ya shiga shima ya samota kalarta da komai da komai dan ayi mishi ado a gidanshi shima. A ita ga matar mai kuɗin banza idan na bayar gobe ya siyo wani. Ita ya siyo domin ke…, bashi da tabbas idan ya koma siye ya samo irinta , ta yuwu a canja kala ko kuma a samu banbancin company. Shin ba’a shiga haƙƙi ba….? Saboda haka idan dai namiji ya siyo abu ya kawo miki lallai yana da dalilinshi……
Ai na baka ya rabaka da abunka. Ni kike faɗama wannan maganar dan kin ɗaukeni abokin wasar ki ? Yayi maganar cikin fushi yana tashi zaune. Ni zan siyo miki abu ki bayar dashi ? Nayi miki magana zaki faɗamin na baki ya rabani da abuna….? Yayi maganar yana saukowa daga saman gado , miƙewa nayi da sauri. Cikin firgitacciyar murya yace idan kika fita sai nai miki shigar bulet………
08/02/2020
*JAMILA MUSA…*
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN…*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa…
*JAMILA MUSA…*
*SAI NA AURI D ‘ K*
🅿 —— 10
Shafin nan daga farkon shi har can² karshenshi. Sadaukarwa ne gareku “ya “ya masu albarka.
*ABDULRAHMAN B ‘ K LAWAL*
&
*JA’AFAR B ‘ K LAWAL*
Ina roƙar Allah subahanahu wata’ala da ya albarkaci rayuwarku. Ya jiɓanci lamurranku ya jiƙanku ya ɗaukaku darajarku yasa ku gama da duniya lafiya. Ina roƙon ubangiji da yasa kuyi kyakkyawan ƙarshe. Allah ya dafa muku ya kareku da kariyarSa , ya tsareku da tsaronSa a duk inda kuka shiga yasa albarka a rayuwarku ya ƙulle idanuwa da zuciyoyin duk wani gurɓatacce daga gareku. Allah yasa ku dace a gidan duniya da ƙiyama. Allah yai muku albarka don darajar fiyayyen halitta Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam. Ameen ya Allah. Duk mai san manzan Allah S. A. W yace amin….. Duk wanda yace amin , ya Allah kasa ya gama da iyayenshi lafiya. Idan kuma sun rigamu gidan gaskiya Allah ka jiƙansu ka sadasu da rahmar ka , kasa can ya fiye musu nan har Babana…. Allah kasa sun huta. Mu kuma ka kyautata namu ƙarshen idan ajalinmu yazo Amin.
Idanuwa na cike da hawaye nace ai dama ba fita zanyi ba haƙuri zan baka. Na ƙarasa maganar ina ƙoƙarin durƙusawa ƙasa. Tausasa murya nayi cike da ladabi na furta kayi haƙuri insha Allah bazan sake ba. Komawa yayi ya zauna danshi yana da karyayyar zuciya , ko yana furta sai na kasheki………. Saina kashe² idan dai zanyi kuka ko yaga na ɓata rai zaice An mata bakijin magana kaza². Da lallausar murya ya furta gaskiya banji daɗi ba. Kuma karki sakemin irin haka daga yau…? Nace tom. Duk abinda ni nawa ne ? Idan dai har nine na siyoshi da hannuna koma miye ko mene ne ko wane iri ne karki kurkusa ki yanke hukunci ba izinina na faɗa miki. Na sake cewa tom. Ni kwanaki da zan aske ya nuna gemunshi ba kuka kikayi ba ? Shiru nayi ina kallon ƙasa kamar mijin da matanshi suka ritsa a ɗakin “yar aiki.
Ke me yasa kikayi kuka ? Cewa kikayi in rufa miki asiri ko ni ina so idan kika ga masu gemu kiyi ta kallonsu ne ? Cikin ɗaga murya yace tou da irin wannan dalilin da zaisa ki kalli wani mai gemun a waje , tou nima irin wannan dalilin ne yasa na siyo rigar nan. Ko an faɗa miki niba mutum bane ba ? Ance miki ni nawa idon bai iya kallon mata ba ? Ko an faɗa miki ni banajin irin yadda kike ji ? Ko an faɗa miki niɗin dutse ne ni da banajin yanayi a jikina iye ? Ya faɗa yana nuna kanshi da ɗan yatsa. Tou irin abinda kikeji idan kika kalleni da yanayin da kikaji idan kika shafa fuskata ko kika zo kika rumgumeni , duk irin yanayin da kikeji idan kina shashshafa ko ina a jikina ni nafiki na wuce na zarce ki jin irin wannan yanayin. Ko sai ke kaɗai kike so a burge ki ? Wannan ai rashin adalci ne, zalinci ne. Ji nakeyi kamar ince miki ban yafe ba. Fashewa nayi da kuka nace Allah ya isa zakayi min ne ? Cikin ɗaga murya yace dan in nuna miki girma da ciwon da naji wallahi akan bayar da rigar nan da kikayi ? Yau da kin sameni akan tsini duk wanda ya tsaya miki da sai nasa kin anso rigunan nan…. Cikin shashshekar kuka nace dan ci baya ? Kece kika ci baya mai shiga haƙƙi miji. Har wasu banzaye sunfi mijinki mutunci , “yan gidan namu ne banzaye ? Suɗin , duk wacce kika gani a cikinsu idan ta dafe kan mijinta shiru zakiji. Irinki ne masu duhun tunani mutane ke rabawa da miji. Kila ma kin basu labarin ni na siyo sai su ɗauka , ke baki iya sakawa su bara su riƙa sakowa suna burgeshi , kina can kwance kina yarinta za’a buga wasan a barki da hauka. Idan ma kika ɓatamin rai na hasala da yawa duk shegiyar dana sake gani a gidan nan saina bata kashin bala’e. Me yasa nake baki kuɗi ? Dan kiyi rayuwarki karki shigamin rayuwa kije kiyi huɗɗarki da mutanenki ko na hanaki ? Ko nace karkiyi ? Ban takura miki ba ban shiga rayuwarki ba An mata , na barki kiyi sabgar gabanki dan kema ki zama mai “yan ci kamar yadda ko wane ɗa yake da “yanci , amma kin ɗaukeni kamar wani lusari ko an faɗa miki tsoro yasa na barki kike abunda kika ga dama ne ? Bana san na matsa miki ne ke kanki idan na takura miki rayuwar gidan nan bata miki daɗi. Nawa ne ba naki ba.
Ko kayanki ne ba nawa ba iye ? Ke kika siyo su ne ? Nine na gani ya burge na siyo domin ki , ki saka nima inji shauƙi inje irin yanayin da kike shiga idan kika kwanta jikina , ke wai bakya gane komai ? Komai sai an fito ɓaro² an fallasa miki saboda kina da jakin kwalwa. Da kinga na fara sauke²n kaya baki da zama lafiya. Kar in bada miki wannan , kina so kiga na saka wannan , ke wannan yana miki kyau. Ko nace bana sanshi sakani gaba kike kitaimin kuka ke mai idon fitar da hawaye. Shin yanzu ke ba da kanki kike fidda kayan dake baki ra’ayinsu nawa ki bada su ? Duk yadda nake san abu idan kika ce baki sanshi dole haƙuri nakeyi dashi. Duk yadda bana san abu idan kika cemin kina so haƙuri nakeyi. Sanyaya murya yayi yace duk dai dan in burgeki. Amma da yake baki da adalci babu abinda ya dameki inyi farin ciki ko kishirya haka. Ki burgeni ko karki burge kedai kanki kika sani burinki in miki kiji daɗi. Wannan shine rayuwar farin ciki…..? Ya ƙarasa faɗa yana kaiwa katifa duka , baki da adalci sam² kullum baki da burin burgeni saidai neman hanyar musgunamin. Tou daga yau tunda iskanci ne abun naki na rantse da girman Allah kika sake ɓatamin rai saina lalata miki fata…. Tom. Zazzaro ido yayi yace karki cemin tom akan komai kice bazaki ƙara ba………. Ya faɗa yana rufe idanuwanshi. Da sauri nace bazan ƙara ba insha Allah. Hanya ya nunamin in fitar mishi daga ɗaki. Da sauri na fice na barshi yana ta mita…..
Tsaye take a kitchen tasha ado kamar zataje gasar wanka sai fitar da wani irin sirrintaccen ƙamshi takeyi. A gabanta kuwa kiret in kwai ne take ta dandaƙa ba sassauci. A gefenta kuma “yar matsadiyar wayarta iphone ce keta rero waƙoƙin turanci ita kuma tana rakiyarsu da bakinta. Wata irin zundumemiyar ashariya Yazeed ya ciko bakinshi da ita ya zundumawa Jiddah dake ta farfasa kwayaye……. Wandon jikinshi kuwa sai riƙonshi yake a hannu yana ƙoƙarin ɗaure belt dan wandon ya tsaya. Kuturmar dumadu…..? Kwan zaki cinye dan uwarki…… ? Waye yace miki anacin ganyen filawar da aka jera dan ƙawata ƙawar gida ? Cike da masifa Jiddah tace kai kaima dan uwarka ! Ko an faɗa maka shiru² tsoro ne wai iye ? Idan baka so inci kwai kawai ka bani sakina inyi gaba ai muma a gidan namu anacin kwan. Cike da ɓacin rai Yazeed yace kin taɓa ganin majiyyaci a maƙabarta ? Ai asibiti shine majiyyaci yake zuwa dan ganin likita , shine zai dubashi ya gano ciwonshi ya bashi magani sai ya samu waraka da izinin Allah. Maƙabarta kuwa gidane na matacci , wannan gida da kika ganshi nahir jinyace daga gareni idan kuwa har kika fita a gidan nan gawarki ce aka fidda. Ni bana aure dan saki saidai inci uwar fatar mace tai iskanci. Aurena yana nan ram² baya girgiza no saki an no barkono yaja yaji da bakinshi. Ni nan da kika ganni matakin iskanci na taka bansan iyakar nahiyoyin rashin kunyar dana ƙyetara ba. Ɗan iska ne ni na nunawa a satilayit banda mutunci ga muni banda kyau ko nai wanka….. Da ke a tunaninki na aureki domin kisan wuta ? Nine ma zaki kashe wuta dani ? Tou yanzu na kunnu nayi ta ci gaba da ci daga nan har a tsaida ƙiyama. Bana sanyi bana siƙewa bare kuma kiyi tunanin zan mutu.
Ai wannan auren ko auren da aka daura a coci bai kaishi ƙarko da aminci ba. Yaci uwar auren coci ya zarta na kotu kuma. Yadda bakya tunani auren ya wuce inda kwalwarki bata iya hasasowa saboda ya linka auren zobe dan auren Yazeedu auren kabari ne. Kuma haka gidana yake idan an shigo ba’a tafiya saidai idan za’a tafi kabari , nunawa yayi da hannunsa yana ci gaba da cewa wannan nasan zahiri ne tafiya ɗaya ba dawowa. A bakin tarihin rayuwarki waye kikaji ya shiga cikin ramin kabari ya fito ? Tou ba’a fita sai ranar da ƙiyama ta tsaya , wato ranar yauma tubalasra’il. Ranar girbe abinda ka shuka , ranar da uwa bata gane ɗanta miji idan yaga matarshi zaisha kwana. Tou gidan nan maƙabartarki ne a nan kabarinki yake idan kinga kin fita a gidan nan mutuwa kikayi dan ƙaniyar iskanci. Ya ƙarasa maganar yana shaƙe wuyan Jiddah tare da cewa biyamin kwai na….
Yana shaƙe da ita yaci gaba da cewa shin bana faɗa miki abincin gidana adon idon duniya ne ba ? Dakel tace e , Yazeed yace amma kika ce kinji kin yadda ko ba haka nayi dake ba ? Cikin jin zafi shaƙa tace haka ne. Riƙe wuyanta yayi da hannu ɗaya yace duk kwai ɗaya dubu ɗaya na siyo abuna. Kuɗin mota da kuɗin kunna gas a gidana ba ranar sanwa ba. Bakina dana ɓata wurin ciniki , kin yanka albasa ba’a kan ƙa’idar ma’ikata ba. Zagin miji wanda babu shi a kundun tarihin musulci zunubi ne mai girma , domin wanke kai daga wutar Allah neman gafara da biyan kuɗin diyya dubu ɗari. Cin zarafin miji kin daƙile min guyuwa akan ƙalubantar ciyarwa kince gidanku akwai abinci. Domin samun sassauci kwanciyar kabari cikin salama zaki biya dubu hamsin domin wanke kai daga bugun mala’eku. Naira budu tamanin na neman yafiya ne domin kiyi kwanciyar kabari cikin salama. Da hannun da bai riƙe wuyanta ba ya fara lissafun kuɗin a wayarshi.
Yana lissafa kuɗin yake cewa yau kuma anyi buking ina a wasan danbe ki biya kuɗinki da wuri ki yanki tikiti tun kafin ƙarfina ya ƙare. Ki bada budu goma tunda ke ta gida ce , zan siyar miki dashi ne akan farashi mai sauƙi amma ba haka ake siyarwa ba dan kada jibi ince miki dubu talatin ki fara wallahi² , cikin wahalalliyar murya tace bana so. Basai kinyi muradi ba kuɗin gado da katifa na yafe miki tunda ke matar gida ce. Kuɗin kwai naira dubu talatin. Cikin kakari Jiddah tace ai ba duka naci ba , damuwarki ne wannan inji Yazeed yaci gaba da cewa + naira dubu biyar ta-ra akan kin tari numfashin miji yana magana kina sako mishi baki….. Duka abinda kuɗinki suka kama dubu ɗari biyu da tis’in da biyar , amma ɗari 3 zaki bayar hada ladar lissafi dubu biyar , ya ƙarasa maganar yana sakin wuyarta ya turata can baya. Riƙe wurin daya shaƙa tayi tana ta tari , ƙuhul² kamar sakin mayu.
Wai wannan wane irin zalinci ne ? A fusace ya nufi wurinta ya ɗaga hannu yace zan……. Da sauri ta duƙe. Wayarta ya ɗauka ya miƙa mata tare da cewa maza inji alart. Jiddah na kuka tayi ma Yazeed transfer. Dariya yayi bayan yaga tabbacin kwanciyarsu a asusun bankinshi ya rumgumeta yana sumbatar ta. Ina sanki haɗaɗiyar matata abun alfahirina bugun zuciyata , gaskiya yafa kamata azo a ƙulla hanyar neman wasu kuɗin kafin asusunki yayi shiru , ya faɗa yana fita daga kicin in sweetheart kisha shagalinki lafiya , lambar lokacin ki shine. 0 3 4 9 am. Wato yana nufin lokacinta da zai bata na katin danbe da ta siya shine 03:49am ya yada mata katin yayi gabanshi……. Kuka Jiddaah tai tayi tana Allah ya isa. Saida tasha kukanta har ta gode Allah ta kira Nabeela ta rattafa mata komai tayi ƙari akan abinda yayi mata ta kulle da cewa kuma yace baya sakinta. Abunka da ɗan uwa Nabeela taita kuka ta kira Rabiya ta faɗa mata. Rabiya ma taita tsinewa Yazeed wai zata faɗawa Dikko wallahi sai an kaso auren nan , yasan ashe Yazeed tsinannen Allah ne yasa aka haɗa auren saboda cuta irin nashi kaza² , taya Yazeed zai kulle yarinya a gida ba abinci yana bata gwale² sai duka ? A yinin ranar haka sukai ta yaɗa magana tsakanin su “yan ɗakinsu.
Daga baya suka bawa Jiddah haƙuri tare da tura mata kuɗi ta siya abinci kafin a samu mafita saifa Yazeed ya sakota ɗan iska mara mutunci anyi masa rana zai yiwa mutane dare. Rabiya da kanta tazo har gida taba Dikko labari , mugu yaji mugunta yasha dariya harta zarce musali. Saida yasha dariyarshi sannan ya turawa Sultana saƙo tazo palonshi , bayan naje yace Rabiya ta maido labari baya. Ran Rabiya kuwa ya hayaƙa taita zagin Dikko , waishi wane irin ɗan iska ne ? Ta faɗa mishi ciwo yana ta wata dariyar iskanci ? Cikin dariya yace bakinki ko nawa ? Fuuu Rabiya tai zuciya ta ɗauki jakarta , Dikko yace Hajjaju tsaya da Allah , naƙi in tsaya tunda kai ɗan iska ne. Allah ya baki haƙuri karki tafi. Tsoki tayi ta tsaya a bakin ƙofa , daga ni harshi duk fita mukayi , jingina yayi da ƙarfen bene ya ɗora hannuwanshi ta baya ya rakuɓe kamar mijin ɗiyar soja da yayi dukawa ita a barek kuma itace da gaskiya , haɗe rai yayi yana kallon Rabiya nima kusa dashi naje na tsaya ina kallonshi. Gyara bakinshi yayi shima ya kalleni. Murmushi nayi shi kuma ya sake gaggaɓewa da dariya…..
Rungumeshi nayi nima ina dariya , safko hannunwan shi yayi ya riƙeni. Wai anci ƙaniyar iskanci mata na buking in mijinta , ita da haƙƙinta a nuna mata fin ƙarfi , kam balasti nan taff ya jinjina kanshi da mamaki cewa “yan iska duniya basa ƙarewa ko kunyar faɗa ma baiji ba tirrr. Dariya itama Rabiya tayi amma badan ranta yaso ba , haka dai da damuwa , ciki muka koma duk a palo muka zauna. Dikko yasa aka sake karanto labarin ni da bana nan naji da kaina.
Shi kam Yazeed ma baida mutunci ko tsoron Allah bayayi ? Taya matarshi zata siyeshi dan yayi kwanciyar aure da ita ? Duk a raina nayi magana , tun daga wannan bansan inda zance su yaci gaba da tafiya ba , hankalina da tunanina kuma ya koma karatun rayuwa ta , ta baya. A gajiye na kwanta jikin Dikko ina ƙara hasko rayuwa da yadda ita kanta rayuwar tayi min hajijiya.
Maganganun Dikko da kuma dalilinshi na sawa a karanto min rayuwar gidan Jiddah. Shima wannan duk hikima ce , yana so inyi gyara ne a inda nake da matsalolin zamantakewar aure. Sai zan tukan Inna , taƙaitacciyar jiyar zuciya na sauke dakel a hankali na furta Allah ya jiƙanku iyayena yasa kun dace da kyakkyawar makoma. Saukeni Dikko yayi daga saman jikinshi zaije ma Rabiya rakiya. Nidai ban bisu ba nace ta gaida gida ina daga kwance….. Duk inda kake ka godewa Allah kuma ka nuna haƙuri da jajircewa. Bazafa a gane matsalar ba sai tafiya tai nisa. Allah ka rufamin asiri ka ƙarawa mijina haƙuri da halina , Allah kasa in daina mishi abinda baya so.
Tun daga wannan rana kamar anmin allurar natsuwa haka na zama wata baiwar Allah , har abun ya dami Dikko danshi a tunaninshi ko banji daɗin maganarshi akan “yan gidanmu shiyasa nake fushi ? Me yake damuna ne ? Ko banda lafiya ? Idan yayi min wani abu banji daɗi ba inyi haƙuri kuma in faɗa masa miye bazai sake ba. Nace masa babu komai amma hankalinshi ya gagara kwanciya.
Ko yau a makaranta burus² nake kamar garin kwaki bai jiƙu ba. Shima daya kawoni makaranta dai ranshi bai mishi daɗi ba , wai shi baya san wannan fushin da nakeyi , dan Allah in saki raina mana , ya zanta haɗe mishi rai shi bayajin daɗin gani na a irin wannan yanayin , ko na gaji da ganinshi yaje hutu idan naso ganinshi saiya dawo ? Nace ba komai , tou kiyi murmushi mana An matana…… Yayi maganar yanayin murmushi mai tafe da yaudararren kallonshi. Kaɗan na yaƙe bakina tare da kwantar da kaina gefe kaɗan nayi mishi ɓarawon kallo kamar liman yaga wawan zama , so kike dai in koma gida da baƙin ciki ko ? A , a , tou wai meke damunki ne ? Ba komai , cike da ƙunar zuciya yace An mata wai yaushe kika zama munafuka ne ? In banda munafurci ni zaki riƙa munafurta ? Me nayi miki ne iye ? A kwana biyun nan kina ta ƙoƙarin riguzamin farin cikina laifin me na aikata ? Gaskiya ce na faɗa bayan nan miye aibu na iye…? Babu , hmmm yayi tare da gyara zamanshi yace jeki……. Fuuuuu na fita ban rufe motar ba. Bin bayanta yayi da kallo. Banyi tafiya mai tazara ba na dawo raina a duƙunƙune nayi ma motar shigar bulet nima. Da sauri yaɗan ja kanshi baya. Kusa dashi na tsallaka na dafa hannuna a jikin gilas in murfin motar da yake zaune ɗayan hannuna kuma a saman kujerar da yake , na sakashi tsakiyata kenan , wasa nayi da girarena sannan na kakkaɓa mishi ido da logo mai ibar yanayi muuuuuu muah nayi masa a bakinshi. Wahalallen murmushi yayi tare da fitar da sautin numfashi a gajiye yana ƙoƙarin riƙoni na sauka a wurin na zauna saman kujerar mai zaman banza sannan na fice daga motar….. Murmushi yayi tare da rufe murfin motar yaja yai tafiyarshi.
Cass² coss….. Gaba ɗaya class in idon kowa ya koma kan Mai gilashi. Tana tafe tana wata irin girza mai tada hankali ta huro kwan cingom ta ciki ta hankaɗe kanta sama ga ƙaton gilashinta ya cinye rabin fuskarta. Duk lokacin data ajiye ƙafarta domin taka tazara wurin tafiya sai kaji kacau , tana ɗagawa zakaji ta sake wani irin kuka cauu coss , buɗe hannayenta tayi kamar zata rumgume wani take cewa. Aini kwarƙwassa ce tashi mai gida da gidanshi. Turnuƙuƙiy faɗan ibilas yaron idan baka sha duka ba kasha ƙura. Zama tayi a saman decks ta fara kirara kanta tana coka ma wani malami zagi. Malamin dake cikin ajinmu yace mata ta fita…..? Sch bag inta ta ɗauka ta fara tako. Wai su sune jihar katsina , kuma taurari a cikin duk wata jaha dake nigeria , tana alfahiri da karuwancinta domin shi ya kaitagacin nasara , tana alfahiri da tarihinta tana bugun ƙirjinta da zuwa nahihohin afirika da tayi ta silar kasuwancinta , duk wanda ya nemi ya ƙalubalantar mata sana’a zata sa a ɓatar dashi a gari. Malamin yace ta fita karta mishi ranshin kunya…..
Saida ta fita gaban aji ta kallo “yan kilas tace. Duk ɗalibi ko ɗalibar dake ajin nan wai tasan asalin kowa da tarinhin rayuwarshi har principal , shima malam dake tsaye tasan ko ƙafa nawa ne da ɗigo nawa na gidanshi {{ ƙarshen sani kenan }}. Kuma duk marecen ranar lahadin ko wane sati yana bi ta wurin gidan “yanci yana wucewa. Malam ci gaba yayi da rubuta babu a saman allo. Tsoki Mai gilashi tayi cewa idan yace ƙarya ne sai in faɗa mishi cikin motar da yake zuwa…. {{ furuci ne na “yan tasha , tana nufin karuwanshi , shi ya gane yaren amma “yan aji basu fahimci yaren ba sai mu damu ka ɗan karanta karatun bariki }} yo ai mu munsan komai wallahi shiru kawai muke muna ƙyalewa , wallahi babu wanda ya isa yasa naci gurasa inta wani wahalar da kaina wurin neman kayan haɗi ni ba mayunwaciya ba , ra’ayi ne abun ba muradi ba , bana ra’ayinta ne kwata² bare inci ta wahala tayi ta gurjemin makoshi , masu ra’ayi sai su siya suci ko ba ƙuli nasu ra’ayin ne ansa a haka tunda duniyar tana da faɗi biyan buƙata ga masu buƙata. Ba dalili na tattauna goro ni banci sigari ba , “yan aji…… ? Iye , shin ana dole ? A , a , gaba ɗaya suka ansa matsuwa da rashin wadatuwar muhalli kesa masu bada gidajen haye faɗa girman gidajensu dan suyi kasuwa. Amma a tunani na ra’ayi ne rayuwa ɗaki ɗaya da wani , babu abinda zaija min haɗiyar kwaɗo ina kallon kifi. Kuma bari mutum ya sake kai ƙarata yaga yadda zansa shi biya karatun bebe dan a tafiyar ai ba dole , kuɗi mutum yake bayarwa a bashi ɗaki a hotel idan har aka samu matsalar ruwan bayi ko rashin wadatuwar hasken wutar lantarki ƙorafi yake a canja mishi wani. Da lafiyata bani rayuwar tsohon gida bare rufin daya sha “yan dabaru ya faɗo ya kasheni. Kallon rainin wayau tayi mishi tare da cewa wutar lantarkinka bata da haske idan an hana kuwwa ai ba’a hana tsalle ba. Ka , taga ni anan nasan inda zan tarfaka.Tana faɗin haka tabar ajin. Shi kuma malam ya fara zage² yana fidda mutane waje.
Nima gaggaɓewa nayi da dariya , na farko dai su matan aure ba’a dukansu kuma ba’a zaginsu , ƙa’idar makarantar ne saida a haɗasu da mazajensu suja musu kunne idan kuma aka wonasu da yawa za’a koresu daga makarantar. Ci gaba nayi da dariya sosai ina kallon Malam domin dai maganganu ne masu zafi ta faɗa mishi a hikimance irin tasu ta “yan tasha. Kenan shi malam yakai tayin kasuwarshi ne wa Mai gilashi taƙi yadda , kamar yadda take nufi bai da gudun tafiyar dokin da take so , shine taƙi ansar tayinshi shi kuma yakaita ƙara yana goga mata laifin ƙarya….. Kallona yayi tare da cewa nima in fita in bar mishi aji. Ta window Mai gilashi ta leƙo tare da cewa fito in baki labarin yadda yake tafiyar da nashi dillanci. Cewa yayi in zauna. Ƙin zama nayi na fice waje nima , ina tahowa yace zan faɗawa mijinki kin fara abokai marasa tarbiya. Daga waje Mai gilashi tace shima Malamin baida ita…..
Har na fita waje ina dariya , dariya Mai gilashi tayi tare da cewa ɗan iska tsoho ɗan nakusa exp kai….. ? Ɗan an rubutamin best before ritayar….. Ta ƙunduma wata irin ashariya ta “yan tasha masu lasi. Leƙowa yayi yace mu tashi daga nan. Kallona yayi yace wallahi saiya faɗawa mijina iskancin da nakeyi. Mai gilashi tace kafi zuciya sauri kuma duk saina tona muku asiri , ni zan turo nawa shugaban har makarantar sai yasa an rufe munafikan banza kuci tuwon gidanku kuci na kasuwa , na makarantar ma dan haɗama duk sai kun cinye ku uwayen zalama. Ƙara kakkaɓewa nayi da dariya , nan ma magana ce mai jimla ta faɗamishi. Baiyi magana ba ya koma ciki ita kuma ta fara magana…
Izzar karuwanci ake gaya miki Sultana. Karuwanci na ni bana matsuwa bane ba. Na ƙara isa ne da neman suna sai inji nakai wata shegiya. Ga ciyamomi , sanatoci ministoci ham shaƙan “yan kasuwa kiga an nuno kamilin mutum a talabijin yana ta wani bubbuɗe ido dana ganshi nasan na shanye rubutun nayi gaba. Nayi mu’amula da mutanen dani bana iya lissafosu adadin yawansu amma ina da jerin sunayen duk namiji daya haɗa ƙirji dani , sassauta murya tayi cewa idan aka fiddo dubun maza a garin nan ai inaji ɗaiɗaiku ne banja zariar wandonsu ba…… Tsoki tayi cikin takaici tace amma har yanzu gwamnatin jaha bata san da zamana ba. Fashewa Mai gilashi tayi da kuka tana cewa Allah yasa kar in mutum ban shiga cikin talabijin ba , a nuno ni a matsayin tantiriyar karuwar data buwayi kowa a gari. Nidai kawai a jinjina min shine burina , idan ba da list ina zan tafi ba saina faɗo sunan kowa ta yadda lungu da saƙo idan na wuce ansan nima nakai jajirtacciyar karuwa.
Kidai ci bugun banza , dan duk wanda kika faɗo sunan Babanshi da sunan kin zare inajin kafin ki fito daga gidan talabijin ɗin katsina gaba ɗayanta ta haɗu. Yadda ake sara na nuna cewa saidai kiji ance attakabir wallahi gunduwa² zasuyi miki gawarki ma kanta baratayi kyan gani ba. Jakarta ta buɗe ta ɗauko leda mai layi² tana cewa sai ince duk subi layi……. Idan zasu sassarekin ? Ke ana maganar arziƙi kina san kawo min mutuwa wallahi , mtsww anshi nan ni kinji.
Ansa nayi na buɗe , wasu irin duwatsu ne masu masifar kyau kalar burgewa. Meye wannan ? Jigida ce banza. Jigida haka kuma ? Ey mana , irin ta saman ƙuguna ce , sirrin jaka sai kin ɗaura a ƙugunki. Ke ina kika samota ne ? Karki ɗaukeni wawiyar layi kinji. Buɗo idanuwa tayi sosai tace wanna jigidar babbar sirri ce , idan na fara lissafo miki “yan wasan data ciyomin zakisha mamaki gwargwadon yadda kikayi ɗimuwa. Ba katako bane banza duwatsu ne na sirrin rayuwa. Kinga wannan jigidar idan basai ta hana mijinki fitar dare ba kice bamai madubi nake ba. Da ɗan yanayin tsoro nace jigidar magani ce ? Kusa dani ta matso sosai tare da cewa magano…. Maganin ƙaniya… ? Ba’a wanka da ita na farko kenan , sannan na biyunsu ba’a kwanciya da namiji da ita. Maɓalli gareta kawai ɓallewa zaki idan zaki shigar jami’ar gadon aure. Amma mu masuyi dan kasuwa muna kwanciya da ita ne dan ƙararta itace ke buga kwalwar maza a taƙaice. Idan dai kin kwanta da ita tou lallai karkiyi wanka da ita domin kina bata ruwan wanka ta tashi aiki…..
Kuma da kikeji tanayin ƙara bawai itace da kanta takeyin motsin ba , kece zaki cire ƙyashi ganda hasda da baƙin cikin rayuwa kiyi tafiya da isarki. Tashi tayi tai tafiya lafiya lau , tace kinji kukan tane ? Nace a , a , tace an kallo ni ne ? A , a , wani yasan na wuce ? A , a , tou tsaya kiji sharrinta. Wata irin girgiza tayi tare da fara bada matakala. Wani irin kuka jigidar ta farayi coss׳. Sake tafiya tayi tace cakas² cas² , ta saman inda muke ta diro ƙasa cosssssssssssssss.. Cissssssss duk malaman dake kusa da inda muke a cikin aji saida suka leƙo. Dariya tayi tare da cewa ai da gayyarmu muke komai idan mutum yayi kuka muna da tsumman goge hawaye….. Aikinta ga maza ne bayan shekaru biyu take tashi daga aiki. Kyauta na baki wannan idan tayi miki kinji kina muradi saiki riƙa bada kuɗinki a siyo miki.
Zata fara bani labarin abinda ya haɗata da malamin dake cikin aji , da Alhajin da suke gidanshi aka aiko ana kiranta. Tashi tayi ta tafi ni kuma nabi jigidar nan da kallo. Tunani na farko daya zomin shine wasiyyar Inna , da tace kar inyi wani abunda mijina banyi shawara dashi ba. Shin da yaddar Dikko zan ɗaura ko kuwa da yaddar zuciyata….?
Har aka tashi makaranta ina tunani. Yau ba Dikko yazo ɗaukata ba Ashiru ne. Kuma dana koma gidan faɗa. Har an faɗa mishi abinda nayi a makaranta. Shi mutuwa zaiyi , ina zai saka kanshi , kinsamin ciwon zuciya sai na tafi na bar miki gidan nan , badai zaki barni in zauna lafiya ba ko ? Idan nayi miki faɗa kiyi zuciya dani kaza². Duk haƙurin dana bashi rufe idonshi yayi bai saurareni ba. Yaci gaba da masifa shi saiya haɗa kayanshi yanzu²n. Bazaki sake gani na ba sai kiyi duk iskancin da kika dama ? Kuma idan ya kama yarinyar nan sai ya kasheta…………. Tou shikenan kaje ka kasheta , kuma wallahi sai nayi kuka , wayyo………… Allahna na kurma wani irin ihu na nufi ɗaki da gudu. Jin ya daɗe bai shigo ba nasan yayi zuciya. Fitowa nayi har yanzu yana nan zaune a inda yake. Daga sama ban sauko ba nace ai sai ka tambayeni me nayi kuma shi malamin me yayi min ? Kawai anzo an karanta maka ƙarya da gaskiya ka hau ka zauna. Gani ina da hawan jinin masu juna biyu. A asibiti ance na rage yawan damuwa da ƙuntatuwa. Kullum saika ɓatamin rai ga ciki kuma , shin dakai da cikin duk sai kunsa na mutu. Idan kin mutum ko baccin rana nayi in huta da halinki. Ƙaramin yaro yafiki daɗin zama. Mtsww. Shigowar Abbakar palon yasa nayi shiru. Shima bawan Allah a bindige yake da ganin idonshi yaji bala’en mace. Dikko bai kalleshi ba nima kuma ban koma ba ina daga sama duk ina kallonsu.
Magana yayi ƙasa² , banji abinda yace ba saidai shi Dikkon yayi murmushi mai ciwo. Ƙara kasa kunnuwa nayi amma duk iyakar masifa ta banji abinda suke faɗa ba , saida suka gama ƙus²ɗinsu Abbakar ya fita. Yana fita Dikko ya fara faɗa. Wai ashe Abbakar shima ɗanyen kai ne mahaukacin banza baima san matarshi tafi wannan wayau ba ? Wai me yace ne ? Tsoki yayi sannan yace wai matarshi zai kawo kiyima nasiha. Nace mishi tou wallahi ya rufa ma kanshi asiri karma ya kuskura matarshi tasan hanyar gidan nan idan kuwa ba haka ba tou fa lallai zamanshi da ita ya ƙare. Fashewa nayi da kuka cewa wannan baƙar shedar kayi min kuma…….? Ƙarya nayi ? Yanzu ba tsayawa kikayi daga nan kinamin rashin kunya ba ? Na tambayeshi shin tana baka abinci ? Yace min ey , tana maka sannu da zuwa yace ey , tana wanka tana wanke ido tana gayu ? Ey. Rashin kunya take maka ne ? A , a , nace tou idan dai ba tauye haƙƙinka takeyi ba ka koma kaita haƙuri nima haƙuri nakeyi , nace mishi gaki nan rashin duka yasa kwana biyu kin warware.
Shiru nayi na juya mishi baya ina magana ƙasa². Tsoki ya sakeyi tare da cewa Allah dai yaso ban faɗa mishi haka ba , cewa nayi dai yayi haƙuri bance kema fama nake dake ba. Kawai dai haƙuri na bashi cewa mata ai lallaɓasu akeyi , ni abinda ya ban takaici wai ke kallon mai hankali yake miki , har yana tutiya zai kawo matarshi tayi koyi da halinki , baisan nima ƙurmusa min takaici kike ba , yadai kamata kisan abinda kike gashi nan har za’a fara baki gabata. Kace ya kawota in mata nasihar. Ki fara ma kanki sannan kiyi ma wani , yana faɗin haka ya fice daga palon…….
Mai gilashi daga inda aka kirata tana gama abinda take gidansu Sharifa ta wuce. Anan palon gyatimar Sharifa aka zazzage kolin rashin wayau. Daga uwar har ɗiyar dan ɗimuwar tunani Mai gilashi duk ta maidasu wasu lusarai…. Mama wallahi matarshi ce duk take ta shige da fice. Yadda yake san Sharifa kika ga gaba ɗaya ya ɗauke wuta tabbas wata irin gagarumar jifa ce , sai kunyi da gaske kun ƙara miƙewa dan wannan tarayyar da babu “yan al’adu ai nasan da tafiyar bata yuwu ba. Tayi maganar dan bugun cikinsu. Ai nan uwar Sharifa ta saki baki taita hawa gefen layi , ina shi Malamin naku ne Mama ? Sharifa dake full charge tace yai tahiya tayi maganar cikin muryar mashaya tana layi. Cikin faɗa na duniyanci Mai gilashi tace gaskiya Mama kuma da laifinku. Laifin meye nawa ni a ciki ? Saboda Allah Mama kuɗan ƙiyasta dihun kai da wayayyar rayuwa , maza fa yanzu idonsu kallon rana yakeyi , akwai wanda baya san mace ? Taya Sharifa zata riƙa zuwa zance da hijabi dan Allah ? Su wa’annan “yan duniyar ai bakya nuna musu hijabi ba domin wayayyar rayuwa zaki fahimtar dasu kin iya , cake take dan haka maganarta bata fita.
Mai gilashi tace da Allah rufewa mutane baki muyi magana da magabata. Shiru Sharifa tayi Mai gilashi taci gaba da cewa Mama ni ina da Malami acan Zandar aiki yake kamar yankan wuƙa , saidai shi aikinshi sai an ɗebo fitina zama ɗaya yake buga aiki fitina ta koma tayi bacci. Malamin shine kika ga ya ɗauremin ƙugu nake baza hajar iskancina kasuwa². Kuɗin mota dana aiki duk ni zan bayar idan buƙata ya biya saiki bani abu na. Mamar Sharifa tace wane irin malami ne sai an jawo fitina yake aiki ? Izzar aiki ake gaya miki Mama , su bala’en suke kwantarwa dan dai kawai su nuna muku jajircewar su a wurin iya aiki , kuyi shawara sannan ku taro bala’e ni zan tsotse muku duk dafin masifar bala’en. Miƙewa tayi ta jawo Sharifa suka fito waje. Wuri suka samu dan ɗan keɓancewa gefe tace ke jaka bakuzo kun daki matar Dikko ba , sautin maganar kaɗai ke fita amma bakajin maganarta. Mai gilashi tace idan kunga dama kuzo ku daketan , tana faɗi haka tayi gaba abunta.
Shegu masu wayan tsiya , na gano kuma kuna haɗawa da ɗan tsibbunku , fashewa Mai gilashi tayi da kuka tana tafe a mota tana cewa Allah ya tsinemiki albarka Sharifa. Kin cuci rayuwata ƙarshe na ɓuge ga zaman b q , wai me nayi miki ? Laifin nena aikata haka da ciwo a rayuwarki ? Me na tsare miki a duniya ? Haɗu barimi rabuwa idan kowa ya tuba shine kika bini kika daƙilemin tafiyar sa’ar rayuwata. Na rantse da girman Allah yadda kika hanani kema sai kin jibge a gidan mai gadi ko ɗan share²n filawowi. Shima malamin naku zan ganoshi duk sai watse a sarari kuma idan na tashi uwar watsi zan muku yadda za’ayi rabuwa ko gaisuwa babu tsakaninku dashi. Wayarta ta ɗauka ta kira Sultana. Saida ta gama karatun da zatayi ta kashe wayarta tana cewa ki auri D ‘ K in zan gani , dani dake dashi da ita matar tashi an watsa kifi abinci a ruwa……..
Misalin ƙarfe 10:19 na dare. Kai mai karatu ka tuno wacece ni tun farko dana fara baka labarin rayuwata. Na kira kaina da ma’abociya iya shafa turare tsantsar kyau da cikakken body. Da gudu turaren dake jikina ya fita daga jikina ya tafi……… Saida ya zagaye kaf ilahirin gidan sannan ya dawo mazauninshi. Ƙarar tafiyar takalmina da ƙaraurawar da jigidar keyi ya haɗu yake fitar da wani irin halakken sauti mai daskarar da zuciyar duk wanda yaji sautin. Na wanku daga jiki har kayan dana saka. Fili na iba na fara bada taku. Pa – Pi dake kwance yana kallona yace unguwa zakije….? Ƙaniyar anguwa. Dariya yayi tare da cewa kuma wayyayi baci cau ba. Kusa dashi na matsa nace niɗin ce banyi kyau ba ? Dariya yayi tare da rufe idanuwanshi yace waca nike wayyayi… Tsoki nayi cikin jin haushi na koma gefen gado na zauna. Buɗe idanuwanshi yayi tare da cewa baci zuwa ? Ka rufe min baki munafiki kuma bazan sake zuwa dakai ko ina zanje ba tunda kace banyi kyau. Ɓata fuska yayi ya fara kuka yace wayyayi waca ne. Cike da masifa nace ka rufemin baki kuma bana sanka. Shiru yayi ya tura ɗan yatsashi cikin hanci yana kallona. Ka daina kallona. Sauka yayi daga saman gado yana kuka , duk kiran da nake mishi tafiyarshi yayi yabar ɗakin.
Yaya wai Momy tace bata sona. Tsoki Dikko yayi yace ka wuce ka bani wuri. Gefen kujera ya raɓe yana kallonshi cikin kuka yace kaima baka can Pa – Pi cikin ɗaga murya yace fita ka bani wuri nace…. Fita yayi da gudu yana kuka kaima wayyayi na fata dakai , Daga ɗakin Dikko wurin Ashiru ya tafi kai ƙara…… Tashi nayi tsaye ina miƙewa naji jigidar nan tayi wata irin tsuwwa , cassssss……. Burgeni abin yayi na ƙara bada tako ina matsawa jikin madubi. Tana cossss casss. Dariya nayi na samu abin wasa kamar yaro sabon tafiya da takalmi mai tsuwwa.
A wannan yanayin Dikko ya sameni , shi kuma ya biyo Pa – Pi ya dakeshi daya ce wai ya ɓata dashi. Kamar wani gele ya kafeni da ido yana muzurai. Murmushi nayi danni ina cikin shauƙi ne , iska yaja ta baki sannan yace ina Pa – Pi….? Kaje can ka nemeshi mana. A fusace ya shigo ciki , gudun da nayi dan hawa saman gado yaba jidar nan damar yin ihu sosai , cacasss.. Cosss cisss² cuuu. Wahalallen dariya Dikko yayi dakel a gajiye yace menene ke ƙara……? Yayi maganar yana ƙoƙarin riƙo ƙafata. Da sauri na fizge nayi baya. Tsaya in gani mana. Yayi maganar yana fizgoni da ƙarfe. Da sauri ya hanakaɗe rigar jikina ya kunce zanin jikina. Na tsani jigida sai kin cireshi……… Wace karuwa ta baki ita…..? Ni zaki maida mahaukaci ki riƙa kaɗamin ƙaraurawa , da kokawa ya kamata yana ƙoƙarin tsinkawa. Karka tsinkamin abu , saina tsinka ni ɗan iska ne da zaki riƙa min alama iye ? Yayi maganar yana gauramin mari in sakar mishi hannunshi dana riƙe , cizon hannun nayi cike da ɓacin rai nace bazan saki ba , kai……………. Ni kika cizarma hannu. Saina kashe ki…. , a tsorace nace shikenan tsaya baka so ko ? Ey bana so An mata. Shikenan bara in ciro maka , nayi maganar idona cike da hawaye. A tausaye ya kalleni ni kuma na cire jigidar na miƙa mishi. Taro hannunshi yayi dan ansa yana kallona…………..
11/02/2020
*JAMILA MUSA…*
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN…*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa…
*JAMILA MUSA…*
*SAI NA AURI D ‘ K*
🅿 —— 11
Hararata yayi yana jinjina kanshi baraki bani ba. A shagwaɓe nace umm² ina maƙale kafaɗa daga kwance. Tou bani ya sake tambaya a karo na biyu da kwantacciyar murya. Kuka na farayi ina cewa nidai ka barmin kayata idan baka barmin ba aradu kashe kaina zanyi….. Hawowa yayi saman gadon a shagaɓe yace baki iyawa. A hankali na juya mishi baya ina shashshekar kukan ƙarya na rufe idanuwana tare da ɗora hannun damana a saman fuskata. Kusa dani ya kwanta ya fara ƙoƙarin cire hannuna daga saman fuskata.
Juyowa nayi da sauri na riƙeshi. Yiyh…. Yaja ajiyar zuciya da yanayin buƙatuwa tare da lumshe idanuwanshi da shauƙi. Wai me yasa ne…. ? Da yanayin matsuwa yace riƙe jigidarki mayi magana daga baya.
A makare na fito daga ɗakina da sauri. Yau na makara ko kalaci bazan tsaya yi ba. Ɗakinshi na wuce yana ta wani tattare²n wasu “yan guntattakin tarkacen dashi buƙatuwar shi ne , a ɗan zumuɗance nace muje na makara fa. Ba tare daya kalleni ba yayi ɗan gajeren tsoki wai ya manta bai faɗamin ba zaiyi tafiya. Cike ɓacin rai na matsa kusa dashi da hannuna na tambayeshi cewa ina kuma zakaje ne ? Nima ban sani ba saina fita , cika idona yayi da hawaye da siririyar murya nace haba Dikko bana baka haƙuri ba ? Shine kuma zaka tafi ka barni ? Riƙe kunnuwa na nayi a dai² lokacin hawayen idona suka samu damar gangarowa a saman kumatuna cewa dan Allah na bari na ƙarasa maganar ina riƙeshi. Tunda na baka haƙuri sai kayi haƙurin kuma ka bari idan na sake sai ka tafi haba Dikko…….. Na ƙarasa maganar ina ɗagowa daga jiki nai mishi jigataccen kallo.
Kiyi haƙuri bazan wani daɗe ba. Ya faɗa yana taɓa hancinshi da ɗan yatsa manuni. Nima gaskiya idan ka tafi yau zanji kamar ince ban yafe maka ba , taƙaitaccen murmushi yayi tare da duƙawa yana gyara takalmin ƙafarshi. Ci gaba nayi da cewa tou kafa sani tafiya yau gaskiya shiga haƙƙina ne idan ka tafi ka barni zanji irin yanayin daka faɗamin jiya dan Allah , wallahi idan ka tafi gaskiya zan shiga tashin hankali. Da sauri ya ɗago kanshi ya kalleni da yanayin damuwa yace ke meye haka ? Ai gaskiya na faɗa idan ka tafi fa matsala za’a samu. Riƙeni yayi jikinshi ta baya da kwantacciyar murya yace wace irin matsala ƙaramar yarinya? Faɗamin inji mana yayi maganar yana wasa da gashin gemunshi a jikina. A kasalance nace kawai dai zanyi kewarka , mtsww yaja tsoki dan a yadda na fuskance shi ba haka yaso in faɗa mishi ba.
Rufe idanuwanshi yayi cewa taya ake kewar miji ? Faɗomin da me zaki ibe kewa yayin da kike tunowa idan muka kasance a inuwa ɗaya ? “Yar marainiyar dariya nayi cikin yanayin jin kunya nace Dikkkkoooo. Wata sheɗaniyar dariya yayi mara sauti mai ƙarewa da hmmm An mata kenan , yanzu dai idan na fahimceki kar inyi tafiya ? Ey wallahi kawai muyi zamanmi mu daina faɗa na ƙarasa ina juyowa na rumgumeshi. Me yasa baka san jigidar da aka bani ?
Takawa ya farayi ina kwance a jikinshi har zuwa bakin gado yake cewa. Mace ita gaba ɗayanta ƙyalƙyali ce , da hannunshi ya nuna yana ci gaba da cewa tangaram ne saboda su mata an haifesu ne domin kwalliya shi yasa ana haifarta ake mata huje dan ado. Baki ga komai na mace yasha ban²n dana namiji ba ? Maganarta tafiyarta kallonta sigarta da komai nata ya ban²ta. Tayi ado da kayan ado masu burgewa da ɗaukar hankali kamar zinari saboda yana gyara mata jini. Ko cikin duhu kikaji maganarta basai an faɗa ba kinsan ita mace ce , domin zakiji maganarta da sanyi² cikin natsuwa tako nagarta matsayi da kuma aji. Ha kuma maganar namiji yake. Kalli takalmin ƙafata kinga irin nawa da naki da ban²ci , naku masu ado ne na maza kuma ko oho. Ayi masu wani tsini² a saka musu duwatsu da maɗauri macen kenan shi yasa komai nata yake da burgewa. Ni ina san matana ta kasance mai ado da zobe , “yan hannu , ɗan kunne tsarkar wuya da ƙafa amma tsabar sharri yanzu ba damar mace ta saka tsarƙar ƙafa shike nan an kaita wani wurin daban dan rashin adalci. Hmm itama dai ado da ita wani ɓoyayyan sirri ne. Jigida duk tana cikin kayan ado na mata sirrinta daban ne amma matan bariki su suka sanshi shi yasa sukafi yin amfani da ita….
Mata 10 idan kika tarasu zaiyi wuya a cikinsu kaf ɗin su ki samu mace ɗaya data saka jigida a ƙugunta. Amma idan zaki tara karuwan da suka san kansu suka goge suka kuma daɗe tare da sanin sirrin bariki zaiyi wuya kika haɗa mace 10 ki samu mace biyun da ƙugunta bata ɗaura jigida ba….! Dalilin ɗaurata da sukeyi ni nasani amma bazan faɗa ba. Dalilinsu na sakawa da motsinta ai sunsan abinda take haifar da , kuma nima nasan dalilinsu. Nine dai ke baki isa ki ɗaurata ba tunda bana ra’ayi amma duk abubuwan da kikaji na faɗa a farko idan kika saka wannan ra’ayi na ne har tukuici ma saina bayar. Nidai dan Allah ka barmin abuna in saka , An mata na barki a saka lafiya amma da sharaɗi , tom , karki sakata ki fita , na yadda , duk kuma lokacin da kika buga ƙaraurawar tou fa lallai zanzo kuma kinsan ni bana zuwan banza. Wannan shine idan kin yadda ni da kaina ma zan ɗaura miki ita….. Na yadda , kin yadda ? Ey na yadda , banajin yi haƙuri babu wani wallahi² , jinjina kaina nayi tare da tabbatar mishi da ey na amince. Saukeni yayi daga jikinshi yace ina zuwa , inda ya ajiye jigidar yaje ya ɗauko da kanshi ya zagayamin ita so adadin ruɓin daya ruɓanyata a ƙuguna. Nima na shiga sahun mata masu ɗaura lambar ƙugu.
Yau banje makaranta ba haka kuma Dikko baiyi tafiya ba. Yadai shiga gari. Pa – Pi kuma yana wurin Momy dan tun jiya da yaje yakai ƙara wa Ashiru ? Ashirun cewa yayi suje yakai shi wurin Momy. Shine yakai shi kuma yace a faɗa mana dani da yaya ya fata damu , kuma duk bamuyi cau ba wayyayi. Itama Momyn goyuba bata hatu ba. Shima Yaya baiyi cau ba. Dokin ma shima baiyi cau ba. Itama motarshi bata da cau ta Dady tafi hatuwa. Kuma kada mu sake muma muzo musu gida.
Saida na gama hidimar gida kaf duk abinda zanyi nayi na ƙare sannan na ɗauki wanka na kulle wanka da wani irin kafirarren leshi mai sauƙin nauhi. Nasha ado da duwatsunan wuya kunne hannu da “yan yatsu. { bawai dutse ba no׳ cikin tsarabar da mai gida ne ya kawo na saka wani daga ciki dan burge shi a wannan sansanyar maren sakaliya. } na wani kawo ɗaurina dai² da zamani na kafe wankan dashi. Naɗan yayyafa ruwan turare bawai yadda kamshin zai zama mai cutarwa ba haka kuma bazai tashi zuciyar mai shaƙa ba. Cikin kujera na koma na soke da zama irin na matan masu kuɗi ina ta ƙasaita ni matar Dikko. Wayana dake gefe ta na ɗauka na kira Mai gilashi , cikin sakonnin da bata wuce 30 ba ta shiga , tana shiga ta ɗauka. Bayan gaisuwa nace mata maganar jigida wai meye sirrin ne ? Ke malama wannan jigida da kika ganshi yasha ban² da jigidar da zaki je kasuwa ki bada kuɗi ki siya kinji ? Wannan ɓoyayyar sirri ce kuma bawai na baki dan kije ki saka weldrop kiyi ajiyarta ba , ki ɗaurashi a ƙugunki hajiya kiyi tafiya da isarki.
Halbawarta ɗaya tsallen zuciyar duk namijin daya ji kukanta , adadin buguwar zuciyarshi adadin buƙatuwa , ke wannan jigidar bala’enta yasa sukayi mata suna da huce takaici. Baga namiji ba har kishiya saita shafa miki lafiya , idan uwar naci ce da rashin zuciya taita zama tana haɗiyar baƙin ciki , idan kuma tunburƙuƙu ce wato mai zuciya a maƙoshi filin gidan zata barmiki. {{ miye ribarki idan kin kora wata ? Idan ta tafi ma wata zata zo , itama idan kika sake korata wata rana a kawo wacce kema zatayi out dake…. }} Ma damar dai zaki motsa ? Idan har tayi kuka tou fa lallai ke kasuwa ya buɗe ba gareki ba garemu masuyi domin kasuwanci.
Hmmm amma ni kinaji da farko Dikko cewa yayi baya so fa , dariya tayi tare cewa ɗan duniya wai ko yace miki akan wani dalili ne ? A , a , kawai dai yace bana ɗaurawa danshi wai baya ra’ayin lambar ƙugu. Sake sheƙewa tayi da dariya tace kai kiyi haƙuri amma duniyanci mijinki ya shafe tudun da bakya tunani , yanzu ina jigidar ne ? Ce masa nayi dan Allah ya barmin ina so , shin ya baki ita ne ? Ya bani mana gashi a ƙuguna ɗaure. Taf lallai kam Sultana sannu da ƙoƙari. Yawwa na faɗa ba tare dana sake magana ba ita kuma taci gaba da cewa. Baice miki komai ba bayan haka ? Ni baicemin ba ? Karfa kiyi ƙarya ? Ai kinsan ni ƙarya ba ɗabi’a na ne ba. Ki ranste baice wani abu ba , Mai gilashi kinsan bana san ayi ta tsayuwa a magana ɗaya mu matsa gaba ko macimma matsaya. Gaskiya sirrin irin jigidar nan rufaffen sirri ne , buɗeshi da sanin matsayinshi sai tuɓaɓɓin mata. Mafiya yawan maza dubu a cikin ƙaso miliyan zaiyi wahala ki samu namiji dubu dake ra’ayinta , domin ɗaurata cikar duniyanci ne shi yasa mafi’akasari mu matan bariki ne mukafi amfani da ita. To ke me yasa baraki sakawa naki ba idan dai harshi mai ra’ayi ne domin gyara adonki da burgewa. Sarƙa “yan kunne zobe da ɗan hannu duk domin mata akayi su , shin “yan hannun basa ƙara ne ? Ke kanki da kika saka shin ya kikeji kanki dan Allah idan suka motsa ? Mata masu hikima sune suka san yadda abun yake badawa , amma iya ado dasu sai jajirtaccin mata masu duniya , ƙasaitacci bugun farko a filin sanin sirrin rayuwar zaman takewar aure.
Idan dai har ke mace kinsan damarki da haggu bazakiyi sake ko sakaci da ado ba. Kaso casa’in na mata , auna sauke min gashin kansu kiga yadda suffarsu zata zama ? Amfanin wanka da ma’anar yinshi ya tattara a wurin mu da mukeyin shi. Idan har mace ta sauke gashin kanta domin rashin buƙatuwarshi idan har ta haɗa da girarenta wane suna mu zamu kirata dashi ? Duk da dai cewa gaban rigarta ya turo. Zuwan farko ba’a kallon structure saidai a kalli yawan ado da wanka. Buƙatar duk data barki barin gashin kanki da gyara , gyaran gira a duk ƙarshen mako ko wata dalilin ne ya kamata yasa ki kasance cikin ado da kayan ado masu burgewa. Misali , macen data bar gashin kanta bujur² bata tajewa ba kitsawa da banbanci da wacce ta gyarashi , wacce ta kitsashi kuma fitar ainahin kyawun fuskarta yafi na wacce ta taje ta barshi a kunce , matsayin “yan kunne da rashin su a jikin mace tamkar ƙururrumar buta ce mara murfi. Kallo ɗaya zakiyi mata ta baki kyankyami ko amfani zaki da ida tou zakiyi shine ba cikin natsuwa ba , kema kanki idan kikayi baƙon kunya kinajin kunyar bashi ita yayi amfani , tou haka macen da babu ado matsayinta yake a wurin mijinta. Gugar zana , fushi ga masu ɗabi’ar riba ga masu ɗaukar gyara.
Idan baki manta ba kwanaki na fara baki labari akan naje asibiti ranar da muka zo gidanki dasu Hadiza ko ? Umm , yawwa tou tsaya kiji kaɗan daga ɓarnar jigidar Mai gilashi. Tunda na ɗora idona akan Alhajin da muke zaune a gidanshi raina ya biya dashi , duk wata alama da akeyi nayi mishi ɗan iskannan yaimin taurin kai. Gadai yadda abun yake…..
Banda murƙushe² babu abinda Mai gilashi takeyi. Lokaci bayan lokaci ita Hadiza takan ce mata sannu , haka suka kasance a asibiti har layin ganin likita yazo kan Mai gilashi. Tunda ta miƙe ta fara tafiya hankalin duk wani mace ko namiji dake wurin saida ya kallonta har ta shiga inda zata ga likita , tunda ta maida ƙofa ta rufe bayan ta shiga taci gaba da bada tako jigida taci gaba da kuka , wuri ta samu ta zauna inda marasa lafiya ke zama domin shi likita yayi miki “yan tambayoyi dan gano damuwarki. Tana zama jigidar ta bada wani zutt² domin dai²tuwa kamar yadda mai sarrafata tayi.
Kiran sunanta likita yayi bayan ya kalli fayil inta sannan yayi ɗan rubuce² yake tambayarta abinda yake damunta ? Ciwon sha’awa shine amsar data bashi , ummm ? Ya sake tambayarta a karo na biyu , a ɗan yatsine ta sake cewa ciwon sha’awa nace maka , kallonta yayi tare da cewa ban fahimta ba ? Kauda kanta tayi gefe cewa kai likita ne ko kuwa dai ? Meya sameki ne ? Nadai fahimce ka kanajin daɗin kalmar nan kaji , sake maimatawa tayi , shiru yayi bai sake tambayarta ba , ita kuma ci gaba tayi² da maimaitawa cike da iskanci. Hajiya ai naji , yawwa wai idanma bakaji ba dan dai kasan nidai bana gaji da faɗa ta ƙarasa maganar tana faɗar kalmar sha’awa. Rubutu yayi a fiyel ɗin sannan ya rubuta mata magunguna yace ta ɗauka taje ta siya….!
A malam likita da sauri haka har ka gano ciwona ? Bayan kuma ni banyi maka bayani ba ? Ɗauka ya faɗa a ɗan ɗaure. Taɓa takaddar tayi tare da dafa hannunshi da yake turo mata cewa idan kuma ban ɗauka ba fa ? Sai kici ƙaniyarki , murmushi tayi tattare da salon yaudara tace saidai kai kaci min ita , ta faɗa tana masa kallon saka shi a tarko take ci gaba da cewa ka taɓa ganin inda aka yanka ka kaci kanka kuma bayan ka mutu ? Adireshin gidanta kawai taci gaba da faɗa mishi tare da ɗaukar biron gabanshi ta juya takadar daya rubuta mata maganin ta rubuta lambar wayarta , sakaran likita mai zubar da abinci a tsari. Tana faɗin haka ta miƙe ta fara tafiya , jigida kuma taci gaba da tsuwwa , kamar wani gelele haka ya bita da kallo , saida tazo bakin ƙofa tace ai nasan maganin ciwona ɗan raini , bana muradin shan maganin saidai in shanye mai rubutawa. Harararshi tayi irin ta kwaɗayi sannan ta riƙo saitin jigidarta ta kakkaɓa mishi , wani irin ihu tayi cocas casss chuss , na barka lafiya ta fice daga ofishin…. Dariya yayi bayan Mai gilashi ta fita tare dayin ɗan gajeren tsoki yana jinjina ma lambar iskancinta…… A maimakon abinda ya kawoni saina ɓige da karatun ƙarya domin amfani da wata manufa sai nabar waccan buƙatar nayi amfani da wacce ta samu. Likita ya biyoni kuma na ƙaddamar dashi a jam’iyata.
Alhajin da muke gidanshi kuwa , can wurin gantalina na ganshi ya rumgumo wata tsohuwar mace. Matsalar gidanshi shi matarshi ma’aikaciyar gwamnati ce , bata da lokaci da safe da dare kuma tana bacci. Ba’ayin wata shaƙuwa sai weekend. Idan ɗan abu yasa tayi masa sai tasa a kira mata ni , inzo inyi mata kaza². Ɗan sharomin ɗakin Alaji fita zanyi na makara Office ? Ɗan dafa mishi tea da Allah na dawo a gajiye , idan na dafa zatace ɗan miƙa mishi ya cika tsattsafa. Tsayayyen namiji ne mai ji da kuzari , yana da shekaru kusan hamsin da “yar ɗoriya amma nidai a hakan yayi min wallahi. Ina buƙatarshi , karo na farko nace masa Alhaji zan baka jikina wurin E yane idan dai har zaka iya jurewa har gari ya waye. Ka more ƙuruciyata da tsufanka ni kuma in more da dukiyarka. Yamin wulaƙanci ya korani.
Shine dana ganshi da wata mace a hotel naje wurinshi nace masa Alaji wai miye banyi ba ? Sirrin da akayi da ɗaki ai ya isa ayi da tsakar gida. Bai bani amsa ba ya wuce sha’aninshi. Wata rana ina gyaran ɗakinshi ya shigo dan gaskiya yayi faɗawa matarshi akan ta daina tura mishi ni ɗakinshi taƙiji , ina gyaran gado ya shigo zai wuce toilet , aiko na bishi ina cewa ina ne zakaje haka ? Ka tsaya in raka ka….. Shigewa yayi ya kullo ƙofa. Da gudu na fita na nufi sashinmu.
Jigida ta na ɗauro na dawo , daga nan na fara ɗanashi a tarko shima , dan gaskiya da bana ɗaura jigida a gida sai zan fita saina gane ashe duk inda ka kasa kasuwarka siya akeyi saidai idan baka baza abun siyarwa ba. Ashe da wauta nake ƙoƙarin jibgawa rashin saka hannun jari a gida dan na fahimci rashin ɗaurata a gida yin hakanan babban kuskure ne , tou jigida ce ta ciwon ɗan wasa a gida. Tun yana ɗan satar kallona har ya fara dogon kallo. A falonshi dai in goge tv na sakar mishi zani. Shikenan nan fa muka riƙa ɗauke wuta tare , tana can tana bacci ya kulle mata ƙofar ciki ni kam ya buɗemin ta baya naje mu shige bargo ayi dani ba matar gida ba , maganin macen da bata taya miji bacci kenan.. Tun daga wannan ranar nayi saving nashi a alminjar na jawo banza izuwa cikin duniyar rayuwata. Kashi saba’in na kuɗinshi nice nake cinye kaso arba’in , matar gida taci goma mijina yaci biyar Alhaji da sauran matan waje suyi maleji da sauran. Karatuna motar hawata kuɗin mai da duk sauran buƙatuna shine abu a sauƙi fa dare da yawa na ɓata kafin na taka babban matsayi. Malaman makarantarmu suma dai muna ɗan rage yinin karatu a ofisoshinsu. Na samu kuɗi wannan harkar fiye da yadda bakya tunani Sultana amma dai matsalar har yanzu ko gwamna ban samu gani ba , bayan kuma naji ance manyan karuwai gwamnati tasan da zamansu. Ashe ban sani ba farashin karuwanci yanzu ta faɗi har haka ƙasa wan²r. Tirr da karuwancin zamani marar digi wallahi. Karuwan wancan ƙarnin su sukaji daɗin karuwanci banda karuwan yanzu da gwamnati take ma hassada , a iya a hasko ka a talabijin domin a bawa sauran masu sha’awar shiga karuwanci su shiga da ƙwarin guiwarsu gwamnatin jaha ta daƙile wannan hanya. Jinjina ga gwamna mai kishin jahar sa , mai daƙile gudun tafiyar ɓarna a yankinshi. Allah ya ƙarawa mai girma gwamnan jihar katsina lafiya da nisan kwana…… Irin wannan shuwagabanni muke fatar samu masu daƙilar da ɓarna suyi ƙoƙarin bada ƙwarin guiwa wurin kafuwar ci gaba da ƙoƙarin koyar da ci gaban rayuwar yara masu tasowa , da su gane shi iskanci ba wani riba bane dashi.
Mutanen kirki masu daraja su suka dace da a nuno hotunansu a akwatin talabijin ba mutanen banza ba , na gari sune abun nunawa duniya domin al’umma tayi koyi dasu , tsakanin karuwa da talabijin saidai a nuno hoton shegiya ana zaneta…… Hmmm gaskiya Nana Mai gilashi ina zuwa nayi baƙuwa zan kiraki zuwa anjima idan kuma ban samu kiranki ba sai mun haɗu makaranta…. Ina faɗin haka na ajiye waya inawa baƙuwa barka da zuwa. Bata ansa sannu ba tace ashe yasan baya nan yacemin yana gida ? Mai bin Rabiya ce , kila yana kusa ki kirashi kiji , ina faɗin haka na gaisheta tare da wucewa ciki dan gabatar da sallah magrib.
Dikko shida Pa – Pi ya dawo can ta matsoshi da Momy itama yayo mata yaji , yace itama wayyayi ya fata da ita abincin su ma babu daɗi Momy goyuba ta iya , zagi yayi ta zane mishi baki yace bazai ƙara zuwa ba kuma ko ta ganshi idan tace Pa – Pi zaice ya manta ta. Shi Yaya baya dukanshi. Shine ya tattara kayanshi Dikko yana zuwa ya biyoshi. Tashi na har nayi mata abinda zatayi gulma wa mijina , bayan sun gama tattaunawa tace Dikko kabar matarka ta ɗaura jigida ? Ra’ayinta ne kema kije ki sakawa mijinki. Amma ai baka san jigida yaushe ka fara so ? Da matata ta fara ra’ayin ɗaurawa sai kawai nima naji ina muradi domin tayi farin ciki. Zata sake magana yace dakata da Allah , ke “yar uwata ce matsayinki daban hurimin matata daban. Kiyi magana abinda ya shafeni dake matsala ta gida na ko gyara abinda ya shafeni da iyalina ni ba yaro bane ba nasan abinda ya kamata. Dikko kar kamin rashin kunya kaji ? Ko nayi miki dai ai nasan bana buguwa wurinki. Tou ko dukana zakayi ne ? Haba ina zanyi abun kunya in daki Yayata yayi maganar yana murmushi. Ai da irin haka namiji ke zama mijin tace , ba tare daya kalleta ba yace ni mijin kan tace ne ni. Tana so dai ta suko Sultana Dikko ya tare kuma har sukayi firarsu suka gama ta tafi ita Sultana bata sake fitowa ba.
Cike da farin ciki ya nufi ɗakin An mata. Pa – Pi na kwance wai daga nan yake bawa Mamanshi labari ita dake toilet tana wanka. Shigowar Dikko ɗakin ne yasa yace Yaya zoka nan kaji ya nuna mishi kusa dashi , naƙi inzo ba cewa kayi ka ɓata damu ba , dokina ma baiyi kyau ba ? Ai sai kayi bacci zan maida ka wurin Momy , ɗan guntun tsoki yayi yana turo bakinshi yace ai babu yuwana da wannan Momyn wayyayi ya ƙarasa maganar yana harara… Tou zo kaji. Saukowa yayi yazo inda yake tsaye , kaje kace ma Ashiru ina gaishe shi. Har ya fara tafiya yace kuma dani jakaje ? Dakai zanje mana kayi zamanka idan ka dawo bazanje dakai ba , can janjauna ce kazo ? Ey mana , kuma Pa – Pi kayyayi facci ? Kayi bacci Babana kanayin bacci ina zuwa sai kawai in saka a mota. Amma wayyayi ban zuwa wurin Momy can gackiya , nima bazanje ba kaidai jeka , da sauri ya fita daga ɗakin yana gunguni.
Lumshe idanuwanshi yayi tare da sauke ajiyar zuciya a wahalce bayan Pa – Pi ya fita. Da gudu na fito daga toilet suuuuuu na taho na shige jikinshi. Murmushi yayi amma bai riƙeni ba yace yarinya ya akayi ne ? Kawai inayin farin ciki na faɗa ina fita daga jikinshi na fara tafiya cikin salo mai ibar hankali jigida kuma ta fara ihu. Rufe ɗakinki yayi ni kuma naci gaba da kakkaɓa ƙugu , shima dariyar yayi yaɗan tako da zamarshi. Dariya na sakeyi tare da hayewa saman gado dan a tunanina ko zaimin cuta ne. Cike da shauƙi shima ya hayo gadon ya riƙeni yana shaƙar iska cike da muradi. Zuƙewa nayi ya sake riƙoni a gajiye ya rumgumeni jikinshi da yanayin ƙuruciya. Wai shi shine nake kaɗawa ganye ko ? Saiya lullusani a daren nan , wannan ƙugun da nake masa ingije dashi zai bani labari dan masu garinmu…..
A “yan kwanaki biyun nan dai ban leƙa makaranta ba , gida kawai domin yafi min daɗi saboda mun buɗe sabuwar rayuwa da muke raya kawunanmu cikin tsantsar soyayyar da bama san rabuwa da juna. Rabon da muyi faɗa ko wani yaji fushi harya ɓatawa wani rai yanzu mun daina , Dikko ya jajirce yana ta kwatanci da nuniya. Ranshi fes domin duk yadda ya bada saƙo anshewa nakeyi shi yasa yakeyin farin ciki. Mai gilashi ma a gefe tana ta ɗirkako nata bakin gwargado amma duk abin nan dai Dikko bai haƙura da Sharifa ba Dady yana ta tunatar dashi akan muhimmancin auren sati na gaba za’a saka rana , Yusra dai har yanzu babu ruwanshi da ita kuma ta sameshi har G R A domin sasanci a ranar ta auna iskancin da tunda take duniya bata taɓa ganin namiji da irin shi ba , ta tsorata dan bata taɓa ganin aljani akan namiji ba sai a wurin Dikko , saida tayi fitsarin tsaye saboda firgita , tunda ya rufeta ta inda take tura tsiraici shi yasa ta tafi gabanta gaɗi ta kama tuɓe²n kaya , tunda Yusra take a duniya ita bata taɓa ɗana ya namiji yake ba sai akan Dikko taso taji su kuma mazan ya tasu darajar take ? Anan ne fa yayi bakandamiyar shi. Tunda ta samu aka fito da ita dakel saida tayi jinyar fargaba. Wannan Yusra ba ko wace ce ba itace Yusran data ɓata Sadiyya matar Dikko na farko. Kuma ita bata san shi Dikko ya auri wata Sadiya can ba. A jirgi ta ganshi taji ya mata , nan tayi mishi bariki irin namu na mata hardai suka rabu bai bata numbershi ba. Amma da masifa saida taje ta samoshi…..
Jiddah kuwa wuta kawai take sha a gidan Yazeedu. Shidai Dikko yace ba ruwanshi , kuma bazai wani je ko yayi magana wa Yazeed ba , can suje su babbake ba abinda ya dameshi da sabgar gidan kowa dan shima baya so a shiga sabgar nashi gidan bare har a samu damar sawa matarshi ido. Taje ta sakata An mata ta wala abunta , duk wanda ya taɓota zaici ubanshi ne kawai abunshi , amma idan tayi iskanci shine zai bata wahala kuma dare yayi su shige bargo asha soyayya.
Gadon Inna kuwa suma danginta cewa sukayi ai basai an bani komai ba , dan duk abinda za’a bani ni na girmeshi inji su. Basu bani ba ko tayinshi basuyi min ba haka suka sha shagalinsu kuma suje suma kansu sukayi ma. Halima da abiyar zamanta suna can suma suna cuɗa zaman kishi , Halimatu taga ta kanta ɓarowo hannun maza.
Saida nayi sati ina hutun da babu dalili. Ranar da naje makaranta a ranar Sharifa tayo zugar karuwai suka bani kashin bala’e dakel aka ƙwaceni a hannunsu. Mai gilashi itace aka sa ta kawoni gida ita da Farisa. A waje muka haɗu da Dikko shi zai fita mu zamu shiga , fita nayi na nufi wurin motarshi ina kuka. Mai gilashi itama da kalar sherinta ta fito shima Dikko fitowa yayi cikin tashin hankali. Dakel nakejan ƙafa cikin wahaltuwa kamar zan mutu saboda bala’e , muna haɗuwa na kwanta jikinshi ina ƙara yawan kuka na , cikin faɗa yace me ne² ? Da shashshekar kuka nace karuwanka ne ta dakeni , cikin rashin fahimta yace wace karuwa kuma ? Nanfa Nana Mai gilashi ta ɓalle ta fara rattafa sharri kamar an tirke musulmin da yayi ridda. Tana bashi labari jikinta yana ƙyarma shi kuma zuciyarshi tana fin jirgin sama tashi. Dakel ya haɗe yawun ɓacin rai zufa ta tsirgo mishi da yaga jini nabin jikinta. Lokacin daya ɗago Sultana tuni ta some , wannan kenan…..
Bayan wasu shekaru…..
Wancan duka da Sharifa ta gayyato akayi min saida akayimin aiki. Dukan ya janyo min matsaloli , giccewar ɗa a ciki {{ breech }}. Zubar jini mai tsanani daya ƙi tsayawa. Bayan anyi hoton ciki wato {{ scanning }} sai likita ya sanar dasu cewa akwai buƙatuwar yimin aiki na gaggawa saboda placentar ta safko , matsalar bugawar zuciya da sama da yadda ya kamata wato {{ fetal tachycardia }} sannan kuma matsalar bugun zuciyar akwai alamun zai koma ƙasa ga yadda ya kamata wato {{ fetal bradycardia }} duk da ganin cewa lokacin haihuwa baiyi ba , nan sukayi ta allureni da alluran da zai taimaka lafiyar ɗan kafin ayi aikin. Suka kuma shirya sanya baby a kwalba da kuma ci gaba da yi mishi wasu allurai har zuwa wani lokaci saboda l b w ciki wata bakwai. Satinmu shidda a asibiti aka sallamemu muka dawo gida da wani ɗan magen yaro suka haɗomu da wanin zanin raino mukai ta fanan goya yaro ta gaba daga ni har Babanshi. Pa – Pi kuwa tunda yaga wannan ɗan mitsitsin ɗa ya daina ɗagama gidan ƙafa koda wasa. Ba’ayi taron suna ba wannan umarni daga mai gida yaro yaci sunan Baba Binna muna kiranshi da Khalifa.
A ranar da sukayimin dukan kuwa Dikko a wurin ya barni ya shiga mota cike da ɓacin rai ya tafi neman Sharifa. Mai gilashi da taimakon wasu daga cikin yaranshi suka tafi asibiti dani. Duk wanda yaji bana lafiya acan ya sameni kafin wani lokaci duk wani ɗan uwan Dikko ya bayyana idan dai yana kusa. Dikko kuwa ya nemi Sharifa harya gode Allah bai ganta ba , ita kuma daƙiƙiyar taita kiran Mai gilashi. Ƙarshe Mai gilashi cewa tayi Malam yace da zaiyi mata aiki amma daya buga ƙasa ya gano ta taɓacin amanar wata aminiyarta , wani attajiri ɗan siyasa yazo auren ita aminiyar ke kika rufe ciki wai haka yace , shine nace shin ko kin gane ko wace ce ? Iyakar tunanin Sharifa ta kasa hasasowa. Mai gilashi tace tou daƙiƙiya wannan ba ko bace nice….. Kuma nice nan na shirya komai ta yadda kika gani na rusa miki wannan auren jaka , tunin duniya nake ƙufule dake yadda kika hanani ci ga kaiwa ga nasara tunda naji kince SAI KIN AURI D ‘ K nace ma zuciyata idan dai ta bari kika aureshi saina rabata rayuwa da gangar jikina. Nice nan na ɗauki nauhin komai na shirya na kuma gabatar , idan kika sake kirana zan saki sauran hotunan wa duniya naki kamar yadda kema kika ɗauki hotuna na da nake a gurɓataccen yanayi kika samu nasara wurin ganin kin hana auren. Kin hana nawa kema na hana naki 1/1 sai kuma kin sake , idan kuma kika sake kirana saina shafe farin ciki daga rayuwar ahalinki tana faɗin haka ta ajiye waya.
Shi kuma a ranar har dare yana gidansu yana yayyafa ruwan rashin mutunci , waishi ko shi baya dukan An mata tunda ta samu ciki. Shine aka samu wata tsagera taje tayo gayyar ƙatti ? Waishi maza zasu dakar mishi mata ? Da ciki aka dakar mishi mata ? Har dare yana can yana abu ɗaya , Momy tace a fitar dashi ta daina ganinshi , wannan riƙo da akayi mishi da zumar lallashi shikenan ya birke ya fara sai kashe , waye yace wai a riƙe shi ne ? Yace baya so ana taɓashi kaza². Shikenan fa ya mimmiƙe ko za’a tashi duniya saiya ramawa An mata dukan nan bazai yadda ba , wai ko an faɗa musu jakace matarshi ? Sai ayi mishi abu dan cuta idan kuma yayi magana sai ace bashi da haƙuri , tou saiya rama kuma bamma gajiya duk wanda yayi mata sai yayi mishi ko waye kuma ko wacece…………. Daga nan ya ɗauke.
Dady kuma tara su Ashiru yayi yace gaba ɗayansu sun cuceshi sun kuma munafurceshi. Me yayi musu sukayi mishi haka ? Bayan su sukace mishi Babanshi ya warke ya haƙura ya daina neman magani , me yasa² ? Me yasa sukayi mishi haka ne ? Wannan ce soyayyar da suke bugun ƙirji cewa suna iya bawa Babanshi fansan rayukansu ? Karo na farko daya ga cin amana zahiri. Ba kuma zai sake yadda da kowa ba. Haƙuri Ashiru ya bashi sannan ya buɗe mishi gaskiyar lamarin yadda yake cewa.
Rashin lafiyar da Mai gidansu yayi bayan ya samu sauƙi. Sun faɗa mishi abinda Mustapha yace , amma sai kuma wata matsala dashi dai Mustaphan yace. Wai asirin da mutum yaci a abinci da wanda mace tayi “yan maƙale² dashi a jiki ta kwanta dana miji wannan asirin wahalar fita gareshi wallahi. Cikin magungunan dashi Al ‘ Ameen ya bawa Sadiya da sunan taimako yace wannan na kayan mata ne , shine taje tayi amfani dashi kuma shi Al ‘ Ameen ya bawa Mai gida magani a london , sanin manufarshi da aikin maganin bamu sani ba kuma shima Mai gida bai sani ba , wannan dalilin ne yasa yace yaso ya haɗu da Al ‘ Ameen akwai tambayoyin da zaiyi mishi. Gadai asiri an fitar na fili amma na jiki bai daina tasiri ba , ganin bai warke ba yasa yace kawai bara ya haƙura da Hajiya yaci gaba da sabgoginshi dan yasan bazata yadda ta sake zama dashi ba , a ranar daya bar gidan gwamnati ya koma gidanshi lalurar ta tasoshi a gaba , daga nan ne ya tafi jinya bayan ya dawo ya ƙarƙare aurenshi da Hajiya Jiddah yace itama Hajiya Sultana zai jira yaji me gidansu zasu ce. Shidai Allah ya sani shima yasan tunda yake a duniya rayuwarshi bata taɓa san wata mace ba wallahi sai a kanta.
Akanta ya san soyayya kuma akanta ya farayi ma shaƙuwa kuka , itace macen farko daya sa hannu ya daka a duniya wacce bata gidansu ba , kuma itace mutum ta farko data ɗaga hannu ta mareshi , yace shi a gidansu wallahi baisan wani abu da ake kira duka ba , tayama za’ayi tunanin dukanshi bayan kowa sanshi yake amma zuwanta rayuwarshi yasa ya anshi hukunci mari daga iyaye , itace macen da ta ɗaukeshi kamar wani sa’arta kuma bata iya zuciya dashi. Shine yace a yadda suka rabu yasan har abadan duniya ta gama dashi ashe ba haka ba. Yayi alƙawari har abadan duniya ya gama aure zai jira daga gidansu ita Sultana ayi magana kawai zai haƙura da ita , yasan babu uwar da zata haƙura tabar “yarta ta zauna da shi da kuma lalurashi. Yayi kuka shi da kanshi yaji tausayin kanshi.
Kamar ya haƙura amma ya kasa. Duk abinda yakeyi zaiyi zuru yana tunani , idan zaici ko zaisha zaiyi murmushi yace ko a wane hali kike ? Ya shiga ɗimuwar rayuwa da zaucewa ganin zai ida warwarewa yasa yasha ta dubu ya tafi gidansu bayan ya fara tura Abbakar. Bayan ya dawo da itane yake faɗa mata ya warke dan abinda yasa ya ɓoye mata kila idan tasan har yanzu yana da damuwa bara ta zauna dashi ba.
Sa hannun masu sa hannu a ciki Ashiru ya faɗawa Dady , Bilki yasa aka kira mishi tana zuwa ta fara zazzaga rashin mutunci. Wai ita zai tirke ? Tou tayi taje tayi yayi maganinta , ta fara azaƙaƙura rashin mutunci nan fa gida ya ruɗe aka fara tone²n asiri , Dady yace Bilki sai ta bar mishi gida , “ya “yanta suka fara kuka Dady zai tona musu asiri. Ita kuma cewa takeyi su daina kuka ya saketa, saboda mahaukacin ɗanshi zai tara yaran Dikko a gabansu yaci mutuncinta ? Har nawa ma Dikkon yake ? Wato shi tunda baya nan bara yayi a gaban yaran Dikkon idan shi Dikko ya dawo daga duniyar ɗimuwar rayuwa su bashi labari yaji daɗi.
Har tsakar dare ana abu guda Momy ita kuma tana cewa sai an warkar mata da ɗa wallahi. Kuma shi Dady karma ya kuskura ya saki Bilki dan wallahi bata riƙe mashi “ya “yanshi , Dady yace ko bata riƙesu shi ya isa ya kula da rayuwar yaranshi. Har Dikko ya dawo ba’a gama faɗa ba , shine ya bawa Dady haƙuri akan kar yayi saki wa Aunty Bilki , Dady yace tou kinji haƙuri yake bani akan ki duk ke kinyi masa abu na rashin kyautawa. Cewa tayi wallahi idan dai akan Dikko zaiyi haƙuri ya zauna da ita wallahi ta haramta zaman aurenta dashi , nan suka sake buɗe sabuwar rigima Dady yace saboda Babanshi yayi haƙuri rigima dai da tashin hankali har aka rabu , ita bata zama albarkacin Dikko saboda bata ƙaunarshi kuma sai ta kashe Dikko ta ɗauki alƙawari a gaban Dady , dariya Dikko yayi cewa inma ki kasheni ko ki fasa lumfashi yana wurin Allah sai lokacin daya so zai tsinkeshi. Shawara ɗaya zan baki kidai bi sannu domin ni ko hassada mutum ya cikamin saiya lalace……
Jiddah ta ladaftu domin Yazeed ya zabga mata bulalar saki mai ɗan bara’un zafi. Tayi iya ƙoƙarinta a koma G R A da ita amma ina ? Nima na rama maganar data faɗa a lokacin aurena nace nima G R A nawa ne ni ɗaya daga ni sai yarana. Umar Faruk {{ Pa – Pi }} Aliyu {{ Khalifa }} DIKKO {{ Junior }} Maryam {{ Ummie }} sai ayarin gidanmu da kuma wanda naso nima nace mata Dikko nawa ne ni ɗaya. Bata ga Sharifa ba da tace SAI TA AURI D ‘ K yadda ta ƙare ? Taje tayi haƙuri tayi maleji da Yazeedu. Dole ta lallaɓa ta koma gidanta kuma ya rage iskancin hanaci masa abincin gida saidai shine yake auna musu kamar “yan boarding.
Mai gilashi ta rabu da tsohon mijinta tana Abuja tana aure sa’ar rayuwa dabance , wato duk iya iskancin mutum idan Allah yaso mishi jin daɗi saiya shiryar dashi.
Halimatu dai ƙanwar Hadiza bata samu kwanciyar hankali ba saida tayi waje road da ita ga miji ya samu ƙarin matsayi a wurin aiki. Ta dafe kan mijinta ram an shiga lugudan wuta…..
Amisty Mardiya Hafsa Aunty Suwaiba kowa tana can tana ansar wuta dai² da irin rayuwar data aikata a zamanin ƙuruciyarta , duk wadda bata mori rayuwar ƙuruciyarta da kyakkyawar ɗabi’a ba ƙarshen faɗan tayi makauniyar ƙarshe.
Sharifa dai har yanzu ba’a samu anyi aure ba. Ita dai Mai gilashi ta haye ta ibi filin abuja suna can sunacin duniyarsu. Tacemin kila dai tana da rabon a nunota a talabijin tunda ta auri ɗan siyasa nikam nace mata kila dai aljannun shiga talabijin gareta.
Jamila Musa gareki jinin katsinawa.
Tam Alhamdulillahi Hajiya Maryam ko nace Hajiya Sultana. Duk dai baki faɗa mana shin Mai gidanki ya warware ko har yanzu yana ta faɗar saina kashe ki…….. *Sultana:•* Murmushi ni harma kin bani dariya , gaskiyar lamari Mai gida Dikko dadai sauƙi ba kamar cancan baya ba , dan mafi akasari saina ɓata mishi yake wannan ihu kuma ai kinsan yanzu ba’ayi. Gulmar Dady kukeyi ko ? Inji Pa – Pi tou bari in kirawo shi , ɗage kanshi yayi tare da cewa Ya…………………..Ya……..
Abun arziƙi ai yayi bari kiranshi kar yazo ya karkashemu muma a bar mutanen Qerau da jimami…….
Alhamdulillah
Masu biye da labarin kwarata anan ne ubangiji ya bani ikon dakatawa. A madadin duk wani bakatsine ko ina yake a faɗin duniyar nan muke ma duk wani daya karanta littafin kwarata fatan alkari domin nuna muku halakci da kara irin namu na katsinawan Dikko. Kai har wanda bai karanta ba kyakkyawar fata da dubun gaisuwa ta musamman data fito daga yankin jihar katsina,
Jinjina da gaisuwa gareku Kanawan dabo tunbin giwa , saƙon gaisuwa da jinjina a gareku mai kyau albarkacin Umar Sanyi.
Alhamdulillah.
🔚
Rubutawa.
*JAMILA MUSA QERAU….*
14/02/2020
Na barku lafiya. Cike da kewarku , sai Allah mai kowa mai komai ya sake haɗamu idan muna da rayuwa a cikin labarin *ƁOYAYYAR SOYAYYA…*
*JAMILA MUSA ce…*