Ma’aurata Muhimmancin Jima’i Da Sanyin Safiya
Don Ma’aurata Muhimmancin Jima’i Da Sanyin Safiya.
Fassara Aliyu Adamu Tsiga
Cewar Farfesa Musa Yakubu, na jami’ar Ilorin, a wata lakca da ya gabatar mai taken “Knocking Down the Barriers to Four O’Clock Activities”
Yaye Hijabin Da Ke Tsakaninka Da Muhimman Al’amuran Karfe huɗu na safiya, ya bayyana jima’in sanyin safiya a matsayin wani makami mai linzami da zai iya tarwatsa rashin walwala, ko rashin jituwa, rashin fahimta da kuma uwa uba fatattakar matsalolin hawan jini da lalurori da suka shafi zuciya.
Shehin malamin ya gabatar da ƙasidar ne a wajen taron gabatar da ƙasidun tabbatar da shehunnan malamai a matsayin farfesa mai cikakken iko karo na 163 na jami’ar ta Ilori da a turance a ke kira da “Professorial Inaugural Lecture”
Shehin Malami Musa Yakubu ya bayyana cewa, yin jima’i sau uku zuwa huɗu a sati na taimakawa matuka wajen inganta rayuwar soyayyar ma’aurata, ya kuma ƙara danƙo da ingancin auren shi kansa
Farfesa ya ce ” Bincike ya nuna cewa jima’i na ƙara ƙarfafa lafiyar garkuwar jiki ta hanyar samar da wani tsaro na musamman ga ƙwayoyin halitta hawa na farko da ke kare jiki daga kamuwa daga zazzaɓi da mashaƙo.
Har ila yau, jima’i, na ƙara hauhawar ƙwayoyin halittar Immunoglobin A (IgA). Shi wannan Immunoglobin ya na ɗauke da sindaran “Antibodies” da ke baiwa jiki wata kariya ta musamman daga ƙananan ƙwayoyin cututtuka dangin Bakteriya, da Bayros, da Tokzin (bacteria, viruses, toxins)”
Farfesa Yakubu ya ci gaba da cewa “Jima’i na taimakawa mace (matar aure) wajen daidaita lokacin al’adarta ya kasance babu tangarɗa tare da inganta samun lafiyayyen bacci”
Jima’i na sanya jikin ɗan adam ya saki wani sinadari mai suna Oxytocin da ke ƙarawa mutum walwala da nishaɗi tare da inganta kusaci tsakanin ma’aurata biyu da kuma barinsu cikin farin ciki a duk lokacin da suka kammala jima’i”
Jima’i na tsawon minti 20 kacal na taimakawa jiki ƙona calories 150 (wani sinadari da ke samar da makamashin zafi ga jikin ɗan Adam)
Farfesan na Biochemistry ya ci gaba da cewa “Jima’i shi ne mafi ingancin hanya da Ubangiji ya baiwa mutane don samar da nishadi, walwala da kuma ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin ma’aurata”
Farfesa ya ce duk auren da ma’auratan ba sa iya gamsar da junansu ta fuskar jima’i, aure ne da kai tsaye za ka iya kira da mataccen aure”
Rashin gamsar da abokin zaman aure, ko shakka babu ya na daga cikin sanadiyyar mutuwar aure babu iyaka a Nijeriya, a saboda haka Farfesa Musa Yakubu ya ja hankalin ma’aurata da su nemi hanyoyi sahihai na warware matsalolin jima’i a gidajensu.
Zamu cigaba InshaAllah