Hausa Novels

Mafarin Lamari Hausa novel complete

[12/23/2017, 18:37] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Related Articles

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that – our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
*MAFARIN LAMARIN*

 

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*

 

©Zeetty

_GARGA’DI_
_Wannan labarin nawa da abin da ya k’unsa, duk mallakar marubuciyar ce. Saboda haka sai a guji juya, ko sarrafa wannan labarin batare da izini ba. In kunne yaji…….._

_TUNATAR WA_
_Wannan labarin kagaggen labari ne, don fad’akarwa da Nisha d’antar da masu karatu. Saboda haka sai a guji yin zargi ko zaton cewa anyi wannan labari ne domin a musgunawa wani ko wasu, haka sunaye da garuruwan dake cikin wanna labari, an sane kawai don k’ayata labarin._

_GAREKU MARUBUTA_
_Ina kira a gareku, da mu gyara rubutun mu, musan abinda zamu dinga sakawa dan gyara rayuwar k’annemu da ‘ya’yanmu, kar mu 6ata musu tarbiya da sakawa yara buri, abinda bazai yiwu ba a wannan zamanin mudaina rubutawa, mutuna online novels mafi akasari ‘yan mata yanzu sun raja’a a kansa, dan Allah muhankalta._

“`NOTE“`:- *Masu karatu kuyi hak’uri bazaku samu cigaban Labarin littafin Hanyar libiya ba, saboda wani dalili mai karfi, ku gafarceni, dalilin haka nema yasa nafara sabon novel.*

*LITTATAFAN MARUBUCIYAR*
*HANGEN DALA*
*DAGA ALLAH NE*
*HANYAR LIBIYA*
*’DABI’A*
*ZUBAR HAWAYE*
*NAMIJIN DUNIYA*

“`BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.“`

PAGE 1-2
Shigowa gida yayi ko sallama babu, yafara ball da wani baho daya gani a gefen tsakar gidan, cikin bala’i yafara magana”aikin banza aikin wofi, ni za’a kawoma iskanci a cikin gidan nan?, toh zan yimiki wulak’anci, Aysher ina kike, yooo gani d’an iska ko? Ina magana kina ciki kin maidani shashasha, kai uban giji kayi mana arziki ina ganin wulak’anci a gurin matar nan, bazaki fito ba saina shigo har d’akin na nakad’a miki duka, a gaban ‘ya’yan naki kaza uwar son ‘ya’ya.?”

Da sauri har tana cin tuntu6e ta fito, tana cewa”kayi hak’uri Abban Aslam, wallahi Afra ce take so tayi bacci, shine nake lalla6ata dan nasamu tayi bacci na k’arasa aiki na.”

Doguwar tsaki ya saki, kafin yafara magana cikin kumfar baki”Kinji tsiyar ba, daga anyi miki magana sai kice ‘ya’ya sai bala’in son ‘ya’ya, wuce kibani guri nidai Allah kawomin ranar da zan rabu da wannan bala’in, saboda banda kud’i kin mayar dani d’an iska, shashasha ko?”

“Kayi hak’uri Abban Aslam ba haka bane, ka gafarceni idan na 6ata maka rai.” Ta k’arasa fad’a tare da juyawa dan komawa d’akin ta.

Fusgota yayi kafin ya wanketa da mari, yafara magana cikin hargagi”Ehhh mana wato gani d’an iska ina magana kin tafi kin barni wato nagayawa iska ko.?”

Hanunta dafe da kuncin ta tafara magana tana hawaye tace”Kayi Hakuri Abban Aslam, kace natafi, na juya domin tafiyar, amman yanzu kace nayi maka badai-dai ba, kadaure ka sanar dani laifin dana aikata gareka kake hukunta ni, ta wannan hanyar dan Allah, auren so mukayi ni dakai, bawanda akayima dole amman kwata-kwata baifi zaman shekara d’aya mukayi cikin kwanciyar hankali ba.?”

“Hmmm tuhumata kikeyi,? Nace tuhumata kikeyi, tunda na aureki wane cigaba nasamu sam babu wani cigaba kullum sai komawa baya nakeyi, duk abokaina sun fini kud’i da arziki, nikam tabbas na auro mai farar k’afa, zama nin nan ina ake auren so? Sai dai auren kud’i, to bari kiji dakyau, ina nan nasa ayimin binciken matar aure, auren jari zanyi, ‘yar alasawa, muga tsiya, shashasha kawai.”

Yana gama fad’in haka yasa kai yafice dan barin gidan.

Komawa tayi da baya ta shige d’aki, zama tayi ta rafka tagumi, shin me natsarema Abban Aslam lokaci guda ya canja min?, talaucin nan bani na d’ora mana ba, lallai nice ma mai farar k’afar?, ikon Allah.

Bayan ta gama komai ta gyara gidan tsaff ta d’auko turaren tsinke mai rangwamen kud’i ta kunna, kud’in da Yayanta Nasiru ya bata shekaran jiya da taje gida dashi ta sake amfani yau dan yimusu cefane, Macaroni ta dafa da dankalin turawa, ta siyo d’ayen kifinta ta soya ta watsa a ciki.
Bayan ta gama komai ta share gidan, ga goge ko ina tsaf, tashiga wanka ta fito ta kimtsa, cikin kwalliyarta mai sauk’i, hak’ik’a AYSHER tanada kyau, koda ace batayi kwalliya ba, dubeta yanzu kamar bata ta6a haihuwar yara har guda biyu ba.

Tana zaune a falo ya shigo yana cika yana batsewa, salama yayi ciki-ciki, Aysher ta amsa tare da fad’in”Sannu da dawowa Abban Aslam.”

“Yauwa sannu” ya fad’a a dake.
Tace”Me zaka farayi wanka ko cin abinci.?”
“Bazanyi wankan ba, nace bazanyi wankan ba ko dole ne, zoki mak’ureni nayi dole uwata.”

“Yi hakuri barin kawo maka abinci.”
(Tak’arasa fad’a tare da mik’ewa dan zuwa kawo mashi abinci)
Try ta d’auko mai d’auke da food flask da plate da cokali, ta k’araso gaban sa ta ajiye tare da bud’ewa ta zuba masa, ruwa ta d’auko a roba ta ajiye masa a gaban sa, duk yana binta da kallo saida ta gama tace”Bismillah”
Yace”Kina wani yimin abu isa-isa idan tak’amarki yau ban baki kud’in cefane ba kiyimin list, in sha Allahu zan biyaki idan nayi kud’i.”

“Kayi hak’uri duk maganar baikai haka ba.”

“‘Daukar abincin yayi yafara ci kamar dole, daga k’arshe dai zagewa yayi, yaci yayi kat, kafin ya mik’e a 3 seater, yana satan kallon matar sa, tayi masa kyau take wani sha’awata ya lullu6eshi.”

“Zan shiga ciki Abban Aslam saida safe, saika shigo.”

Yace”Aikin kenan, toh banyadda ba kijira nagama kallo, har lokacin tashina yayi mushiga tare, inada buk’ata, kinsan ai dole zan buk’ace ki wannan kwalliya haka dan tsabar jarabarki ta motsa shiyasa kika yimin ita, kijira zan biyaki hakkinki, kar Allah yakamani kodan saboda haka narasa ganin dai-dai, barin gama mushige dan nasan ko kinshiga ciki ba bacci zaki iya ba, mayya kawai.”

Maganar tasa tayima Aysher ciwo, amman ba yadda zatayi, komawa tayi ta zauna tana kissima abubuwa dayawa a ranta, wato yanada buk’atar ta amman shine zai juya maganar kanta, Allah kayimin agaji……..

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/23/2017, 18:37] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

 

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*

 

©Zeetty

PAGE 3-4
Washe gari da wani masifar yatashi, ko karyawan safe bai tsaya yayi a gidan ba.

Ita dai Aysher baiwar Allah fara gyaran gidan tayi tsaff tayima yaranta wanka ta shirya Aslam yatafi School.

Tagumi tayi tana tunanin halin mijinta da zaman su na da, da kuma na yanzu, tashare hawayen dake zubowa daga fuskar ta, hannu ta d’aga tana rokon Allah ya kawo mata mafita, amman cikin ranta ta kuduri wani abu a cikin sa.

12:00pm yashigo gidan da sallama kafin ya d’ora daga inda ya tsaya fad’i yake”Ke matsiyaciya fito, za’ayita ta k’are nagaji da wannan bak’in talaucin naki, daman tunda naga kinnace saini abin yabani mamaki, ashe kinsan kalarki wato mai farar k’afa ne ke, Mamana da kanta yau tace na hak’ura da wannan auren da kullum babu cigaba sai ci baya.”

Cikin K’walla Aysher ta fara magana”Kayi hakuri Abba Aslam, karka rabu dani a wannan yanayin, koma zaka sakeni ina rok’onka Alfarma kabarni nayi zaman ‘ya’yana dan Allah.”

“Mtswwww kinji tsiyar taki ba?, ana magana sai ki fara cewa yaran ki, toh ke kika haifarmin su, kinsan dai ke kad’ai bazakiyi cikin su ki haife ba, sai da taimakona, yara kuma ‘ya’yana ne dan haka zan sakeki yau basai gobe ba, ko Allah zai azurtani na huta da wannan bak’in talaucin da kika jefani tunda na aure ki, gurin aiki nawa ina kai takadduna amman haryau ba wanda suka kirani.”

“Kayi hakuri Abban Aslam idan har kayi hakuri ni kaina akwai lokacin da zan rabu dakai, lokacin nakejira yazo, zan rabu dakai rabuwa ta har abada.”

“Zancen banza zancen wofi, sai sanda kika gama tatseni na rasa wanda zan kama sannan kikeso na rabu dake ko?, muna fuka dabadan nasan halin yan gidan ku ba kuma yayan ki abokina ne, dasai nace ko mayya na aura.”

Kafin Aysher ta bud’i baki tace wani abu taji duka ta ko ina a gaban k’aramar yarinyar ta, Aysher tana kuka Afra tana kuka, baikula suba saida yayi mata ligis kafin ya tsalleke k’afarsa yabar gidan ko kallon ‘yar tashi baiyi ba, ballantana ya waiwayo yaga halin da matar tashi take ciki.

A hankali Aysher ta rarrafa taje kusa da ‘yarta ta rungumo tana lallashinta, itama yarinyar tasa hannu akan mahaifiyar ta alamar tana lallashinta, abin gwanin ban tausayi.

Aysher tana yashe a tsakar gidan takasa motsawa nan da can, saboda jikin ta gaba d’aya yagama tsami ciwo yake mata, 1:00pm k’anwar ta Maryam tashigo gidan Hannun ta d’auke da Aslam wanda yataso daga school suka had’u a hanya.

Dasauri Maryam ta saki hannun Aslam ta zura da gudu, dan ganin halin da yayarta take ciki, ta k’arasa tare da kamo hanun ‘yar uwar nata tana girgiza mata kai tana cewa”Aunty kardai ace haryanzu bakiyi girman daina duk ba a gurin YAYA SAMIR?, toh wallahi anyi na farko, anyi na k’arshe, yau saina fad’ama Umma da Baba dan wallahi bazaiyiwu ki zamo jaka a gurin sa ba, bayan duk hallaccin da kikayi masa a baya, aiban manta da d’an kunne da sarkarki da Gold da kika siyar kika bashi kud’in akan yaja jari ba, yace ya had’u da ‘yan damfara bayan shine cikakken madanfari saboda tayaya zaka bada kud’i kace ayi maka kud’i, saboda son banza, toh yau za’ayita ta k’are dole ya rabu dake Aunty Aysher.” Cikin fad’a da 6abin rai Maryam take fad’in haka kasan cewarta masifaffiya ce ta k’arshe.

Cikin sanyin ta Aysher ta d’ago kanta tace”Kiyi hakuri Maryam karki fad’a a gida, wannan abun yazamo sirri tsakanina dake, karki manta sau nawa Baba da Yaya suke zuwa sunayi masa fad’a akan dukan nan amman haryau ya kasa bari, idan kika fad’a agida raba auren za’ayi dan haka Yaya yace, nikuma banshirya rabuwa dashi ba yanzu, dan haka dan Allah kirufamin asiri, akwai lokacin da zaizo dole na rabu dashi, kid’auka wannan abin da Abban Aslam yakemin a matsayin tawa kaddaran da zan tarar a gidan aure na, taimaka ki juyemin ruwa nayi wanka, na shirya ko zanji sauk’in ciwo jikin nan Maryam.”

_”Aunty Aysher bazata ta6a canja wannan sanyin halin nata ba, shiyasa take cutuwa dayawa.”_

Cikin Zuciyar maryam take fad’in haka, sannu Aunty Allah kawo miki mafita, (tafad’a tare da kamo hanun yayar ta dan Zuwa band’aki). Ameen Maryam (tabata amsa)

Aslam da baisan wainar da ake toya ba, bayan baya gida amman jikin sa yabashi cewar Abban sane yayima Momy irin abin da yake mata kullum a gaban su (Duka).

Aslam yanada wayau kasan cewar shi yaro d’an shekara shida yana primary Two a School, haka Islamiyya yana Aji 2 duk aji d’aya yake tafiya da boko da Arabiyya.
Binsu yayi da kallo cikin Zuciyar sa yana mai k’ara tsanar Abban nasa.

Da taimakon Maryam Aysher tayi wanka tare da gasa jikinta, bayan tafito Maryam ta bata maganin ciwon jiki tasha anan bacci ya d’auki Aysher, bacci mai cike da alamun wahala.

Da wurwuri yadawo gida hanun sa d’auke da wani farin takarda, fuskar sa tana d’auke da alamun farin ciki.
Da sallama yashigo gidan ya tarar da Maryam a kitchen tana d’ora musu abincin dare, fuskar ta a tur6une ta gaisheshi, ya amsa da fara’a sosai yak’ara da cewa”Maryam kece a gidan namu, ya su Umma da Baba?”

“Suna nan lafiya” tabashi tare da shan toka (lols ‘yan skt)

“Ina Momy’n Aslam?”.

” Tana d’aki a kwance batajin dad’i.”

Sai yanzu Samir ya tuna da abinda yayi mata da safe kafin ya fita, cikin mutuwar jiki ya shige d’akin da take kwance.

A zaune yasameta tayi tagumi, yashigo da sallama ta amsa tana murmushin yak’e kafin tace”sannu da dawowa Abban Aslam, ya k’ok’ari?.”

“Alhamdulillah Sulty na, yau Allah ya kar6i addu’ar mu, ga takaddata ta d’aukar aiki a NNPC.”

Hannu Aysher ta d’aga sama tare da fad’in”Alhamdulillah, Allah nagode maka Allah maji rokon bawansa, nayi maka murna Abban Aslam Ubangiji yasa kafara a sa’a.”

Kai ya gyad’a yana fad’in”Ameen ameen Sulty na, kifagar ceni dan Allah.”

Shiiiiii Aysher tayi masa alamun yayi shiru kafin tace”karka fara Maryam tana gidan nan, kabari sai ta tafi.”

_Cikin zuciyar sa mamakin sanyin halin Aysher yakeyi da hak’urin ta, yana godiya da Allah baisa ya datse igiyar auren su dayayi niyyar yi yau ba._

“Bakomai Sulty barin je na dubo miki magani, ina ne yake maki ciwo yanzu.”

“Bako ina dan nasha magani, kasan cewar na tanadeshi tuntuni, saboda irin haka.”

Kallon matar tashi yay, yana tausaya mata abubuwan dayayi mata, kafin ya girgiza kai yafice dan barin d’akin.

Aysher kuwa mamaki ne ya rufeta yaushe rabon da Abban Aslam yakirata da wannan sunan *SULTY* tun farkon samun cikin Aslam.

 

“`Kukasance tare dani, dan jin farkon tarihin wad’an nan ma’aurata.“`

MAMAN HANAN
ZAUTEN LITTATTAFAN HAUSA
[12/23/2017, 18:37] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

 

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*

 

©Zeetty

PAGE 6-7
Cikin lokaci k’ank’ani al’amura suka canjama Samir da Aysher, kai tsaye aka bashi gida a NNPC dake cikin Quaters na Kaduna, komai da komai ansa a gidan bazasu shiga da komai ba sai kayan sakawan su, dan haka Aysher tayima ‘yan uwanta sallama da danginta, suka d’auki hanyar kaduna, bisa rakiyar k’awanta da wasu daga cikin dangin Mahaifiyar ta.

Kwanan sh d’aya ‘yan rakiya suka juyo dan komawa gida, Aslam da Afra ansamo musu makaranta anan cikin NNPC Quaters d’in. Wani kana kallonsu Aysher da Samir a wannan lokacin dole subaka sha’awa, dan tabbas hutu yazo musu sosai, gaba d’aya sun canja, musamman Aysher tak’ara wani fresh da haske, gata daman tubarkallah akwai kyau.

Satin su biyu da dawowa Al’amura duk sun canja, wani kulawa da soyayya Samir yake yima matar shi, wanda baita6a yimata ba a farkon.

Tausayin matar sa sosai yakeyi idan yatuna da abubuwan daya aikata mata abaya, lallai talauci baiyiba, dole anemi tsari dashi, kullum tunanin samir kenan a gida ko Office idan yakad’aice.

Fara aikin sa bada dad’ewaba aka k’ara masa matsayi a gurin aiki, wannan abu bak’aramin dad’i yayima Aysher da Mijinta ba.

Washergari har gurin aiki Aysher tarakashi bayan sunkai su Aslam School, tare suka bud’e sabon Office d’in Abban Aslam. Suka shiga da bismillah addu’a Aysher tayima mijin ta sosai kafin su shafa.

Samir rungumo Aysher yayi yana hawaye “Sulty na, kiyafemin na zalunceki dayawa, na biyewa sharrin shaid’an da zugin abokai, dan Allah kigafarceni (yak’arasa fad’a tare da k’ok’arin durk’usa mata).”

Saurin dagoshi Aysher tayi tana share mishi hawaye kafin tace”Abban Aslam na yafe maka, amman dan Allah nima kayimin alk’awarin idan natashi neman wani abu a gurinka bazaka hanani ba.”

Dasauri Samir yace”Namiki Alk’awari Sulty na, banga abinda nake dashi a duk duniyar nan, dazaki nema nakasa yimiki ba, anjima za’a kawomiki sabuwar motar ki, saboda yanzu hanun ki ya fad’a, zakidinga taimakamin dakai su Aslam makaranta da d’auko su.”

Kai kawai Aysher ta gyad’a masa.

Soyayya Samir yake nunama Sulty Aysher sosai.

*BAYAN SATI BITU*

Komai yawuce a gurin wad’an nan ma’auratan.

Ranar Monday da misalin k’arfe 2:00pm, akayima Samir waya daga School d’insu Aslam cewa yazo yad’auki yaranshi dan andad’e da tashi a School kuma gashi ankira wayar Madam akashe.

Arikice Samir yabar Office kai tsaye School d’in ya isa, yad’auki yaranshi ransa a 6ace, yana mamikin inda Sulty ta tafi batazo tad’auki yaransu a School ba, wayar ta kuma a kashe, Afra sai surutu take masa amman yak’i kulata, yana tunanin halin da zaije ya riski matar sa a ciki idan sun k’arasa gida.

Yana Parking yafito yabud’ema yaran baijira fito warsuba yasakai cikin gidan da sauri, yayi amfani da da key d’in gurinshi ya bud’e gidan, kiranta yafarayi yaji shiru, kai tsaye d’akin ta ya nufa dammmm kirjinsa yabuga sakamakon ganin Akwatinan Aysher a zube a kan gado, babu babban cikin sa, a hankali ya k’arasa kan gadon, ya k’arasa kan gadon cikin sanyin jiki, takadda yagani akan gadon a hankali yasa hannu yad’auka ya fara warwarewa, rubutun Aysher yagani kamar haka:-

_ASSALAMU ALAIKUM_
_Abban Aslam kayi hak’uri da hukuncin dana yanke a tsanin zamana dakai, zanyi hakan ne bawai dan bana sonka ba, a’a sai nace duk duniya bayan iyayenka nafi kowa sonka._
_Karka manta da alk’awarin dakayi min nacewa duk abinda na nema a gurinka zaka yimin, bakomai nake soba Abban Aslam dan Allah kataimaka ka sauwak’emin, murabu dakai rabuwa na har abada, bawai dan bana sonka ba saidon lokacin da nakejira yazo kenan naci gaba da hak’urin zamadakai, dan inaso na k’aryata duniya cewar ni mai farar k’afa ce, nashanye duk abubuwan da kakemin, har zuwa yanzu da Allah ya axurta ka, nayanke rabuwa dakai._
_Kataimaka kayimin abinda nakeso cikin ruwan sanyi, wallahi wallahi nagama zama dakai har abada, sai naji daga gareka._
_Ma’assalam._
*Matarka a baya, Aysher Muhammad Rogo.*

 

Muje zuwa…….

 

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: [11/19, 5:59 PM] Zeetty: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

 

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*

 

©Zeetty

“`Ayimin afuwa wajen rubuta PAGE nayi kuskure 5-6 zan saka, but nasa 6-7 so yanzu zan gyara.“`

PAGE 7-8

Samir yana gama karanta wannan wasik’ar ya sunkuyar da kansa k’asa yanajin zubar wasu hawaye masu zafi daga idanuwan sa, hak’ik’a abokan sa sun kaishi sun baro, yakasa yadda da k’addara, lallai imanin sa bai zamo cikakke ba, daga kansa yayi yana tunanin irin abubuwan daya aikatama Sulty Aysher a baya, lallai da wuya ta iya yafe masa………….

~ASALIN LABARIN~

_Aysher Muhammad rogo itace yarinya ta 4 a gurin iyayen ta Dr.Muhammad Rogo da Fatima, Isah ne babba sai Usman,Auwal sai Aysher, Hadiza da Auta Maryam._

_Iyayen Aysher ‘yan boko ne musamman Mahaifin ta wanda likitan hak’ori ne, Aysher sun had’u da Samir ne tun tana aji biyar a makarantar sakandire, abokine ga Babban yayanta Isah, tare suka gama karatu a B.U.K, kuma margayi malam Bashir amini ne sosai a gurin Dr.Muhammad mahaifi ga Aysher._

_Malam Bashir malamin makaranta ne kafin mutuwar sa, mutum ne nagari mai halin dattako._
_Sosai Dr.Muhammad yakar6i maganar auren Aysher da Samir, dan yasan halin mahaifin sa, kuma yana ganin hankalin Samir d’in ganin yadda suke tafiyar da al’amuransu da d’ansa Isah._
_Dakanshi ya samo musu aiki tare da Isah a ma’aikatar kar6an haraji ta garin kano, Aysher tana gama karatun Sakandire aka sha bikinta da Angon ta Samir._
_Farkon zaman auren su abin sai son barka ga duk wanda yaje gidan, wani irin soyayya suke yima junan su, wanda basa iya 6oyewa a gaban kowaye, mafi akasari ba’ason zuwa gidan musamman ranar Week end dan Samir dakan sa yayi gargad’i da hakan, a cewar sa, wannan ranar, ranar sa ne shi kad’ai, salon bai canja ba a lokacin da Aysher ta samu ciki, kulawa yake nuna mata sosai tare da tsantsar soyyayya ga abinda zata haifo masa._
_Lamarin yafaro ne bayan Haihuwar Aslam, lokacin yanada shekaru uku, a wannan lokacin sabuwar gwabnati ta hau kujerar mulkin kano, dan haka aka sallami ma’aikata dayawa, cikin su harda Samir. Hankalin Dr.Muhammad yayi bala’in tashi dajin wannan labarin._
_Shikansa Samir dafarko yad’auki al’amarin dacewa kaddara ne, amman daga baya yasamu wasu shaid’anun abokai suka zugeshi da cewa had’in baki ne daga gurin surukin nasa idan ba hakaba, meyasa ba’a kori Isah ba?, wannan kawai anyine dan a tozarta Samir d’in._
[11/19, 6:57 PM] Zeetty: _Dan anga yafara tara Iyali, tun Samir bai d’auki maganar da mahimmanci ba, har yad’auka, dan haka lokaci guda yafara canjama Sulty shi, abu kad’an idan tayi saiya rufeta da masifa da bala’i, wata rana har dukan ta yakeyi agaban Aslam, tun yaron baya fahimta har yafara ganewa, a haka Maryam k’anwarta tazo takawo mata ziyara wata rana ta risketa jiki duk shatin bulala kamar wata Jaka, hankalin Maryam yatashi dan haka takira yayan su Isah a waya tana sanar masa, hankalin sa a tashe ya k’araso gidan ganin irin dukan dake jikin k’anwarsa wani tausayin ta ya kamashi._
_Bayan ankaita asibiti binciken likita nafarko daya fara ganowa shine, Aysher tana d’auke da hawan jini, Dr.Muhammad ransa ya6aci dajin haka, yakuma tausayama ‘yar sa, dan yasan may be tana fuskantar matsala a gidan mijin ta, dan su kansu yagama canja musu baya zuwa gidan, idan suka had’u da Isah saidai Isah yayi mishi magana._

_Bayan ankirashi awaya an sanar masa suna asibiti fad’a yafarayi tare da borin kunya yana fad’in”akan meye za’ad’auki matar sa a kaita asibiti batare da sanin shiba, saboda an gama rainashi anga bashi da kud’i ko meye?,_ _ran Isah ya 6aci dajin haka, dan haka yaso bashi amsa, amman Mahaifinsa ya dakatar dashi, tahanyar nunama Samir cewar sunyi kuskure yayi hak’uri._
_Hakadai Zaman yaci gaba da kasan cewa, dan wata rana idan yayi mata dukan ma kulleta yakeyi a d’aki, dan gudun kar ‘yan gidan su, suzo suganta ballantana a taimaketa._
_Abokan sa suna ka’ara ingizashi musamman wani mai suna Kabir da cewar matuk’ar baya k’untatawa Aysher bazai huce takaicin abinda mahaifinta yasa akayi masa ba (Kajifa mai karatu)._
_Dan haka yak’ara kaimi wajen sambad’o mata rashin mutumci, horo da yunwa, baya bata kud’in cefane, akwai sanda tasiyar da Gold d’inta tabashi kud’in yaja jari, yace ‘yan damfara sun kwashe kud’in, idan yatashi zaginta kuwa sai yace”Shashasha wawuya wadda batasan ciwon kanta ba, muguwa irin mugaye masu bak’in hali, mai farar k’afa”, wannan zagin yana damun Aysher tasha zaunar dashi tace “meye laifin datayi masa”, sai yace”Mahaifinta yasa an koreshi a aiki, dan mugunta kuma duk inda yaje neman aiki mahaifinta yasa an toshe ba’a d’aukar sa, dan haka itama tayi bankwana da jindadin gidan aurenta.”_

_Dukan dayayi mata nak’arshe shine wanda ya sumar da Aysher, yatsallake yabarta a kulle a d’aki, Isah yakawo matarsa ziyara gidan Aysher yatarar gidan shiru sai kukan Aslam, kuma ya buga ba’a bud’e ba, dan haka yakira aka 6alle k’ofar anan yatarar da Aysher yashe a tsakar gida alamun bata numfashi, cikin tashin hankali yad’auki Aysher dan zuwa Asibiti._
_A wannan lokacin Aysher har targad’e yayi mata a guri biyu, (wannan wane irin zalinci ne kadaki mace, sannan ka kullota a gida kota rayu, kota mace, lallai dole a raba auren nan, dan Samir mugu ne, bason Aysher yakeyi ba), tunanin da Isah yakeyi kenan a ransa._
_Toh bayan Aysher tawarke Samir yagama borin kunyar sa da bayarda hak’uri, dan Isah yace saiya sakar musu k’anwa, Dr.Muhammad ne yakashe rigimar da cewar Samir yayi alk’awarin bazai sake bugun Aysher ba, nan take yayi wannan alk’awarin dan yanason matar sa tsabar talauci ne kawai da kuma zugan abokai._
_Bata sake zani ba, dan duka da zagin cin mutumci sai abinda yak’aru a gurin Samir, a haka aka samu cikin Afra, albarkacin cikin yarage mata wasu abubuwan, har aka haifi Afra, idan kaga Aysher dole kasan tana cikin wani hali duk ta rame ta lalace, Kabir yacema Samir” Hakanne dai-dai abokina, kaci gaba da aiki dole idan mahaifinta yaganta ransa ya6aci, kaga karama abinda yayi maka akan ‘yarsa.”_
_Sosai Samir yake amfani da shawaran da Kabir yake bashi, aganinsa bashi da wani aboki masoyi sama da Kabir d’in._
_A haka dai har aka haifi Afra, wulak’anci salo-salo ga kyara da hantara a gaban ‘ya’yanta, idan tayi magana ya wanketa da mari, Aysher tak’i fad’a a gida, dan a cewar ta akwai lokacin da zata rabu dashi, lokacin da Allah yasa yasamu aiki, zata nemi ya sauwak’e mata._

*Mai karatu kaji irin halin da Aysher ta tsinci kanta a gidan auren ta, menene ra’ayinku?.*

A hankali Samir yadawo daga duniyar tunanin daya tafi, yaji ihun yaran sa a falo, dasauri ya mik’e yafito ya samesu yace”kuzo kuje kushiga mota natafi gurin Momyn ku”, da sauri Suka ruga suna cewa”Abba yunwa mukeji.”

“Zan siya muku abinci a restaurant kuyi shiru” dan bayason damuwa, mafita yake nemowa kansa, baya fatan Aysher ta tona masa asiri a gurin mahaifinta bayan alk’awarin da ya d’aukar masa na cewar yad’aina gasa mata aya a hannu…………

 

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

 

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*

 

©Zeetty

*I Dedicated this page to you Gimbiya kilishi, babu wanda yakaiki son MAFARIN LAMARIN, SADAUKAR WA GAREKI*.

PAGE 9-10

Lokacin da Aysher ta iso kano gidan Iyayen ta, Mahaifin ta tasamu a k’ofar gida yana zaune yana alwalar sallah azahar, ya ta gaidashi ya amsa tare da tambayarta” lafiya kuwa Aysher da rana tsaka haka?”

Tace”Lafiya lau Baba”
Shige ciki toh barin je masallaci.

Da fara’ar ta ta shige gidan, ta samu Mahaifiyar ta tana tsakar gida, d’agowa tayi taga Aysher cikin fara’a tace”lale marhabin da mutanen kaduna barkan ku da zuwa kunsha hanya.”

Aysher dai batace mata komai ba saima fara’a da taketayi, ta shige falon su.

Bayan ta samu Nutsuwa tayi sallah tare da cin abinci, Mahaifin ta ya aiko kiranta zuwa falon sa, ta mik’e ta tafi, ta sameshi a zaune gaisheshi tafara yi kafin yasake tambayar ta “ko lafiya tazo haka, kuma batare da yara ba?.”

Tace”Baba dan Allah ku gafarceni akan wannan hukuncin da nakeso na yanke, Baba dan Allah kubani goyon baya na rabuwa da Abban Aslam, yanzu ne nakeda wannan lokacin, yanzu ne zan nuna masa cewar niba mai farar k’afa bace kamar yadda yake cewa tunda saida yayi arziki na nemi rabuwa dashi, Baba na tabbata duniya bazata zageni ba akan hakan, baza’ace na rabuda shi dan talaucin sa ba.”

“Bangane abinda kike nufi ba Aysher, yimin yadda zangane.”

Aysher tace”Baba so nake Abban Aslam yabani takadda ta na rabuwa dashi har abada.”

A razane Mahaifin nata ya kalleta tare da tambayarta dalili.

Taci gaba da cewa”Baba Abban Aslam bai ta6a canjawa ba, akan abinda yakemin abaya, kamarsu duka, zagi da cin mutumci, duk kuwa da irin jan kunnen dakai da yaya Isah kukayi masa baidaina ba, nayi hakuri ne banzo na fad’a a gida ba, saboda jiran irin wannan lokacin dan idan kuka raba auren mu a wannan lokacin duniya zata zageku, ace dan bashi da kud’i ne, sai yanzu Baba dan Allah karku takuramin na koma gidan sa, banason ko ganin fuskar sa ne.”

“Bawanda zai takuraki, sha kurumin ki k’anwata, Allah miki Albarka.”

Bawanda yasan da shigowar sa (Yaya Isah) tsakanin Baba da Aysher sai jin maganar sa sukayi,

Dan haka Baba yakasa bata amsa, gaishe da mahaifin nasa yafarayi, kafin yace”Baba kaduba maganar yarinyar nan dakyau, ni daman nayi mamakin jin shirun Aysher, amman kowa yaganta yasan tanacikin damuwa, Baba bazata koma ba, mu nuna masa cewa akwai banbanci, ni kaina Baba abinda yake mana a lokacin raina yana 6aci, dan akaine kake dakatar dani, abarshi yazo muji daga gareshi.”

Kai kawai Baba ya gyad’a musu kafin yace Aysher ta tashi ta tafi, bayan fitar ta suka ci gaba da tattaunawa, shima abin ya6ata masa rai, wato Samir baiji duk maganar dayayi masa ba da nasiha ai talauci ba hauka bane.

*********

Misalin k’arfe 5:00pm Samir ya iso k’ofar gidan surukan nasa, kana ganin sa kasan yana cikin damuwa, ya taras da Yaya Isah a k’ofar gida, fitowa yayi bayan ya gyara parking, tare da bud’ewa yaransa sufito, da sauri suka ruga zuwa cikin gidan kakan nin nasu.

K’arasawa yayi gurin Isah, ya mik’a masa hannu sukayi musabaha, kafin yafara gaishe da Isah, Isah ya amsa ba yabo babu fallasa, tun daga nan jikin Samir yafara yimasa sanyi, dan da alama Aysher ta fasa kwan.

Dan haka yace ma Isah”Abokina dan Allah Baba yana nan kuwa?.”
“Eh yana ciki Bismillah daman kai nake jira kazo na wuce gida, mushige daga ciki.”

Kai tsaye falon Baba suka shiga, bayan gaishe-gaishe, dakin yayi Shiru dan haka Samir yafara magana kansa a k’asa”Baba nayi laifi ku gafarceni, ku taimaka Aysher tadawo dakin ta, mu reni yaranmu ni da ita, dan Allah Baba.”

Isah yayi farat zai fara magana Baba ya dakatar dashi kafin yace”Bakomai Samir ayanzu komai yana hannun Aysher idan ta amince zata dawo dakin ta falillahil hamdu, idan kuwa bataso bazamuyi mata dole ba, dan ita keda za6in zama dakai, nidai takaicina guda d’aya ne, rashin jin maganata da bakayi ba, amman bakomai, wannan yaron (Isah dan baya kiran sunan sa, d’an fari ne) muje ka turo masa Aysher.”
Tare suka fice dan barin falon, mintuna kad’an saiga Aysher ta shigo hanunta d’auke da hanun yaranta Aslam da Afnan tayi sallama tashigo, da sauri Samir ya mik’e tare da rik’o hanun ta, ya zaunar da ita jikin sa har rawa yakeyi, idanuwan sa cike suke da hawaye, yafara magana da cewa”Sulty baikamata ki yanke mana irin wanna hukuncin ba, Sulty baikamata su Baba suji wannan maganar ba, haba Sulty yanzu idan kikamin haka kinyi adalci kenan, kiduba yaran mu, zasu koma marayun dole, Sulty dan Allah tashi kishiga gida ki kwaso kayanki mu wuce gida dan Allah.”

Shiru Aysher tayi masa kamar bazatayi magana ba, kafin daga baya tad’ago babu alamar karaya a fuskarta tafara magana”Abban Aslam kayi hak’uri nariga nayi rantsuwa wallahi bazan cigaba da zama dakai ba, sanda kake zagina, kana cimun mutunci baka duba yaran mu ba, asalima a gaban su kake duka na da zagina harda cimun mutumci, kayi hak’uri Abban Aslam, arzikin ka bazai saka naci gaba da zama dakaiba, bazai rud’eni na manta da abubuwan dakayi min ba, na barka ‘ya’ya kuma nabarsu a hanun Allah, zai dubamin su, akwai marayun da suke rayuwa babu uwa babu uwa sun bar duniya, wasu ma *GIDAN MARAYU* (Littafin Sistoh na Beauty Queen), anan suke rayuwa dan haka Allah yadubamin su, rok’ona gareka shine tunkafin rayuka su gama 6aci, ka sauwak’emin cikin ruwan sanyi ayau kafin kabar gidan nan.” Tana gama fad’in haka tabar d’akin, kotakan yaranta bata biba.

Shiru Samir yayi dan shikam ko sama da k’asa zasu had’e bazai ta6a sakin Sulty Aysher ba.

 

 

 

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: [11/26, 8:51 AM] Zeetty: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

 

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*

 

©Zeetty

 

Dis page is Dedicated to *AYSHER* All over the world, *_Sosai nake sonku, Sosai nakeyi daku up up Aysher._*

 

PAGE 11-12

Samir dayaga duk antashi anbarshi a falon har uwar gayyar wato Aysher, cikin sanyin jiki yakamo hannun yaransa, a hankali yayi musu magana kamar mai rada yace”Kuje kuyima Momy sallama zamu tafi.” Afnan da nok’e tare da cewa “Abba mudai kabarmu anan ko kuma a tafi da Momy”, dariyar yak’e yayi cikin dauriya domin kuwa gab yake da fashewa da kuka yace” Kuje Afnan, Aslam kama mata hannu Momyn ku zata dawo very soon, kuma saboda school ne kuma exams zaku fara dana barku.”

A hankali Aslam yakama hannun kanwarsa suka shige cikin gidan, shi kuma Samir yafita dan jiransu a mota, ya sunkuyar da kansa akan sitiyari yafad’a kogin tunani, Isah ne yafito ya bubbuga masa glass d’in motar ya d’ago da kansa da sauri ya kalleshi, Isah yace keep calm my friend, gasu Aslam nakawo maka, muna jiran takaddar Aysher pls koda text msg ne ta waya kayi mata mun hutar dakai zuwa. Cikin sanyin murya Samir yace”haba Isah kaifa babba ne, kaida zaka dai-daita al-amarin kuma kaine mai ruwa da tsakin ayi sakin?”, murmushin takaici Isah yayi kafin yace”ashe kasan da hakan baka dubi girma naba kake dukan k’anwata da azabtar da ita a gaban yaran cikin ta”, girgiza kai Isah yayi kafin yakara cewa”Aslam shekarun shi 6 yanzu, Afnan 3½ but yanzu da suka shigo cikin gida cewa sukeyi Momy kitaso mutafi, Abba bazai sake dukan ki ba da zagin ki, kinga ai yadaina tunda muka dawo gidan ‘yan gayu, toh Samir tayaya zaka goge wannna hoton a zuciyar yaranku for God sake?, jeka kawai akwai Allah amman wallahi saika saki Aysher.” Yana gama fad’in haka yasakai yabar gurin, cikin sanyin jiki Samir ya saka yaranshi a mota yajasu sai Kaduna.

A gida komai ya cakud’ema Samir aikin Office ga hidiman yara, lallai yasara Matar shi Aysher, ashe ba karamin aiki takeyi ba a gidan, shiyake musu wanka break fast, lunch da dinner kuma saidai suyi take away, yara sun dawo marayun dole idan kagansu dole su baka tausayi, Samir yana bama kanshi kwarin gwiwar cewa wannan week end din idan yatafi kano tun friday sai sunday zai dawo shida matar sa, yakira wayarta yafi a kirga baya zuwa da’alamar ta canja layine saboda shi, Ohhh shikam Kabir yakaishi yabaro da muguwar shawarar daya dinga bashi.

Haka al’amuran suka cigaba da tafiya har zuwa ranar juma’a, sai da Samir yajira aka taso ‘yan school kafin yashiryasu yadauki hanya zuwa kano, kaitsaye gidan su Aysher yafara tsayawa yatura yaran tare da fad’a musu cewar zaizo anjima shida Baba Mu’azu (Kanin Mahaifinsa).

Aysher taji dad’in ganin yaranta, nan kakar su tafara nan da nan dasu, Maryam ma ‘yan matan ABU anzo hutu, dawowanta tak’ara zuwa yayar tata tana sake tuno mata wasu abubuwan data manta dasu wanda akayi agaban ta, kalmar mai *_MAI FARAF K’AFA_* sosai yake 6atawa Aysher ranta idan harta tuno dashi.

Da daddare Baba Mu’azu yazo tare da Samir, Baban Aysher suka fara sallama dashi, bayan yafito tare da dogon gaishe2, Baba Mu’azu yafad’i dalilin zuwan nasu” wato Mal. Muhammadu yaron nan Samir tazo gurina tare da sanar min irin aika-aikar dayayi hak’ik’a ni kaina banso zuwa ba saida yad’aukomin Mahaifiyar sa, dan Allah ayi hakuri adubi zuri’an da Allah yafara basu, Uwata ta koma d’akin ta dan Allah.”

Shiru Baba yayi dan yana bala’in jin kunyar Mal.Mu’azu amman hakan bazaisa a fasa hora Samir ba dan haka yafara bama Mu’azu labarin irin gashin ayar da Samir yayima Aysher harda kiranta da yake _MAI FARAR K’AFA_, duka da zagin cin mutumci, sau biyu ina zuwa har gida nayi masa nasiha ashe baya shigarsa, baifasa ba dan haka ni babu abinda zace anan kuyi hak’uri. Shiru Mal Mu’azu yayi kafin yace”Naji takaicin wannan lamari, naji haushi uwata tanada gaskiya wallahi danasan hakane da ban zoba, ni kunya duk ta kamani, sai kaje kanemo abokan naka da suke baka shawara suzo maka bikon matar ka, ba ruwana.”
Cikin 6acin rai yayima Alh.Muhammad sallama yatafi kotakan Samir baibi ba.

Alh. Muhammad ma tashi yayi yashige gidan yabar Samir a zaune tagumi yayi shi kadai yasan abinda yakeji cikin heart dinsa.
[11/26, 10:29 AM] Zeetty: Haka Samir yagama hutun karshen makonsa yakoma batare dayasamu had’in kan Aysher ba, har abokansa yakawo mata Aysher tayi musu tass (haka masu sunan suke akwai hakuri, amman fushin su bakyau).

A haka dai har aka shafe wata guda batare da Aysher ta sauko daga dokin nak’in data hauba, tarantse bazata koma ba, dole Samir yad’auko Mahaifiyar sa yakomar da ita kaduna saboda kula da yara.

Ranar wata Asabar Samir yashirya kamar kullum amman wannan karon da takaddar sakin Aysher mai d’auke da saki 1, yatafi kano tare da alwashin zaiyi ma Aysher saki d’aya ko zata sauko su mayar da auren su, idan harta huce kuka yayi sosai kafin ya rubuta saki d’ayan, sosai yakeson Sulty, amman kaddara da son zuciya gashi yarabasu.

Koda yaje batare daya ja dogon lokaci ba yasake bama Aysher hakuri, amman tace tanakan bakanta dan haka yad’auko takadda idon sa sanye da bak’in glass bazaka gane yanayin dayake ciki ba, ya mikawa Aysher farin envalope d’in tare da check na kud’i, kafin yadaure saboda kukan zuciyar da yakeyi ya durk’usa yana cewa” Sulty kigafarceni, ina fatan zaki huce very soon nazo mu mayar da auren mu, ki zauna da yaranki, ga kud’i kirike a hanunki zan aiko miki da motar ki dana siya miki, ki taimaka ki bani sabon number ki koba komai zamuyi zumunci albarkacin su Aslam, ki d’aukeni yaya abokin shawaranki pls.”

Cikin sanyin jiki Aysher takarba ta saka masa number tana mika masa wayar tabar falon da sauri saboda wani kuka daya taso mata.

Samir ma ikon Allah ne kawai ya mayar dashi gida kaduna, kamar amafarki yasaki Sulty shi.

 

Muje zuwa dan yanzu za’afara chakwakiyar.

 

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

 

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*

 

©Zeetty

PAGE 13-14

Cikin sanyin jiki Samir yajawo motar sa tare da barin k’ofar gidan, wayar abokin sa Kabir yakira yake shaida masa cewar yaufa ya saki Sulty, wani ihu Kabir yasaki tare da cewa”Like seriously abokina?”, shiru Samir yayi yakasa bashi amsa dan yana tunanin wannan farin cikin da Kabir yakeyi kuma na menene?.

“Hello! Samir kanajina kuwa, da gaske kasaki Aysher?.”

“Eh Kabir zanyi maka wasa ne da wannan zancen da ko a mafarki banyi tunanin faruwar shi ba?.”

“Kayi hak’uri abokina kad’auki hakan a matsayin jarrabawa, kaidaga hutu ma ya sameka, karabu da jangwam, kaidai Allah baka wadda tafita kawai.” Cewar Kabir.

Samir yayi wani huci tare da fesar da iska mai zafi, kamar Kabir yana kallon sa yace”Har’abadah bazan samu kamar Aysher ba, dagaske nayi rashin da bazan ta6a mayarwa ba, nidai fatana tasamu mu dai-daita kafin ta kammala iddar ta mu maida auren mu, bari dai zankira ka idan nasauka zan wuce kaduna ina hanya.”

“Okay saika kira Allah tsare.”

Wani ihu Kabir yasaki, tare da cewa “Alhamdulillahi yau burina yacika, zan samu gwarzuwan zuciyata, shege harda wani cewa zaka maida ita kafin ta gama idda, ai duk yadda yaza’ayi saina zuge ka baka mayar da ita ba, har sai tagama idda lokacin kuwa tazamo allura cikin ruwa, barin harzarta zuwa na fara kaima mahaifinta gaisuwa, yasan da zamana tun wuri.” Zancen da Kabir yakeyi kenan shi kad’ai yana zaune a fine time restaurant, ya mik’e dan barin gurin.

Dole ne na hanzar ta zuwa gidan su Aysher yanzu danyi mata jaje, daman bata san ina daga cikin abokan Samir ba, shiyasa nak’i zuwa bata hak’uri karta ganeni, tsarina ya lalace (Kabir ke fad’in haka cikin zuciyar sa).

“`******“`
Aysher kuwa tana shiga falon Mahaifiyar ta da takaddar sakin a hannun ta, neman guri tayi tazauna kafin tafara kuka mara sauti.
Umma batayi yunk’urin hanata ba, saida tayi mai isar ta tayi shiru dan kanta, kafin Umma tayi magana”atoh daman shi mutuwar aure ai ciwo ne dashi, banda haka wane irin baki ne da nasiha banyi miki ba?, amman keda Yayan ku da Mahaifinki kuka kafe akan maganar shegen taurin kai irin naki kamar mutanen farko, tare da goyon bayan su, kiyimin shiru gaki ga gidan na.” Tana gama fad’in haka tamik’e tabar falon.

 

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: [12/1, 8:28 AM] Zeetty: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

 

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*

_Happy Maulud to all ‘Darika muslim Brother’s & Sister’s around the world._

*Ina maka murnan zagayowan watan haihuwarka AHMAD YAKASAI, Allah k’aro shekaru masu albarka.*

_Kucigaba da kasancewa dani domin fuskantar sak’ona danakeson isarwa a wannan labarin, lamarin sosai yana faruwa kamar yadda wata tayimin magana ta Pc kamar haka:-_

*+23480534553…..*
_Assalam Maman Hanan sunana Maman Ayman, dan Allah kici gaba da labarin MAFARIN LAMARI jinshi nakeyi kamar labarina kike bayarwa, sai dai akwai dan banbanci, amman wlh yadda Samir yakecema Aysher mai farar kafa haka mijina da danginsa inaso naji yadda karshen labarin zaizama,muna tare dake ubangiji yakara miki basira, inayinki sosai burina wata rana nazo naganki marubuciyar DABI’A da Mafarin lamarin labaru masu taba zuciya nagode, kiyi saving number na dan Allah, sunana Maman Ayman._

*AMSA*
_Wslm! Nagode Maman Ayman Allah bar zumunci, naji dad’in addu’arki, zanyi saving number ki, In sha Allah idan nagama rubutawa zanyi miki wasu tambayoyi idan badamuwa, Nagode. Maman Hanan ce_

 

©Zeetty

PAGE 15-16

Bayan Sallah magriba Kabir yazo k’ofar gidan su Aysher, ya faka motar sa a gefe yakulle motar yafito, kai tsaye gurin Mahaifin Aysher ya dosa yayi masa sallama ya amsa, ya durk’usa har k’asa ya gaidashi ya amsa fuska a sake, can Alh. Muhammad yace”Sai dai bangane waye ba.?”

Sosa kai Kabir yayi da mukullin motar sa kafin yasake duk’ar dakai alamar mara gaskiya yace”Baba gaskiya baka sanni ba, nadai zone zan wuce natsaya mugaisa, zantafi a huta lafiya.” Yak’arasa fad’a bayan yamik’e dan barin gurin.
Mamakine sosai yakama Alh. Muhammad amman saiya saki fara’a yadinga shima Kabir albarka, sosai Kabir yaji dad’i dan haka yace in sha Allahu zandinga zuwa muna gaisawa Baba idan nazo anguwar nan.

Bakomai yaro nagode sai kazo d’in.

Mota Kabir yakoma yashige zuciyarsa cike da murnan tarkon sa na farko ya d’anu (ma’ana yafara samun sa’a).

Sosai Alh.Muhammad ya kwantar wa da Aysher hankali, dan duk yadda taso da mutuwar auren bayan anyi mata kuma lamarin ya bugeta sosai. A hankali kuma komai ya wuce mata, ta maida hankali wajen kammala iddar ta, gefe guda kuma Isah yafara mata chuku-chukun samun makarantar School of Nursing dake Aminu kano teaching Hospital.

Samir ma yana kiranta lokaci zuwa lokaci dan bayason takura mata da kira, so yake saita huce sosai kafin ya dawo da maganar komen ta, koda kuwa ace tagama iddar tane, sosai Kabir yake k’ara zugashi dan ganin yacire Aysher a ransa, ballantana ma da Samir d’in yasake samun k’arin girma a NNPC d’in aka mayar dashi Abj, sosai Kabir yace dan yarabu da Aysher ne cigaba ma yanzu yafara gani yasa ido. Maganar sa basa samun matsuguni a zuciyar Samir yadda suke shiga haka suke fita, dan yanzu a shirye yake koda kuwa ace zai sake komawa gidan jiya (talauci) indai zaisamu sulty ta dawo zai hak’ura.

Aysher takirashi tayi mishi murnan samun k’arin girman da yayi, yaji dad’in haka sosai godiya yashiga yimata kafin yace”Dan ma bana tare dake Sulty dukiyar nan ai duk na banza ne, kigafarcini dan Allah.”

“Komai fa yawuce Abban Aslam, haka Allah ya nufa, ni dai bayan komai ya lafa kataimaka kasamowa su Aslam Uwa dan Allah, Mama ta huta itama dan lokacin hutun ta kenan bazai yiwu tayi fama da jikoki ba tagama daku.” Tak’araaa fad’a tana dariya.

Mamakine cike a zuciyar Samir “wato Sulty yana mata maganar komawarta gidan shi, ita kuma tanayi masa maganar yayi aure.”

Huci yasaki mai zafi kafin yace”Nagode da shawara, d’auka ba dole bane nagode Sulty sai anjima.” Kashe wayar yayi Aysher tabi wayar da kallo “kai Abban Aslam akwai rigima, nikam ai nagama zama dakai (tafad’a a zuciyarta).”

*BAYAN WATA UKU*

Abubuwa dayawa sun faru, ciki harda komawar Samir NNPC na Abj, tubda yasaki Aysher baisake zuwa kano ba, sai dai suna waya sosai da Aysher.
Aysher kuma takammala iddar ta, a dai-dai lokacin da admission d’inta na samun makarantar Nursing yafito, dan haka takira Abban Aslam take sanar mishi akan yayi mata addu’a tafara a sa’a.

Takaici ne ya lullu6eshi (Lallai Sulty bata da tausayi) dan haka yace”Sulty manya, karatu ma kika koma, babu ranar aure kenen ko.?”

“Abban Aslam ai nasan saika rigani aure, dan Allah kadaure kayi zama hakan ba girmanka bane, idan kayi nikuma sai nafara niyya.”

“Kedai Sulty wato nacire rai a shigowa layin zawarawa kenan, shikenan, zan d’aure naduba maganarki kodan gujewa fad’awa halaka, dan nikam ba dutse bane, inada lafiya sha’awa dole nayita, dan ma Allah yana kareni, amman zan gud’aure nayi auren kodan ragema kaina zafi, bari idan nakoma gida zankiraki muyi wata shawara.”

Sosai Aysher taji haushin maganar Samir, dan gwanine wajen iya sosayya, wato aure zaiyi kuma yadinga kwana d’aki d’aya da matar wani kishin sa wanda bata ta6a jinsa ba sai a ranar taji yasauka a Heart d’inta, dan haka a hankali tace”Toh Abban Aslam saika kira, Allah taimaka.”

“Ameen Sulty nagode.”

*YASEERA*
Yarinya ce yar gata a gurin iyayenta Alh. Auwal Matamaki da Matar sa Dr.Salma, ita kad’aice ‘ya mace cikin su uku da Allah yabama iyayen ta, kuma itace k’arama, yarinyace marajin magana, a turai tayi karatu tun daga Secondry har jami’a, babanta babba ne a NNPC na Abj, Mahaifiyar ta kuma lecturer ce a jami’ar gwagwalada dake Abj.
[12/1, 10:36 AM] Zeetty: Dawowar Yaseera gida tadawo dawasu miyagun halaye na shaye-shaye da bin maza, dan tun tana shekara 14 takware da mu’amala da maza sanadiyyar fyad’e da wani bature yayi mata, shikenan Yaseera tazama idan ba’ayi mata ba batajin dad’i, kafin daga baya tagano wannan rayuwar tafi komai dad’i, a hankali takoyi shan kayan maye harda giya da hodar iblis(cocaine), har allura take yima kanta, a can turai (America) tayi alk’awarin aure da wani bature d’an asalin k’asar america, har zobe yabata itama tabashi kowa yasaka a hanun shi.

Dawowar ta gida bayan kammala karatunta Mahaifinta ya girgiza da ganin wannan al’amari na halayen d’iyarshi guda d’aya tilo Yaseera, hankalin sa baisake tashi ba saida ta sanar mishi alk’awarin auren da sukayi da johnson. Sosai hankalin Alh. Auwal mataimaki yatashi dajin haka, dan haka a ranar da aka dawo da Samir k’ark’ashin sa a Abj sati biyu yad’auka yana lura da d’abi’un sa, a hankali yagano yanada halaye masu kyau, dan haka yabinciki Samir ina matarshi, dan binciken dayasa akayi mashi akan Samir d’in anshaida masa bashi da mata. Samir ya sanar mishi cewa”sun rabu, bisa ga wani kaddara amman yanasaka ran dawowarta komin daren dad’ewa.”

Alh. Auwal bai tsananta tambayar shi ba, saima fatan ganin lokacin dayayima Samir, kafin yabashi labarin yarinyar sa Yaseera, da rayuwar datayi a turai da sabuwar halayyar data koya acan, yak’ara dacewa “na yaba da halayenka Samir shiyasa kakai matsayin nan a d’an shekarun ka dafara aiki, kanada hakaye masu kyau dan sosai nayi bincike a kanka, yanzu haka taimakona zakayi, kayi jihadi Allah zaibaka lada wajen auren ta, nasan idan ta aure ka zaka taimaka wajen nutsar min da ita, hakan bazai hanani idan katashi dawowa da uwar ‘ya’yanka ba nasa hannu wajen zuwa maka bikon ta, dan Allah kataimakamin nayi tunanin aurar da Yaseera a wannan lokacin shine zai kautarmin ita daga fad’awa auren k’asurgumin k’aton arnen nan bature wato Johnson. Ina jinka meye ra’ayinka.?”

Gumi sosai Samir yafara sharewa kafin yace”Naji buk’atarka ‘yalla6ai, kabani lokaci zanje nayi shawara nan da kwana biyu zakajini.”

“Dan Allah kayi shawara maikyau, nagode saina jika.”

Yamik’e tare da ficewa daga office d’in Alh. Auwal d’in.

Muje zuwa

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

 

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*

*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
—-
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
—-
*CHECK OUR BLOG’S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
—-
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*[email protected]*

©Zeetty

PAGE 17-18

Da daddare Samir yakira wayan Aysher yake shaida mata yadda sukayi da uban gidan sa, bai 6oye mata komai ba, dan haka jikin Aysher yayi sanyi tana tunanin wacce Abban Aslam zaikawo gidan sa, a matsayin Uwar ‘ya’yansa karo na biyu shin mai irin wannan halayen da d’abi’un ta cancanta tabama yaranta tarbiyya kuwa.? (Tambayar da Aysher take yima kanta kenan a cikin zuciyar ta).

“Hello! Aysher kinajina kuwa.?” A sanyaye tabashi amsa da cewa”Inajinka Abban Aslam wallahi jikina ne yayi sanyi danaji halayen Yaseera, amman da farko harna fara murna da farin cikin su Aslam zasu samu sabuwar uwa ashe abin ba haka bane.”

Samir yace”toh yaza’ayi Aysher nida aka taimakawa, dan ni akaran kaina bazan iya samo matar aure a karo na biyu ba gaskiya, dan haka zan amince da Yaseeran kawai tunda alfarma yanema da kuma neman shiriyar ta da gudun fad’awa auren kafuri, idan har ta shiryu ta dalilina ai inada lada.” Ya numfasa yana jiran yaji ko Aysher zatace wani abu amman yajita shiru dan haka yaci gaba da cewa”ai duk laifinki ne, Allah ma munayi masa laifi ya yafe mana ballantana d’an adam, na baki hak’uri Aysher kink’i hak’ura daga k’arshe ma dan tsabar takaici wai kinkoma makaranta, hmm duk laifin Isah ne amman bakomai, Allah yasa mudace.”

“Ameen thumma ameen, bakomai naji bayanin ka, ka’amince masa kawai Allah yasa hakan shine mafi alheri, lallai zamuzo kaduna muna ‘yan d’aukar amarya, abani kwangilar had’a kayan aure.” (Aysher tafad’i haka cikin dauriya da raha domin 6oye damuwa daya ziyarci zuciyarta na wucin gadi.)

“Mtswww kinji matsalar ki ba, wato ko irin kishin nan bakyayi alamar kindena sona, toh sai anjima zankira ki idan naje gidan, dan munyi waya da Mahaifin ta yace duk shawarar dana yanke naje gida na sameshi, idan har na amince sai a kirata mugaisa dan haka sai kinjini.”

A sanyaye Aysher tace”toh Allah yakaimu saika kira d’in, nagode Abban Aslam.” Suka katse wayar.

*******

Wata kyakkyawar matashiyar budurwa na hango, tana kwance akan wani makeken gado hanun ta rik’e da waya tana chat da saurayinta Johnson, tana fad’a mishi yadda tayi missing d’inshi sosai. Gefen ta roba ne mai d’auke da lemon Fanta wanda tayi mishi sirki da codein tare da k’wayar tramol tana shansa a hankali, wani sanyin dad’i ne yake ziyartar zuciyar ta yayin da take shan wannan fantan (haka take yi, koda yaushe friedge d’in dake d’akin ta baya rabo da lemu ka, wanda akayi masa sirki da sinadarun kayan maye dangin su giya, da k’wayoyi, har jikin ta yasaba da shansu, ko da tasha baya sakata maye, batare da sanin iyayen ta ba). Muryan yaseera harya bud’e tsabar shaye-shaye.

Da daddare Samir ya dira gidan su Alh. Auwal Mataimaki, kai tsaye akayi masa masauk’i a falon bak’i. Mintuna kad’an saiga Alh. Auwal yafito yana duba agogon hanun sa, hannu yabama Samir sugaisa, amman Samir yakasa mik’a masa, durk’usawa yayi yana gaisheshi ya amsa fuska d’auke da fara’a”lafiya lau Samir, ya gidan da yara?”

“Duk lafiya Alhamdulillah.”

“Masha Allahu, Malam Samir lallai kacika alk’awari, ya ake ciki?, Allah yasa muji alheri.”

Kai Samir yasake duk’arwa k’asa kafin yace”eh yalla6ai bakomai na amince Allah sanya mana alheri.”

Fara’ar dake d’auke a fuskar Alh. Auwal bazai misaltu ba fad’i yake”Alhamdulillahi Samir nagode Allah yayi maka albarka, bana buk’atar komai daga gurin ka sai sadaki, nan da sati biyu masu zuwa za’a d’aura aure saika sanar da manyan ka, barin shiga na turo maka ita.”

Kafin Samir ya baci amsa Alh. Auwal ya mik’e tare da ficewa daga d’akin, yana sa6a babban rigar sa.

Samir harya gaji da zama a falon saboda jimawa da yayi a zaune, ita kuma bata shigo ba, ya d’auki ruwan da aka kawo masa tare da lemo, ya zuba ruwan a kofi yakafa a bakin sa yafara sha, wani kamshi yaji yafara ziyarta hancin sa kafin ya hangota tashigo falon, jikin ta d’auke da wasu matsatstsun riga da siket mai lak’abin (Jahannama ga fasinja), k’afar ta kuwa d’auke yake da wani dogon takalmi mai tsini, siririya ce sosai Yaseera.

Ta k’araso cikin salon yauk’in ta idanuwan ta sunakan Samir, _kai wannan guy d’in yayi bala’in had’uwa, zan aure shi kafin na auri Johnson, shi yana Nigeri’a, Johnson yana Amerika._ (Cikin zuciyar ta Yaseera take fad’in haka).

“Hi! My dear watz up?.”

Samir daya tsaya yana k’are mata kallo, zuciyar sa cike da takaicin irin shigar rashin mutuncin dake jikin ta, shi sam tun shigowar ta kallo d’aya yayi mata, batayi masa ba dan baza’a had’ata da Sulty d’inshi ba.

A firgice ya juyo dan jin an hure masa ido.

Cikin gabjejiyar muryar ta tace”haba D-lovely inayi maka magana kayi shiru why, Dad yace zamuyi aure nan da 2 weeks dan haka i can’t wait to see dat day, saboda sosai kayimin dan haka zan shayar dakai zumar da baka ta6a shan irin sa ba, me kace.?”

Shiru yayi mamaki yana sake rufe shi, jiyayi ta kawo masa wani irin runguma da sauri ya mik’e daga gurin, yana fad’in”subhanallah Yaseera meye haka, kanki d’aya kuwa?.”

“Toh D-lovely inason na nuna maka yadda nake sonka ne, karka bani kunya mana kanayin abu kamar ba wayayye ba, meyasa kazo mud’anyi romancing before katafi, karage zafi.”

“A’a nikam natafi sai na sake dawowa, daga ganin ki bakya cikin hayyacin ki.”

Yaseera tace”Okay D-lovely sai kadawo d’in, tashi d’aya naji na kamu da wani irin soyayyar ka gami da zazzafar sha’awar ka, nifa yanzu codien na sha kwalba d’aya kawai D-lovely kaga ai bansha da yawa ba.”

“Uhmmm baki sha ba kam, sai nazo bye.”

Samir bai jira cewar ta ba yafice a falon da gudu, dan ganin tana shirin kawo masa wani runguman.

Da daddare yakira Aysher a waya, tana d’auka yafara magana wanda daga jinsa tasan yana cikin damuwa yace”Sulty kinga abinda kika jawomin ko?, wai yau da ‘yar codien nayi gamo matar da zan aure, totally batayimin ba k’afuwan ta kamar marad’in acca, jiki kamar sanda, baki ga abinda tayimin ba daga zuwa na (kwashe labarin abinda yafaru a gamuwar sa da Yaseera yayi, yafad’ama Aysher).”

Tausayinsa sosai ne yakama Aysher bayan yagama bata labari a hankali tace”kayi hak’uri kawai Abban Aslam kataimaka masa waje gyara masa tarbiyarta kamar yadda yanema Allah zai dafa maka, in sha Allah zaka samu lada.”

Cikin murya mai rauni Samir yace”daman nasan haka zakice, bazaki ta6a jin haushin hakan ba, bakomai nagode wallahi da ace ban amince masa ba tun farko, wallahi da na fasa, shiyasa yayimin dabaran cewa sai na fara amince masa kafin naganta, saboda yasan halin ‘yar tasa bakomai sai da safe.”
Diff ya kashe wayar baijira cewar Aysher ba.

 

Muje zuwa…..

 

MAMAN HANAN
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: [12/6, 12:43 PM] Zeetty: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

 

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*

*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
—-
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
—-
*CHECK OUR BLOG’S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
—-
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*[email protected]*

©Zeetty

🍀🍀🍀 *SABODA ABOTA* 🍀🍀🍀
Na
Fatimah Muhammad (Ummancy)
*_Hak’ik’a na jinjinama wannan hazik’ar marubuciyar tamu, wanda tayi mana bayani akan yadda mu’amala yake kasancewa tsakanin Mace da Namiji, Matan aure masu zuwa gurin aiki, dan Allah kuyi amfani da darasin da kuka karanta cikin littafin Ummancy, Up up Fatima, sai munjiki a sabon littafin ki Allah k’ara basira._*

PAGE 19-20
A wannan daren Aysher kasa rintsawa tayi, dan haka ta d’auro Allah tafara jero nafila dan neman za6in Allah tsakanin ta da Samir.

Washe gari bayan Samir yagama breakfast kafin yatafi office yake shaidawa mahaifiyar shi maganar Yaseera ‘yar gidan ogan shi, sai dai ya 6oye mata mugayen d’abi’unta da kuma dalilin dayasa mai gidan shi yabashi auren ta.

Sosai taji dad’in maganar dan itama rashin mata kusa da d’an nata yana damunta, dan haka tashiga jero addu’o’i tare da sanyama lamarin Alheri.
Shi dai Samir fuska ya k’ara had’awa, ko amsa addu’ar nata bayayi, ya kai duban sa kan yaranshi yace”Aslam da Afra ku shirya tunda kuna hutu idan nadawo daga office mu wuce kano.”

Ihun murna yaran suka shigayi da tsalle suna fad’in “yeeh! Yau zamuga Momy da Mama.”
Cikin ran Samir tausayin yaran sa ne yasake kamashi, _Aysher hakkina nida yaran nan idan yatashi tambayarki bazakiji dad’i ba._ (Samir ke fad’in haka cikin zuciyarshi).

Mama ce ta katse mishi tunanin shi da cewa”Samir tafiyar dare zakayi da yara k’anana haka?.”

Ya bata amsa yana tafiya bayan yad’auki briefcase d’inshi”a’a Mama yau bani da aiki sosai, dawuri zandawo mutafi kema idan zakije saiki shirya mutafi tare.”

“Ai kuwa zanje, ka saukeni Garin Malam, daga nan saina sanar musu da biki.”

“A’a Mama dan Allah karkiyi wani gayya tunda bana farko bane, uban amaryan da kanshi yace babu wani taron biki (yafad’i hakane saboda bayason azo aga kalar amaryan tashi, abinka da surutun mutanan k’auye ‘yan garinmu lol).”

Mama tace”toh saika dawo dai Allah tsare.”

“Amin.” Ya amsa tare da ficewa daga falon.

“` *******“`
Samir sun shiga cikin garin kano ana kiran sallah magriba, domin saida ya fara tsayawa a hanya ya sauke Mama a garin Malam (wani d’an k’auye ne farkon shiga kano, kafin a k’arasa kura).

Su Aslam yatura cikin gidan Kakan ninsa (gidan su Aysher), shi kuma yayi saurin d’aura alwala domin shiga masallacin dake k’ofar gidan su Aysher, ya samu jam’in sallar magriba da akeyi.

Da gudu yaran suka shiga gidan, suka tarar Aysher da Mama suna Sallah, dan haka neman guri sukayi a falon suka zauna, Mama ce tafara idar wa dan haka kallon su tayi tana murmurshi tace”A’a maigida takobi, saukar yaushe a garin namu?.” Gaisheta Aslam yafarayi kafin yace mata”yanzu mukazo Daddy ne ya kawomu.”
Mama ta mayar da kallonta kan Afra tace”kishiyata ko gaisuwa baby? Sai kumburo baki kikeyi.”

Afra cikin shagwa6a tace”ba kink’i kulani ba, sai Aslam kike kulawa shikenan ai bari Momy ta idar da sallah nasan zata kulani.”

Baki Mama ta rik’e tana fad’in “ohh ni na shigesu, toh kiyi hak’uri kinji kishiya.”

Dariya Aysher taketayi musu yaran sunbata mamaki, rabon da tagansu wata biyu kenan, sun k’ara girma sosai.

“Aslam da Afra drama kenan, kunzo zaku takura Mamana da surutu ko?.” Cewar Aysher

Aslam ne yafara gaisheta kafin Afra, k’arasawa jikin Aysher sukayi suka kwanta, lokaci d’aya suka sauke ajiyar zuciya. Aslam ne yafara magana da cewa”Momy anbamu hutu, Dady yace zamuyi sati d’aya anan kafin yadawo yatafi damu, wai bikin shi saura sati biyu Momy zakizo?, yauwa Momy meye ake nufi da *gida idan babu mace kango ne?.”*

Ajiyar zuciya Aysher tayi kafin tace”Ohh Aslam surutu da tambaya, toh wanne zan fara amsa maka a ciki?, waye yake cewa gida idan babu mace kango ne?.”

Cikin sauri Aslam yace”Daddy ne mana kullum sai yayita fad’an haka, bayan yad’auko hoton mu da akayi mana babba ranar da muka koma kaduna yanata kallo, Momy har kuka Dady yakeyi.”

“Shiii ya isa haka, zan fad’a maka abinda ake nufi da kalmar amman saika k’ara girma, kuma zanzo bikin Dady.”

Mama dai tana gefe ta zuba musu ido, bata sako musu baki ba, cikin zuciyarta fad’i takeyi _yaran Aysher Allah ya sako musu dabara da wayau, Allah dai ya raya._

Wayar Aysher ne yake kuwwar neman a gaji, alamar kira yana shigowa tana dubawa taga Samir ne dan haka tayi hanzarin d’auka.

“Hello.”

“Kizo ina falon Baba.” Abinda ya fad’a kenan baijira cewarta ba ya katse kiran.
[12/6, 1:08 PM] Zeetty: Ta shiga falon da sallama, ya amsa mata kafin tanemi guri ta zauna, ta fara gaisheshi ya amsa babu yabo babu fallasa.
Falon yad’auki shirun wasu ‘yan mintuna shiru bawanda yayi magana, Samir ne yagaji da shirun dan haka yayi gyaran murya kafin yafara magana da cewa”Sulty ina cikin damuwa, nayi dana sanin ka6ar wannan aure na Yaseera yarinyar gaba d’aya bata da hali, muryan ta kamar na Maza lamarin nata sam babu sha’awa, Sulty duk kece kika janyomin *Mafarin lamarin* da’ace angani da mata Oga bazai ta6a yimin tayin auren ‘yar sa ba.”

Aysher ta bud’i baki zatayi magana wayar Samir yafara kuwwa alamar kira yana shigo masa, ya duba number da ake kira yaga bak’uwar Number ce dan haka ya share yak’i d’auka, ba’a hak’ura ba aka sake kira, Aysher tace”kad’auka kagani mana ko waye.”

Dan haka Samir ya danna yad’auka amman yak’i magana. Daga d’aya 6angaren yaji ana magan. “Hello! D-lovely kana jina Amaryace Seera Baby.”

Na shiga uku! Kalmar da Samir ya fad’a kenan tare da katse kiran, yakalli Aysher yace”Sulty itace fa, nikam wannan yarinyar wace irin mayya ce haka, a ina ta samu number na?, danni bani na bata ba da hannu…..” Wani kiran ne yasake shigowa Aysher tace”kad’auka kaji abinda zata ce maka dan mu gama magama dare yanayi (ta fad’a cikin alamun kishi).”

Samir ya d’auka bayan yasa maganar yadda Aysher zata iya jin abinda Yaseera take fad’a.
“Hello! D-lovely wai baka jina ne, toh daman zan fita zuwa club ne shine Dad yace saina tambayi izinin ka, amman fa baisan cewa club zanje ba dan Allah karka fad’a masa, shine Dad d’in yabani Number ka, toh ya kake gani naje?, zan na samo abin ta6awa ne wata k’ila ma nayi sa’ar samun cocein (hodar iblis), dan na kwana biyu bansha ba tunda Dad yasa aka kwashemin kayan maye na a gida, shiyasa nakeso ayi auren nan nasan bazaka takurani ba ko D-lovely?. Wata rana ma zan baka kasha, zan koya maka shiga duniyar sahara kajika a sama-sama…….”

Diff Samir yakatse wayar yadafe kansa da hannu.
Yakalli Aysher hawaye yake fitarwa mai ciwo yace”Sulty i’m finished! Natashi daga aiki nikam, kinji tsinanniya zata koyamin yadda akeshan kayan maye, Sulty shin ko baki yafemin bane?, hak’k’inki yafara tambayata tunkafin aje ko ina, barin je nikam auren nan nafasa saidai sanadiyyar haka a koreni daga aiki.”

Muje zuwa

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: [12/10, 4:46 PM] Zeetty: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

 

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*

 

©Zeetty

_Na sadaukar da wannan page d’in gareku, Maimunat Idris Sani Beli da Fauziyya D. Sulaimain, Ubangiji ya kara basira sosai nake biye daku._

PAGE 22-23
Mik’ewa Samir yayi da niyyar barin d’akin, Aysher tayi saurin shan gabansa tare da cewa”Abban Aslam kakwantar da hankalinka, babu abinda yafi k’arfin ubangiji so u have to calm down ur mind pls dawo kazauna muyi shawara. A sanyaye Samir ya dawo ya zauna akan kujera, ruwa mai sanyi Aysher tafara bashi yasha lokaci d’aya yasauke kofin tare da ajiyar zuciya.

Aysher ta kalleshi cikin sanyin muryarta tace”Abban Aslam ka kwantar da hankalinka, kaucewa wannan aure ba k’aramar matsala bace tunda kariga ka amsa da bakinka banason kazama k’aramin mutum mai magana biyu, tayiwu Allah ya nufeka da wannan auren ne ta dalilin haka Yaseera ta shiryu…….”
A fusace Samir yace”Ni zan shiryar da ita, wannan kangararriyar yarinyar?.”

“Ba nufi na ba kenan Abban Aslam, Allah ne mai shiryar da bayinsa amman tayiwu kaine sanadiyar hakan.” Aysher ta fad’a cikin sanyin murya.

Shiru Samir yayi yakasa cewa komai, nan dai Aysher taci gaba da bashi shawarwari tare da kwantar masa da hankali har saida yasamu nutsuwa. Kafin ya dubi Aysher yace”ke yaushe zakiyi auren toh? Tunda yaukam nak’ara tabbatarwa da cewa bakya sona, bazaki iya komawa aure na ba.”

Dariya Aysher tayi kafin tace”Kacika rigima Abban Aslam yaushe-yaushe nafara karatu? Wata biyu kenan fa amman kanayimin maganar aure, saina gama karatu, bismilla ga abinci.” Tak’arasa fad’a tare da jawo farantin da Mama ta shiryo abinci a ciki. Kad’an Samir yaci abincin, yakalli Aysher cikin tu6une fuska yace”Sulty zantafi dare yayi, gasu Aslam zasuyi one week, sai kutaho tare dasu lokacin bikin zandawo gobe kafin na wuce.”
Murmushi Aysher tayi ganin yadda Samir yake magana kamar dole tace”bakomai sai kazo din, Allah yakaimu lafiya ka kularmin da kanka.”
Mik’ewa Samir yayi tare da k’ara d’aure fuska yace”Ina ruwanki da ni da zakice na kula da kaina, sai da safe.”

Ficewa yayi a gaggauce, baijira cewar Aysher ba.
“Abban Aslam rigima.” Aysher tafad’a tare da mik’ewa bayan ta tattare kayan abincin dake falon.

“`******“`
Kabir yana d’aya daga cikin wad’anda suke zuga Samir kan amincewa da auren Yaseera, dan tsakani da Allah Samir ya yadda da Kabir d’ari bisa d’ari.

Kabir yana lissafe da ranar da iddar Aysher zata cika, dan haka tana cika ya garzaya gidan tunda yaje gidansu Aysher sau uku yana aika yaro ayi mishi sallama da ita, yaron sai ya dawo da amsar cewa”tace koma waye yayi hakuri, ba zata samu damar zuwa ba.” Zuwanshi uku ana bashi wannan amsar dan haka ya hak’ura tare da k’arama Aysher lokaci, cikin zuciyarsa ya d’aura aniyyar cewa bazaije bikin Samir Kaduna ba tunda yasan Aysher dole taje.

Yaseera na hango kwance akan makeken gadonta, takira Johnson a waya suna magana cikin harshen turanci tace”Haba Jonh nace maka karka damu, idan nayi wannan auren zanzo na aureka, nifa kawai inaso naji yadda guy d’in yake ne, dan haka nakeso na aure shi, kota wane hali saina koya masa shan kayan maye.”

Shiru Jonhson yayi kafin kuma daga bisani yace”okay ina jiranki promise? (alk’awari).”

“I promise u my love (Nayi maka alk’awari masoyina).”

Shirye-shiryen biki ya kankama sosai gidan Alh. Auwal mataimaki suke shiri,, Yaseera amarya dakanta take yima kanta shiri tasha wancan, ta matsa wancan, haka dai. Bangaren Samir babuwani shiri dayakeyi tunda uban ango ya hutar dashi kayan lefe, dan haka ya zuba ido shidai kawai sadaki yake jira ranar tayi yaje ya bayar, Mama tanata shiri danma Samir ya dakatar da ita gayyato jama’a.

Alh. Auwal mataimaki da kansa yakira Samir ya shaida masa waliman da abokansa suka shiryama ango da amarya tare da rokon alfarman Samir yataimaka yaje, hakanan Samir ya amsa badan yaso ba.
Ana gobe d’aurin aure Aysher ta sauka a garin zari’a badon ranta yaso zuwa ba, sai dan takura mata da Samir yayi, a gidan wani kawunta ta sauka dake zaune a kaduna anguwar sarki ta sauka ita da yaranta.

A kuma ranar ne za’ayi walimar da Alh. Auwal ya shaidama Samir, dan haka Samir baisamu had’uwa dasu Aysher ba a wannan ranar.
[12/10, 5:06 PM] Samir ya isa wajen da Alh. Auwal ya fad’a masa domin yin walimar bikinsa da abokansa suka shirya ba don ransa yaso ba, tare suka tafi da wani abokin aikinsa mutum d’aya wato Ahmad, amma abinda ya fara gani ne a gurin ya bashi mamaki, waje ya cika da ‘yan mata da samari a takaice dai party aka shirya, kuma sabanin yanda ya zata zaiga manyan mutane sai yaga qawayen Yaseera. Haka dai ya zauna ba dan yana so ba kawai dan ya isa wajen ne, haka akayi party ba yabo ba fallasa, Ansha kayan shaye shaye a wajen, shima Samir haka aka bashi wine ya kwankwada ba tare da yana da masa niyar akwai alocohol (giya) a ciki ba……..

Muje zuwa

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/31/2017, 21:35] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

 

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*
*_We are here to educate, motivate, and entertain you reader’s._*

 

*INA JINKU A ZUCIYATA*
*_Beauty Queen_*
*_Mmn Noor_*
*_My madaya_*

*Alfahari nakeyi daku sosai.*
*_Zauren littattafan hausa_*
*_Duniyar marubuta_*
*_Mace mutum group_*
©Zeetty

PAGE 24-25

Sai wajen 12:00am aka gama dinner wanda suka kirashi da sunan walima, irin bad’alar da sukayi a gurin baki bazai iya fad’arsa ba. Ahmad abokin Samir shima dayake dan duniya ne, yana d’an kora ruwan giyar dan haka yasha abinsa son ransa, haka Ahmad yakama Samir zuwa gurin mota dan lokacin Samir baya cikin haiyacinsa, Amarya taso sutafi tare da Samir amman Johnson dayazo mata biki yahanata zuwa a cewar sa yakama musu hotel suje su kwana dan yima juna bankwana kafin lokacin nasu bikin (subhanallah! Kunji wani lalacewa Allah shirya mana zuri’a).

Aysher bata samu halattar gurin walimar ba kamar yadda Samir ya gaiyaceta, dan batason zuwa taga Samir da wata a matsayin matar da zai aura (kishi), dan haka kawai ta zauna a gidan kawunta inda ta sauka kenan, kiran wayar Samir ta dingayi bayan anyi sallar magriba, dan taji yaushe zaitafi walimar amman shiru ba’a d’auka ba har wajen isha, Aysher duk ta damu a ganinta ko Samir yayi fushi ne dan tak’i zuwa gurin walimar auren sa. Dan haka ta dinga kira akan cewa yayi mata kwatancen gurin walimar amman shiru har zuwa k’arefe 11pm (na dare) tanata kira bai d’auki wayar ba, dan haka Aysher ta hak’ura da kira ranta a 6ace”meyasa Abban Aslam baizaiyi mata uzuri ba (tunanin da Aysher takeyi kenan cikin zuciyarta).”
Rashin sani! Dan kuwa Samir tunda zaishiga masallaci sallah magriba yasa wayar a silent saboda zafinkan maganar zuwa gurin walimar nan ya manta bai cire ba, dan haka duk kiran da Aysher takeyi masa baisani ba, bai kuma d’auko wayar ya duba ba har zuwa lokacin da ya isa gurin walimar ya kora ruwan kwalba (giya) cikin rashin sani.

Kai tsaye gidan Samir, Ahmad ya nufa da shi bai direshi a ko’ina ba saida yakamashi har cikin falo ya shigar dashi kafin ya juya dan zuwa nashi gidan.
_Mama bata gidan, tana gidan wasu ‘yan uwanta dake cikin anguwar kawo, saboda gyare-gyare da Alh. Auwal mataimaki (Uban amarya) yasa aka sakeyima gidan tare da sabon fenti dan zuwan amarya._

Samir a falon ya baje, bacci yayi gaba dashi, bashi yatashi farkawa ba sai wajen asuba, mamaki yadingayi yadda akayi yadawo gida can kuma yafa tunanin abinda yafaru dashi da kuma abinda yayi na k’arshe a gurin party nan, cak tunanin sa ya tsaya sanda ya tuno da cewar ashe fa wine Ahmad yazuba masa a kofi shida Yaseera suka sha a lokaci guda bayan yaciyar da ita cake itama ta ciyar dashi.

Kai Samir yadafe tare da ambatar innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! A fili a hankali yad’aga hannuwansa sama yana fara cewa”astagfirillah ya Allah natuba, Allah karka kamani da laifin da na aikata cikin rashin sani, Allah ya isa tsakanina dake Yaseera bazan ta6a yafe miki ba tun kafin kije gidana burinki yafara cika a kaina, kinfara bani ruwan maye nasha na kwana batare danasan a wani hali nake cikiba, hak’ik’a zaki yabawa aya zak’inta randa kika shigo gidana.” Abinda Samir yake ta fad’a kenan cikin zuciyarsa kafin daga bisani yatashi yaje yad’auro alwala yafara Sallah nafilfili tare da rok’on gafarar ubangiji.

*************
Yaseera kuwa kwana sukayi suna aikata bad’ala ita da Johnson, dakyar tasamu ta lalla6eshi yabarta ta tafi dan k’arfe 11:00am za’a d’aura aurenta da Samir (kunji lalacewa Iyayenta kuma basu binciki ina take ba).

A haka ta lalla6a ta tafi gidan mahaifinta dake Anguwar dosa, lokacin anfara cika ‘yan d’aurin aure, a haka tayi horn mai gadi ya bud’e mata gate ta kutsa ka motar cikin gidan.

Bawanda ya tambayi daga inda tadawo, a haka har lokacin d’aurin aure yayi babu ango sai abokansa da kawun sa (waliyyin Samir), abokansa suka d’inga kiransa a waya shiru wayar a kashe a haka har aka d’aura auren babu ango babu labarinsa.

Samir dai yana sane da lokacin da za’a d’aura masa aure, yayi kuma alk’awarin cewa bazai halatta ba dan haka nema yakashe wayar sa tunda ya dinga kiran wayar Aysher tak’i d’auka dan tayi fushi “wayyo Sulty meyasa bazaki d’auki wayata na fad’a miki matsalata ba, na sha giya na kwana cikin maye.” Samir ya fad’a a fili hawaye yana zubowa daga fuskar sa,gyara zama yayi, yayi kwanciyar sa saboda har yanzu abar bata sakeshi ba (ni kuwa nace rashin sabo).

Sai bayan yayi azahar sannan yashirya lokacin yafarajin dai-dai, dan haka bai saurari gidansu Amarya ba kai tsaye gidan da Aysher ta sauka ya nufa.

Sallama yasa akayi masa da ita, batayi niyyar fitowa ba amman dan batason matar kawunta ta gane akwai matsala tsakanin su yasata tura masa yaransa da sak’on cewar gatanan fitowa. Fitowar Aysher yayi dai-dai da sauke wani nannauyar numfashi sa Samir yayi, kwalliya tayi mai sauk’i dayake Aysher mai kyau ce dan haka tayi kyau d’in ba k’arya, fuska a had’e ta k’araso gurin sa tafara gaidashi ya amsa yana wadata fuskarsa da murmushi tare da cewa”kaina bisa wuya my Sulty, nasan nayi laifi amman ki tsaya kiji dalilina kimin uzuri pls.”
Aysher ta cuno baki tare da cewa”Abban Aslam me zance, tunda daga fara hidimar biki kamanta damu jiya sau nawa ina kiran wayarka shiru ba’adauka ba.”

Samir yace”yi hak’uri Sulty, kaina bisa wuya wayar tawa tun da zanyi sallah magriba nasa a silent na manta.” Daga nan Samir ya kwashe irin aika-aikar da Yaseera tayi masa a gurin party wanda suka kira da sunan walima yak’arasa fad’a yana zubar hawaye yace”Sulty yanzu ace matar da zan aura tunkafin akawota gida na tafara d’uramin kayan maye, gaba-gaba bansan abinda zata aikatamin ba, nikam in sha Allahu tunda sun d’aura ko ruwan gidanta bazan yadda nasha ba Allah ya isa bazan yafe ba.”
Dariyane yakama Aysher ganin yadda Samir ya dage yana fad’a iyaka gaskiyar sa, amman ta kanne ta dinga kwantar masa da hankali har ya sauko ya d’aukesu a motar sa dan zuwa gidan danginsa dake kawo inda anan ake hidimar bikin nasa.

Hango Yaseera nayi tana waya tare da cewar Johnson ya shiryo mata k’wayoyi masu k’arfi da hodar iblis yasa a cikin jaka maikyau zata aiko a kar6an mata dan dasu za’a kaita gidan miji sune rayuwarta.

Misalin k’arfe 5:00pm aka kai amarya cikin kwates na ma’aikatar NNPC (nifanare), ‘yan kai amarya basu jima da zuwa ba sukayima amarya sallama dan komawa gidajensu bisaga umarnin uban amarya.
Yaseera bayan fitar yan rakiyarta, ta shiga neman wayar angon nata dan yau kwata-kwata bata sameshi ba wayar sa a kashe, so take ta tambayeshi yadda yaji sanda ya shiga wancan duniyar (maye) amman taji shiru har zuwa lokacin da aka kawota gidan, dan haka d’akinta ta shiga ta d’auko akwatin da Johnson yabawa k’awarta lisa Baby ta kawo mata, ta d’auko cocien (hodar iblis) ta fara zuk’a dan a cewar ta lamarin na yau babbane, zataso taji yadda guy d’in nan yake dan he is extremely hand son, dole sai ta had’a da kayan zuwa duniyar sama, tuni ta fita haiyacin ta ta fara buga kanta da gefen gad’on da ta ke kwance dan ta kwana biyu bata zuk’a ba…………

_Shin ya rayuwar Samir zata kasance da ‘yar maye. Kuniyoni._

 

Muje zuwa

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/31/2017, 21:35] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

 

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*

__________

________________
“`WE ARE HERE TO EDUCATE, MOTIVATE, AND ENTERTAIN YOU READER’S.“`
_________

_________________
📚 zaku iya samun littattafam mu a Facebook 👇🏼
Fb.me/
ZAMANIWRITERSASSOCIATION

📩 zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏼
[email protected]

©Zeetty

PAGE 26-27
Samir bashi ya shigo gidan ba sai wajen k’arfe 9:00pm, da kyar Aysher ta lalla6eshi yataho shi kad’ai dan yace dole sai da ita zasu taho, tayi masa alk’awarin zuwa gobe in sha Allah sai su taho da su Aslam gaba d’aya.
Cikin sanyin murya yayi sallama bai damu a amsa masa ba dan yasan mamallakiyar gidan a yanzu balallai bane tasan mahimmancin sa, d’ak’in sa na da ya nufa wanda ya mayar da gadon Aysher d’akin, dan koda yasa aka loda kayan d’akin Aysher dan a kaimata kano bai yadda ya had’a da gadon ba, gad’onsa ya saka mata cikin kayan saboda daman yafi tsada kuma duk shiya zuba musu lokacin da zasu dawo kaduna.

Gefen makekiyar gad’on ya dafe kansa tare da fad’in “Hasbunallahu wani’imal wakil! Allah ka kawomin canji cikin rayuwata, Allah ka tabbatar min da abinda yake alheri a rayuwata.” Yana gama wannan addu’ar ya shige band’aki dan watsa ruwa kotakan amaryar sa baibi ba.

Da asubah ya farka yaje ya d’auro alwala dan zuwa masallaci, yafito falo zai fice sai kuma yafasa ya sakai d’akin Aysher nada, wanda yake d’akin Yaseera a yanzu, ya sa hannu ya bud’e cikin sa’a k’ofar a bud’e take, hango amaryar tasa yayi baje a kan gado tana shak’ar bacci gefenta kayan mayenta ne datasha jiya ta barsu babbaje a gurin, sallati Samir yayi cikin zuciyarta kafin ya k’arasa kusa da ita, ko kayan bacci bata saka ba tun kayan da aka kawota dasu jiya je, bubbugata yafarayi tare da fad’in”kitashi lokacin sallah yayi.” Inaa sake gyara kwanciyarta tayi, Samir yakasa hak’uri cigaba yayi da bubbugata dakyar ta tashi, cikin alamun har yanzu tana cikin maye tace”No ka barni ba kullum nake sallah ba, yau hutawa zanyi sai gobe, bacci nakeji kazo mukwanta kaima ka hak’ura.” Ta k’arasa fad’a tana yunk’urin jawoshi jikinta da sauri Samir ya bar d’akin dan lamarin Amaryar tasa gaba yakeyi bawai baya ba.

******** ********

Wajen k’arfe 10:00am (na safe) Samir yashirya ya fito tsaf, haryakai bak’in k’ofar fita saiyayi wani tunani, juyowa yayi da baya ya koma d’akin Yaseera haryanzu tana kwance amman idanunta biyu, da sauri ta tashi tazauna tana fad’in “D-lovely good morning, shine jiya ka barni ni kad’ai baka dawo da wuri ba, kamanta kazo ka kwashi garar amaryar da aka kawo maka cos you don’t care of me, ko baka sona ne?, shine kawai nasha abubuwana nayi mankas saboda namanta da damuwar da kasani ciki jiya, for good sake nasan ba haka akeyima amare ba, d’okinsu akeyi.” Samir dai kasa tanka mata yayi, mamaki da al’ajabi duk ya cikashi, dan bai zaci lamarin Yaseera kai haka ba, girgiza kai yayi kawai yasa kai ya fice dan tunawa da alk’awarin sa da Aysher kuma yau zata koma kano saboda karatu.

Yad’auko Aysher da yaransa ya kawosu gidan, kar6a mai kyau Yaseera tayi musu tare da ajiye musu kayan biki dangin su dubulan da alkaki drinks da cake, sosai ta karb’esu hannu bibbiyu har Aysher na mamaki kodai Samir sharri yakeyi mata dan baya sonta, amman kuma ai Abban Aslam bazai mata k’arya ba, haka dai Aysher tayita wad’annan tunanin har lokacin tafiyarta tayi, tayima Yaseera sallama Samir yatafi rakata tasha tahau mota, dan tayi sallama da gidan kawunta. Dakyar yaran suka rabu da ita wato Aslam da Afnan shi kansa Samir d’in kawai k’arfin hali yayi dan yanzu yak’ara tabbatarwa da cewa yayi rashin Sulty mace tagari.

********* *********

Haka al’amarin zaman nasu ya kasan ce tsakanin Samir da Yaseera, bawani zaman lafiya, Yaseera bata iya girki ba, kullum Samir shikenan wajen yawo a gida jen sai da abinci, baya dawowa gida sai bayan k’arfe 9:00pm, dan haka Yaseera har yanzu takasa samun kan D-lovely d’inta, shawara tayi dan haka takira k’awarta saboda masifar sha’awar da yake damun ta, shawara k’awarta ta bata, sosai Yaseera tayi na’am da wad’annan shawaran.
Gidan su takira a waya cewar a turo mata ‘yar aikin gidan su zasu tayata aikin abinci, batare da 6ata lokaci ba aka turo mata su, ta basu odar girkama Samir abincin gargajiya tuwon shinkafa miyar agushi, wanda yaji naman tantak’washi da tsokar nama, gefe guda sun had’a masa lafiyayyen zo6o wanda aka sanya mashi cucumber, cikin mintuna kad’an suka kammala aka shirta a dining table, nan da nan ta sallamesu, fitar su ba wuya Yaseera ta d’auko wata k’waya mai bala’in k’arfi guda d’aya ta nik’a yayi laushi ta watsa cikin kofin da zo6on yake ciki, ko ita bata shan wannan k’wayar saita rabashi 4, amman yanzu ta jefama Samir guda 1, akan cewa ya shanye.

 

Burin Yaseera yana cika?

Mezai faru idan Samir ya kora zo6on nan?

Ku kasance dani

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/31/2017, 21:35] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*

__________

________________
“`WE ARE HERE TO EDUCATE, MOTIVATE, AND ENTERTAIN YOU READER’S.“`
_________

_________________
📚 zaku iya samun littattafam mu a Facebook 👇🏼
Fb.me/
ZAMANIWRITERSASSOCIATION

📩 zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏼
[email protected]

©Zeetty

PAGE 28-29
Samir yau yadawo gida da wuri, kuma a gajiye dan haka kai tsaye ya fara wucewa side d’inshi, ruwa yafara watsama jikinsa kafin ya fito falo ya zauna, kamar yadda yakeyi kullum dan kallon labarai.
Su Aslam suna d’akinsu sunyi bacci tare da mai kula da su da Samir ya d’auko, ba su da wata matsala da Yaseera, saidai bata basu kulawa amman tana jansu a jiki bata musu mugunta.

Cikin salon rausayar ta Yaseera ta k’araso gurinshi, tana karairaya da yauk’i, kan cinyar shi ta zauna tare da rataye hannuwanta a wuyansa, cikin muryan shagwa6a tafara magana da cewa”D-lovely kayafemin duk abinda nakeyi maka, nasan cewa auren nan anyimaka ne bawai dan kana sona ba, amman meyasa bazaka iya taimakawa mahaifina ba akan abinda yanema, wato shiryuwata duk da nasan Allah ke shiryar da bawansa, amman wallahi D-lovely nima inaso nadaina 6atamin ran da kakeyi da daina kulawa dani shine yasani nake shan kayan maye a gidan ka, saboda na manta da wasu abubuwan, amman dan Allah D-lovely kataimaki rayuwata gurin ganin na shiryu saboda na zamowa yarana uwa tagari.” Tak’arasa fad’a tana sheshshek’ar kuka.

Jikin Samir yayi sanyi sosai, gashi baya son yaji mace tana kuka dan haka yace”is Okay ya wuce, ki nutsu kigyara rayuwarki da sauran lokacin da yarage miki tashi ki je ki kwanta.”

Cikin sharen hawaye Yaseera tace”In sha Allah D-lovely nagode, but yau inason na baka mamaki dan haka nasa an shirya maka girki, masu aikin gidan mu da kansu sukazo nasa sukayi maka abincin gargajiya so pls zo muje kaci, nima very soon zan fara girka maka da kaina, but for the first time a tarihin auren mu yau zomuje kaci girkin gidan ka.”

Mamakine yakama Samir, bayason musanta mata tunda sosai shirin take nema, kuma gashi yunwar yakeji daman tunaninsa yasha tea ya kwanta, amman bari yaje yaci abincin da Yaseera tasa aka shirya masa…….
“Come on! D-lovely taso muje pls, don’t say no.” Yaseera ta katseshi da fad’in haka tare da kamo hanun sa, haka yamik’e yana biye da ita har dining area.
Zaman yayi ta fara zuba masa abincin tuwo da miya, sosai Samir yaji dad’in ganin abincin saboda yakwana biyu baici ba, dan haka ya zage ya narka, saida yaseera ta lura yaci abincin sosai kafin ta zuba masa had’in zo6o, nan ma haka ya dinga sha kamar ba gobe dan yanason zo6o sosai cikin lemukan gargajiya, ya na cikin shan kofin zo6o na uku da Yaseera taketa zuba masa yana kowara, nan labari ya canja gaba d’aya yajisa cikin wata duniyar, yafita daga haiyacinsa ga6a d’aya, Yaseera ya hango ta juye masa zuwa kammanin Aysher, subhanallah da sauri ya jawota kamar mayunwacin zaki, yafara aika mata da sak’on kiss yake aika mata dashi ta ko ina, dayake Yaseera a buk’ace take kuma gata gwana ce sosai, nan ta k’ara rikita Samir da nata salon soyayyar, gaba d’aya suka afka cikin duniyar masoya da kyar Samir ya yunk’ura ya d’auketa sai Bed room d’in sa.
_Asuba tagari._

Haka Yaseera taci gaba da amfani da k’wayar maye tana afkawa Samir, tana kuma samun damar yana biya mata buk’ata yadda takeso, batare da yana cikin hayyacin sa ba takashe wayoyinsa, yaran sa ita ke kaisu School ta d’auko su, ko kuma ta tura mai aiki ta taho da su Napep, abokan aikin sa har gida sukazo nemansa, tace musu yatafi k’auyensu kuma babu network, kowa mamakin hakan yakeyi saboda rashin fad’arsa a gurin aiki abashi izini, gashi Samir yana bin doka, tafe dai tafe dai har aka kwashe sati guda ciff Yaseera ta mayar da Samir d’an maye bashi da aiki saidai ta bulbula masa k’waya cikin lemo yasha daga nan sai bacci, sosai Yaseera take sashi a gaba tana masa dariya gami da cewa”kaima kaji yadda mukeji shege, har kana cewa ka tsani halaiyata gashi a sannu nasaka ciki, kullum cikin maye.”
Samir baya iya budar baki yace mata uffan, saboda k’wayar tayi masa k’arfi gashi kullum take bashi guda ya shanye, wanda ita kwatarsa take sha.

************

Gefe guda Kabir yafara samun kan Aysher, dan yanzu idan yaje gidan tana fitowa idan ya aika suyi zance, har labarin yaranta tabashi, dan bai nuna mata yasan mijinta ba, ballantana yaran da suka haifa.

A hakan dai harya samu yashawo kan Aysher ta amince ya kawo sadakin sa, bisa taimakon malamin sa dayayi masa aiki akan haka, kafin akawo sadakin Aysher tayita kiran wayar Samir tasanar masa amman wayar sa akashe, dan haka bata wani damu ba dan yanzu zuciyarta soyayyar kabir ne cike a cikinta.

Muje zuwa

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/31/2017, 21:35] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*
________
______________
“`WE ARE HERE TO EDUCATE, MOTIVATE,AND ENTERTAIN OUR READER’S.“`

_________
______________

©Zeetty
📚zaku iya samun littattafan mu a face book 👇🏻
Fb.me/
ZAMANIWRITERSASSOCIATION

📩zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏻
[email protected]

*MY BEAUTY QUEEN HAKIKA INA ALFAHARI DAKE, ALLAH BAR ZUMUNCI.*

PAGE 30-31
Samir yana cikin wannan hali, kwatsam Mama (mahaifiyar sa) ta sauka a gidan saboda jin shirun yayi yawa kuma gashi bata samunshi a waya, bata kuma da number Yaseera. Sanda mama tazo gidan bata samu Yaseera ba ta tafi gurin Johnson suyi sallama zai koma America, kuma tana sauri tabar k’ofar d’akin a bud’e, sallama Mama ta dingayi taji shiru ba’a amsa mata ba gashi yaran duk sun tafi Makaranta, Baba mai aiki ta tafi tahowa dasu, cikin sa’a Mama ta danna kanta d’akin Samir na da wanda yazama na Yaseera a yanzu, sallama tadingayi taji shiru, hango Samir tayi kwance akan gado yanata shek’a bacci, da sauri Mama tak’arasa tana bubbuga sa tare da tambayarsa ko lafiya? Sam Samir baisan tanayi ba, jijjigashi Mama takeyi shiru gashi dai a zahiri yana numfashi amman babu abinda yake iya motsawa a jikin sa. Ihu mai k’arfi Mama ta saki, kafin tafice daga d’akin da sauri wajen kwates d’in ta nufa gidan dake kusa da na Samir taje tafara bubbuga k’ofar da k’arfi, kana kallonta kasan cewar a rikice take, Emanuel yak’araso ya bud’e k’ofar cikin gur6atacciyar hausar shi yafara tambaya”Mama lafiya kuwa (dayake yasanta d’an zaman da tayi a gidan Samir din).”

Kuka Mama tafarayi tana nuna masa k’ofar gidan Samir gami da cewa”Samir gashi can bashi da lafiya baisan inda kansa yake ba, mara bansa da gawa numfashi.” Duk da cewar Emanuel bai fahimci abinda take nufi duka ba, amman yad’an gane wasu dan haka yace”Jesus, what is wrong with him?, kwana biyu baya zuwa office, i call him but his phone is switch off, na tambayi Madam tace min he is travel, ashe yadawo babu lafiya, muje Mama barin fito da mota, just now am back, na zo d’aukar wasu taddune daga office.”

Ita dai Mama dayake ba fahimtar abinda yake cewa takeyi ba, dan gaba d’aya a rikice take, ko ina a jikinta rawa yakeyi, da sauri ta koma gidan Samir d’in ta shiga d’akin, tayi yunk’urin d’aukar sa amman inaa, bazata iya ba dan haka ta jira har Emanuel ya shigo yana fad’in”excuse!” Mama da sauri tafito ta nuna masa d’akin da Samir yake kwance, kasan cewar Emanuel k’atoton inyamuri maji k’arfi dan haka ya cicci6i Samir yasashi a mota.

*********
Suna isa asibitin dake cikin kwates din, kai tsaye aka wuce da Samir A & E (Accident and emergency) likitoci suka taru akansa dan gano abinda yake damunsa, jikinsu yayi sanyi matuk’a, sanda suka gano musabbabin matsalar tashi, dan haka Dr. Hussain yafito yana sharce gumin dake fuskar sa, ya k’araso ya samu su Emanuel wanda yakasa komawa Office, bayan yakira ya shaida musu abinda ke faruwa. Dr. Hussain yace”kubiyoni zuwa office, pls inason ganin wani na kusa dashi.”

Da sauri Mama da Ema suka k’arasa office d’in kowa zuciyarsa cike da son jin abinda yake damun Samir.

Dubansu Likita yayi kafin ya sauke idonsa akan Mama ya k’ura mata ido, kafin yace”daga gani kece Mahaifiyar wannan mara lafiyan, shin zan iya fad’ar matsalarsa a gaban wannan ko kuma yabamu guri?”.

“Zaka iya likita, da badan shiba, bansan yazanyi na kawoshi asibiti ba kafad’a kawai ba matsala.” Cewar Mama.

Likita yace”wato Mama a zahirin gaskiya binciken da mukayi mungano cewar Samir yasha magungunar maye masu matuk’ar k’arfi, wanda sune sanadiyyar jefashi cikin wannan halin da yake ciki, wanda bamu da tabbas d’in cewar k’wakwalwarsa tanada cikakken lafiya a yanzu, har sai ya farfad’o k’wayar ta sakeshi, wanda zaikai nan da wasu kwanaki, sai kuyita addu’a kar ya samu ta6in hankali, wanda warkewarsa zaiyi wahala sai wani ikon Allah.”
Kuka Mama tafara gami da salati tana fad’in”wallahi likita d’ana ba mashayi bane sai dai idan wannan matar tashi ce ta sashi a wannan muguwar hanyar, dan tun farko abinda yasa ya guji aurenta kenan, ‘yar maye ce sosai, ya Allah kabama Samir lafiya.” Sosai Mama take kuka abin tausayi.

Emanuel wanda bai gama fahimtar bayanin likita gaba d’aya ba, dan da hausa aka yima Mama bayani, sai da yasake tambayar likita cikin harshen turanci yayi masa bayani sosai, nan shima ya shiga cikin tashin hankali tare da fatan Allah yabashi lafiya. A asibitin Ema yabar Mama ya koma office tare da alk’awarin zai fad’awa Yaseera dan suzo asibitin kar hankalinsu yatashi.

A6angaren Yaseera kuwa, tariga su Baba dawowa gida dan haka ta shigo falon da ‘yar guntuwar wak’ar ta, bata damu da ganin gidan a bud’e ba, kasancewar basu da wani matsalar 6arayi a kwates d’in, kai tsaye d’akin ta, ta nufa inda Samir yake a kwance wayam tagani sanda takai kallonta kan gadon ta, taga babu mijinta kwance a gurin. A rud’e ta fice daga falon, sukayi kici6is da Anatu (matar Emanuel) zata shigo gidanta, da sauri Ana ta tareta da cewa”thank God! Kadawo, Ema yanata kiran wayana, yana tambayana ko kadawo?, nazo three times kenan.”

“Ke Anatu kin cikamin kunne, fad’amin meye yakawoki gurina dan inada matsalar da tafi zuwanki yanzu.” Yaseera yafad’a cikin muryar fad’a.

“Sorry Madam, Ema yace mijinka ba lafiya, yana cikin Hospital d’in asibitin nan so yace ya fad’a maka, kar hankalinka ya tashi.” Ana tana gama fad’in haka tabar k’ofar falon Yaseera.

A lokacin kuma Baba tadawo daga d’auko su Aslam daga school.

Kai Yaseera ta dafe tare da fad’in”Oh my God! Waye yazo ya ga D-lovely cikin wannan halin har yakaishi asibiti? Kodai Emanuel ne?”. Dan haka a fili Yaseera tace”sai naci kutmar uban Emanuel, zai fad’amin dalilinsa na shigomin gida bama nan.”

Baba kuwa tanaji Yaseera ta ambaci hakan ta fara fad’in”sai hak’uri Uwar d’akina, labarin dana samu a kwates d’innan shine, shida Anatu yara hud’u suka haifa yanzu haka, kuma har yanzu ba suyi aure ba, wai sai nan da shekara guda mai zuwa, dan haka kinga irin wad’an nan k’abilun balallai bane susan darajar aure, yara 4 fa Uwar d’akina, zaman zina sukeyi wanda Allah ya tsinewa mai….”

“Ke rufemin baki, tambayarki nayi? Duk kin cikani da surutu to dan uban babanki banason ji ba kisan tashin hankalin da nake ciki ba, ki wuce ki cire musu uniform mu tafi asibiti D-lovely ba lafiya.”

Cikin sauri Baba ta ja hannun su Aslam zuwa d’akinsu dan canja musu kaya, bataji haushin zagin da Yaseera tayi mata ba dan kuwa tasaba da hakan, ballan tana yau ya hadun mata da ciwon miji.

A hanyarsu ta zuwa asibiti Yaseera takira wayar Mahaifinta cikin Kuka take sanar masa Samir bashi da lafiya, yana asibiti wasu ne suka kawoshi gida yau da asuba cikin yanayi na maye………….

 

Muje zuwa

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[12/31/2017, 21:37] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*
________
______________
“`WE ARE HERE TO EDUCATE, MOTIVATE,AND ENTERTAIN OUR READER’S.“`

_________
______________

©Zeetty
📚zaku iya samun littattafan mu a face book 👇🏻
Fb.me/
ZAMANIWRITERSASSOCIATION

📩zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏻
[email protected]

PAGE 32-33
Kuka sosai Yaseera taci gaba dayi a cikin motar, tana driving tana face hanci, Baba mai aiki fad’i takeyi sai hak’uri Uwar d’akina Allah yasakama uban gida na.

Cikin wannan halin suka k’atasa asibitin, idan kaga Yaseera saika rantse da Allah bata da wani masaniyya game da halin da Samir ya tsinci kansa a ciki, da tambaya suka k’arasa d’akin da aka kwantar da Samir din.

Da gudu Yaseera tak’arasa gadon da yake kwance kamar gawa, ta kwanta akan kirjinsa tana kuka sosai mai had’e sheshshek’a tare da fad’in”Allah yasaka maka D-lovely, duk mugun daya aikata maka hakan Allah ya baiyanashi, bazamu ta6a yafe masa ba.”

Cikin wannan halin Mahaifinta yazo ya risketa, tare da wasu ma’aikatan NNPC gumi ne ya fara tsatstsafowa daga fuskar Alh. Auwal Mataimaki yasa hankici yana sharewa, kallo d’aya yayima Samir yaji tausayin shi yakamasa, tabbas an zalunceshi, shi ba mai shaye-shaye ba an mayar da shi d’an maye k’arfi da yaji, dan sunje ofishin likita yayi musu bayanin duk abinda yake faruwa akan Samir d’in.

Goge k’wallar da ya fara zubowa daga idanuwansa yayi na tsabar tausayama Samir, kafin yafara magana da cewa”Allah yasaka maka Samir Yaron kirki, yanzu daga nan ofishin ‘yan sanda zan wuce, zamu kai report dan a fara bincike akan wad’anda suka aikata masa wannan mugun aikin, tabbas ba zamu yafe musu ba ko sassauta musu akan hukuncin da za’ayi musu ba, ko da ace munada kusanci mai k’arfi tsakaninmu…..

 

 

Kululululu cikin Yaseera ya kad’a, ta sake fashewa da wani matsanancin kuka wannan na tausayama kanta ne idan asirinta ya tonu.

_Ayi hakuri da wannan._

Muje zuwa

MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[1/2, 15:53] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐

*MAFARIN LAMARIN*

DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER’S ASSOCIATION (Z.W.A)*
________
______________
“`WE ARE HERE TO EDUCATE, MOTIVATE,AND ENTERTAIN OUR READER’S.“`

_________
______________

©Zeetty
📚zaku iya samun littattafan mu a face book 👇🏻
Fb.me/
ZAMANIWRITERSASSOCIATION

📩zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏻
[email protected]

*Godiya ga duk ‘yan k’ungiyata Zamani writer’s association.*

*_Zauren littattafan Hausa group._*
*_Duniyar Marubuta group._*
*_Hausa novels only group._*
*_Indabawa online writers._*
*_Musan juna group._*
*_Hussain Atk._*

✈✈✈✈✈
*JIRGIN SO*
✈✈✈✈✈
*Labarine wanda yake zuwan muku tare da King Boy Isah, marubucin Mijin Aljana, Aljanar Fatima, kukasance tare damu dan hawa Jirginso.*

*KUNA RAINA*
My Beauty Queen
Ayush Iilyasu
Mmn Noor
Mmn twins
Mmn Namma
Shaxee
Nasmat
Kamala
Zaid
Rahamat Rufa’i Nalele (Samarin bana)
Queen Hausy (K’urmin daji)
Namcy (Zainab)
Da duk wanda ban fada ba kuna da yawa ana tare.
PAGE 34-35
Kabir yanacan anata shirye-shiryen bikinsa da Aysher, saboda amincewa dayayi zataci gaba da karatu a gidansa, ita dai Aysher hankalinta ba’a kwance yake ba saboda rashin samun wayar Samir da batayi, kullum idan takira a kashe.

Hakan ne yasa hankalinta yatashi, takasa hak’uri dan haka ta tambayi Baba akan cewar yabarta taje tadubo su AFNaN ko a ranar ta dawo, Baba yace saiyayi shawara.

Samir kwanansa uku kwance a gadon Asibiti, Mama ke kwana a gurinsa dan fir Yaseera tak’i yadda da kwanan, a cewarta wai zaman asibiti firgitata yakeyi dan haka Mama tace taje bakomai ita zata dinga kwana dashi.

Ranar kwana na 4 da Yamma lokacin Aysher tazo sun gaisa da Mama gami da jimamin abinda yafaru, Samir yana kwance kamar gawa sai numfashin dake fita jifa-jifa, hakan ne zai tabbatar ma da maikaratu cewa yana raye.

Alh. Auwal yashigo d’akin tare da Yaseera kamar yadda yakeyi kullum da yamma saiya lek’o asibitin, bayan sun gaisa Mama tare da tambayarta yadda mai jiki ya kwana, Mama tace”Jiki da sauki Alhamdulillah.”

Wani kallon-kallo akeyi tsakanin Aysher da Yaseera,saboda Aysher tana kallon idanun Yaseera tagano cewar bata da gaskiya, amman kasan cewar Aysher macece wayayya dan haka tadanne duk abinda yake zuciyarta, ita tafara gaishe da Yaseera, Yaseera ta amsa tana wani irin yauk’i.

Alh. Auwal ya kalli Mama yace”Haj. Karki samu damuwa likita yace zai iya farkawa daga kowane lokaci, kuma nasaka a cigaba da binciko mana wad’anda suka aikata wannan abun, in sha Allahu asirinsu yana gab da tobuwa su kansu ‘yan sandan yanzu jiran farkawar Samir din suke dan akwai wasu tambayoyi da zasuyi masa.”

Hawaye Yaseera tafara sharewa, Mama ta kalleta tace” ‘yar nan kukan yayi yawa, tunda abin nan yafaru kusan kullum cikin kuka kikeyi, gashi daga gani bake daya bace, kuma ba’ason mace mai juna biyu da sanya damuwa a rai.”

Aysher ce mai goge mata hawaye tare da k’ara bata hakuri.

Suna cikin haka k’afar Samir yafara motsawa, a hankali gaba d’ayansu suka maida kallonsu kanshi, kafin daga bisani ya bude idanunsa a hankali bakinsa d’auke da salati.”

Nan take d’akin yadauki kabbara, kowa fuskarshi dauke da fara’a sa6anin na Yaseera da ta zazzaro ido kamar an tarke kare a kitchen, murd’awa cikinta yayi yayi hanyar band’aki da gudu.

Da sauri Mama da Aysher suka k’arasa gurin Samir suna tambayarsa jikinsa, a hankali yabud’i bakinsa yace”Mama lafiya naganmu anan, meke faruwa dani, ina Yaseera?” Wad’annan sune tagwayen tambayoyin da Samir yayima Mahaifiyarsa.

Alh. Auwal dake gefe a tsaye sai lokacin yak’araso jikin gadon ya dafa kan Samir kafin yace”Samir matarka tana nan lafiya, mungodema Allah daka farka cikin hankalinka, saboda haka yi gaggawar sanar damu wad’anda suka aikata maka wannan mugun abin, dan a d’auki mataki akansu.”

Shiru Samir yayi kafin daga bisani yace”a fitar da hukuma daga wannan maganar, saboda rufuwar asirinmu dan kuwa ba kowa bane ya aikatamin haka face Yaseera matar da nake aure…..”

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, mekake cewa Samir?” Tambayar da Alh. Auwal yayima Samir kenan.

Ita kuwa Aysher batayi mamaki ba domin daga ganin yanayin Yaseera tasan cewa ita keda alhakin hakan.

Mama kuwa salati tadingayi tana fad’in” ‘yar nan meye Samir yayi miki kikeson ganin bayanshi, tare da yi masa wannan mummunar aika-aikar?”.

Kunyace ta rufe Alh. Auwal dan haka yafara k’walama Yaseera kira data kasa fitowa daga band’aki yana cewa”ina kike dan ubanki fito, shegiya munafuka algunguma.”. Cewar Alh. Auwal

Shiru Yaseera tayi kamar bataji abinda yace ba ta zauna cikin band’akin.

Ku biyoni cikin littafi na biyu.
Dan jin yadda Yaseera zata kasance idan asirinta ya toni.
Ya labarin Kabir, shin auren yana yiwuwa kuwa?.

MAMAN HANAN ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button