Labarai

Matar Aure Tayi Garkuwa da Mijinta ta Karbi Kudin Fansa

Matar Aure Tayi Garkuwa da Mijinta ta Karbi Kudin Fansa

Rundunar ‘yan sanda reshen Jihar Akwa Ibom da ke kudancin Najeriya ta kama mace mai shekara 40 da zargin yin garkuwa da mijinta tare da karɓar kuɗin fansa naira miliyan biyu.

A ranar Juma’a ne ‘yan sandan suka gabatar da Joy Emmanuel Sunday ga manema labarai tare da wasu mutum 29 a birnin Uyo bisa zargin aikata laifuka daban-daban.

 

Joy ta ce dole ce ta sa ta yi garkuwa da mijin nata mai suna Emmanuel Sampson Ebong saboda ba ya biya mata buƙatun aure sannan kuma ya gudu ya bar ta da yara.

Ta ƙara da cewa lamarin ya sa ta kama ƙananan sana’o’i don ta ciyar da yaran yayin da shi kuma ya je ya auri wata matar daban, abin da ya sa ta shirya garkuwa da shi ke nan don ta samu kuɗin ciyar da su.

Sai dai ta ce: “Wanda ya karɓi kuɗin fansar bai ba ni kasona ba kuma ko kuɗin ban gani ba.”

Mijin nata da aka ceto ya ce an sace shi ne a ranar 21 ga watan Yuli, 2022 a gidansa.

 

Kuci gaba da kasancewa da wannan shafin mungode da ziyartarku.

Kuma kada kumanta ku’aje mana ra’ayinku a comments box dake kasa mungode.

©Funeyy.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button