Matsalolin da Budurwa Keshiga Bayan Bayarda da Kanta ga Saurayi
Matsalolin da Budurwa Keshiga Bayan Bayarda da Kanta ga Saurayi
1• Idan budurwa taba da kanta ga saurayi yayi zina da ita, to daga lokacin zedaina yadda da ita, ko wayarta yaji tayi ƙara saiya zargi wani abu, Kuma koda ƙaninta ya ganta sai ya zargeta, balle kuma ya ganta da wani saurayin daban.
2• Samari da yawa suna guduwa daga lokacin da suka aikata zina da ‘ƴan matan da suke so.
3• Duk saurayin da yayi zina da wata wacce yakeso, to daga ranar zai fara yiwa iyayenta kallon sakararru.
4• Maza ne sukafi yawan fallasa sunan mata idan sunyi zina dasu, basa iya rufe aisirinsu, saɓanin su mata basa iya bayyana wannan sirrin, koda acikin ƙawayensu ne.
5• Da yawan samari idan sukayi zina da ‘ƴan matansu, sukan bawa abokansu labarin abinda yafu, har wanima ya kan tura wani abokin nasa wai shima yaje, ya kwashi rabonsa.
6• Namiji yana iya zina da mata ba adadi, kuma daga baya ya auri macen da yakeso, saɓanin idan mace tayi zina koda sau ɗaya ne, ta rasa wannan darajar tata, kuma bazata iya dawo da itaba duk yadda zatayi.
7• Idan mace ta taɓa yin zina koda sau ɗaya ne, kuma tazo tayi aure daga baya, to idan mijin data aura ba mai addini bane, baisan ƙaddara ba, da ƙarfin imani ba, to bazai taɓa daina zarginta ba, saida kawai ya ɓoye mata.
Dan ALLAH ‘ƴan mata kudaina yarda samari suna ɓata muku rayuwa.
Dan ALLAH ku taimaka ku tsare darajarku da mutuncinku.
Zina bala’ice….Masiba ce a cikin al’umma, sanna tana jawo a kasa samun yara masu tarbiyya.
ALLAH ka tsare mana imaninmu, ka bamu ikon kaura cewa zina.
ALLAH ka horewa kowa yayi aure kuma ka azurtamu da abokan zama nagari Ameen.
*SHAWARA*
Dan Allah duk macen da ta karanta wannan posting din namu ta taimaka tayi forwarding dishi ga yan uwa mata masu aure..
Kuci gaba da kasancewa da wannan shafin mungode da ziyartarku.
Kuma kada kumanta ku’aje mana ra’ayinku a comments box dake kasa mungode.