Gyaran Jiki

Fa’idar ajiye zuma a gida, cututtuka 5 da take magani 9

Fa’idar ajiye zuma a gida, cututtuka 5 da take magani 9

 

Zuma dai wata abace wadda banda tsantsar zakin da Allah ya zuba mata na dandano a baki tana da amfani a fanni lafiyar jiki, inda take maganin wadansudangin cututtuka a jikin dan adam.

Idan har baka taba lura da fa’idar zuma ba akwai bukatar ka tanadi kwalba guda ta zuma domin jarabawa. Ga jerin wasu cututtuka guda biyar da zumar ke magani:

 

1. Zuma na rage yawan yin tari Zuma na da matukar amfani musamman a lokacin sanyi inda take maganin tari.

A cewar kungiyar likitocin yara kanana ta duniya bisa la’akari da wani bincike da ta gudanar zuma ta kasance magani tari ga yara sama da 100.

Haka kuma iyayen yara sun tabbatar da wannan zance inda suka ce zuma ta dara sauran magungunan da ake amfani da su domin maganin tarin.

2. Zuma na warkar da rauni Wannan magana nasan za ta ba wasu daga cikinmu mamaki kwarai da gaske.

Tun shekaru aru-aru da suka wuce a kasar Masar mutane sun kasance suna shafa zuma a saman rauni idan suka ji ciwo.

 

Har ila yau ana amfani da wannan hanyar domin warkar da rauni a jiki.

3. Zuma tana kara kaifin basira Yana da matukar muhimmanci mu lura da abinci da muke ci ya zamana wanda zai kara mana kaifin basira ne.

Zuma tana karawa mutum kaifin basira da lafiyar kwakwalwar tasa ita kanta tare da ba shi lafiyar jiki kamar yadda masana suka ce.

4. Zuma na taimakawa wurin narkewar abinci a ciki Zuma nada matukar muhimmacin wurin magance matsalar gudawa inda take taimakawa narkewar abinci a cikin dan adam.

Wannan yana rage matsalar gudawa kasancewar abincin zai narke yadda ake bukata a ciki.

 

5. Zuma na maganin kurajen fuska (finfus) Zuma idan aka hada ta da sauran nau’in itace irinsu lemun tsami,gayen fiya da sauran wadansu ganyayyakin domin shafawa a fuska su na maganin kurajen fuska wanda aka fi sani da finfus.

Mutane da dama wadanda suka yi amfani da wannan maganin sun bamu tabbacin ingancinsa wurin magance kurajen fuskan.

 

*SHAWARA*

Dan Allah duk macen da ta karanta wannan posting din namu ta taimaka tayi forwarding dishi ga yan uwa mata masu aure..

Kuci gaba da kasancewa da wannan shafin mungode da ziyartarku.

Kuma kada kumanta ku’aje mana ra’ayinku a comments box dake kasa mungode.

©Funeyy.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button