Raye rayen da Tahir Fagge keyi da Yan’mata bayinsa bane Asiri Aka Masa
Abinda Tahir Fagge Yake Yi Ba Yinsa Ba Ne Asiri Akai Ma Sa
Tahir Fagge Addu’a yake buƙata ba zagi da tsinuwa ba daga gareku, domin shi wannan FLOOR ɗin da kuke gani yana hawa yayi rawa ba ordinary FLOOR ba ne da muke gani wani waje ne mai masifar kiranye ba kowane yake hawansa ya daina cikin sauki ba.
Duk wanda bai taɓa taka ƙafarsa a Gidan Wasa ba shine bai san masifar kiranyen gidan ba, idan zuwa gida wasa ya kamaka barinsa aiki ne ɓare kuma ace kana hawa FLOOR kayi rawa.
A Gidan Wasa ne zaka ga duk masifar son da Namiji yake yiwa Motarsa amma yazo ya bayar da ita ya koma gida a ƙasa wani har bashi yake ci don yaje yayi liƙi ya dawo kasuwa a ɗaureshi.
Nasan mutanen da suke siyarda ƙadarorinsu don suje gidan wasa su liƙa kuɗi. Ko last week akwai wanda aka bani labari saboda karayar arziki ya saka gidansa a kasuwa zai siyar ƙarshe sai abokinsa ya bashi kuɗi ƙarshe ance an ganshi a gidan wasa yana liƙa kuɗin.
Gidan Wasa wata Duniya ce mai zaman kanta wacce shigarta babu ranar fita sai idan Allah ya taimakeka! Koda kuwa babu wanda ya yi maka asiri bare kuma Tahir Fagge da ake cewa asiri aka yi masa.
Duk da abinda yake yi ba daidai ba ne ba amma fa saboda shi Ɗan Film ne aka fi yayata abin saboda sananne ne amma idan kaje Gidan Wasa zaka ga wanda ya kusa haifarsa yana rawa a FLOOR da jikokinsa, Allah Ya a shirye mu, Amin.
*SHAWARA*
Dan Allah duk macen da ta karanta wannan posting din namu ta taimaka tayi forwarding dishi ga yan uwa mata masu aure..
Kuci gaba da kasancewa da wannan shafin mungode da ziyartarku.
Kuma kada kumanta ku’aje mana ra’ayinku a comments box dake kasa mungode.