Salon Soyayya da Sakonnin Soyayya na Maza da Mata
Salon Soyayya da Sakonnin Soyayya na Maza da Mata
a yayin da masoya suke gudanar da soyayya a tsakaninsu, dole ne sai an dinga yin ta cikin kaffa-kaffa.
Nuna zumudi da matukar fito da maitar soyayya a fili, shi ke sanya gajiyawa ga dayan da ya zamo abokin tarayya a soyayya, don haka dole ne sai anyi ta cikin taku da nuna kulawa amma ba’a zake da yawa ba.
Masu iya magana suna cewa, “ido wa ka raina…? Amsar kuma itace, wanda nake gani kullum” ba a ce kar ki/ka dinga kula masoyayarka ba sai dai ana so kar ka cika nuna zakewa.
Ko a wajen zuwa tadi/zance/hira, kar ya zamo ka nace har a gaji da kai.
Da yake yanzu zamani ne na amfani da social media ko waya hannu ,to ko ba ka je ba zaka iya aikawa da dan gajeran sako don masoyi/ masoyiya ta san kana tare da ita.
Don haka masoya su kula da wannan, domin yawan naci yakan haifar da matsala, nacin zuwa hira a kowanne lokaci nacin kiran waya, har ma da tura sakon text messeges a wasu lokutan wasu lokuta masoyi/masoyiya za taiya warewa don turawa masoyinta sakon nuna soyayya da kulawa haka nan wani lokaci masoyi zai ware wanda zai iya ziyartar masoyiyarsa domin zantawa, da gabatar da wasu batutuwa don kara dankon soyayya a tsakaninsu rashin kulawa kuma zai iya jawo wasu matsaloli su faru ga masoyan, amma dai an fi son kulawar ta zamo mai tsari, tsari mai kyau ta yadda masoyi/masoyiya ba zata gaji da masoyinta ba, ko kuma masoyi ya gajiya da masoyiyarsa ba dole ne ya zamo an samu kyakkyawar mu’amala ta soyayya da kauna tare da amincewa juna ta hanyar da zata zamo mai tsafta kuma ya kasance ana dan bada gaf saboda yin nazarin abinda kanfi saurin farantawa masoyi ko masoyiya rai tare da samar da kyakkyawan nishadi mai armashi.
✥✥✥. **SAKONNIN MASOYA** ✥✥✥
💗 na tabbatar so yanayin sa yakan sauya daga farin launi zuwa kore.
💗 sonki yana cikin zuciyata, amma ina kokwanton kada ya zama tsuntsu ya tashi, idan har na ya kasance kin ci gaba da nuna rashin kulawarki a kaina.
💗 kyakkyawa mai kyan tsari,a duk lokacin da nake kallonki, tamkar kyakkywar fulawa mai furanni ma’abota debe kewa da sanya nishadi a zuciya ki kan zamo min.
💗 kiyi min agaji, ki tausaya min, ki tallafe ni, ki amince dani a cikin zuciyarki, sonki ya gama shiga jikina.
💗 kada ki bar ni shawagi tamkar tsuntsu a sararin SAMANIYA. SONKI NAKE HAR ZUCI.
❀❀** MAZA **❀❀
●- kyauta ta musamman a gare ki, ke kadai, domin faranta ranki ya abar kaunata, baya ga kaina dana baki, ga kuma kyautar FUREN SO.
✦ abar alfaharina, ina sonki fiye da adadin lissafinki, adadin da zai iya zamowa tamkar zubar ruwan sama a lokacin damina.
Ke kadai ce tawa.
✦ na zamo tamkar agwagwa, ina iyo a cikin kogin sonki.
Da za ki tallafa, da kin kawo karshen iyon da nake yi da ninkaya domin gudun gazawar gwiyawuna a lokacin da igiya ruwa ta nadeni.
Na kasance tamkar kifi a cikin ruwa, idan nayi gabas sai kuma na dawo nayi yamma, idan nayi kudu, sai kuma na dawo nayi arewa.
❊❊** MATA **❊❊
✥ dawainiya nake da sonka a cikin zuciyata, da sannu zaka fahimci ni masoyiyarka ce ta hakika, na zana zanen fulawar so a tafin hannuna nayi nufin nuna maka domin ka fahimci yanayin zancen da sonka yayi a cikin zuciyata.
✥ ina sonka tamkar yadda ba zan iya bayyana maka ba, ina sonka tamkar yadda baza ka iya kirga adadin ruwan sama ba kada ka zubar da hawayenka, yayin da wani ya bata maka rai, tuna da wacce kake so, ka ke kauna, sai zuciyarka tayi fari.
ina sonka abin kaunata na kasance a cikin masi kasa bacci yayin da dare ya tsala, bani da komai sai tunaninki, har wani lokacin gari kan waye ban iya runtsawa ba nasan wannan yana faruwa ne saboda irin tsantsar soyayyar da nake miki.
Shin ko kema haka ne? Tattausan lafazin ki abin kwatantawa.
Komai naki daban dana sauran ‘yanmata da zan kwana ina misalta kyawun halittarki, ba zan iya kaiwa karshe ba, koda kuwa zan wanzu ina yi har karshen rayuwata.
Hmm wanna harda matar aure ko mijin aure yana iya aiki text messege ne.
KU KASANCE TARE DA SIRRIN RIKE MIJI
YABO NA MUSAMMAN GA DUKKAN MASOYAN DA SUKE RIKE ALKAWARIN JUNA TSAKANI DA ALLAH,
BEGE
KAUNA
MASOYA
MURMUSHIN.