Labarai

An maka Ado gwanja, Safaru, Mr442 Murja da Ummi shakira a Kotu Akan Bata Tarbiya

Kotu ta umarci ƴan sanda su cafko su Ado Gwanja, Safara’u, Mr 442, Murja Kunya, Ummi Shakira da sauransu domin bincike

 

T@wagar wasu lauyoyi sun maka wasu gungun mutane da ake zargi da yada Alfasha a cikin al’umma a Kotu, wadanda suka hada da mawaki Ado Gwanja, Mr 442, Safara’u, Dan Maraya, Amude Booth, Kawu Dan Sarki, Murja Ibrahim Kunya, Ummi Shakira, Samha M. Inuwa da kuma Babiyana.

Cikin wata takarda da kotun majistare dake Bichi, karkashin mai shari’a, Jostis Bello Musa Khalid, an bukaci kwamishinan yan sanda na jihar Kano, ya gudanar da bincike akan wadanda ake zargi.

Tunda fari dai wani lauya ne mai suna Barista Badamasi Sulaiman Gandu Esq, ne ya bada wa’adin kwanaki uku ga hukumomin da abun ya sha fa akan su dauki mataki ga mawakin Hausa Ado Gwanja, akan wata sabuwar waka da yayi mai taken “Chas” wacce ake zargin anyi amfani da kalaman batsa a cikinta, idan kuma ba haka ba zai garzaya kotu.

To sai dai yanzu a iya cewa lamarin ya girmama, domin a cikin kunshin lauyoyin da suka maka wadancan Mutane a kotu, bayan barista Badamasi, akwai, Barista Muhd Ali Hamza Esq, Abba Mahmud Esq, Muhd Nasir Esq, L.T Dayi Esq, da kuma G.A Badawi.

Daga Cikin abubuwan da akayi kara akansu sun hada da yin wasu wakoki da sukayi karo da addini da kuma al’ada, masu ta ken “War” da kuma “Chas” wanda Ado Isa Gwanja yayi, sai kuma sauran da ake zarginsu da hawa kan wakoki suna tikar rawa da kuma wasu abubuwa da suka ci karo da addinin musulunci da kuma al’ada.

Karanta Kadan Daga cikin Ra’ayoyin mutane:

 

  1. Allah ya shirye mu ga ba ki daya don alfarmar annabi Muhammmad s a w
    Allah ya Farantawa Duk Zuciyar dake Ƙaunar𝘼𝙣𝙣𝙖𝙗𝙞 𝙈𝙪𝙝𝙖𝙢𝙢𝙖𝙙 𝙎.𝘼.𝙒
    Allah ubangiji yasa annabi Muhammmadu s a w yacece mu gobe kiyama.
  2. Allah wadaran naka ya lalace. Dama wallahi mun hasashen wannan ISKANCI da sunan HAUSA FIRM zaikawo ga wannan matsaya, yau kuma gashi tunba mu mutaba gashinan akan idon mu munfara gani.Ya Allah muna rokonKa ka kawomana karshen wannan barna na kannywood.
  3. Tofa,
    Ubangiji Allah ya shirya mu Amma Ina ganin abun da Kamar wuya hanasu wadannan abubuwan da sukeyi saboda, inde bawai su Suka ji tsoron Allah suka Dena ba, Ina ganin zaiyi wuya a hukunta su
  4. Ba dole ma Allah ya rinka jarabarmu da masifu kala daban daban ba duk halinmu ne ya jawo mana don ma muna cin albarka cin manzin Allah (S A W) ai da tuni Allah ya gama halakamu Allah ya shiryar dasu ameen
  5. Ni a ganina tarbiya dai indai mutum bashi da shi, don kafin wayannan su waye Yan arewa na kallon Yan kudu, Bata tarbiya Yana Chan. Ku kyale mutane, kowa yayi daidai wallahi ya sani.

Mr 442 da safarau

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button