Gyaran Jiki

Maganin Sanyin Mara (Infection)

MAGANIN SANYIN MARA(INFECTION)

IDAN KA KARANTA KA TURAWA SAURAN YAN UWA DOMIN SUMA SU ANFANA:

 

Bayani gane da maganin sanyin mara(infection)wanda a wannan zamani yake addabar maza da mata masu aure da marasa aure, insha Allah ga maganin sa.

 

Kamar masu fama da

1. Kaikayin gaba
2. Zafin fitsari
3. Ciwon mara
4. Fitar farin ruwa
5. Fitar kuraje
6. Kankantar gaba.
7. Daukewar shaawa.

Dadai sauran matsaloli da sanyin ke haddasawa. insha Allah indai suka juri yin wannan hadi Allah zai basu waraka, kuma zasu sami sauki.

Amma wani jan hankali guda.

Mutane da yawa suna da gaggawa wajen neman magani, babu yadda za’ai kana dauke da ciwo tsawon wasu shekaru ya riga yayi maka katutu(chronic)sannan kace zaka sha magani cikin kankanin lokaci ka samu sauki.

Bawai hakan baya faruwa bane, amma dai a rika bi a hankali da kuma bin ka’ida domin samun dacewa.

ABINDA ZAA NENA.

1. Garin Kusdul hindi
2. Garin habbatussauda
3. Lemon tsami
4. Lemon zaki.

YADDA ZAA HADA.

Da farko zaka samu garin habbatussauda kamar chokali 10 cikakke
Garin kusdul hindi chokali 20 cikakke shima. sai ka hade su waje daya ka chakuda.
Za’a rika diban hadin kullum chokali 1 da lemon tsami guda 2 lemon zaki guda 2 duk a hada a tafasa da ruwa cikin kwanan sha bayan an tafasa shi sai a sauke a tace shi a rika sha sau 4 a rana kofi dai dai.
Idan kana da iyali tare zaku sha kullum haka har wata 1.

Insha Allah zaa samu sauki da waraka daga Allah.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button