kannywood

Kalaman Soyayya zuwa ga budurwa 2022

Kalaman Soyayya zuwa ga budurwa

Kowani lokaci idan na kalle ki, sai na yi murmushi, cikin farinciki in ce; “Ke ce abinda na taba mallaka mafi daraja a wannan duniyar” Ke gwana ce a yadda ki ke,

 

Hatta hasken dukkan taurari, ba za’a kwatanta su da hasken kyallin idanuwan ki ba,

Akwai milyoyin hanyoyin da zan ambata miki cewa; Ina Son Ki. Amma na rasa wanne zan ɗauka, duk wanda zan ɗauka, sai in ji tamkar bazai bayyana adadin son da nake miki ba. Kawai dai Ina Son Ki sau malala gashin tinkiya.

 

Ina son rayuwata kasa da yanda nake sonki, ina sonki sama da yanda nake son rayuwa ta, ita kanta rayuwar babu ita idan har babu ke, domin ke ce cikamakin rayuwar!

@Abar Kauna.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button