Labarai

Lauyoyin da suka kai ƙarar su Ado Gwanja, Mr. 442 da Safara’u suna ɓata ma Kansu Lokaci ne Kawai

Lauyoyin da suka kai ƙarar su Ado Gwanja, Mr. 442 da Safara’u suna ɓata ma Kansu Lokaci ne Kawai

_______________________________________________________

Kamar yadda muka sani wasu gungun Lauyoyi Musulmai su 9 sun kai ƙorafi a gaban babbar kotun Shari’ar Muslunci dake zaman ta a garin Bichi inda suke chajin wasu gungun mawaƙa da kuma wasu ‘yan Tiktok akan waƙoƙin da su mawaƙan suke yi wanda sukace sun saɓa da koyarwar addinin Musulunci.

 

To abinda nake so mu sani anan Shine:
Ita fa Shari’ar Musulunci Constitution ya bamu damar yin amfani da ita ne da hannun dama amma kuma ya karɓe da hannun hagu, me yasa ? Dalili shine Shari’ar Musulunci fa a dokar Nigeria ba komai bace face al’ada, ita kuma al’ada a dokar Nigeria akwai wasu ma’aunai da sai ta tsallake su sannan ne za’a iya yin hukunci da ita, saboda haka ba lallai ne dokokin musulunci ko hukunce-hukuncen musulunci su zama sun karɓu a kotunan Nigeria ba.
Misali: alƙalin Shari’a Court zai iya yin hukunci daidai da koyarwar Shari’ar Muslunci amma kuma idan har ya zama yaci karo da dokar ƙasa to idan ka ɗaukaka ƙara za’a iya yin watsi da wancan hukuncin na kotun Shari’ar Muslunci saboda me ? Saboda ya saɓa ma Constitution, to kuma kamar yadda Babi Na 1, Sashi na 1 na Constitution din ya faɗa shine: Duk wata doka kowace iri ce kuma ko dokar wanene tana ƙasan dokar Constitution ne, idan har taci karo da Constitution to dole a watsar da ita a ɗauki ta Constitution.

 

A takaice, Alqur’ani ko dokokin Allah suna yima Constitution biyayya ne, amma shi Constitution baya yima dokokin Allah biyayya.

Don haka, kamar yadda na faɗa cewa akwai ma’aunai guda uku da ake auna kowace doka ta al’ada daga cikin su har da dokar Musulunci, wanda idan ta tsallake waɗannan ma’aunan to za’a iya yin hukunci da ita, amma tana kasa tsallake ɗaya daga cikin su to za’a watsar da ita, ma’aunan sune:

 

1• Repugnancy test:

Matakin farko za’a ɗauko wannan hukuncin na Musulunci ne a ɗora shi a wannan ma’aunin domin aunawa.

So, Repugnancy test Na nufin ya zama al’adun basu saɓa ma ɗabi’ar mutum ba, kuma wannan shine yafi matuƙar wahala wurin tabbatar wa a kotu na, domin ƙarin bayani duba Shari’ar da akayi tsakanin Okonkwo v. Okagbue
Kamar yadda Justice A. Y. Ya faɗa shine ko su waɗanda suka tsara waɗannan ma’aunan ba zasu iya baka cikakken bayani ba akan abinda suke nufi da wannan, don hana kunga hanya mafi sauki kenan wurin yin watsi da duk wani hukuncin da suke ganin baiyi daidai da ra’ayin su ba.

2• Incompatibiliy test:

Shi kuma wannan wani nau’in ma’auni ne da ake amfani dashi wajen tabbatar da cewa wannan al’adar shin za’a iya amfani da ita ko kuwa, za’a tabbatar da hakane idan aka auna aka ga bata saɓa ma dokokin ƙasa ba, idan kuwa har ta saɓa to za’a yi watsi da ita ne kai tsaye.

3• Public Policy test:

Wannan shine ma’auni na uku wajen tabbatar da cewa wannan al’adar wato hukuncin zai iya zama karɓaɓɓe idan har ya zama ya tsallake wannan ma’aunin.
Don haka, idan har akwai wani hukunci na Musulunci da ba’a so, za’a iya amfani da wannan ma’aunin a dakatar dashi sai ace ai ya saɓa ma Public Policy test, saboda shi Hukuncin Musuluncin a dokar Nigeria al’ada ne kawai ba wani abu ba.

Don haka, nake ganin waɗannan lauyoyin suna wahalar da kan su ne kawai amma babu abinda zai faru, koda kuwa Kotun Musuluncin ta kama su da laifin ta yanke masu hukunci to ina tabbatar maku sai an rusa wannan hukuncin domin kuwa za’ace ae ya saɓa ma ma’aunan da ake gwada al’ada, kuma ya saɓa ɗin.

Don haka, inda sun sani to ba kotu ya kamata su kai su ba, a’a irin wannan Bill din da nayi Proposing irin shi ya Kamata su hadu suyi Proposing, sannan suyi mobilising mutane akan su matsa ma majalisa lamba akan lallai ta amince dashi a matsayin doka, to In sunyi haka Shikenan ina da tabbacin zasuyi Nasara akan duk wani mawaƙi ko wanda suke ganin yana yin abubuwan da ya saɓa kamar yadda suka faɗa, amma dai a haka to ina da tabbacin babu wata nasarar da za suyi, domin waɗannan mawaƙan da ‘yan Tiktok basu zagi kowa ba basu tashi hankalin kowa ba, to dokar ƙasa kuma ba zata sanya masu ido ba, amma da anyi wannan dokar Shikenan, case closed.

Bissalam
Shehu Rahinat Na’Allah
9th September, 2022

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button