Gyaran Jiki

Abubuwa 10 Da Suka Kamata Ma’aurata Suyi Bayan Jima’i

Wasu Abubuwa 10 Da Suka Kamata Ma’aurata Suyi Bayan Jima’i:

ZAMANTAKEWAR AURE GA MA’AURATA:

Ba wai kawai saduwar jima’i bane yake baiwa ma’aurata karin soyayya da kusantar juna ba. Akwai wasu halaye da Ɗabi’un da ma’aurata idan suna yiwa junansu duk bayan ko wani kwanciyar aure tofa a kullum zasu kara danƙon soyayyar auratayya su.

 

A wannan darasin zamu kawo muku wasu abubuwa 10 Da suka kamaci ma’aurata su kasance suna yi a duk bayan kammala jima’i.

1: Yiwa Juna Godiya: yana da kyau ma’aurata su rika yiwa junansu godiya a duk bayan jima’i saboda yadda kowane cikinsu ya bada tasa gudunmawar wajen dada dawa guda.

Hakan nan kuma kowannensu ya kashe sha’awarsa ne ta halasta ce hanya albarkacin guda.

 

Wannan yasa yiwa juna godiya duk bayan jima’i yana da kyau.

2: Tsaftace Al’auran Juna: Yana da kyau duk bayan kammala jima’i ma’aurata su tsaftacewa junansu jiki kamin su shiga wanka.

Mace ta tsaftace dukkannin inda jikin mijinta ya baci. Haka shi ma mijin ya tsaftace mata nata.
Bai dace ba da zaran ma’aurata sun gama jin dadi sai kowa ya shiga gyara jikinsa da kansa.

3: Yin Wanka Tare: Bayan kammala jima’i yana da kyau ma’aurata su shiga suyi wanka tare. Su cuncuda junansu. Haka yana kara danƙon soyayya matuka ga ma’aurata.

4: Ciyar Da Juna: Mafi yawan mutane suna son cin abinci bayan kammala jima’i. A irin wannan ya dace koda guda baida sha’awar ci, to ya zauna tare da gudan yana ciyar dashi ko suna ciyar da juna. Wannan salo na soyayya bayan jima’i yana kara kusantar ma’aurata.

5:Tattaunawa Akan Jima’i : A wannan lokacin yana da kyau ma’aurata su taba batun jima’i n da suka kammala a yanzu. Idan akwai abunda aka yi wa guda da bai gamsar dashi ba sai yayi magana.

Idan kuma dukkaninsu sun samu gamsuwar da suke bukata sai sun kambama juna tare da jandadawa juna salon kwanciyar da suka fi bukata ko kuma Wasannin Motsa Sha’awa.

Irin wannan hiran yakan baiwa ma’aurata daman gano abunda suke so da kuma abunda suke ki a lokacin jima’i.

6: Kwanciya Tare: bayan kammala jima’i yana kara shakuwar ma’aurata. Ya dace duk bayan jima’i kada kowa ya koma ya kama shifidarsa daban sai kuma lokacin jima’i ne zasu sake hadewa kuma.

7: Rungumar Juna: Bawai kawai ma’aurata su kwanta a shinfida guda ya wadatar ba. Yana da kyau sun rungumi juna a yayin kwanciyar tasu.

8: Yiwa Juna Kalaman Soyayya : Idan an rungumi juna ba kuma gum za ayi ba kamar kurame ba. Yana da kyau a wannan lokacin maauarata suna shafa juna suna kuma zuga juna na kyau ni’ima ko halitta da kuma soyayyar da suke nunawa juna.

9: Rakiya Da Kida: Kamar yadda aka saka kida ko waka ko wata sarewa mai rasta zukata. Haka nan ma lokacin da za ayi kwanciyar barci ya dace a saka a wannan lokacin na kwanciyar barci.

10: Sumbatar Juna: Kada ma’aurata su sake barci ya kwashe su ba tare da sun yiwa juna Sumbatar karshe ba.

Da zaran ma’aurata sun ji alamun barci na zuwa. Wannan good night kiss ba ƙaramin tasiri bane yake dashi a tsakanin ma’aurata ba.

Da fatan ma’aurata zasu daure suyi amfani da wadannan matakan. Allah Ya bada ladan Daɗaɗawa juna.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button