Gyaran jikin Amarya Kafin Sati Daya
GYARA JIKI AMARE KAFIN SATI DAYA:
( fatan ta yi laushi da sheki)
๐ฟ man zaitun
๐ lalle
๐ฟ kur-kur
โ madara peak
Zaki hade wadannan kayan hadin guri daya, sai ki kwaba su ki shafe jikinki da fuskarki, zakiyi wannan hadin kafin ki shiga wanka. Idan ya bushe a jikinki sai ki murje sannan sai ki shiga wanka jiki yana yin kyau yayi sheki
GYARA JIKI 2:
Wannan hadin shi akecewa kafi TURGEWA
๐ฟ kur-kur
๐ฟ dulka
๐ฟ zuma
๐ฟ kwai
๐ฟ lemun tsami
Ki hade su guri daya ki samu ki kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma yafi kwabin lalle ruwa, sai ki shafe fuskarki Idan kuma har dajiki kikeso, sai ki shafa harda jiki
Bayan (1hr) sai ki shiga wanka zaki ga yadda jikinki zai goge
GYARA JIKI 3
( fata ta yi laushi da sheki)
๐ lalle
๐ kwaiduwar kwai guda 3 ( yellow )
๐ manja cokali 3
๐ต kur-kur
Sai ki kwaba su guri daya ki shafe jikinki zuwa (1hr) daya, sai ki yi wanka da ruwan zalla da ruwan dumi ki shafe jikinki da ita sai ki kuma yin wanka
KYAN FUSKA:
Sai ki hade su guri daya ki kirba su cikin turmi, ki mulmula ki rinka wanke fuska zaki ga yadda fuskar ki zatayi
๐ฟ dettol
๐ฟ sabulun Ghana
๐ฟ garin zogale
๐ฟ farar albasa
GYARA FUSKA;
Wanna hadin wanda ya kesa fuska tayi haske da annuri takun Kore kurajen fuska.
๐ bawon kankana
A samu bawon kankana sai a rinka goge fuska da shi yana gyara fuska tayi sumul
GYARA FATA
๐ Lemun tsami
๐ bawon kwai
๐ kur-kur
Zaki hade su guri daya ki daka su sai ki rinka wanka dashi fatar mace zata goge tayi kyawun gaske
GYARA FATA:
๐ ganye magarya
๐ sabulun salo
Zaki daka ganyan magarya sai ki zuba a cikin sabulun salo ki rinka wanka yana gyara jiki
GYARA FATA
โข ganyan magarya
โข man zaitun
โข man habbatussauda
Ana daka ganyan magarya a zuba cikin man zaitun da man habbatussauda shi ma yana gyaran
***
GYARA FATA
๐ฟ lalle
๐ garin ridi
Ana amfani da lalle kafin ki shiga wanka sai ki kwaba ki zuba garin ridi ki shafe jikinki zuwa (1) hr sai kiyi wanka
GYARA GASHI
Man zogale
Man kwakwa
Man zaitun
Zaki hade su guri daya ki rinka shafawa a kanki
GYARA GASHI
๐Man zogale
๐Ganyan magarya
๐Kanunfari kadan
Sai ki hade su guri daya ki rinka shafawa a kanki yana sanya tsayin gashi ya kuma yi laushi
GYARA KAFA:
Baki ba zuwa wajen wanke kafa madarar kinyi amfani da wannan hadin
๐ธยถ man shanu
๐ธยถ man kwakwa
๐ธ man ridi
๐ธ man alayyadi
Idan kafa tana tsagewa ko tana kaushi da daddare zaki hada wadannan mayamayen guri daya ki shafa a kafa in zaki kwanta bacci daddare sai ki daure da Leda da safe ki wanke da ruwan dumi ki shafa man zaitun da man ridi
MAGANI CIWON SANYI
Duk macen data ke son ni’ima ta tabbatar mata, koda yaushe ta kasance cikin ni’ima to lallai ya zama dole ta magance matsala ciwo sanyi
TOILET INFECTION
Domin magance wannan matsala ta samu wadannan kayan
๐บ hulba
๐บ bagaruwa
๐บ habbatussauda.
Ki hada hulba da bagaruwa guri daya, ki dafa idan ruwan ya sha iska sai ki zauna a ciki, kuma ki samu man habbatussauda kiyi matsi dashi.