Gyaran Jiki

Amfanin Cin Ayaba Ga Maza

Amfanin Cin Ayaba Ga Maza

Ayaba tana cikin jerin kayan marmari da suka yi fice ga cimakan Danadam. Sai da mafiya yawan mutane sun tafi akan fahimtar mara lafiya ne yafi bukatart cinta.
Wasu masu lafiyan kuma suna cinta ne ba tare sun san alfanunta a likitance ba. Suna cine ko dai saboda sha’awa ko saboda ciki ya dauka.
Ayaba tana da matukar mahimmanci a jikinmu musamman ma mu maza, sai dai kadan daga cikin mune suka san hakan.
Ga wasu alfanun da ayaba take da shi ga duk namiji da yake yawaita cinta a kullum.

1: Karfin Kashi Da Wanke Hanta-  Da yake Ayaba tana dauke da sinadarin potassium da yawa. Hakan yasa duk na mijin da yake yawan cinta zai kara masa karfin kashi da kuma tsaftace masa hantarsa inji masana.

Ganin yadda ita wannan sidarin na potassium ke fita daga mafitsaran mu, yawan cin Ayaba zai maye gurbin sinadarin calcium ya kuma inganta karfin kashi namiji baya ga wanke masa hanta da yake yi.
Sannan ita Ayaba tana kara lafiyar zuciya ga mai cinta. Saboda yawan sinadarin potassium da kuma karancin sodium a tare da ita. Hakan yasa take kara lafiyan zuciya ta kuma hana mutum hadarin kamuwa da ciwon hawan jini.

 

#bincike
2: Rage Shuga Da Bunkasa Garkuwan Jiki-  dayake Ayaba na dauke da sinadarin Vitamin B6, hakan yasa yawaita cinta zai daidaita maka shugan dake jikinka ya kuma karawa garkuwan jikinka karfi. Inda zata maida wannan shugan na jikinka daga carbohydrates zuwa glucose. Sai dai ga masu ciwon shuga wasu likitocin na hanasu cinta gaba daya ko kuma su rage.

#bincike
3: Ayaba tana dauke da wani sinadari a jikinta mai suna tryptophan, wannan yasa idan namiji yana yawaita cinta zata samarmasa da wani sinadarin da ake kira serotonin nan take. Ita kuma mafaninta shine ta cirewa mutum damuwa daga zuciyarsa ta rika sashi annashuwa.
Don haka masana suka ce duk mai yawan cin Ayaba kullum cikin walwala yake.

 

Ganin yadda gajiyan jiki yake yawan sa mutane su rasa sinadarin potassium nan take. To cin Ayaba guda daya zai maidawa namiji sidarin na potassium guda 400 milligrams idan namiji yaci guda daya a rana bayan kammala aiki na gajiya. Nan take zaka ji watsai a jikinka.

Haka nan kuma masana suka ce mai yawan cin Ayaba kwakwaluwarsa na kara budewa ne basa mantuwa saboda yadda take samarwa kwakwaluwan mutum karin lafiya.

4: Rage Girman jiki- Duk namijin dake son ya rage kiba na girman jikinsa, ya yawaita cin Ayaba zai ga jikinsa ya ragu cikin karamin lokaci.

Kaman yadda aka sani duk wani kayan marmari yana da alfanu a jiki, saboda Samar da abunda masana suke kira Fiber. Cin Ayaba guda a rana zai samarmaka Kaso 12 na wannan fiber din a duk rana idan namiji yana ci.

 

Musamman bayan da mutum yaci abinci mai nauyi ya samu Ayaba ya ci. Tana shiga zata rugurguza duk wani abincin da zai iya haifarwa mutum kiba a jikinsa.
#bincike
5: Taimakawa Wajen Dagargaza Abinci: Duk mai yawan amfani da Ayaba ba zai samu matsalar zagawa ba a lokacin da bukatar hakan ya kama. Domin ita Ayaba tana ragargaza abincin da mutum yaci ne domin samun damar fitar da abunda ba a so na jikin mutum ta hanyar zuwa bandaki.
#bincike
6: Warkar Da Cutukan Asthma, Ulcer Da Mashako- Masana suka ce yawan cin Ayaba na maganin cutar nan ta asthma, ulcer da kuma mashako.

 

A cewar masana, Ayaba tana dauke ne da abubuwan da zasu hana kamuwa da wadannan Cutukan, da kuma Warkar dasu idan wanda yake dauke da irin wannan cutar zai yawaita cinta.
#bincike
7: Motsa sha’awa-Tryptophan wani sinadari ne dake cikin Ayaba. Idan namiji yana yawan cinta zata kara masa yawan ruwan maniyi, sakamakon hakan kuma zai tayarwa namiji sha’awa.
Yawan sinadarin bromelain da kuma vitamin B da Ayaba take karawa namiji a jikinsa, nan take zai ji sha’awar sa na Jima’i ya taso masa.

Sai dai wannan alfanun ba wai ya takaita bane ga maza kawai ba. Dukkanin wadannan abubuwan da muka jero na alfanun da ayaba take samarwa, ita mace zata iya samunsu. Saidai da yake maza ne ke yawan gwagwarmaye, yafi dacewa su yawaita amfani da ita.
Da fatan mazan da basu amfani da Ayaba, sai su soma, masu amfani da ita su kara himma. Wadanda suke cinta ba tare da sanin alfanunta ba, yanzu sunji wasu daga cikin su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button