Hausa Novels

Sirrin soyayya guda 5

ZO NAN, SAURAYI DAN SOYAYYA!

1- Kada kaga macen da kake so a yau, kuma ka furta mata kana sonta a yau din, akwai ganganci da rashin sanin soyayya a cikin yin hakan,

Related Articles

Yi kokari ka fara samun kusanci da ita, tare da kulla abota da ita na tsawon wasu yan kwanaki kadan, a nan zaka fahimci irin macen da ta dace kaso ta ce ko kuma akasin haka take?

2- Na haneka da yin doguwar soyayya da mace, irin soyayyar da zaka riski masu yinta sun shafe shekara da shekaru suna yinta, kaso mafi yawa na irin wannan soyayyar karshenta bai cika zuwa dakyau ba, ku takaita soyayya a waje, ayi aure, bayan anyi aure daganan ku dora soyayyarku daga inda kuka tsaya har zuwa karshen rayuwar ku,

3- Ka zamto me sirri a cikin soyayyar ka, dukkan saɓanin da zai gifta tsakanin ka da masoyiyarka, kayi kokarin boyeshi ta yanda babu wanda zai sani, har zuwa lokacin da zaku daidaita tsakanin ku,

Mace da Namiji marasa sirri mutanen dake kewaye dasu suna musu kallon gidadawa waɗanda basu san kansu ba, domin shi wanda kake kawowa sirrin zamanka da matarka/budurwarka shi baya kawo maka nasa sirrin,l.

 

4- Ka so macen da take burgeka, kada kaso wadda take burge mutane, ka so wadda kake so, kada ka so wadda mutane ke so, ka auri mace, idan har kana da hali duk rintsi kada ka bari a aure ka,

5- Ka kasance me kyautatawa a cikin soyayya, amman ka kyamaci dabi’ar roko daga wurin dukkan mace, domin mace me roko idan har bata dainaba wannan rokon zai iya zama silar lalacewar rayuwar ta,

Domin samari yan yankan wuta sunfi son mace me roko, domin idan kika rokesu suka baki, tabbas kema za su rokeki domin ki basu,

Ka rike waɗannan shawarwarin, za su amfaneka anan kusa.

~ Abubakar Haruna Sani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button