Gyaran Fata da gyaran fuska
KYAN FUSKA:
Sai ki hade su guri daya ki kirba su cikin turmi, ki mulmula ki rinka wanke fuska zaki ga yadda fuskar ki zatayi.
1.dettol
2.sabulun Ghana
3.garin zogale
4.farar albasa
GYARA FUSKA:
Wanna hadin wanda ya kesa fuska tayi haske da annuri takun Kore kurajen fuska
* bawon kankana
A samu bawon kankana sai a rinka goge fuska da shi yana gyara fuska tayi sumul
GYARA FATA:
1.Lemun tsami
2.bawon kwai
3.kur-kur
Zaki hade su guri daya ki daka su sai ki rinka wanka dashi fatar mace zata goge tayi kyawun gaske
GYARA FATA:
1.ganye magarya
2. sabulun salo
Zaki daka ganyan magarya sai ki zuba a cikin sabulun salo ki rinka wanka yana gyara jiki
GYARA FATA:
*ganyan magarya
*man zaitun
*man habbatussauda
Ana daka ganyan magarya a zuba cikin man zaitun da man habbatussauda shi ma yana gyaran.