Gyaran Jiki

Kadan daga Cikin Halayen Matan Social Media

HALIN MATAN SOCIAL MEDIA 70%:

Yamnata suna complain akan samarinsu basa kulawa dasu to su samari ai ba mahaukata bane
In kaji mace tace saurayinta yana kulawa da ita nufin ta fa saurayin da zai sa ta a gaba yayi ta kashe mata kudade yana mata dawainiya kamar bai san zafin kudaden ba ko kuma ba wahala yake yi ya samu ba

Mace idan kace mata kwana biyu bana ganinki online sai kayi sa’a ne ma zata ce maka data ne matsalanta wata sai kaga tana neman daura maka nauyin siya mata waya

Wata zaka ce mata tachi abinchi kuwa kawai sai ta fara magana maganar ka siya mata kaza ko shawarma wata zatayi status kamar tana cikin damuwa kana mata reply zata fara maka maganar bata da kudi

Gaba daya in kasan baka da kudi to kar ma ka fara cewa zaka wani bawa mace kulawa wlh ko kiranta ka fiyeyi don kaji yadda take kafin ta daga wata sai ta fara zaginka tace wannan ya chika takura

Kulawa a wajen wasu matan ka tanadi kudi kawai daga sun dan yi motsi ko yaya ne ka jikasu da kudi amma duk wani kiran wayarka da wani zuwa zanchenka da wani yi mata text duk na banza ne
Allah yashirye mu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button