Shin Ko Kasan illar Yin Zina
Minene zina
KA TAƁA YIN ZINA?
Zina kala kala ce Hawa Hawa ce Iri - Iri ce Wata tafi Wata Muni.
-1.Yin zina da uwa ko ƴar'uwa ko ƴa, da dukkan maharramai, Wannan shine mafi muni a cikin zina, wanda ake hukuncin kisa ga wanda ya aikata._
-2.Yin zina da matar aure matar maƙoci, wannan zina ce tare da cin amana, akwai haƙƙin Allah da haƙƙin maƙoci da haƙƙin aure. Kuma alhakkin sa kamar ya yi zina sau goma za a rubuta masa._
-3.Yin zina da matar aure da miji mai aure, wannan akwai alhakki da yawa akan su, na cin amanar aure da keta alfarma sa kuma ga hukuncin kisa ta hanyar jefawa a kansu. Idan an kama su._
-4.Yin zina tsakanin mai aure da mara aure, ɗaya ya na da hukuncin kisa ɗaya ya na da hukuncin bulala ɗari da ɗaurin shekara._
-5.Yin zina tsakanin bazawari da bazawara, duk sun aikata babban laifi kuma idan shedu suka tabbata a kan su, su na da hukuncin kisa ta hanyar jefewa a musulunci._
-6.Yin zina tsakanin saurayi da budurwa, waɗanda ba su taɓa yin aure ba, hukuncin su, bulala da kuma ɗaurin shekara a wani gari ga namijin kawai.
-7.Yin zina ko Fyaɗe ga ƙaramar yarinya, wannan yana da muni kwarai da gaske, kuma wasu daga cikin malamai suna ganin hukuncin kisa ga wanda ya aikata haka._
-8. Zina wata babbar musiface da bala’i da dukkan sharri, da take ruguza al’umma, take wargaza iyali, take tarwatsa gari, take rushe mutunci, take jawo karayar tattalin arziki,da fatara, da tsiya, da annoba, acikin rayuwar dai dai ku, da gidaje, da unguwanni, da gururuwa, da kasashe, da duniya baki daya._
Zina itace cikakkiyar fitsara, a cikin zina ake samun dukkan sharri kamar haka:
1- Raunin Addini
2- Raunin Akida
3-Karancin Imani
4.Rashin kunya
5.Rashin kishi
6. Rashin mutunci
7.Rashin kwarjini
8.Rashin hasken fuska
9.Duhun zuciya
10.Rashin kima
11.Rashin Nagarta
12.Rashin Nutsuwa
13.Rashin Amana
14.Fushin Allah
15.Cikawa babu imani
16.Azabar Allah.
Allah ka tsaremu da zuri'ar mu daka afkawa bala'in Zina