Amfanin Zuma Guda 5 Akan Gyaran Jiki da Fata

Amfanin Zuma Guda 5 Akan Gyaran Jiki da Fata

Abubuwa 5 da zuma ke iya yi wa fata:

zuma wani abu ne mai daɗi, mai siffar ruwan zinare ana samun sa ne daga ƙudan zuma da wasu kwari masu alaƙa da su, kamar ƙudan zuma.

Zuma yana da fa’idodi da yawa ga lafiyar jikin dan adam. Baya ga wannan, ana iya amfani da zuma a matsayin maganin gyaran fata . Bari mu kawo maku abin da zaku iya amfani da zuma kuyi;

Na daya Domin samun Fata mai sheki: Idan kuna son fata mai sheki, to zuma ita ce mafi kyawun sinadarin halitta don ba ku wannan shekin da kuke bukata. Zaku iya hada danyen zuma da ruwan aloe vera. Sa’annan, ku shafa hadin a fuskar ku kafin ku kwanta barci da dadadare.

Na biyu Domin kawar da Busasshen Leɓe: Zaku iya kawar da busheshen leɓe ta hanyar amfani da zuma. Abu ne mai sauqi, sanya danyen zuma a lebban ku kafin ku kwanta barci! Kuma ku farka da lebe mai taushi da santsi.

Na uku domin kawar da tabo : Shin kuna son share wannan tabon da ke fatar ku? Toh abun da kawai za ku yi shi ne amfani da asalin ɗanyen zuma na halitta a fatar ku. Sai a bar shi da daddare kuma ku ga 
Yadda fuskar ku zata kasance washe gari.

Domin kawar da gishirin fuska watto blackheads: Don kawar da gishirin fuska, abin da kawai za ku yi shine cakuda zuma da ruwan lemo, sannan ku shafa a wuraren da abin ya shafa kafin ku kwanta barci.

Domin magance Kuraje: Cire kurajen fuska cikin dare daya ta hanyar sanya danyen zuma a wurin da abin ya shafa sannan a rufe da bandeji. Washe gari sai a dauraye fuskan da ruwa.