YADDA AKE YIN MAN KWAKWA DA KUMA AMFANINSA
YADDA AKE YIN MAN KWAKWA DA KUMA AMFANINSA
YADDA AKE YIN MAN KWAKWA DA KUMA AMFANINSA
YADDA AKE HADA MAN KWAKWA
Ababe da za’a bukata
•Kwakwa
•Ruwa
Yadda za a hada A samu Kwakwa mai kyau, sai a 6are 6won a kankare
bayan kwakwar ya rage farin kawai. Sannan a yayyanka ta kanana saboda
ta yi saukin markadawa. A zuba ruwa da dan dama a cikin blandar sai a
hada da yankakkiyar kwakwar. Sai a markada har sai markaden ya yi
laushi sosai. A sami a bin tatar kamu a tace ruwan kwakwa sosai. Za a
ga ruwan kamar madara. Za’a iya ajiye markadadden ruwan kwakwa na
kwana daya ma ga wadda ba ta da firiji. Ko kuma a saka shi a firiji domin
ruwan ya hadu sosai. Bayan kwana daya za a ga madarar kamar kindirmo
a saman kwano. Sai a kwashe wannan madarar da aka tace a zuba ta a
cikin tukunyar suya. Sai a dora tukunyar a kan wuta. Haka za a yi ta
juyawa da cokali har sai wannan madarar ta koma kamar ruwan kasa mai
dan duhu. Sai a sauke a sake tacewa. Za a ga man kwakwar ya fito tsaf.
Sai a sami kwalba a ajiye ana amfani das hi yadda ake so.
MAN KWAKWA YANA DA AMFANI DA YAWA GA LAFIYA
Ga kadan daga cikin ayyukansa:
1- Taushin fata – Ana iya shafawa kamar man jiki a shafa a ko’ina har
wuya. Wannan zai sa fata tay laushi da taushi.
2- Man fuska – ana shafawa a zagage kwayar ido da shi yana maganin
bakin da ke fitowa zagaye ido.
3- maganin tamushewar fata na tsufa. Idan ana shafa man kwakwa yana
maganin wannan.
4- Kwantar da fata yayin aski – Man Kwakwa yana gyarawa masu aski,
kamar maza masu yawan yin kurajen fuska, sakamakon gyaran fuska da
sauransu, yana warkar da kuraje.
5- Man goge hakora – akwai magungunan wanke baki dayawa amma
wannan na daban ne ku hada man Kwakwa a gauraya dan kadan a sa a
‘Brush’ a goge baki da shi.
Ayi sharing don Allah