Yadda Ake Gyaran jiki

Gyaran jiki

GYARAN JIKI

Za mu fara da sinadaran gyaran mama, wannan hadin na farko da zan rubuto yana karawa mace girman nono kuma sam ba ya faduwa. Ko da a ce tana shayarwa ne idan har tana amfani da wannan hadin sai dai mu ce Allah san barka.
Uwargida, ki nemi wadannan kayayyakin:
1). Farar shinkafa
2). Garin Alkama
3). Garin habbatus sauda
4). Garin Ayaba (Plantain).
5). Gyada mai malfa (mai zabo)
6). Aya
7). Madarar gari.
8). Zuma

Za ku bare bayan plantain sai a yanka shi, a shanya ya bushe, sai a daka, a hada da garin alkama da garin farar shinkafa, sai a hada aya da gyadar a markada a tace ruwan. Bayan nan, sai a dora kan wuta a zuba garin Plantain da alkama da farar shinkafar da muka hade a guri daya, sai kuma ku zuba garin madara da zuma, ku dama ya yi kauri sai a rika sha safe da yamma. Idan kina shirin yin yaye ne, to ki sha sati biyu kafin yaye, kuma ba kya shayarwa, za ki iya sha, sai ki tanadi rigar mama, wato Brazier mai kyau, wanda zai rika tallafawa mamanki su tsaya sosai, ki rika sakawa. Ki yi haka na tsawon sati biyu, da yardar Allah za ki samu biyan bukata. Allah ya tamake mu.

Idan kuma baki da halin siyan duka wadannan kayayyakin da na ambata to kina iya yin kunun alkama ki rika sha sau biyu a rana, amma za ki rinka sa madarar gari, wato kunun alkama da madara ke nan. Ko kuma ki sami garin hulba, ki tafasa ki rika gasa nonon da shi, sai kuma a shafa man hulban a kan nonon a ga abin mamaki sannan kuma a fasa kwan salwa a shafawa nonon, kuma a fasa guda uku a sha su danye. Insha Allahu za a dace.
Ga kuma gyaran jiki da fuska gaba daya
fata tayi laushi da shezi zaki tanadi ababe
kamar haka:
1. Man Zaitun
2. Lalle
3. Kur-kur
4. Madarar ruwa (peak)

Za ku hade wadannan kayan hadin guri guda sai ku kwaba su ku shafe jikinku da fuskar ku, za ku yi wannan hadin kafin ku shiga wanka idan ya bushe a jikin ku sai ku murje sannan sai ku shiga wanka, wannan hadin ya na sa jiki yayi kyau da sheki insha Allahu.

Za ku iyayin wannan ma wanda ake hada:
1. Kur-kur
2. Dilka
3. Zuma kwai
4. Lemon tsami

Za ku hade su a guri guda ku samu ruwan ku kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma ya fi kwabin lallen ruwa, sai ku shafe fuskanku, idan kuma har da jiki kuke so, sai ku shafa harada jiki bayan awa daya sai ku shiga wanka za k ga yadda jikinku zai goge. Das da izinin Allah. Domin wannna hadin shi ake kira Dalleliya.

 

Ga kuma wani hadin har wayan na gyanan fatan jiki zaku tanadi:
1. Lalle
2. Kwaiduwar kwai 3
3. Manja cokali 3
4. Kur-kur

Sai ku kwaba su guri guda ku shafe jikinku zuwa awa guda, sai ku yi wanka da ruwa
zalla sai ku jika duka da ruwan dumi ku shafe jikin da ita sai ku kuma yin wanka.
Allah ya taimake mu.

Idan kuma gyaran fuska ku ke so sai ku tanadi:
1. Dettol
2. Sabulun Ghana
3. Garin Zogale
4. Farar albasa.

Sai ku hade su guri guda ku kurba su a turin ku mulmula ku rinka wanke fusku za
ku ga yadda fuskarku za ta y i kyau. Wannan kuma hadin yanasa fuska ya yi haske ya yi kyau da annuri ya kuma kore kurajen fuska za’a tanadi abae kamar haka: Bawon kankana sai a runka goge guska da shi yana gyara fuska ya yi sumul.

Ga kuma wani hadin duk na gyaran fatar jiki shi ma wannan hadi ne na musamman
wanda ya ke sa fatar mace ta zamo tana tare da shauki da laushi kai har ma zaki ji
jikin ki yana wani damshi damshi wannan hadi ne da yawanci amare ka wai ake yi
wa shi. Za ku tanadi ababen kamar haka:
1. Ayaba
2. Lemon tsami
3. Tataciyar madara
4. Kwai daya

Za ku sami ayaba mai kyau ku bare k matse da hannuku, ko ku markada a
blenda ya yi laushi, sai ku zuba tataciyar madara ku fasa kwai kamar guda daya
amma farin zaku zuba sai ku matse lemoun tsami ku gauraye shi ku shafa a
jikin ku ya samu kamar tsayin awa daya, sai uk yi wanka da ruwan zafi, idan har
kuka lazinci yin haka kamar kwana uku za ku sha mamaki.